Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rike Mara tana ta murkususu da juyi Bayan ta bude kofar,Da gudu Yan aiki suka Kira Anna,Anna ta Fito da gudu tana Kai Kar a Bari ta mace min a gida na shiga uku,dakin Ilham Anna ta Fado,ita kuwa Ilham ta sake sankamewa,Anna ta rude karfa ya ta mace min a gida ku dakko min waya na Kira Taufeeq yazo ya dubata.
Cikin Yan aikin Hannatu ta tafi da gudu ta dakkowa Anna waya ta Mika Mata,Kamo min Number Taufeeq Zaki ga alamar kan zakara a jikin lambar,Hannatu ta Riga tasan Anna duk numbobinta dake waya Babu suna Alama aka sa kawai,wani lemo,wani mota,wani jirgi, Taufeeq Kuma Kan zakara aka sa Masa,Hannatu ta kamo tare da Danna Kiran Taufeeq sannan ta bawa Anna wayar,Bugu Daya Taufeeq ya daga,Alo Kai kazo yanzu na shiga uku yarinya zata mace min a gida,cikin talakawan gidana gata a sankame, Anna yanzu fa na Tashi daga bacci ko wanka banyi ba, yau Lahadi Babu Office malam kazo na fada maka tana fadar Haka ta kashe wayarta.

Ilham tana ta faman murkususun karya Anna tace Yar iskar yarinya jarababbiya kin dame mu mayya yanzu za a Zo a duba ki,karki sake ki mace min a gida,Yan aiki tuni sun koma bakin aikinsu,Anna ce kadai tana jiran Taufeeq, A gurguje Taufeeq yayi Wanka da Brush,Jallabiyya kawai ya saka ya leka wajen Ummi yaga baccinta takeyi ma,Bai tashe ta ba kawai ya wuce ya Shiga Mota da kansa yayi Driving zuwa gidan Anna.
Taufeeq Yana zuwa yaga Hannatu ta nuna Masa dakin Ilham tace Anna tana ciki wajenta.

A nutse ya Isa kofar Room din sannan ya kwankwansa tare da cewa Anna gani nazo,Shigo Mana kaga wannan Jarabar yarinya,tunda tazo gidan Nan take sa min Ciwon Kai,Taufeeq Yana shiga ya Iske Ilham ce take ta kukan karya tana murkususu tana wayyo marata,Taufeeq har ga Allah yayi zaton period takeyi,Amma Mamakinsa da safe kwalliya a Fuskarta ba alamar cuta na damunta,Skert din atamfa ne a jikinta tare da wata Yar Guntuwar vest fara tayi kyau matuka, kanta ba dankwali gashin nan gashi Nan yalala.
Tana Jin Taufeeq ta Kara kyararrabewa tana kuka sosai Kamar gaske,Anna tace Wai ke wacce irin Yar iska ce ne? Ga Likita yazo Amma kin cika Mana kunne bazan iya Jin wannan kukan naki ba shegiyar murya Kamar an kunna Generator, Anna ta fice tana cewa kana Gama dubata ka Fito Ina jiranka a Palo na,Kuma kayi sauri ban son wannan mayun kauyen su saka a gaba,Fuuu Anna tayi part dinta.

Taufeeq dai tsayawa yayi kikam Dan Bai San me zaiyi Mata ba idan ba Allura ba,Ilham tana tabbatarwa Anna ta tafi ta kyalkyale da dariya,Tana magana kayi hakuri wlh jiya kasan na Dade a gidanku cewa tayi sai Gardi ya zaneni shi yasa nayi cutar karya,lafiya nake fa,Dan Zauna anjima kadan sai ka fita kace na samu bacci,Harara Ya ballawa Ilham Yana bin dakin nata da kallo fes dashi komai a shirye, Gefen katifar Tata ya zauna Ba tare da ya kula Ilham ba, Chocolate ta dubo cikin wani Dan karamin kwali ta Mika masa guda Daya gashi kasha bani da abin bawa Babban bako, Karba yayi yasa a aljihu, Ilham tace Ina Umminka ya jikin nata? Lfy take ya furta fuskar nan a turbune, Kai kuwa ka dinga fara'a Mana kafi kyau,Sai kizo ki matsa Fuskata Dole nayi fara'a cewar Taufeeq,Ilham tace Allah da gaske kakeyi na matsa sai kayi fara'ar? Kallonta yayi yace Bari naga hankalinta a fili yace ae matsa.
Gabansa ta matso da sauri ta Sa Hannayenta ba zato ta tallafi fuskarsa ta matse da karfi tana cewa to Yi dariyar inye..Inye..yaron Ummi,dariya ta kusa kwace Masa a ransa yace Lallai yarinyar nan Bata da kunya.
Muryar Anna Suka ji ta saki Salati.

