Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunje se Mutum ya kore su ada kafin faruwar hakan suna sana'oin su na cikin gida amman takai ta kawo Komai suka kasa babu mai saya Hatta saurayin ma da Aunty Murja take faɗa ai ya taɓa biyo Ummi amman haka Umma ta fita ba'asan mai tace masa ba bai ƙara dawowa ba ita ko sa'adah dama babu wanda ya taɓa cewa yana sonta har zuwa wannan Lokacin.

"Ki dena tunani sa'adah sabida kada Ki kamu da wani ciwon sannan Ku dinga addu'a sabida sharrin maƙiya"
Shawarwari Aunty Murja ta bata sukai sallama Sa'adah ta koma gida ɗaki ta shiga tana zama ana kawo wutar nepa Muryar Umma ce ke tashi a tsakar Gida inda take cewa.

"Babu shegiyar Munafukar matar da zata kuma shigowa gidannan a haɗu ana gulmarmu"

Sallamar Baffa daya dawo daga kasuwa da yake yana zuwa bakin asibiti yana siyar da kayan Miya ita ta katse maganganun da Umma take batai masa ko sannu da zuwa ba tahau Zuba masa ƙorafi.

"Dama inusa kai nake Jira ka shigo ka rabani da ƴaƴan muntari su fita daga harkata data ƴaƴana babu su babu mu bamu haɗa iri dasu ba se zaman waje ɗaya to tun wuri kai Musu kashedi a matsayin ka na ƙanin Uban su"

Baffa yay ƙasa da Murya cikin tsoron faɗan Umma yace.
"Haba talatu Me yasa zaki dinga ɗaga Muryarki akan waɗancan ƴaƴan hau ɗin ƴaƴan fata ki kwantar da hankalin Ki Kwanan nan ma zasu bar mana gidanmu Ki ɗan ƙara haƙuri Kuma zan ja musu Kunne"

Tana karkaɗa Ƙafa ta warci ledar hannunsa ta buɗe ta wani ƙyafe bakinta.
"Tsire fa nace ka kawo mini ba balangu ba" kafin tai wata maganar Zubaidah babbar ƴarta ta fito daga ɗakin su ta warce Ledar tayi ɗaki aguje Tun kafin takai ga zama ta soma cin naman tana dariya Zubaida kenan Ƴar madara ta raina uwar Kamar me Kuma gashi duk ƴaƴan ba wadda take so kamar zubaida bata cas bata as tana daga kwance zata ci zata sha ko waje seta kama take fitowa Kai sarki ubanka talaka sunan da matasan Unguwar ke Kiran zubaida dashi kenan sabida girman kanta.

Ga mamaki Umma batai magana ba sema ɗakin ta data shige tabar Baffa a waje wanda ya nufi ɗakin su Sa'adah dan ya kafa Musu sharaɗin Fita daga sabgar matarsa da ƴaƴanta.

Ɗaga labulan yayi Ba ko sallama ya zubawa Ummi idanu wadda ta Jingina da kanta kafin yayi gyaran Murya wanda yasa Ummi ta ɗago........

