Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamota nan sai daria sukayi gaba dayansu tuni Iklas ta share hawayenta,shi kuwa Omar shagala yayi da kallon Iklas Tana dariar birgewa.Wani kayataccen kallo yake mata da yasa ta kasa jurewa ta shige toilet.da Sauri Omar ya shirya dan kar ciwo yaci karfinsa. Sallah yayi yau har nafeela yayi.inye su Omar an fara farfadowa.
kayanta na jiya Iklas tasa ta fito itama tayi sallah da addua.
Kafin ta idar tuni Omar ciwo yayi karfi.

Zama tayi kusa dashi,kafadar ta tana gugan tasa sai ga Omar ya warke.hannunsa ta kama suka fita sashen Mama. Gaba daya suna palon ana jiransu kuwa.
Kwace hannunsa Omar yayi ya koma jikin Baffah yana gaishe da kowa tare da musu Godiya.kowa ya jiki sukayi masa,tafawa sukayi da Sultan da Raj suna masa signa da ido suna kallon Iklas.

Duk yanda yaso dannewa sai da suka bashi daria.Iklas kuwa suna gaisawa ta tafi dakin Ummi,tsantsara kwalliya tayi ta sa wata atamfa super cikin kayan da Omar ya taba dinka mata,bata taba sawa ba sai yau.Riga da skert sun kamata das tayi kyau,tasa red jambaki in ka ganta sai ka rantse yar shugaban kasasun

Sai kamshi takeyi ta fito kowa kallonta yakeyi ,Omar ji yake kamar ya lasheta duk da cewar ciwo ya fara cinsa,su Baffah ciwon omar daure musu kai yakeyi.

Gomnati na zuwa taji kunyar rike Omar gaban su Mama,Gaba daya barin palon sukayi,Sultan da Raj ne kawai suka zauna ganin kwakwaf.
Omar sanye da wando 3quatr marar nauyi baki da blue,rigarsa blue itama,Iklas zama tayi kusa dashi wai kunyar Raj taji sai ta sa hannunta kasan cinyarta,ta danne hannun da cinya a hankali ta dinga tura hannun ta kasanta har ta tabo cinyar Omar.bata sani ba su Sultan na kallonta ai kuwa suka kwashe da daria,Raj yace mu ki daina kunyar mu ki kularmana da Frnd.ga breakfast dinku can.
Harara Omar ya zuba musu ya fara magana.





Asmabaffa
[8:58AM, 4/10/2018] ‪+234 810 468 7075‬: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

80-85


By
Asmabaffa



READERS PLS A DINGA HAKURI DANI IDAN ANGA TYPING ERROR.JINJINA GAREKU CIKIN CONTAINER.



To kome ya faru ai da laifinku kuna gani an hadani zama da baliga waje daya ko muharramata bai dace ba akan wani magani,idan ban warke bafa kunsa ina ta aikata sabon Allah.
Murmushi sukayi Sultan yace kaji munafiki Raj wai mu zai dinga Rainawa hankali shi a dole Ustaz,kyaleshi mu wuce zanje office ni cewar Raj tare da mikewa,Omar ya fara gaku nan yan iskan gwauraye kullum Ku dami mutum,daria sukayi calm down Frnd da me ka fimu?mene marabar kwado da gaya,gwara mu bamu dandana ba kai fa tunda ka dandana kullum a damuwa kake cewar Sultan, tuni Iklas ta toshe kunnuwanta jin musun da suka fara yafi karfin kunnenta.
Kun auna arziki da wannan yarinyar wajen da sai kun gane kurenku cewar Omar.su sun manta Iklas na wurin.ficewa sukayi kowanne ya nufi office.

Mikewa Omar yayi tare da fincikar Iklas zuwa dining,ina zuwa ta mike tare da komawa room din Omar ta dauko maganinsa ta dawo.

