Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

MASOYANA READERS NA GAISHEKU,MASU COMMENT AKAN WANNAN NOVEL ALLAH MUKU ALBARKA GABA DAYA INA GANIN SAKON KOWA.



Fafur Omar yaki yarda saima room dinsa daya shige ya bar Iklas waje tana tunanin yanda zata bude kofar,hakura kawai tayi ta kyale Saleem a waje yana jira.tunda Saleem yaji Iklas shuru shuru yasan bazai wuce wannan shedanin yayan nasu bane ya hanata fitowa
Tunda Omar suka bar su Baffa da salati cikinsu ba Wanda ya kara koda tari,Suna a haka Sultan da Raj suka shigo,tambaya suka fara yi Lafiya sunga Mama ta rafka tagumi,da kyar Baffa ya fadawa su Raj halin da ake ciki,suma sosai suka sha mamaki,
Sultan ne ya fara Baffa da kun sani Baku kori Omar ba,da kun barsu sunyi bayani,Omar nasan baya abu ba reason,me yasa ba a fada min a waya ba nazo wajen,Mama kema kin manta halayen Omar masu kyau,na tabbata zai wahala idan Omar zai iya aikata abinda muke zargi,

Raj ma haka ya fada Baffa da Mama sai sukaji dama sun tariyo baya sun tsaya sun saurari Omar,sun yanke hukunci cikin bacin rai,ta leko ta koma ga Omar amma sun koreshi,Baffa ne ya dubi su Raj..Sultan yanzu mafita daya kusa ido a garin nan,da sauran abokan Ku da security duk inda aka ga Omar a kawo minshi har gida,in yaki binsu a kawoshi ta karfi ko da igiya Ku dauroshi a kawo min shi,
Aje a sanarwa mutane,nan take suka fara waya tare da hada connection,shima Baffa haka,kwana 2 tsakani aka sallami Baffa,yana hutawa ya koma gidan su sahar wannan karan sunci sa'a an lallaba iyayen sahar da sahar sun dawo da ita gidan Omar,sahar kuwa dama kudi take so ta karba wajen Omar masu yawa tattalin arzikinta yayi kasa shi yasa ta yarda ta dawo..yayinda da taci gaba da sheke duniyar ta.

Tana nan tana jiran ganin an dawo da Omar gida,bayan dawowar Sahar Baffa da yan uwansa suka je bikon haj.rahina,sai murna su sadiya sukeyi,gogar kuwa dama ta samu rana ta bude mata sai shanya,dama abinda take nema kenan Baffan su Omar ya lallaba ya dawo da ita.
Sultan dasu Raj da sauran mutanensu sun fara aikinsu ba ji ba gani,kullum basa zama Neman Omar sukeyi ba dare ba rana,

Iklas ta gaji ta yanke shawarar sanarwa da Ummi abinda ke faruwa da Ya Omar,tausayinsa takeji sosai gwara ta fada ko Allah zai sa a nemo masa magani,Omar kuwa kullum addua yakeyi sosai akan matsalolinsa,
Yau Ummi ce ta dauko naman ganda ta jikashi a cikin ruwa a wani bowl,Omar ta mikawa da soson karfe da wuka Umaru gyara wannan yau ganda nake son ci,ragadada zan bararraka mana,Omar kuwa bin naman gandar yayi da kallo Ummi wannan tsohon abin tun na last year ai ki bari a siyo mana fresh mana,yaushe za aci guba a ciki,kaga idan baza ku gyaramun ba to na dauke abina ban son iyayin banza,ke uwar yan lissafin duniya matso kema ki tayashi Ku gyara da sauri,yanzu in aka gyara wannan yaji hadi kamshi ne zai cika unguwar nan,murmushi Omar ya saki Wanda ya janyo hankalin Iklas ta kafe Omar da ido tana kallon kyan da murmushi ke masa,
Ummi nifa ban iya gyara abin nan ba cewar Omar tare da toshe hanci,sannu gayu mutanen Allah Iklas matso ki koya masa kuyi maza.

