Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a takure,zafi ya dameshi,ala dole zai danyi kwanaki a gidan nan kafin ya tafiyarsa,ina Sam bazai iya rayuwa haka ba,komai a takure,dan karami kamar yana prison haka yake jinsa,dan ma akwai wuta available, Daren ranaar gaba daya ya kwashi bacci cikin nutsuwa,har makara yayi,sai 9am ya farka,su iklas yau ma Sunday ba schl,tuni har sun gama gyara gidan kawai ummi ce bata karasa musu breakfast ba,fitowa waje yayi dan toilet ma sai iya ta tsakar gida dole,brush ne a hannunsa da wani tsadajjen toothpaste, omar kwai kunyar a kallar masa jiki shi yasa da 3quater da singlet farare ya fito,harda towel dinsa,kallon yan gidan yayi yaga duk sunyi wanka kowa radau dashi,iklas ya kalla wacce ta wani hakimce a farar kujera tana latsa kuturwar wayarta,ummi ta kitchen tace umaru ka makara ni na hana a tasheka saboda naga akwai gajia jikinka,guntin murmushi yayi ya wuce toilet,kalar sabulun omarma daban suke,yana Shiga wanka iklas ta shige room dinsa zuruf ta gyareshi fes fes,aka dame masa bed,roomfreshner da turaren wutar data sa masa yafi na ko ina yawa.

Palo suka hallara da kayan break ana jiran oga dan kwalisa ya fito,sallah yayi da addua ya shirya cikin wata jallabiyya dark brown yayi kyau,,duk gidan ya dau kamshinsa,yana fitowa ya gaisar da ummi,ta amsa tana tsokanarsa da bakunta,suhaila kuwa tsam ta mike zata je wajensa iklas ta riketa ram,zauna malama zaki je ki kama hawan masa jiki,jikinkine? Ya fada fuska tamke,ummi tace kyale iklas da iyayinta,sharesu tayi ta gaishesa ya amsa tare da jawo suhaila kusa dashi,

Kunun gyada ne da chips girkin yayiwa omar dadi,kallon ummi yayi yace amma daga ji tsohon hanu ne yayi girkin nan ko? Daria ummi tayi sosai tasan sarai iklas yake tsokana,

Iklas kuwa haushi taji ta katse maganar da tsohuwa yau zanje wuse market,a dawo lfy saura ki kwaso wannan yan iskan gwanjunan dangalallu da kike kwasowa,

Baki ta turo ta Mike ta wuce room dinsu,omar kuwa har fadi yake anya kuwa iklas ba aljanu gareta ba lol,ya matsu ta tafi kasuwa ya sace book din nan da yake gani tana lissafi,so yake yaga wai me take rubutawane kullum,

Yaso ya hanata fita amma wannan kudirin nasa yasa ya rabu da ita,fitowa tayi sanye da atamfar da omar ya dinka mata red da yellow Riga da skert,tayi kyau sosai das da ita,ansha jambaki maroon,bata daura dankwali ba,gyale siriri ta yafa a iya kanta,gata jajir da ita ta haske ko ina tal,duk suna zaune Palo ta fito,idon kaka ummi omar ya faka ya dallawa iklas harara,ya mata nuni da ido kan ta koma ta canja gyale babba,ko tasa hijab,kafada ta make cike da shagwaba ta buga kafa alamar taki din,ido ya zaro ya daure fuska yayi kamar zai mike ya kamota da gudu ta fada daki,ta dauka kamata zaiyi,tasan muguntar omar dan bata manta wahalar da Tasha ba cikin motarsa,

