Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaƙi bawa Mama damar bin shi.

Da wani irin tsantsar farin ciki ta bar Falon Abbah direct Bedroom ɗinta ta isa tana zuwa ta kulle ƙofar tare da zira Key ajiki.

Ta ɗauki wayarta tana kiran Numbern Alhaji jamilu yayan tane uwa ɗaya uba ɗaya, Shi take bi kuma dukkan wani makirci tare suke ƙullawa don su gina kansu sabida yadda take da ƴaƴa mata gani take nan gaba Anwar ne zai gaje rabin Komai in batai da gaske ba.

"Yaya barka da dare" ta faɗa.
Daga nashi ɓarin yace mata.
"Lafiya lau shafa'atu yaya ake ciki ne?"
Ta gyara zama a gefen gado.
"Yaya da alamun fa wannan Lokacin Anwar zai bar mana kamfani, Saboda ban taɓa ganin Yadda ran Alhaji ya ɓaci irin na yau ba dan bana hango soyayyar nan a idanunshi ta Anwar sai tsantsar ƙiyayya da zargi kuma shima kasan Anwar da zuciya kamar Kuturu da wuya ya koma Office"

Alhaji Jamilu yayi wani basaraken Murmushi tare da cewa.
"Ta yaro kyau take bata ƙarko ai yadda nai masa babu yadda za'ai ya iya fita, sabida duk wata Ƙofar da zata nuna akwai saka hannun shi wajan fitar kuɗin ta nuna sabida haka nina san dole ya bar mana kamfanin mu cigaba da cin gashin kammu haka kawai yaro yazo ya zame mana jaraba komai mukai akan Idanunshi"

Dariya take sosai.
"Ai yaya kafin Alhaji ya rasu se na kwashe dukkan dukiyar shi dan Ni mai ƴaƴa mata nice a ƙasa sabida haka shiyasa tun yanzu nake cin kaso na"

Murmushin mugunta yayi.
"Haka ne shafa'atu sabida haka zamu dage damtse" tai Murmushin itama.
"Yaya zan turo account ka turo mini kasona dan kuɗin suna da yawa ka ɗau kaso ɗaya ka bani biyu" ya wani haɗe rai.
"Ki bari mana a gama bincike In komai ya daidaita saina baki naki haba kefa akan Kuɗi baki da sauƙi, Ni burina wannan shegen yaron yabar mana waje mu sarara na koma kan Kujerata ai tunda ya sake ya hau saman Kujerar da nake kai wallahi Koda asiri sena sabau tashi"

Dariya take har tana ƙwarewa.
"Yaya kenan kana ganin wannan dutsen zai biyu ta sauƙi? to ban hanaka ba amman zaka kashe kuɗi sosai ni ai tun akan auren Hanan na daina kashe Kuɗi ba inda ban jeba amman Ko gezau shiyasa na shiga tunanin anya ma kuwa shi kaɗai ne ko ga rashin auren sa ma ina ga ba lafiyayye bane  shiyasa yanzu ba boka ba malam kirsa ta kaɗai ta isheni se yadda nai da ubansa"

Dariya suke kafin su cigaba da maganganun su akan Mugun Nufin su na farraƙa ɗa da ubansa sabida suyi raraka da babake re akan Dukiyar da basu suka haɗata ba.
Sun jima suna waya kafin ta kashe wayar tana wani irin murmushi.

Daga ɓarin Alhaji jamilu yaja tsaki yana hararar wayar.
"Shegiya mayyar kuɗi babu abin da zan baki Ni ɗan iska ne Kullum ina wa Mijinki Hidima kina amfani dani kina ƙaruwa kullum maganarki gado ƴaƴa ni bani da ƴaƴan Ko bana son suci gadon nawa a haka zanta Binki ina Moruwa dake"
Matarshi tayi dariya tana furta kalmar "Lallai Kuwa Kayi Mini daidai ai na lura da shafa koda yaushe kanta ta sani tana ganin kamar baka san mai kake ba bayan ita ce babbar sakarai wadda bata san abin da take yi ba"

Dariya sukai Alhaji jamilu yana shafa tumbin sa "Nan gaba kaɗan nine ma mallakin Kamfanin Kurfi tex se na kawar da kowa" yana faɗa yana wata irin dariya!



