Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki qara samun wayewa akan zaman aure inshaa Allahu, na san baki wani group dan qauyancin ki yawa ne da shi Aeeshaa,"


"Hhhhhhh aiko Adda Bilqis na gode sosai,sai d safe, ki kwana lfy,ina gaida yarona,"


"Allah ya kaimu, ki shafan kan babyna,"



Sallama sukai, a cikin daren Bilqis ta turawa Haermeebraerh no Aeeshaa, cikin sa'a kuwa tana online, nan da nan tayi adding din ta.


Aeeshaa tai sallama ta gabatr da kan ta, nan mutanen dake kusa suka amsa mata daga nan ta yi shiru ta nutsu tana kallon yanda ake shan hira a gidan, tin daga nan ta fara gane halayen mutane kala2 a duniya, kowa da irin halin shi, ita a rayuwar ta banda iyalin ta bata taba intermingling da wasu mutanen ba.


Washegari kuwa da ta tashi da sassafe ta duba sai taga hira har ta kasa bi, saboda yawa,


'To su kwana suke hira ne? Bari zan tambayi Adda Bilqis naji mutanen nan akwai surutu'


('Yan group din Haermeebrah basu surutun banza malamar su komai aka ce mai amfani neπŸ˜šπŸ™„ba laifi wasu har gudu suke wai hira tayi yawa🀣🀣🀣🀣)


********************

Wasa2 Aeeshaa tayi wata biyu kenan a gida, amma Khaleefa zuwan shi uku, Hajja na kora shi,daga baya yace ba zai sake zuwa ba, dama yana zuwa ne dan Baban shi dake masa fada akan yazo ya bada hakuri banda haka sho me zai kawo shi, Hajja na nan tana qara bincike akan shi.




Wata ranar asabar da Aeeshaa ba zata taba mantawa da ita ba, da safe, ta hau IG, kawai tana duba picture, sai ta shiga inda taga hotunan Hadiza kwanaki, tana shiga tai ta kallon rubutu da hotunan flower masu kyau, tana kalaman soyayya, sai da ta duba pictures wajen guda biyar sannan tayi gamo da hoton daya birkita mata lissafi,hankalin ta ya tashi, tana maimaita kallon hoton dan tabbatar da anya gaskiya ne Hajja ta banko qofa cikin rudani itama, dauke da wasu takardu masu kama da hotuna a hannun ta................



*Annnnngamuuuu bammmmm* πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*






Page 20:






Hawaye ne me ta zuba aa idon Aeeshaa, wa take gani, yau ko ba soyayya a tsakanin su bai kamata ba abinda Khaleefa ya mata, ko ba komai mijin ta ne, sun jiyar da juna dadin auratayya, har sun samu qaruwa, akwai 'yan uwantaka a tsakanin su,




"Me ne ne? Me kk wa kuka? Mijin ki ko? Taso muje parlour, na kira kowa kafin na shigo, mu jira zuwan su,"




"Bar abincin nan kiga muje muji me Hajja ke wa kira na gaggawa haka da safen nan,"


"To Babansu amma da ka dan sha tea din nima sai na sha kasan muna da ulcer bamu san za a dade ko ba za a dade ba; zauna mu shanye kawai sai mu tafi,"



"Muyi sauri,"


A gaggauce suka shanye tea wanda ya sha kayan hadi yayi kauri, suka fito a tare, a ganya suka hadu da Hassana da Baban Sabeer da Ummeen shi, gaisawa sukai sannan suka rankaya.



Hajja da Baba General na zaune dik inda ran su ya ke ya kai qololuwar kuma qarshen baci, gaban su Baba ne ya dinga faduwa, yau me ye wannan ya faru mai tsanani, dika2 qarfe 9 ne yanzun amma tashin hankali irin wannan ya faru da zai dauke walwalar gidan gaba daya.


Umman Aeeshaa ake jira, dan zaman har da ita ya qunsa.