Hijab tasa yellow me hannu yakai tsayin Rabin cinyarta,ummi ce ta kalleta da mamaki tace yar albarka ko kefa,Ashe kin fara hankali,a lallai shi yasa akace komai da lokacinsa,Allah miki albarka yar nan,sai kin dawo kinji jikalle,tana fita ta leko kanta taci sa'a su ummi surutu suke da suhaila,a hankali ta dan girgiza labile yanda omar zai gani,kallon wurin yayi ai kuwa suna hada ido ta murguda masa baki,shi daria ma ta bashi,a take ya saki murmushi ya nuna kansa irin ni?ido ta karkada far far ta daga kai alamar eh din,kai ya jinjina alamar zaki dawo ne.ummi ce ta juyo wuf iklas ta sake labile ta bar gidan,shi kam ogan naku wani matsewa yayi.ya dauki remote ya kunna TV,

Kaka ummi ce tace to ni umaru na shiga zan dan matse,bacci nakeji,to ummi a fito lfy.iklas kuwa kayan ta kwashe ta maida kitchen,tana fita Omar ya sadada a dauke jotter iklas ya shige dakinsa,

Kwancia yayi a bed ya fara dubawa,murmushi ya farayi ganin harda date take sawa,kuma kome ta rubuta sai ta zanashi,Daddawar miya ya fara gani tace ta Dari biyu for 1mnth,sannan yaga ta zana daddawa,su tattasai,da sauran kayan abinci

Yanaa ci gaba yaga irin bashin da take bi su ma gasu nan,ga wani bangaren business dinsu ne,abinda ya bashi daria kwandala in ta shiga ko ta fita sai ta rubuta,wani bangaren ma planning rayuwarsu da budged tayi na 1-2yrs,bai gama shan mamaki ba sai dayaga ko bako in akayi sai ta rubuta tayi lissafi nawa aka kashe a kansa,rufe littafin Omar yayi yana daria ganin an rubuta har dambum naman da ta bashi kwananki,komai na rayuwar gidan na lissafe a cikin littafin,gajia yayi da karantawa dan kato ne littafin,ga lissafi da rubutu kaca kaca mayar mata abinta yayi inda ya dauka,a Palo yaga suhaila na kallon cattoon, kwancia yayi a 3seater yana tunanin rayuwarsa,da mamansa halin da take ciki,

Yana wannan tunani tare da adduar Neman agajin Allah suka tsikayo sallamar iklas ta dawo,tana shigowa ta durkusa tasan tayi laifi,sannu da hutawa oga sir


Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

20-25


By
Asmabaffa




Tana kifta ido fiki fiki da gani bata da gaskia,sum sum ta wuce,sannu da zuwa anty cewar suhaila, tsayawa tayi ta dawo wajen suhaila,baby ya gida,kinyi karatu kuwa?anty Sai anjima zanyi, to Allah kaimu..me kikaci after break? Ba komai anty..so kike ulcer ya kamaki ko,juyawa tayi ta shiga kitchen,cake ta ebo da fresh milk ta dawo palo,a gaban suhaila ta ajiye gashi nan maza ki cinye,komawa kitchen tayi ta ebo wasu snacks ta kawowa omar harda juice yasan tabbas iklas sai ta rubuta cikin jotter dinta omar yaci cake da lemo,

Shi Sam baya son zaki juice kawai ya sha,iklas tana kitchen tana girki Omar ya shiga kitchen din,gwagwa take ta yi wajen yanka wata kaza amma ta kasa dan ta mata tauri,sai huci takeyi tana yarfe hannu,kusa da ita ya matsa hannu yasa ya karbi wukar,tsorata tayi sosai,ido suka hada tace kash wlh har naji tsoro,kazar ya fara yanka mata,tana gefe tana mamaki yanda ya iya aikin mata,sharp sharp ya yanka mata,satar kallonsa takeyi tare da yaba kyau irin na omar,shi wai to baya daria ne,mutum kullum shuru haka,omar kuwa yaji ajikinsa tana kallonsa,yana gamawa ya wanke hanunsa da liquid soap,yana juyowa ya dungure mata kai sai da ta kusa faduwa,kina kallona kamar baki sanni ba wth ur big eye,nuna min kayan abincinku cewar omar,

nuna masa tayi yaga suna da su amma sun kusa karewa,wayarsa ya kunna ya kira wani daga cikin yaransa,kwatancen gidan ya masa ya umarceshi ya kawo kayan abinci gidan,3hrs tsakani aka cika gidan da abinci.amma basu ga omar ba domin yana dakinsa bai son a San Inda yake ma kwata kwata,su kuwa yaransa sun zata yana office ko gidansa,ummi kuwa rasa bakin godiya sukayi a wajen omar,

