Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wani babban malamin Izala Baffah ya fadawa matsalar Omar,malamin yace Ku nemo yarinyar da yaron naka yace Alhaji sannan nasan wacce addua zan tofa masa a ruwa yasha.dole sai naga yarinyar na mata wasu tambayoyi sannan ayi addua.

Address din gidan su Iklas Omar ya bawa Su Sultan, gaba daya Mama,Raj,Baffa da Sultan suka rankaya zuwa jin ya lafiyar Iklas da kuma daukota a kawowa Omar maganinsa.








Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

70-75

By
Asmahbaffa


KUNA BIRGENI MASU COMMENTING KUNE NAWA .KHADY CHAFE ALBARKA.



Tsala tsalan motoci har biyu suka dau hanya daya motar Mama da Baffa dayar Sultan da Raj Yanda suka ga unguwar su Iklas ta talauci basuyi zaton zasu ga gidan su Iklas me kyau haka ba,sallama sukayi Mama ta kutsa kai cikin gidan,Ummi da Suhaila suna Palo suna kallo,Iklas kuwa tana dakin Omar sai kuka da tunaninsa takeyi gaba daya ta rame sabo da bata cin abinci,
Kamar kullum yauma sanye take da jallabiyar Omar milk color tana kan bed din sai shinshina wata T-shirt dinsa takeyi tana lumshe ido,gaisawa Mama sukayi da Ummi dama nice mahaifiyar Omar da sauri Ummi ta zabura Umaru Dana sani yaron kirki dan mutunci? sai Ummi ta fara kuka yaron da muke ta nema an saceshi,ki kwantar da hankalinki Omar yana wajenmu bari a kira sauran Mazan ma kiji bayanin komai cewar Mama.

Da sauri Mama ta kira su Baffa su shigo,suna shigowa kowanne ya zauna a kujera,Ummi ce tace ina zuwa bayin Allah,a sukwane cike da murna ta shiga wajen Iklas tashi anga Umaru Ashe yana wajen Mamansa,gasu can yan uwansa sunzo domin yi mana bayani ki fito ayi a gabanki,ki fara kawo musu lemo da sauran kayan dadi,
Iklas tsalle ta dira tare da murna kamar bakinta zai yage,rawa ta farayi tana Anga ya Omar...duniya sabuwa fil a kwali,ras nake jina wlh yau bacci harda munshari kuma zuwa wajen Omar ko ba tayar mota eh....eh....eh...Omarun mu.tana juyi.daria Ummi tayi tare da komawa wajen baki suna gaisawa.

Iklas tsabar Murna ta Manta Rigar Omar ce a jikinta ta fito palon Gaba daya bakin suka zubawa Iklas ido,Raj ya zunguri Sultan a lallai dole mutumin ya rude yarinyar ba karya,gaskia dai cewar Sultan kaga ma rigar namijice jikinta kuma wlh kamar size din Omar ce rigar,Raj yace kuma ta mata kyau wlh.
Baffa ma sosai ya tabbatar wannan Ummi ce me kai sako gidansu me hankalin nan.
Mama kuwa ita dai tana son ummi bata San me yasa ba.Masu karatu karku manta Iklas da suna Ummi tayi amfani a gidan su Omar lokacin da takai sakon takarda.

Tsugunawa Iklas tayi har kasa farin cikinta yaki boyuwa haka ta gaishesu baki kamar gonar auduga,kitchen ta wuce ta kawo musu lemuka da snacks,sannan ta nemi wuri gefen Ummi a kasa ta zauna,
Baffa ne ya fara magana tare da basu labarin gidansa da komai nasa tas har lokacin da Omar ya bar gida,haka Mama ma,sannan Iklas ta basu tun farkon haduwarta da Omar har karshen da aka daukeshi mota ta bigeta,
Godiya sosai su Baffa suka yiwa su Ummi suma su Suka musu tasu.Mama harda bawa Iklas Hakurin ci mata fuska da sukayi da kazafi,Mama ta kalli Iklas 'Yata Ashe sunanki Iklas ko ?Murmushi Iklas tayi Tare da sunkuyar da kai kasa cike da kunya tace ayi min afwa Mama.'yar kaniya cewar Ummi.

