Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masallacin ma bayan sun Idar da sallah Nasiha malam yake wa Anwar tare da Nuna Mishi mahimmancin Mahaifi yana gargaɗin shi da kada ya sake ya Juyawa mahaifin shi baya duk abin da Abban sa ke masa ya Jure watarana sai labari.

Sai da sukai sallar Isha'i suka dawo Coffee kawai Anwar yasha yayi wa Innah sallama yabar Ɓangaren Har Lokacin Khalid bai dawo ba,sabida yaje taɗi ne wajan Wadda yake Burin aura.

Sai da yazo Cire kaya ya ga wannan wayar ya ajeta a bedside drawer ya ɗaura tawul a ƙugun shi ya shiga wanka.


Sa'adah Gaba ɗaya a hargitse ta ƙarasa part Ɗin Mama tana shiga suka ci karo da kande da sauri kande ta Cewa sa'adah.
"Yawwa ƴata zo muje Na nuna Miki wajan namu ki gyara kayan ki kafin Mama ta kiraki" suka rankaya zuwa sashin nasu wanda sai an fita daga sashin mama sannan za'a shiga nasun Ƙaramin ɗakine mai gado guda Biyu sai banɗaki da tv a ɗakin da Komai dai na rayuwa dama kayanta kala Biyar tazo dasu sabida haka Ninke su tayi ta ɗora a gefen gado sai a sannan taga gidan layi kansu ita da Ummi Gabanta ne ya faɗi tabbas ta yarda wayarta a sashin wannan masifaffan to tayaya zata ɗauko kiran da Kande yi mata ne yasa ta miƙe tana tafe tana tunanin yadda zata ɗauko wayarta Mama ce ta umarci kande akan ta kaiwa Husna ita Bin bayan Kande tayi zuwa ɓangaran Jerin wasu ɗakuna Guda Uku na farko suka Shiga ƙamshi da sanyin sa suka mata maraba acikin Hancinta sai da kande ta rissuna sannan ta Cewa Matashiyar da batafi sa'adah a haife ba "Hajiya ƙarama ga mai aikin da mama tace a kawo Miki Ki ganta" a lokacin sa'adah ta kalli mai jegon tana Jinjina lallai Kuɗi ƙare magana sa magana ne bada ban haka ba wannan ƴar yarinyar ma nawa take da kamar kande zata dinga Rissuna mata kande ce taɗan Daki kafaɗun sa'adah wadda tai saurin Fara gaishe da Husna.

A yatsine Husna take amsawa kafin tace.
"Kande zaki iya komawa Ke kuma yaya sunan ki?" kande ta tashi ta fita Sa'adatu kuma tace mata.
"Sunana Sa'adah"
Taɓe baki Husna tayi tana Jijjiga yaron dake kafaɗarta.
"Ba wani abun zaki mini ba kawai zaki na tayani rainon Yaron nan ne baku ma cewa nayi Ki taɓa mini shiba No Kayan kashin sa da fitsari da gyara Mini ɗakina zaki na yi sai dai Inna ga kina da tsafta zaki Dinga Goya shi In yana Kuka zamu dinga baki Dubu Hamsin a wata tunda zanyi wata Uku Ƙila kafin na Koma sabida Babanshi zai yi tafiya"

Sa'adah tayi shuru bata ce komai ba.
"Sa'adatu ko kuɗin yayi miki kaɗan ne?" Cewar Husna, Ajiyar zuciya sa'adah tayi.
"A,a Aunty Dama"
Sai tayi shuru Husna tace.
"Dama meye? faɗi mana kuma ki daina ce mini Aunty ki ce Mini Husna Ko Maman Bassam yafi ai amman Aunty Nida banfi sa'arki ba ai kamar Yayi Girma"
Murmushi Sa'adatu tayi tana yaba Kirkin Husna babu laifi tana da sauƙin kai in ta lura.
"To Maman Bassam dan Allah in babu damuwa ina son ki bani Kuɗin wannan watan dazan fara aikin sabida mahaifiyata da bata da lafiya don dalilin tama yasa nazo aikin Zan bawa ƙanwata a sai magani da abin da zasu ci"
Husna tai Murmushi tare da janyo hand bag ɗinta ta Lissafo kuɗin cas ta miƙawa Sa'adah wadda garin sauri har hannunsu yana Gugar na juna Godiya taita yiwa Husna kafin Ta sallameta akan Zuwa dare tazo ta soma aiki Ko bassam ya ɓata Pampers ɗin shi.
Tana ƙoƙarin fita daga ɗakin suka ci karo da wata Budurwa fara zata shigo Da sauri Sa'adah ta Zube tana bawa Budurwar Haƙuri wadda taja tsaki tare da Kife Sa'adah da mari tana furta.
"What kind of ignorant person? are you not looking in front of you?" Taja tsaki Fuwww tabar wajan ta nufi Cikin ɗakin hawaye mai zafi ya zubowa sa'adah daga Kuncinta Ga mari ga tsinka jaka uwa uba bata san mai ta faɗa mata da turancin ba dan ita ba iya turanci tayi ba Dan karatun nata sai a hankali da ƙyar ta samu tai candy wanda yau taje Ne Gobe taƙi zuwa.
Ta shi tayi tabar wajan Ta nufi ɓangaren su Kifewa tayi a saman gado tana hawaye.
Taji zafin marin ba ɗan kaɗan ba Tuno da Masifaffan ɗazu tayi gabanta ya faɗi da sauri ta Lumshe ido tana murmushi gaba ɗaya Zafin marin ma yabar mata Kuncin ta tuna masifaffan ɗazu wanda Hotonsa ke yawo a cikin Idanunta.*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*





