Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hanani sukuni kinji wata yaudara wai aure na zeyi Kuma bai ce yana sona ba dama ana aure haka?"
Aunty Murja da Ummi dariya sukai kafin Aunty Murja tace mata.
"Taso kar yaga Mun zaunar dashi mayi maganar a gida ai ba zamu bar wannan damar ba"
Tashi sukai tare da tattare abubuwan su A motar ma sai da saadatu tai masa taurin kai don yace ta shigo gaba tace ita a baya zata zauna sai da taga ranshi yaɗan ɓaci sannan ta shiga aikuwa har suka je Gida bai yi mata magana ba Ko kallonta bai yiba yana dire su yabar wajan faɗa Aunty Murja ta rufe ta dashi tana cewa.
"Ke bada ban soyayya ba uban me wannan Mutumin zai dake ba ajin ki bane shine zaki watsi da damar Ki, Wannan fa wani Luɗifi ne Allah yayi Miki Karki wasa da damarki saadah Ki gwada bashi dama baki san abin da Allah ya Ɓoye ba"

A bakin Ƙofar Gida suka rabu da Aunty Murja suka shiga gida ita kuma ta shiga nata Gidan.

Gidan nasu kamar babu kowa ɗaki suka buɗe suka shiga Hajiya duk ta ɓata Jikinta sabida haka basu zauna ba saida suka gyara Hajiya tas sannan Suka Shiga sabgar gabansu.

Saadah ta kasa gayawa Ummi abin da Anwar yayi mata ta dai ce mata shine ya kawo ta Jiya ya nemi ta daina aiki agidan su yau kuma yace mata auren ta zeyi yadda Ummi ta shiga Murna ne ya bawa saadatu mamaki.

Har dare saadah tana zuba ido ko Anwar zai dawo ya dubata amman shuru babu shi babu Ɗuriyar sa wasa wasa har tsayin kwanaki Uku babu Anwar Babu labarin sa suna samun abinci wajan Aunty Murja sannan Kamalu yana basu ɗari biyar Kullum Tunda ta dawo Gida Kamalun daya zo Taga yanayin sa kamar yaɗan sauko Har faɗa yay ma Abbati na dukan daya mata to wannan Rufin asirin ne yake riƙe dasu saboda har zuwa wannan kwanaki Anwar bai kuma zuwa wajanta ba Tun tana shiga ɗaki tai kuka har ma abin ya zame mata Jiki Dan wani Bin ko zama tai sai taita tunanin shi A yanzu ta yarda da soyayyar shi ta shiga zuciyarta tun ranar data ganshi taji Tana yi masa wata irin soyayya mai wuyar a fassarata.

Yau Kimanin kwanaki Biyar rabonta da Anwar Aunty Murja ce ta shigo Gidan da yamma sabida Aunty Murja bata shakkar Umma kai tsaye take Shigowa gidan.

Zama Aunty Murja tayi a kusa da Saadah taɗan kalleta kaɗan.

"Ni kam saadah kina fama da zazzaɓin dare ne?"
Saadah tai Murmushi mai ciwo tare da cewa.
"Mai kika gani wallahi lafiya ta ƙalau"
Ummi ta kalli Aunty Murja tana cewa.
"Nima na rasa me yake damun ta Kullum sai ta Ɓoye kanta taita Kuka nasha kamata tana Kuka to amman naga kamar bata son nasan damuwarta ne shiyasa nai mata shuru"

Saadah ƙasa tai da kanta bata Iya cewa komai ba saboda ita kaɗai tasan yadda take ji acikin zuciyarta game dashi.

"Saadah meke damun ki? sannan ina wanda ya ɗauko mu daga asibiti ina maganar ku ta tsaya?"
Ƙirjin saadah ne yaɗan Buga kaɗan ta ɗago ta kalli Aunty Murja sai ga hawaye na zuba daga idanunta anan Aunty Murja ta gano bakin zaren Damuwar saadah Cikin Hikima Aunty Murja tace mata.