Safa da marwa Anwar yake a ɗakin sa ya goya hannunshi a baya Duk sanyin AC ɗin ɗakin shi bai hana zufa falfala gudu a saman fatar jikin shiba Normally dama shi mutum ne mai yawan zufa sabida gargasar dake Lulluɓe da fatar jikinsa.

Sunan Allah ya dinga ambata da sauri da sauri yana sassarfa kafin ya nufi gaban mirrow ya dafa ya sunkuyar da kanshi idanunnan ya kaɗa Yama kasa tuna komai kawai karkaɗa kai yake yi ba ƙaramin Juriya yayi ba wajan danne zazzafan hawayen dake son zubo masa a hankali ya ɗauko wayar shi ya shiga yima Abba transper na kuɗin shi.

Bayan kamar mintina goma wayar ta doka ƙara! sunan Abba na yawo Akan screen ɗin

Ya ɗaga kafin yakai ga magana.
"Zan dawo maka dasu sabida bata account ɗina ka ɗiba ba, ka kaiwa jamilu cash tare da shaida a rubuce"

Daga haka ya datse Kiran bayan Mintuna kuɗin suka dawo masa

Faɗawa saman gado yayi yana ambatar Ubangiji dan shine kaɗai zai kawo masa ɗauki a haka bacci ya ɗauke shi batare daya shirya ba dama abin ka da jikin wahala an sha zirga zirgar aiki washe gari ƙarfe bakwai daidai ya shirya cikin baƙaƙen suit babu abin da ke tashi a jikin sa sai ƙamshin haɗaɗɗun zafafan turarukan shi yana tafe yana ɗaure Igiyar Cover shoe ɗin ƙafafun sa kafaɗun shi Kuma ɗauke da jakar Computers a tsaye yake bayan ya gama ɗaure takalman cup ya ɗauka yana zuba tea da zafi zafi yake Kurɓar tea ɗin kafin ya gama ya dire cup ɗin ya kama hanyar fita.

"Allah sarki Yaya sai haƙuri fa da mahaifi karka fasa fita Office dan Allah"

Ya juyo yana mata Murmushi wanda ta jima bata gani a saman kyakykyawar fuskar shiba.

"Hajiya shafa'atu kin taɓa ganin ɗa yayi fushi da ubanshi Akan me zanyi Fushi da dukiyata bayan ni ake tattalawa"
Ya faɗa mata yana zira idanun shi cikin nata ya ɗage mata girar shi Guda kafin yabar mata falon Cikin tafiyar shi ta Jaruman maza


Zaman dirshan tayi tana yarfe zufa da ƙyar ta saita kanta ta nufi part Ɗin Abba kuma tana tunanin maganar shi mai kama da harshen damo.


Tana kuma zama a falon saƙon haihuwar Husna ya ziyarce ta wanda Mijin Husnar ya sanar da ita umarni ta bashi akan ya sama wa Husna ticket ɗin Kano ya amsa yana kashe wayar ƴan uwa ta shiga kira tana sanar Musu Husna ta samu baby boy kafin a hankali ta Kira Hadiza mai kawo musu ƴan aiki ta ce mata tana son yarinya Budurwa wadda zata dinga Kularwa da Husna jaririnta da sauran Hidimar Mai jego daga haka sukai sallama akan Hadiza zata kawo mata wannan Haihuwar ita ta mantar da Mama tunanin maganganun Anwar wanda tuni Gida ya ruɗe da shirin zuwan mai jego Tun kafin ma ta diro Gidan ƴan uwa suka soma zuwa da ƙawayen mama sabida harka in aka ce maka ta mai shi ce to ko ba dan Allah ba sai anzo.

Da matiƙar farin ciki Hadiza ta shirya zuwa gidansu sa'adah sabida daman tunda suka rabu take Nanata tausayin yaran acikin zuciyarta to yau dai Allah ya nufa Gidan Alhaji Sule Kurfi suna neman mai aiki zata gwada kai wannan yarinya ko Allah yasa a dace.