Sun gaida iyayen nasu inda suka amsa cikin daurewar fuska, sunq zaune suka ji tsaiwar mota, a zaton su Khadeeja ce ta iso, sai suka ji shigowar mutum kao tsaye yana sallama a tsakar gida.



Baban Sabeer ne ya leqa, dan shi ne qarami a mazan, wani matashi ya gani baqi kyakkyawa, amma rudani da tashin hankali bayyane a fuskar shi, ko gaisawa da Baban Sabeer bai ba ya hau fadin abinda ya kawo shi.



"Suna na Ammar Abdallah, ni abokin Sabeer ne na wajen aiki, yanzu haka mun kai Sabeer AKTH saboda bashi da lfy matuqa, ciwon yaje ya dawo, yau abun yayi yawa, yace a kawo shi gida, sai muka ga ya kamata mu kaishi asibiti ne in yaso sai nazo na sanar,"



Wata iriyar zufa ce ke karyo wa Baban Sabeer,

Baban Khaleefa ne ya fito

"Abubakar lfy? Meke faruwa,"

"Yaya Sabeer dina na asibiti ba lfy tin daga can Ibadan aka kawo shi nan AKTH"


"Subhanallahi, Hajja, Baba, ya kamata mu wuce asibiti Sabeer ba lfy,"



A kidime yake shiga ciki yake sanar dasu, inda suma suka tashi hankalin su a tashe suka nifi motocin su, sai AKTH.



Qarfe 10 daidai suka isa, Ammar ne ya musu jagora zuwa inda aka kwantar da shi, Aeeshaa kukan ta ne ya qaru, Yayan ta ba lfy, Ohh Allah yau wace iriyar rana suka tashi da ita ne?

'Allah ka sauqaqa mana abinda ya tinkaro mu na musiba, ya Allah mun miqa komai a hannun ka ka mana maganin dikkan abinda yake damun mu babba da qarami'





Ummeen Sabeer itama kuka take, Sabeer ne kwance sambal baya motsi sam, numfashin shi na fita kadan2 da gani da kyar yake samun shan su.



"Ina likitan daya ke kula da shi? Me aka ce yana damun shi?"



"Baba sai dai kuje kuji, muna kawo shi ogan mu ya koma ni na tsaya, so ban san meke damun shi ba"



"Muje ka nuna mana office,"


Suna shiga Dr. Ya dago daga duba wasu takardu, da alama gwaje2n da akai ma wani ne,tashi yayi tsaye ya miqa ma su Baba General hannu, da su Baban Sabeer da Khaleefa, bayan sun gaisa ya musu izinin zama a kujera, sun zauna cikin qaguwar suji meke damun dan nasu.



"Da farko ni ne Kakan Sabeer Abubakar da aka kawo maku daxu, wannan mahaifin shi wannan kuma yayan mahaifin shi, munzo dan mu san meke damun dan mu,"



"K masha Allah, dama yanzu nake son naje na sa a taho da magabatan shi, ni suna na Dr. Naseer Umar, yaron ku a bisa gwaje2n da mukai mun gano yana dauke da matsanancin ciwon malayria, thypoid, da kuma hawan jini, jinin shi ya hau sosai, wanda muke tinanin ko tsananin ciwo ne ko kuma wani damuawa yake dauke da shi, yanzu mun masa allurai, na malayria da thypoid, mun saka mashi magunguna ciki, inshaa Allah muna saka ran samun nasara na da wasu 'yan kwanaki, na hawan jini ma mun samu muna kan bashi kulawa akai, inshaa Allah za a samu nasara nan kusa,"






"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun,wai me ya kawo ma sabeer hawan jini ni Muhammad? Me zai dami yaro matashi haka?"