Fuska ya Bata sosai Ba shiri ta janye Hannayenta ta matsa gefe, Mikewa yayi ya fice a fusace Wai shi a Dole Yana jan Girmansa,Anna tace Allah ya kamaki Yar Iska au jikan nawa kike shafawa saje Hannu duk kaushin Talauci, Ilham tace Baki gani dai dai ba,Taufeeq yace Anna idonki ya lalace gaskiya asibiti Zan kaiki yarinya Ina Mata Allura kice tana taba min gemu,nayi kalar da Irin wannan zata tabawa jiki? Kuma na kyaleta Bata Sha maruka ba, Anna tace yanzu dama ba Fuska naga tana shafa maka ba? Taufeeq yace ba gaskiya idonki ya nuna Miki ba,Idonki ya tsufa baya gani dai dai, Anna tace inko Haka ne Lallai sai an yanka min Glass a asibiti,Taufeeq Kiri Kiri ya rainawa Anna hankali yace idonta gizo yayi Mata,Dole ta yarda,tuni Ilham ruwa ta Sha an fasa zaneta sabo da Taufeeq Yana zuwa Wajen Anna tace meke damunta?

Taufeeq ya kalli Anna yace jinin Haila ta Fara,zazzabi da Kuma jininta ya nuna Bata samun Hutu,sannan Ana yawan dukanta Idan akaci gaba da dukanta Zuciyarta zata iya bugawa ta mace miki a gida, Anna ta dafe kirji tare da cewa na shige su dama da ganin yarinyar Nan kayan aras ce,baza tayi karko ba,kalar cuta ce kawai,Haka Taufeeq ya tsara Anna yayi tafiyarsa.
Tun daga wannan Rana Anna ta rage sawa a doki Ilham.

Bayan sati biyu Ilham da mujaheed sun Gama tsara yanda za ayi bikin Ilham da Taufeeq ba tare da an samu matsala ba, Su Taufeeq sunji tsarin Suma yayi musu,haka ya bawa Umminsa labarin yanda za ayi ya auri Ilham,Ummi tace Amma duk Ranar da Anna ko Baffa Suka gano gaskiya ko Yan Uwan Baffa wlh Akwai matsala Babba, sannan zasu ce sai ka saketa Ni Kuma bana fata kayi aure ka saki matarka har abada.
Inshaallah ba abinda zai faru cewar Taufeeq.

Bayan Sati Daya Taufeeq ya Kira Baffansa yace Baffa na samu matar Dana ke so zan aura,Baffah yace Kai Alhmdllh naji Dadi Yar wacece a kasar Nan? Taufeeq takaicin rashin wadatar zucin Baffansa ta kamashi Amma ya danne yace Yar gidan Gomnan Jigawa ce,Abinda yasa yace Jigawa yasan Baffansa bashi da kowa a Jigawa,baya zuwa ko Business Bai San kowa a can ba,Kai Kai masha'allahu yanzu kayi babban zabe,gashi ma ban San waye Gomnan jigawan ba,Taufeeq yace ae ai yanzu ma Yana kasar Germany yace Idan za a tura manya akwai Yayansa da Kaninsa wajensu za a je Neman aure.
Baffa anji me kudi Gomna guda ai ba wani bincike yace zan sanarwa Su Kawu sai su Shirya ka Basu Address suje ayi tambaya asa Rana,Taufeeq yace sai na kaisu da kaina ma, ok Allah ya kaimu Sunday sai ku tafi kawai,Ni bazan shigo Nigeria yanzu ba, sai Idan bikin yazo,Allah ya kaimu.

