Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.

Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,

Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.

Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,

Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.

Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?

Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.



Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

45-50

By
Asmabaffa



Na gode masoyana Allah karo karfin ido.



Kiciniyar kwace kanta takeyi amma ya mata rungumar karfi,da kyar ta fara zamewa cikin magagin bacci omar yace 2nmt pls.....tsayawa tayi cak tare da lafewa ita dama iklas ta Dade da son ta jita a kirjin omar,bata San me yasa ba kuma ta rasa dalilin da yasa jikin omar ke birgeta.sun dauki minti biyar haka omar ya dawo normal,jinsa yayi manne jikin mace ai bai San sanda fancakalar da iklas daga jikinsa ba,sai da ta fado kasa daga bed din.

Masifa ya fara IKLAS karo na farko da Omar ya kira sunan iklas,wani zirrrrrrrr taji lokacin da omar ya furta iklas,kallonsa tayi tare da tsilli tsilli da ido tana Sosa gashi,me ya kawoki dakin nan,mikewa yayi idonsa jajir ya damki kunnenta,kara ta saki kadan,ba kyajin magana ko iklas,am I ur mate? Ke bakya banbance tsakanin maza da mata,bayan yan iskan da suka saukeki dazu kinga bance miki komai ba shine zaki sauke iskancinki kaina ko?

Ina ina ta fara ....to wai...wai ba kaine ka janyoni jikinka ba kuma ka rokeni kan na tsaya,har hawaye kayi fa wai kar na tafi,kuma kace kai dadinka kake ji,kukan karya ta fara yi,kuma ni taimaka maka nayi,daga taimak....shut up tashi ki fita mayyata kar ki kuma zuwa min room kije kiyi raping dina,ki samin kazamin jikinki duk dazu wasu gardawa sun gama goga jikinsu a naki.

Kuka ta saka masa harda rufe ido da hannu,dama nasan yar iska zaka na kallona,na rantse da Allah billahillazi la'ila ha illahuwa Allah daya ragemin hanya sukayi shine suke kokarin tabani sir.

Kaga Allah kallo wurin da suka dinga marina akan naki yarda ai kaga jinin ma ko,ni ban wani gani ba ke dai kawai kin lalace jikin maza kike so,in auren kike so ayi miki mana,har kayan daki zan miki, cewar omar

Iklas tsalle tayi ta make kafada Allah kiyaye na haihu na ragwaje,ai nasan ma yanda kake ji dani baza ka bari amin auren wuri ba,tunda kai kaka tana jin maganarka.

Igbo za a aura miki tunda su kike biyewa suna lagudaki.hawaye ta fara, wlh sir na fada ma ni ba yar iska bace,Omar yasan gaskia kawai maganinta yake son yi sabo da ta daina ganganci.

rike haba iklas tayi kamar gaske tace ohh sir wai kai wanne mai kake shafawa ne?mene kuma?hmmm jikinka Allah ya Omar kamar flour baka ji ba.daria ce ta kwacewa omar,ga iklas tayi wani zaman cin tuwo a kasa, banza omar ya mata.

Minti 1 iklas tace yaya?kinga get out,kofa ya bude mata tare da kamo hannunta ya tankada keyarta waje ya rufe kofar,sai da ta kusa faduwa kasa,tunawa tayi bata fadi kiran da ummi tace tawa Omar ba,jikin kofar ta Dora kanta ya Omar kazo inji ummi muyi break,tsaki yaja ke kinfa isheni kije zanzo wanka zanyi...ok.

Kamshin omar da suka ji shi ya basu tabbacin fitowarsa wani danyen yadi ne sanye jikinsa light blue,har kasa ya gaida ummi,umaru wannan kwalliya haka kamar me zuwa zance?amshe zancen iklas tayi haba ummi ke ba dama mutum yayi kwalliya sai kice zance zai je to shi ya omar wa yake da ita,ina yake fita Da har zaiyi wata budurwa, to uwar shishigi ki bari umaru ya bani amsata mana,

Murmushi omar ya saki ummi bikon matata zanje,tayi yaji sabo da rashin ganina da batayi.sallallami ummi ta fara yanzu umaru kana da mata amma baka fada min ba,ayi hakuri ummi,yanzu ma so nake iklas ta rakani can.dole kaje ai baka kyauta ba umaru.

Da karfi iklas tace bazanje ba kaje kai kadai ina ruwana da wata matarka,ni nasa ka aureta,zamana takeyi,kai ta shafa can kaje da wata badai ni ba.cike da masifa ta mike zata shige daki,omar kuwa daria kawai yakeyi kadan kadan wannan masifa ta iklas da takeyi,riko hannunta yayi tunda bazaki ba suhaila jeki shirya ki rakani,

Tana zaune suhaila ta fito sanye cikin English wears Riga da wando masu kyau,ummi ta gyara mata gashinta,wuce iklas tazo yi iklas kuwa kafa tasa wa suhaila ta shatile kafarta ta fadi kasa,kuka ta fashe dashi me karfin gaske,rufe iklas da masifa ummi tayi.

Omar da ummi ne suka lallasheta da kyar,gani tayi da gaske tafiya zasuyi,fuuuu tazo ta wuce su tare da bangaje omar,mota ta gani rantsatsiya a waje, omar na danna remote ya bude iklas ta balle murfin gaban motar ta shige,

Shi kuwa omar murna yayi a ransa dama haka yakeso,a baya ya zaunar da suhaila shima ya shiga.yasan idan ba iklas tafiyar baza ta yiwu ba saboda definitely ciwonsa zai tashi,amma idan iklas na kusa ya riketa sai ya warke

Tafiya sukeyi sun fara shiga abuja city iklas kawai kumburi takeyi kamar zata ce wayyo na shiga uku na lalace

Tunda suka fara tafiya omar ciwonsa ya fara tashi kawai zufa yakeyi ya rasa inda zai sa kansa, ba shiri ya sadada hannunsa ya riko hannun iklas,da karfi cike da masifa ta fisge hannunta,naga Wanda zaka rike ai yau.

Omar ta kansa yakeyi kawai shi yasan me yake ji,suhaila ce dake bayan mota ta mikowa omar hannu gashi ya omar ni ka rike nawa hannun ka kyale na anty.iklas juyawa tayi a fusace ta zubawa suhaila rankwashi ta make hannun wai ni sa'arki ce,ina ruwanki da shi,ba a son hannun naki to.

Omar na nishi da kyar yake tukin motar kallon iklas yayi idonsa yayi jajir,ki daina dukanta ke iskancin da kikeyi a garin nan wa ke dukanki,kunya iklas taji tace to a kyale maganar kana fama da kanka,hannunta ta miko masa ungo gashi ka rike na taimakamaka.yatsunsu ya sarkafe wuri daya yaci gaba da driving,5mnt omar ya dawo garau dashi,yayinda iklas da shi suka shiga wani hali na shauki kowannensu ji yake jininsa na masa wani yammmm.....yammmm.

Wani katafaren barbing saloon Wanda yake hade maza da mata omar ya parker,mata maza birjik ciki ana gyaran gashi,matan manya da yaran manya,da manyan masu kudi sune a cikinsa,turawa ne masu aiki a ciki.gurin ya hadu kamar a turai,

Fitowa yayi sakale da hannun iklas kamar chewgum,tafiya sukeyi cike da izza,iklas ta raina kanta kyaune kadai ya ceceta,dan duk tafi matan ciki kyau nesa ba kusa ba,sai kallonsu akeyi,suhaila na kusa da ya omar.bangaren mata ya fara kaisu yana zaune,iklas ta karbe daya hannun ta mika masa daya hannun gashi rike wannan dayan ya samu ya huta.

Kujera aka ba omar yana zaune gaban iklas hannunsa rike da nata haka akayi mata gyaran gashi aka gama,suhaila ma an mata,sunyi matukar yin kyau,su Kansu masu saloon din sunyi jinjina.

Wurin maza suka koma wannan karan iklas aka bawa kujera ta zauna gaban omar rike da hannunsa,masifu kawai take ji a jikinta na kamar sha'awa amma ta rasa gane mene take ji.

Omar kuwa a cikin jininsa yake jin bala'in sha'awar iklas wacce bai taba ji ba,amma haka ya daure ya cije.tunda aka fara gyarawa Omar suma iklas ta fara turbine fuska,idan ta kalli Omar sai ta tabe baki,wlh ka cuci kanka ko kyau bakayi ba,minti daya ko biyu zata kalleshi tace ko kyau,wai dole za a je bikon mata.

Gajia Omar yayi yace tunda sahar na son kalarsa ai alhmdlh dama dan ita nayi.mutumin da ba a sonsa anyi yaji an barshi wooooooo....cewar iklas,duk rashin fara'ar Omar iklas daria take sashi.

Haj rahina ce gaban baffan su omar,pls baffan yara 1million nake rokonka ka bani zan canja motata.hajia rigimarki ta isheni duk motocin gidan nan,omar fa baya bari motoci su shekara yake kawo sabbi,jin baffa ya ambaci omar yasa ummansu sadiya daure fuska,kaga alhaji ni ba zancen tambadadde nazo kamin ba,dan iskan yaro Wanda tsabar bin matane yasa ya bar gida.wa ya sani ma ko a waje tayo cikinsa....bata rufe baki ba taji saukar lafiyayyun mari har uku...kunci ta dafe tare da tsagewa da kuka tana kururuwa ta cukume baffa da kokawa tare da danna masa ashar,ai kuwa baffa ya sa kafa ya harbata gefensa,ta bigi center table,

Takadda ya dauko ya rubuta mata saki daya,tare da dafe kansa da kyar ya karasa dakinsa.faduwa yayi kasa yayi sharab...mama wacce abin ya faru kan idonta da kuka ta dago baffa,sannan ta kira maza masu aiki da driver suka kwashi baffa zuwa hospital.

Gaskia kowa ya ga yanda omar ya hadu sai ya kyasa,mata sai kallonsa sukeyi,da yawa suna so su kawo kokon bararsu na love amma yanda suka ganshi kankame da hannun iklas yasa suka ja baya, sai kallo daga nesa,

Take away ya musu na abinci kala kala sannan ya kamo hanyar gida,dadi ne ya kama iklas sosai ganin baza a je bikon sahar ba.

Sabo da murna sai labari takewa Omar,suna isa gida iklas ta hango saleem, da Sauri ta bude mota zata fita,Omar yaga saleem sarai,rigar iklas ya rike gam, kallonsa tayi yace muje gida waccen dan iskan zaki je wajensa ko?

Naji ai na fasa zuwa,to sakeni muje gida mana,kayan suka shigar gida,a cikin motar omar ya bar key din iklas na kusa dashi ta kwace hannunta taje wajen saleem da gudu ta karasa, har sun fara hira akan business da aikin gomnati yanda ake cuwa cuwa kudi na shigowa, wajensu Omar ya taka yaje cike da takama ya zubawa iklas rankwashi muje gida,cike da shagwaba tace ya omar da zafi fa,gani yayi zata bata masa lokaci kawai ya sunkuceta ya sabata a kafada. mutanen layin sai daria sukeyi GOMNATI ta hadu da dai dai ita.



Asmabaffa
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

50-55

By
AsmaBaffa

Daukan da Omar ya mata bai direta ko ina ba sai daya kaita har Palo sannan ya jefata a kujera da karfi tare da shigewa room dinsa,
Sosai Iklas taji zafi yar kara ta saki ohhh tare da dafe hips dinta..ko juyowa baiyi ba bare ya San me take ciki.
Lokacin da su Omar sukaje saloon daya daga cikin yaran Maman Omar tare da wani abokin Omar tabbas suma sunga Omar sun fito daga saloon hannunsa rike da na wata kyakyawar budurwa.