Baffa ne yayi gyaran Murya ya roki alfarmar Ummi ta bashi Aron Iklas za a yiwa Omar magani,ita kuma Mama shawara ta kawo akan a daura aure tsakanin Omar da Iklas kawai tunda yana rike hannunta haka kuma ba san ranar warkewarsa ba,idan kuwa matarsa ce komai zaizo da sauki,sabo da gudun shedan gwara idan da aurensu ba Wanda zai damu.
Ummi ce tayi magana duk naji batunku gaskia sai dai na Baku Aron Iklas sabida ko sec schl bata gama ba,kuma Allah gatanmu ita ce gatanmu,sannan Ummi itama ta fara basu tarihinsu Iklas kaf.sun tausayawa su Iklas gaskia.

Baffa ne yayi magana Kaka gaskia abin a tausaya muku ne,kuma lallai Omar yayi abin kirki, wato ni Ku koma gidana da zama ke da kanwar Iklas, zan dau nauyinku babu matsala,kome kuke so ba matsala ga part din Maman Omar ne a wajenta zaku zauna abinda kuke so shi za ayi,kuma munyi muku Alkawari baza a fadawa Omar wannan auren ba har sai shi da kansa yace yana sonta zai aureta sannan mu bayyana masa,gudun kar mu aura masa ya zalinceta ma tunda babu wanda yasan zuciyarsa itama kuma yarinya haka ya dace ace da aure tsakaninsu amma bai dace ace kamarsu suna taba jikin juna ba kuma da niyyar magani shedan ake gudu.

ummi ma ta yarda da maganar su Mama kuma idan Iklas ta auri Umaru to tayi dacen miji.Ummi tace Alhaji na yarda da zancenku amma rigimar gidanka nake tsoro,karki damu Ummi nan gidan da kuke ciki Ku zuba yan haya Ku koma gidana fatanmu ki amince a daura musu aure.
Kefa 'yata?ya kika gani kin amince cewar Baffa yana kallon Iklas,har Ga Allah Iklas bata son aure yanzu gashi ko schl bata gama ba bare ta fara aikin Gomnati burinta.ita burinta ta fara aikin Gomnati sannan tayi aure ko banza ta huce takaicin da namiji.ga kawarta Fauziya kwanan nan ta samu teaching amma sai wanka take dauka rannan ma ta siyi fili a garin Abuja,ba ruwanta fantamawa take amma ita auren wuri za a mata abin haushi.
Mata sai ci gaba sukeyi ita kuwa mijin ma da za a bata bai San ya aureta ba,ba sonta yake ba,gashi me mata,wlh badan Omar bane da ko sama da kasa zata hade baza ta taba aurensa ba.

Amma kunyar Baffa da tuna Alkhairin da Omar ya musu,ya maidasu mutane yasa Iklas tace ta Amince kallonta kaka tayi tana mamaki,la..la...la..kaji yar banza mara kunya shi yasa gata nan kullum kayan Omaru take sawa daria akayi gaba daya tare da zuba mata ido.
Turo baki Iklas tayi cike da shagwaba kai Ummi komai sai disgani.yo in ba munafunci ba me ya kaiki ko kunya babu wai ae kin amince.dama na Dade da ganoki.cuno baki Iklas tayi tare da shigewa daki.Sultan ne ya kalli Raj sukayi daria yace lallai Omar dan Iskane shi yaga abinda ya gani yarinyar tayi fa.

A wajen Baffa ya kira yan Uwansa 20mnt suka zo su uku,Baffa da dayan dattijon walliyan Iklas,sauran kuma sukayiwa Omar,nan take suka dan taru a masallacin Unguwar harda liman nan aka daura Auren OMAR MOHD DA IKLAS,Iklas haushi ma taji an mata aure tana karama gaskia an dauki hakkinta dan ma tana so taga Omar.

Baffa kuwa saida ya gargadi yan uwansa na Amana kada su fadawa Omar an daura masa aure.Baffa sun shigo gidan Alhmdllh an daura Ummi yanzu Ku yi shiri kayan sawa kawai zaku dauka Sultan zasu zo a daukeku Gobe insha'Allah,lefenta da sauransu duk zan mata komai idan lokaci yayi,duk da haka yanzu Mama zata hada mata akwatuna set ko 4 ne kafin na lefe suzo. Allah sa Albarka cewar Ummi.
Sallama sukayiwa Ummi suka tafi cike da Murna.

