Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yan aji,Aiko sai tafi raf raf Wanda dama duk ajin babu me kokarin Ilham, Komawa tayi ta zauna tana gadara,Malam yace Golden girl kin iya kin huta Allah ya Kara basira Dole kiyi abinda kike so,Ilham ta nuna kanta da babban yatsa tace wa zai ja Dani to waye ya Isa.

Ilham tana komawa gida Dabbobinta da takewa Jama'a kiwo tana cikinsu tana Basu abinci da ruwa,ganin Basu koshi ba ta jasu ta dauresu a waje gefen Gida inda yake da ciyawar da zasu ci sannan ta koma gida tayi wanka ta shirya cikin Riga da wandonta data Saba Yan gwanjo tasa Hijab ta fice tare da daukon nikan Rogon Danwake ta tankade shi ta zuba a Leda ta Kulla a ledoji sannan ta jera a saman Faranti ta fice Tallanta.
Tana tafiya da tallanta tana wakokinta na fina finan Hausa ita a Dole ta waye, yau ta Gama zaga Gari sisi Bata Yi ciniki ba har kusan Magrib a gidan Kawarta Hadiza wacce an Riga da anyi Mata aure anan tayi Sallar Magrib sannan ba abinda taci ta dawo gida Babu nasara.

Tana shigowa ko sallama su Halima Basu amsa Mata ba sai hannu da Zubairu ya Miko itama Anty Halima ta Miko Hannu suna cewa a Miko kudin abinci da Zama a gidan wasu,Yau to banyi ciniki ba Amma Anty wlh kina bani mamaki Kanwar Mama na Uwa Daya Uba Daya Amma bakya iya Yi min komai kyauta sai na biya da kudina,idan yaranki ne ai baza ki musu Haka ba gasu Nan Shar Shar Amma Ni wahalata nake da kudi na duk suke yin karatu har suturarsu, Amma Abinci ma sai na biya da kudin kwana, ai ba gidan Yar Uwar Mamanki bane gida na ne cewar Baba Zubairu Rocket,Baki Ilham ta tabe tace Baba Rocket ka dinga Jan girmanka wlh tam yau ba kudi sai kowa ya hakura Kuma.
Anty Halima taja tsaki tace to wallahi yau Ilham Baki da abinci a gidan Nan sai dai ki kwana da yunwa, gobe ma wallahi idan Baki kawo sisi ba ko a gidan Nan baza ki kwana ba, Shuru tayi sabo da ta Dade watarana sai dai ta kwana a kango ko gidajen makwafta matukar bata kawo kudi ba basa daga Mata kafa ko kadan shi yasa Bata da aiki sai Neman kudi.

Washe Gari Haka tayi Yawon,Ilham tayi tallan duniya Amma abinka da sana'ar kauye ba a samu me siya ba,Dole Haka ta dawo da dare Bayan tayi Sallar Isha taci tuwonta a gidan Hadiza Kawarta sai ta shigo gidan Babu sisi, Nan take Zubairu Rocket yace Idan ba kudi ma karki shigo min gida,Anty Halima tace tunda Haka Kika zaba ai sai kiyi waje Yar iska marar mutunci yau kin jawo Mana ko Miya bamu Yi da nama ba,Ilham ta Riga da ta Saba da kwanan kango,Kayan tallan ta ajiye tayi waje kawai,Amma Sai Anty Halima ta fatalo Mata kayan tallan Suka tarwatse a kasa Garin rogon ya zube,Ilham tana gani idonta ya cika da Hawaye Amma ko juyowa Bata Yi ba ta tafi abinta, Gungun Maza Yan Wiwi suna ta shaye shaye Suka hango Ilham Hamza yace ga Ilham can an korota yau Bata ba da kudi ba,gashi Dan gidan me Gari saurayinta baya nan dama shi yake kaita gidansu tana kwana.
Ilham kuwa duk yan Wiwi ta rigada ta sansu sun Saba sosai sabo da kwanan waje, Direct wajensu ta nufa can Jikin bishiya kusa da Daji ,Sallama tayi musu Suka amsa Mata,Sagiru yace Ze Golden ya akayi ne, Kun San komai an Koro Ni Ilham ta furta, kiyi hakuri kinji Allah zai saka Miki cewar Saleh shima,ba damuwa ai na saba ta furta,Kabiru ya Miko Mata wiwi yace Dan Sha Ze Golden damuwarki ta yaye,Hamza Aji garau ne yace karki Sha mu Kamar kanwarmu kike Ilham,Karki yarda ki Sha komai ba tarbiya
ba ce,Murmushi tayi tace na gode Hamza Aji Garau Kuma Ina gode muku ba karamin taimaka min kukeyi ba,da wasu ne wlh sai dai kokarin lalata min rayuwa Allah ya bani ikon kyautata Muku Nima,Ameen Suka ce suna Mata kirari Ze Golden.