Lallai sunyi mamakin Omar ashe tafiyarsa yayi yana sheke ayarsa da mata,amma ake ta nemansa ana cewa ya bata.
Abokin Omar wato Raj ya daukin alkawarin zuwa ya fadawa Maman Omar cewar sunga Omar a saloon da mace.

Haj.Rahina ta dauki akwati da sauran abubuwan amfaninta kadan tare da Tara yaranta tayi musu hudubar banza sannan ta bar gidan ta koma gidan babban yayansu da ke zaune a garin Abuja shima.
Tasha fada wurin yayanta saboda yayanta Alhaji Magaji mutumin kirki ne sosai ya nunawa Rahina kuskurenta amma Sam ko a jikinta sai ma kara kaimi da tayi wurin son daukan fansa,kuma ta sa a ranta dole sai ta koma gidan Alhaji Mohd.

Tunda su Maman Omar suka dauki Alhj Mohd wato Baffa suka yi hospital dashi gado aka basu bayan aune aune da bincike ya tabbatar yana dauke da ciwon hawan jini kuma ya masa babban kamu,sosai ake kula dashi a hospital Mama ta tsaya tsayin daka wajen mijinta,ita ke jinyar sa,su sadiya ma suna zuwa dubiya amma kullum idan sunje sai sunci mutuncin Mama tare da habaici da zage zage.
Mama na mamakin wai ga mahaifinka a gadon asibiti rai a hannun Allah amma su sadiya suna shirme Allah kyauta.

Sultan ma kullum yana kan hanyar dubiya,kuma shi ke kula da Baffa kasancewarsa likita babba,abokan su Omar ma kungiya kungiya suke zuwa dubiya,kamar yau ma Raj yazo yana dakin da aka kwantar da Baffa tare da wannan yaron me yiwa Maman Omar hidima duk wani aike me nisa da wasu abubuwan wannan yaron wato Nura shi ke wa Mama kusan same age suke da Omar.kuma Nura yana da dangantaka tsakaninsu da Raj.gasu frnds ne shi da Raj,shi yasa suke yawan fita tare duk da cewa Raj me kudi ne,

Raj suna zaune kusa da Mama suna hira sama sama yayin da Sultan ke gyarawa Baffa kwanciya,Raj ya kalli Mama hade da gyaran murya Mama akwai wata magana da nake son fada miki,wato yau kwana uku kenan abin na damuna,gaba daya dakin Raj aka zubawa ido har Baffa da ya samu sauki shima ba a barshi a baya ba,
Naje kusa da saloon in da Nura mun karbi sako a hannun wani Mama wlh munga Omar ido da ido ga Nura nan ki tambayeshi kiji,har kokonto mukayi sai da muka karasa har kusa dashi amma kafin mu is a wajensa sun shiga mota sunyi mana nisa,kuma Mama abin mamaki Omar da mace budurwa zankadediya muka ganshi rike da hannunta da wata yarinya zasuyi same age da suleim dinki,

Sultan kuwa an zo wajen nan ya karbe zancen da cewa haba Ashe nima ba gizo idona ya min ba don nima rannan tabbas naga Omar a garden kingdom sun fito shi da wata charkwadediyar budurwa yarinya karama,Mama kamar yarinyar da ta kawo miki sakon envelop da tace Omar ya bata,kuma kamar wata me tallan kwai a titi da Omar ke taimakawa,
Daga Mama har Baffa Kansu ya kulle,to ko dama maganar Haj.Rahina gaskia ce da tace Omar na gari sheke ayarsa yakeyi bin mata yakeyi,yaushe Omar ya zama haka,maybe zaman London ne ya lalatashi ko kuma rashin samun kulawa daga wajen matarsa ne.
Gaba daya su Mama da Baffa sahar suka daurawa laifi sai kuma Omar da ya biyewa son zuciya tare da zubar musu da tarbiyar gida da mutunci.