Hand globe Omar ya nemo yasa a hannunsa wai kar hannunsa ya dauki warin naman,Iklas kuwa tuni ta fara gyaran a garin yi ta fallatsowa Omar ruwan a fuskarsa ruwan ya sauka a kumatun Omar,sorry cewar Iklas tare da ci gaba da dirzar gandarta,kyankyami ya kamashi Omar ya fara wanke fuskarsa da ruwa bayan ya gama ya dawo yana wlh kika kara bata min jiki sai na miki wanka da ruwan wanke naman gandar nan,

Baki Iklas ta tabe ya Omar dama shan ice cream ka kaimu shi nake sha'awa muje pls da dare,harara ya watsa mata kin isa ma na kaiki daga nan ki kaini wajen su Baffa ko?haba dai ni na isa da wanne idon zan kalli Mama cewar Iklas to shike nan zan kaiki ke da Suhaila amma yau sai dare zamu fita,dadi Iklas taji sai washe baki take,kara fallatsawa Omar ruwan naman tayi a farar T-shirt din dake jikinsa,
Haushi yaji kin kara bata ni da warin abin nan saboda kin rainani fuskarsa a daure ya dan ebo ya shafawa Iklas a fuska sai daria take tana rokonsa ya bari,yatsunsa ne suka sauka kan lips dinta wani taushi yaji tare da shagala wurin shafasu yana yawo da yatsansa kan lips dinta,goce fuskarta tayi gaskia ya Omar baka kyauta min ba ,jiba face dina ta fada cike da shagwaba kamar zatayi kuka,

Sannu yan mata ni da kika min har sau biyu fa,Ummi ce ta fito daga daki tare da kallon bowl din taga ba abinda suka gyara kawai jagwalgwalo sukeyi musamman Omar ma,dauke bowl dinta tayi tace kuje Ku karaci shashancinku,haba Ummi ki kawo mu karasa miki cewar Omar,a'a kuje na yafe.

Cike da shagwaba Omar yace Ummi kalla rigata yanda jikarki tamini da ita gaskia ta tashi ta wankemin abata,yanda Omar yayi shagwabar abin daria kamar yaron da aka yaye jiya,Sosai ya bawa Ummi daria a ranta tana lallai Omar masu kudin gaskene naira da gata ya gama ratsa jininsu.

Iklas kuwa bata San sanda ta kyalkyale da daria ba dan shagwabar Omar abun daria gashi tayi mugun yi masa kyau,Omar kuwa ya manta Ummi ba Mama bace ga Iklas kusa zata rainashi dan shi a zahirin gaskia bai San yayi bama don kallon Ummi yake kamar Mama.
Daure fuska Omar yayi tare da shigewa room dinsa,kayan jikinsa ya cire ya fito ya fada toilet tare da sake feso sabon wanka kaji fa dan gayu readers,
Wasu kayan ya canja jean fari da wata tsadajjiyar T-shirt baka me rubutu fari an rubuta I do what I want da many an baki,
Kallonsa Ummi tayi Umaru sarkin wanka ga iya shiga oh matarka tana shan kallo.murmushi kadan yayi Ummi kenan na gode.

Kallonsa Iklas tayi da kyar ta iya Jan numfashi sabo da kyan da Omar ya mata,amma a fili tabe baki tayi cike da masifa wai ke Ummi an fada miki ya Omar bafa ya son matarsa kuma fa itama ta tsaneshi kudin sa take so,ita bata son aure tafi son aikin Gomnatinta,kuma yar isk......Omar ne ya cire kafarsa daga hadadden takalminsa ya dora tafin kafar a kan Iklas ya dungura kanta kasa ya danna sabo da Omar a tsaye yake jingine jikin bango yana danna waya.
Ba shiri Iklas tayi shuru tana nishi,Ummi kuwa ta gama gane Iklas kishin Omar takeyi amma ita kanta Iklas bata gane hakan ba.
Iklas ta dauka abin na Omar wasa ne,suna hada Ido taga idonsa ya canja yayi jajir kamar dai ciwonsa zai tashi don jikinsa har rawa yakeyi.da kyar Ummi tazo ta janye Omar tana ke in banda shirmenki Iklas me ya kaiki tsara karya kan matar mutum fada Ummi tayi mata sosai,ita kuwa Iklas mamaki abin na Sir Omar ya bata.

Maza ni yar banza me Jan fadan tsiya kije kiyi wanka ga magrib zatayi,da sauri Iklas ta shige wanka,Omar kuwa sai daya dauki like 5mnt ya dawo normal daga jin yanda zuciyarsa ke masa zafi.
Bayan sunyi sallar isha Iklas ta dan Dasa kwalliya tasha Riga da skert English wears tayi matukar daukan kyau,shape sosai ya fito ta dan yi acuci da gashinta tare da yana mayafi karami,kwas kwas tasha choge,tana fitowa Omar ya watsa mata wani kallon koma ki canja shiga,ba shiri ta juya ta sa shadda dark purple duk cikin kayan da Oga Omar ya mata ne.