Ba Wanda yasan me akayi,saleem yana wajen aiki bai San komai.Ummi da Suhaila Kadai su suka gama shirya kayan tas,Iklas na daki tana kuka an daura mata aure bata fara Aikin Gomnati ba.shike nan miji zai rainata,komai sai ta tambaya.Ummi ce ta sameta a daki ta fara fada ke wato baki San lallashi ba ko,akan an miki aure kike kuka,Gata fa akayimiki,samun miji irin Omar ai sai an tona,Allah ya rufa mana asiri kina hauka,kin fi so mu tagayyara ana kiranku goyon kaka,'yayan mace,in ma zaki daina wlh ki daina taimakonmu sukayi mune abun tausayi idan kince bakya sonsa mata Dari zasu soshi,

Da Sauri Iklas ta shigo ai wlh ba a isa an aure Omar ba shi din banza ya Isa ma,itama matar tasa na tsaneta.daria Ummi tayi to kince ba kya sonsa kuma...to wai ke Ummi nifa aikin Gomnati nake ji kar ya hanani.

Yau naji shashasha ke ai Hutu kika samu,to bari kiji mata masu mushen tunani su ke tunanin sai sunyi aiki Gomnati za su sayi sabulu ko Omon wanki,Idan kin cika mace ba abinda miji bazai miki ba.Aikin mace shima yana da amfani,amma ki gane ko bakiyi boko ba indai mijinki na dashi kina kyautata masa ta ko ina baki Gaza ba to ba wani matsayi da baza ki taka ba.

Mata nawane ko A basu sani ba kuma suka zaga kasashe, sun hau motoci na Alfarma, duk wani jin dadin duniya sun gama ji duk ta silar miji, suci takaucinsu tare kuma yayi kudi ki famtama sai marasa tsoron Allah Wanda nasan Omar baya cikin irinsu.

Haka Ummi tayi ta yiwa Iklas nasiha da koya mata dabarun aure.
Iklas kuwa jin Ummi takeyi tasa a ranta dole fa sai tayi aikin Gomnati domin ta tsaya da kafafunta.

Washe gari da misalin 5pm Sultan da Raj sunzo da dankara dankaran motoci guda biyu daya aka zuba kayan akwatunan su Iklas daya kuma aka kwashe su sai city.Iklas kirmishishi bata kuka ganinsu tare da su Ummi.

Tun daga gate Ummi da Suhaila suke kallon haduwa,suna fitowa daga Mota Najja kanwar su sadiya ta fito da gudu ta koma part dinsu tare da kiran gaba daya sis dinta har Umma kallon su Iklas sukeyi ta wani window suna kus kus,Sadiya tace Ku kyale munafukai zamu gano kulla kullar da makirar tayi, wlh duk sai munci Ubansu sai sun bar gidan nan.

Suhaila daki daya aka hadasu da Suleim,Abdallah sai wani likewa Suhaila yakeyi,Iklas kuwa cewa tayi wajen Ummi zata zauna Mama tace ki dai zauna kawai amma Mijinki Marar lfy fa bari dai tukun a kawo Omar anjima mu gani inda yuwuwar zaman zai kasance.

Sahar kuwa tuni ta kara guduwa gidansu wai Omar yahaukace,iyayenta sukace tayi zamanta dan kar ma a kawo Mahaukaci Omar watarana ya sheke musu yarsu tilo.

Omar a daddafe yayi Sallar isha su Sultan suka daukoshi a mota sai gida,Raj gani yayi Omar kamar zai mutu tun kafin su Karasa gate ya kira Mama a waya cewar ta turo musu Iklas waje Ita kadai zata iya shigo da Omar gidan.

Rankatakaf Mama, Iklas, Ummi dasu Abdallah suka fito Baffa shigowarsa kenan daga masallaci shima yaci Birki wajen motar su Sultan.

Da kyar su Raj suka fito da Omar daga mota,Kamshin Iklas Omar yaji da sauri cikin mawuyacin hali ya dago kasa ai kuwa sukayi 4eye da Iklas wacce tuni ta fara kukan tausayin Omar duk ya rame ya fita a tunaninsa, Da kyar Omar ya wara hannayensa biyu cewar Iklas tazo gareshi.Mutanen dake wurin sai kallon su sukeyi cike da tausayi. Su sadiya ma suna daga cikin gate sun leko ta wata yar kafa.

Iklas da gudu ta karasa wajen Omar tare da fadawa jikinsa tayi lamo a kirjinsa shi kuwa ya kankameta a jikinsa,hannuwanta tasa tare da tallafo kumatunsa tana Sir sannu ya Omar ciwon nan ya baka wahala,Iklas ina ta Neman ki su Mama basa tausayina,no ya Omar sunfi kowa tausayinka fa,riko hannunsa tayi zo muje na baka abinci juyowa sukayi sai sannan Iklas ta tuna da mutane a wurin kunya taji zata zame hannunta daga na Omar taji ya kara damkeshi rada ya mata a kunne muje ni wlh yunwa nakeji.

Su kuwa su Mama Murna da Mamaki sukeyi ganin Omar na Rike Iklas ya warke ya dawo sumul Mutum kamar kowa.Sultan ne yayiwa Iklas Magana ya kika tsaya kuma kuje ciki gamu nan zuwa,ki kaishi part dinsa akwai komai ciki har abinci an kai.




Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GIMNATI
ⓂⓂⓂ

75-80

By
Asmabaffa



WANNAN SHAFIN NAKUNE MASOYANA.




Rike yake da hannunta har suka shiga part din Omar.Su sadiya wani uban tsaki suka ja Ashe shegiyar marar kunyar yarinyar nan ce take wannan iyayayin da shishigi, Aisha tace haba no wonder ina ganinta naji na tsaneta Ashe yar bakin gida ce wlh sai tayi dana sanin zuwa gidan nan.
Part dinsu suka koma kowa na fadin kalar nata muguntar da zasuyiwa Iklas.har palonsa Iklas ta kaishi dole tare suka zauna kamar chewgum haka ta zuba masa abinci ya tsaya yaci sosai da yawa sai da yajishi dam sannan ya Kali Iklas ina Ummi da Suhaila yanzu zasu shigo Good yace.

Yana son ya saki hannun Iklas Gudun kar Mama ta ganshi yana jin kunya gata ita ba matarsa ba,yana wannan tunani su Mama suka shigo gaba dayansu,suna masa sannu,mamakin Omar yaga Sam su Ummi basu damu ba da suka ganshi rike da Iklas.
Baffa ne ya shigo tare da malamin nan kowa waje ya samu ya zauna,Malam Usman ya kalli Baffa yace Alhmdllh mun godewa Allah lallai Allah da iko yake,dama Baffa ya sanarwa Malam usman batun auren da sukayiwa Omar yaji dadi shima malamin yace dakyau kar a sanarwa kowa yanzu tukun a bari ya warke. yanzu wannan yarinyar dole ta zauna kusa dashi har ya gama shan ruwan adduarsa Wanda a kalla na 3wks ne,a dakinsa zata dinga kwana dashi har agama komai,Omar kansa ya kulle sabo da cuta za a sabawa Allah su kwana 1room da wata.

Kallon Baffa yayi Baffa kwana 1room da itafa haramunne za a sabawa Allah,karka damu Umaru ba abinda zai faru mun yarda daku,ta lafiyarka mukeyi cewar Ummi.
Shuru Omar yayi zuciyarsa cike da tsoro,kwalayen ruwan faro aka shigo dasu na addua,dama malamin yanda sukeyi Ku zaku kawo ruwan roba carton din dasu ke addua ciki su Baku abunku a tsaftace ba shan cuta,Omar ma su Baffa kwali biyu suka kai na faro,sai kudin su za a basu masu tsada domin dubu Dari da hamsin malam usman ke yi ba ragi.

Bayanin maganin ya fara musu a bashi yasha da safe Rabin jarka ragowar Rabin kuma da dare ya zauna a kan towel a shafe masa shi a jiki gaba daya,ga wannan ya mika musu man zaitun shima an Masa addua ciki kullum a shafa masa da dare a jikinsa,yau Ku fara bashi su.kome ake ciki Alh kamin waya..Godiya sukayi Masa ya mike ya tafi.
Sultan da Raj ma jaddadawa Iklas sukayi kan ta kular musu da abokinsu sannan suka tafi gida,tuni su Suhaila sunyi bacci,Mama yau har hira kadan sukayi da Omar ammafa har yau rike yake da hannun Iklas,hannunta yayi gumi ya gaji.