Taufeeq yana gamawa da Baffansa yaje har gida lokacin Ilham tana mopping a dakin Anna Taufeeq yace Anna Nafa samu matar aure,Nan take Anna tace saurara min Malam Azeema ko Mujaheeda Yan uwanka a cikinsu zaka zabi Mata,Taufeeq yace Haba Anna wacce fa nake so ba wajen Wasa bane Anna Gidan Gomna wa zai je gidan Gomna da wasa,? Kai Dan nan yanzu yar gidan Gomna guda ka samo? Cab Ashe za a Sha bidiri birede kyale su Azeema Allah ya Basu nasu Mai kaunarsu,Yar Gomna ba Wasa ba mulki kadai Alfarma ne,Haka nake so ace jikana ya samo Yar asali Yar manya,yanzu yaushe za a kawo Mana ita mu ganta,Taufeeq yace yanzu Tana Uk sai Next wk Inshaallah zata shigo Zan kawota ta kawo gaisuwa,Shewa da guda Anna ta saki, tace ranar wannan biki sai nayi rawar da ban taba Yi ba,Allah maka Albarka,Ilham mamaki ya cikata yanda Anna ta haukace akan Yar Gomna,duk kudinsu Wanda sunfi wasu Gomnonin kudi ma.
Ilham tace wow Allah ya Sanya Alkhairi Jikan Anna zaiyi aure Allah ya kawo namu muma
Ilham ta furta tare da kallon Taufeeq a sace ya daga Mata gira Daya,ita Kuma ta kanne Masa Ido daya, Anna ce ta dakawa Ilham tsawa je ki kawowa jikana fura me sanyi a cikin fridge wa zai soki a Haka ballagaza ai ke me aurenki sai irin masu gadi ko malamin makarantar Islamiyya.







AsmaBaffa
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰





NA KUDI NE






36-40








'YAR KWANGILA IS
DEDICATED TO
MAI DARAJA
🚨RABIU MUSA KWANKWASO.







Official







By
AsmaBaffa





RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku ne 300.

TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

YAR KWANGILA ga me so a sata a group Naira dari Biyu ne 200.

Zaku iya siye ta wannan Hanyoyi

Accnt number
2177560408, Yahaya Garba Muhammad, Zenith Bank.

Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Tura katin waya Mtn ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.





Page naki ne
Mrs Chief.






Fura Ilham ta dakko a nutse ta kawo gaban Taufeeq ta durkusa har kasa ta ajiye, jikin bowl din ya taba yace ya naji ba sanyi sosai? A Ina Kika dauko wannan Furar? Ilham kanta ta Sosa sannan tace a Rumbum Dadi na dakko, Mene kuma Rumbun Dadi? Taufeeq ya tambaya, Caraf Anna ta karbe zancen tace Yar kauye Wai Fridge ne Rumbum Dadi kullum Haka take cewa har dukanta nayi a Haka Amma Taki gyara halinta baza tace fridge ba sai Rumbum Dadi.
Dariya tazowa Taufeeq wuyansa Wai Fridge ne Rumbun Dadi,sai da ya duba Maganar Kuma yaga Fridge ya Dace da Sunan tunda kayan Dadi ake zubawa a ciki,Ilham zare jikinta tayi ta tafi Kar Annan ta mare ta tasan halinta.

A ranar Anna ta Kira su Hajiya Maryam yaranta ta sanar musu Taufeeq zaiyi aure,suna ji ance Yar Gomna sai farin ciki tuni sun manta da yaransu su Azeema da suke so Taufeeq ya aura, kawai mulki da kudi suke hangowa, ai muma wani satin zamu Zo gaba dayanmu idan munzo sai a kawota Muna Nan mu ganta,Anna tace Haka za ayi kawai.
Duk Abinda ake ciki Ramcy tasan me ake ciki Ilham tana Bata labarin komai, Ramcy ma da Rabiu manager suna cikin mission na gaba idan biki ya matso.