"Kar ku damu, ganin damuwar ku sai ya qara jefa shi wani hali, ku kula da shi sosai, muma zamuyi iya qqarin mu, inshaa Allah,"


"Dr. Mun gode sosai Allah ya saka d khair"



Sallama sukai suka fita,Umma ce zaune tana ta sharbar kuka itama, mutuwar mijin ta ce ta dawo mata sabuwa, haka aka fada mata mutuwar miji katsahan, Allah ya kare mata Sabeee din ta, shi yasa bata son saka kowa a rai, kar abinda tafi so ya tafi ya bar ta, harda Umman Sabeer din aka hadu ana taba hakuri, su Baba General na fitowa suka miqe zuwa wajen su, tare da watsa masu tambayoyi, Baba Khaleefa ne ya masu bayanin komai, kuka suka rikice suna yi, Hajja ce mace mai kamar maza ta bankada masu tsawa,


"Bana son iskanci, me kukan ku zai masa? Sauqi zai bashi? Yanda kuke jin quncin ciwon nashi ya fi ku jin azaba, dan shi a jikin shi yake, kuda ya kamata ku masa addu'ar samun sauqi zaki cika masa kunne da kuka, ya tashi yaga kuna kuka ku sake rikita shi ya zaci ciwon ajali yake ko? Dalla ku rufe mana baki ku bar mu muji da abinda ke damun mu, kai kira min wannan dan iskan yaron naka,"



"Khaleefa na can yana shiryawa yau za su shaqatawa Abuja da Becca,ga shi ya yiwa Hadiza alqawarin zai je Abuja aiki zai kai shi zai kai mata tsaraba in ya dawo, tana nan tana murna da masa fatan dawowa qalaou.


Wayar shi yaga tana walqiya, zuwa yayi ya daga a zaton shi Becca ce ko dubawa bai ba ya dauka.



"Babe gani nan zuwa ki shirya, yau sai Abuja ta san da zuwan mu, zamu raqashe, babban club zaki kai mu wanda ya amsa sunan shi, bana son qaramar harka,"




Jiri ne ya fara diban Baban Khaleefa,



"Khaleefa CLUB????"



Da gudu Khaleefa ya datse kiran, yana zaro ido waje, qirjin shi ne ya fara bugawa da qarfin tsiya, ji yake kamar ranshi zai fito dan tashin hankali da damuwa, qafafun shi da hannayen shi har zufa suke.


"Wayyoo Allah na ina cikin tashin hankali,"



Hadiza na gida, tana jiran taji motar shi ta masa Allah kiyaye daga qofar gidan su.



Shiru har 11 ta gota bai fita ba, Wuf tayi zata fita Goggo na ta kwala mata kira ko waigawa, a gidan Khaleefa ta tsaya tana maida numfashi.



Tana shiga ta gan shi a parlour yana kaiwa da kawowa, ha kalin shi a mugun tashe, ya kai ya kawo, ya kai ya kawo yana sosa kai,



'To ai zama na ma a gida hadari ne, yana iya shigowa indai Baba ne ya ci mutunci na, gwanda naje gidan a gama komai a can, in anan ne maqota da mutan unguwa suka ji ai mutunci na ya zube'



Shafo shi tayi daga sama zuwa qasa ta baya,da sauri ya juya,



"Hadiza me kk anan? Bance maki tafiya zan ba?"


"Haba angon Deejee? Naga shiru baka fita ba shi yasa,"




"Ango kuma, baki da hankali, baki san tashin hankalin danake ciki ba ne shi yasa, fita kar wani yazo ya gan ki anan,"



"Daidai kenan, kaga sai kawai a jira na haihu a daura mana aure, dan ba a aure da cikin shege,"




"Whatttt????? Ciki? Nawa? Inaaa in kin isa shege ne ni, bar nan fitaaa!!!




"In fita inje ina? Ai Baba Khaleefa ko Daddy zan ce tinda ku 'yan gayu ne, ba inda zani, sai ka san ya za kai da ni, ka auren a haka ba wanda ya san ina da cikin ka na wata biyu, ko kuma ka kyale ni na tona mana asiri, kasan dai kai ne zai zama maka sabo, ni ko a jikina, kaji na fada maka,"




"Wayyoo Allah na, yau meke faruwa ne?............





