Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mutumin ga tarin takaicin ɓatar da ɗari huɗun da sukai a banza babu Biyan buƙata.

Sallah Ummi tayi Ita kuma sa'ada ta zauna tana Gogewa Hajiya Jikinta sabida zazzaɓin daya rufe mata Jikinta.
Ummi ta idar tazo Kusa da Sa'adah wadda ta zurfafa acikin Tunanin Neman kuɗin maganin Hajiya.

"Ummi kin san me?" cewar sa'adah Ummi tace "Ina ko zan san me Nida ba akuya ba" saadatu tai murmushi halin ummi se ita "Kawai Hajiya ce take bani tausayi" Ummi tace "Bake kaɗai ba naki ne yafi nawa Fitowa Fili amman a zuci kamar na fiki dan na gama yanke shawarar bada Jikina dan Hajiya ta sami lafiya tunda mazan sun zama Mayu" Buge mata baki sa'adah tayi "Karki Kuskura Ummi wannan shine abu mafi Muni da zaki sema Hajiya ta Mutu Kuma kin riga kin yada Ƙimarki Mu cigaba da addu'a dama duniya kurkukun Mumini ce"

Ummi hawaye ta soma tana cewa.
"Ina tuna yadda Hajiya kafin ta soma ciwo take yi mana hidima Ki duba koda sallah Mune abin kallo tunda mahaifinmu ya rasu Hajiya bata taɓa bari Munyi Kukan rashin saba tana cewa Mu amana ne a wajanta bata da kowa se Mu amman yau Mun kasa sai mata maganin Dubu ashirin" Sa'adah tai Murmushi mai ciwo.
"Haka Allah yaso Haka Allah yaga dama Wannan ma dan ya gwada imanin mune amman Nina fiki damuwa Ummi Ina kukan gazawa ta ga ciwon hajiya to ya zamuyi Allah ya bawa Hajiya ƴaƴa maza amman dasu gwara babu Ki duba fa kamar ba ita ta haife suba"
Ummi tace.
"Ni share babin suma nake yi wallahi Gobe ma fita zamu yi da wuri Muga abin da Allah ze mana dan Allah kima daina batun waɗancan marasa amfanin"

Daga tsakar Gida suka Jiyo Muryar Umma da Jamila Umma tana tuhumar Jamila daga Ina take tun safe ta fita bata dawo ba se yanzu Jamilar ce take cewa Umma.
"Fita nai don na ciko Cikina da abinci Na gaji da zaman yunwa ko anyi Girkin ma bama Ƙoshi Ke Umman nan kowace mace tana sana'a amman ban da ke Duk maƙotan ma Kinbi Kin ɓata dasu sabida faɗan ki In ke kin Jure Yunwa nikam bazan iya ba"

Umma ta ɗaga Murya.
"Jamila daga gidan uban wa kike Ba tambayata yunwarki ba Tambayarki nake daga ina kike tun safe kin saka ƙafa Kinbar Gidannan se yanzu zaki shigo mini Gida so Kike ki jamana abin faɗa maƙiya su mana dariya"

"Kai umma kai umma abin fa sirrine Kinga dai ga wannan nasan baki ci abinci ba Ƙila tunda Baffa bai Shigo ba amman karki sake ki bawa cima zaunan can waɗanda basa cas basa as niko kasuwancin kai da kai na soma mai tarin riba"

Umma ta soma Murmushi kasancewar ta mace mai bala'in son abin duniyar tsiya da kwaayi.
"To jamila duk dai abin da zaki kada ki kuma kaiwa dare"
Zubaida ce ta fito a fusace tana Cewa jamila "Da wa kike naji kina maganar cima zaune to in ma damu kike Mu dai Alhamdulillahi Tunda bama bin maza" Umma seta hau salati tana tafa hannu "Zubaida sharri zaki wa jamila maƙota suji To Ta Allah ba taki ba Kasuwanci ta fara kema In zaki cire girman kai ki fita ki nemi kuɗi to dan na gaji Kuba aure ba kuba sana'a ba inji da kaina mana"

Zubaida tace "Lallai Umma sabida jamila ta baki Kuɗi yau ni kike gayawa haka to a makkan dazan biya Miki idan nai Kuɗi" Dariya jamila tayi "a haka zaki ƙare buri ne ze kashe ki Ina kika ga kuɗin zuwa makan kai sarki Kullum kina ɗaki riƙe da waya mai kyauro Buri da ƙarya sun cika rayuwarki kina geto area amman Fake life ya cika Miki Kanki wadda in za'a ƙureki ba lallai Ki iya karanta ABCD zuwa Z ba"