"Kodai tun daga ranar bai Kuma zuwa ba?" saadah ta ɗaga mata kanta alamun "Ehh"

Aunty Murja tace "Shine kika rame haka lallai soyayyar taki da gaske ne Hajiya saadah an faɗa soyayya ai maganin ki yayi Ko nine haka zan Miki haba ai Nima kaina naga alamun ranshi ya ɓaci Ƙiri ƙiri Kika ƙi shiga motar shi fa Kuma Shine ya biya Miki Komai na asibiti dan da Mijina ne zai Biya zuwan shi yaje wajan likita ya biya Komai amman dan baki da Kirki agabanmu Kika dinga Nuna halin taurin kanki zuciya yayi ina ga baki da Number shi da se Ki masa waya"

Saadah ta ɗan zaro ido tana cewa.
"Ni bani da Number shi Aunty Murja ina ganin fa dama Yaudarata zeyi Ina shi ina Aure na Ɗan Gidan Alhaji Sule Kurfi ne fa naji Wadda ta kaini aiki gidan tana gaya Min To Aunty ina wannan mai Kuɗin ina ni"

Ta faɗa cikin karaya.
Murmushi Aunty Murja tayi.
"Ni kuma gaskiya banga yanayin shi yayi kama da mayaudari ba, sabida daga gani ba yaro bane Kuma yana da Nutsuwa nafi zaton Fushi yayi ko wani uzirin kin san manya fa sai an Musu uziri Ko kuma Hidimar Gida"
Murmushi Saadah tai.
"Bashi da mata gaskiya ni dai ban san mai ya hana shi zuwan ba"
Aunty murja ta zaro ido.
"Bai da mata tabb Allah yasa rabonki ne wannan ai Kika aure shi zaki Shagwaɓarki son ranki dan naga yana da shekaru kawai dai bamai Kule Kule bane amman ai yaci ace yana da ƴaƴa ma Kita addu'a kuma ki kwantar da hankalinki Kinji"
Aunty murja ta dinga kwantar mata da hankalinta.
Har ta ɗan sami Nutsuwa sallama sukai Aunty Murja ta koma Gida daran ranar Saadah labarin Anwar taita bawa Ummi wadda Ummin ta lura Anwar yayi wa ƴar uwarta Shigar sauri cikin zuciyarta.

*************

Yana tunanin anya bai shiga haƙƙin taba baya son takurawa Mutum sabida haka sai ya yanke shawarar rabuwa da ita Ko hakan zai sa ta samu Nutsuwa sabida haka koda yaje Gida ya tarar da Ɓacin ran Abba sosai na sallamar da yayiwa Alhaji jamilu haƙuri ya bawa Abba wanda ya Umarce shi akan lallai lallai ya mayar da Alhaji jamilu kan Kujerar shi.

Daga cikin Gida Duban Duniya Kande tayi wa Saadah bata ganta ba, sabida ko kaɗan bata kawo cewar Da Anwar suka Fita ba Ganin har dare yayi babu Saadah yasa ta sanar da Mama wadda mama ta kira Hadiza tace mata ba'aga Yarinyar data kawo ba Hadiza tace bata nan tana ƙauye amman In ta dawo zata Je Gidansu Yarinyar da haka Suka bar maganar sabida Hidimar Sunan Husna da suka Shiga Ita ta ɗauke hankalinsu daga Bibiyar Ina saadah tayi.
Kuɗin data bari ma Da kande ta kaiwa Husna cewa tayi ta Riƙe Kande taita Godiya Hanan kuwa data ji Saadah ta tafi har Rawar Murna tayi sabida dama bata ƙaunar yarinyar Ko kaɗan.


Anwar ya shiga sabgar gabanshi sai dai duk yadda yaso ya cire saadah a zuciyarshi abin ya faskara ko Rufe idanunshi yayi Hotonta yake gani Gaba ɗaya jiyay ya shiga damuwar rashinta.