Saura Kwana Biyar a kawo matar da Taufeeq zai Aura Yar Gomna Ilham ta Samu Anna tace zata je ganin gida,Anna Baki ta tabe tace a dawo lafiya ko na daureki ke da kafafunki, haka Ilham ta hada kayanta tayi Mata sallama Amma Dubu uku kacal Anna ta bawa Ilham bayan taga yanda Ilham ke Mata aiki dabbobinta sun samu lafiya sunyi bulbul sanadin Ilham Amma Bata gani.
Ilham tana Fitowa gate ta mike Titi sai da tayi nesa da Gidan Saddeeq yazo ya dauke ta a mota,gidan Kanwar Babarsa ya Kai Ilham zata zauna a can kafin lokaci yayi.

Saura Kwana biyu a kawo Yar Gomna su Haj Asmau,Haj Zeenatu da Haj Maryam suka dira a Rivers State su da yaransu kaf maza da Mata Bataliya guda,a gidan Anna Suka sauka Mahaifiyarsu,Baffa ne kadai babu a cikinsu,Taufeeq ma kullum sai sun kirashi yazo anyi hira anci Abinci tare,baya sonsu sabo da yasan basa kaunar Umminsa,tunda Suka Zo Kuma Babu wacce tace bari taje ta duba Umminsa ko yaransu sun hanasu zuwa.
Azeema tunda taga Taufeeq sonsa ya dawo Mata sabo ta rude a ranta fa Dole sai ta auri Taufeeq nan gaba,Itama Mujaheeda Haka burinta ta auri Taufeeq ga Husna ma,ko wacce a cikin yaranta akwai me son ace ita Taufeeq ya aura ya Kara ko ta biyu ce da ita.

Ana gobe za a kawo Yar Gomna gaba Daya Suka gigice da gyaran gida Ana tana ta faman shirye Shirye,Ita Dama Ummi tasan komai.
Washe Gari Anna da yayanta harda yan Matan jikokinta su Azeema kitchen Suka fada Ana shiryawa Yar Gomna girki na Alfarma iri iri,gida ya dauki gyara da kamshi,Anna harda Nemo Driver ta bashi kudi tace maza ka siyo min Kwan lantarki a sa wancan kwanar Kar tazo dare yayi taga duhu Bai Dace ba.
Hajiya Asmau tace ga kudi a siyo abinda za a zuba Mata take away Wanda zata nuna a gidansu asan tazo gidan girma,Yar Bag zaku samo me kyau da tsada pls Azeema Kar ayi zaben Shirme na yan kauye,Zeenatu ta zaro kudi zasu kai dubu Hamsim tace ga wannan kuje ku taho da turaruka masu tsada Kal biyu,Maryam tace ai ni tunda naji yar girma ce tun daga Abuja na shiryo Mata kayan makeup na garari.

Mujaheed da Sadeeq tuni sun siyo Readymade riga me tsadar gaske Wanda dama masu sa irinsu sai yaran Gomna ko Shugaban kasa, Wata doguwar Riga ce Silver da mayafinta, Saloon Suka Fara kai Ilham gashi ya dauki gyara aka tarashi a tsakiya akayi Mata acuci dashi yayi kyau,ga Lalle ja da Baki an zana Mata ya hadu ko Amarya haka ta ganta ta kyale,Tana dawowa gida Abinci Yar Uwar Saddeeq ta kawo mata taci ta koshi,sannan tayi wanka tare da Brush, daukanta Suka sake Yi zuwa Wajen makeup, aka Yi Mata make up ta gaske gaba Daya Ilham ta canja kamanni, Idan Babu makeup sai kaga Ilham Kamar wata Balarabiya Amma yanzu Ana Mata kwalliya sai ta koma Yar India kawai, Rigar tayi mugun Yi Mata kyau cif cif jikinta,daga baya ta zobe tana Dan jan kasa, har Yafa Mata gyalen sune Suka shirya Mata yanda tayi kyau matuka ta koma Yar Shugaban kasa kawai.

Saddeeq kasa dauke idonsa yayi dayaga yanda Ilham ta koma,Mujaheed ya Kira a waya,yace ku Fito Mana an Gama Mata fa Ni gida zan wuce sai mun hadu,Muna Hanya ma yanzu zamu karaso,Ilham tana zaune 5mt sai ga Mujaheed ya shigo yace Zo mu tafi,Baki ya saki Yana kallon Ilham shima,Murmushi tayi tabi bayansa tana taku dai dai,Takalmi Suka Bata golden da Wata arniyar jaka Golden itama ta rike, Tana lekawa waje Ilham ta Saki baki.

