Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba tare da tace komai ba,fuskarsa ya matsar saitin tata ba tare da ta shirya ba carab taji yana kissing dinta kamar zai cinyeta,kwace kanta tayi da kyar sai fushi takeyi sosai,Omar har ya fara fita daga hayyacinsa,ba wasa a fuskarsa yace tashi mu tafi gida,kafada ta make ya daka mata tsawar da ba shiri ta mike tsaye,duk iya shegen Iklas tana mugun tsoron Omar,hannunta ya kama ya hada mata kayanta a yar Jakarta data dauko ya sata gaba suka fito, ba Wanda ya kulasu sukayiwa su Mama sallama ya zaga ya bude mata mota ta shiga,shi kuma driver ya bude masa ya shiga,suna bayan mota driver ya jasu,Omar sai janta yakeyi da magana amma ita shuru shuru da kyar takeyin Magana sarauta ta motsa.

Take away ya musu na abubuwan ci suka karasa gida,koda suka fito daga motar daukanta yayi kamar jaririya har bedroom ya ajiyeta bisa gadon sannan yabi lafiyar jikinta ya kwanta rabinsa na jikinta,har nishi takeyi amma batayi masa magana ba,wifey ki huce mana pls bana son fushinki, a hankali tace ni fa ba fushi nakeyi ba,ka dan dagamin jiki zaka kashe min Baby,murmushi Omar yayi ya saba da shiriritar Iklas ko ya idan ta nutsu sai yaga kamar fushi takeyi,baya son ya ganta shuru shuru,yafi so ya ganta kullum cikin nishadi da barkwancinta tana sashi nishadi,sabanin yau daya ganta ba yanda ya saba gani ba,komai in yace sai yaga ba wani surutunta ba labari kawai sai yaga ta yarda,
Abincima yana sani yasan tana son kaza gashashiya fiye da sauran nama,ko ya kawo naman rago sai yaga taki ci,amma kaji tana ci sosai,
Ko a girki tafi yin amfani da kaji.

Naman tsire na rago ya mika mata ya dauke kazar yace yau wannan zaki ci,sai yaga ba musu ta fara ci,da ace Dane da tuni ta turmusheshi a kasa tace zata kwace kajin.
Kajin ya mika mata wasa nake miki ga naki,karba tayi ta fara ci nan ma,da kansa yayi mata wanka ya shiryata,har yau sai ya ganta taki cewa komai,kuma a fuska yaga bata fushi bare yace wani abu.
Tunani ya farayi anya kuwa Gomnati lafiya take yau,kai da a kwai matsala gaskia.

Har suka kwanta batayi magana ba,hugging dinta yayi sosai kamar zai tsaga mata kashi amma baiji tace komai ba,kunnenta ya riko da hakoransa ya dan cija kadan still ash...kawai tace tayi Gum.

cikin salon rada a hankali murya can ciki yace Wifey yau lfy kike kuwa?meke damunki?mikewa tayi ta zauna akan bed din tana cije lips,Lfy wai mene ne?kuka ta barke dashi sosai wannan ba shagwaba,kuka takeyi sosai,
Gaba daya Omar ya rude ya shiga damuwa wannan kukan na Iklas yasha bam bam da sauran kukanta daya sani ,bai taba ganin wannan kukan na Iklas ba.
Shigarda ita yayi jikinsa sosai yana tambayarta meke damunta,sai da taci kukanta ta koshi sannan tace Wallahi na gaji da cikin nan,Dan Allah ya Omar kasa a cire min cikin nan,tana kuka tace wallahi ya isheni na gaji dashi dauriya kawai nakeyi.yanzu ma Chinese yake ta min a cikina har ciwo nakeji,duniyar tayi min zafi haka kawai nake jin bakin ciki.