Yau kimanin sati rabon shi da ita dafe yake da ƙirjinshi dake yi masa zafi Yana kwance a saman Doguwar Kujera a falon shi.
Khalid ya shigo cikin shirin fita.
"Lafiya na ganka a kwance ba zaka fita Office bane?"
Khalid ya faɗa masa yana zama a gefen shi.
Tashi yayi tare da yamutsa fuskar shi kaɗan.
"Bana jin daɗi yau ba zan fita ba"
Khalid yaɗan tsira masa ido.
"Innah ma tai min Complain na yadda ka sauya kwana biyu Zamu iya shearing Matsalar ka?"
Anwar ya jingine kai da Jikin Kujerar yana sakin numfashi.
Khalid ya miƙe a zuciye.
"Ka mayar dani soko Ni ko meye ina sanar dakai Anwar akwai abin da ke damunka Ko wannan yarinyar ce?"
Da sauri ya ɗago yace.
"Wa kenan?"
Khalid yayi Murmushi tare da cewa.
"Ban sani ba kafini sanin ta ay wadda na zo na tarar dakai da ita ban san dai alaƙarku ba amman nasan matsalar baze wuce daga wajan taba"
Anwar yayi Murmushi.
"Yes ita ce kasan Ni bana yaudara ban taɓa yin soyayya ba bare na yaudari ƴammata wallahi Auren ta zanyi sabuwar mai aikin gidan ce..........
A takaice ya gayawa Khalid Komai dake faruwa.
Khalid yay dariyar shaƙiyanci.
"lallai ka shiga da yawa akanta zaka fasa zuwa Office daɗi na da Gobe saurin zuwa da kana ganin kamar bani da abinyi Ko kadai Ji yadda soyayyar take Ko?"
Anwar ya harari Khalid cikin wasa tare da cewa.
"Ni dai ka bani shawara raini ne bana so gaskiya Kuma ban iya rarrashin mace ba bare na lallaɓata"
Khalid dan dariya har da ƙwarewa.
"Aifa shiyasa naga kana kwance ka dafe Ƙirji kaga tashi Muje Office daga nan sai Muje wajanta Ko?"
Tashi yayi ya shirya suka fita har suka kai Office labarin saadah yake bawa Khalid yana jaddawa Khalid yadda yake Jin tausayin ta.
Khalid ya dire Anwar a office ya wuce shima wajan la'asar suka tashi ya Kuma Biyowa suka tafi tare don Anwar bai fita da Mota ba.

A ƙofar Gidan su saadah sukai Parking Khalid ne ya fita ya sami yaro yace yaje ya kira Musu saadah acikin wancan Gidan Sanda yaron yaje saadah tana bacci Ummi ta tasheta Fuskarta duk ta Kumbura idanunta ya ƙara Girma ta sa Hijabi ta fita Ido Huɗu sukai da Khalid wanda ta ɗan shaida shi sabida haka sai ta ƙarasa wajansu ta ɗan tsaya daga Nesa batare data yi magana ba...........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*



*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*20*

Idanunta ya zubawa ido yaga yadda suka kumbura sukai wani irin Girma Fuskarta tayi jajir gaban shi ne yaɗan faɗi kaɗan cikin wani irin yanayi yake Ƙureta da kallon shi, Kafin yaja ajiyar zuciya Tunda ta fito ta Tsaya a wajan bata ƙaraso wajan suba sai Khalid ne yayi masa Inkiya wadda tasa Dole shi ɗin ne ya fito daga Mota yazo Inda take.

"Mata masu Mulki, Nayi Laifi ne?" ya faɗa yana ɗage mata Girarshi Guda ɗaya.

Hararar shi tayi tana Juya masa baya da sauri yakai hannu zai Juyo da ita sai Kuma ya fasa ta hanyar mayar da hannunshi yana yarfewa.
"Kinga ɗan juyo kalle ni kaɗan"
Ya faɗa a rarrabe.

Ƙin juyowar tayi sabida gaba ɗaya ganin shi da tayi sai take Jin wani irin yanayi kamar taita masa Kuka ko ta sami salama a zuciyarta.

"Nine ko mami ayyah ki haƙuri dan Allah" ya faɗa a hankali.

Maganar tashi ce ta kashe mata Jikinta da wani irin yanayi a tare da ita ta juyo sai dai tayi ƙasa da ƙwayar idanunta.