*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *14*

Yana tsaye a gaban clothesset ɗinshi, ya ciro wasu  soft sleepwear masu kalar fari ya shirya kanshi Cikin su ya fesa turare ajikinshi Kan gado ya hau ya kwanta yaja blanket ya rufe rabin Jikinshi a hankali yake karanto addu'oi yana tofawa gabas da yamma Kudu da arewa, Kafin ya sanya hannu ya rage hasken ɗakin yabar iya  sleeping lamp, a hankali Yake sakin Numfashi sama sama yake jin ringing wanda ba kalar nashi bane hasali ma shi sai da ya kashe wayoyin shi kafin ya kwanta bacci dama haka tsarin al'adarshi yake sai yayi swich Off na wayoyin shi sannan yake yin bacci.

Idanunshi da suka soma sauya launin kalar su sabida baccin daya fara kamasu ya buɗe ya jefasu Kan ƴar ƙaramar wayar dake Bedside drawer kafin ya miƙa hannunshi ya ɗauko wayar ya tsirawa Number Idanu UMMINA da babban baƙi aka rubuta wayar ta katse still Wani kiran ya shigo ya ɗaga kanshi yana kallon ɗan ƙaramin Agogon dake Jikin gadon shi ta hasken sleeping lamp ɗin daya bari Ba wani dare ne yayi ba amman da yake Lokacin Sanyi ne yasa garin yayi shuru sosai Musamman Cikin Gidan da ƙafafun Ma'aikatan dake Hidimar kaiwa da kawowa tai saurin ɗaukewa.

Ƙara wayar tayi  Massage ne ya shigo.
"Sa'adah ki ɗauka mana zan baki labarin Baffa"
Abin da kawai aka rubuto Kenan Gaban shi ya faɗi ya tsirawa saƙon Idanu Yana maimaita Sunan acikin zuciyarshi wanda Girma da Ƙimar sunan baze faɗu a bakin shiba Sa'adah ya Kuma nanata wa acikin ranshi yaɗan cije laɓɓansa yana sakin Iska ta cikin su.
Kira ya kuma shigowa da sauri kamar wanda ake bawa Umarni ya ɗaga wayar ya kara a saman Kunnen shi da ɗan ƙarfi Muryar mace ke sauka cikin Dodon kunnen shi wadda bata tsaya taji maganar wanda take wayar dashi ba bare su gaisa kawai magana take sakaka babu stop.
"Sa'adah ina ta kewarki Hajiya taci abincin da kika bamu harda naman sai dai Baffa yayi Cin Mutunci sosai har yana cewa in Allah ya yarda sai Kin kwaso abin Kunya Yaya Kamalu ma yazo ya gama zage zagen sa harda cewa a nuna masa Wadda ta kawoki aikin sai rufe Ƙofa nai sabida yana ƙoƙarin dukana amman dai yau tashin hankalin sa yafi na Kullum Sa'adah ko zaki haƙura Ki dawo Gida don ita kanta Hajiya Tunda Muka Fito take hawaye har na koma Hawayen take sai da na rarrasheta gashi bata da bakin magana"
Sai da takai aya a maganar sannan tace.
"Wai ni kam kin zama kurma ne sa'adah ina ta magana kin mini banza?"
Da sauri Anwar ya kashe wayar gaba ɗaya ya juya ya kwanta sai dai baccin yaƙi zuwa idanunshi kamar farko dama shi matsalar shi kenan In yana bacci aka tashe shi to da wuya in zai koma ta sauƙi Dire ƙafafun shi yayi a ƙasa ya kunna hasken ɗakin ya janyo system ɗin shi ya ɗora saman Cinyar shi ya kunna ya shiga tura saƙonnin Office har wajan 11yana aiki da ita kafin ya kammala ya aje Fita yayi daga bedroom Ɗinshi zuwa Falo yana duba tea flask ko zai samu ruwan zafi aciki sai dai babu Kuma yadda yake Jin sanyin nan sosai in bai Using da ɗan ruwan Ɗumi acikin shiba tabbas akwai damuwa Zira slippers yayi ya fita zuwa cikin Gida a dining ya zauna yana dudduba Tea flask ko zai samu duk wanda ya duba wayam yaja tsaki kaɗan Hanan ce ta fito daga Bedroom Ɗinta sanye Cikin Riga da wando na Bacci Cotton sai ɗan ƙaramin Hijab data ɗoro akai yunwa take Ji kamar taci Babu tana Isa gaban  dining ta sauke ajiyar zuciya Ganin Ya Anwar zaune ya sunkuyar da kanshi kamar mai Tunanin wani abu ayyanawa tai dama ace sunyi aure suna zaune acikin Gidan sune.

