Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwantar Da hankalinka ba wani ciki,haka ake ciki ba cuta r laulayi?ni rawa ma nake son yi,remote ta dauk tare da danna kida,
Omar ne ya karbi remote ya canja waka tare da karo vol na speaker yace oya tashi kimin wannan rawar, to ai slow music ne sai dai in ka mike tsaya saboda wannan rawar kalarta kenan ya dace ace da namiji,

Kawai kimin na gani pls cewar Omar nanfa Iklas har bending down takeyi a slow,omar ya tuna tana da ciki kar ya zube,ya kashe kidan du,Gomnati zo kiji wata magana?tana zuwa ya dauketa yayi ciki da Ita suka Lula wata duniyar ta ma'aurata.

Omar ya kara mannewa Iklas saboda cikin ya kara sa mata wani sweet din daban,Iklas ta kammala degree dinta,yayinda take zuwa office din Omar yawanci tare sukeyin aikin,aikin Hajji da Umrah sunje da yawa,yau Omar yana Office Iklas ta hade cikin wani unique material kamar yan mata,ta shirya girkinta a dan wani basket me tsananin kyau,prince yana wurin Baba Karime,driver ne ya kaita Office din Omar,tana zuwa building din mutane sai gaisuwa ake kaiwa,yayin da Omar yace sunanta Gomnati,kowa da Gomnati yasan Iklas,ya fito mutane yaransa suna take masa baya zaije Sallah,ya hango motar Iklas an kawota,da Sauri ya sallami mutanen ya karasa wajen motar cike da takama,dakansa ya bude mata ta fito,hugging dinta yayi,wata siririyar sukaji tayi musu sallama,juyawa sukayi dan ganin ko wacce,wata yar budurwa ce zata kai 25yrs sai mayen kallo takewa Omar tare da cewa sunana xahra Eabraheem,ina aiki a company ka,pls ko zan iya ganinka,
Wani matsiyacin kallon Omar yayi mata tare da Kallon Gomnatinsa sannan yace ki tambayi my heart idan ta yarda fine,Iklas wacce ta gama kumbura sabo da kishi matsawa tayi jikin Omar har dagen kafa takeyi wai dole sai ta kareshi Xahra na kalle mata miji,Da masifa Iklas tace u r fired from ths company as from 2day kar na kara ganinki,

Allah sarki Xahra ta jawowa kanta kuka ta farayi tana ba da hakuri,Omar yace my peace a barta pls,ba tare da Iklas ta kalleashi ba tace baka da wannan damar yaro,dariya Omar yayi yanda Iklas ke kuri da nuna takama kamar company ta
Yace kalli mutane yanda suke bina suna biyayya ke kuwa yar cukula dake sai ki tamin tsiwa,baki ta turo cike da shagwaba ni a haka kake zuwar min? zigidir kake zuwa duk wani tabo dake jikinka na sani,su kuwa fa sai ka dau wanka,
Hanci ya lakuce mata tare da mika mata key din Office bari nayi Sallah kar na rasa jam'i,kiss ya manna mata a goshi sannan ya wuce,

Xahra ce ta karaso wajen Iklas tana rokonta akan a yafe mata,karki damu amma dole na canja miki Company,gaba Iklas tayi da basket dinta na food tace wa Xahra follow me,
A kujerar Omar ta Office ta zauna tana juyaya da ita nan take tayiwa Xahra transfer zuwa company da Sadiya ke kula dashi,sai godiya take.
Tunda Iklas ta zauna take faman shigar da kudi ta computer tana calculation,Omar yana shigowa ta nuna masa komai sai murna yakeyi Gomnatinsa wise ce,

Iklas yanzu ta mallaki kadarori da dama,sosai take juya kudade itama,Suhaila da Ummi sai abinda suke so take musu,frnds,da dangin mijinta du tana kyautata musu da arzikinta da karfinta,har tallafi take kaiwa gidan marayu tare da Dora Omar akan harkar taimakon talakawa sosai,
Gidan Kajin Mama wata rantsatsiyar mota ce ta shigo bayan mintuna Omar ya fito cikin shiga ta Alfarma kamar wani sarki,budewa Iklas yayi ta fito wow Iklas ta gama zama queen,handbag dunta na hannun Omar,Prince ma yana gabansu ya hade sosai,Iklas da yaron cikinta Wanda batasan tana dashi ba,
Ma'aikatan sun San Iklas amma basu ganeta ba sun zata bakuwa ce tazo daga kasar larabawa,yanda suka ga Omar yana hugging dinta yasa suka gano matarsa ce,wani cikinsu yace daga Kuwait naji ance ya auro matarsa
Sai da Iklas ta sanar dasu cewar Itace Gomnati me siyan Kwai da Apple,sai mamaki sukeyi suna tayata murna da farin ciki,wai dama Ashe Allah yayi itace matar Ogansu kamar wasa suka taba haduwa a wajen,har fada sukayi ranar,gashi Ashe har sun haifi Prince,
Iklas Karin Abashi tasa Omar yayi musu,ita kuma ta raba musu kyautar kudi,sannan suka bar wajen,Ma'aikata sai Albarka suke sa mata sosai,tare da mijinta,ranar sunsha Addua.