Wani azababben tausayin Iklas ne ya lullube Omar ganin iya gaskiyarta ta fada ba wasa ba shagwaba a cikin zancen.ga wani mugun sabuwar kaunar Iklas data kara yi masa dirar mikiya,
Cike da lallashi yace kiyi hakuri kinji ai kin kusa haifoshi saura 3-4mnths an wuce rabi kinga an kusa,da ace nasan haka ciki yake wlh da bazan yarda kayi min ba,kayi ta yimin wayo na yarda gashi ni kadai nake shan wahala,Dana yi yaji ma kin zuwa kayi saboda ka samu abinda kakeso,baka damu dani ba,

dama Ashe su Ummi gaskia suke fada min namiji ba dan goyo bane, naki ji na dinga yi musu rashin kunya akanka,da na sani wlh da suka fadamin namiji ba dan goyo bane to da tuntuni Dana goyaka na shiga cikin rana da kai na zame zanin goyon na sakeka a tsaye ka fado ka kwala kanka da kasa ya fashe.sosai Omar ke dariya sai yanzu hankalinsa ya kwanta yaji dadi Gomnati ta samu saukin jikinta,dama shi haka ya saba da Gomnati,bai so ya jita shuru.cike da so da kauna ya dinga bata hakuri baije biko da wuri ba,da kuma cikin daya sa mata yana damunta,dole yasan masu ciki basa jin dadin rayuwarsu.
Lamo
tayi tana jin lallashinta da yake tayi da kalamai masu dadin gaske,har ta samu tayi bacci.

Washe gari da safe bai iya zuwa office ba ganin Iklas kamar bata jin dadi,abincinma shi ya musu indomie suka ci,suna zaune a Palo suna kallon news Iklas na cinyar Omar yana mata tausa ko maganar kirki batayi,zumbur ta mike tsaye wayyo ya fara naushina yau harda kafafunsa yake ta min,dan Allah ka kaini asibiti bani da lafiya,shine lafiyar taki ai wannan naushin da yake miki wannan yana nuni lafiya yake Babyn cewar Omar, zama Iklas tayi tace kai wannan naushin da a fuska ya min da tuni ya fasa min hanci,murmushi Omar yayi ya shiga shafa cikin yana kanafa nausar min wifey daga yau ka dena in ba haka ba zaneka zanyi,dariya Iklas tayi yanda Omar ya dage yana yiwa yaron fada kamar an haifoshi.
Gobe ne ranar zuwanki awo ma ai ba sai a duba lafiyarsa ba,OK tace Allah nuna mana goben,karar doorbell sukaji,Omar ne ya mike tare da bude kofar,mamaki ne ya bayyana a fuskarsa ganin Sadiya da Aisha yau sunzo gidansa a ransa yace Allah sa lafiya dai,
Iso yayi musu suka shigo har palon,Aisha cikinta haihuwa ko yau ko gobe,cike da girmamawa Iklas ta tarbesu da fara'a, lemo da ruwa ta kawo musu sannan ta gaishesu,Omar sai dadi yakeji Iklas ta dauki nasiharsa akan yan uwansa,sosai suke hira,sun Dade a gidan,Iklas tayi musu girki sunci sun sha,suna ta jin dadi,Omar ne ya kare musu kallo da gani an San basa jin dadin gidan miji.

Sadiya fatan dai lafiya kuke zama da mazajen naku,sunkuyar da kai Sadiya tayi cike da kunya tace Hmm kai dai ayi zaman hakuri kawai yaya Omar,amma batun zaman jin dadi babu,ganin maganar yan uwace Iklas mikewa tayi zata bar wajen suyi sirrinsu,Aisha ce tace ina zakije kuma?yanzu zan dawo,no kinga zo ki zauna ai an zama daya haba sai kace wata bare,
Dole Iklas ta dawo ta zauna,nan Sadiya ta fadawa Omar irin Halin da suke ciki,daga Omar har Iklas sun tausaya musu matuka,dama shi yasa duk me Neman jefa wani cikin masifa kansa zai fada karshe,
Omar yace amma kun San da haka kuka ki fada a karbo muku hakkinku,Aisha tace hmmmm yaya to ya zamuyi mudai munga rayuwa,Umma ce duk ta jefa mu cikin wannan Halin Dan Allah yaya Omar ka yafe mana,munyi kuskure Wanda a lokacin nutsuwa bata zo mana ba.karma Ku damu kanku ni bakuyi min komai ba,ba wata Matsala kuma zan nemi mazajen naku,haka sukai ta godiya sannan suka shiga motarsu suka tafi.