"Tunda ka tafi baka dawo ba sai yanzu?" ta faɗa batare da shirin maganar zata fito mata ba.
Murmushi yayi mai sauti.

"Nayi laifi ki min uziri yanzu dai nazo da Khalid zamu gaisa sai mu wuce anjima zanzo"
Daga haka ya ciri wayar shi ya Kira Khalid dake Cikin Mota wanda ya fito ya ƙaraso wajan Sun gaisa da saadah Sama sama ya koma Mota babu wata Doguwar magana a tsakanin ta da Anwar yayi mata sallama suka wuce da wani Irin Farin ciki ta shiga Gida tana bawa Ummi labari.

Anwar Gaba ɗaya ya ishi Khalid da maganar saadah a mota Suna zuwa Gida bayan sallar magariba Ya shiga wajan Malam Har ɗaki bayan sun gaisa da malam a nutse Anwar yace.

"Dama abin da yasa nazo wajan ka"

Sai yayi shuru, Innah ce ta shigo tana Dariya.
"Ka gaya masa mana kona gaya masa Yanzu Khalid yake min albishir"
Da sauri Anwar yabar ɗakin Innah ce take shaidawa Malam wanda yay hamdala ga Allah.

Lokacin da Innah ta gama gayawa malam maganar da Khalid ya gaya mata akan yarinyar da Anwar Ɗin ya ke so Malam ya kalleta.
"Allahu akbar Amman naji daɗin wannan lamari, Mu babu ruwanmu da Kuɗi tarbiya Muke wa In sha Allah zansa ai min binciken halin yarinyar In ta gari ce Alhamdulillah sai nai wa Sulaiman magana"
Da Farin ciki Innah ta Bar wajan malam taje ta sami Khalid a falo yana cin abinci ta sanar dashi yadda sukai da Malam wanda shi Kuma ya sanar da Anwar sabida Shi kam Anwar su Innah sun zama surukan shi.

Bayan sallar isha'i yayi kwalliya cikin brown shadda Ɗinki half body batare daya sanya Hula ba sai baza ƙamshi yake ya ɗauki Mota zuwa Gidansu saadah wadda itama Tun magariba datai sallah ta zauna ta tsara kwalliya Cikin wani Yellow Boyal da sukai da sallah yau saadah harda su Jambaki da kwalli Ummi sai dariya take mata bayan ta idar da sallar Isha'i yaro ya shigo yace ana sallama da Saadatu.


Lokacin Umma tana Girki a tsakar Gida ta dubi yaron tana cewa.
"Kai koma dai ka ƙara tambaya zubaida ko zainura Ko jamila dai Ko?"
Yaron yace "A,a saadatu aka ce Inji wani mai Mota" saadah naji taja mayafinta ta fito hannunta riƙe da tabarma.

Ta gaban Umma ta wuce wadda tabi saadah da kallo bakinta a sake yaushe tai sake har aka fara sallama da su saadatu.

Cikin wata salon tafiya take ƙarasawa wajanshi da ike akwai hasken wutar Nepa yana kallonta shi kuma yana Jingine a jikin Motar shi Bakin shi cike da far'a wadda bai taɓa irin taba.

"Mamina kinyi kyau ma sha Allah"
Ya faɗa sanda ta ƙaraso wajan shi rufe Fuska tayi da hannayenta tana Murmushi.
Ya sa wayarshi yana haska fuskarta.
"Yanzu wannan adon duk Ni kaɗai gaskiya sai na bada Tukwici"
Dariya tai kaɗan tana Nufar Ƙofar Gidan Aunty Murja ta shinfiɗa masa tabarmar a saman dakalin Gidan.

A hankali tazo gabanshi tace masa.
"Ka ƙaraso ka zauna"
Yabi bayanta suna tafe kamar ango da amarya.
Zama sukai a tare ta gaishe dashi daga nan shuru ne ya biyo baya sabida babu wanda ya taɓa Hira acikinsu Kowa wannan Ne karon shi na farko.