Maman omar kullum addua da kuka take zabgawa,harda kannensa su abdallah,su Aisha bangaren haj rahina sai murna sukeyi yayinda labari ya riskesu,Wanda hakan Sam baiwa sadiya dadi ba,an cuceta bata dau fansa ba,ga asarar kudin da tayi,Haj.rahina kuwa sai dadi takeji tana nishadi,baffa kuwa manager ya kira ya tabbatar omar ba a San inda yake ba shi ke kula da komai.gaba daya baffa ya daina walwala da farin ciki,Sam haj rahina ta kasa gane kansa,domin ko sakar mata fuska bayayi,tattarowa yayi suka dawo Nigeria,

Waje waje gari gari suke bincike,sultan ne a gaba kullum basa zama Neman omar sukeyi,sadiya na hango ta Tara yan dabanta su wajen shida,tace isa a.c da usy a boy ya kuke ganin za ayi,kudina zaku bani ko kuwa yaya za muyi?isa a.c ne ya saki daria yace ke hajiya karki kawo yawa mana,ya kike mana shirme ne,a boy yace dalla malama saurara yasin sai na sokeki da wuka,karki raina mana hankali mana,ji mana ke ai munci kudinmu,taimako daya za muyi miki duk ranar da muka ganshi idonmu idonsa zamu cika miki burinki,idan kuma bamu gani ba sai ki ware kawai ko ya kukace.a boy ya zuki sigari ya fesawa sadiya yace ware kawai hajia kar ki bari na canja mind dina na murde miki wuya

Tsorata sadiya tayi jiki na rawa tace kuyi hakuri ko me kukayi dai dai ne,hakan ma is OK,motarta ta figa a 100 ta bar wajen,a boy ne ya kalli yaransa suka kwashe da daria kana yace men this girl inaaaa ey na bad girl,she stingy bad.wani ciki ashar ya kunduma yar kut...da wani dry leg nata,ko shape babu komai flat.

Hajiya rahina tsabar yawan bokayen da tabawa aiki ba a San Wanda aikinsa ya ci omar ba,kowa kawai ta yarda kawai.ciki kuwa har karyar su HAJ bilki kawayenta.

Dare ya tsala kishirwa ta fito daga room dinsu shan ruwa,tazo Palo ta jiyo nishi dakin omar sosai abin tsoro,lallabawa tayi ta shiga dakin omar a hankali ta murda kofar ta shiga,

A kudundune ta Ganshi ya hada gumi yana ta karkarwa yana nishi,da gani mafarkin abin tsoro yakeyi,sai ciccijewa yake yana tirje tirje,tausayinsa iklas taji sosai karasawa jikin gadon tayi ta zauna gefen bed din hade da kura masa ido,A hankali tasa hannunta a kafadarsa kamar jira yakeyi ya juyo a sa hannu biyu ya damke hannun hade da kankamesa a kirjinsa,shuru iklas tayi tana matukar tausayawa oga,da gani matsala ce jikinsa babba,ba tare da ta zare hannunba ta Kurawa hadaddiyar sumarsa ido,tasha gyara tana kyalli yalala da ita,kamar TV haka ta kurawa surar Omar ido,ta shagala sosai sai da ta share lokaci me tsawo,farkaawar da Omar yayi ita ta dai daitawa iklas nutsuwarta,

Zumbur ya mike zaune yana kallonta tare da mamakin rike hannunta da yayi a kirjinsa,mamakin iklas shine yana rike hannunta taga ya daina karkarwar tsoron,sannu oga sir,hannu takai zata taba wuyansa,make hannun Omar yayi ya watsa mata harara mind ur business pls,ruwa kawai zaki kawo min nasha,ni ba irin su Emma bane as u can see musulmi ne ni,so u better get ths in to ur skull, ki daina gigin taba min precious skin dina.