Wannan magana ta fusata Zubaida wadda take kallon jamila a ƙanwa ta uku amman tana gaya mata magana kuma umma taƙi cewa Komai sabida jamilar ta bata Kuɗi aiko tai kan Jamila da Duka Umma ta tare tana "wallahi ba zaki ƙara mata wata gajiyar akan wata ba taje tai aikin ta dan ta rufawa kanta asiri zaki zo Kina dukan ta"

Jamila na kuka umma ta kamata tana ce mata "Muje ciki ni wannan faɗa naku kamar kaji abin yana damuna kamar waɗanda aka farraƙa Allah yasa ma ba kowa agidan da an mana dariya"

Ɗaki suka shige suka bar zubaida a waje duk yadda Umma ke sonta da Jin tsoronta yau jamila ta ƙwace fadar tata sabida Kuɗin data bawa Umman Jikin zubaida yayi sanyi tana shiga ɗakin su Zainura ta saka shewa.
"Duk yadda nake nuna Miki halin Umma kin kasa fahimta yadda Take shakkarki Inda zaki dinga bata na kashewa da kinfi haka Ƙima amman nina gaya Miki kwanan nan zaki sha mamakinta da jamila dan seta ƙwacewa kowa fadarsa a wajan Umma"
Tsaki Zubaida tai.
"Keni bazan iya Abin da jamila take yiba gaskiya Ba zan iya rayuwa da mazan banza ba Muna daga kwance zamuci arziƙin Mu Gobe ma Bikin wata ƙawata zani"
Dariya zainura tayi tana cewa.
"Zubaida kai sarki kenan an sanki ba'a san makwantar ki ba ƴar ɗangote wannan Buri naki yana bani dariya wai kina daga kwance zaki ci arziƙinki to ta ina bayan seka tashi ka nema arziƙin yake zuwar maka Ni kaina wannan kwanciya ta isheni ga Mu da baƙin Jini kamar an mana laƙani da hatimin jaɓa Jamila zanbi Nima ta nunan kasuwancin kai da kai data soma"
Zubaida taja tsaki tana danna wayarta data sha ɗauri da kyauro tana Wani ƙyafe baki kamar tana kallon kashi Zainura mai zata yi idan ba dariya ba.

Su sa'adah rufe Ƙofarsu sukai Suka saka Hajiya a tsakiyarsu bacci wahala da gajiya ya ɗauke wanda sam basu bi takan maganganun su Umma ba dan basune a gaban su ba Mafitar da suke Nema itace a gaban su 09022260850

*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *007*

Da ƙarfi yake taune ƙasan Laɓɓansa waɗanda sukai jajir kamar zasu fidda Jini se wani irin zazzafan Huci yake fesarwa Muryar shi takai maƙura wajan dashe wa duk yadda yake son fahimtar da Abbah Cewar ba shine ya Fitar da Kuɗin ba bai ma san ta yaya aka fitar dasu ba Abba yaƙi yarda sema ƙara Masifa yake yi masa Ta cikin wayar dake kare a saman Kunnen shi.

Ya mutsa takardun dake shaƙe a saman table ɗin gaban shi yake ya tura Allon computer dake kallon shi ta faɗi ƙasa ta tarwatse bai damu da yadda ta fashe ba duk da Uban kuɗin da aka narka wajan siyan ta Baya gane komai a wannan Lokacin dama yana da wannan matsalar Idan ranshi ya ɓaci gaba ɗaya Jikinsa mazari yake Manya Manyan Lumsassun Idanunshi Masu fari kamar Ruwa sun Koma jajir Gaba ɗaya Huci yake yi Sedai bai da damar Mayarwa da Mahaifin nashi martani Abba baya bincike ga komai Idan ya faru sedai ya ɗora Alhakin Akan ɗan sa Tilo Namiji Guda ɗaya daya mallaka a duniya.