09022260850
Auta



*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *004*

Ɗago idanunta tayi ta zuba akan shi ya wani haɗe ranshi kamar bai taɓa dariya ba, Kuma kamar ba yanzu ya gama rawar Jiki a gaban Umma ba.
"Ke ina ƴar uwarki ku fito tsakar Gida ina son magana daku"
Ummi da take Jin hannunta kamar ze karye sakamakon dukan data sha a wajan Abbati a haka ta amsa wa Baffa da cewa.
"To Baffa"
Ya juya ita kuma Ummin ta Shiga uwar ɗaki wajan Sa'adah wadda take Sauya kaya zuwa wata yagulalliyar Doguwar Riga ta bacci da baya Ummi ta koma tare da cewa sa'adah Idan ta kammala Shirin Baffa yana Kiransu Gaban sa'adah ya faɗi Nan da nan tsoro ya cika ta Ita dai Allah ya bata tsoro Har addu'a take Idan tai sallah akan Allah ya rage mata wannan yawan tsoro.
A gurguje ta sa rigar ta ɗora Hijabi akai suka fito yana tsakar Gida ya kama Ƙugun sa suka tsugunna a gabansa.
"Baffa gamu"
Ko kallonsu bai yiba.
"Na ganku mana ƴaƴan banza to bari Kuji na gaji da ganin Ɓacin ran talatu In baku kama kanku ba zan tattare ku kuda Nakasashshiyar uwarku Ku bar min gidana"
Sa'ada bakin ta har yana rawa wajan Furta masa kalmar "Dan Girman Allah Baffa kai haƙuri In sha Allahu Ba zamu Kuma ba in ka kore mu ina zamu je bamu da kowa se kai Baffa"
Ya saki wata dariya tare da cewa "Ni meye naku Kuma ina ƙara jaddada Muku In kukai cikin shege babu wadda zata dangana kanta dani sabida Ina jin yadda maƙota suke faɗin yawon da kuke Fita Nidai babu ruwana"
Baƙin ciki yazo wa Ummi Wuya duk da tana jin jiki amman haka ta yunƙura zatai magana sa'adah ta Damƙe hannunta tana ƙifta mata ido da yake tsakar Gidan ya cika da hasken farin ƙwai yasa Ummin ta gane da ƙyar takai zuciyarta nesa wajan danne abin da ya taso matan.

"Baffa Kai haƙuri zamu Kiyaye"
Sa'adah ta faɗa Lokacin Almajirin Aunty murja yayi sallama yana cewa Ina ne ɗakin su sa'adah Gaban Sa'adah ya faɗi tana kallon Almajirin da babbar Kular abinci a hannunshi Ummi se Lokacin tai magana tace.
"Gamu kawo nan"
Zata amsa Baffa ya amshe tare da cewa.
"Kai yaro daga ina?"
Almajirin yace.
"Daga Gidan Aunty Murja wannan Gidan mai kallon naku"

Da sauri Umma ta fito tana cewa.
"Kagani ko Inusa? wannan Murjar ita take zuga su Kullum seta zo sun haɗu a ɗaki suna zagin mu sabida haka kaja mata Kunne ka fita ka sami Mijinta babu ita babu mu.

Ummi ta kalli Umma tana mamakin sharrinta wato idan Umma tai maka wani sharrin seka raina kanka Baffa ya kalli Almajirin yana cewa.
"Muje kamin sallama da Mijinta akan talatu senai shari'a da uban kowa agarin nan" zai fita da kular Umma ta warce tai ɗaki da ita suka bar su Sa'adah a wajan Da ƙyar Sa'adah taja Jiki tabar wajan sabida takaici tabbas zuciyarta ta kusan Bugawa da wannan Ƙuncin rayuwa da ƙasƙanci da suke fuskanta.

Almajirin Aunty murja yayi sallama Cikin Gidan Mijinta yana tsakar Gida yana Alwala Almajirin yace ana sallama Gaban Aunty Murja ya faɗi sanin halin Mijinta mafaɗaci ne sedai Kuma In ka fahimtar dashi abu yana da saurin fahimtar ka.

Ta shiga damuwa Na yadda bata gaya masa Abin da ya danganci su sa'adah ba kuma tasan ta yuwu wannan Baffan nasu ne yazo wajan Mijin nata Har almajirinta yayi mata sallama tana tsaye Ganin dai Wannan tsaiwar ba zata fusheta ba yasa ta koma falon ta tana addu'ar Allah yasa kada Baffan su Sa'adatu yay nasara akan Mijinta.

Mijin Aunty Murja ya ƙarasa wajan Baffa dake tsaye Suka gaisa kamar abin arziƙi.
"Dama na kawo maka ƙarar matarka ne"
Mijin Aunty Murja ya cika da mamaki sanin matar shi bata ma shige shigen maƙota kuma ba'a taɓa kawo masa ƙararta ba suna zaune lafiya kusan Shekara Biyar Haihuwa ce kaɗai Allah bai basu ba.