Wajen maza sunfi su Goma zaune suna ta shaye shaye suna ciye ciye Ana Hira Wasa da dariya,Ilham Ce kadai mace a Gefensu itama tana zaune kusa da Hamza Aji Garau sanye da Hijab dinta.
Whot Suka sa a tsakiya Suna buga game din Wanda Ilham ta shiga Ana Yi da ita sosai ta iya wajen su Hamza,Tana zaune Sagiru ya kwaso tattabarunsa da yake kiwatawa guda takwas,a lokacin Suka yanka su Suka gyara su Ilham tana zaune har suka wanke tare da Barbada gishiri aka kunna wuta suka Fara gashi ana ci,Sagiru yace sabo da Ze Golden aka yanka Naman Nan,da girma ya Fadi gwara jari ya karye,sai dariya sukeyi Har Ilham, Hamza Aji Garau ya cire babbar rigarsa ya bawa Ilham yace gashi naji an Fara sanyi,dake Hamza akwai Tsafta rigar fes tana kamshi da warin Wiwi Kuma,ta rigada ta saba Jin warin baya damunta.

Ilham taci Naman Nan suna ta whot har tsakiyar dare,bacci ya Kama Ilham ganin Haka Hamza ya Mata Shimfida a gefe yace kwanta a Nan Kinga duk gidajenmu irin na Fulanine Babu daki daban bare mu kaiki gidajenmu Kuma dukkanmu da aurenmu za a samu matsala da matanmu, Ba damuwa ta furta ta kwanta tare da dunkulewa waje Daya tana ta kuka tana Tunanin Rayuwarta ace mace kamarta a wajen maza zata dinga kwana sau da yawan lokaci.
Kwana sukayi suna shaye shaye Yayin da Ilham ke zuba baccinta hankali kwance har Gari ya waye a wajen Suka yi Sallar asuba har Ilham sannan Saleh ya bawa Ilham Dari biyar kyauta yace tafi gida,Aiko ta mike tare da zuba musu Godiya Hamza ya Rakata har kofar gidansu ta shiga sannan ya tafi abinsa.







🥰🥰
Masu siye za'a saka ku a group din novel din,Dari biyu ne 200, Amma Wanda Suka siya bayan an Gama posting sai complt to Dari Uku 300 ne sabo da ya Zama complt an Gama.
😘

Ina kaunarku fans. ko Baki Siya ba matukar fan Dina ce ke Ina sonki.







Asmabaffa.
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰







NA KUDI NE








2






FREE PAGE






Official







By
AsmaBaffa






'YAR KWANGILA IS
DEDICATED TO
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.🚨






RASHIN SA'A Cmplt
Naira dari uku 300 ne

TA GYARU Cmplt
Naira dari Uku 300 ne

'YAR KWANGILA
Dari biyu 200 ne kafin a Gama Complt,bayan an Gama Kuma ya koma dari Uku shima 300.

Ga masu Bukatar siye ta Bank ga accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad,Zenith bank.

Zaku Iya tura number katin waya Mtn ta WhatsApp ko Sms ta Nan
08033933642

Masu bukatar Transfer Kati ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668

'Yan Niger masu bukata ga Number da zaku nema
+227 90 79 59 39.