Kafin aci komai zaka sha wannan fa kar a manta,yatsina fuska yayi Oh my God wlh kina takura min a duniya why kike min haka wai haka kawai zaki dinga bani wahala kina sani yawan magana,tsoro taji yanda taga yana kakkafe ido sabo da fadansa
Hannunsa ta kara rikewa sosai haba ya Omar kana wahalar da shari'a kasanfa abinda ya kawo ni hidanku in baza ka sha ba zan bar gidan nan kawai ta fada da kalar tausayi,to ki tafi mana wani ya kawoki,gata fa ake maka,lfy ake nema maka,haba sir.karba kasha kaji....bazan sha bafa abunda jiya tsutsa na gani cikin ruwan,kai ya Omar kaji tsoron Allah wannan ruwan da yake neat,to yanzu ma gasu can ina gani a ciki.fafur Omar yaki shan magani wai tsutsotsine da ruwan
Abincin dining Iklas ta kwashe to wlh baza kaci ba sai ka sha magani.idon Omar yayi jajir ya dago wlh ba Wanda ya isa ya bani magani,ko Mama ce? Eh ko waye na fada muku.
Matsawa yayi zai damko Iklas wayyyyooooo Mama ta kwashe da gudu,fitowa su Mama sukayi gaba daya har Baffah ana lfy Iklas.tana haki tace wlh bazan iya ba zaneni zaiyi fa akan magani yaki sha wai tsutsa ne ciki.
Baffa ne ya kira malam a waya ya fada masa komai,daria malamin yayi yace alhmdllh aiki yana kyau,dole ayi masa wayo yasha,karku damu sharrin jinnu ne komai zai warware insha'allah.

Baffa ne ya lallashi Iklas kan ta jaraba bashi ita kadai zai yarda da ita.komawa sukayi daki akabar Iklas a tsorace.dabara ce ta fado mata
Dakin Ummi ta shiga kamar gaske ta jawo akwati ta wuce ta gaban Omar Wanda ciwonsa tuni ya tashi,a gigice ya kalleta,gyale ta dauko ta yafa tana fadin tunda mutum yaki shan magani mene amfanin zaman sai na tafi gida ai bazan bari wani ya sake ganina a duniya ba.
Da Omar ya shareta sai kuma yaga da gaske takeyi domin har ta fita compound na gidan.

Iklas kuwa na fita suka ci karo da Aisha tana leken munafunci a kofar part din su Mama.zuwa tayi wajen Iklas tana yatsina fuska cike da rashin mutunci,su munafuka kuma nan aka dawo kenan aka tare,yayan matsiyata dangin jaraba yayan tsinaniyar Uwa,kafin ta rufe baki Iklas ta kwada mata mari,Aisha ta daga hannu zata rama taji an rike hannun gam tare da zuba mata wanu Marin sai da ta daina gani na wani few seconds, dagowa tayi taga wanne me tsautsayine haka Omar ta gani tsaye yana huci idonsa jajir,ai mukus tayi taja baya tana kuka sai wajen Ummansu. hannun Iklas ya kama tare da jawota cikin Palo,ita kuwa sai kuka takeyi.harda Karin shagwaba na ganin Omar.
Kwace hannunta tayi ka kyaleni ni tafiyata zanyi kuma zan dawo na dauke su Ummi,a sanyaye ya matsa jikinta kamar zai janyota jikinsa ya rungume,habarta ya dago da yatsa daya ya sauke mata kyawawan idonsa cikin nata har wani zaiba zaiba Iklas ke hangowa cikin idon Omar,a ranta tace tab kaga aljani wannan kyau haka.
A sanyaye Omar yace ya isa haka badai akan magani zaki tafi ba?kai ta daga masa wai eh,to bani zansha ko micijine a ciki zan sha.tausayi ya bawa Iklas sosai,murmushi ta saki tare da rungumeshi kadan haba ko kaifa,murmushi yayi ya janye jikinsa haka kawai baliga na rabarsa karfa yaje ya aikata barna,daria take sosai dama ita tsokanarsa takeyi ganin bai San matarsa bace ai kuwa zai sha tsokana cewar Iklas a ranta.kunji fa gulma wajen Iklas tana jin dadinta dai kawai.
Ganin tana tunani ya dungureta ta kusa faduwa,dawowa hayyacinta tayi ta dakko masa maganinsa.tana dakkowa ya bata fuska to gashi sha kaji pls...kafada ya make kamar yaro.
Kaifa kayi alkawari zaka sha masifa ya fara Allah karki bari na fara dukanki a gidan nan.me yayi zafi haka ya Omar?yi hakuri kasha kaji yi tayi kamar zata fara kuka sannan yace to bani na sha badan halinki ba.
Murmushi tayi tace haaaaa bakin kulle bakinsa yayi in danki ne ko sa'anki zaki wani cemin Haa bakin ke nifa baki isa kin juyani ba.da kyar ya yarda zaisha maganin ba karamar wahala Iklas tasha ba.