Baffa ransa ya kara baci da jin wannan magana,yasan Raj da Sultan baza suyiwa Omar sharri ba,gaskia suka fada,lallai Omar ya bashi kunya zai kuma hadu da hukuncinsa duk ranar da suka hadu.Mama kuwa harda kukan bakin ciki Omar ya watsa musu kasa a ido,amma ya za tayi dole addua ce mafita,
Sosai su Sultan suka Shiga kwantarwa da su Baffa hankali tare da yi musu alkawarin nemo Omar,dan sunce zasu sa ido sosai a kansa.zasu Dana masa tarkon da dole sai ya fada tare da damke wannan tsinaniyar karuwar tasa wato Iklas.

Kwana biyu tsakani Baffan Omar har yau jiki yaki sauki sabida damuwa jinin yaki sauka wahala yake sha wanda sai da su Sultan sukayi Dana sanin fada musu cewar sunga Omar.
Mama abin ya hade mata ga rashin lafiyar miji ga rashin Omar dinta tare da jin mugun labarin yana neman mata.

Su Iklas anyi musu hutu daga Ta boko har islamiyya,sabo da haka Iklas ta rikewa business dinta wuta yanzu ma tace sana'ar saida danyen kifi zata fara,kudin da ta samo gidan Maman Omar su ta tattara kaf ta siyo katuwar freezer sabuwa dal ta ajiye a kitchen,saura kawai ta fara saro kifi,duk tsare tsaren Iklas Omar bai sani ba,
Dukkansu suna zaune a tsakar gida da yamma lis,Iklas na kwance a kan katuwar tabar ma da wata Rigarta doguwa ta atamfa tayi kyau,Suhaila na kan cinyar Ummi kwance tana karanta Arba'una hadith, Omar yana kan carpet gefe tare da laptop sai nunawa Ummi wakar shata me ganga yakeyi,Ummi har gyada kai take tana Allahu akabar oh kaji mazan jiya,Allah sarki jiya ba yau ba,Umaru danno min ta Ali makaho da Dan kwairo naji..daria yakewa Ummi ganin abu ba wani Dandano amma Ummi dadinsa takeji ko dan azamaninsu ne akayi wakar,

Iklas littafinta ta dakko tana ta buga lissafin sana'ar kifi da zata fara domin gobe take sa ran sarowa,juyowa tayi dan Allah Ummi a canja mana wakar zamani amma wannan mu bama fahimtar me suke cewa,kaka Ummi dalla mata harara tayi aike ba hankali gareki ba amma ai sune sukayi wakoki masu ma'ana,tabe baki Iklas tayi pls ya Omar kai mana wakar Timaya ko ta Devido,
Ai kece Timayan see ur mouth anki a kunna miki manya na maga kina shiga ciki cewar Omar,murmushi Iklas tayi cike da shagwaba ta ajiye littafin dake hannunta kajika ya Omar da nawa ka girmeni,ai ko zaka girmen kadan ne,hmm na San da auren wuri nayi da tuni na haifi kamarki,ummi ma tace fada mata Umaru in banda rashin kuya dudu shekararki nawa saboda kinyi tsayin kafa,dadin abun dai a gaban Umaru kika fara Al'ada,ba wani iyayi da zakiyi masa ,kukan shagwaba Iklas ta fara haba Ummi wai mene haka dan Allah,kunya Iklas taji sosai,Omar kuwa masu rayuwar London ko a kwalar rigarsa,saima kafe Iklas da yayi da kallo,idonta ta dauke daga kallonsa a ranta tana kai Sir din nan dan duniya ne harda kallo na.
Su dama Maza munafukaine abinda suke so kenan dama taji frnds dinta suna fada a schl.