Ga naku page

Mamu Galadima
Malakso
Mrs Hass@n
Khadija A Hamza.







Rabe Rabe Ilham ta shiga Yi zata shiga gida jikinta futu futu sabo da kwanan da tayi a wajen yan Wiwi gaba Daya warin Wiwi takeyi kamar ita ce ta Sha, Rukayya da Bilkisu ne Suka Fara hango Ilham zata shigo gidan,Bilki tace Laaaa Anty Kinga Ilham tana ta faman lekowa Kamar mayya,Anty Halima tana wanki ta juyo tare da lekowa Suka hada ido da Ilham kuwa,Tace shugo munafuka Idan kin samo kudin,Harara Ilham ta zubawa Anty harda murguda Mata Baki,Ni kike zagi?Anty ta tambaya,Kai Ilham ta daga Wai ae tana daga Zaure,Kwafa Anty taja tace Bari Zubairu ya fito daga bayi kiga yanda zai Miki.
Fadin Haka ke da wuya sai ga Zubairu ya fito daga Toilet da kafa Kamar ta Dan Kaciya Yana Talau Talau,Sai faman shinshina Hannunsa yakeyi ko me yake ji oho,ga Ilham cewar Bilkisu,Zubairu ya zabura Yana dube dube yace nasan ta samo na cefane ta shigo Idan Kuma Bata samo ba to ta koma Inda ta Fito gaskiya.

Ke Halimatu nifa da Kika ganni bana kaunar rike Dan wani a duniya ko kadan,na tsani Dan wani wlh matukar Zan riketa baza ta dauke min nauyi ba ta hutar Dani wajen neman na cefane to wlh sai dai ta bar gidan nan,bazan iya ci da Dan wani ba,na bada wajen kwana kyauta bazan iya ba,sabo da Haka ta kawo kudi,sannan nafi so ma ta Fito da miji ko na bada ita sadaka Idan Kuma ba haka ba a kaita aikin shara da wanke wanke Birni ta dinga samo mana kudi kawai Amma Idan ba Haka ba nifa bazan yarda ba musamman yanzu da nake sa rai na kusa yin kudi zan siyi mota sabuwa fil.
Anty tace nima Dan ta Zame min Dole ne Yar yayata ce shi yasa Amma Ina dalili yarinya gaba Daya ta hana yarana farin jini ko samari Basu da su sai ita kadai ake rububi kowa yazo Ilham,Dan kawai tana da kyau Amma nawa ai sunfi ta shigar Kaya masu kyau.

Anty tace cikin fushi Ke Ilham shugo tun kafin Zubairu yazo ya Miki dukan tsiya cewar Anty, Ilham tana daga Zaure tace Na zubabawa gyatumarsa zagi bazan zo ba Kuma kudi gasu da yawa bazan bada ba,Tafi Tayi tare da murgudawa Anty Baki ta wani rike kugu,Kwafa Anty ta ja tace Zan kamaki ne.
Ilham tasan idan ta Shiga gidan duka Zata Sha wajen Anty sai ta lallabo ta jefo kudin ta labe a zaure,Zubairu da Anty ganin kudi sun manta ma Ilham tayi musu rashin kunya,Zubairu yace to shigo Mana Yar banza ai yarinya ce akwai kuruciya Dake damunki yaushe zamu biye Miki,Ilham tasan ta bada kudi ba matsala sai ta wuce,wanka tayi ta fito ta Fara aikinta na yau da kullum Wanda ta Saba.