Baffa ma jaddawa Iklas yayi cewar ta kula da Omar ta Saki jiki ba kunya.sanna suka wuce part dinsu ita da Baffa,Ummi ma tayi nata sannan ta tafi,shi kam Omar tunani yake wai meke damun su Mama zasu hadashi daki daya da balagaggiya
Kallon Iklas yayi yaga ita Sam ko a jikinta,harkarta takeyi tana latsa waya.kina jin fa su Mama wai ki kwana Room dina,ba tare da ta kalleshi ba tace to ya na iya?me zan yi ciki lfy fa za a nema maka.muje ciki kayi wanka ,fuska ya daure in sa'ankine zaki dinga sani abu wai?ko na miki kama da yaronki?lallai ka samu lfy sir ,muje pls ni bacci nakeji gwara ma ka taso,ni dai yarinya baki isa kin hau bed dina ba wlh,ba dan iska bane ni.

Murmushi Iklas tayi to badan tsoro ba ka sakar min hannu mana yanzu a gani,baza a saki ba din,to kaga kuwa ai Kaine babban......sai ta tuna Oga ne fa wannan da sauri ta kulle bakin ta,saukar wasu rankwashi taji kwas masu zafi a kanta Omar ya zuba mata,
Ouchshsh.....tayi kara tana Sosa kai,shice da shagwaba tace da zafifa zaka kasa kwakwalwata ta hadu da jini.
Mikewa yayi rike da hannunta suka shiga Room dinsa,sakin hannunta yayi ya shiga toilet da kyar yayi wanka saboda ciwon ya tashi,kafin ya fito ta dauko kayan baccinsa tana ta sauri ya fito kar ciwon yayi karfi,
Ai kuwa a wahale ya fito da sauri ta matsa kusa dashi ta rike hannunsa sai dayaji ya dawo normal ya kwace hannun ke nifa kina yawan sani aikata sabo kin dameni fuska daure yayi maganar,
Fushi Iklas tayi ta mike fuuu ta dauko maganinsa da malamin ya kawo,to ko shima wannan din baza ka sha ba,ae bazan sha ba kije kira min Mama, fita tayi direct part din Mama taje kofa ta kwankwasa Mama ta fito Iklas lfy? Wlh Mama Ku fada masa ni matarsa ce yaki yarda ma yasha maganin komai fada yake min wai iskanci ne,kalla inda ya rankwasheni fa Mama,

Kuma yace kije wai, murmushi mama tayi rigimamme ke kuma in banda abinki hakuri akeyi ai da marar lfy kuma kin San bai San matarsa bace ke,ni bazanje ba babu abinda zan masa kece me yin duk abinda ya dace kuma mun koya miki komai sabo da haka kije kowa yaji da mijinsa,nauyi ne kanki kije ki kula da mijinki.

Jeki Allah tashe mu lfy,komawa iklas tayi itafa an takura mata an lakaba mata aure.komawa tayi ta sameshi ciwo ya tashi gadon tahau ko kulashi batayi ba ta dauko addua ruwan faro ta tsiyaya a glass cup ta mikar dashi zaune da yake ciwon na cinsa karba yayi ya sha,ta kara bashi sai da ya sha rabi kamar yanda malam yace sannan ta dauko zaitun nan ma da kyar ya bari ta shafa masa yana ta lumshe ido sabo da dadin yanda take shafa masa kamar kar ta daina,sai mamaki yakeyi yarinya karama da abun mamaki,kato dashi take iya kula dashi haka,rigar ta dakko zata sa masa ya bige hannunta kin ma isa ke wai ni danki ne?mikewa tayi ta koma wata hadaddiyar kujera ta hutu ta kwanta,badai haka zaki kwana ba? kazama kije kiyi wanka,itakam ta gaji mikewa tayi tayi wankanta ta fito sanye da kayan jikinta,kije ki dauko kaya mana,mikewa tayi ga mamakin Omar yaga ta bude sip dinsa ta dauko farar jallabiyarsa ta koma toilet ta fito sanye da ita a jikinta,tayi kyau sosai.shanya waccan kayan tayi a toilet dinsa,fresh milk ta tsiyayo ta bawa Omar a baki ta sha itama suka kora ruwa tayi kwanciyarta,shi kuwa Omar ciwonsa yakeji,sai masifu yake karba