Ganin Motoci guda biyar an shirya su a layi Hadaddun gaske sauran duk Securities ne masu tsaro,Ta tsakiya Kuma ba kowa, Mujaheed ne ya bude Mata bayan ta Shiga wani kamshi ya daki hancinta,Taufeeq ta gani ya zauna Kamar Ango yasha Wata Shadda kamar Golden kalar takalminta da jakarta,ba karamin kyau yayi ba Kamar a sace shi,Kallota yayi kawai itama ta kalleshi idonsu ya Sarke Dana juna,wani Abu taji a jininta da sauri ta kaucewa tunanin.
Sai satar kallon Taufeeq takeyi,Wani waje ya Dan jawo a motar turaruka Suka Bayyana,kala Biyu ya Mika Mata yace shafa wannan yanzu.
Kallonsa ta tsaya Yi yace action bafa gaske bane ki daina kallo na,Murmushi tayi ta karba tare da shafawa,Kamshi me Dadi ya tashi sannan motocin Suka tafi a hankali Kamar wani sarki aka dakko.
Mujaheed kuwa dariya ya dinga Yi shima ya shiga motarsa yabi bayansu zai ganewa idonsa Shooting film.

Su Anna suna Jin dirin motoci suka Fara fesa turaruka suna gyara kwalliyarsu,mazan kuwa su Ahmad jikokin Anna samari suna compound Wai zasu ga karyar Taufeeq mummuna zai aura ko Kuma yane,sunji Yar me kudi ce yar Gomna Amma ya kyawunta yake.
Motoci ne Suka dinga shigowa Cikin gidan Anna,Sai leke suke ta Window suna,Azeema harda Tsalle wayyo kaga motoci Lallai wannan sai Yar masu da Mulki.
Anna tace Kan Uba kaga matakan tsaro harda sojoji lallai Taufeeq yayi Dace.
Su dai su Ahmad jira sukeyi suka kyanta kawai,Matakan tsaron ne Suka budewa Taufeeq ya fara fitowa Yana baza kamshi ya zaga cike da Izza ya budewa Ilham,Ilham gabanta sai faduwa yakeyi tana ganin za a ganeta, Kamar zata Yi kuka,Dukawa Taufeeq yayi a hankali yace karki Bata Mana aiki Kuma ki nuna soyayya muke sosai ki nuna a turai Kika yi rayuwa da rayuwar turawa Kika Saba, irinsu su Anna ke so tsageru masu nuna zalama akan Namiji Marasa aji sosai su a ganinsu ita ce wayewa, masu leke ta window cewa suke kaga love,Uhm sai anyi Hira ma kafin a shugo Mana.

Ilham sai lokacin ta Fito Taufeeq a hankali yace ga yan sa Ido nan maza ki kula,a hankali Ilham ta Sa Hanninta cikin na Taufeeq a tare Suka ji Wani Yarrrr tsigar jikinsu ta tashi lokaci Daya Wanda Basu taba Jin irinta ba,Taufeeq a ransa yace Ashe Haka take Laushin fata, itama Ilham jinjina Laushin fatarsa takeyi a ranta.
Murmushin karya kowannensu ya saki suna tafiya a nutse Taufeeq Yana Yi Mata rada a kunne karfa kiji tsoro ki dage pls
Ilham tana yake hakora kadan tana cewa to Inshaallah.
Su Anna kuwa Ana leke ta sama cewa suke gata kuwa me fara'a gaskiya suna son junansu,kalleta wata muguwar Kyakyawa, ga Naira ga Kyau la'ilahaillallahu cewar Ahmad, Ina ma nine na sameta cewar jabir zan iya cinye Naman jikinta,irin wannan idan Ana Making love on Bed zaka iya Jin ma Kamar ka cinye su danyu haka zaka ji, Fu"ad yace ai idan nine da wannan to gaigayar jikinta zan na yi kullum zata Yi Dadi daga gani.
Mujaheed ya shige ciki tuni ya kame a kujera yana dariya a ransa.

Da Sallama suka shiga Palon Anna,Haj Zeenatu kadai Suka Iske,tana washe Baki jiki na rawa tace Surukarmu barka da zuwa Have a Sit, Sauran ne Suka Fito gaba Daya,har mazan ciki Suka dawo kowa ya zubawa Ilham Ido,Har kasa Ilham ta duka ta gaisar dasu Anna,Anna da sauri ta amsa tana cewa Allah dai yayi muku Albarka yaran nan,yasu Execelency? Haj Asmau ta tambaya,Ilham tana Dan Murmushi sama Sama da uwar gadara tace He is fine sunce a gaishe ku, ita a Dole Yar manya duk da Mujaheed Suka tsara abinsu, Sai janta suke da Hira tana basarwa, a hankali ta juyo tare da kallon Taufeeq da wasu narkarkun idanuwanta cike da Shagwaba tace Babyna kasa a kawo musu sakon Daddy Daya ce a Basu.
An Gama ranki ya Dade cewar Taufeeq,Anna Sai kallon Ilham takeyi sai taga kamar ta santa Amma ta kasa Gane a Ina ta santa,haka Yan aikin ma da Suka jere abinci sai kallon Ilham Sukeyi Amma sun kasa ganewa.
Mujaheed Yana ta kallon ikon Allah.

Kaya su laces masu tsada aka shigo dasu Ilham tace gasu inji Mama,Ta zaro dubu dari Uku Wanda Taufeeq ne ya Bata tace gashi Inji Daddy yace sai ya shigo Gari zaizo na musamman,Anna tace Kash ai ba sai ya bada Haka ba,Amma ba a maida hannun kyauta baya kice mun gode Allah ya Kara arziki,Taufeeq Da kansa ya zuba Mata Lemo ya Mika mata,ta karba,Ilham tana kallon lemo me Dadi tana son Sha gashi Kuma cikin Film ne, Dole ta Dan Sha kadan ta hakura,Abinci iri iri tana ta hadiyar yawu Amma ba damar ci,Taufeeq ta radawa Dan Allah naci da yawa? Da Ido yace a'a Dole ta Dan tsakuri kadan ta Gama,jimm kadan ta kalli Taufeeq tace muje ya kamata na wuce gobe kasan zan wuce Paris, Alright let's Go, Ilham ta mike tayiwa su Anna Sallama,Anna gaba dayansu har bakin mota Suka raka Ilham,Anna tace da kaina Zan budewa Jikata kofa,ta budewa Ilham ta shige mota,tace na gode Anna,ya ma Kika ce sunanki? Amatullah cewar Ilham,Suna me Dadi Allah ya kiyaye Hanya a isar mana da gaisuwa wajen His Excellency,zai ji Inshaallah.

Taufeeq ma zagawa yayi ya shiga mota Suka ja motocinsu Suka bar gidan baki Daya,Ilham ta dinga kyalkyala dariya, Guess House din Taufeeq Suka wuce gaba Daya domin tattauna next Mission da za ayi, Drivers da securities suka sallama suka tafi da motocin baki daya ta rage daga ta Saddeeq sai ta Mujaheed sai na Taufeeq kala hudu a gidan hutawar nasa.
Suna fitowa a tsakar gidan Suka tsaya gaba daya har Ilham suna kyalkyala dariya,Suna gwada yanda su Anna sukayi,Saddeeq yace Dole mu Sha kida yau Plan A ya hau saura B, Ilham ta cire takalmanta masu tsini ta zubar a gefe tare da jefar da Jakar,zata zauna kenan Saddeeq ya saki kida a peaker dake palon,Tsabar farin ciki sai da Ilham ta kada Kai a Zaune,Suka dinga dariya, Ilham tace a bani lemo Nasha na huce takaicin Wanda na gani na kwalele, Saddeeq ne yake ta rawarsa dama shima baya Jin kunyar rawa,suna kallonsa Ilham tace Kai ba Expert bane sosai.
Taufeeq shi Kanshi Idan ya tuna Anna dariya ce take kamashi harda sawa Ilham katuwar ledoji kala uku a booth,Tana shan lemo tace bacci nake ji? Dare fa yayi Sallah zamuyi mu tafi Zaki ce bacci zakiyi cewar Taufeeq,Ilham tace ayi Sallar ku tafi gida ni a barni a Nan yau na Dana kwana a gidan Nan hadadde,Idan Zaki iya kwana a gidan Nan ke Daya fine,Taufeeq ya furta,Ilham tace na kwana a kango ma tun ban Kai Haka ba,Mujaheed yace au Bari muyi Sallah ki bamu labarinki muma mu Baki namu,ok Ilham ta furta tare da Mikewa ta shiga Bedroom din data ga dama.

