Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayaya ya gano ta bayan Ƙofar falon tana rufe.
Ta jima tana kokonton binsa tare dajin faɗuwar gaba kafin tai Shahadar Bin bayanshi wanda shi tuni har ya Koma cikin falon Taja ƙofar ta buɗe ta shiga a Lokacin taga wani farin namiji ya shiga Cikin wata Ƙofa da waya a kunnen shi tai saurin ɗauke idonta daga kallon shi tare da mayar da akalar Idanun nata zuwa ga Masifaffan Jiya wanda yake kwance a saman Doguwar Kujera Jikinshi sanye da Baƙar jallabiya.

"Ina kwana"
Ta faɗa bayan tai ƙasa da ƙwayar idanunta.
"Mai ya kawo ki nan ko yanzun ma ɓatan kai kika yi?"
Anwar ya jefa mata tambayar.
Girgiza kanta tayi.
"Tom ina jinki"
Tayi masa shuru.
"Okay ba zaki magana ba? Ko Abin break kika kawo Mini dama kin barni da kewar baƙin shayin ki"
Ta maimaita maganar a zuciyarta.

Da sauri ta Kuma girgiza kanta.
"Tab duk rashin maganata yau naga wadda ta fini yaya sunanki ma?"
A hankali ta furta.
"Sa'adatu"
Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana Lumshe ido.
"Wow Nice name Mamina!"
Ita dai shuru tayi masa.
"Yanzu ina so ki kawo Min irin wannan shayin na jiya amman ki tafi da wancan Flask ɗin sai ki zubo man aciki"
Ta maimaita hausar tashi a bakinta tabbas hausar bata ba kano bace hausar tai kama da katsinanci.
Ta tashi kamar wadda ƙwai ya fashe acikinta wurga ido take ko zata ga wayarta amman bata gani ba.

Ta gefen shi ta wuce ta fita daga falon Ba tare data bari wata maganar ta Kuma haɗa suba.

Tana Ƙoƙarin Fita daga part Ɗinshi suka ci karo da Mama wadda ita kuma lokacin ta fito ne daga wajan Abba wani irin kallo mama take aikawa da Saadah wanda kallon yasa saadatu ta saki Flask ɗin shayin dake hannunta Nan da nan Jikinta ya soma wata irin rawa kamar zata saka Ihu sabida kallon da mama take mata kallo ne mai kama da na Zargin wani abu
Murmushi mama tayi cikin ƙwarewa da barikanci.
"Saadah ko? kece mai aikin Husna da Hadiza ta kawo Mini jiya?"
Da sauri saadah tace.
"Ehh nice barka da rana"
Mama tayi Murmushi.
"Ɓatan kai kikai na ganki daga sashin Yaya?"
Zufa ce ta karyo mata da sauri tace.
"A,a Shine ya ce na dafo masa shayi dama jiya ne na dafa masa yau ma yace Mini na dafa masa"
Mama tai Ƙoƙari wajan Ɓoye mamakinta sai ta sauke ajiyar zuciya.
"Okay naga kamar Flask ɗin ma ya fashe zo Muje na baki ragowar na Babansa ki Miƙa masa Duk abin da yace Ki masa kiyi masa Kinji Shima yarona ne"
Kalmar ta bawa Saadatu mamaki ƙwarai na cewa duk abin da yace tai masa tayi masa wannan kalmar kamar akwai gyara a cikinta.
Bin bayan mama tayi zuwa Ɓangaren ɗakunanta wanda ta zaunar da Saadatu a falo, ita kuma ta shiga cikin ɗakin,Jim kaɗan ta fito tana Murmushi tare da Miƙawa Saadatu Sabon Flask.
"Karki ce masa nina baki Kice tsautsayi ne ya samu wancan ya fashe a hannunki Shine Kika zubo masa a wannan Ki tabbatar yasha Kinji Saadatu sa'ar mata duk abin da ya buƙaci yana son ci Ki zo ki faɗamin Ni zan baki Ki bashi a zummar Ke kika sarrafa masa Kinji"
Mama ta faɗa tana Murmushi Saadatu ma Murmushin tayi tare da cewa.
"To mama bari na kai masa"
Da farin ciki maɗaukaki a fuskar mama ta bi saadatu da kallo tana ayyana yau haƙona zai Cimma ruwa cikin sauƙi ashe wannan yarinyar Ni alkairi ta zame Mini.