*Shiga Google ka gani dan latsin hammata kawai*


*ku yi manaji da wannan dan ban son aje ku kuna jira ne amma wallahi yau na dan gaji da typing, thank u for the love and du'as, Allah ya amsa ya saka maku kuma da alkhairi*
πŸ’…πŸΌ *KUN MAKARO* πŸ’…πŸΌ








*BY HAERMEEBRAERH*









Page 21:









"Tsakanin ki da Allah yanzu ba zaki bar gidannan ba? Kin san irin tashin hankalin da na ke ciki yanzu? Ji nake yanzu haka kmar na bace a dain gnina haka nake ji,"



"Hhhhhhh kasan me? Kana ban mamaki da kunya, kai fa namiji ne, ni mace ina murje ido na nayi abinda nake so, amma kai sai ka na wai tsoron gidan ku, zawarawa yanzu iri na daidai ne masu kame kan su a gidajen su, amma dik fita mike farauta, ba tare da an gane ba, yanzu ni in ba Goggo na ba mutan unguwar nan da ke yawan gani ina fita ina dawo d dare ba a hanya muka hadu da kai zaka rantse ina ma da aure, ai ba dole sai ka yi abu kowa ya sani ba,(ta manta cewa Allah na ko ina, mala'iku na tare da ita, akwai mai rubuta komai take) look, u have to grow up, ka manta da wani zancen me mutan gidan ku zasu ce ka shana kafin lokaci ya qure maka, shawara na baka,"



Qwan !Qwan ! Qawan !



Cikin Khaleefa ne ya bada wata iriyar qara, kashin shi ya bushe yau,bai taba ganin fushin mahaifin shi ba,ba kuma ya fata, ya kama ta ya nemi mafita, ba katangar d xai iya kamawa ya haure a gidannan da ya haure, qara knoking akai d qarfi.


"Kaje kaga ko waye ko na leqa, bana son qara, tinda na samu cikin nan,"


"Fuck u Hadiza,don't u ever talk about that darn pregnancy, or else,"


"Or else what? Or else what i said? Kana nufin wannan shaqar da ka min zata sa naji tsoron ka? Zata sa na aje dikkan qudirin dake zuciyata, Khaleefa sai na haife maka abinda ke ciki na, sai ka dauke shi da hannun ka ka rada masa k mata suna, the best thing shine yanzu yanda ka shaqe ni ka qarasa kashe ni da dan ka ko 'yar ka sai na san kai tantiri ne,"


Da qarfi ya sake matse ta, amma taurin kai irin na Hadiza ko rintse ido batai ba, sake ta yayi daidai lokacin da wayar shi ke ta tsuwwa, cikin rawar hannu ya daga, Becca ya gani a screen har da hoton ta,kuma Hadiza ma ta gani, murmushi tayi, bata ce komai ba har ya daga,


"Hello sugar, zo ka buden qofa mutan unguwar ku kar su cinye ni d kallo,"


"Whattt ar u mad? What brings u here, dn't i tell u to wait for me, how did u even knw my home? Oh my god i am so dead"



Kashe wayar yayi ya fita cike da damuwa, yana budewa ya fizgo ta ciki, fadawa tayi jikin shi ta lafe kuwa abin ta, da sauri ya rufe gidan, nan matasan unguwa suka fara tsintse, ana nuna shi, ana gulmace.


"Daga tafiyar matar shi gida har ya fara kawo arna, dan wannan ko musulma ce iyayen ta ba a gari suke ba,"


"Kai dalla kauce waya fada maka wanda iyayen su basu gari kadai ke shiga irin wannan? Na rantse da Allah wata ma uwar ta ke sai mata damammun kaya ko ta kai mata dinki wajen telan da zai fidda mata komai, kuma a gavan ta za a auna ta, ko ka manta nima tela ne?"