Cike da jin dadi ta bashi yasha sai fushi yakeyi,da kanta ta cika masa tumbi da abinci yayi dam.sannan suka zauna suna kallon film har Mama da Ummi suka fito suma, suna mamaki tare da jinjinawa Iklas,
Ummi tace yar jakar uba Hajiya kinga yarinyar nan na fada miki kokari gareta ko waye sai ta iya ji dashi. Ummi ta dan daki kafadar Iklas Gomnati uwar yan lissafi kenan.daria sukayi dukansu har Omar dake jikin Mama Iklas sai kunya yakeji dan Omar ya riketa gam,
Omar shugaban yan shagwaba yanda ji yan manne jikin Mama sai lallabashi akeyi cewar Ummi sai tsokanar Omar takeyi.Suleim,Suhaila,da Abdallah su suka fito suma sai wajen Omar suka manne masa,Suhaila ya jawo kusa dashi beauty ya garin,daria yaran sukayi.Mama ce ta gaji ta koresu.

Mama ta saka Suhaila schl both islamiyya da boko class daya da suleim.Abdallah kuwa dama yayi candy tussia zai tafi karatu.
Sadiya da Aisha sun fito da mazajen aurensu,sadiya wani Alhaji Dan Bala zata aura yana da kudi matansa 2 ita ta uku gidanta daban ya Gina mata.Aisha kuwa Yusuf dinta dan me kudi gaba daya a turai ya taso can ya girma.an kawo kudin aurensu yayin da Baffa yace su canja mazaje wannan Sam basu kwanta masa ba sukace su gaskia in za a musu aure a musu haka,in ba haka ba su hakura gaba daya,su rike aikin Gomnatinsu.shi kuwa Baffa ya karbi kudin aure aka sa biki nan da 3mnths.

Haj Rahina tinda ta dawo taga Baffa ko harkarta bai wani cika shiga ba.wani bokanta ta sanarwa tace dole in tana son samun nasara sai ta kawar da Iklas nesa da su.cuku cuku ta fara yayin da kawarta Hajia Binta ta hanata aiwatar da hakan,ta yaudareta kan akwai wasu manyan aiki da ta kai ayi musu a kasar arna kudu.
Hajia Binta kuwa malamanta ta bawa aiki kan a hana Rahina aiwatar da kudirinta kan Omar da Iklas,dan haka da Umma Rahina ta tasarwa aikata sharrinta sai wani abun ya faru Wanda dole sai ta kasa aikatawa,abin ya dameta,ta rasa wai meke damunta,amma tunda hakane zata sa su Sadiya suyi komai,ai tana da jininta.

Omar bacci yake ji tuni ya fara baccinsa jikin Mama,Ummi kuwa tana can tana gyarewa Iklas kayanta tunda yanzu bata da wani lokaci,Gajia Mama tayi ta dauke kan Omar ta maidashi cinyar Iklas tace idan ya farka Ku koma part dinsa ta wuce Iklas... Tuni Iklas ta fara hawaye ita wai yanzu haka zatayi rayuwa duk ta gaji jikinta ciwo yakeyi,shike nan ita baza ta huta ba,kuma itama baccin takeji fa,ga shi an koma schl wayyo aikin Gomnatinta,

Omar sai baccinsa yakeyi hankali kwance,Sai daya tashi dan kansa ganinsa yayi kan cinyar Iklas,sai haushi yakeji ansashi aikata sabon Allah.ko kulashi Iklas batayi ba sabo da haushinsa takeji an takurata.
Kallo ya kare mata ke bakya damuwa wai hada jiki da mazan wasu?haushi ya kara turnuke Iklas bata San sanda ta kwanyawa Omar mintsini a cinya ba har cije baki takeyi dan mugunta,shakota Omar yayi ai kuwa Iklas dole me karfi yau baza ta kyaleshi ba,said suka fara kokawa tukuru suka kaure, shi Omar a hankali yakeyi da tsokana amma Iklas ita da gaske takeyi sai nishi takeyi wlh bazan dinga kyaleka ba na gaji ina ma Abu kana zagina.
Sosai Omar ke shan dariar Iklas ita dole fada takeyi,Iklas da kanta ta gajiyar da kanta kawai ta fashe da kuka nan take Hankalin Omar ya tashi baya son ganin kukan Iklas,