Shine ya katse shurun ta hanyar Cewa.
"Kamar yadda zan ce Miki Sunana ANWAR SULE KURFI mu ƴan katsina ne zama ya kawo Mu nan Nine babba wajan babana Nike jan ragamar kamfaninshi Bani da mata shekarata arba'in da ɗori ina fatan zaki aure ni nan bada Jimawa ba nake son ki kasance matata"
Ya faɗa yana kallonta Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta.
"To Allah ya zaɓa mana mafi alkairi"
Da sauri yace.
"Amin kina sona?"
Ta Ɓoye Fuskarta a tafin hannunta kafin ta ɗaga kanta alamun Eh.
Kamar an Fisgi maganar daga bakinta tace.
"Ina mamanku?"
Shuru yayi kamar baze magana ba can yace mata.
"Tashi na rakaki gida amaryata"
Shikenan har angama Hirar ta faɗa a ranta har bakin Ƙofar Gida ya kaita ya damƙa mata Kuɗi masu yawa a hannunta yace suyi amfani dasu sallama sukai ya tafi.


A guje zubaida ta faɗa ɗakin Umma tana Kuka tare da cewa "Wallahi Umma shine yazo wajanta Umma ina sonshi Ki taimake ni Umma Irin kalar Mijin dana ke so ne" Umma ta tallafi Haɓarta Tun ranar da Zubaida taga wannan Mutumi wanda yazo wajan sa'a bata ƙara Nutsuwa ba yau Umma taga abin da yafi ƙarfinta dan zubaida haukace mata tai da Koke Koke Da ƙyar ta samu ta rarrasheta tai Shuru Umma ta faɗa nazarin ta ina zata fara.

Cikin satin wata irin shaƙuwa ta shiga tsakanin Anwar da Sa'adah Kullum sai yazo wajanta Baffa daya ga Anwar Da zai soma tijara Tunda Anwar yazo ya gaidashi ya bashi Kuɗi shikenan Baffa yay Muƙus Su Saadah rayuwa ta sauya sabida Anwar Ya tsaya Musu a satin dayay yana zuwa daidai da Suttura sai da ya ɗaukesu ita Ummi suka je suka Zaɓo kaya masu yawa Ya kaisu wajan Ɗinki yasai Musu kayan abinci Mai yawa Haka zalika yace wa Baffa yana son ai gyaran Gidan kafin Biki Baffa Ba shiri ya amince sabida a wannan Lokacin Umma ma ta kasa gano kan baffa sabida Kuɗi.

Satin daya kama na sama aka Gyare Gidansu saadah tas har kayan ɗaki aka sauya Musu wanda Umma ma taci albarkaci dan hatta Solar mai 24 hours aka saka Musu Kuma cikin satin malam ya gama Binciken shi an tabbatar da saadah bata da wata Illah sabida haka Malam ya kira Abba wanda bai musu ba daya ji maganar yay fatan alkairi Tare da cewa malam ai shine Uban ango ba shiba sabida haka shi Gudun mawa ce tasa cikin satin da malam da wasu daga Cikin ƴan uwa suka kai Kuɗi da sa rana wata Guda Gidansu Saadah.

Hajiya tana daga kwance amman Kukan farin ciki take haka zalika Kamalu daya kasa zaune ya kasa tsaye tunda aka kawo Kuɗin Sa'adah ya ke fitar da kuɗi yana basu Suna shiga kasuwa sabida yanzu babu laifi kamalu yana Jin ƙansu sosai ba kamar da ba Anwar yace baya Buƙatar Komai daga garesu amman kamalu yace ba za'ai haka ba ko yaya gwara An kaita da abin da Sukai mata Shirye shiryen biki Kota ina Ya kankama daga gidansu Anwar Innah nata shirin Haɗa lefe ita dasu Safiya waɗanda Suke ta ɗaukin Bikin sabida rabon su da biki Tun na Ya Khalid wanda kusan shekara takwas da auren matar shice tazo haihuwa ta rasu tun daga sannan bai ƙara aure ba Ko zancen auren ma baya so shiyasa ba kowa ne ma yasan ya taɓa aure ba.