"Haka ne fa, Sagir, ni kai na nan abinda qanwata da babarmu keyi ai sai addu'a kun san komai ai,ko na masu wa'azi ba sa dauka, da sun ganni sai suce ga ustaz nan, gemuna kuwa yayata har ja take tana cemin dan taure tsabar sun raina sunnar Rasulullah, ai gemu ba abin zagi bane komai munin wanda ya tara shi, gemu sunnah ce, sai dai in an tara shi dan koyi da arna,yanzu dai mu bar maganar su, Allah ya shirye su, shine abinda zamu iya aikatawa, yawan zancen su zai iya sawa.muma Allah ya jarabce mu da wani sabon da ko tuba ba zamu samu damar yi ba,"


"Haka ne kuwa,"




"Sugar ina ta jiran ka baka zo ba, gashi jirgin mu ya kusan tashi, dan bana son tafiyar mota ina ta kiran ka baka dauka ba, shine na biyo ka,"


"Ba wani sugar malama,kin ko san a tashin hankalin da nake yau? Wama ya nun mki muhallina, dubi shigar ki kin san zaki zo nan, tsakani da Allah ai sai ki gyara,"


Kallon kan ta tayi daga sama har qasa, shigar black tai matsattsun kaya sosai, shape din ta ya bayyana, hatta da jan bakin data shafa baqi ne, sai bakin tabarau, da ta manna, ga cingam tana ci cakal2, ta yi bala'in kyau, gashin nan har duwais.


"What is wrong with my outpit? Kana gani dogon wando na saka,"



"Kinga ya isa, yanz ba ta wannan nake ba, iyaye na ina kyautata zaton yazu suna hanya,ban san me ya tsaida su ba ma basu iso ba,.......



Sanar da ita komai yayi, tsaki ta ja mai tsaho sannan ta kunna kan ta cikin gidan, tana tafe tana magana, sai qoqarin tsaida ta yake kar ta hadu da Hadiza,


"Haka zaka shirya ka dakko jakar ka mu wuce ba zan asarar kudaden dana kashe ba hotels uku na kama mana, in min gama da wannan mu koma wancan, sannan clubs ba su zafi dik na aje mana, so ba zaka rusamin shaqatawa ta ba, lets go, go and bring ur...........wowww...... who the fuck ar u?"



"His fucking mate, don't u knw?"



Hadiza ce kwance akan doguwar kujera, ta cire kayan ta tasss, tana kwance alamar jiran Khaleefa take ya dawo su dora daga inda suka tsaya, Khaleefa sake yayi d baki, makircin Hadiza bai da na biyu, Rebecca dariua tayi, dan tafi Hadiza karuwanci, ta san in an fara ko an gama ko ana tsaka da yi, ta kuma san makirci kala2, Khaleefa ne xai mamakin hakan, Hadiza a zaton ta za ai bala'i, dan haka a shirye take, sai ta sha mamaki.


Kau da kai Becca tayi, ta zauna, qafa daya kan daya,


"I am waiting, go inside and bring ur baga out,"



Kamar raqumi da akala,haka yaje ya dakko jakar shi, Becca ta miqe Khaleefa na gaba,Hadiza na bin su cikin tashin hankali, in khaleefa ya wuce ya barta da cikin nan ya zatai,bata san ranar dawowar ta ba, har gate ta bi su, Becca cikin dariya ta ce.



"Baiwar Allah, Hadiza ko? Kar ki mamaki, na sha ganin cheep chats din ku ke da shi, so na san ki sarai, qaramar karuwa, karuwar gida, ki koma ki saka kayan ki, kafin gyatuma ta fito ta gan ki tsirara gidan maqota, ta yanke jiki ta fadi, ni nan da kk ganni karuwanci na da ajin shi da kuma sa albarkar iyaye, ke da iyaye basu sani ba shine ya maida ke qaramar karuwa komai zaki ba zaki ya nawa ba, yanzu zani neman kudi, kuma na shaqata da mijin wata kuma kwarton ki, inna samu kudi na ikawa iyaye na ke fa? In kin samu sai dai ki boye ki kashe da dari da dari biyu,"



Wata dariya ta sake, ta shige mota, Khaleefa ya wurgawa Hadiza Keys din gidan, yace ta ce ma Goggo yayi tafiya, ya barta ta kular masu da gida,




Wasu hawayen bala'i da masifa ne suka sukar mta, ita aka ci wa mutunci haka.