Washe Gari Friday ranar kasuwa da safe Ilham ta shirya cikin Riga da skert Yan kanti Wanda sunji jiki da mayen Hijab dinta red ta Fita zuwa kasuwa abinta, Kitse ta dauka a katon tire ta Shiga zaga kasuwar tana Talla tana cewa Karyar Mangyada da manja ta kare, karshen Tika tiki tik Dan ubanki masu Mangyada da Manja,Zaki garki da maiko sai kitse, Azo a kwashi Dadi ga Kitse me kyau na shanu,Me gida kaji miyar matarka wata kamar Lalle babu Kan gado,ka Fara Jin Haushin Uwar gida,wani ma har ta Kai ga ka Kara mata kishiya itama Amarya Bata San sirrin ba sai su Zama iri Daya ka Fara Dana sanin auren sabo da miya Babu Dadi,to me share muku Hawaye tazo,Ga sirrin Azo a siyi wannan kitse me Zaki da Gardi a gwada, duk Wanda ya gwada baiji dadinsa ba ka dauki Carbi ka ja mini Allah ya Isa kafa dubu,Ilham Me kitse Allah ya kawo ta.
Haka Ilham ta dinga Talla tana ciniki, tana cikin Tallanta wasu motoci na Allah tsine uwar me karya guda Uku da matakan tsaro Suka biyo ta tsakiyar kasuwar dama kasuwar tasu a Kan Hanya take ta raba titi a tsakiya Dole idan Zaka Shiga Garin sai ka bi ta kasuwar.

Yuuuuu Yan Kauyen suka bi motocin da kallo har Ilham,a kasuwar suka tsaya wani Cikin securities din ya bude mota ya fito da sauri ya Tambayi wani Dattijo me siyar da maganin gargajiya yace Malam Dan Allah sassaken wata bishiya muke nema an ce a Nan haka ake samunta,Dattijon yace ya sunanta? Sansana sunanta security ya Furta,Dattijon yace tabbas akwai ta Amma tana cikin Garin nan,kaga waccen me Tallan kitsen to akwai Bishiyar ma a kofar gidansu kuje da ita ta Baku,Ilham Dattijon ya Kira,ta karaso da gudu,yace kuje da mutanan Nan ki sassako musu Bishiyar Sansana ta kofar gidanku,to Amma Bari na ajiye farantin Tallan,da gudu ta juya ta kaiwa Me kitse kudin ciniki da farantin shi Kuma ya Bata ladanta.

Dawowa Ilham tayi Inda motocin suke duk ta hada uban Zufa, Security din kuwa tuni ya sanarwa ogansu yace a sata a mota,cikin Motar tsakiya ta Oga aka budewa Ilham ta shiga wani kamshi da sanyi ya daketa Amma sai tace ita baza ta Shiga ba tsoro take ji sai dai ta shige gaba su bita a baya,Yin duniya Ilham Taki shiga sai da Dattijon nan yayi Mata magana sannan ta Shiga a hankali Cike da tsoro,Wani Farin matashi Hadadden gasken gaske ta gani Amma ya wani kwanta a kujera ya wani Yi kwanciyar Isa da gadara sannan ya rufe fuska da Magazine,ganin irin Haduwarsa ta surarsa da cikar zatinsa Ilham tasan Fuskarsa ma ta hadu shi yasa ma ya rufe ta Dan Kar agane Masa kyau.
Kamshi ne kawai ke fesowa daga jikinsa,Sanye yake cikin kana Nan Kaya wandonsa black Jean ne a dagargaje Creazy Jean pencil,da wata Riga me gajeren Hannu ruwan toka.
A hankali Ilham ta zauna can nesa ta rabe a jikin window, security ne ya rufe kofar sannan Suka ja motocinsa zuwa cikin Gari kofar gidan su Ilham,kida sai tashi yake kadan kadan a motar da Ilham ke ciki.