Aunty Murja ita ta tsaya wajan gyara saadah Kullum tana gidanta tana gyarata da magungunan sanyi masu Inganci wanda BINTU SPARE AND MORE +234 706 733 8694, ta ke saida wa,dan sai da suka gama dana sanyi sannan Aunty Murja ta kuma siyo mata na gyaran Ciki duk a wajan BINTU SPARE AND MORE ɗin dai dake garin kanon dabo mandawari titin na goda magungunan masu Inganci ne dan gaba ɗaya da saadah na amfani dasu saida ta sauya dan sai hanata ma Ƙebewa da Anwar Aunty Murja tayi sabida sai a samu matsala sai da yay ta naci Aunty Murja ta yarda yake zuwa da yamma.

Biki ya rage sati Guda aka kawo Lefe wanda Ya girgiza jama'ar Unguwa Umma kam ƙaramin hauka ta Dinga yi sabida ruɗewa Ƴaƴanta Kuwa babu wanda ya iya fitowa waje sabida baƙin ciki.

Saura Kwana Uku Biki saadah tai Ƙunshi tai gyaran gashi kana kallonta kaga amarya haka zalika Ummi itama tai Shirin biki ga gida ya soma haɗuwa da ƴan uwa dan danginsu na ƙauye ƴan uwan mahaifinsu sun zo Sun cika gida ana ta sabga.

Saura kwana Biyu ɗaurin aure Lokacin katin ɗaurin aure ya zaga ko ina daga cikin inda ya zaga harda kamfanin Su Anwar wanda ya sami Isa wajan Alhaji jamilu kuma a ranar ne Mama tasan da maganar auren Anwar itama ta hanyar ganin katinan ɗaurin aure a Falon Abba.

Ta shiga damuwa sosai amman bata nuna ba sai ɓige da kukan abba ya nuna mata ba ita ta haifi Anwar ba tunda har zai Nemi aure a kasa gaya mata a fili ta faɗi hakan amman a zuci ba haka bane Kukan baƙin cikin Auren ne fal aranta.
"Nima ɗan gayyane Shafa'atu su baraka ne suke Biki ke kuma naga kin gama Hidimar Suna ai bazan takuraki ba" Cewar Abba tambayar shi ta shigayi a ina Yarinyar take yace shi ina ze sani tunda Ba shiga sabgar auren yake yiba Mama a Ƙufule ta tashi ta nufi part Ɗinta tana zama a falonta Alhaji Jamilu yayanta ya shigo a haukace da katin ɗaurin auren a hannunshi.

"Shafa ta yaya Mukai sake har wannan yaron zai aure nan da kwana Biyu bamu sani ba ya zama Dole Mu lalalata wannan aure"
Mama tai Murmushin takaici.
"Yaya ina son a yau ba se gobe ba Ka nemo mana gidansu wannan yarinya Ko ta yaya a fasa auren nan da ita a ɗaura da Hanan sabida In ƴata ce agidan Ko ta yayane dai Dukiyar tamu ce Koda Mutuwa yayi Muna da kaso mai yawa saɓanin wata can taci sabida nasan in muka raba auren nashi da ita yadda Mahaifin shi ya saɓa gayya cewa zeyi a ɗaura da Hanan tunda yasan tana son Anwar ɗin tunda ga yadda lamarin yazo Na aje makamin Rai na koma na son tabbatuwar aure sabida da arziƙi a garin wasu gwara a namu garin"

Jamilu ya watsa mata kallon baki da wayo aranshi yana ayyana sonkai irin nata wato duk wannan Tashin hankalin akan ƴarta take sabida Dukiya a fili yay dariya yace.
"Wannan Duk mai sauƙi ne Turomin Kuɗi masu yawa sabida wannan aikin dole sai da GUMBAR SUSA"
Babu wani tunani mama tai masa transper Kuɗi masu kauri sukai sallama ya tafi a ranar jamilu ya Nemo Gidansu saadah sabida akwai kwatancen Gidan ajikin kati sabida a ƙofar Gida za'a taru kafin a haɗu zuwa masallacin ɗaurin auren anan ya sami kwatance da komai.