Da gudu ta koma ciki ta saka kayan ta ta kira wayar Khaleefa yaqi dagawa, message ta tura masa, akan zata je gidan iyayen shi ta nuna masu cikin jikin ta.


Har ya kidime Becca ta amshe wayar, ta aika mata message, akan in taje ta tabbatar sun gano na shi ne, shi yayi gaba.



Hadiza kuka ta fashe da shi kamar zata shide, tana son Khaleefa da abinda ya mallaka, bata taba sanin akwai wata ba bayan ita,ta zaci kawai gidan karuwai yake dan leqawa ya samu wadda ta masa kawai ya gama ya dawo, ashe yana da ajajjiya kuma kwararriyar karuwa haka? A zaton ta da Aeeshaa kawai zata buga kishi,kuka ta saka sosai, ta qudir ta sai ta bata shi wajen Aeeshaa kuwa.


Rufe gidan tayi ta kai ma Goggo makulli ta shige daki, Goggo sai magana take mata akan me ya same ta tai kuka,bata amsa ba ta shige ta kwanta, ta ci gaba da kukan ta, har daki ta bita amma ta mata rashin kunya ta kore ta, fita tayi tare da yi mata addu'a, dik abinda ke damun ta Allah ya yaye mata, ya kawo mata sauqi, Allah kuma ya shirya mata ita.



***********************







Hajja tin da ta ga yanayin Muhammad bata sake tambayar shi me ya faru ba, dan ta san Khaleefa ne ya qunsa masa wani baqin cikin shima,ga shi suna asibiti so bata sake magana ba, bari har su gama jinyar Sabeer ta sa a dakko mata shi ko a ka ne, ta ci mai uwa.



Sabeer yayi sati biyu a asibiti kafin ya ji sauqi a sallame shi, Aeeshaa na nan na shayar da Ameerah wadda tayi qiba sosai, Aeeshaa ma haka, sun yi kyau kamar ka dauke ka aje gaban ka kai ta kallo.



Tinda ya samu sauqi yaqi yarda ya kula Aeeshaa, wani irin zafi yake ji a qirjin shi saboda kasancewar ta a gaban shi amm bida iko akan ta.



Aeeshaa ta kula da hakan, tin kowa na ganin zafin ciwo ne, sai ya zamana kowa ya ga ita daya yakewa hakan, to ko akwai abin da ta masa ne? Iyayen sun dauke ki tsakanin su ne sun daidai ta kn su, sun fi kusa.


Aeeshaa abun na mata ciwo sosai, ita kullum tan tinanin ya yake amma si bama ya son ganin ta, yau dai har bangaren su zata sai taji me ne ne ta masa.




Ta shirya Ameerah sai qamshi take, itama ta shirya cikin doguwar rigar lace, mai kyau, ta yafa mayafi a kafadar ta, amma ta rufe wuyan ta, ta dau wayar ya ta nufi bangaren su Sabeer, har zatayi sallama taji maganar Sabeer,



"Ammar ba zaka gane ba, fada mata bashi da amfani, tayi aure, kn tinanin ina musulmi zan samu matar wni nace mata wance ina son ki, to me kenan? Ta bar mijin ta ta dawo min kk nifi? Ai ba zai yu ba, sai na sa mata tinani, a banza, ko ta fara so na kuma da auren ta, ko muyi ta aikata sabo ni da ita, ko zan mutu ba zan taba fadan abinda ke raina ba, na riga da NA MAKARO, akan son ta, an riga ni,"




Wani irin tausayin Yayan nata ne ya makama ta, hawaye ta share, ko wace ce wannan yake so bai samu ba, har yake ciwo? Lallai she is so lucky to be loved by Yah Sabeer.



Kuka irin na yara Ameerah tai, ai kawai Aeeshaa sai ta sa kai, kamar zuwan su kenan,


Da sallama ta zauna, dan nesa da su, ta gaida Ammar, ya amsa cikin sakewa da kare mata kallo, lallai dole Sabeer ya kidime akan wannan halitta,


"Yah Sabeer ya jiki? Allah ya qara maka lfy, ya sa kaffara ne, As'alallahal azeem, rabbul arshil azeem, an yashfika Yayana,


Bari na koma, dama na shigo na ga jikin ka ne, dik da baka son yi min magana, Allah ya baka hakuri akan dikkan abinda na maka ba da sani na ba, ko da sani na,"


Tana kaiwa qarshe hawaye masu zafi suka sauka mata, rintae ido yayi, saukar hawayen ta kamar wuta aka sa masa a qirjin, Ammar fita yayi dan ya basu waje.


"Aeeshaa ki daina damun kan ki, kin sani a da mun shaqu, amma a yanzu ke matar aure ce, ko kinga ina wasa da su Bilqis ne? Dik da yayuna ne su dole akwai tsakani, su din ba muharramai na bane, su Hassana da Hussaina sune zan iya sakewa sosai, ina fatan yanzu kin gane dalili na? Ki daina dmun kan ki kinji qanwata?"



Daga kai tayi tana murmushin jin dadi, Yah Sabeer daban ne a cikin maza, ya san dokokin Allah, kuma yana kare su, ina ma haka Yah khaleefa yake, nan da nan ta tina shi, qirjin ta sai da ya buga dan faduwar gaba, tinowa tai da Hoton su da ta gani shi da Hadiza, Hadiza na nuna shi a matsayin mijin da zata aura a iG, suna cikin motar shi, ga ice cream gaban su, yana bata a baki sukai hoton.



Da sauri ta dauki Ameerah zasu fita, fuskar ta ba walwala sam



"Lafiya Ayshaa?"


"Ba komai Yah Sabeer"


Da Ammar ta hadu, ta wuce shi, Ammar shigo wa yayi yana kallon Sabeer da bacin rai,


"Wai kai yaushe zaka daina wannan halin kafiyar? Ance maka ka fada mata ko ka sassauta mata ku koma normal, ji yanda ka bata mata rai, yarinya kamila,"



"Nifa ba ni bane, kawai mun gama magana naga ta tashi kamar ta tina abu ta fita, mun gama magana mun fahimci juna, kawai naga ta hade fuska ta fita cikin sauri, na tambaya tace ba komai, me kk so nayi,"






Har Ammar zai magana Hassana ta shigo dauke da magani da abincin su, ajewa tai,ta masa sannu, Ammar kallon ta kawai yake, har sai da Sabeer ya taba shi,

"Ka fa kiyaye, yaya ta ce,"


"So? Ni ban girme ka ba? Ko dan ina abota da kai? Shin in ma sa'o'i muke da kai mace ai ba ta yi wa namiji kadan sai dai in bai balaga ba,"


"Da gaske kk yi kana son ta?"


"Kwarai d gaske in dai zata so ni, a shirye nake na aure ta, kana ganin a iri na gidan ku akwai mummuna ne ko mai mummunan hali?"



Shiru Sabeer yayi, shi dai iya sanin shi babu, amma yana zargin khaleefa bai da halin kirki, dik da ba zai nuna hannu akan wani laifin shi ba amma dai bai da halin kirki haka yake zargi,


"Gaskiya babu, a iya sani na,"



"Then zan saka kai kawai Alhaji,"

Tafawa sukai, Ammar na qara jin labarai akan Hassana.






***********************






Aeeshaa na komawa ta samu Hajja,ta kunna Data, dan ta nuna wa Hajja abinda ta gani, saboda qarin aure ba da sanin su ba babban abu ne,kumq Hadiza for that matter.



Hajja ke waya,



"K, aiko min da su gida kamar wancan, kuma ka ci gaba

Please Login or Register in order to submit comment