Ilham mamaki ya kamata taga ko motsi baiyi ba bare ya kalleta Kuma yasan mutum ya shigo motarsa,Baki Ilham ta tabe sai Kuma tayi magana tace Malam ka Bude fuskarka ka Sha Iska Ni ba kyawunka Zan gani ba ma,Idan kyaune gidan kazo Nima Kyakyawa ce, Kuma Ina da Tsafta kawata kuwa Hadiza baka santa ba ko? To kazama ce,nice ma nake Dan zuwa Ina gyara Mata gidanta Amma mijinta Haka yake zuwa ya kwanta a ciki,Amma fa wallahi akwai shi da cin Dadi,Indai nama ne baza a fada masa kullum sai yaci,idan naje a San mini nacinye abina, Tunda Ilham take surutunta ko kallonta baiyi ba bare yayi magana,Amma Bata hakura ba tace idan Zan je makaranta Antynmu Naira goma take bani kacal Amma yayanta sai ta Basu Naira Talatin Talatin Dan Allah anyi Adalci nan? Haka nake karba ya zanyi mamata ta rasu da Abba na,da tuni Ina wajensu Ina Jin dadina,a siyo mana nama,ai wallahi kaga a kauye muke ko? to bana cin tuwo da wasu shirmen su Rice bana ci,ba abinda ya Dameni da su,nifa ba komai nake ci ba sai kawai me Dadi irin su Indomie Funkaso,kosai ko naci gurasa ta Kuma Dan kadan,ai shi yasa Yasin kowa a Garin Nan ake cewa Ni kalar masu kudi ce sabo da halayena,to gado nayi Abba na da Mamata baka gansu ba Yan gayu ne.

Driver ne ya katse Ilham yace Hajiya nuna min layin gidan naku,Ilham tace gashi can wancan rubabben gidan Wanda duk Garin Nan Babu kamarsa a lalacewa,Murmushi Driver yayi Suka nufi gidan,Ilham tace uhm Bari nayi Shuru Ni dai kasan a Garin Nan cewa akeyi bana magana,kaga gidan su Danliti mun wuce makwaftanmu ne gidansu masifaffu ne,cikin sigar rada tace Kalla kalla gidan su Shamsiyya mayya ce wannan,gaba Daya mayu ne a gidan sai da Suka cinye mutane dari a Garin Nan Nima Allah ne ya tsallakar Dani Amma da tuni nice ta dari da Daya,rannan har sun kamamin kafa ta Fara Ciwo Allah yasa Suka saketa na warke,Da yatsa ta nuna wata bishiya tace kaga Bishiyar dabinon Iya Babar su Hauwa,itace ta shuka abinta.
Laaaaa Allah sarki kaga inda muke yin Wasa kullum a can wajen nake zama,Ilham tana ta surutu har anzo kofar gidansu Bata sani ba sai da Driver yace anzo maza kiyi sauri.

Ilham ta kasa bude mota sai Driver ne ya fita ya bude mata ta fice da gudu ta fada gida,tana Shiga kudin data samu a kasuwa ta mikawa Anty wacce ke Tambayar Ilham lafiya? Ko kulasu Ilham Bata Yi ba sai ma cewa tayi Baki da Hurumin jin sirrina tunda Baki daukeni 'ya a wajenki ba, ta dauki fatanya ta fice da gudu tana Fitowa ta hau bishiya da Sara,tana sassakowa,sai da ta sassako da yawa sannan Security ya Mika Mata leda ta zuba musu a ciki Suka koma mota zasu tafi Oga ya sauke glass kawai Iya Hannunsa Ilham ta gani fari Tas me kyau, ya Miko mata kudi Yan dubu dubu zasu Kai dubu goma,Ilham ta bude Baki tace a'a ba ruwana ni dai wlh ku tafi da abinku,Zubo Mata da kudin yayi a kasa,wata muryarsa me shegen Dadi da sanyi Ilham taji yace Na gode,ya maida glass Tana Kallo motoci Suka bar kofar gidansu Suka tafi abinsu.

Ilham da sauri ta kwashe kudinta tace angode Allah sarki na Saba da shi,zanyi kewarsa, rau rau tayi zata Yi kuka ta Furta me yasa ka Bari na Saba da Kai? da na sani na bika ka tafi Dani...kudin dake hannunta taji an Kai Masa wawar fisga an kwace kudin du da aka bata,muryar Zubairu da Anty taji suna cewa annamimiya Allah ya kamaki da tuni kin boye kudin kin barmu da Yunwa munafuka.
Kuka Ilham ta saki har ga Allah ta so kudin nan ko Dan ta dinka sabon Uniform ta Dan dinka atamfa gaba Daya Bata da kayan sawa masu kyau,Uniform dinta ma yasha maho Amma ba yanda zata yi Dole tana gani ta hakura.
Ilham gida ta shige ta Iske suna ta murnar kudi wanka tayi kawai ta fice yawonta gidajen kawayenta Wanda gaba Daya anyi musu Aure tuni Ilham ce Anty ta hanata mazan aure sai na banza,indai me son Ilham ne da aure tasan ba Wasa sai ta Hana Ilham Zuwa zance wajensa,Amma idan na banza ne sai ta korata Dole taje.