Iklas tana gidan Mama Omar ya barta ita da Prince suje su kwana daya,zai je gobe ya daukosu,Gomnati an baje suna musu dasu Najja da Ummi sunce ciki ne da ita Gomnati tace lallai kuna bata bakinku,dan kunga na canja jin dadine mijina yana kula dani,ba wani ciki Omar yace sai nayi 5yrs zan kara haihuwa,gwara ku kyaleta cewar Mama.

Shuru sukayi suka kyaleta,sunyi shirin kwanciya sai ga kiran Omar a wayar Iklas, hello honey? Kinga ba wani honey Ina compound fito mu tafi gida,kaifa kace na kwana honey, ae na sani ai na fasa yanzu,amma saida ka bari na fada musu,in ba so kike raina ya baci ba kawai ki bar musu Prince kizo mu tafi gida ko kuma nazo cikin gidan na daukeki,,

Shagwaba ta fara yanzu dan Allah ka kyauta min?hmm zo muje gida kyayi shagwabar a can,dit ya kashe wayar,Kinga ki tashi kibi minji kar yazo yana yi mana rashin kunya da tijara a gidan nan akanki nasan yanzu kwa zama Aljanu cewar Ummi,
Ikkas tana fushi ta dauki Jakarta da kayanta,ta barwa Prince nasa tayiwa Mama Sallama ta fita,

Shiga motar tayi tana kumburi,Sorry my heart na kasa bacci ne shi yasa cewar Omar, Gomnati tace muje kawai nasan me kake so,amma baka kyauta min ba ka sani ko?haka kake min sai ka amincemin naje Unguwa yini ko kwana sai kace ka Fasa ka dawo ka daukeni,ko ka turo driver ya daukeni,
Baza ki ganeba my liver bana gajiya dake ne,bana iya hakurin rashinki kusa dani, nima ai bana iya hakurin dakai kawai dai ina daurewane,ke kina iya daurewa ni kam ban iyawa wlh,na gaji ma Hutu zamu dauka muje london, a'a muje saudiya kaga an kusa aikin hajj cewar Iklas, duk inda kike so ai nan Zamuje Gomnati ba a ja dake,
Dukan wasa tayi masa kadan a kirji,ka gani ko ban son Tsokana,suna shiga gida da kyar suka iya shiga bedroom kamar zasu cinye juna tun daga compound,sun kwashi sabon Amarci a ranar.
Abdallah an zama katon saurayi ya gama degree ya dawo,yayinda ya like shi Suhaila zai jira tayi Candy ya aureta,Itama Suhaila tana son Abdallah sosai.Suleim kuwa tace karatu zatayi me zurfi kamar Yaya Omar.Najja kuwa ansha bikinta Iklas sune kan gaba,amma Omar ya hanata sakewa,kullum yana like da abarsa, an kai najja Sokoto,ta auri wani local gvt chairman.
Aisha ma ta kara haihuwar lafiyayyen da Namiji,Sadiya kuwa yanzu Allah ya bata ciki wata 2,mijinta kamar ya cinyeta,sauran kannensu su biyu suna part din Mama tana kula dasu.

Iklas taga cikinta yana ta girma,gashi kamar alamar ciki take gani,tabbas su Ummi sunyi gaskiya,lallai maganar Omar cewar Allah ya nuna musu Ishara gata ana mata allurar planning gata da ciki yanzu,
Kuka ta sakawa Omar daya dawo,wlh honey ciki ne dani na shiga Uku,
Har asibiti Omar ya kaita aka tabbatar ya wuce 3mnths,Omar da kyar ya kwantar mata da hankali ta hakura,tasha kuka kuwa,Omar Sam bai nuna yasan tana da ciki ba tun tuni.biyeta ya dingayi yana lallashi da salon wayonsa harta hakura.