Saadah na tafiya tana tunani haka ta Nufi sashin Anwar tana ƙoƙarin shiga taga Giftawar wani ya fito daga Falon Tana jiyo sautin Muryar Shi yana cewa.
"Khalid ka dawo mana Mu gama kallon" wanda take tunanin wanda ya fita ɗinne Khalid.
Da Murmushi a saman Fuskarshi ta same shi a zaune a ƙasan carpet sallamar tace tasa yaɗan Sauya Fuska zuwa yadda take a Kullum wato a ɗaure.
Ta aje masa Flask ɗin zata tashi yace mata.
"Ɗan bani Cup a dining mana"
A ranta tace ya cika Saka aiki sai ta Miƙe ta ɗauko masa.
"Zuba min"
Da alamun shi bai ma Lura da sauya Flask Ɗin ba.
Ta zuba mai ta miƙa masa.
Tea ɗin yana turiri ya ɗauka zai kai Cikin bakinsa Da sauri ta sanya hannu ta ture Cup Ɗin wanda ruwan zafin bai sauka a ko ina ba sai a saman Fatar hannun Anwar...........
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥

​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *16*

Ji tayi kamar Ruwan zafin a nata hannun ya sauka sabida haka sai ta saki ƴar ƙaramar ƙara tana Rintse idanunta, Da sauri takai hannunta saman Nashi hannun tana Murzawa wanda hakan Yayi daidai da sanda Fatar Hannun nashi ta Kwaye baki ɗaya wajan yayi wani irin ja naman wajan har wani farin ruwa ya tara.

Toshe bakinta tayi da hannunta tana zaro idanunta waje gaba ɗaya Jikinta rawa yake hankalinta yayi matiƙar tashi.
"Dan Allah kayi haƙuri"
Ta faɗa Muryarta tana wani irin Rawa hawaye na bin saman fuskarta.
"Ya isa tashi kije"
Ya faɗa a hankali kanshi yana sunkuye sai faman taune ƙasan laɓen shi yake da alamun zafin na ratsa shi dan dai kawai namijin duniya ne shiyasa ya daure amman in da mace ce babu abin da zai hana ta saka Ihu.
"Dan Allah kayi haƙuri"
Ta kuma faɗa tana share hawayenta gaba ɗaya tsigar Jikinta tashi take.
"Jeki abin ki"
Ya kuma faɗa, Lokacin ya ɗago idanunshi wanda yayi ja kamar zeyi aman wuta tsoro ne ya kuma kama zuciyar Saadatu.
Sai ta matsa can nesa dashi tana Leƙensa.
A hankali ya tashi yana yarfe hannun ya shiga Bedroom ɗinsa Minti Kusan Goma ya fito sanye da wasu kayan wannan Karon Farin yadi ne mai shara shara ba Hula akan shi sai Makullin Mota.
Bai ce da ita komai ba ya ratse ta gefenta ya wuce sai tashin Ƙamshin mayen turaren shi na Tom ford Oud wood daya bar mata acikin hancinta.
Shi kam fita yayi zuwa Wajan Motar shi ya shiga da hannu ɗaya yaja kanshi zuwa wani ƙaramin Clinic Domin ayi masa dress ɗin hannun nashi sabida kawai dauriya yake amman ya Ƙonu iya ƙonuwa sai dai ko kaɗan bai ga laifin ta ba, sai ma mamakin shi daya ƙaru wanda ya zurfafa acikinsa mai yasa zata kare shi ai da ta bari yasha tea ɗin da gaske ya gane An sauya Tea flask ɗin kawai ya nuna kamar bai gane bane, Yasan da Biyu ta tankwaɓe Shayin dan kar ya sha ne to mai ya ruwanta da Kare shi Mamakin abin da tai shine ya tsaya masa acikin zuciyar shi yasan komai dake faruwa acikin Gidansu kawai nuna wa yake bai san Komai ba Domin a zauna lafiya.

"You will have an hour's rest because of your body and symptoms of fever but I will give you an injection now"
Cewar Likitan bayan ya gama duba masa wajan daya ƙone ɗin.
Anwar dake zaune saman Kujerar dake facing likitan yaɗan Girgiza kanshi.
"Bani son allura Doctor dama bani jin daɗi kwanakin nan"
Ya faɗa a taƙaice.
Murmushi Likitan yayi.
"To amman dai ka ɗan kwanta ka Huta tunda kaima ka zama yaro Gudun allura kake"
Ya faɗa yana Dariya ƴar kaɗan.
Bai yarda ya kwanta a clinic ɗinba bayan ya kammala komai sukai sallama da Likitan ya fito da ƙyar yake driving Haka ya ƙaraso Gida a daddafe yayi sallar azahar aikuwa zazzaɓi yace mai salamu alaikum a nan saman carpet ya kwanta abin tausayi ya cure Jikinsa waje ɗaya yana ta rawar sanyi dan ko bedroom ɗinshi bai iya kaiwa ba so yake ya kira Khalid ma yazo ya kira mai Likitan shi amman ina ya kasa.