"Yaya"
Ta faɗa.
Da sauri ya ɗago idanunshi da har Lokacin kalar su bata dawo daidai ba yaɗan Haɗe ranshi.
"Baki iya sallama ba?"
Taɗan tura baki kaɗan kamar wata Ƴar Baby.
"Kayi haƙuri bazan kuma ba"
Ƙoƙarin Tashi yake da sauri ta dafe hannunshi ta hanyar ɗora nata akai wani matsiyacin kallo daya watsa mata ne yasa tai saurin sauke nata hannun.
"Ammmm yaya dama dama" ta faɗa tana Ƙifta ido.
Ya saki Huci mai zafi kafin ya silale ya zauna a saman kujerar daining ɗin.
"Please bring me a cup of tea now" a hankali.
Shi kanshi bai san maganar ta fito daga bakin shiba da sauri ta bar wajan tana shiga kitchen ta ɗauraye tukunya a cikin sink ta zuba ruwa cikin tukunyar tare da sugar wanda bata san adadin yawan shiba ta Kunna cookergas Minti Biyu ya tafaso ta Juyo masa a Cup ta Fito ko Tea spoon bata saka aciki ba gaba ɗaya jikinta ya ɗaukanta da ta burgeshi Yana turiri ya amsa yana Ƙoƙarin kaiwa cikin bakin shi sabida yafi son yaji shayi na Ƙona mai baki yana ratsa masa Jikinshi Kurɓa ɗaya ya furzar dashi yana kallonta ta kwa zuba masa ido kamar zata haɗiye Shi.
"Ke wace irin Sakarai ce kamar ki baki Iya dafa tea ba?" ya faɗa yana ɗan zaro mata idanunshi kaɗan Ƙwalƙwal Idanunta yayi gaba ɗaya Jikinta yayi sanyi Faɗa ya dinga yi mata hawaye yana bin Kuncinta dama shi abin faɗa baya yi masa wahala musamman gareta sabida tace tana son shi a yadda ta Lura kenan.

Adaidai nan Sa'adah ta fito daga Ɗakin Husna wadda ta gama wanke kayan da Bassam ya ɓata na kashi tana tafe tana yarfe hannunta gab da zatabar falon taji sautin maganganu kamar na namiji tana ɗaga kanta Kuwa idanunsu suka haɗu dana Juna ai tattare Skirt ɗinta tayi zata sa Gudu tana cewa Yana aikin nashi kenan masifa.
"Ke zonan Ke Kuma tashi kibar Min Gurinnan kafin nai Ball dake"
Da Gudu Hanan ta miƙe tana Kuka tana share hawaye sai dai haɗa idanun da sukai da Sa'adah ne yasa Hawayen nata ƙafewa tana Bin sa'adah da kallo wadda ganin Hanan yasa gabanta ya faɗi wannan Ta ɗazun ce wadda ta mareta har tai mata turanci Tsaki Hanan taja Cike da Kishin Sa'adah wadda tun kallonta da ita na farko taji tana Kishin ta sabida kyan ta yayi yawa.