Da wajan la'asar hadiza ta fito daga gidanta ta hau mota zuwa Gidansu sa'a wanda yau suka tashi da farin cikin Mijin Aunty Murja ya sai wa Hajiya magani sabida haka sai suka kasance cikin walwala da farin ciki a wannan rana duk da tarin habaici da Umma take yi Musu amman su hakan bai dame suba.

Ana yin la'asar sa'adatu ta fito da wanki tana yi a bakin Rijiya ta sunkuya tana saɓe kayan taji Muryar Hadiza tana sallama a tsakar Gidan nasu.......

*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*




*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*12*

Da murmushi a saman fuskar sa'adatu take amsa sallamar Hadiza Bayan ta tsame hannunta daga cikin ruwan wankin.
"Lahh Baba Hadiza ce a gidan namu? sannu da zuwa" ta faɗa tana Dariya Hadiza taja kujerar gaban Sa'adah tana cewa.
"Nice Sa'adatu yaya gida da Jikin Tsohuwar taku?" Sa'adah tace "Alhamdulillahi Hajiya jikin nata da sauƙi Mu shiga daga ciki"
Hadiza ta miƙe suka ƙarasa ɗakin su Sa'adah Ummi tana bawa Hajiya abinci Tana ganin Hadiza ta faɗaɗa Far'a tana gaisheta Ruwa Sa'adah ta miƙowa Hadiza ta fita da sauri ta ƙarasa wankin ta dawo Lokacin Ummi da Hadiza suna ta hira wadda rabi akan yanayin ciwon Hajiya ne Sa'adatu ta zauna bata ce komai ba tana ta murmushi dama ita bata da yawan surutu ummi ta fita magana.
"Ƴata wajan kifa nazo,Dama akan maganar aikin da muka aje ce wadda nace idan na samu zan gaya miki"

Sa'adatu ta gyara zama tana sauraron Hadiza.
"To An samu anan gaban ku Layin Muhalli Gidan Alhaji Sule Kurfi shahararran ɗan kasuwar nan ƴar sace ta haihu uwar ke son wadda zata ke taimakon mai jegon wajan raino da sauran hidindimu"

Sa'adatu tace "To Alhamdulillahi aikuwa nagode Yanzu zamu je ko sai Gobe?" hadiza ta gyara zamanta tana cewa "Ai da yake na kwana ne yanzu zaki haɗa kayanki Mu tafi gudun kar a kawo masu wata" Jin aikin kwana yasa sa'adatu ta sauya yanayin Fuskarta nan da nan ta ɗaure Fuskarta "Ni dai bana son aikin kwana Baba Hadiza inna tafi Waze dinga kula da Hajiya Ummi abubuwan zasu yi mata yawa bayan haka ma ban taɓa Nisa dasu ba tun da na taso" Hadiza tai Murmushi tare da cewa "Yaro yarone Ko baki tare dasu ai kina da abin da zai riƙe su wannan aikin da zaki yi zai taimaki mahaifiyar ki dan ina miki kwaɗayin zakkah da sauran alkairai Kuma bama jimawa zaki ba ina ga daga ta gama wanka koma kafin Lokacin kin gama fa sai dai a ƙara samar Miki wani sannan kuna kusa daga kin ji kina son gida zaki tambayi Hajiya ki zo damma gidan akwai jami'an tsaro amman ni zan mata bayanin Komai da Komai"
Ummi ita ma duk jikinta yayi sanyi amman sai ta daure dan ta ƙarawa sa'adah ƙarfin gwiwa "Dan Allah Sa'adatu kije ko dan ma kuɗin maganin Hajiya in danni ne karki damu Zan mata komai In sha Allah dama in da nice zan tafin ke zan ke tunani kodan Mutan gidannan amman ni kam karki damu Babu abin da zai gagare Ni Da yardar Ubangiji Allah yasa ki shiga a sa'a Allah yasa silar ƙarshen wahalar mu ne aikin naki dan wani abun in yazo ka ƙishi sai kaga ya zame maka alkairi"