Da wani irin farin ciki na cin nasara Mama take waya da Hajiya turai matar yayanta Alhaji jamilu.
Daga ɓangaren Turai ta ɗauki wayar tana dariya tare da kirari wa Mama.
"Kin ci gida kinfi ƙarfin matar Gida ƙanwata ta kaina yaya ake ciki?"
Mama tana dariya tace.
"Da saura Hajiya turai yau dai Allah yayi aure da marar kwabo, Husna ta sami wata yarinya mai aiki Jiya tazo to ina tunanin dutse yayi tunbuɓe da farar fata harya shagala, Ni kuma nai amfani da damata na shigar da Ƙoƙon barata"
Hajiya turai dan dariya har ƙwarewa tayi sabida jin Yadda Ƙiri Ƙiri Shafa'atu ta mayar da sunan ɗan Mijin nata dutse.
"Ki gayan yadda zan fahimta mana shafa kin bani maganar a rabe"
Mama ta gyara zama acikin Bedroom Ɗinta ƙafa ɗaya kan ɗaya gefenta yankakkiyar tufa ce take cinta ga sanyin Ac tana ji ajikinta.
"Husna ta ba tazo ba, To shine jiyan aka samo mata ƴar budurwa saboda taimako danni Abban su yana nan Kin san ina tare dashi Lokacina bai da yawa, To gaskiya yarinyar Tana da kyau dan bama zaka ce zatai aiki ba to Nafi zaton Wancan Dutsen son yarinyar yake koma dai meye bani da masaniyya dan in ba waccan matsiyaciyar baraka ba, Baya yarda da kowa agidannan sai ko ɗanta Amman abin mamaki shine jiya Yasa yarinyar ta dafa masa shayi yau ma haka tun Jiya Hanan tazo tana Kuka tana shaida Mini Nace tai Haƙuri zan ɗauki mataki, Na kama yarinyar ta fito daga sashin sa da bakinta tace Shine yace mata ta dafa masa shayi Jiya yau ma haka, Inda na yarda da ita nasan ba Munafuka bace shine data gayan jiya ma yace ta dafa masa Kinga banga na jiyan ba na yau na gani amma ta gaya Min sabida haka zanyi amfani da ita wajan Cimma Burina zanyi amfani da ita wajan ganin bayan ANWAR"

Adaidai nan sa'adah ta juya da sauri tabar falon mama sabida tazo ne ta shaida mata ta kai masa shayin amman an samu akasi ya ƙone dan duk azatonta yaron Mama ne sai dai koda ta kawo kanta taji abin da yafi ƙarfin kanta.

Dariya Hajiya turai tayi.
"Tabbas Shafa kinyi kyan kai Duk magungunan da muka amso muka rasa yadda zamuyi dasu kinga ga hanya nan duk abin da yace yana so saiki bata takai masa a zummar ita tayi Koda wasa kada ki Kuskura Ki nuna da wata manufa a ranki Ko ita yarinyar karki Nuna mata cewar ga abin da yake zuciyarki"
Dariya mama tayi.
"Aini hadari ce sa gabanka inda kake so! ƙaryar Mutum ya gane abin da yake rai da zuciyata, Ni yanzu ta rai nake bata so ba Burina naga bayan anwar so nake ya mutu kamar yadda Bokan daya bamu maganin nan ya tabbatar mana da in yaci zai Mutu Mutuwar da babu wanda zai zargi komai to Burina kenan dan ni yanzu bata soyayyar da Hanan take masa nake yiba sabida nasan ba ze taɓa auranta ba yadda zuciyarshi Ɗinnan take kamar dutse, To na fison ya sheƙa naci kare na babu babbaka ko ma Huta da Ƙulla Tuggu nida yaya Mutuwar sa ita ce mafita kaɗai, Don inna barshi a raye tabbas zai aure Kuma zai haihu"
Dariya Turai take kafin tace.
"Tabbas in ya rasu zamu huta ne da Ƙulla masa sharri wajan Ubansa Kinga daga nan kowa ya huta, Amman Kina ganin maganin zai aiki dan Mun kai wata Shidda fa da amso shi"
Mama tai Murmushi.
"Ko jiya nai waya da shi ya tabbatar da inna sami hanya nai ta zuba masa yana ci a hankali zai ratsa Jikinshi rana ɗaya za'a wayi gari aga baya duniyar Kinga ko yanzu Tunda har yana cin abincin wannan yarinyar ai shikenan Magana ta ƙare, Haba ni ai ban taɓa ganin Dutse irin Anwar ba baya cin Komai fa namu sai ruwan zafi kaɗai zaizo Dining ya ɗiba ya zuba sugar da Lipton tea ko ya haɗa coffee yasha amman bayan su duk Irin Girki daze gani baya ci, Sai dai Baraka ta girka masa, To kinga shi ruwan zafi ta ina zan zuba magani aciki bayan fari ne tas wannan jaraba damai tai kama Har yanzu Burina yaƙi cika"
Da haka sukai ta tattauna maganganunsu na Mugun Nufi akan Anwar.