Bai San sanda ya rungume Iklas ba yana jijjiga ta tare da shafa bayanta,lakwas tayi tana goge idonta,cikin rada ya tambayeta kin gaji ne?kai ta daga masa wai eh,bacci ko?nan ma cike da shagwaba ta daga masa eh.to shine abin kuka kalli yanda kika farfasamin jiki da dukanki dama haka kike da karfi harda naushina fa kikayi ko dai kin taba zama a China ba a sani ba.
Fashewa da daria Iklas tayi da ta tuno haukar da tayi tana ta kokawa da Omar bayan ita ta wahalar da kanta,hannunta ya kama suka wuce Room dinsa cike da shauki,Iklas tasha mamaki ganin har an gyara ko ina neat yana kamshi,suna shiga Omar ya dauketa kamar baby ya daurata bisa bed maza kema yi baccin tunda naga adawa kike dani kina min bakin ciki nayi bacci ke bakiyi ba,akan Mama ta dorani kan cinyarki kike bakin ciki.murmushi tayi abinta ta juya masa baya sai bacci.

Shi kuwa a.c ya rage mata ya lullubeta da hadadden bargonsa ya shige toilet domin yin wanka gashi yau so yake Iklas ta rakashi masallacin juma'a sallah,ya Dade bai je ba.
Sai 1 Iklas ta farka Arba tayi da kyakyawar fuskar yana zaune kasan bed hannunsa kan cikin Iklas kansa bisa bed yana ta bacci shima.minti kadan ya bude idonsa ya dorasu ana Iklas wacce ta shagala wajen karewa halittarsa kallo.
Kunya taji ta mike tayi hanyar fita daga room din,pls ki shirya za muje masallaci yau.OK tace tare da komawa dakin Ummi.
Ummi sosai ta kara yiwa Iklas nasiha tare da nuna mata muhimmancin miji.shiryawa Iklas tayi cikin wata rantsatsiyar doguwar Riga baka me adon Golden,cikin akwati set 4 da Mama ta bata kafin a hada mata lefe.
Yana gyalen tayi a kanta,ta sa takalmi Golden da da jaka Golden masu tsadar gaske,kamar balarabiya haka ta fito.walwali kawai takeyi.
Ummi ta yiwa sallama ta wuce dakin Mama da fara'a Mama ta tareta ina zuwa haka?Mama ya Omar zan raka masallaci zaiyi sallar juma'a.
A dawo lfy a kula sosai kinji.to Mama insha'allah cewar Iklas.
Har room din Omar ta kara komawa sai taku dai dai takeyi,a jikin mudubi ta ganshi da gani kasan karfin hali kawai yakeyi,wata mashahuriyar danyar shadda ya sa ita ba fara ba ba kuma milk ba,yayi matukar kyau dan dagwas dashi,sumar nan taci kudi luf luf da ita,turaruka masu tsada ya fesa sannan ya kwashi wayoyinsa,Iklas an saki baki ana kallon zasu makara kawai hannunta ya rike suka fito cike da taku me birgewa.

Yaran Umma suna tsakar gidan sai gulma akeyi.wucesu sukayi Omar wata gangamemiyar mota fara Sol ya nufa driver ya ba key ya tukasu suna Kane bayan mota, har masallacin da Omar ke zuwa.
Bai fito daga mota ba sai da aka tayar sannan ya saki Iklas yaje yabi sahu,ana idarwa ya dawo cikin mota wajen ta,driver ya jasu ya fada Masa wani park yace can zasu je.shima wajen shakatawar manya ne,da Iklas dinsa ya fito.nama ya siya musu da abubuwan ciye ciye anan suka zauna cikin lafiyayyen wajen inda aka tanada saboda masu zama suci a wurin.

Kafarsa ya dauka daya tare da zare takalminsa ya dorata kan kafar Iklas gaba dayansu wani yanayi zazzafa suka tsinci Kansu ciki tare da son kasancewa da juna.cike da farin ciki a zukatansu suka dinga baje girki a cikinsu.

Sun mike zasu tafi sai ga Sultan da Raj suma tafawa sukayi suka fara yiwa Omar cakaki Jan Iklas yayi suka fara tafiya,kafin su karasa mota,dan saurayin da ya taba bige Iklas ya karaso wurinsu har wani kishi yake shifa bai yarda ba Iklas yake so.