Washe gari da wuri Iklas ta saro kifinta Carton daya na gwajin kasuwa,Omar yana bacci bai San Iklas ta fitaba,sai fitowa yayi yaga Iklas na shirya kifi a fridge Omar ya shiga kitchen din dauko furarsa dagashi sai jallabiya fara me hula dai dai jikinsa gashi sabo da baya fita baya shiga rana ya kara haske sosai skin dinsa har wani sheki takeyi,
Kamshinsa ne ya bigi hancin Iklas a take jikinta ya mutu murus,kasala ta sakko mata,ta gefenta ya raba zai wuce jikinsa ne ya gogi nata baisan sanda a hankali yace ushshsh shshi sabo da wani irin yanayi daya tsinci kansa ciki.furar ya ebo a glass cup tare da zuka,ke me kike yi haka,duk wannan kifin da wa zaki cinye?kallonsa Iklas tayi tare da murmushi tace au baka da labari ai kifi zan fara siyarwa danye,da kudin da Baffa ya bani na kafa jarin,kaga sana'a goma maganin me gasa,kaga kala kala nakeyi kenan,
Jinjina son kudi irin Na Iklas yayi a ransa,idanuwansa kyawawa masu matukar haske ya zubawa Iklas Wanda yasa Iklas dimaucewa hade da jin kunya,sunkuyar da kai tayi ta tsinkayo muryar Omar ba a nan gidan za ayi wannan sana'arba,baki isa ki cika mana gida da karni ba,duk sana'ar da kikeyi bata isheki ba sai kinyi kalar wannan,haba mene aibun wannan sai da kifin,ummi ma fa da kyar ta yarda wai bata so nayi,nidai ina son siyarwa sai nayi,

Tamke fuska yayi to baki isa ba,ba a gidan nan ba na fada miki idan kuma kinga ina wasa dake kiyi na gani,da shagwaba tace pls Sir nasan in ka fada Ummi bayanka zata bi,ke kika sani ni kam na gama magana ko ki je ki mayarwa Wanda kika siyo wajensu ko a cinye a gida,ko ki bayar kyauta,tab lallai inyi asara ba riba,sai dai ka biyani kudin Dana kashe in kuna so na daina,
Zare ido Omar yayi ina wasa dake,tsorata tayi ta fara bin bango tana rabewa hade da tafiya kadan Kadan ta fice da gudu daga kitchen din tana ae na fada a biyani kudin Dana kashe tare da kulewa dakinsu.

Daria Omar yayi sosai ya fita shima,washe gari da safe Omar ya fito da brush da toothpaste zai shiga toilet sai ga Iklas ma ta fito tana kallon Omar ta wuce da sauri ta rigashi shigewa toilet din.Ummi sakin baki tayi yau naga yar banzar yarinya,ke dan bantan ubanki fito Umaru ya shiga,kyaleta Ummi zanyi maganinta,daki Ummi ta koma tana cewa kunfi kusa.

Iklas kuwa har ta fara brush Omar ya jawo rigarta kiiiiiii ya jefota waje,kafin ya rufe toilet di Iklas ta kara bankawa ciki,murmushi Omar yayi oh..yanzu na gane me kikeso Ashe wanka kike so na miki,damkota yayi kamar zai fara cire mata kaya tuni Iklas ta fara kuka tana Neman agaji,da gudu ta fito daga toilet din,Omar ya rufe kofar tare da Jan tsaki karamar yar iska da kin tsaya kin gani.
Iklas kuwa a ranta tace kut lallai Sir cikakken dan iskane.yau Iklas shiri tayi tsab domin zuwa gidan su Omar so take ta dubo masa lafiyar su Mama,fito tayi Palo tare da yiwa su Ummi sallama,da sauri Omar yace muje tare unguwar na kaiki,batayi musu ba ya kira a take aka kawo wata new Car din.

Tofa kunji masu karatu.



ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

60-65

By
Asmahbaffa




Please Login or Register in order to submit comment