Ummi suka yiwa sallama suhaila na bada sautun chocolate, suna fita already mota sabuwa dal tana waje kamar yanda suka saba,yau Omar ba fara'a fuska daure Iklas tsoronsa takeji kar ya shaketa,a tsorace ta miko masa hannunta gashi ka rike kar a samu matsala cike da bacin rai ya fisgi hannun sai da kashinta yayi kara.

Da sauri sukayi take away na abinda suke bukata suka shiga mota,suna hanyar fita daga wurin Sultan da security suka shigo wurin Sultan bai gane motar ba saboda Omar bai fiye yawan hawa mota kala kadan ba,kullum cikin sake motoci yake,

Omar ma bai ga shigowar su Sultan ba yana can ya Lula duniyar tunani,suna dawowa gida a bakin kofar Omar ya tsayar da Iklas kallon kallo sukeyiwa juna,u hv to be very careful wlh kika sake kika fadawa wani yanda ciwo na yake sai nayi maganinki ya fadi tare da tallafe mata keya tas ya zuba mata rankwashi kwas.

Kanta ta dafe tare da turo baki tana dire dire da kafafu kallonta Omar yaa tsaya yi sai kuma yaji ta birgeshi tare da bashi tausayi,nan take ya tsinci Kansa cikin farin ciki gaba daya damuwarsa ta yaye,
Hannu ya mika da niyar rungume ta,ita kuwa Iklas ta zata dukanta zaiyi da gudu ta goce ta zura gida da gudu wayyo Ummi ta fada palon, daria ma ta bawa Omar.
Yau ko girkin dare ba Wanda yaci abunda Omar ya siyo musu shi aka baje aka ci aka sha akayi dam.

Wurin 3wks kenan su Sultan suna aikin neman Omar amma shuru Allah baisa sun hadu da Omar ba,
Ummi kawo mu siyo miki naman miyar cewar Omar,to Umaru kuje da Iklas akwai dan nisa tsakaninmu da wajen da muke siyarwa,yawwa Ummi kinga ma dan wasa kafarmu cewar Iklas tare da zaro hijab dinta iya cinya me hannu,Omar kuwa jallabiya ce fara jikinsa,
Suna fita ya rike hannun Iklas kamar kullum suna tafiya amma Iklas ce kadai ke bashi labarin babanta da babarta da suka rasu,
Sai kallonsu akeyi kamar sabon aure kowanne naji da nasa radadin kyan.
Sunsha tafiya a kafa har baabban titi suka tsallaka sun siyo, sun bar wurin me naman kenan wasu suka parker da motoci wajen guda biyar,kartai ne manya manya wajen su biyar suka fito daga cikin mota daya, basuyi wata wata ba suka fisge hannun Omar daga na Iklas tare da make iklas gefe can har sai da ta fadi kasa,da gudu Omar yayi kanta da niyar dagata,wasu manyan kartin ne suka sake fitowa su hudu,sukayi sama da Omar tare da cusashi a mota,
A gigice Iklas ta kama ihu da fadin barayi Ku taimakamin jama'a sun sace minji,kajifa Iklas wai miji, help me pls my husband oooo shuru babu Wanda ya jita wurin ba mutane gata abj ne,

Motocin sun Fara tafiya Iklas na kuka ta zo tsallaka titi mota ta banketa a kan idon Omar domin yana bayan mota sun daureshi tam tam da igiya saboda sunga ya fara fisge fisge kamar me aljanu,Wanda su basu gane ba ciwon omar ne ya tashi sosai ba Iklas kusa.

Omar na kallon mota ta bige Gomnati ya rushe da kuka a motar kamar yaro,ga zafin ciwo gashi mota ta bige masa iklas Gomnatinsa.
Tuni kartan nan sun sanarwa Baffa da Sultan cewar sun kamo Omar,murna sosai sukayi baren ma Mama.

Omar har yau hawaye yakeyi ga zafin ciwo,duk wani masoyin Omar suna nan sun hallara damkam a compound din gidan,ana son tarbarsa bakin kowa a washe.
Iklas kuwa tuni jama'a sun taru a kanta,labari ya watsu mota ta bige gomnati, kaji fa popular. Wani dan saurayine me dan saukin kyau ya fito daga motar da ta kade Gomnati,baiyi wata wata ba ya sureta sai asibiti.