Sa'adah jikinta rawa kawai yake ɗakinsu ta faɗa ta shiga Toilet tai zaman Dirshan aciki sai Kuka take Dama har yanzu akwai Mugaye irin haka tabbas Umma Muguwace ajin farko amman tana zaton wannan matar Babar Umma ce tunda gashi nan tana ji da Kunnenta zata ga bayan Wanda take zaton ɗan Mijin tane.

Tarin tambayoyine a zuciyar sa'adah sai dai wa zata tara dasu ta yaya zata kare rayuwar Bawan Allah wanda ake farautar ranshi.
Jikinta gaba ɗaya yayi sanyi domin bata san ta  inda zata fara ba ajiyar zuciya ta saki kafin ta tari ruwa ta wanke Fuskarta ta fita waje ta zauna tare da rafka tagumi.

Har wajan bayan sallar azahar tana takure sai da baba kande ta shigo sannan ta ɗan saki Jikinta tana son sanar da Baba kande zuciyarta Kuma tana kwaɓarta akan bata san halin Baba kanden ba kar ta gaya mata maganar ta zamo mata matsala.

Sai da rana ta ɗanyi sanyi wajan ƙarfe Uku sannan ta sanya Hijabinta tabar ɗakin kai tsaye Wajan Husna taje ko tana da aiki samu tai suna bacci sai ta rufe musu Ƙofar tabar wajan...

"Saadatu sa'ar mata"
Muryar mama a bayanta.
Jikinta ne ya soma rawa Nan da nan gabanta ya yanke ya faɗi kafin tayi ta maza ta juyo tana Murmushi.
"Sannu da fitowa Hajiya"
Ta faɗa tana zubewa a ƙasa.
"Tashi mana Sa'ar mata ya kuwa sha shayin nashi Kinsan yayan nasu ne da Jin ƙyanƙyami"
Sa'adah tai murmushi kaɗan.
"Eh sai da naga ma yakai Cup ɗin bakin sa sannan na baro Wajan"
Mama ta wani zaro ido.
"Da gaske?"
Sai kuma ta gyara Nutsuwarta.
"To shikenan duk abin da yace yana so ki fara sanar dani kafin ki kai masa karki yarda na sami labarin Kin kai masa abu ba tare da sanina ba"
Da sauri ta girgiza kai tana cewa.
"In sha Allahu Hajiya"
Mama tabar wajan saadatu tabi ta da kallo.
Tsaki Hanan taja wadda take kwance saman doguwar Kujera tana hararar saadah wadda ta miƙe zuciyarta tana Ingizata akan taje taga a wani hali Bawan Allah nan yake.
Fita tayi daga falon kai tsaye ta Nufi sashin Anwar.*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*