Kamar kullum da dare Sun Gama cin tuwon shinkafa miyar kuka,Ilham ita Tuwo Bai dameta,tace Anty Dan Allah a cikin Kudin Nan Dan bani dari biyu na siyo Indomie na dafa da kwai? Da masifa Anty Halima tace Lallai yarinya mantawa kike yi a Nigeria kike ko? Ko kin manta ke Marainiya ce? To ki daina Kai kanki inda Allah Bai kaiki ba idan ma zaki kwashi tuwo ki kwashe shi,Sabo da mun samu kudi yau shine yasa har kuka ga Tuwon shinkafa, da ace babu daga na dawa sai masara, Baba Zubairu Yana gefe yace to kinji sai a bi duniya a sannu,a taka a hankali yawwa...sallama wani yaro ya kwada ko amsawa Anty Bata Bari anyi ba tace lafiya Malam? Ilham Wai tazo Inji Alhaji Amadu,kace Bata Nan Kuma anyi Mata miji Kar ya sake zuwa Wajen Ilham sai dai Bilkisu itace a layi cewar Anty Halima ganin Yana da kudi Yana da kudin da zai auri Ilham gashi wayayye Yana fita Lagos cirani.
Ba a Dade ba wani yaron ya shigo yace Ilham tazo Inji Auwalu,Karaf Anty tace wanne Auwalu? Yaron ya furta yace Auwalu makarmo na gidan su Jafaru me Trader,Ok kace gata Nan,Anty tasan Auwalun bazai iya wani aure ba,fama sukeyi da kansu ma,Dan karamin Baki Ilham ta turo tace gaskiya Anty kina shiga rayuwata gaskiya Allah yaji Kan Mamata da Abba na Amma Ni wlh gwara a siyar Dani,Mikewa Ilham tayi tare da yin fatali da kafar Bilkisu data miketa a Kan Hanya tayi waje cike da bacin Rai.

Tana fita tace da Auwalu makarmo to sarkin kankamo Ni Ina da Wanda nake so ka daina zuwa wajena,Makarmo ya washe Baki zaiyi magana Ilham taja tsaki ta shige gida abinta, Koda Ilham ta kwanta bacci kwana tayi tana Mafarkin me motocin data sassakowa magani Amma Bata ganin fuskarsa ko a mafarki sai dai ta ganshi a motar Nan ya rufe fuska da magazine.
Da Asuba Ilham tana farkawa tace Dan banzan mutum sai mafarkinsa nakeyi ko maye ne ban sani ba Dole nayi turaren tagargaje,Aiko tana idar da Sallah ta ebo Tagargaje na Zubairu ta zuba a garwashin wuta tare da lullube kanta sai da ta shanye hayakin Nan tas gidan ma ya dauki Hayaki,Ilham tace nayi maganinsa sannan tayi wanka tasa Uniform dinta matacce ta tafi schl.