Iklas ta kara darasi dama ance duniya makaranta gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.sai godiya take wa Allah daya bata miji Omar,a ranta tace dole na nemo makaman yaki na zaman aure na kara rike mijina,nan take ta buya a kitchen ta kira Angel da princess kawayenta nutsatsu wayayyu,duk da basuyi aure ba tasan suna da hankali,murya kasa tace dan ubanku kuzo akwai matsala dit ta kashe wayarta ta koma wajen Omar.
Kallonta Omar yayi Gomnati ya akayi ne?yaushe kike so a nemo miki Admission a university? Kai ana ta kai wa yake ta kaya,sai na Haihu Kuma akwai wasu harkoki Dana ke so naga na gama saita su sun hau tsari tukun,
Ba kya son Aikin Gomnatin ne yanzu,Honey dafa ba yanzu bace nayi hankali tun yaushe yaushe rabon da kaga na dauki jotter ina rubutu,gaskia da nayi shirme Honey.
Omar daria yake a ransa matar da yanzu ta gama bashi dariya da shiriritarta amma wai kuri takeyi tayi hankali.

Ibzzy Boy yau Monday sai da ya tabbtar Omar yana Office sannan ya hadawa masu gadin gidan wayo yace Frnd din me gidan ne sako yazo karba,.
A Palo yaga Ilkas da cikinta a gaba tana shan water melon da madara,kanta bako dankwali daga ita sai wata dangalgalar riga iya cinya me fadi, wani bakinciki da kishi ne ya kama Ibzzy, Iklas mutum kawai ta gani a kanta,abinda Ibzzy bai sani ba yana shiga ciki securities suka kira Omar a waya suka shaida masa,dama ya bar Office ya kusa da gida yanzu baya dadewa saboda Iklas cikin yana damunta.
Minti biyu driver sa ya kawoshi gida,Iklas a gigice ta mike jikinta na rawa ta dauko Hijab zata sa Omar yayi Sallama,Ibzzy da sharbebiyar wukarsa a hannu kamar sabon kamun hauka,da sauri Omar ya kamo Gomnati ya rungumeta kam,itama haka sai rarraba ido takeyi,securities Omar ya kira ya nuna ibzzy da yatsa tunda kai bakin jahili ne ko mahaukacine ban San nufinka kan matata da kake bibiyarta ba amma tunda naga karamin dan Iska ne kai zanyi maganinka,nanfa securities suka kama jibgar Ibzzy, Iklas tace naga dukan wasa kuke masa ku kara sosai,sai da sukayi masa jina jina,sannan Omar ya tsokani Iklas dan yaji kalar muguntarta da take fada tana da ita,wifey a kyaleshi haka?

Ba ayi masa dukan tsoro da yasa naji ba,nafa firgita yaron cikina sai da ya yi tuntsira gudi gudi.
Omar matse dariyarsa yayi to yanzu me kike so a masa?a balla masa kafar left side,Hannun right side sannan ta radawa Omar ayi masa kaciya da fashashiyar kwalaba sai a kyaleshi sauran kuma Allah ya saka min a lahira.
Lakace mata hannci Omar yayi yana dariya wifey muguntarki yawa gareta bayan wannan har na lahira kike nema a kara saka mini.

police Omar ya kira sukayi gaba da Ibzzy Boy.Ibzzy yayi Dana sanin zuwa gidan Omar da yayi,yana kallon Iklas yana ki taimaka min dan darajar Allah ki bawa mijinki hakuri,juya masa baya Iklas tayi tare da kara shigewa jikin Omar tare da cewa gwara ka rufawa kanka asiri ka daina Neman taimakona dama ina jin haushin ka taba kadeni a mota,zan iya sawa a kwankwatsa ma kashin hakarkari,tuni police suka kara rankwala masa Kasan bindiga suka ja shi sukayi gaba dashi.

Cikin Iklas ya cika wata 9 yayi kato da yawa,kullum sai Iklas tayi kuka da dana sanin biyewa Omar da tayi ta samu ciki,da kyar yake lallabata,ganin gaba daya Iklas bata da sukuni yasa Mama tace dole Omar ya dawo da ita gabansu,Omar haushi yake ta ji shi taya zai rabu da Iklas,bazai iya bacci ba ita ba,itace far in cikinsa rayuwarsa ma kaf saida Iklas yake jin dadinta,yanda Omar ke son Iklas da ji da ita ko kansa baya so.amma Mama tace a kaita gida kuma bama irin 1wk ba har sai ta haihu tayi arba'in,abinda ma yafi kona masa rai ma wai Mama tace bazai koma gidan da zama ba sai dai ya zauna a gidansa shi kadai.shi kam bazai Iya ba.shima dole ya zauna a can tare da wifey dinsa,
Iklas anyi laushi in ka ganta kamar ba ita ba ta kanta kawai takeyi,ji takeyi kamar mutuwa zatayi,Ashe haka cikin yake da wahala,yau Omar ya hada musu kayansu zasu koma wajen Mama, Iklas tana zaune ta zumbula hijab har kasa don cikin yayi girma da yawa,tayi jigum da ita tana tunanin lahira.
Duk iyayin nan an ajiyeshi gefe,komai akace tace sai Allah ya saukeni lafiya,amma batun daukan wanka duk har tayi dinkunan suna an ajiye su kala kala.
Omar ma yakai dinkuna da yawan gaske na Iklas, Baby kuwa yasha ksiyayya wajen Omar tun kafin yazo duniya,suna hangar zuwa gidan Mama Iklas tace a kaita wuse market,Omar ya tambaya me zakiyi a kasuwa,hmmm kai dai kasa driver ya kaini,
Umarni driver yabi har wuse market Omar zai bita tace kayi zamanka yanzu zan dawo,minti kadan ya hangota a shagon wata yoruba ,sai gata ta dawo da Leda a hannunta.
Bude ledar Omar yayi ya leka mene wannan black,kwacewa Iklas tayi sabulun salo ne fa baka sanshi ba?me za ayi dashi?jariri akewa wankafa dashi Ummi tace yafi fitar da dirtyn jariri, murmushi Omar yayi lallai kaga me jego nan tanaji kikeyi?kai ta daga masa kawai wai ae.baza a wankemin yaro da wannan sabulun baki ba,in ba dirty zai kara ba wanne dirty zai fitar,cewar Omar.
Kallonsa Iklas tayi yaronka ko nawa,na sha wahalata na dauki ciki 9mnth na haifi abuna ka nuna min iko a kansa, tsokanarta Omar yayi cikin kasa da murya ke kikayi cikin?itama a hankali yanda driver bazai ji ba tace tare dai mukayiwa juna tunda nima nayi gwagwarmaya,amma tunda kace haka u wl see bari na haifoshi Allah sai naga dama zaka daukeshi gwara ka lallabani ka fara kamun kafa,dariya Omar yayi iklas abin dariyarta a jininta yake kawai, ta karfi Iklas ta maidashi yaro shima biyeta yakeyi,hannunsa ya sadada ta cikin hijab dinta ya rungumo dukiyar fulaninta,tare da kwantota jikinsa yana wasa dasu, kamshinsu ya cika motar,kallonsa takeyi sosai yanda Omar ke kara kyau kullum,a ranta tana gaskia Allah ya bani miji tab zuki.

Wasa takeyi da hancin Omar ta lotsashi ta jawoshi,sai rada mata zafafan kalamai yakeyi masu rikita Hankali har suka isa gidan Mama.
Mama ce tace Iklas da Ummi zasu dinga kwana,Omar bai so haka ba yafi so ace Iklas ta koma room dinsa na gidan inda zai dinga lallabawa wajenta
Haba Mama room din yayi musu Kadan ta koma part dina,Harara Mama ta zubawa Omar nan take yayi shuru yasan Mama ta ganoshi,Iklas ya dan dungura da kafarsa yana mata signa wai tacewa Mama room guda za a bata ita kadai,kafada ta make wai taki din,Mama na kallonsu abinda sukeyi, kara tabo hannunta yayi wai ta fada,kafada ta make masa, ya nuna kansa wai ni din?kai ta daga alamar ae, tare da sa hannunta biyu a bayanta kamar jariri ta goya tare da taroshi irin kar ya fado ta sauke hanun tai masa alama da yatsa lalala,wai nufinta namiji ba dan goyo bane.
Da Sauri tayi Inda Mama baza ta gani ba,bata San an ganta ba,Mama a ranta tace ikon Allah yarinyar nan ta fara kunyata ta fara girma,bata San Iklas kawai da dalilinta na yin hakan ba,dan tasan Omar wuya yake bata ne, cikinta ya girma kuma shi bai San kadan ba,ga wahalar cikin dake jikinta ba wata cikakkiyar lafiyace gareta ba.

Mikewa Mama tayi,yana ganin haka ya matsa Kusa da Iklas yana rokonta ta zabi room ba lallai nasa ba,amma ta zauna ita kadai,hmm dear kenan ka bani tausayi,langabewa yayi sai rokonta yakeyi ta canja room, saida da ta kalli gabas da yamma kudu da arewa taga ba kowa sannan ta matsa jikinsa tana shafa fuskarsa kayi hakuri baby this time around bazanwa Mama gardama ba,kayi hakuri zaka dinga zuwa wajena kullum muna gaisawa.

Cike da jin haushi Yace kice kawai baza ki fada ba,amma mene a ciki, su Mama fa wayayyun iyayene, to nidai yau bazan iya ba dan Allah ka dinga salalawa honey cewar Gomnati, a zuciye Omar ya mike ya bar gidan gaba daya.

Iklas tace ka dawo ma ka samenii ,Iklas kanta ta tambaya a fili wai ni mene yake damuna haka ne?wai sai inji ina ta hankali kullum,yanzu jibi irin kunyar Dana nuna gaban Mama, lallai idan na haihu haka zan d
yi,ina share jaririn ina basarwa watarana na hanashi nono,yayi ta tsala ihu sai an hadani da Allah da Manzo.



AsmaBaffa

Tnx alot, love u all
ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

185-190



By
AsmaBaffa.





Omar tunda ya tafi cike da bacin Rai a zuciyarsa,haka ya koma gida yaji gidan ya masa fadi wayam ba masoyiya, nan ma yaji ba sauki bazai iya rayuwa haka ba,mikewa yayi ya fesa wanka 3qutr yasa da riga T-shirt masu matukar kyau sun dace da jikinsa,gashin nan sai kyalli yakeyi,Omar ba dai kyau ba ,karshe wajen kyau
Yau da kansa yayi driving shopping mall ya shiga duk abinda yasan Gomnati na so shi ya jidar mata ya siyo mata lafiyayyun gasassun kaji da ice cream ya wuce gidan.

Sallama dauke a bakinsa ya shiga palo,Ummi ya gani da su Suhaila,Mama na gefe tana waya da Baffa,da Ummi suka gaisa suna ta hira har Mama ta gama wayar,cinyar Mama ya kwanta sai shagwaba omar ke zuba mata kan ta barshi ya zauna gidan,amma Mama bata kulashi ba bare ta bashi amsa,

Ya rasa me ke masa dadi a duniya,daurewa yay ya cije tare da mikewa,nasu kajin da kayan ciye ciyen ya mika musu,ya kwashi na Iklas yayi dakin Ummi kai tsaye,Iklas na zaune tana bincike a wayarta ya shigo da Sallama yana ta wani cin magani,kamar zai maketa,daria ma ya bata
Kallonsa takeyi yayi kyau sosai,sannu da zuwa zumana,ko kulata baiyi ba yayi zamansa gefen bed din yana fushinsa,tana sani tace waya taba min kai ne my soul?a office ne? Harara ya dalla mata,
Allah huci zuciyarka Ogana idan ma wani ne ya bata ma,zaki sani ne indai nine zan rama,yanzu nan tun akan
Maganar room ce kake fushi haka?kayan ya tura mata ya mike ya koma wajen su Mama ko cikakken minti 5 baiyi ba ya dawo dakin Iklas a fusace cikin fushi yace ke dole fa ki zabi room guda naki na fada miki,
Kin San Halina a gaban Ummi ba ruwana zan iya hugging naki da wasu abubuwan gwara ki rufawa kanki asiri ki koma wani room din da zama,

Kallonsa Iklas takeyi da cikinta a gaba har ya gama fadansa,dariya tayi wacce ke kara mata kyau,sai kallonta Omar yakeyi da sha'awa komai na Iklas me kyau ne,baya gajiya da ita,tsayawa tayi da dariyar tace to kullum kullum da katon cikin ma baza ka bari a huta ba,ko tausayina baka ji zama da kyar tashi da dabara amma kai ba ruwanka,yanzu an dawo dani dan na huta jiba yadda kake min rigima,kayi hakuri na haihu nayi Arba'in,a fusace yace au harma arba'in Ashe kece mijin ma,to Honey zoka danneni ka kwata,

Murmushi yayi Iklas rigima kenan,zaki ga sanda zan danneki ne ai,dan kawai yanzu kinyi nauyi ne dole a biki sannu amma da sai kinyi bayani,nasan zaka iya ai oya zo muci abinci ka daina rigimar kai kasanni bazan bar mijina cikin Matsala ba dole akwai mafita ka daina bata bakinka,nayi yaji ma na nemoka baka zo biko ba bare yanzu da dole nima su Mama sukayi min,Ummi kakata ce ba wata kunyarta nakeji ba,

Sai yanzu ya dan samu nutsuwa da farin ciki,matsowa yayi tare da zama gabanta murmushi dauke a fuskarsa zama yayi sosai a gaban yana shafa ckinta,daga bisani ya jawo naman yana yankowa ya sa abakinsa sanna ya hade bakinta da nata yasa mata naman ta cinye tana kada kai uhmmmmm kaji dadin bala'i kuwa,
Haka ya dinga ciyar da ita har ta koshi,yau Omar a part dinsa ya kwana gidan Mama ba tare da kowa ya sani ba,Iklas kuwa tayi tunanin dama Omar dakinsa zai kwana,dan haka gaba daya tausayinsa takeji hade da wani sabon sonsa,da sassafe ta shirya kanta cikin doguwar rigar a tamfa,sama ya matse kasa ya bude sosai ya boye cikin ta,fitowa tayi sadaf sadaf zata shiga dakin Omar,suhaila ta gani da suleim zazu tafi schl,Anty ina kwana suka gasheta sukayi gaba da gudu,ita kuma ta fada room din Omar a kan bed ta hangoshi yana ta baccinsa cike da nutsuwa,komawa tayi ta sa key a kofar saboda tsaro.