Da wannan ƙarfin gwiwa da Ummi ta bawa sa'adah suka samu harta haɗa ƴan kayanta a Ledar Viva baƙa Aikuwa data fito daga ɗaki da Ledar kayan idanun nan nata sunyi jajir tasha Kuka ta Ƙoshi zuwa tayi gaban Hajiya ta rungume ta tana kuka Hajiyar ma hawaye take a fili sa'adatu take cewa.
"Wallahi zuciyata ciwo take Mini na rabuwa dake Hajiya amman yaya zanyi rayuwar tafiya take Lokaci Gudu yake bamu da mataimaki sai Allah kullum Jiya i yau, akan dole zan tafi na nemi Halak ɗina don na taimake ki bamu da kowa sai Allah Hajiya Allah ya baki lafiya Haƙiƙa zanyi kewarku"
Ummi ma duk yadda taso danne nata kukan Hakan bai samu ba domin sai ta fashe da kukan itama Rungume Hajiya sukai Hadiza sai barin ɗakin tayi tana Share hawaye haƙiƙa Ƴammatan ababan tausayi ne rayuwar su abar tausayawa ce shiyasa tunda taji halin da suke ciki ta kasa samun kwanciyar hankali har sai da ta ga Sa'adah ta sami aiki sannan hankalinta ya kwanta tasan koba Komai zata rage wasu abubuwan sosai da Kuɗin albashin nata.

Rufo ƙofar sukai suka baro Hajiya dan Ummi zata raka sa'adah dan taga muhallin da za'a kai ƴar uwar tata Ɗakin Baffa suka shiga sabida yau bai fita ba wai baya jin daɗi yana fama da Mura sukai sallama ya amsa musu Ummi ce ta faɗi maganar.
"Baffa sa'adatu zata tafi Gidan aiki shine tazo yi maka sallama"
Sai Lokacin ya ɗago yana binsu da kallo.
"Ita bata da bakin magana sai ke tsagera to Allah raka taki Gona in kuma ta kwaso abin Kunya ta nemi wani Gidan ba nawa ba"
Ummi tai saurin cewa.
"Tunda tsanani da rashi da Buƙatar taimako bai saka ta zubda Ƙimarta ba In sha Allahu rabbi Neman halak alkairi ne a gareta"
Tana faɗa masa hakan taja hannun sa'adah suka bar ɗakin suna ji yana zagin Ummi harda cewa sai tazama karuwa In sha Allahu su dai fita sukai dan Ko Umma ba suyi wa sallama ba domin Itama babu alkairi a harshenta.

Suna tafe suna Ƙus ƙus daga gani sirri suke ita da ummi Hadiza ta Juyo tana cewa.
"Dan hankalin ku ya kwanta Zan ranta wa sa'adatu dubu takwas Muje wancan shagon Ku sai wayoyin hannu Kona dubu uku da ɗari biyar biyar ne sai Ku sai layuka sai ku dinga waya ina ga hakan zaku fi samun kwanciyar hankali In yaso duk sanda Allah ya hore mata sai ta bani Kuɗina"
Godiya sukai mata aikuwa suka je shagon Sukai sai wayoyin waɗanda suke clean Tare da sim card suka saka harda katin naira ɗari ɗari bayan sun gama suka tafi aikuwa bakin su yaƙi Rufuwa sabida farin Ciki Da ƙafa suka je har Layin Muhallin wanda tsiran su babu Nisa Tundaga farkon layin Suka sha Jinin Jikinsu sabida yadda manyan Gidaje suka cika layin a gaban wani ƙaton Gida Hadiza ta tsai dasu Gidan da fasalta kyan sa da tsarin sama ƙauyanci ne sai da Suka sha tambayoyi kafin abari su Shiga farkon Gate Ɗin wanda kafin sukai Cikin Gidanma sai da aka Kuma tsaida Hadiza har waya akai Cikin Gidan kafin a bari su Shiga daga Ummi har sa'adah bakin su ya rufe hadiza Kuwa Mita take tana sababin Kamar masu tsaron Gidan basa gane Mutane Koda yaushe kazo sai an maka tambayar tsiya Sukam su Ummi baki ya ɗinke dama akwai irin Gidajen nan a ƙasar nan ama cikin Unguwar su lallai mai Kuɗi ya Huta.

Numfashin sa'adatu ya tsaya na wucin gadi sanda suka je bakin part Ɗin Mama dan wani azababban Kyau da tsari part Ɗin yake dashi wanda kwatan tashi ma ɓata Lokaci ne Da ƙyar suka iya buɗe Ƙofar Babban Falon da girman sa ya kusan zautar da tunanin su sa'adah tsarin sa da dukiyar da aka narka masa ce ta Firgitasu wannan rayuwa kamar ba za'a mutu ba zama sukai Mai aikin dake kaiwa da Komowa a falon ce ta kawo Musu ruwa da abinci Shinkafa da Miyar kaji da lemo Hadiza ta zage tana ci Ita kuwa Sa'adah Ledar Kayanta ta zazzage ta Ƙulle kayan a ɗankwali Nasu abincin ta Juye a ledar tana cewa Ummi idan taje Gida suci da Hajiya ta bawa Hajiya naman sosai taci Yadda Sa'adah tayi ɗinne ya ƙara Birge Hadiza lallai yarinyar akwai tausayi da Jin ƙai sai da suka kammala ko ace Hadiza ta kammala kafin Mama ta fito daga ɓangaren Bedroom Ɗinta Sa'adatu da Ummi suka gaishe da Mama cikin ladabi ta amsa a sake tana cewa.
"Hadiza ki mini afuwa ina tare da baƙi ne ƴan barka ina yarinyar take?"
Sa'adatu ta ɗago idanunta wanda suka haɗa ido da mama Sa'adatu ta saki Murmushi yayin da Mama kuma taji gabanta ya faɗi kaɗan.

"Wannan ce Sa'adatu sunanta marayu ne dan Allah Hajiya A dinga taimakonta mahaifiyarta tana fama da shanyewar ɓarin Jiki dole ce ta fito da ita ma aikin"

Mama ta ɗan yamutsa fuska.
"Idan ban da abinki Hadiza meye na wannan jawaban zatai aiki zan biya ta babu rashin ci babu rashin sha a gidannan ga part ɗin mai aikina can Kande su zauna tare Sabida Kin san duk na kori ma'aikatana mata sai kande kaɗai na bari tana Mini Girki da gyara mana ɗakunan barcin mu yanzu maza nake dasu suke mini komai domin matan da kika kawo Min ban yi dace ba gaskiya basu da tsafta shiyasa duk na sallame su, To idan ita ɗin naga bata da matsala zan iya ɗaukar tama gaba ɗaya sabida Alhaji yana faɗan yadda maza ke mana share sharen Gidannan gaskiya"

Hadiza ta kuma yin ƙasa dakai tana wa Mama godiya kafin maman tace.
"Ba damuwa Zaku iya tafiya hadiza zaki ga saƙo ta bankin ki anjima"

Sannan ta ɗaga Murya tana Kiran.
"Kande! kande!"
Da sauri wannan mai aikin data kawo Musu abinci tazo ta zube a gaban mama Dattijuwa ce sai dai da ƙwarinta sosai, mama ta kalleta "Kande ga mai aikin Husna nan ki kaita ɓangaren ku kin sami ƴa" kanden da far'a ta ɗauki Ƙullin kayan Sa'adatu tana cewa "aikuwa dai na huta zaman kaɗai ci damma da kayan kallo"
Mama ta tashi ta koma inda ta fito Hadiza ta kalli kande tana cewa.
"Dan Allah ga amanar tanan Kande Ƴata ce ta zumunci" kande tayi Dariya "Wallahi Hadiza karki damu waɗanda kika kawo ma da Hajiya mama ta kora ni bamu taɓa samun saɓani da suba sabida tace Mini kece kike kawo mata masu aiki Nice kaɗai ta samu a wajan wata ai ɗa na kowa ne Nima ina da su a ƙauye"
Tashi sukai Hadiza da Ummi suka fita kande Kuma ta Nufi ɓangaren su da kayan sa'adatu wadda tabi su Ummi don yi Musu rakiya kamar ba zasu rabu da ummi ba sun Rungume Juna suna Ta kuka sai da Hadiza ta ɓanɓare Ummi Sannan Suka rabu da Junansu.

Sa'adatu kuka take sosai haka ta juyo idanunta ko gani bayayi sosai a maimakon tayi part ɗin da aka kaita sai kanta ya juye ta nufi wani part ɗin na daban wanda ita sam bata tantance wanda aka kaita da shi ba Sai da ta shiga falon taga bambancin Girma da kuma tsari dan wannan bai da girman wancan kuma bai da wasu tarkace acikin sa daga Saitin Kujeru sai kayan kallo sai shinfiɗaɗɗan carpet sai Manyan haɗaɗɗun labulaye sai azababban ƙamshi mai kama Hanci data ke shaƙa Ƙoƙarin juyawa take don ta koma sai dai ƙafafun ta sun sage ne Lokacin data ɗaga idanunta dan ta kalli Motsin data ji ajikin Ƙofar dake kallonta idanunta ne suka Shiga cikin nashi.......
*YANKAN ƘAUNA...I! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne Mtn ko Airtel card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*




*ZAINTUNA MULTI TRADE KANO*🔥🔥

*KOMAI DA RUWAN KA SHINE TAKEN MU MUNA ARHA MUNA RAHUSA GA DUKKAN KAYAN MU DOMIN SAUƘAƘAWA MASU SIYA*

*A ZAITUNA MULTI TRADE MUNA SIYAR DA*

*KAYAN GWANJO*
*KAYAN KITCHEN*
*KAYAN ELECTRONIC*
*GADAJE*
*KUJERU*
*KAYAN SAKAWA NA YARA DA MANYA DA JARIRAI*

_A WANI ƁANGARAN MUNA YIN_
*GRAN JIKI*
*ƘUN SHI DA BABU IRIN SA*
*MUNA DA TURARUKAN WUTA HUMRA*
*MUNA DA MAGUNGUNAN MATA*
*GUMBAR UKU BALA'I*
*GUMBAR TABAJE*
*GUMBAR BUJENTA JAGAB*
*GUMBAR SAKA MAI GIDA IHU*
*MUNA DA ZAFAFAN KAYAN MATAN DA BABU IRIN SU*🔥🔥
*MUNA DA SUPLEMENTS*
_ZAITUNA MULTI TRADE MUNA YIN_
*MAKE UP NA AMARE DAMA WAƊANDA BA AMAREN BA*
*MUNA YIN SALOON*
*MUNA DA YADIDDIKAN MATA DA TAKALMAN SU*
_A ƁANGARAN ƘWALAMA KUMA MUNA_
*SIYAR DA ƊANYUN KAJI MASU ARHA DA GIRMA*
*MUNA YIN PEPPER CHICKEN MAI DAƊIN GASKE*
*MUNA SIYAR DA KAJIN BIKI SUNA*
*MUNA DA EXCLUSIVE KAYAN SAWA DON AURE KO SHA'ANI NA FITA KUNYA KU NEMEMU*
*KADA KU MANTA AKWAI KAYAN GWANJO MASU AMINCI MUNA FASA DEALER DAGA NAN HAR SALLAH*

*MUNA DELIVERY NATION KO INA A FAƊIN ƘASAR NAN*

*ADIRESHINMU NA NAN A GARIN KANO MARMARA OPPOSITE ASIBITIN YARA NA MARMARA TITIN NAGODA KU NEME MU A WAƊANNAN NUMBOBIN WAYAR KAMAR HAKA*
08136259679 / 07067338694/ 08036426589/08067336110/08060235089/07048985018 MUNA MARABA DA MASU SIYAN ƊAIƊAI KO SARI AKWAI RAGI NA MUSAMMAN GA WAƊANDA SUKA SAI KAYAN GWANJO MUTUM BIYAR NA FARKO

*MULTI TRADE KANO*🔥🔥
*YANKAN ƘAUNA..!!*🌹

*NA*
*AUTAR MANYA*

ADABI WRITTER'S ASSOCIATION

*13*

Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarci Ƙirjinta a hankali ta soma Rintse idanunta tana jin wani irin Baƙon lamari yana mamaye mata dukkan sassan Jikinta a jikin bango ta rakuɓe kuma taƙi ɗauke idanunta daga Cikin Nashi kamar yadda shima ya kasa ɗauke idanunshi daga kanta Lumshe idanunta tayi tare da sauke wata Ɓoyayyar ajiyar zuciya tana sake Ƙure shi da manyan idanunta Tunda take bata taɓa ganin Namiji mai kyau irin shiba Kyan sa baze misaltu a gare taba sai dai daga kallo ɗaya taji wasu irin sinadarai masu kama da alamun so suna shiga cikin zuciyarta.

A hankali taji saukar amon! muryar shi cikin Kunnenta wadda sauran kaɗan Fitsari ya zubo mata daga Jikinta a ɗan tsawace Kuma da ɗan sauti kaɗan yace mata.

"who are you? And what are you doing in my living room?" Har lokacin Idanunshi suna kanta yana yi mata wani irin sassanyan kallo na ƙasan ido irin kallon da ƙarya ne ka gane ina Mutum yake kallo ajikinka.

Hannayenta ta haɗe tana jin faɗuwar gaba Haɗa magana take yi acikin bakinta amman ta kasa Furta wa sabida wani Irin kwarjini da yayi mata Ji take gaba ɗaya Girman shi ya cika mata wajan duk da ba wani Ƙiba Gare shi ba amman Yana da tsayi sosai Kuma shi ba fari bane Baƙi ne Amman yana da Kyau mai tsayawa a zuciya Musamman Idanunshi Suna da Girma Kuma sun taimaka wajan Fito da zahirin Kyan shi Hancin shi dogo mai ɗan faɗi kaɗan sai madaidaicin Bakin shi wanda yake Ba jaba kuma ba Baƙi ba sai wata irin Ƙasumba data Cika masa Fuska wadda ta haɗe da Gemun shi dayay tsayi sosai Sumar dake Lulluɓe da saman Kanshi ita ta bawa sajen shi damar saukowa ya haɗe da ƙasumba da Gemun shi Yana da ƙaton tabon abin sallah, Gaba ɗaya Jikin shi kwantacciyar Gargasace wadda ta ƙarawa fatar Jikin shi baƙi sai dai Hutu da Jin daɗi sun sami damar taimako wajan ƙara Murje fatar shi tai wani Irin Luwi luwi, Haƙoranshi farare tas sanda yake mata magana Sanye yake Cikin Blue black Trouser sai white shirt wadda ta kama masa Jikinshi sosai daga tsakiyar shirt ɗin a buɗe take wadda ta bawa Ƙirjinshi damar bayyana a zahiri kana iya hango kwantaccen Gashin daya kwanta masa a saman Ƙirjin ya fito har wajan wuyan shi.

A hankali sa'adatu ta saukar da idanunta a ƙasa dan Ko rabin tsayin shi bata kai ba.

Anwar mamakin yarinyar yake mai kama da bebiya sai kuma ƙare masa kallo take kamar taga sabuwar Halitta tsaki yaja tare da daka mata wata razananniyar tsawar data sanyata Zurawa aguje tabar falon A daidai wannan Lokacin ta saki sabuwar ƙaramar wayarta wadda suka siya sanda zasu tawo.

Ya sunkuya ya ɗauke wayar tare da zirata a Pocket ɗinshi dama fita zai zuwa Part Ɗin Innah daga nan kuma ya wuce masjid.
Sabida haka fita yayi daga falon ya rufe Ƙofar part Ɗinshi yana tafe yana jan ƙaramin tsaki yana tunanin ma anya lafiyayyace yarinyar da haka yakai part Ɗin Innah gaba ɗaya suna falo Malam ne ya gangaro da Keken Guragun shi zuwa falo a daidai wannan Lokacin Anwar yake zama a saman One seater ganin Malam yasa ya tashi da sauri ya taimaka masa wajan Turo shi zuwa Cikin falon malam faɗa yake wa Innah akan tabar Tv a kunne bayan tana Jin ana kiran sallah da sauri ta kashe tana bashi Haƙuri Anwar Tura malam yayi suka fita masallaci Koda suka je

Please Login or Register in order to submit comment