"Ina jinka wani abun tayi maka Allah ya baka haƙuri amman nayi mamaki da kace ƙarar matata ka kawo Mini"

Baffa ya ce.
"Ƙwarai matarka data ke shiga Gidana wajan Ƴammatan data gani aciki to ba ƴaƴana bane, Yara ne ƴan iska Ni kaina sun isheni ga baƙin Jini kwanaki a masallacin Juma'a har sadakar su na cigiya ba'a samu wanda ya taya ba to babu matarka babu su yau naga har abinci takai Masu ƴaƴa ne Marasa kunya sun isheni sun ishi rayuwata duk yadda zan kwatanta maka halin yarannan ba zaka fahimta ba amman dai nina san ba ƴaƴan arziƙi bane ba"

Mijin Aunty Murja yaji ransa ya ɓaci Amman bai nuna wa baffa ba yace.
"To in sha Allahu zanyi Mata magana kayi haƙuri ba zata kuma shiga ba In banda abin Murja babu mai son hurlɗa da ɗan iska"

Baffa yayi masa sallama ya tafi dama da ire iren waɗannan zantukan Baffa yabi ya ɓata su Sa'adah a layin Shiyasa kowa yake Musu kallon baibai se wanda Allah yasa yasan halin da suke ciki ne yake Musu Uziri.

Mijin Aunty Murja ya shiga gidan kallo ɗaya tai masa tasha Jinin Jikinta.

Seda suka Nutsu a falo Sannan ya dube ta.
"Mai ya haɗaki da ƴammatan can Gidan Kina kallon Baffan suma yana kuka da halin su bare ke ina ruwan ki dasu har Kike basu abinci ba tare da sanina ba to ni ina rayuwata Cikin Rufin asiri ba zaki ja min surutun layi ba"
Murmushi Aunty Murja tayi tare da tsira masa idanu har ya gama maganganun sa cikin faɗa.

"Wallahi Allah Bai gaya maka gaskiya ba Nima ada yadda ya gaya maka haka nake Musu kallo sabida Ina jin yadda ake yi dasu Inna je Kitso can Gidan se yau da Babbar ta fito tana Kukan neman agaji akan Yayanta yana Dukan ƙanwarta shine na shiga Abun babu daɗin faɗi rayuwar yaran abin tausayi ce nai kuka ba ɗan kaɗan ba dama jira nake kazo mu san abin yi"

Ya fuskanci matar tashi tiryan tiryan ta shiga gaya masa halin data ga su sa'ada aciki sanin wacece matar shi yasa bai musalta mata ba amman seya Kalleta da kulawa yace.
"To ta yaya kike ganin zamu tallafa Musu sabida Mutum mai sharri abin tsoro ne na fahimci kamar da baki suke aibata yaran"
Aunty Murja ta jinjina kai tare da cewa.
"Dama shine matsalar Amman kayi shawara se Muga wani taimako zamu basu wanda zai Riƙe su dan ina gudun kada babu tasa su fara harkar banza Tunda babu laifi yaran suna da kamun kansu daidai misali"

Ce mata yayi zeyi shawara abin da ya yanke ze sanar da ita da haka suka shiga wata Hirar ta daban.

Jikin Hajiya ne ya rikice ta dinga wasu irin surutai tana zubar da Miyau abin daya ɗaga wa su Sa'adatu hankali kenan ga maganin Hajiya ya ƙare dama wani bin Ciwon nata kamar shigar Jinnu yake amman dai Likitan ta ya shaida masu wani bin masu lalurar suna haka, ga Hajiya babu baki bare tace ga inda ke mata ciwo yadda suka ga dare haka suka ga rana da sassafe Sa'adatu taje shagon kamalu babban yayan su don ta sheda masa ga halin da Hajiya take ciki dan yazo Ko zasu kaita asibiti Abin mamaki dubu ya cillo mata yace suyi kuɗin Mota shi bashi da kuɗi ta sunkuya ta ɗauka bata koma gida ba titi taje ta kira mai napep Ita da Ummi suka tallafo Hajiya zuwa napep Ɗin Direct asibitin Murtala suka wuce da ita Koda mai napep ɗin ya sauke su bai karɓi kuɗin suba yace su barshi sukai yi masa Godiya suka kama Hajiya zuwa CIkin asibitin in da suka zauna Zaman Jiran yankar katin ganin Likita Koda layi yazo kansu Sun sami nasarar Ganin Likitan masifa yahau yi Musu akan sakacin da sukai Har Jinin Hajiyar tasu yakai Maƙurar hawa Ita dai Sa'adatu Haƙuri take bawa Likitan magani ya rubuta Musu Tare dayi Musu Gargaɗin lallai su Nemo shi su bata sabida Komai yana iya faruwa Jikin sa'adah har rawa yake bayan sun fito tana tafe tana haɗawa da Gudu zuwa pharmacy dan ta siyo maganin Da dubu ɗayan hannunta gani take In bata sai maganin ba Hajiya ƙila ma ta Mutu...........Autar manya 09022260850