*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *17*

Rasa yadda zatayi ta shiga cikin falon nashi tayi, ga zuciyarta ta ɗokanta da taga a cikin wani irin hali yake, Daga tai nufin buɗe ƙofar falon sai ta dawo da baya ta wani dafe ƙirjinta da hannunta wanda Ƙirjin nata ke faman Lugudan duka dum!dum!
Sau wajan uku tana yin hakan a karo na huɗu ne taji zuciyarta ba zata jure ba sai kawai ta Buɗe Ƙofar ta shiga Duk da rana ce amman sai yanayin falon ya koma kamar Duhun dare sabida Manyan labulayen dake zagaye da falon ga hasken shima a kashe yake tsaye tayi tana murza hannunta sabida bata kawo yana ciki ba tana Ƙoƙarin saka ƙafafunta don ta Juya taji sassanyar Muryarshi wadda tai kama data marar lafiya.
"Mami zonan"
Sai tayi duru duru ta rasa da wa yake wa kuma yake Kira sai ta kuma Ƙoƙarin tafiya.
"Please mami zonan ki Miƙo min wayata"
Cak ta tsaya tana jan numfashi Ita ce Mamin kenan meye dalilin shi na Ɓoye mata suna alhalin tana ƴar aiki a gidansu kuma duka duka Jiya tazo Gidan nasu Amman har ya sauya sunanta, Tunanin datai na sunan nata ko Wani suna ne gare shi mai Daraja yasa taja ƙafafunta da suka mata sanyi Ta ƙarasa Wajan shi.

Jingine yake da Jikin Bangon ɗakin ya cusa kanshi a tsakanin Cinyoyinshi Hannun shi mai Ƙunar Kuma yana dafe da Ƙuncinsa.
"Sannu a ina wayar taka take?"
Ta faɗa bayan ta zube a gabanshi.
Da hannu ya nuna mata wayar dake yashe acan ƙasa tai saurin Miƙa masa tana jada baya Fuskarta ta sauya hankalinta a matiƙar tashe.
"Nice sanadi dan Allah kayi haƙuri tsautsayi ne"
Muryarshi ce ta katseta yana magana a hankali.
"Khalid kazo ka kiramin Doctor Please"
Daga haka ya katse wayar falon ne yayi tsit.
Daga shi har Saadatu babu wanda yayi magana Minti kusan Biyar sai ga Khalid ɗin wanda ganin Mace a wajan Anwar ya bashi mamaki, amman bai nuna ba ya shiga Kiran Doctor ɗin a hankali saadatu ta tashi zata bar falon Muryarshi ta katse ta.

"Mami kin iya shara, Dan Allah share Min Bedroom ɗina ki wanke Min Toilet"
Amsa mai tayi tana tashi Khalid ya bita da kallon Mamaki bakin Khalid fall tambayoyi amman ya gaza Furtawa sabida ba lokacin tambayar bane Minti kaɗan doctor yazo allura yayi ma Anwar tare da bashi magunguna.

Khalid ya tafi raka doctor Bayan ya dawo ya tarar Anwar na bacci Sabida haka sai ya fita.
Tsananin mamakin tsaruwar Bedroom ɗin ya sanya Saadatu sakin baki dan tasha ƙauyanci kafin ta gyara masa gado ta Share ɗakin ta goge tas bayan ta gama da nan ta shiga toilet nan ma wanke shi tayi duk da babu datti tazo ta haɗe kayan shi da suka zubo ta gyara ta Kunna turaren wuta sai la'asar ta gama Sabida bata da zafin nama.

Lokacin data fito falon Baccin yake har Lokacin bai farka ba, sabida haka sai ta wuce ta fita zuwa sashin su.

Lokacin data ƙarasa Husna ta tashi daga baccin Gyara mata ɗaki tayi a gurguje ta kammala mata komai sabida akwai baƙi sosai a babban falon Gidan bayan ta gama ta shiga wajan su tana shiga ɗaki zama tayi a bakin gado tare da rafka tagumi tana ganin kanta abin tausayi Amman Mutumin nan yafi bata tausayi fiye da kanta sabida kana kallon shi kasan yana da tarin damuwa.

Tsintar kanta tayi tana mai ɗaga hannu tana hawaye tana roƙar Allah daya yaye masa damuwar shi, Bayan ta shafa ta cigaba da mamakin dama masu Kuɗi suna da damuwa har haka.

Kaɗaici kewa duk ya dami saadatu.
Haka ta zauna har akai magariba bayan ta idar da azkar sabida har Lokacin bata sami tsarki ba Fita tayi Kitchen wajan Baba kande ta taimaka mata wajan Haɗa Girkin dare baba kande se mita take na yadda yau taita sauke ɗora sabida baƙi ƴan barka.

Bayan sun kammala Saadatu tukunya ƙarama ta samu ta zuba ruwa da kayan haɗin shayi ta Ɗora tana tsaye ya tafasa ta juye ta haɗa komai cikin Dogon tray ta fita dashi zuwa ɗakin su sai da aka yi sallar Isha'i ta miƙe bayan ta watsa ruwa gami da sauya kaya ta ɗauki tray ɗin ta nufi wajan shi tana tunanin koya ci abinci Gaba ɗaya tausayi rayuwar shi take bata tana Jin ina ma zata ji labarin shi koda kaɗan ne domin daga gani akwai abubuwan dake tare dashi.