Shirmen Ilham duk makarantar da aka sata idan taga dama ba ita zata je ba sai wacce ba ita aka sata ba sai ta tafi can,Babu Wanda ya santa take shigewa aji,yau ma tana sauri tace yau makarantar Kofar kudu zanje ajin su Bilkisu, bazanje tamu ba,Haka kuwa taje ta shige ajin su Bilkisu Ana ta kallonta da mamaki sabo da Uniform dinta daban ba iri Daya bane,har Malam ya shigo aji ya ganta Amma baice komai ba yayi zaton transfer aka Yi Mata daga wata makarantar, Yana koya musu Geography yace wace zata fada min yanayin da ke faruwa lokacin Hammatan Season? Da sauri Ilham ta daga Hannu tare da Mikewa tsaye.
Malam yace yes, Hammatan Season shine lokacin Hammata Dake jikin mutum take wari da Hamami, a wannan yanayi manya Wanda Suka balaga da kazamai Wanda basa wanka sukanyi wari matukar Babu gyara,A yanayi na Hammata idan Ana Iska takan shakata,Malam Baki ya hangame Yana Jin Ilham,Ilham tace yo Ni ka zuba min Ido kaima bazan cire ka ba gaskiya zan fada matakar Safina tace Haka kake baka asketa baka kula da ita har kitso za a iya Yi,Ni bani na fada ba matarka ce,shi yasa kazo kullum ka Dame mu da lokacin Hammata, Tana Gama fadin Haka ta fice da gudu ta bar makarantar Baki daya Bata tsaya ba sai a gidansu,dalibai Suka dinga yiwa Malam dariya sai ajin ya Bari sabo da kunya.

Bayan wata Biyu Babu abinda ya canja a rayuwar su Ilham,har Lokacin Babbar Sallah tazo yau ta Kama ranar Idi da safe, Ilham anyi kwalliya cikin Atamfa Wata shara shara wacce ake cewa baccinki ya ja Miki da Hijab dinta kusan ta Riga kowa zuwa masallacin a gabanta akayi komai Sannan akayi Sallar Idi sabon takalminta a Nan Ilham ta cire ta kalli wasu Mata Wanda Bata sansu ba Basu santa ba tace ga takalmana ku taho min dashi gida tayi Tafiyarta da kafafunta ba takalmi har taje gida.
Suma Matan a Nan Suka tashi Suka bar takalman Ilham,sabon takalmin da kyar Anty Halima ta siya Mata Amma Ilham ta barshi a masallacin ta haye Machine tayi gida.

Da sallama ta Shiga gida lokacin Anty tana kwashe tuwon Sallah na danyar shinkafa miyar Taushe Tasha Manja,Ilham tace a bamu tuwon Sallah mu kwasa,Harara Anty ta zuba Mata tare da cewa Dake Ubanki ne yayi cefanen ko? A'a Ina Ubana zaiyi cefane Yana lahira Kuma Inshaallah Yana Aljanna firdausi Yana kwankwadar Barasar Aljanna,Wa ya sani ma ko da ita yake karyawa a kabari Kuma Ni nasan Zubairu sai dai yasha Kunun Jahannama Baki wuluk me kauri, Bilkisu wacce ko Sallar Idi Bata je ba tana zaune tana gyara gashinta ta mike ta cakumi Wuyan Ilham suka Fara kokawa,Bilkisu ta fadar da Ilham kasa,Ilham tasa kafa ta shatile kafafun Bilkisu ta fadi kasa itama,Zubairu Rocket ne ya Fado gidan da bala'i yasha shadda Red jajir da ita dau sabuwa ta Sallah, Dan Ubanki Ilham Kashe min yata zakiyi? Karki manta fa gidan ubansu ne wannan,Alfarma ake Miki,Baki Ilham ta chokalo ta dauki Tuwo a plate,Tsaya na zuba Miki miyar da kaina karki zabe Naman muguwa cewar Anty ta fisge kwanon,Anty tana zubawa Ilham miya ita Kuma Ilham tana cewa ni wajen man Zaki yado min,Miyar Sallah baka shata da Mai ba me kayi kenan ai naji kawai Mai Yana biyo min har gwiwar Hannuna shine nasan Anyi sallah,Mayya gashi Nan tafi cewar Anty bayan ta Gama Zubawa Ilham miyar da Mai.

Bayan Sati biyu Ilham Sam Bata da Lafiya tana zazzabi Bata samu damar fita buga buga da neman kudinta ba sabo da Haka tana Jin sauki Zubairu da Anty Halima Suka takura Mata akan Lallai sai ta Nemo kudin cefane,tasan idan Bata je ta samo ba sai dai tayi kwanan kango,masallaci ko ta roki Alfarma ta kwana gidan wasu makwafta.
Dole ta lallaba tayi

Please Login or Register in order to submit comment