Kafin ta hankaɗeta da sauri Sa'adah ta takure a bango tana raba idanunta Yi yayi kamar bai ga abin da Hanan ɗin tayi ba.
"I told you to come here, ko zan cinye kine kin wani tsare ni da ido....." sai Kuma yayi shuru Lokacin Hanan takai ga Bedroom ɗinta.
Iya ko zan cinyeki ne ta gane da kin tsare ni da ido amman sauran bata fahimta ba.
A hankali take jan ƙafafunta zuwa wajan shi ga falon babu kowa.

Tana zuwa gaban shi Kwarjinin shi ya cika mata Ido zubewa tai jagwab ta zauna agaban shi tana sauke Numfashi.

"Kin iya dafa shayi"
Bai jira mai zata ce masa ba.
"Ki dafa ki kawo Min wannan ɓangaren da kika shigo ɗazu"
Daga hakan yabar falon da sauri.
Sabida yana matiƙar Buƙatar shayin Kuma yasan yanzu Inna tayi bacci bare yace ta dafa masa shi kam bai iya komai ba bare ya dafa da kanshi shiyasa ya zaɓi sabuwar mai aikin da bai san wani aikin take taka maimai agidan ba data dafa masa ganin da yayi kamar zatai tsafta.

Sa'adah tai tagumi Cike da tsoro Hajiya tana gargaɗinsu Da kada su sake su Keɓanta da Namijin daba muharramin suba a duk inda suke su kare Mutuncin su.

Tun kafin Allah ya jarabci Hajiya da lalura take gaya Musu hakan Gaba ɗaya Gidan sunyi bacci kawai sai ta kama hanya tayi ɓangarensa dan bata da Ƙima.
To kuma in bata kai masa ba hakan zai zama laifi dan daga gani Yana da muhimmanci acikin Gidan.
Ajiyar zuciya ta saki domin ko hanyar Kitchen ɗin ma bata sani ba.

Sai kawai ta tashi ta Nufi ɓangaren su alwala tayi tai kwanciyarta sai dai Ƙirjinta cike yake da tsoron abin da zaije ya dawo.
"Sa'adatu ki tashi kici abinci naga kin ɓata Lokaci wajan Hajiya Husna"
Da ƙaramin sauti tace.
"Baba na ƙoshi"
Tsaki taɗan ja wanda yasa Baba kande tace mata.
"Sai haƙuri Sa'adatu amman kika kwantar dakai zaki ci arziƙi"
Sai ta tashi zaune.
"Baba kande bama wannan ba, Wanine yace wai na dafa masa shayi nakai masa ɓangaren shi Ni bamma sanshi bafa Kuma dare yayi kina kallon ɓangaren babu kowa"
Baba kande tace.
"Waye kar dai Alhaji Ƙarami ne?"
Taɓe baki Sa'adah tayi.
"Wani dai mai faɗan tsiya mai ido kamar na Mayu"
Dariya Baba kande tayi.
"Ki rufawa kanki asiri Ki kai shayin nan Alhaji ƙarami ne lallai Yarinya kinzo Gidannan da ƙafar dama Tunda nake ko ruwa bai taɓa cewa na bashi ba Sabida haka maza tashi Muje na Rakaki Kitchen Ki dafa ki miƙa masa Ina wa Muhammad Anwar kyakykyawan zato ba zaki same shi daga cikin lalatattun maza ba In sha Allah yadda kika kai lafiya haka zaki dawo"
Badan taso ba sai dan bata son yiwa baba kande Musu ne.
Taja hijabi ta ɗora saman kayanta tana data sanin Gayawa baba kande maganar suka tafi zuwa babban Kitchen Ɗin Gidan wanda faɗin tsaruwar shima ɓata bakine Wasu Irin sinadaren haɗin shayine daga saudi ake kawosu baba kande ta nuna mata tana tsaye A kan sa'adah ta kammala haɗa shayin wanda dan tsananin Ƙamshi da kayan haɗi har kauri yake da mazarƙwaila aka dafa da zuma bada suga ba ta Juye a wani Dogon Kofi mai ƙananun Ƴaƴa ta ɗora a tray Baba kande ta Nuna mata Part Ɗin Anwar ta Nufi kai masa ciki sai dai Duk Notikan Jikinta sun saki sabida fargaba.........*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI  MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥


​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*15*

Jikinta a matiƙar sanyaye wanda yayi kama da wanda aka tsoma ta acikin ƙanƙara haka ta buɗe Ƙofar falon nashi ta shiga, wawiyar ajiyar zuciya ta saki Lokacin data ƙarasa shiga Cikin Falon Sanyi ne da ƙamshi suka cika ta, Kamar mai tsoron wani abun haka tai saurin aje tray ɗin hannunta tana Ƙoƙarin Juyawa domin ta koma sabida bata Ji alamun da Mutum cikin falon ba sai kawai taji sautin Muryar shi ta fita a hankali.
"Kawo mini shi nan matsoraciya kamar wani zai kamaki"
Gabanta ne yayi wata irin faɗuwa harda dafe Ƙirji tayi kafin ta ɗan zaro idanunta kaɗan wanda hakan yayi matiƙar yi mata kyau.
Ɗauka tayi ta ƙarasa gabanshi yana zaune ya miƙe ƙafafun shi ya ɗora ƙafar shi ɗaya akan ɗaya.
Ta ajiye a gaban shi.
"Zuba min ki miƙo min"
Ya faɗa a dake.
Sosa idanunta tayi tana hamma! kafin ta ɗauki Cup ta tsiyaya masa aciki Ta miƙa masa Tsirawa hannun shi ido tayi kaɗan, Abin ya birgeta ko ina gashi ne kwance hatta a saman yatsun shi.
Tana miƙa masa ta Miƙe zata tafi.
"Zauna har na gama sai ki tafi da kayan" ya faɗa yana Kurbar shayin batare daya tsaya firfita shi ba.
Wani irin haɗaɗɗan Ƙamshi da daɗi mai ratsa zuciya ne ya shiga Kwanyar shi ya Lumshe ido yana kurɓar shayin cike da mamaki dama ance yawanci ƴaƴan da suka taso Cikin rashin wadata sunfi Ƙoƙarin iya komai saɓanin ƴaƴan da iyayensu keda hannu da shuni waɗanda Suna kwance ake Musu komai

Jingina kanta tayi da Jikin Kujera duk jinta take a takure ita gaskiya hakan ya zama takura a gareta sai dai bata da damar yi masa Musu Ya ɗauki wajan Minti Goma sha biyar kafin ya sallameta tana tafe tana haɗa hanya tsoro fall zuciyarta sabida yadda Ko ina yayi tsit a gidan.

Tana aje kayan a kitchen ta Rufo Ƙofar part ɗin Maman ta nufi nasu Koda taje Baba kande tayi bacci Ƙwan ɗakin ta kashe ta kwanta ba jimawa bacci ya ɗebe ta cike da Wani irin yanayi a tare da ita.

Anwar sai wajan 2 na dare bayan ya kammala nafilolin shi ya shiga Bedroom ya kwanta bacci washe gari ranar Sunday babu Office sabida gaba ɗaya ma'aikatan Kurfi Tex basa fita ranar Sunday Hutu suke Baccin shi yasha dan sai wajan 12 ya farka shima Khalid ne ya shigo ya tashe shi daga baccin suka fito falo suna kallon Ball.