Baki iklas ta tabe a fili tace sannu muslimu daga taimako,kuma hannuna kai ka kamashi zuwa jikinka anji hannun yarinya me laushi ba a sababa an wani kankameshi,wuf ta fece daga dakin,dan dai kawai ta tausaya masa ne amma da wlh baza ta kaimasa ruwan ba,

Ruwa ta dauka faro da glass cup ta koma room din,sadaf sadaf ta ajiye can nesa dashi a tsorace take kadan take jira ta zura da gudu,kafafunsa ya daga hade da dafa cinya alamar zai mike,kararaf ta kwasa da gudu ai kuwa ta daki kofa da hancintaa garin gudu ji kake fas,wayyoooo ta furta hade da rike hanci,kara kwasa tayi da gudu zata arce,caraf omar ya riko hannunta ba tare da yayi magana ba ya cire hannun da ta rike hancin,

Jini kadan ya gani alamar ta fara habo kadan,gashi kan tsinin hancin yayi ja ya kwarzane kadan,tissue ya dauko ya matsa jikinta sosai suna jin numfashin juna,tuni jikin Omar har ya shocking yana rawa a cikin jininsa,

Ita kuwa iklas wani kasala kasala taji kamar ya danyi hugging dinta haka taji,daurewa kowanne yayi cikinsu,hannu yasa ya dago fuskarta ya goge mata hancin tas,yana karewa pink lips dinta kaallo,kamar ya dan.....lol

Kije toilet ki wanke cewar omar, mika mata tissue yayi har wacce ya goge mata hancin, jeki nyt.cike da tunanin kyan dirin Omar ta fice,toilet ta shiga sannan ta koma dakinsu,

Kaka ummi ke kuwa iklas zawo kikeyi ne?kin Dade daga cewa zaki sha ruwa sannan kiyi fitsari,ummi bigewa nayi da kofar toilet kinga habo ma nayi,sallallami kaaka tayi tana ta faman yiwa iklas saannu,harda shafa mata magani a hancin wajen da ta kwarzane,

Ni kuwa nace su iklas badai iya karya ba.kwanciya sukayi kowannensu cike yake da tunani kala kala,iklas an kalli ceiling anyi kuri da ido ana tuno kasancewarta tare da Omar dazu,duk sonta da aikin gomnati sai taji da tayi tunanin salary ko ta gama schl ta fara aiki,ga mota tana ja,suna zaga kasashe ita da su suhailanta sai taji yanzu kamar tafi jin dadin tunanin oga omar,kawai fuskarsa in ta tuno dadi take ji,a'a juyi ta karayi taja tsaki,yanda omar ke daure fuska ta tuno sai taji sanyi,a ranta tace oh zuciyata yanzu fushin nasa ma birgeki yakeyi tab,da kyar bacci ya sace iklas,bangaren omar kuwa mugun mafarkin da yayi yake tunani,ga tunanin family dinsa musamman mama ko a wanne halin take oho,rayuwar da yake ciki yanzu ya tuno da iklas me kwai sai yaji dan sanyi a ransa,ya yanke shawarar yanda zai sa iklas ta masa wani acting yanda zaiji lafiyar mama da baffansa,hade da kwantar da hankalinsu,yasan iklas tsab zata iya,ko ya wannan abu zai kasance readers oho,za dai muji nan gaba.da wannan shima yayi bacci,

Da safe su iklas sunyi shirin schl,omar kuwa fitowa yayi so yake yaga ya hancin iklas yayi,uniform ya gani sun mata kyau,bai taba ganin wacce uniform yawa kyau haka ba irin iklas,kallo ya kare mata suka gaisar dashi,ummi ma ya gaisheta,iklas ya kalla ya kara fakar idon ummi ya dagawa iklas gira daya,hade da nuna hancinsa yana murmushi me kayatarwa,tasan tsokanarta yakeyi ba wani dubiya,baki ta turo,ta juya masa baya tana yaba muguntar omar,ummi ta juya tana gyarawa suhaila jaka ya dan ja hijab din iklas kadan,waigowa tayi itama ta dage masa gira daya,alama yake mata da hannu kamar kurame,kaka ummi ta tarfa su,sosai sun bata daria,umaru shirmen iklas kake kulawa ko,so kake ka koyi shiriritarta naga alama,ummi kalli hancin ta fa,hmmm umaru baka da dama ai jiya a bayi ta bige da kofa,ta dade tana habo,da kyar ta samu tayi bacci,daria omar yayi sosai jin karyar da iklas ta tafka,kallonta yayi suna hada ido ta kifta masa wai ya rufa mata asiri,kafada ya rike alamar yaki din,kaka ummi na kallonsu tace ohhh yau kuma umaru kurame kuka zama haka,wlh ka daina saurarar iklas,ummi wannan jikar taki bata ji ne cewar omar.

wani yaronsa daban Omar ya kara kira ya gwada masa gidan su iklas,dalleliyar wata motar omar ya dakko ya kai su iklas schl,sai kallon su iklas akeyi a schl.

Shima dai Wanda ya kai su iklas schl bai San daga ina omar ya kirashi ba,gashi ko wanne da new sim yake kiransu,kuma yan amanarsa yake sawa aikin Wanda yasan duk runtsi baza su bashi matsala ba,kowanne sai ya gargadeshi kar ya fadi ya kirashi a waya.

Iklas kam yau daga schl company ta wuce ta saro kaya,yaron omar ne ya kaisu ko ina ya dawo dasu gidansu sannan ya tafi

Kafin su iklas su dawo omar ya fadawa ummi zai aiki iklas gidansu ta gano masa lafiyar iyayensa,umaru kai da kanwarka sai ka nemi izinina,dadi yaji sosai su iklas na dawowa ya sata ta shirya cikin doguwar Riga da mayafinta,wajensa taje yana zaune tsakar gida a kan kujera sanye da Riga armless fara,da black jean gashin kansa ya kara yawa,

Ummi tana Palo suhaila na gefenta suna kallo da cin abinci,envelop ya mika mata nan ya Shiga tsara mata yanda zata yi acting a gidan nasu, hhhhhh iklas ta kama daria yanda taga Omar ya gwada maganar mata, kallonta ya tsaya yi,yanda daria ke matukar yi mata kyau, tsayawa tayi da dariar ganin omar ya kafeta da ido,daga bisani tace action ta fara gwada masa yanda ya koya mata har kara masa idea tayi,sosai sunji dadin moment din,iklas uwar shirme ji tayi inama suyi ta yin wannan film haka me dadi.

Kudi ya mika mata na taxi tare da address ta tafi kuwa.yau zata ga gidan su oga da family nasa,ya za aga haduwar su cewar iklas.

Sahar kam sai Allah ita cewa tayi Omar makaryacine yana can London munafiki za a ce ya bata kato dashi,to saceshi za ayi dan haka iyayenta suka ce ta dawo gida tayi zamanta tayi aikinta.haka kuwa akayi ta kwashe komai nata tas ta bar gidan cike da nishadi ta samu yanci.

Tun daga waje iklas take kallon haduwar gida kamar baza a mutu ba,gate ta buga,masu gadi wajen biyar suka leko ganin tsaleliya iklas suka ce wannan da gani kawar yan gidan nan ce,suma mamakin kyan iklas sukeyi kamar larabiya,gashi da ganin rigarta ta masu kudi ce,dama a rigunan da Omar ya batane tasa daya,

Da sauri sukace ta shiga suna ciki,tana shiga nan ta rantse a ranta da zata yi bacci ta farka ta ganta a wannan gidan to cewar zatayi ta mutu tana aljanna.



Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

25-30

By
Asmabaffa



Page din nan naki ne DIYAR KATIBI.



Tunani iklas tayi domin omar ya gwada mata yanda gidan nasu yake ba tare da tasha wahala ba ta gane part din maman omar,shiga tayi dakin part din tare da danna door bell din da omar ya fada mata,abdallah ne ya bude kofar,iklas dauke da hand bag a hannu an wani shanye hannu irin na wayayyun mata,kallon abdallah tayi da ganinsa kasan kanin oga omar ne,

Kallonsa iklas tayi pls mama nake nema,OK shigo tana ciki cewar abdallah sai bin iklas yakeyi da kallo yanda yaga baby me kyau haka,shiga ciki tayi salati take maimaitawa a ranta yanda taga tsaruwan palon,a kujera ta zauna abdallah kuma ya hau sama domin kiran mama,suleim ce ta fito cikin shirin islamiyya,sannu da zuwa ina yini cewar suleim,lfy zo mana mu gaisa cewar iklas,zama tayi kusa da iklas,can iklas ta kunna video recording a wayarta tana daukan suleim,wani katon pic din omar ta gani a palon,suleim waccen yayankine?ae anty amma ya bace,an nemeshi ba a Ganshi ba,mama kullum sai ta yi kuka tana ta addua,dady ma addua yace mana mu dinga yi,kinga su anty sadiya kuwa nurma sukeyi sosai,har kida suka kunna a gidan nan,suleim kwai surutu.

Yanzu in suka ganmu da mama suyi ta mana daria,kuma anty sahar matar yaya omar ta gudu gidansu wai ba za ta zauna gidansa ba,gaban iklas ne ya yanke ya fadi jin an ambaci matar yaya omar,dama yana da mata? Take taji wani bakin ciki a ranta,gabaa daya jikinta yayi sanyi,cikin kankanin lokaci suleim ta bawa iklas labarin gidansu,duk da batasan su waye anty sadiya ba,suna haka mama ta fito ita da abdallah,yi tayi kamar tana latsa waya nan kuwa video take musu,tsugunawa tayi cike da ladabi ta gaisar da mama,mama kuwa me aiki tasa ta kawowa iklas kayan motsa baki,

Ganin kalar girkin hadadde yasa iklas sauka kasa ta baje kamar gidan ubanta ta kama cin abincin cikin dabara takewa kanta video record tana cika baki da abinci,

Mama da abdallah har suleim daria sukeyi ita kuwa iklas tana sani tayi haka dan su saba da ita,sai da taci ta koshi sannan ta kalli mama tace mama wlh har na dawo hayyacina bakuga wahalar Dana sha ba kafin na gano gidan nan,kwashe kayan mama tasa akayi,yan mata meke tafe dake ne? inji mama,sultan ne yayi sallama ya shigo palon,iklas taso ta ganeshi amma ta rasa Inda ta sanshi,shima bangaren sultan hakan take sai kare mata kallo yakeyi ya kasa ganeta,domin tun iklas na tallan kwai ya taba ganinta,yanzu kuwa ta kara haske,kiba,kyau da girma.

Zama yayi suka gaisa da mama,iklas ma ta gaisar dashi,shi dai sultan wannan bai taba ganin me kyau irinta ba sai me tallan kwai da apple ta Frnd dinsa omar,kai har muryarma suna kama,amma wannan da gani yar masu kudi ce,waccen talakace haka Allah ke ikonsa wani ba dangi yayi kama da wani duk a ransa sultan ke wannan tunani.