Asmahbaffa
Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ


65-70


By
Asmahbaffa



Wangale gate din su Omar akayi tare da jera Shiga wakeken rangadeden gidan da motocin gaba daya wannan kartan sukayi,Omar Wanda ya gama galabaita gashi an kawoshi har gidan da bazai iya rayuwa ciki ba,ji yake kamar za a zare masa numfashi yayin da motar da yake ciki ta shiga cikin gidan iyayensa,kafin ka bude ido Omar ya fara shuru shure da make make,gashi an daure shi kamar wani huhun goro,mutanen da suka taru za a tarbi Omar jiran fitowarsa kawai sukeyi suna washe Baku,Abdallah da suleim sai zumudi sukeyi,yayin da kungiyar haj.Rahina suka tsaya suna zage zage da masifa,aikin banza akan wannan fasikin suka wani taru aikin banza cewar Aisha,

Bude motar akayi wasu mutum biyu suka fito da Omar dake cikin mawuyacin hali,Mama salati ta kwada tana hawaye ganin halin da danta yake ciki,da karfi Omar ya fisge kansa tare da girgije kartin nan daga jikinsa sai gasu kasa zube,huci kawai yake yana gurnani,kara ya fasa tare da zubewa kasa a yana ta birgima daga nan ya suma gaba daya numfashinsa ya dauke,mutanen dake wajen ko wanne salati da lahaula yakeyi,Mama kuwa kan Omar ta fada tana kuka haka ma su suleim,da kyar Baffah ya janyesu,su sultan ma har hawaye suka digar tare tausayin Omar,duk wani masoyin Omar sai da ya tausaya masa,su haj.Rahina kadai ke murna tare da shigewa part dinsu suka saki sautin kida.
Sahar dake wajen itama domin sai da aka shigo da Omar sannan tazo wajen tana ganin abinda yakeyi tabe baki tayi ta kalli Baffa ta yatsina baki a kyaishi psychiatric hospital,
Harara Baffa ya watsa mata ya wuce wajen Omar,ita kuwa sahar glass dinta baki ta kafta a fuska ta shige dalleliyar motarta ta koma inda ta fito.
Kwance daurin da akayiwa Omar Sultan yayi,sannan suka taru aka dauki Omar aka kaishi room dinsa Wanda yasha gyara,wasu Allurori Sultan ya masa,gaba daya kowa ya tafi gida Sultan da Raj ne kawai zaune suna jiran tashin Omar suga taya zai farka.
Mama da Baffah harma da su Abdallah suna palon Omar sunyi jugum jugum suna jiran tsammani,Umma Rahina tana ta yiwa frnds dinta waya cike da Murna tana basu labari,haj Binta tana jin labarin haushi taji taga lallai in tayi sake nan gaba Burin Rahina zai cika,don haka tace Sam wlh bazai yiwu Rahina ta fini kudi ba dole na wargatsa shirinta,sai na karya wannan tsafin da ta yiwa Omar. su sadiya kuwa rawa kawai suke takawa.

Hospital Iklas kwance tana bacci saurayin da ya bigeta yana kusa da ita yana jiran tsammani tare da karewa surarta kallo,
Saleem yana jin labari a rude ya fada wajen Ummi,da sauri ta tari saleem yawwa saleem maza ka bimin bayan Iklas daga aikensu amma har dare ya kusa yi,Ummi bafa lfy Iklas wai tana asibiti mota ta bigesu,innalillahi wainnailairrajiun,Ummi sai kuka Suhaila ma hakan dannan in sun mutu Ku fadamin,Ummi ba kuka za kiyi ba zo mu tafi kawai asibitin mu San a wanne hali take,guruf guruf Ummi ta sa takalmi ko mayafima suhaila ce ta mika mata hijab a waje,saleem rike da hannun suhaila suka shiga taxi suna bulayi har Allah yasa wani ya musu kwatancen asibitin da aka kai Gomnati.

Fadawa dakin sukayi sai ganin Gomnati sukayi kwance saurayin na gefe,Ummi da Suhaila sai hawaye suke sharewa,Ummi na oh mun shigesu tsautsayi yasa na aikeku da nasan haka zata faru da ban fara ba sai ta kara fashewa da kuka,saurayi kuwa sai hakuri yake basu,haushinsa ummi taji ta juyo da masifa kwalabar ubanka dan jakar uba zaka dakeni ka hanani kuka ne?