A airport na Abuja Omar da Iklas suna manne da juna wannan tafiyar an bar Prince wurin su Mama,Jannat matar Saleem da tsohon cikinta zasu tafi egift suka gaisa da Iklas tare da wucewa wajen nasu screening din.
Omar tun kafin a fara yi musu screening domin zuwa kasa me tsarki,yana wajen Iklas dinsa,minti 1,2 yazo ko kina bukatar ruwa?juice?snacks etc haka yake tayi ko yazo ya danyi Hugging dinta yana kissing dinta,a chair ma daya zauna tana kan cinyarsa, yana ta lallabata,sai shagwaba take masa,tun mutane basa kallonsu har suke kallonsu suna sha'awarsu kamar wasu turawa ana zuba love,
Tashi Omar yayi tare da dawowa wajen Gomnati dauke da ruwa Faro ya mika mata,kiss ta bashi a kumatu,wata tsohuwa ce ta matso kusa dasu ta fara zazzaga musu masifa,wannan aikin hajjin zakayi kuwa dan nan,wannan baza ka barta kuyi Ibada ba,kabi ka like mata,wani Iskanci ne wannan kana lasheta da tsotsa kamar tsohon maye,

Kema da laifinki munafuka ke kike bashi hadin kai wannan bazai barki kuyi addini ba,,ka hana kanka ka hana wani ibada saboda Iskanci ya ratsaka, tsaki tsohuwa taja tare da komawa cikin mutane tana ci gaba,Maman Khayree ce tace dan Allah Iya ki kyalesu haka,irinkune kuke jawowa yara na muku rashin kunya,yo bazan fadi gaskiya ba fisibilillah yaran nan har karar tsotsa kakeji kamar suna shan alawa,mu bamu San wannan ba,ohh ni Delu karshen duniya yazo sai ta fashe da kuka,kaji fa tsohuwa da karfin hali.
A jirgi ma Delu ta sawa su Omar Ido,idan Omar ya rungumo Iklas ko yayi wani abun sai Delu tayi masa dakuwa wato ambola,dariya take bawa su Omar ma

Iklas ana Madina,ita kadaice yau ta koma hotel dinsu bayan ta dawo daga masallaci tayi Sallar Isha.
Darul salam Hotel ta shiga har Room dinsu ita da Omar sai yatsina takeyi ta gaji,tana shiga Room dinsu Omar yana kwance yana hutawa da alama bai Dade da dawowa ba shima,Hi dear kawai tace tare da shigewa toilet,wanka da Brush tayi ta fito tayi shirin Bacci,shima Omar hakan yayi,tana zaune tana zuba kamshi tare da cin Apple,zuwa yayi ya zauns kusa da ita tare da rungumota jikinsa yace wifey najiki so silent,mene kara narke masa tayi tace wash na gaji massage nake so,
Kwantar da ita yayi on bed flat ya Fara mata tausa me dadi,yaga ta fara masa bacci sai ya koma yi mata cakulkuli,nan ta fara dariya sosai,ba shiri ya tsaya tare da cewa me nake gani a hakorinki kamar Gold teeth guda daya a hakoran sama gefen right side?dariya Iklas tayi tare da cewa my King Hajiyayye kenan, na koma Hajiyayye nima,yau naje hospital aka samin,haba inta zuwa Sadiyya ko hakori daya babu,ya ka gani my King yayi ma kyau,idan baiyi ba baka so na cire,

Omar Wanda ya tsaya ya kasa motsi saboda yanda hakorin makkan yayiwa Iklas mugun kyau,da Sauri yace no ina so kinga yanda yayi miki kyau kuwa wifey,I love it. Bakinta ya fara tsotsa kamar sweet,nan Iklas ta fara sarrafa Oganta Omar,kafin kace me sun zauce akan juna,nishin sweet tare da furtawa juna sweet words masu wuyar fassara da nauyin dauka ga me karamin kai.sunna suke daffakawa ba kama hannu kamar su hadiye Kansu.



ALHAMDULILLAH

da Allah ya bani dama da ikon Kammala wannan littafi nawa,ina fata ya fadakar ya nishadantar tare da fatan kunji dadinsa masu karatu.

Masu comments akan wannan littafin Ma'aikaciyar Gomnati,masu bibiyarsa kullum,da masu tambayarsa idan ba ayi posting ci gaba ba,duk kowa ma da kowa naga sakonku,bani da bakin Godiya Tsakanina daku sai Addua,naji dadi, nayi matukar farin ciki ba adadi.naso na sa Sunan duk wasu masu comment a Novel din nan domin karramaku readers amma ba time.gaba dayanku NA GODE NA GODE KWARAI
Allah ya biya muku bukatunku. Love u all.really miss u.kamar kar na daina typing wannan Novel wlh amma ba dama.Allah sarki Iklas da Omar dina.


Littafina me zuwa bayan sallah idan Allah ya kaimu da Rai da Lafiya shine:

✳CIRANIN AMANA✳

Ina fatan yafi MA'AIKACIYAR GOMNATI komai da komai Insha'Allah.

Allah sadamu da Alkhairinsa, Allah sa muyi azumi lafiya mu gama Lafiya.Allah ya Bamu lafiya me dorewa,ya Gafarta mana zunubanmu, ya Bamu Nisan kwana me amfani,ya samu a Aljanna,ya tseratar damu daga wuta,ya azurtamu da arziki me amfani duniya da Lahira.


GODIYA DUBU DUBU MALALA GASHIN TINKIYA MUTANENA.



AsmaBaffa.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment