Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maza,Amma wannan banzar ya Furta Yana nuna Matarsa yace ita Taki Sha.
Saiwar wata bishiya da yawa goje ya mikawa Halimatu yace gashi wannan kullum Zaki Sha na tsawon sati daya Amma kullum baza kiyi ko wacce Sallah ba har sati guda, wani garin magani ya bata yace wannan a cikin ruwa Zaki dinga zubawa kullum kina Sha har ya Kare Amma wannan zakiyi addiniki ba matsala, wani ganye ya Bata yace wannan jikawa zakiyi a kwano da ruwa ki barshi sai yayi sati Uku a jike sannan ki Sha Zaki ga yanda Zaki tsumu,wlh ko kidan tauri Kika ji a waya an kunna sai tsuminki ya tashi,duk wani karfe bazai ciki ba,Idan ma bakya son Wanda zai hanaki Sallah sai a canja Miki da wani.
Halima tace yawwa goje a bani Wanda zanyi Sallata ba matsala bana son barin Sallah akwai matsala.

Karba yayi ya canja Mata wani kalar yace wannan Zaki iya addininki lafiya Lau, Amma duk ranar da zaki fita daga gida ta baya baya Zaki fita,kina Fita ta gaba to wani tsumin zai karye,Halima tace an gama Goje na gode,nawa ne kudin? Goje yace ke mace ce na bar Miki kyauta,Godiya Halima tayi sannan ta koma gida ta fara gudanar da Shan maganinta, Bilkisu tace Anty Ke Ana neman maganin Boka ko Malam ke Kuma na Yan tauri kike karbowa? Anty Halima tana Shan maganinta tana cewa kyaleni Bilki shine maganin Rocket,Dan Allah Anty karki kashe Abbanmu cewar Rukayya Kanwar Bilki,Murmushi Halima tayi tace to ai dama ba kakeshi zanyi ba Amma zaici Ubansa da Mai da yaji,ke Anty Dan Allah ki Bari cewar Bilkisu,Kin Isa Aure Bilki ki Nemo miji kin fa dameni wlh bakya cas bare As.

Anna kuwa Bata sa an Zane Ilham ba Kamar inda tace,Bayan Kwana biyu ta Kira Ilham ta sanar Mata ta fasa kaita aiki gidan gonar taji Ilham ta iya Tausa da girki ga iya aikace aikacen gida,Ilham tafi kowa jin Haushi ta tsani Anna Bata son Zama kusa da ita sabo da muguntar Anna gwara a kaita gidan Gonar Amma tace ta fasa abin baiwa Ilham dadi, Yau Ilham makara tayi Bata Fita bangaren Anna da wuri ba,Anna tana jiranta har ta fusata,Ilham taci kwalliya cikin atamfarta yellow and black riga da skert ta kafe daurinta duk Hajiya Uwani ce ta dinka musu tare da koya musu kwalliya da dauri, ta fito kenan Daga part dinsu Headphone a kunnenta tana Jin kida tana rawa da kanta irin kida yayi mata Dadi tana tafiya a nutse,Gate taga an wangale motoci guda biyu rada rada Suka shigo gidan,Bayan Sunyi parking Dayar Mujaheed ne ya fito a motarsa,Dayar Kuma Taufeeq ne Driver ke tukashi Yana Baya ya kame,Sai da Driver ya fito ya bude Masa sannan ya fito, yau Friday yasha Wata shadda me tsadar gaske wata kala ita ba green ba ba Kuma light blue ba,hannun links cif cif yayi azabar kyau gashin nan yasha gyara,ga wani Half shoe Daya Sa na gagara,Mujaheed wani Yadi yasa me kyau Fari yayi kyau matuka,a Hankali Mujaheed yace yarinyar can Allah yayi Mata kyau,ban taba ganin wacce take da kyau Haka ba a kasar Nan, Taufeeq yace na santa na ganta ya Kai sau biyar,Bata Gari bace,garari kawai takeyi,Murmushi mujaheed yayi yace naga tana da karfi da kuzari da karfi gata da Alama zata Yi shishigi ko ita zaka aura kawai? Baki Taufeeq ya tabe yace Bata da kunya Ni Bata Yi min ba bana sonta,au dama wacce kake so kake nema? Nayi tunanin kawai a biyata kudi tayi maka aiki shike Nan a sallameta,Taufeeq yace haka ne Amma wannan baza tayiwa Ummi ba,Mujaheed yace Ni Kuma wlh naga kamar Ummi zata so ta,Taufeeq Yana wani tabe Baki yace to ku gwada ku gani Ni Dan kallo ne,Kuma ya za ayi da Anna? Zamu san abin Yi cewar Mujaheed.

Ilham tazo gaf dasu Bata San me suke cewa ba ta cire Headphone dinta ta duka har kasa tace Ina yini? Mujaheed ne kadai ya amsa ta wuce wajen Anna abinta.
Tana shiga Anna ta daga Mata tsawa jeki waje ki kalli Rana yau Zaki ji a jikinki, Ilham tace to Kanwar Firauna, tayi waje Anna tace Ni Kika zaga Dan Uwarki,Ilham ta juyo tare da lekowa ta kalli Anna ta bugi cinya tace ah..ah..ah sumbuka, kwafa Anna taje tace zanyi maganinki yau.
Wani katon Gardi marar Imani Anna tasa Ya samu Ilham a waje tana zaune a Inuwa abinta tana Jin kida,kawai sai Ruwan Bulalai taji ta ko Ina suna sauka a jikinta,Mikewa tayi zumbur da ihu Amma gardin nan ya rike Ilham Kam ya Zane tas sai da ya farfasa Mata jiki sannan yayi tafiyarsa ya barta Nan tana cin Uban kukanta.

Su Taufeeq ne Suka fito zasu tafi,Mujaheed yace lafiya ke Kuma fa? An..Anna..ce tasa aka zaneni...bayana ya fa..fa..fashe cewar Ilham tana Sheshekar kuka,Rigarta ta dage ta baya tace kalla kalla,abinka da farar fata sai ko wurin yayi jajir fatarta me kyau,Taufeeq Wai shi Utaz harda rufe Ido yaki kalla sai ma mota ya shige abinsa, Driver yaja mota dai dai saitin Ilham Taufeeq ya sauke Glass kadan ya jefo Mata Handkerchief fari tas me kamshi kudi ta gani yan dubu dubu har guda goma ya jefo Mata again tare da dage glass din motarsa sama.
Cik ta daina kukan ta dauki handkerchief din ta shinshina kamshinsa tare da kwashe kudin ta boye sai taji wani sanyi da kwarin gwiwa,ta mike tsaye tace Anna...Anna...wlh sai na Rama duka na a yau ba sai gobe ba,ai ke ba Kanwar uwata bace, Garden ta shiga ta samo wata danyar Yar Bulala me kauri a jikin bishiya ta boye a dakinta.

Sai da ta Bari cikin tsakiyar dare kowa ya kwanta Yana bacci ta fito tare da lallabawa tana sanda har zuwa dakin Anna, Dakin Duhu sosai Tana saman lafiyayyen gadonta tana kwasar bacci sai Munshari takeyi, Ilham ta tsaya a Kan Anna tare da daga Sandar iya karfinta ta saita kirjin Anna ta kwada Mata sandar,Wani zullo da tsalle Anna tayi, ta Gama firgicewa sai Ihu ta saki ga duhu Bata ganin komai,Kafin ta mike Ilham ta sake dagewa iya karfinta ta bugawa Anna a gadon Baya sai da fatar wajen ta daye,Anna lalube ta Fara a duhu tana Neman agaji da Ihu tana a taimakeni ihuuuuu jama'a, ta Uku Ilham ta dage tare da sake Zabga mata a Dan shamulallen duwawun tsohuwa Anna, zafi ya Gama ruda Anna saman Bed ta fada tare da kifa cikinta a Kai tana birgima da Nishi,Sandar Ilham ta jefar tayi waje a hankali ta lallaba ta koma dakinta tare da kwanciya tana cewa ai wlh dama nace sai na Rama kadan Kika gani,kwanciya Tayi abinta bacci ya kwashe ta.

Washe Gari da rarrafe Anna ta Fito tana ihu tana cewa barayi ne Suka shigo Yan fashi ne,Waya ta dauka ta Kira Danta Baffan Taufeeq Yana dagawa ko gaisawa basuyi ba tace Alo Alo ka turo min Yan Sanda jiya Yan fashi ne Suka zo,Subhanallah ya furta yace Amma dai Basu taba min lafiyarki ba ? Hmm Kai dai Bari ai yaga yaga Suka Yi min saura kadan su karairayani, Subhannallah Bari na turo Taufeeq sannu Annata Allah ya kiyaye gaba Bari ga Taufeeq Nan.
Dukkan ma'aikata yan gidan sunji dukan da Anna Tasha sai Murna sukeyi suna cewa wannan barayi Allah yayi musu albarka, Haka tasa wata dattijuwa me Mata Shara da Mopping ta gasa Mata jikinta,Amma tace ke baki iya gashi ba ku kira min Ilham tazo ta gasa Ni.

Ilham tana zuwa ta ebo ruwa me zafin masifa tasa towel,Anna ta gyarawa kwanciya a saman Kujera tare dasa kafa ta danne saman Wuyan Anna yanda baza ta iya dagowa ba,sai ta jiko towel din da ruwa me uban zafi sai ta samu ta dodanawa Anna a Kan rauninta, Nan take Anna ta saki Ihu dai dai lokacin Taufeeq yayi Sallama tare da shigowa Palon ya Iske Anna daga ita sai skert na ciki a tube,Nonon Nan yayi yaushi Kamar slifas,Nono yayi sujjada sharab,Ilham ko a jikinta tasa kida da Headphone a kunnenta Bata ma Jin kukan Anna kawai Wuta take manna Mata ta ko ina.
Anna ta hada uban Zufa tana ya Isa haka Amma Ilham ko ji Bata Yi kawai Yi takeyi,Taufeeq Yana zaune ya harde kafa yana latsa katuwar wayarsa,a sace Ilham take kallonsa Shigarsa ta yau ce Take birgeta,kana Nan kayan sun masa azabar kyau gasu color me kyau kamar wani Bature.







AsmaBaffa
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰






NA KUDI NE








26-30







'YAR KWANGILA IS DEDICATED TO MAI DARAJA
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.







Official







By
AsmaBaffa






RASHIN SA'A COMPLT AND
TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku ne ko wanne.

'YAR KWANGILA
Naira dari biyu ne 200 ga me so a sata a group.

Zaku Isa siya ta wannan Hanyoyi Kamar Haka

Accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, Zenith Bank.

Transfer Kati ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Masu biya ta hanyar tura katin MTN ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'yan Niger masu bukata ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.






Page naku ne
Wacy
Meenal
Hadiza Mukhtar







Tun Taufeeq Bai kallon Su Anna har Karar Anna ta ja hankalinsa ya kallesu yanda Ilham take Mata mugunta tsantsa shi ya bashi dariya,Dan Wlh ta birge shi tayi maganin muguntar Anna, Taufeeq ne ya gaji da ihun Anna yace pls take it Easy, Ilham tayi Murmushi tace she is not carry On the Back Wai nufin Ilham itama turanci yayi Wai Dan Kar Anna ta Gane tace Anna ba Yar goyo bace da turanci.
Taufeeq Baki ya tabe Bai gane Turancin Ilham ba, Anna ganin Ilham da Taufeeq Sunyi magana ranta ya baci tace ke an Gama gashin tafi dakinki,Wai dan Kar Ilham ta Saba da Taufeeq jikan Anna.

Ilham wata katuwar paper ta dauka a dakinta bayan ta koma,Rubutu tayi Kato a jiki Dan kadan ta tsaya a jikin Window tana jira Taufeeq ya fito tunda Dole sai ya wuce ta kusa da Window dinta,Bata Dade ba ya fito zai tafi gida wajen motarsa da yayi parking dai dai zai shiga Motar Ilham ta kira shi da Dan karbi jikan Anna? Waigowa yayi tare da kallon Inda yaji Muryar Ilham,Takardar ta bude ta window dinta tare da dago Masa sama yanda zai iya karantawa, takardar ya kurawa Ido yaga ta rubuta
mun gode da
Taimako.
Yana Gama karantawa ta dakko wata ta bude tare da Dago Masa sama again itama ya karanta
Kudin da ka bani
Rannan da shi nake
Cin Abinda nake so
Ina godiya.
Yana karantawa tace Dan tsaya Dan Allah karka gaji ta sake Bude Masa wata takardar
Ka taimaki Marainiya
Na gode Allah ya biya
Maka bukatunka.
Yana Gama karantawa a boye yace ameen a fili kuwa ko kula Ilham baiyi ba ya shige motarsa Suka bar gida.

Hajiya Uwani Tana asibiti Nan take ta shiga nazari ta gano su Ilham ne Suka hada Mata wannan shocking din sabo da Ilham ce kadai ta shiga room dinta da dare domin gyara Mata Bed,a Fili Hajiya Uwani tace Allah ya hadani daku Nan gaba Yan Iskan Yara Wanda Basu San mutunci ba,na kashe dukiyata a kanku ban amfana daku komai ba Kun gudu,Kun cinye min kaji Kun arce Allah ya hadani daku, dai dai lokacin da Hajiya Uwani ke sambatu lokacin Likita yazo tare da sallamarsu suka tafi gida.

Bayan sati Uku Anty Halima ta Gama tsuminta na maganin Yan Tauri,Zubairu Bai san Tasha ba,Shigowa yayi gida da masara kwano Daya Yace gashi a Sarrafata ko dambum masara ayi mana mu kwashi Dadi,Anty cike da harara ta Fara yayyafa Masa masifa ka kawo kudin Zogale dasu gyada ne a'a ko Garin masarar kawai zamu turara mu ci, ba kudin sabulu,ba Omo,bare sutura ba uwar da kake tsinana mana,wlh baka da amfani a rayuwar mu,da kai da babu duk Daya,Mene amfaninka? Zubairu takaici ya lullube shi yace Amma ban taba sanin ke ba matar rufin Asiri bace sai yau,butulu,duk da Haka da kuke rainani ni katanga ce a gare ku wlh da Zan mutu sai kunyi kuka da idonku, Heeeeee Anty tayi shewa tare da Furta Ayyiriri Nanaye mu ai ko ka mutu bamu da haushi dama ni nake ciyar da gidan idan ka Wulla lahira yo sai me Allah na tuba, Kwafa Zubairu yayi,Anty tace in ban tauna Reza da Hakorana ba kace shegiya nake,In dauki wuka in keta jikina ba komai bane a wajena Zubairu..Zubairu...Zubairu sau uku kaji na Kira sunanka ko? To ka kiyayeni ni yanzu ba haliman da bace,Mari Zubairu ya zubawa Anty Nan take ta Fadi kasa a sume,Ko kulata baiyi ba yayi waje abinsa,Bilkisu tana kuka ta kwarawa Anty ruwa tabi Bayan Zubairu tana Abba Dan Allah kazo Kar Anty ta mutu, idan ta mutu akai gawa ...idan ta mutu akai gawa ba abinda ya dameni, Muryar Anty suka ji tana idan ka Isa Dan uwarka,idan Kai Dan Sunna ne ka dawo gidan tana magana Hannunta rike da wata katuwar wukar yankan rago,bacin Rai yasa Tsumin Anty ya motsa jikinta ya Fara tsuma Kar...Kar....Ihu ta kwala ta Fara kirari
Sai Ni Halimatu Sa'adiyya me suna biyu
Babar Bilkisu Kanwar Hafsatu Ehoo ...wuya a gidan Zubairu Rocket,Wuya a kauyen Arma, Wuya...wuya...Karo Dani ba Dadi ,wuyaaaaa a gidan Nan, matsa Bilki ba dake nake ba,Nice Halima naci dubu sai ceto,Wuya a dambum Masara,ji kake wani Hayya Hayya...to Halima ce ta karaso...

Yaran Halima su Bilki Suka fashe da kuka sunga uwarsu Kamar ta haukace,ta rasa maganin da zata Sha sai na Yan tauri maza,Duk Abinda akeyi Zubairu Bai sani ba,Bai ma San Tasha wani maganin tauri ba,Tunda ya fita bai tsaya ko Ina ba sai gidansu acan ya cika tumbinsa sannan yasa aka aika Masa da wani gida sabo da Yara.

Zaune Ummi Take saman bed dinta dake bedroom,Hawaye take zubarwa ita kadai,Bata San ma tana kukan ba har Taufeeq ya dawo daga Office yazo zai ce Mata ya dawo ya Iske Umminsa tana kuka Wiwi,kuka me ban tausayi, ledar take away dake Hannunsa ya saki ta Fadi kasa,Da sauri ya Karasa wajen Umminsa tare da daukan littafi Yana tambayarta
Lafiya Ummina?
Ko Yan aiki ne?
Baffa yazo ne
Meke Faruwa Ummi pls
Karanta tabayoyinsa ta Gama kawai ta girgiza Masa Kai alamar ba komai,Rubuta Masa tayi
Kayi Aure kawai,
Shi Taufeeq ya Rasa me wannan aure zaiyi Wa Ummi data damu kanta,Amma tabbas yasan ba Wai Dan yayi aure take kuka ba akwai dalilinta, Hannayensa yasa a hankali ya shiga goge Mata Hawayenta yayinda Idonsa yayi jajir sabo da tsananin bacin ran da yake ciki,A nutse ya rubuta Mata
Ummi indai akan Aure
Ne wlh zanyi very soon
Ki daina damuwa,me
Auren nawa zaiyi Miki Wai Ummi?
Aure Rahma ne Taufeeq Yana Kore matsaloli da dama,ka cika min Burina tun Ina
Raye Dan Allah.
Zanyi..zanyi..Ummi ya Bata amsa kamar shima zaiyi kukan.

Bayan kwana Biyu Anna ta warke daga dukan da ta Sha ba tare da Taufeeq ya Kira police ba,ba Kuma asan waye ya aikata hakan ba, Yau Anna ta Kira Uba Babban Ma'aikaci a gidan gonarta,Uba Yana durkushe a gabanta Ilham Kuma tana gefe tana Sauraron Anna itama domin kiranta Anna tayi, cike da gadara Anna tace Uba dauki Ilham kuje ta duba min dababbobina ance Basu da lafiya cuta sukeyi duk sun rame ga yawan mutuwa da sukeyi,Uba yace wlh an Rasa matsalarsu har malamin dabbobi Muka Nemo yace zasu warware Amma Shuru, kaji ne kadai suke da cikakkiyar lafiya, Ilham bishi kuje ki duba su tunda kince kin Iya kula da Dabbobi,Ilham tace Dole fa sai anyi musu Allurai wlh tunda kunce ramewa sukeyi da kumfa a bakinsu zai wahala ba ciwon Hanta bane ya kamasu,Anna kudi ta kawo zasu Kai dubu goma ta mikawa Uba tace ungo Idan ta kama za ayi musu Allura ka siyi komai da kanka karka ba wa wannan ban sani ba ko kudi take so,Ilham a ranta tace Jikanki dubu goma ya bani kyauta da su nake cin abinda naga dama.
A Fili Ilham Bata ce komai ba Sanye take cikin Hijab Amma a ciki kana Nan kayane a jikinta,Uba ne ya kalleta Yana Murmushi yace tashi mu tafi Kanwata,Ilham ma murmushin ta sakar wa Uba Wanda yake mata Masifar kyau Dimple dinta ya loba,Galala Uba ya saki Baki Yana kallonta,Sai da tace muje sannan a firgice Hankalinsa ya dawo jikinsa,Uba Dattijon matashi ne gashi ba kazami ba tas dashi kullum,Fitowa Sukayi Ilham ta Hango Taufeeq da Mujaheed Sunyi parking Mujaheed Ke Driving.

Taufeeq ne ya fara fitowa cikin shiga ta Alfarma wani Yard ne a jikinsa Sea blue ba karamin kyau yayi ba,yau harda wata sa hula a kansa cif ya Dan Murzata a gaban goshi yanda matasan zamani ke sawa baya Kuma ga gashinsa nan me dan yawa lub lub baki wuluk, Sajensa da Dan gemunsa das das Yana sheki,Mujaheed kuwa Kananan kaya yasa shima ya Gama hadewa Mujaheed Yana da haske Amma ba can ba,matashi Dan gayu Gashi Kyakyawa ne shima irin Sadeeq shi Kuma Fari ne Amma siriri ne shi,dukkan abokan Taufeeq Babu baya a haduwa da Kudi masu kudi ne gaba Daya,suna kaunar juna gaba dayansu suna zaune lafiya Babu bakin ciki.
Mujaheed Yana ganin Ilham a hankali Ya cewa Taufeeq gafa Amaryar Nan,In ka auri wannan ka Dace wallahi ba karamar Hadaddaiya ce ba,Tsaki Taufeeq yaja Yana Hararar Mujaheed,Ilham Bata San me suke cewa ba Amma tabbas taji tsakin Taufeeq, Uba da sauri yaje Suka gaisa dasu Taufeeq.

Headphone ne a kunnen Ilham Bata sani ba Ashe Da karfi tayi magana tace Uba Muje mana,Kai Amma machine dinka zaiyi Dadi Wlh Uba, Wai Kai da ake ce maka Uba to Uban su waye? Uba Yana washe Baki yace Uban yarana su Walida, Kai Ilham ta jinjina tana kyalkyala dariya tace Machine din Nan naka sabo dashi Dan Allah idan mun hau Titi kayi arubta Dani ka dinga kwanto kana ratsa manyan motoci mu wuce Yuuuut Yuuuut Kamar walkiya,Uba Yana dariya dari yace Aiko na kware Wajen Nan,su Taufeeq suna kallonsu Kuma suna jin Hirarsu,sabo da Ilham Da Karfi take magana,Uba ya gyara machine dinsa yace Hau mu tafi Golden Girl,Ilham ta Dan daga Hijab dinta Taufeeq ne kadai ya hango kana Nan kayan dake jikinta suna da kyau Sunyi Mata kyau harda Yin Wani Ass down ita Yar gayu,Baki Taufeeq ya tabe Yana latsa wayarsa ko wajen Anna Basu shiga wasu kujeru dake Compound ga Flowers da wata Yar rumfa me kyau a Nan Suka zauna me aiki ta kawo musu lemo suna Sha suna Hira.

A idonsu Uba ya fisgi Ilham tayi gaba kadan,ya Kara fisga tayi gaba ta matso baya,ya bawa machine din Wuta Yana fisga Raranran...ya fincika Ilham sai dariya takeyi Tace yawwa Uban su Walidede gate aka Bude musu kadan Suka fice,Mujaheed ya kwashe da dariya Yana kallon Taufeeq yace kana kallon za a hallaka maka Amarya Amma ka barsu,Tsaki Taufeeq yaja yace wlh zamuyi fada da Kai Mujaheed Ina ruwana da ita Ni.

A titi Uba ya Ware machine ya dinga kwanto Yana keta motoci yanda Ilham tace duk inda Suka Ratsa sai an kallesu Ana cewa Allah ya tsare ga wasu can Wanda basa son Ransu, A haka Suka Isa gidan gonar, Ilham Tasha kallon Gidan gonar da Bata taba gani ba,Babu abinda Babu a ciki,Har manja ake sarrafawa a ciki,Bangaren Tinkiyoyi da raguna Uba ya Kai Ilham,Ilham tana ganinsu da uban yawa Amma wasu daga ciki sun rame basa iya cin Abinci sai kumfa da bakinsu yakeyi, Nan take Ilham dama ta san irin wannan Ciwon na dabbobi tace Kaini shagon da ake siyar da abubuwan kiwon dabbobi a can za a samo Alluran da za ayi musu,Uba yace nasan wani waje muje,Nan fa Suka Kara Hawa Machine Suka je shagon,Ilham ce ta lissafa Alluran da take so aka samu kuwa da wani maganin kwaya manya,Uba Yana jira yaji tace a Nemo Likitan dabbobi yayi musu Alluran sai yaga suna komawa gonar Kawai da kanta a katon sirinji irin na dabbobi take zuke ruwan tana ta kunna musu Allurai,Uba yace ya akayi Kika iya? Karambani ta bashi amsa,Kaima Zo na koya maka.

Uba ya Karasa kusa da ita Yana kallo tana ta koya masa yanda ake musu Allurai sai da ya gane Sannan ta bashi ya gwada da kansa,Tare da Uba Suka Gama Yi musu Allurai har suka Gama,sannan magungunar kwaya ta dakasu a saman Wata Leda da dutse ya koma Gari ta zuba musu a cikin Abinci, Uba ta mikawa sauran maganin tace kullum wannan maganin zaka dinga dakawa kana zuba musu a abinci har sati guda zasu warke Inshaallah.
Uba Yana dariya yace to ki karanci bangaren dabbobi Mana kawai? Ilham tace karatu a kasar Nan ai sai Mai gata,bani da me tsaya min na cire karatu a Raina,Uba yace Kinga Kuma da Zaki fadawa Taufeeq wlh zai iya saki Yana da kirki ba irin Yan uwan Babansa ba,Ni ban San wannan Yan uwan Babansa ba cewar Ilham,Zaki sansu watarana Ana nan zasu Zo gaba Daya yaran da iyayensu a Abuja suke Basu da mutunci ko kadan,Kinga duk abinda Anna takeyi? To Bata Kama kafarsu ba Musamman wata tana Nan Kanwar Baffan Taufeeq Hajiya Asma'u Bata da mutunci ko na digo,Baki Ilham ta tabe tace Allah ya shirya.
Sun Dade suna Hira da Uba sannan Ilham tace Uba Dan bani katuwar paper da Biro Zan rubutawa Taufeeq gaisuwa tunda Anna Bata so kowa ya kalli jikanta bare magana ta hada su,Uba ya Bata Takarda tayi rubutu Manya manya yanda ko a nesa ka hango zaka iya karantawa,Muje gida Allah yasa Bai tafi gida ba na nuna Masa ya karanta gaisuwa ta.
Machine Uba ya gyara Suka Ware wuta suna fyalla uban gudu Kamar zasu tashi sama,Gaf da zasu shiga Layin gidan Anna Suka ga Motar su Taufeeq ta fito sun hau babban titi, Uba yace gasu can sun Fita zasu tafi,Da sauri Ilham tace maza Uba bisu ka Sha gaban motar nan tasu yau Inshaallah sai ya karanta gaisuwata, Uba ya sake kurewa machine wuta Dake su Mujaheed a hankali suke tafiya sai ga Uba har ya wucesu yasha gabansu suna tafiya a gefe.

Ilham Kamar wata Yar Siyasa,Mujaheed yace kaga Amaryarka wlh tana Dago Hannu maybe Kai takewa magana,Da sauri Taufeeq ya kalli gabansa ya daina latsa wayarsa,Ilham Hijab Yana Fil fil, Takardarta ta bude tare da dagota sama yanda Taufeeq zasu iya karantawa,Kamar ta daga Banner ta poster Yan Siyasa, Taufeeq ya sake Bude Idonsa Yana kokarin karantawa rubutun kamar Zane haka tayishi da Babban Baki, mujaheed ma kokarin karantawa yakeyi suka ga an rubuta
Ina Yinka Taufeeq
Gaisuwar Dazu ce
Dama na manta Ban
Gaishe ku ba
Ina Kwana?
Ku gaida gida,ka
Gaishe min Da
Mamanka,ance
Balarabiya ce ko?
To ka

Please Login or Register in order to submit comment