A ransa sai dariar zagin kaka yakeyi,a fili sai hakuri yake bayarwa,kai da Allah ka rufe min baki cewar Ummi.likita ne ya shigo tare da cewar Goggo a daina hayaniya pls ta kusa farkawa,bata da wata matsala Allah ya gajarta wahala.
Likita ina daya saurayinfa?wanne fa?dama su biyu aka bige?da Sauri saurayin yace no kaka wannan kadai na bige banga namiji ba,kan kakane ya kulle to Ina Umarunsu,dole su jira farfadowar Gomnati suji ina Omar ya tafi.sosai Ummi ta damu rashin sanin inda Umarunta ya Shiga.

Baccin 6hrs Omar yayi sannan ya farka,ciwon dai yana nan sai dai Omar jikinsa Sam ba karfi dakyar yake daga yatsansa sabida Allurar da Sultan ya masa.
Hawaye Omar ya fara ga ciwo na cinsa ga tunanin mota ta kade masa Gomnati, Sultan ne ya lura da farkawar Omar,da Sauri shi da Raj suka nufi wajensa,Mama,Baffa dasu Abdallah duk sun banko cikin room din,Omar kuwa ido jajir,ga karkarwar jiki tare da danne saitin zuciyarsa da hannu daya,
Sultan ya kai hannu da niyyar taba Omar amma duk halin da Omar ke ciki saida ya make hannun sultan wai kar ya tabashi,Mama ce ta matsa kusa dashi ta riko hannunsa tare da dora kan Omar a cinyarta tana hawayen tausayi,Omar na jinsa a jikin Mama yaji ciwon ya karu,kuka ya fara tare da rungume Mama yana ajiyar zuciya,Baffa ma hannu yasa ya dago Omar jinginashi a jikinsa,

A hankali Mama tace Babana fada min me ya sameka haka?wacce cuta ce ta sameka haka ka kasa fada mana?wai ni wanne ciwo wannan Banana?
Baffa ma haka ya dinga lallaba Omar yana tambayarsa meke faruwa,amma Omar yaki magana,kwanciya ma yayi kan bed yana numfarfashi.

A hankali Omar yayi magana da kyar muryarsa ke fita,Ba..bazan..iy...iya...zama....nan..Gi...dan...dan..ba,Ku fitar.....da...in....Don't...Allah.
In..kuna... So...na...za...una...Ku can...ja... Min gida...pls
Zuciyarsa ya kara dannewa yana idan....Ku...ka...barni... Nan... Mutu....wa... Zanyi sai hawaye ya ziraro daga idonsa.suma du mutanen dakin sai da suka goge ido.
Yaci gaba da I....na..da matsala...a....lafiyata...Ku...fahim.....ce....ni.
Da sauri mutanen dakin suka hada baki da karfi wallahi mun fahimta mun fahimceka Omar.
Murmushin karfin hali yayi Ku...canja...min...wa...ni gidan....ko.....Ku..nemo...min...Gomnati,
To fa mene kuma Gomnati?cewar Mama
Iklas...na...ke ...nu....fi.a...dubo...min...lafiyarta...mo...ta...ta...kad..e..ta....ku memo...mi...n...ita...itace.....maganina.....da karfi ya kara volume cike da zafin ciwo She IS MY MEDICINE MAMA yana fadin haka ya kara sumewa,Sultan wasu alluran ya kara makawa Omar daga suma yaci gaba da bacci,sannan ga drip ya sa masa.kowannensu ya hallara a Palo suna tattauna maganganun Omar ya za a bullowa lamarin,Sultan yace Baffa da farko dole mu koma Neman Iklas a garin nan ina ganin itace Ummi wacce yake rike hannunta,wacce ta kawo sakon envelop gidan nan,kwarai kuwa Sultan cewar Mama.sannan dole fa a canjawa Omar gida a kaishi wani guess house din cikin gidajensa,kafin a nemo wannan yarinyar,sannan ya dace ayi masa maganinsa Hausa cewar Raj.Baffa ma yace dama hakan na fara tunani kawai.haka suka kwana a palon,baccinsu kadan ne.