Baccin Saadatu rabi da rabine a ranar sabida rashin sabo ta saba kwanciyar ƙasan tabarma yau gata a lafiyayyen gadon daya sha katifa wai a haka ma gadon mai aikine ina ga kuma masu Gidan Da asubahi baba Kande ta tayar da saadatu akan ta tashi tayi sallah Miƙewa tayi sabida bata sallah tana fashi wanka tayi da ruwan ɗumi ta gyara Jikinta sosai Ta koma tayi kwanciyarta wajan ƙarfe Goma suka tashi daga ita har Baba kande Bayan sun gaisa Baba kande ta fita Ɓangaren su Mama ita kuma ta zauna gyara Musu ɗakin da wanke Musu bayin su da yake bata da saurin aiki sai wajan 11 ta kammala sannan ta fita ɓangaren maman ita ma tuno Wannan Budurwar ta jiya taji gabanta na faɗuwa addu'ar Neman tsari daga sharrin abin tsoro ta shiga yi taɗan sami Nutsuwa kaɗan kai tsaye ɗakin Husna ta Shiga suna zaune su Huɗu acikin ɗakin Husna tana bawa Bassam Nono sauran ukun kuma ko wacce ta miƙe ƙafa da waya a hannunta a ɗarare Saadatu ta ƙarasa gaban Husna ta rissuna har ƙasa Muryarta a sanyaye tace.
"Maman Bassam ina kwana?"
Da murmushi akan saman Fuskar Husna tace mata.
"Lafiya lau nanny Bassam, yaya kwanan baƙon waje amman Kin ɗan makara Bassam yayi Kashi da tumbuɗi Suna toilet suna jiranki"
Lokacin ɗaya daga cikin Ƴammatan taɗan Juyo tana kallon Saadah kafin tace.
"Ke baki ga mutane bane a wajan Husna wannan wace Irin mai aiki kika samu marar tarbiya ni bamma ga amfaninta ba tunda muna da washing machine a gidannan wankin me zata yi?"
Husna ta ɗan haɗe ranta.
"Ni bana buƙatar Inji ya wanke Mini kayan yaro na sabida Masu kyau da tsada ne Zasu lalace wankin hannun Mutum yafi, Ke kuma Saadah baki ga mutane bane karki yarda a ƙara kawo Min ƙarar rashin gaisuwar Ki dan Jiya Aunty Hanan tace kin ture ta sanda zaki fita daga nan da yamma dan Allah Ki lura"
Saadatu tai ƙasa da kanta.
Tare da cewa.
"In sha Allahu, Suyi haƙuri hakan baze ƙara faruwa ba"
Sannan ta juya ta na gaishe dasu.
"Wow Saadatu ko ma sha Allah dama nice da kyanki Gaskiya kina da kyau" Cewar ɗaya daga cikin ƴammatan wannan ta jiyan ce ta aje wayar hannunta tana kallon wadda ke yabon kyan saadah tsaki taja tare da cewa.
"Kedai anyi banza ina wani kyau anan aba kamar Nunar rana dallah tashi ki bani waje" da sauri Budurwar ta fita tana Gunguni Ita dai saadah tashi tayi tabar wajan ta shiga Toilet Ɗin sai da takai zuciyarta nesa wajan wanke kayan sabida harda panties ɗin Husna da suka ɗan ɓaci da Jini Aikuwa tana wankin tana tara Miyau acikin bakinta zuciyarta na wani Irin tashi haka ta kammala da ƙyar ta wanke toilet ɗin tass sannan ta fito Husna ta shiga wanka ita kuma ta soma gyara ɗakin Bassam ne ya ke Kuka sosai Husna ce ta fito Jikinta duk Kunfa tana wa Saadatu faɗan tabar mata yaro yana kuka "To naji Kince karna taɓa shine shiyasa ban yi Gigin taɓa shi ba amman Kiyi haƙuri" Ta ɗauki yaron tana Jijjigashi, Husna kuma ta koma wankan sai da ta fito sannan ta miƙa mata shi ta fita Kitchen ta shiga wajan Baba kande ta taimaka mata wajan kammala girkin tana Miƙa kayan zuwa dining.

Bayan sun kammala komai suka Ɗibi nasu zuwa ɓangarensu Suna Karyawa baba kande tana Yi mata nasihar kwantar da kai tare da yin biyayya ga ƴaƴan gidan baba kande ta ƙara da cewa.
"Duk ƴaƴan mama basu da matsala sosai su kawai Ka basu Girmansu in kana binsu zaka ji daɗin zama dasu, Mai bala'in matsala Hanan Ita ce babba a ƴaƴan Mama kuma ba ƴar Gidannan bace a golace Fiƙe ake gaya Miki kafi ƙaya tsini, Nima kaina bata ganin ƙimata amman Husna Khairat Ihsan Gaskiya ba sosai Suke da damuwa ba sabida haka Ki kula sosai Saadatu naga Kina da hankali"
Saadatu tai wa baba godiya anan suka cigaba da zama Baba kande ta kawo Musu ƙarshen zaman nasu ta hanyar kamo Musu tashar Arewa 24 Suna kalla Ga kuma sauran Ƙwai da farfesun da suka rage nan Saadah tana kallon Ragowar abin karin Hajiya da ummi suka Faɗo mata wanda Tun Jiya ta shiga damuwar rasa wayarta bare ta Kira Ummi taji yaya suka kwana ƙwalla ce ta taru a idanun saadah tashi tayi ta fita kai tsaye ɓangaren Sa ta nufa tana Tunanin Ko zata ga wayar tata Jin sautin muryoyi na tashi daga cikin falon nashi yasa ta Juya zata Koma wanda adaidai nan taji sautin Muryar shi.
"Wacece anan wajan?"
Tai tsuru Har zufa na karyo mata.
"Zonan ina zaki tafi bayan na kamaki"
Gabanta yana faɗuwa ta Juyo shi kuma lokacin har ya buɗe Ƙofar falon ya koma to

Please Login or Register in order to submit comment