Iklas ce taga sultan na kallonta,shima sai da ta masa video record,mama iklas ta kalla tace mama dama wannan na hoton tayi nuni da yatsanta jikin pic din omar dake jikin bango ne,harrrrr su mama sukayi aka zubawa iklas ido a ji bayaninta,naje company dinsu Neman aiki da dan dadewa,shine aka turani office dinsa naje interview,shine yace bazan samu aiki a company dinsu ba,amma nayi hakuri kuma yana Neman alfarmata na kawo wa mamansa sako,

Shi zaiyi tafiya ne,har naki karba amma ya dage,mama baki gani ba har kuka yayi kan sai nazo gida wajenki na baki sakon,Baku gani ba abin tausayi har kuka ya min cewar bashi da kowa da sukafi mama da baffa,sune farin cikinsa iklas ta karashe tana matsar kwalla,mama tace Allahu akbar da su suleim tuni hawaye na ambaliya a fuskarsu jin labarin omar,tabbas iklas ta tausaya musu amma ta dau alkawarin gano wannan lamarin dake faruwa da omar da family sa ko zata tallafa.

Sultan ke bawa su mama baki bayan sun nutsu iklas ta zaro envelop daga jakarta ta mikawa mama,wannan yace na kawo miki,Allah bai bani iko ba sai yau,

Mama batasan karantawa don bata so ta karantowa kanta bacin rai,sabo da wannan ta mikawa sultan takarda,sultan nutsuwa yayi yana karantawa can su mama suka ga yana daria da fara'a wannan ya nuna sakon dadi ne bana bacin rai ba.

Kwace takar dar mama tayi taga guntun rubutu ne ma,fara karantawa tayi kamar haka:

SALAM......MAMA NAYI MATUKAR KEWARKI BURINA KI DAGE MIN DA ADDUA INA DA MATSALA A LFYR JIKINA,KI BAWA BAFFA YA KARANTA DA KANNENA SULEIM DA ABDALLAH,NAYI KEWARKU,SULTAN MA ABASHI HAKURI,INA NAN A NIGERIA MAMA CIKIN KOSHIN LFY,BANYI NISA DAKU BA,ZAN DAWO SOON,KUNSAN BAZAN TABA YIN ABU BA KWAKWARAN DALILI BA,A SANARWA BAFFA NASAN SHIMA ZAI FAHIMTA.

Dadi mama taji dukkansu sai murna da jin dadi sukeyi,iklas kuwa sai video take musu,mama ce ta rungumeta yata yar albarka mun gode kwarai,kowa godiya yakewa iklas,mama tace yaushe ya baki sakon?ya kai week nawa?sati dayafa kenan cewar iklas,,take kowa ya kara cika da murna,suka tabbatar da Omar yana kusa kuma lfy yake,hankalinsu ya kwanta,

Dakin baffa mama ta nufa yana ciki ta shiga ta labarta masa komai tare da mika masa takardar,yana gamawa ya dago fuska cike da annuri,dama na fada miki ki kwantar da hankalinki yana nan ni nasan son namijin gaske ne, sai mu dage masa da addua,kira min yarinyar na ganta,

Tare da mama suka Shiga dakin baffa,a kunyace iklas ta durkusa har kasa ta gaida shi,da fara'a ya amsa tare da yaba tarbiyarta,mama hakan take,daga bisani mama tace ki saki jikinki duk lokacin da kiga kina da lokaci ki dinga bullowa muna gaisawa,baffa ya kalli hajia baki fada min sunanta ba,oh kaga murna tasa na kasa tambayarta,yar albarka ya sunanki? UMMI kawai tace,bata San wanne suna zata ce ba.

Palo suka dawo iklas ta mike rashe rashe kwance kan 3seater tana ta yiwa kanta selfie,taga gida me kyau,

Suleim ta jawo da uniform tayi musu pic kala kala,abdallah ma haka,mama na gefe amma saida iklas ta dauka da ita,sultan ma kiransa tayi ya manne gefenta ta musu kala 3.duk tayi ne sabo da ta nunawa oga omar.

Sai daria take basu iklas ba boye boye waje ya burgeta ta yaba.sai 5pm tawa su mama sallama,an cika iklas da sha tara ta arziki,mama turaruka,atamfa kala

Please Login or Register in order to submit comment