Raɓewa tayi ajikin ƙofar falon shi sabida jin sautin maganganun dake fita daga cikin falon nashi Allah ya gani ba laɓe tayi ba dalilin tsayawar tata gudu take in ta Koma da kayan shayin Wani zai iya ganinta acikin ahalin gidan shiyasa ta zaɓi ta dakata har baƙin nashi su Fito sai ta shiga takai masa.
"Anwar karfa kai wa rayuwarka Illah shekaran Jiya Likita ya gama faɗa akan ciwon ka yau gashi ka Kuma kwanciya Ni bana son wannan yawan damuwar taka tunda ba cikakkiyar lafiya gare kaba"
Muryar mace ke tashi acikin falon.
Shi kam ba'a jin abin da yake faɗa sabida ƙaramin sauti da yake amfani dashi maganganu suke waɗanda suka danganci ban haƙuri da Nasiha da matar ke masa kafin ta gama ta fito Ɗauke Numfashi Saadatu tayi Lokacin da matar ta gama maganar ta fito daga falon, Wuff saadatu ta faɗa cikin falon tana raba ido yana kwance a saman Sopa jikinsa sanye da Singlet da Dogon wando yana ganinta yaɗan sauya fuska yay kamar bai ji daɗi a yadda ta same shiba.
Ƙasa tayi da kanta bayan tai sallama ya amsa mata a taƙaice.

"Yaya jikin naka dan Allah kayi haƙuri"
Ta faɗa kanta ƙasa tana ajiye Tray ɗin hannunta.
"Ke ni wannan ban haƙurin naki ya isa tashi kije"
Jitai gwiwarta ta saki a ranta take ayyana Saadatu kin zaƙe da yawa tunda bai neme kiba meye zaki kawo kanki Gurin wanda yafi ƙarfin ki.
Tashi tayi zata tafi.
"Zoki ɗauke wannan abun"
Ya nuna tray ɗin da hannun shi mai lafiyar.
Hawaye ne ya wanke mata fuska ta sunkuya zata ɗauka yabi fuskarta da kallo.
"Kukan na menene Tell me?"
Bata yi magana ba domin in da amsar da zata biyo bakinta kuka ne mai ƙarfi ta yaya ta Ƙona shi ya kwanta Ciwo ta kawo masa shayi dan ta duba shi ya gwaleta Ji take kamar ita ce silar Komai na ciwon shi shiyasa taji hankalinta ya gaza kwanciya.
"Mami Come here"
Ya faɗa yana kallonta.
Ta fahimci me yake nufi sabida haka zuwa tayi gabanshi ta zauna.

A hankali ya kalleta.
"Ke sunan mahaifiyata gareki, Aikin me kika zo gidannan sannan ke a ina kike?"
Da nutsuwa ta ɗago taɗan kalle shi.
"Ina layin ɗorawa nazo ne ina wa Wadda ta haihu anan gidan aiki ne..........
Taɗan bashi labarin dalilin zuwanta gidan nasu.
"Ina baki kuɗin maganin mama zaki koma gida ina nufin ki koma ku cigaba da Jinyar mahaifiyarku sabida duk wata ƴa mace Mutuncin ta gidan su ko gidan Mijinta yanzu haka kowa da irin kallon da zai Miki"
Tunda ya soma mata maganar taji girman shi yana ƙara ƙaruwa cikin idanunta shine Mutum Na farko a duniya daya soma taimakon ta a maza batare daya nemi komai daga wajanta ba.
Hawaye ya wanke mata fuska.
"Nagode Allah ya jiƙan mahaifa in sun mutu in suna raye Allah yaja kwana, amman na riga na amshi Kudin wannan watan"
Ya tsareta da girman idanunshi.
"Miye kikai da kuɗin?"
Ya faɗa cikin hausarshi wadda take Nuna Ainihin harshen shi wato na katsinanci.
"Dama zan kai wa Ummi ne sabida kula da Hajiya"
Shuru yayi Kamar baze yi mata magana ba can yace mata.
"I understand you, zaki iya tafiya Ki shirya kayan ki"
Daga haka ya Mayar da kanshi ya kwantar.
Tashi tayi Jikinta duk yayi sanyi harta kai Ƙofar fita ta kuma dawowa.
"Me zan

Please Login or Register in order to submit comment