Dariya yayi yana cewa.
"Nima wannan damar tawa ce ba za'a lalata auren sabida ya auri ƴarki ba matsiyaciya kici Dukiya ke kaɗai Ni ina miki wahala karkiga Cikinmu ɗaya kowa yanzu kanshi ya sani Shafa Nima wannan dama ce gareni wadda zan kashe ANWAR da ita in yaso na kwashe Komai na cikin asusun kamfanin na gudu"
Yana faɗar haka yaja Motar shi yana dariya kai tsaye Gidansu saadah ya Nufa bai sha wahalar samun Baffa ba bayan sun gaisa babu wani Ɓoye Ɓoye Alhaji jamilu ya bayyana wa Baffa ƙudirinsa.
"Yaron nan Ya shigen hanci da Ƙudun dune ina son a matsayinka na wakilin yarinyar nan ka hanashi auren ta ranar ɗaurin aure Nasan wannan baƙin cikin zai sa shi ya haɗiyi zuciya ya Mutu saboda yana son yarinyar ance sosai sannan Kuma yana da ciwon zuciya ni kuma so nake naga bayan shi da wannan damar ga Miliyan Biyar cash inka cikan sauran zan baka Miliyan Goma kaga sha Biyar kenan"

Jikin baffa yahau rawa Yana kallon Alhaji jamilu tunda baffa yake Ko Dubu Ɗari biyar bai taɓa riƙewa tashi ta kanshi ba yau gashi ana masa tayin Miliyan sha biyar sai ya shiga Tunanin zama Miloniya inya sami waɗannan maƙudan Kuɗaɗe babu wata fargaba baffa ya amince suka ƙulla alƙwari ya amshi Kuɗinsa yayi Gida sai da ya adana Kuɗin sannan ya shiga Ɗakin Umma Lokacin ta rafka tagumi ta zubawa zubaida Ido wadda tun safe take zazzaɓi kuma duk akan damuwar wanda saadah zata aura ne wanda take masifar so ita Kuma umma tasan babu wata hanya da zata cusa ƴarta gare shi.

Zubaida na ganin baffa tabar ɗakin zama yayi yana bawa Umma labarin Yadda sukai da Jamilu amman bai nuna mata ya amshi kuɗin ba.

Buɗa Umma ta saki tana cewa.
"Inusa ka amince dan Allah Ko bai baka kuɗi ba ni ama juya auren ya koma kan Zubaida kar ƴarnan ta Mutu"
Baffa ya kalleta tare da cewa.
"To kamar yaya ba zubaida yake soba sannan mu bashi ita"
Umma tai Murmushin jin daɗi bata ɗauka zata sami Biyan buƙata farar ɗaya ba a hankali ta raɗawa baffa maganar sirri dariya sukai suka tafa kamar wasu yara.

Tofa Biki ya kankama kota ina shiri ake Daga ɓarin ango har na amarya.

Saadah tunda suka shiga Hidama bata tsayawa Cin abinci yau ɗaurin aure tunda ta tashi gabanta ke faɗuwa sai ta shiga gidan Aunty Murja tai kwanciyarta ƙarfe 11 na safe daidai tawagar ƴan ɗaurin aure ta fara sauka manyan Mutane daga sassa daban daban wasu jama'ar Abba wasu na Anwar Kafin kace me Ƙofar masallacin da za'ai ɗaurin aure ta shaƙe da ɗan adam.
Anwar da Khalid ankon shadda sukai mai kyau da tsada fara ƙar sun fito fes shaddar sai ɗaukar ido take yi Khalid ke jansu zuwa wajan ɗaurin auren wanda abokansu keta zubawa Khalid waya kowa ya hallara a wajan ba ango Anwar Kuwa wayar Aunty Murja yake Kira sabida a cikinta suke magana da saadah tunda aka shiga Hidimar Biki.
Koda ya kira saadah ta ɗauka Muryarta a dashe ya shiga tambayarta lafiya ce masa tai ba Komai ta kashe wayar sabida Ciwon da

Please Login or Register in order to submit comment