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *005*

Sedai ƙafafun ta sun sage ne Lokacin data ji Zunzurutun Kuɗin maganin Yawu ta haɗiya muƙut tana share Gumin Fuskarta duk da akwai sanyin Safiya iska tana kaɗawa Amman Hakan bai hana Gumi ya wanke sa'ada ba Ta ina zasu sami Kuɗin maganin Hajiya wanda ayau jikin nata yakai maƙurar wajan rikicewa Zaman dirshan sa'adah tayi tana Rusa kuka hannunta riƙe da Katin maganin Idanunta yayi jajir Fuskarta ta kumbura sabida Kuka.

"Ƴammata Dafatan dai lafiya kike wannan kuka?"
Cewar wata mace baƙa tana tsaye a saman kan Sa'ada Ɗago idanu tayi tana kallon Matar fuskarta tai dumu dumu da hawaye da majina.
"Babarmu aka rubuto wa magani Mu Kuma bamu da Kuɗin maganin gashi Kuma Likita yace lallai se Mun bata in ba haka ba komai na iya faruwa"
Matar ta ƙarewa sa'adatu kallo a fili tace.
"Madallah da Ubangijin daya halicci wannan sura mai kyau Ina fatan Allah ya kare Miki Mutunci ki dama Ƴammata zasu yi koyi da Halin ki gaki dai babu Namijin da baze ganki ya ƙyasa ba amman Kin kare martabar ki dan Kina da surar da waje ma za'a iya fitar da mahaifiyarki amman Baki banzatar da kanki ba Muje naga Babar taku"
Sa'adatu ta share hawaye tayi gaba matar na binta a baya Suka je wajan su Ummi wadda Hajiya ke Jikinta duk Yawu ma ya ɓatawa Ummi Kayanta wanda Hajiya ke zubar dashi.

Suka gaisa da Ummi da matar.
"Allah sarki Ni zan taimaka Muku Yanzu dai Kuzo Muje Ku kai mahaifiyarku Gida ke Kuma seki Biyoni a Janguza Gidana yake Sana'ata kai yara gidan aiki to akwai Gidan da suke son Masu aiki a rijiyar zaki sena kaiki"
Godiya sukai wa matar Suka kama Hajiya suka fita suka shiga napep har Gida matar ta rakasu wadda tace Sunanta Hadiza Gudun magana yasa Sa'adah ta dakatar da Hadiza a waje Bayan sun kai Hajiya Gida Ta fito tabar Ummi tare da Hajiya.

Tafiya sukai Hadiza tana cewa sa'ada ashema basu da Nisa Har Suka tsallaka Titi wani katafaran Gida suka Shiga mai gadi ya buɗe Musu Ƙofa Yana tsokanar Hadiza A wani ƙaton falo suka zauna seda Suka jima a zaune sannan matar Gidan ta fito Sa'ada tabi matar da kallo wadda take ma sha Allah ƙatuwa da ƙyar take tafiya sabida Jikin da Allah ya bata gata baƙa Ƙirin se Uban ƙaton Hanci a ɗage take kallon su Kafin ta zauna da ƙyar aikuwa seda Kujerar ta Loɓa sabida Ƙibarta.

"Hadiza se yau kika ga damar kawo Mini mai aikin gashi jibi zan bar ƙasar?" Hadiza ta fara fadanci tana ƙasa da kai tana cewa.
"Tuba nake uwar ɗakina Ƴammatan ne sunyi wahala"
Se Lokacin Sa'ada ta gaishe da matar wadda ta zuba mata idanu na wasu Lokuta kafin ta kalli Hadiza tana ce mata "Badai wannan yarinyar kika kawon na ɗauka aiki ba?" Hadiza ta sosa kanta.
"Eh ita ce Hajiya anan ma Kusan ku take"
Dariyar yaƙe matar tayi tare da cewa "Ina Hadiza bazan iya ɗaukar wannan yarinya ba ai seta ƙwacen Mijina Gaskiya kuma fita dan Lokacin dawowar shi ya kusa"