Iklas tuni tayi nisa a bacci bata San me yake ciki ba,karfe daya na dare nishin Omar ya tasheta da gudu ta haura kan bed din yau ciwon na Omar ya banbanta da Wanda yakeyi wannan nishi kawai yake fitarwa da gumi shar shar,
Iklas sosai take tausayawa Omar halin da yake ciki,tallafoshi tayi jikinta da kyar ta iya daura kansa a cinyarta ta jingina da jikin bed sai addua take tofa masa tare da shafa kansa,Omar bai San halin da yake ciki ba kawai dai yaji ciwon ya warke nan take bacci ya kwasheshi,Iklas tun tana masa addua har itama tayi baccinta a zaune jingine da bango hannunta kan sumar Omar haka suka kusa kwana,wurin 4am ta zameshi Daga cinyarta ta kifa jikinta ana Omar gashinta me matukar tsayi ya rufesu basu ma san a yanda suke ba haka suka dinga kwasar bacci,har rana ta fito basu sani ba,9am Mama da Ummi suka nufi dakin dan ganin ko lfy anjisu shuru,

Ummi ce ta fara murda handle din tana zura kanta ta juyo ta fito tana mu koma Hajia yaran nan yan zamani ne ,Iklas ba kunya gareta ba ,murmushi Mama tayi tace Allah dai yasa karta fadawa Babana nafiso ya fara furtawaa tukun...to ameen dai cewar Ummi.

10:30am Omar ne ya fara farkawa ji yayi kamar an danneshi hannu yasa zai ture Iklas daga jikinsa dan shi ya manta ma akwai Iklas,bai sani ba dai dai boobs dinta hannunsa ya sauka wani lutsum yaji kamar ya sa a flour,da sauri ya cire hannuwansa ya janye jikinsa,sai sannan yaga Iklas ce, a ransa yace kan uba dama yarinyar nan a bed dina ta kwana?
Wannan batajin magana mayyar mazace,amma koma me ya faru su Mama ne suka jawo wlh ni ba ruwana.tunanin irin laushin jikin Iklas da yaji yakeyi,shi kam gaskia yarinyar nan zata tasar masa da sha'awar da zai kasa control.

Da wannan tunanin ya shige toilet,Iklas kuwa tun farkawar Omar ta farka kunya ce ta hanata bude ido,kai yau sunsha bacci me dadi,Iklas tace yau na shaki kamshinsa da yawa bama na rigarsa ba na jikinsa.

Mikewa tayi tare da mika ta gantsare tana salati sai murmushi takeyi ta fice daga room din da gudu,tana zuwa Palon Mama taja birki tayi turus ganin,Baffah, Mama, Ummi, Sultan da Raj.suhaila suna room suna buga game,Abdallah na koya mata da suleim.
Kunyace ta kama Iklas musamman da tasan da jallabiyar Omar sanye jikinta,ganinta za ace mata mayyar miji,tunda Omar bai San da auren ba.
Komawa tayi Inda ta fito da gudu su Mama kuwa daria ma ta basu,tana shiga dakin Omar ya fito daga wanka idonsa jajir yana jin ciwon amma ba kamar na da ba,da sauki sauki,
Kallon Iklas yayi wai nikam tare aka haifemu ko mene,kin hanani sakewa sai kallon tsaraicina kikeyi bazan dauki wannan abunba ni,to ka bari nayi wanka nayi tafiyata mana.na fita wurin Mama naga mutane su sultan da Raj,

Masifa ya fara yanzu a haka kika je maza suka ganki,jikinki fa yayi showing,Su Raj sunganki?ae har muka gaisa haushi Omar yaji da tsananin kishi baisan dalili ba.a tsawace yace Shiga kiyi wanka ki fitar min daga room,kuma ba ruwanki da ciwona na mutu ma mene damuwarki.

Masifa kai ya Omar wallahi kasha ruwan alwala da cikin zafin nama ya rikota yana nunata da yatsansa kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa tunawa da yayi yanda take matukar kula dashi,damuwa da damuwarsa sakinta yayi kinci sa'a,kuka tuni ya kwacewa Iklas,
Omar kuwa ji yayi ransa ya baci yasa Iklas kuka.

Daga shi sai guntun towel iya kugu da wani a wuyansa karami farare jikinsa sai shining yakeyi ruwa dis dis.Matsawa yayi sosai kusa da ita wani shock yakeji itama wani abu taji yana fisgarta kamar ta rungumeshi,gudun kar alwalarsa ta karye kawai sai ya koma baya yana to me namiki kike kuka,kin kula shi tayi tana kukanta,to sorry yi shuru kinji Gomnati,sai kinyi Gomnati Allah dai ya biya Gomnati ba a ja daku.....daria ce ta kama Iklas sai kuwa ta fara kyal..kyal..kyal...Omar kuwa ci gaba yayi kamota nan

Please Login or Register in order to submit comment