Alwala sukayi tare da Sallar Magrib sannan suka zauna Suna sauraron Ilham ta Fara Basu labarinta kaf tun daga farko har haduwarta da Ramcy da Kuma Manager na gidan Mai, Tana Hawaye ta Karasa Basu labarinta, Su Mujaheed sun tausaya Mata kasa magana sukayi a lokacin, Taufeeq Yana ji Amma kamar baya jinsu kawai Danna Waya yakeyi, Mujaheed ne ya Bata labarinsu Dana Taufeeq Amma Bai fada Mata matsalar Dake tsakanin Baffan Taufeeq da Mamansa ba,Bai fada Mata matsalar su Anna ba da komai kawai Tarihin Taufeeq ya Bata.
Bayan sun shirya yanda plan B zai kasance Suka tafi gaba Daya,Ilham kawai aka Bari a gidan Wai sai ta dana, Key Taufeeq ya Ciro spear ya Bata Suka mata sai da safe suka wuce.
Ilham da kanta ta shiga kitchen tare da Hadawa Kanta Indomie kasancewar ba wani kayan Abinci masu yawa a gidan,kayan tea ne sai Indomie da kayan sha a Fridge.
Bayan tayi Sallar Isha Wanka tayi ta zauna daga ita sai Shirt wandon ciki da Vest ta haye saman lafiyayyen bed din tayi adduar bacci ta kwashe ta.

Washe Gari tunda tayi Sallar asubuta ta koma Bacci sai 1pm ta tashi,gyara ko Ina na ciki tayi daga compound Kuma akwai masu aiki maza,Wanka tayi tare da gabatar da Sallar Azahar,tana Idarwa ta maida rigarta data cire jiya, ta daura dankwalin kanta, Indomie taci da lafiyayyen tea dinta,Wanke Kwanukan tayi ta dawo Palo tana kallon film a tv, har La'asar tayi ta mike ta gabatar da sallah ta zauna taci gaba da kallonta.
Tana zaune taji wayarta tayi kara,tana dubawa taga Mujaheed ne, da sauri ta daga tare da yin sallama,Yace Amarya a bude Mana Kofa,Mikewa Ilham tayi tana murmushi ta bude musu Kofa,Saddeeq da Mujaheed ne Suka shigo da Ledojin take away,Saddeeq yace kaga Mata har ta gyara gidan da mazane tafiya zasuyi kawai, ai kazamai ne maza cewar Ilham, Mj ku nasan Me Aiki kuke sawa suna gyara wannan gida? Kamar kin sani ko tsinke bama daukewa.
Ledojin take away da suka shigo da su Saddeeq yace gashi Nan ko zaki kici gidan Nan ba abincin dafawa,Na gode Tall man Kamar kasan Indomie ta ishe ni,
Kofa sukaji an turo da Sallama,Taufeeq ne ya shigo sanye cikin 3qutr da t-shirt na Shan iska yayi kyau,Bai kula kowa ba ya shiga kitchen yaga ko Ina Neat yasan ma Ilham ce ta gyara,fridge ya bude ya dakko juice Yana Sha Hannunsa Daya a cikin a lljihun wandonsa ya fito, Shima ya zauna kusa da Mujaheed,Ilham tana satar kallonsa tace Ina yini,lfy yace kawai yaci gaba shan lemonsa,Ki ci abinciki mana waccen ledar ki duba kayana Tall man ya siyo Miki ki zaba ki saka kala

Please Login or Register in order to submit comment