Sa'ada ta matsa Jikin Matar ta kama ƙafafunta "Dan Allah Kimin alfarma Nai kona wata ne Mamana zan samawa Kuɗin magani"
Cikin rashin Imani irin na wasu masu haunu da shunin matar taja tsaki tana cewa "Dallah Ku fita bazan ɗauki jaraba da kuɗina ba wannan kyan naki na halaka ai sena Halaka kaina na ɗaukeki" Daga haka ta tashi tabar su a falon Hadiza ta kama Hannun Sa'a suka bar Falon Har suka Fita titi Sa'ada na kuka Hadiza tayi Matiƙar tausayawa Sa'ada sabida haka rarrashinta tayi tare da bata tabbacin zata cigita mata wani Gidan aikin In sha Allahu har naira ɗari Biyu ta bawa sa'ada wadda ta damƙe Kuɗin tayi Gida Koda taje babu yadda Hajiya take Sabida haka hankalinta ƙara tashi yayi Fiye dana farko Saka Hajiya tai a gaba tana Kuka wajan La'asar Aunty Murja ta kawo Musu abinci da Kuɗi tace Inji Mijinta Da murna sa'ada ta Ɗauki naira dubu Biyun Da Mijin Aunty Murjar ya aiko Musu dashi ta fita wajan siyo wa Hajiya magani wani ƙaton Chemist ta je a bakin Titi ta bashi katin tare da Kuɗin ya zuba mata ido kamar maye mai chemist Ɗin kenan, Bayan ya karanta.

"Baby ai kuɗin ki Dubu ashiri ne ba Biyu ba"
Sa'adatu taji wani iri da sunan daya gaya mata amman seta danne tace "I in kana bada bashi ka bani In sha Allahu wannan watan In yazo ƙarshe sena baka kuɗin"
Yayi wata ƴar iskar dariya tare da cewa.
"Haba Baby kina da kaddarar da bama sekin Biya kuɗi ba kawai Ki zo na Rungumeki na taɓa Miki Ƙirjinnan naki da yake shaƙe da dukiya sena baki maganin kyauta kefa mai kyau ce Nai mamakin ma da kuɗin magani ya gagare ki bayan Kina da Dukiya a jikinki"
Sa'ada ta maka mai wata banzar harara ta warci Katin taja tsaki tabar Chemist Ɗin tana ala wadai da halin wasu mazan, Rasa ina zata sa kanta tayi tana jin Allah kada yasa tai saɓon sa akan samarwa Hajiya lafiya Gungun wasu mata ta gani suna doso Hanyar data tsaya da alamun almajirai ne Dab da ita suka zo suna tafiya suna faɗin Irin Kuɗin sadakar da suka samu a wani Gida se maganar ta fisgi hankalinta har sun ƙulewa ganinta seta Bisu tana kiran "Bayin Allah ku tsaya" mace ɗaya ce tsaya sauran ko sukai tafiyar su sa'ada tana Ƙifta ido tana haki tace wa matar "Naji kuna maganar Gidan sadaka dan Allah ina ne nima naje Ko zan samu?" matar badan ta yarda da sa'adah na Buƙatar taimako ba sabida Yanayin Jikinta amman haka tai mata kwatancen Gidan anan kankare Sa'ada tai mata Godiya aiko da sauri ta Koma Gida suka gyara Hajiya Lokacin Magariba ta kawo kai abincin da Aunty Murja ta aiko musu dashi suka ci wanda Ummi ke sheda mata Saƙon Aunty murja na cewa kullum zata ke aiko Musu da abinci dafaffe Inji Mijinta Godiya tai Duk hankalinta yana ga zuwa Gidan sadakar Bayani taiwa Ummi lokacin data ke Mayar da Hijabinta.
"Wai kina nufin sake fita zaki Sa'adah ki huta mana tunda Hajiyar ma ta samu bacci" cewar Ummi a galabaice tace wa Ummi "Bani da Nutsuwa Ummi barni naje ina da tabbacin nasara da yardar Allah" Ummi tashi tsaye itama tayi "Gaskiya bazan bari ki fita ke ɗaya ba Yadda duniya ta lalace" Se Lokacin Maganar mai chemist Ɗinnan ta faɗowa sa'ada ta soma gayawa Ummi tana dariya Rufo ƙofar sukai kamar yadda suka saba suka fita daga Gidan Suna Jin Umma na shewa tana aibata su titi suka Nufa suka sami abin hawa aiko tiryan tiryan sa'adah ta gane kwatancen Gidan ƙato ne ga mata nan Birjik Sunbi layi suma layin suka bi Ana kiran sallar magariba layin yazo kansu Sedai abin mamaki Mai gadin seya Nuna sa'ada yace Ita zata shiga Ciki Ummi Kuma ta tsaya a waje Da ummi zatai magana ganin babu wanda akai wa haka sesu sa'adatu ta dakatar da ita ta shiga Gidan Mai gadin yay mata jagoranci har zuwa babban falon gidan daga nan yayi Mata sallama ya fita a ƙasan carpet ta zauna ta tsure tana raba ido ƙaton Mutum ne baƙi mai ƙaton Tumbi ya fito da jallabiya ajikin sa Ya zauna sa'adah tana gaishe dashi.
"Ƴammata meke tafe dake?"
Tiryan tiryan ta gaya masa matsalar ta Yayi Murmushi tare da Miƙewa tsaye "Biyoni ki amsa Allah ya bata lafiya" Jikin sa'adah na mugun rawa tabi bayan shi Ƙofar wani ɗaki ne a buɗe Kamar an jata haka ta faɗa Cikin Ɗakin aiko tana shiga Mutumin ya kashe hasken ɗakin.

"Dama ina fakewa ne da taimako ina Moruwa da Surar data Burgeni Sabida haka zo muji daɗin Juna na sallame ki kitafi abinki"
Yana faɗin hakan yayi tik haihuwar uwarshi yana shafa tumbin shi................Auta 09022260850

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*006*

Jikin sa'adah ya tsananta da rawa tunda take bata taɓa ganin Namiji a irin wannan yanayin ba Rintse ido tayi tana karanta duk addu'ar data zo bakinta Jada baya take tana Rufe idanunta da ƙarfi sanin Haramun ne kallon tsiraicin wani, Sabida duk da duhun Ɗakin hakan bai hanata ta gano shi tsirara cikin yanayin rashin tufafi ba.
Faɗuwa tai adaidai bakin Ƙofa ai Bata Jira ba aguje ta miƙe tana Gudu kamar ranta ze Fita sabida akwai tazara a tsakanin Falon da harabar Gidan Cikin Ikon Allah da tsarewar sa tana fita daga falon Taga Gate Ɗin a buɗe mai gadin nayin sallah ajiyar zuciya taja ta Zura aguje tana Gudu har takalminta ta yar Ummi data ga Gilmawar sa'adah Da gudu itama tabi bayanta Suna ƴar tsere wanda Ummi da ƙyar ta cimmata Ta kamata Se kawai suka faɗi ƙasa Tum sun Jima cikin Yanayin Hutu kafin Su Tashi zaune amman fa still Jikin sa'adatu rawa yake Ummi ta tsareta da Ido tana kallonta.
"Ummi ashe Mutumin nan ɗan iska ne tsirara haihuwar Uwarshi yayi fa sabida naje neman taimako Ummi Allah ne ya tsare Mini Mutuncina"
Ummi ta Ƙunduma uwar ashar! tana cewa.
"Lallai Allah ya rufa mai asiri bani ya kira ba dase na datse masa Cilla wallahi dama haka suke tsinannu su fake da Guzuma su harbi karsana Allah yay gaggawar Tona masa asiri"
Se kuma ta miƙe sa'adah ta bita da kallo "Ina zaki?" tace mata Ummi tace "Zuwa zanyi Ya biyamu Kuɗin Motar mu kuma na tozarta shi" Sa'adatu tabi Ummi da kallo wani bin intai abu kamar mai Ƙwanƙwamai tai ƙasa da Murya sosai "Allah ya baki haƙuri ban faɗa dan Ki jamana masifa ba Shige Mu tafi Gida" ta kama hannun Ummi wadda har suka je gida Zage zage da tsinuwa take yi ga wannan

Please Login or Register in order to submit comment