Haba baby Iklas rannan naje gidanku akace kun bar unguwar ina ta nemanki,nasha wahala wlh ko sunana fa Baku sani ba,pls ki bani numberki kinji.ya kalli Omar Wanda ya gama hasala.sannu malam, baby wannan yayanki ne?naga kuna kama dashi.Iklas murmushi tayi ta fara magana,



Asmabaffa
[9:00AM, 4/10/2018] ‪+234 810 468 7075‬: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

85-90


By
Asmabaffa



KUJI DADINKU READERS.


Sannu ya gida? Yayana ne mana,mun manta an rabu ko sunanka bamu tambaya ba,washe baki yayi Suna na IBRAHIM ZAKARI ana ce min IBZZY BOY.daria ta kusa kwacewa Iklas yanda yace Ibzzy boy har da daga hannu kamar masu wakar raps.shi a dole nigger.
Omar yaso yayi maganinsa amma ganin kwata kwata ibzzy irin banzayen mazan nan ne sai ya shareshi,Iklas harda jin haushin Omar baya kishinta dan bai San matarsa bace ita.

Waya ta dauko da niyyar karbar number Ibzzy sabi da taji haushin Omar ba ko kishinta,fisge wayar Omar yayi tare da sa yatsa daya a dan chakurkurin kirjin Ibzzy ya tunkudashi baya sai da Ibzzy ya kusa faduwa,da masifa Ibzzy ya tasowa Omar dole sai ya ci mutuncin Omar, daukeshi da wani zazzafan mari Omar yayi Wanda yasa Ibzzy dafe kumatu ba shiri,kafin ya dago Omar har ya finciki hannun Iklas kamar tsinke kawai janta yakeyi har mota ya jefata,driver kuwa yaja a kabar Ibzzy da kumatu kumbure,a fili ya furta kai wlh saina ci uwar guy nan sai naga ubansa dan babarsa.

Gida suka koma a compound suka ci karo da Abdallah zai fita da Sauri yazo wajen Iklas wacce ke kukan masifar da Omar ya zazzaga mata kan Ibzzy.da sauri Abdallah ya kai hannu da niyar sharewa Iklas hawaye Omar ya bige hannunsa,bai gane ba ya kara yunkurowa zai rukota Omar ya shiga tsakani da Sauri ya tsaya a tsakiya,
Ya kare Abdallah kar ya taba Iklas,gocewa Abdallah yayi ya zame ya nufi Iklas anty wa ya Saki kuka kara kai hannu yayi,Omar ya jawo rigarsa baya kiiiiiiii ya dawo dashi baya,
Abdallah sarkin naci kara komawa yayi shima Omar cikin zafin nama ya cakuma Abdallah ya turashi baya yana zan mareka wlh,to yaya kuka fa take, cike da masifa Omar yace ina ruwanka ko huruminka ne ban son shishigi...wuce kasan inda dare ya maka.sum sum Abdallah yayi gaba abinsa yana kallon Iklas,an hanashi lallashinta.

Janta Omar yayi suka wuce wajen Mama... kallon Iklas tayi taga alamar tayi kuka,lfy Iklas me ya sameki?tana shesheka cike da shagwaba tace ba ya Omar bane dan kawai wani ya sanni munyi magana shine ya dinga min bala'i harda murdemin kunne wai zai cire min kunne, dadi Mama taji ganin Omar zai fara son Iklas fa,hmm nace Mama batasan zaman da sukeyi da Iklas ba su kashe su rufe.
Lallashinta Mama tayi tare da balbale Omar da fada,Omar kuwa kememe yaki karbar laifinsa Mama muna tafiyafa ta kama magana da wani dan ta raina min hankali ni ina sauri zasu tsaya bata min lokaci idan zancen takeso yazo gidan mana zasu shiga rayuwata harda cewa wai ni yayanta ne..to ba hanani karbar number sa kayi ba,kinji ko Mama dan karyane fa wai zata karbi number sa, to koma ki karbo mana yanzu tunda baki da hankali
Sai da ka bari muka dawo da ka barni mana tun acan cewar Iklas,gajia Mama tayi da cacan bakinsu tace dan Allah Ku je part dinsa kuyi can ni kun cika min kunne na rasa me gaskia cikinku.