Da dare misalin 11 Iklas ta farka da Kuka wiwi kamar ranta zai fita sai shure shure takeyi an sace ya Omar,Ummi wlh wasu ne suka sace oga Omar,yanzu mu yaya zamuyi mun Shiga uku wayyo sir......wayyo Omar dinmu na mutu Ummi...na mutu Ummi....naga ta kaina...mene amfanina a duniya ni kuma Ummi...tawa ta kare...saleem ne ya riketa yana lallashinta da kyar aka samu tayi shuru,taki cin abinci ma wanka kawai tayi ta fara sallah bayan ta wacce ake binta ta koma yin nafeela ba ji ba gani har sai da ta kai 4am sannan Allah ya kawo nurse suka tsira mata Allurar bacci aka shimfideta tare da sa mata drip.

Washe gari da safe aka sallami su Iklas,gaba daya Gomnati ta birkice,bata uhm bare uhm uhm,ta daina ma magana wai duk cikin Bacin ran sace Omar take,damuwa ta shiga sosai su Ummi sai lallashi sukeyi tare da kwantar mata da hankali,Ummi tace kin San fa Baban Umaru me kudine yana can babansa ya sa a dauko masa dansa,ke banza ce wa zai iya sace Umaru,ai ba a satar manyan mutane yara ake sacewa idan aka dafa su ance sunfi manya dadi..Iklas kuwa dadi taji wai ba a sace Omar ba,daria ta saki kuma fa hakane Ummi ko a radio cigiyar yara kadai akeyi,can mintuna kadan suna Shiga gida Iklas ta fara kuka tayi missing din Omar sai gidan yayi wani iri,

Tunowa tayi da cutar Omar yanzu tasan ma yana can ta tashi kukanta ta kara sautinsa sannan ta ruga da gudu jikin Ummi ta jata Palo suka zauna sannan Iklas ta kwashe labarin cutar Omar ta fadawa Ummi

Ummi ma harda kuka Allah sarki Umaru,Iklas wayon banza ne dake me yasa baki fada min da wuri ba,wannan aikin sihiri da jinnu ne da tuni munyi kokarinmu an karya abin.nan Iklas ta Kara bawa Ummi labarin gidan su Omar kaf,harda dukan da aka mata su sadiya,da sahar matar Omar.sosai Ummi taji haushin Iklas da bata sanar mata ba.
Ke rabu dani shashashar banza gashi nan ai kin jawo matsala da kin fada tun wuri da tuni haka bata faru ba,Ummi shi yace kar na fadawa kowa,yaushe dama ababen dake jikinsa zasu bari ya fada kar a masa addua.

Ummi gobe muje gidan su ya Omar mu gani,ban yarda ba Iklas ki bari tukun muga abinda Allah zaiyi...kawai muyi masa addua,jiki sanyaye tana kwalla tace to Ummi sai kuma kuka ya kwace mata ta rufe ido da tafin hannunta biyo tana tunowa da rayuwar da sukayi tare da Omar.
Yanda ya taimakesu,yake hanata kula kowa,kula dasu,yanda suke fada da kuma wasa da dariya.
Kara tunowa tayi sanda ya shafa mata ruwan naman ganda a fuska sai kuma ta fara daria ga kuma kuka da hawaye duk ita kadai.

Ummi kuwa tausayi Iklas take bata,Suhaila ma damuwa ta shiga babu me siyo mata kayan sawa da sweet.da Sauri Iklas ta shige dakin Omar tana shakar kamshinsa tare da kwancia a bed din tana tunanin lokacin da taga Omar a mota tana talla a kwalta,yanda take kwala masa Kira ta glass din window tana Oga tare da daga hannu,murmushin da Omar ya sakar mata a lokacin shi ta tuna.

Mikewa tayi ta cire kayan jikinta tare da daukan singlet din omar fara tasa, sannan tasa wandonsa short fari tayi kyau dama gata fara,ga gashi har tsakiyar baya.lekowa dakin Ummi tayi taga shigar Iklas daria Ummi tayi ta koma kitchen.Iklas kuwa mayyar Omar a dakinsa ta kwana tana jin kamshi tasha bacci kuwa ji tayi kamar ta rungume Omar shi yasa tayi bacci sosai.

Omar washe gari haka ya farka da ciwonsa yana a nemo min Magani ta,Iklas Mama kuma a fitar dani daga gidan nan,bakwa tausayina Baffa?ba shiri Su Sultan suka sashi Mota tare da kaishi wani rantsatsen gida ga yan aiki da security ko ina.Alhmdllh kuma Omar ya dan ji sauki sauki,har yayi wanka da kyar tare da cin abinci abincin ma saida Raj yace in bai ci ba baza a memo masa Gomnati ba.


Please Login or Register in order to submit comment