Tana dawowa ta haura saman bed din tare da rungumeshi kam tana shakar kamshinsa tare da manna masa kiss a goshi,a hankali ya bude idonsa masu matukar kyau,ganin Gomnati a jikinsa ba karamin farin ciki yayi ba.

Ba tare da bata lokaci ba shima ya Kara manneta a kirjinsa wifey I miss u da kyar nayi bacci jiya,baki zo ba har jiranki nayi,miss u more honey nayi niyyar zuwa bacci ya sace ni,cikinta ya Shiga shafawa ya gudan jini na lafiya yake?haushi Iklas taji yace gudan jininsa wato ya kwace mata mijinta,
Shinema gudan jinin naka,ni wlh shi yasa banso haihuwar nan ba,yanzu sai ka dinga daukansa ni kana shareni,dariya Omar yayi me kishi da danta haka akeyin Maman babyn?ta tsani danta? Kece fa zuciyata gaba daya,cike da shagwaba tace to ai jini yafi zuciya muhimmanci shine zaka ce masa gudan jininka ni a bani zuciya,saboda ka samu da,fari tayi da ido Wanda ya susuta Omar lokaci guda tare da cewa dadin abin ai kafin ayi dan ni aka samu,kuma ai da nane.

Dariya Omar yayi kinsan me kike cewa kuwa wifey? Wannan shine ba kano ba birni,ba cinya ba kafar baya, shi yasa tunda ke danki ne kinga shi gudan jinina,ke kuma zuciyata kinga ai kun kwaceni du ke da baby,ni dai Allah ban yarda ba cewar Iklas ,ok to a bashi zuciyar ke gudan jini ko?kafada ta make abinda nafi so zuciyarka shine zaka ce a bashi ita,dariya Omar keyi yace to na bashi liver ta,da Sauri tace tab bai isa ba bazan yarda ba,Kasan kuwa muhimmancin liver da zakace a bashi ita yama fini kenan sosai fa ina laifin ka bashi yar madaciyar jikin hantar taka tunda shi yaro ne,ko ka bashi timbi ko hanji,

Fashewa da dariyar shiriritar Iklas yayi tare da kara kankameta sosai abin dariyar Gomnati da yawa yake, tafin hannunta ya mannawa kiss yana bin hannun da kiss ya gangaro wuyanta nan ya fara lasar wuyanta cike da salon kwarewa tattare da nutsuwa a hankali ya dinga sarrafata tunaninta ya gushe nan fa suka dinga baje harka,bayan sun nutsu wanka sukayi cike da nishadi,Omar na ta zuba mata albarka, Iklas dinsa dabance,tana shagwaba shi sai abinda yake so,gashi tana fahimtar matsalarsa ko bata so sai ta faranta masa,yanda yake bata wahala bata taba nuna gazawarta,
Burinta taga Omar kullum hankalinsa kwance,gaban kowa tana nuna rashin kunyarta dan ta faranta masa.

Har kaya ita ta sawa Omar tare da shiryashi suka fito fes fes dasu,Ummi bataga Iklas ba tunda taga haka to lallai Omar yana gidan,Iklas ta birge Ummi da take kula da mijinta,
Suna hirarsu kasa kasa murmushi dauke a fuskar Iklas suka shiga wajen Ummi suka gaisheta Ummi tana in kaga Zara kaga wata,suna ta murmushi suka je wajen Mama, tana ganinsu haka taji dadi a ranta amma sai ta tamke fuska ta fara yiwa Omar fada Dama nasan baka jin magana Babana saida ka kwana a gidan nan sabo da mun dauko matarka, ka kiyayeni fa,jikinta ya fada haba Mama nifa gwara ki hakura ki kyaleni dan Allah,Iklas ce tayi magana cike da marairaicewa Mama kiyi hakuri ki kyaleshi.ai na kyaleshi Iklas ya zanyi da shi

Please Login or Register in order to submit comment