*ANWAR SULE KURFI KENAN* MD na kamfanin   *KURFI TEXTILES COMPANY* Dake jahar kano babban kamfanin Kurfi Tex kamfanin Alhaji Sule kurfi wanda ɗansa Anwar ke jagorancin Kula da komai na kamfanin, Kurfi tex kamfanine dake Siyarwa da ƴan kasuwa dama waɗanda ba ƴan kasuwa ba Kayan sawa waɗanda suka haɗa da atamfofi shadda lace dogayen riguna kala kala Kurfi tex suna bada kayan su ne akan sari ga ƴan kasuwa dama waɗanda ba ƴan kasuwar ba, Kurfi tex delar ne dake bawa ƴan kasuwa bashi Kamfanin ya shahara a jahar kano wanda suke zaune a kan titin IBB Kusa da kasuwar kantin kwari Kurfi tex suna tura kayansu cikin ko wace jaha dake faɗin Nageria da sauran ƙasashen dake maƙotaka da nageria Babban kamfanine wanda ya haɗa ma'aikata masu tarin yawa a kowani ɓangare akwai Ma'aikata acikin kamfanin akwai Ɓangaran atamfa akwai ɓangaran lace a kwai ɓangaran shadda akwai ɓangaran dogayen riguna akwai ɓangaran material wani kayan in ka gansu idan ba a kurfi tex ba bazaka taɓa samun suba wannan dalilin yasa kamfanin suke cinikin kayansu daga sun kawo ƴan kasuwa suke aringizo wajan wawashe musu kayan nasu wannan Kuma Cigaban ba kowa bane ya jajirce akan sa har yasa kamfanin yayi fice fiye da sauran kamfaninnika face Mai kamfanin Alhaji sule kurfi wanda kullum baya waccan ƙasa baya waccan wajan Siyo kaya masu inganci domin ya turo su cikin kamfanin nashi duk samfir ɗin daya gani yana ƙoƙari wajan ganin kamfaninshi ya fara kawo su wasu kayan ma shikaɗai yake siyewa ya shigo dasu ƙasar nan ya zuba a cikin kamfanin shi, A wannan Lokacin ne da Girma ya soma kama shi yawanci In bai samu ya fita siyo kayan ba sedai ɗansa Anwar ya fita ya shigo dasu wannan tasa abubuwan sukai wa Anwar yawa shi kaɗai ya rasa ina zai tsoma ranshi.

Alhaji Sule yana ɗaya daga cikin manya manyan ƴan kasuwar da ake jida su a jahar kano dama ƙasa baki ɗaya babban ɗan kasuwa ne mai dukiyar da bai san adadinta ba domin banda wannan kamfani suna da reshinan shagunan su acikin kasuwannin Kwari sabon gari ƙofar wambai da wasu daga cikin manyan Titinan dake jahar kano wanda ya zaɓi wasu daga cikin yaranshi da kuma ƴaƴan ƴan uwanshi suke kular masa dasu.

"Abbah jiya na dawo daga Dubai kaikuma nazo na samu baka kano kana lagos ka bari na huta zanyi magana da chief financial officer sabida dukkan alhakin fitar da kuɗi ko shigowar su seda saka hannun shi da kuma sanin shi"

Abba ya daka wa Anwar tsawa.
"Kaga ka fito mini da kuɗina Nina san waye Jamilu tun kafin kai ƙwari nake tare dashi ada kafin na ɗoraka a wannan Kujerar shine akai Kuma ban taɓa ganin wata matsala ba sabida haka ina sane na bashi matsayin C.f.o sabida gaskiyar shi da riƙon amanar shi"

Anwar yayi shuru kafin ya  soma bawa Abbah haƙuri cikin sanyin Murya duk da ransa a ɓace yake.

Batare da sallama ba Abba ya kashe wayar Anwar ya shiga danna telephone ɗin dake saman table ɗin shi sakataren dake office ɗin C.f.O ya ɗaga wayar.
A hankali kuma cikin nutsuwa yace.
"Tell Alhaji Jamilu that I am calling him now in my office" daga haka yaja wayar ya datse kiran yana jinginar da kanshi saman Kujerar wani irin ƙaton abune yazo ya takure masa acikin maƙoshin sa.
Secteren office ɗin Alhaji Jamilu wanda ke da muƙamin Chief financial officer shine ya sanar da Alhaji jamilu kiran Md wanda Jikin Alhaji jamilu har rawa yake cike da Sauri yabar duk abin da yake yi ya tafi Kiran da Md yake masa seda Sakataren dake Office ɗin Md yaje wajan sa ya bada izinin shigowar Alhaji jamilu sannan Ya bawa Alhaji jamilun damar shiga cikin katafaran Office Ɗin Anwar wanda Ada Alhaji Jamilun ne acikin kafin Shigowar Anwar Kamfanin wanda zuwan Anwar ya kawo sauye sauye da cigaba da dama bada ban waɗannan matsaloli na ɓatan kuɗi da ɓatan kaya da suka fara kunno wa kamfanin ba.

Alhaji Jamilu yaja Kujerar dake facing ta Anwar ya zauna A hankali Anwar ya ɗago kanshi ya zubawa Alhaji jamilu idanu bai ɗauke idanunshi ba har seda ya ɗaga wayar ya kira Chief staff officer tare da Chief Information officer da kuma Chief marketing officer gaba ɗaya manyan Masu muƙaman kamfanin sun halarci zama a cikin Office ɗin Anwar.

Ɗaya bayan ɗaya yake binsu da kallo Alhaji jamilu ne kaɗai zai iya haifar sa amman sauran masu manyan muƙaman basu fi sa'annin shi a haife ba.

"Ko wannen ku idan ya rasa kujerar sa ina nufin idan ya rasa hanyar samun abincin sa ina ga zai shiga hankalin sa ta yaya Kuna Cikin kamfanin nan Kuɗi su dinga ɓata ko mu loda kaya a manyan Motocinmu zuwa wani gari ace motar ta faɗi an sace kaya driver na asibi mai yake kawo haka?"
Ya tsaida idanunshi akan chief information officer kafin yace "Kaine kake da Lasisin ganin dukkan abin da yake faruwa acikin wannan kamfani ta cikin na'urorin dake office ɗinka, sannan alhakin ta yaya har kuɗi masu yawa suka salwanta babu sanin ka?" sannan ya kalli chief marketing officer tare da cewa "Kaikuma kaine mai lasisin kula da ƴan kasuwar dake shige da fice acikin wannan kamfani ta yaya har aka fitar da kuɗi ba tare da saninka ba bayan lasisin Kula da al'amuran kasuwancin wannan kamfani yana hannun ka?" ya Kuma kallon chief staff officer yana ce masa "Babu yadda za'ai ayi wani babban cinikayya acikin kamfanin nan batare da saninka ba sabida kaike da Kujerar shugaban ma'aikatan kamfanin nan baki ɗaya dole komai za'ai seda sanin ka sabida Duk wani staff ɗin kamfanin nan a ƙasan ka yake" yayi shuru tare da ɗaukar Gorar ruwa ya Kora "Alhaji Jamilu Financial Officer ni kaina in zan taɓa kuɗi seda izininka sanin dukkan wani tracking na kuɗin kamfanin nan yana wajan ka mai yasa har waɗancan Kuɗin da suka fita yau kimanin sati Biyu wanda yayi daidai da kwana na Biyar a Dubai suka fita wanda ni ban sani ba don ban signing shigowar wasu kaya ba bare ace an fitar dasu Duk ƙarshen wata nake Turawa Abba komai yana sanin Shigowar Kuɗin sa da fitar su da kuma albashin Ma'aikatan sa wannan karon Kuɗin da suka salwanta sunfi na kowane wata yawa duk da ba genaral total mukai ba wannan duk ƙarshen shekara Muke yi.

Alhaji jamilu ya kasa magana haka sauran ma Anwar ya kuma kallon Chief information Officer yace "Lallai lallai ka tabbatar ka nemo yadda kuɗinnan suka fita da lokacin su da komai haka kai ma Alhaji jamilu Tabbas ka tabbatar ka kawon cikakkiyar Hujjar da kasa hannu har kuɗaɗan nan suka fita batare da sanina ba Chief staff zaka iya komawa kai da Chief Marketing zan ƙara kiran ku"

Daga haka ya tashi yabar su a wajan ya shiga cikin resting room Jakar computers ɗinshi da keyn motar shi se wayoyin shi daya ɗauka Ya fito da sauri sectaren shi ya zo ya amshi kayan seda ya raka shi har wajan adana Motoci Inda motar shi take ya buɗe masa ya shiga Ciki ya zauna a driver seat sannan yakai masa kayan sa back seat sukai sallama Anwar Yaja Motar a nutse ya nufi ƙaton Bakin gate ɗin kamfanin wanda Securties suka cika wajan ɗaga wa Anwar Hannu suke batare daya Ɗago ya kalle suba ya danna hancin Motar shi yabar harabar Kamfanin Gudu yake Lokacin Yamma tayi sosai a ƙofar Gidan mahaifin shi Alhaji sule kurfi dake Unguwar Rijiyar zaki layin Muhalli Yayi parking ɗin Motar shi yana danna Horn masu gadi suka wangale masa gate Ɗin ya shiga cikin harabar Gidan ya adana motar shi bai ko tsaya ɗaukar komai ba dan hatta wayar shi ma A motar ya bari haka ya Nufi Part ɗin shi a hankali ya faɗa saman Gadon shi ya kifa cikin sa zuciyar shi babu daɗi sam wannan tasa tunda Abban shi ya Damƙa masa Dukiyar shi yayi bankwana da Nutsuwar shi Tarin damuwa da Ƙunci ne suka ƙara taruwa acikin zuciyar shi..........
*YANKAN ƘAUNA..I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*









*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
​*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹
        
         *NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

                     *008*

ƙirjinsa ne ya soma ciwo ga wani irin zafi da yake yi masa tun yana iya Numfashi har fitar Numfashin Nasa ma tazo ta gagara a hankali Numfashin sa yake ɗauke wa kafin ya faɗo daga saman gadon tim baya Numfashi A wannan Lokacin bashi da Bambanci da gawa dama haka Yake yi Duk Lokacin da Ciwon zuciyar sa ya tayar masa wani irin baƙin Gudan Jinine ke fitowa daga cikin Hancin sa Adaidai wannan Lokacin Khalid ya shigo Gidan dawowar shi daga Office kenan kasancewar yana ɗaya daga cikin masu kula da Branch ɗin Alhaji dake kasuwar sabon gari Har Khalid zai shiga Part Ɗinsu wajan Innah domin yace tayi Musu Dambu kafin su dawo sanin Anwar Yana masifar son Dambun Shinkafa seya fasa ya tsaya a compound ɗin gidan tare da Fito da wayar shi yana kiran Number Ɗin Anwar wanda seda Khalid yayi masa Five Misscalls amman Anwar bai ɗauka ba A fili Khalid yaja tsaki tare da shafa sumar kanshi yana cewa.
"Wannan Bahagon Mutumin ina ya saka wayar shi Oho! Jin ana kiran sallah Khalid ya Nufi Bakin Jerin famfunan dake Compound yayi alwala ya shiga masallaci Bayan sun idar da sallar ya Nufi Part Ɗin su har ya ƙarasa Falon Innah yana Kiran Numbers ɗin Anwar Amman baki ɗayan su ba'a ɗauka ba zama Khalid yayi Rahma Autar Innah tana Kunna kallo ganin shi ta dakata tana masa sannu da zuwa.

"Ina innah Anwar ya shigo nan kuwa?" Rahma tace "A,a bai zoba Inna kuma tana ɗaki tana sallah" Daga haka tabar wajan sanin idan Manyan yayin nasu suna Falon basa zama su aciki.

Khalid se kiran Numbers Ɗin Anwar yake suna shiga amman har Lokacin bai ɗauka ba se duk yaji babu daɗi sabida da zarar sun dawo daga Office to suna tare Muddin ba Ƙasar Anwar ya bari ba, Ko shi in yaje Lagos ko wata jahar kai kaya.

A haka Innah ta fito tana Murmushi "A,a naga Hassan ban ga Hussainin ba ina Muhammad Ɗin?" Inna ta faɗa tana zama a saman Kujera Khalid cikin rashin walwala yace mata "Tunda nazo nake Neman Layi kanshi amman bai ɗauka ba Duk hankalina ya tashi Innah Ina Malam?" Innah ta Ɗan sauya fuska cikin halin damuwa tace "Malam yana ɗakin sa yana karatun alkur'ani wai nan Saifullahi ko Fatihu yake Jira su dawo daga shago su kaishi Aski amman ya kamata ka binciki halin da Anwar yake ciki sabida kasan yana da matsala wadda bama fatan tashin ta"

Khalid tashi yayi tsaye tare da cewa inna bara ya leƙa part Ɗin Anwar ɗin Ko yana ciki Cikin sanyin Jiki Innah tace "To Allah yasa dai lafiya Kona Biyoka?" Khalid ya ɗan kalleta sanin matsayin Anwar a wajanta Ko shi data Haifa bata Nuna masa Soyayya kamar wadda take nuna wa Anwar "Inna ta Anwar Ki kwantar da hankalin ki Innah bari naje yanzu zan dawo" Inna har bakin Ƙofa ta bi Khalid wanda seda taga ya nufi part Ɗin Anwar Sannan ta koma ciki Khalid yana Jan Handle ɗin Ƙofar Bedroom ɗin Anwar yaji ta buɗe ya shiga ciki ɗakin akwai Duhu sosai wayar shi yasan ya ya lalubi swich ɗin ɗakin haske ya bayyana tarwai wanda Idanun Khalid suka ci karo da Anwar a ƙasa wanwar kamar gawa da gudu Khalid ya saki wayar ya nufi wajan shi gaba ɗaya ya tattaro Shi Jikinsa yana Jijjigashi "Anwar! Anwar tashi mana yaushe Ka faɗi ciwon kane ya tashi garin yaya?" Duk Khalid ya shiga jera tambayar kamar Anwar yana Jinsa bayan shi tuni yayi nisa acikin suman da yayi.

Da sauri Kuma Khalid ya ɗauki wayar shi Allah yasa bata tarwatse ba ya shiga Kiran Doctor wanda shike Duba Anwar Idan ciwon shi ya tashi Doctor ya tabbatar wa da Khalid ya bashi Minti Goma sabida yana kusa dasu ne Gidan shi Khalid ya kashe wayar ya janyo Anwar saman Jikinshi gaba ɗaya Hankalin Khalid a tashe yake A haka Doctor Yazo ya same su wanda Shigowar Doctor ce ta fargar da Ma'aikatan Gidan Sanin Halin da Anwar yake ciki sabida Kowa yasan in kaga Doctor yazo Gidan to ciwon Anwar ne ya tashi Ma'aikatan gidan Sune Suka sanar da Mama abin da yake faruwa da sauri ta zari mayafi Jikinta har rawa yake ta nufi Part Ɗin Anwar Sedai koda ta ƙarasa Khalid ne a bakin Ƙofar gadan gadan ta nufi Buɗe Ƙofar Khalid ya hanata ta hanyar zira key.

"Marar kunya tsohon munafuki ka barni na wuce naga halin da yake ciki kodan bani ce na haife shiba in uwar shice Ni zaka Hanani shiga ne?"

Khalid ya kawar da kanshi bai tanka wa Mama ba wadda hakan ya ƙara fusata ta seta hau masifa Khalid yayi mata banza har Doctor ya fito yana yarfe zufa hannun shi da kayan aikin shi mama bata daina masifar da take yiba seda Doctor yayi gyaran murya kafin ya kalleta "Hajiya kamata yayi Ki fita sabida Maganar ki zata iya Janyo masa matsala" mama tahau Sosa kai tana cewa Doctor "To ai abinne da ciwo Ƙiri ƙiri nazo zanga halin da yake ciki wannan Munafukin ya hanani sabida Ni ba uwar shi bace ba to duk dai tsiya ba ku isa kun raɓa alaƙar ƴaƴana dashi ba" Likita ya mayar da hankali wajan Khalid yana bashi takardar magani tare da yi masa gargaɗin kula da lafiya Anwar sabida zuciyar shi tana cikin hatsari.

Khalid ya amsa Still Rufe ƙofar ya kuma yi yabi bayan doctor yabar Mama a tsaye cike da mamaki Haka halin Khalid yake Shi baya son Ƙunbiya Ƙunbiya yadda Halin Anwar yake haka halin shi yake shine ma yasa zaman su yazo daidai bambancin su kaɗai Anwar baya da yawan Magana Kuma yana da Miskilanci saɓanin Khalid mai Yawan magana da son shiga hurɗar Jama'a.

Khalid bai gigin shedawa innah ba ya shiga Mota ya nufi pharmacy ya siyo maganin da Doctor ya rubuta tare da yi masa takeaway ya dawo Gida har Lokacin Anwar yana bacci sabida alluran da Doctor yayi mishi A gefen shi Khalid ya zauna yana jiran ya tashi Har bayan Isha a lokacin Kiran Innah ya shigo wayar shi tashi yayi ya fita a wannan Lokacin bai Rufe Ƙofar ba yabar ta a buɗe ya nufi part Ɗin su.


Tun daga Ƙofar falo Mama take bambamin bala'i "Sabida bani na haifi Anwar ba yasa ake

Please Login or Register in order to submit comment