Da sauri Omar yace ni Karta zo min room,tabe baki Iklas tayi to me zanci da room din naka ko kace Nazo bazanzo ba tun yaushe na daina kulaka ma,ae naji cewa Oga Sir, yazo zai wuce amma saida ya matso jikin Iklas ya take mata yatsa daya.ihu ta fasa Mama tace maganinki kenan Babana muguntar tsiya gareshi in kika bashi haushi,ki dinga kyaleshi kishinki yakeyi fa ke baki gane ba.
Karki yarda ki fada masa ke matarsa ce kinji ko,kai ta daga,idan ya warke kuma zaki koma schl sosai taji dadi wai zata koma schl,wayyo aikin gomnatinta.

Umma Rahina ce tasa yarta Naja aikin kan tasan yanda za ayi ta shige jikin Iklas sosai har ta jawo musu ita ta dinga shiga part dinsu,kuma ta gargadi su Sadiya su daina nuna mata tsana a fili,ta hakane zasu samu nasara..Sadiya tafi kowa tsanar Omar kawai jiran lokaci take ta kaddamar masa ba tare da kowa ya gane ba.

Ibzzy Boy ya cika da haushin Omar marinsa da yayi,kuma bazai daina son Iklas ba dole ya nemi gidan da suka koma yaje can,domin so yake ko ma ta halin kaka shi dai ya auri Iklas.wasu manyan kawensa mata da suke masa kawalcin mata JALILA WANKAN TSINKE da FATI GOCEWA ya kira ya shaida musu komai wankan tsinke tace haba Ibzzy kar ka ba damu mana kai da kake kullum matane frnds dinka amma ka kasa da wannan kucakar,

Fati gocewa tace ka bari kawai zamu je wajen LAWISA ICEN KABARI harda LADI PIJO wlh sai mun shawo kan wannan yarinyar ba gaggawa a nutse zamu wayar da ita dole ka aureta ita din banza dan uwarta ko da ubanta take kwana wace ita ta kara narko wasu manyan zagi.nan suka taru Ibzzy sai barin kudi yake musu.

Saleem ya kira wayar Ummi ta bashi address din gidan su Omar zai kawo musu ziyara sannan zai ga Iklas dinsa.sai dadi yake ji.har ya matsu Sunday tazo.

Sahar taji labarin Omar yayi budurwa nan ta fara bala'i wlh bai isa ba yana warkewa zan koma gidansa dole na tara dukiya nayi tafiyata,ko wacece bata isa ta rabi Omar ba,kuma ko ya aureta sai na koreta kuma sai ya saketa wlh,kai zan iya hallakata nan Sahar take ta bala'i a Office.wannan alkawarin sahar kenan itama.

Iklas ce tazo sanye da yar wata Riga da kadan ta wuce gwiwa me dogon hannu ce red kanta ba dankwali sai gashi yarab,tunowa tayi bata bawa Omar magani ba tunda sukayi fada ga dare yayi.da tayi fushi dashi amma yanzu ta hakura zata je room dinsa duk da yace karta kara zuwa masa.
A hankali da sallama ta shiga dakin nishin Omar kawai ta jiyo,kan sofa ta ganshi kwance amma dai tunda aka fara maganin suna ganin sauki,da dane da tuni Omar ya Dade da suma,

Karasawa tayi ta dakko maganin wajensa taje ta zauna gefensa kadan ta dago kansa sai sannu take masa yau da yake baya cikin hayyacinsa ba gardama yasha maganin,
Addua ta dinga tofa masa tana sannu kaji ya Omar tare da kara harde yatsunsu waje daya.
A hankali ya dawo normal yau Iklas tsokanarsa taso yi dan haka zamewa tayi ta kwanta cinyarsa,haushi ya kama Omar yarinya ba kamun kai,ta gama lalacewa a dalilin talla.
A ransa kuwa ji yake kamar su zauna haka har abada, zuciyarsa ta gayamasa kai bafa muharramakar ba ce kaji tsoron Allah don yana ganinku,ai da sauri Omar ya daga cinyarsa ya hantsilo kan Iklas ya mikar da kafarsa,
Magagin baccin karya tayi ta wani taho luuuu ta fada jikinsa,zameta yayi daga jikinsa,hannunta daya ta dauka ta wani jefa luuuu kan cinyar Omar,wata zuciya ce tazowa Omar ya dauki hannun Iklas yayi wancakali dashi tare da mikewa ya shige toilet.

Iklas kuwa

Please Login or Register in order to submit comment