Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu ga nasara ba,ba sonta kakeyi ba,ba komai ba aikine zata Yi a biyata dukkanmu mun sani,Haka itama ta sani shi yasa ma tace ba sai an saka danginta a Maganar ba,sabo da idan kun rabu zata koma wajensu watarana kaga Basu San ma ta taba aure a duniya ba,sabo da ta bamu labarin danginta shigarsu cikin auren akwai matsala tunda Bata da Iyaye.
Kaga Malam nifa kudi zan biya ta ba kyauta zata min ba akan me zaka takura min,Haushi ne da takaici ya Kama mujaheed a fusace ya mike yace Bari na kirata,Dan Ummi nakeyi badan Kai ba,Kofar ya murda yaji Ansa key bam ya kwankwasa mata Shuru kawai yaji Taufeeq Yana ta tuntsira Masa dariya,hakan yasa Mujaheed a fusace ya fice Daga Palon zuwa inda yayi parking din motarsa ya Shiga tare da figarta da gudun tsiya ya bar gidan.

Ilham taji bugun kofar idonta cike da bacci ga magagi tanayi ta bude kofar tana tangadi gashin kanta duk yayi buzu buzu ya rufe Mata fuska sai Sosa gashin takeyi,a hankali cikin Muryar bacci tace waye ya buga min Kofa,tunawa tayi da rigar bacci ta Fito bayan Haka ma kanta ba ko dankwali,jikinta ta Fara shashafawa Dan ta tabbatar,aiko Wata Kara ta saki kadan tare da fadawa Bedroom da gudu tasa key Karas karas.
Dariya ta bawa Taufeeq ma Dan shi kararta yaji Bai wani kalleta sosai ba.











AsmaBaffa.
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰







NA KUDI NE




51-55






'YAR KWANGILA IS
DEDICATED TO
MAI DARAJA
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.








Official








By
AsmaBaffa





RASHIN SA'A CMPLT
DARI UKU 300

TA GYARU COMPLT
DARI UKU 300

'YAR KWANGILA
DARI UKU BIYU 200 ga me so a sata a group.

Zaku iya Siye ta wannan Hanyoyi kamar Haka..

Accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, zenith Bank.

Transfer ko Vtu ku tura a Nan..
09032409668.

Tura katin MTN ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number..
+227 90 79 59 39.




Page naku ne
Real Maman walida
Mmn Abida ce
Mrs Naseer
Ummu Sadeeq.

Malakso
Jidder Zaria
Meenal
Ina miko gaisuwa.



Fans Dina masu Sharhi da godiya da masu Yi min Addua Ina matukar godiya Ina kaunarku, Inshaallah Zan kamanta Baku page ko da wasu Basu samu damar siye ba Ina sane daku.

Wanda suka min Sharhi Ko ban Yi Reply ba ayi min Uzuri sai idan ban gani ba ko ya Sa min waiting.








Murmushi yayi kawai ya mike ya bar gidan Shima Baki daya,Bai tsaya ko Ina ba sai gidan Anna, a palon Anna Taufeeq yayi Sallama sun Hadu yaran Anna da jikokinta suna ta tsare tsaren bikin Taufeeq sabo da ba lokaci aka sa me tsawo ba, suna ganinsa Suka ce yawwa gashi ma Yazo Cewar Haj Asmau, Taufeeq event muke so ayi kala Takwas Muka shirya Kasan Dole muma mu kashe Naira sabo da munyi magana da Abdulaziz Baffanka yace ko nawane a sanar maka zamu Yi Shirye shirye Cewar Zeenatu,Haj Maryam tace sai ankuna da za a fitar da sauransu,Baki Taufeeq ya tabe tare da zama a gefen Ahmad Yana cewa Babu fa Wani Event da zamuyi Amatullah tace Bata so ko za ayi kala Daya za ayi Idan an kawo Amarya,kun san fa ita Mamanta ta rasu,itace ya ta farko wajen Mamanta a hannun Matan Uba ta taso sabo da Haka ita Sam Wani party Basu dameta ba kala Daya Zata Yi,ba wani gayyatar mutane zatayi ba sosai so karku damu kanku,Haj Asmau ta Nisa tace wannan kuwa Anya Yar Gomna ce Taufeeq? Nifa Ina da Dan ja,Kefa Shashasha ce ki kalli wannan iya fatarta kawai ai kin San Yar Gomna ce cewar Anna ta hayayyake da masifa,Haj Maryam tace kyaleta Anna taga fa gidan ma common Kanin Babanta da irin kayan da take sawa da komai nata ta daban ce.

Azeema tace Umma tunda Kika ga mun yarda ai mun gano Yar manya ce,mune Yan zamani mu Muka san abubuwan Zamani Babu tantama wannan Naira da Hutu sun ratsata.
Taufeeq yace fada musu dai sister, Anna tace ayi party dayan ai su manya basa shirmen Event irin na talakawa gayyar tsiya, Banga Kuma laifinsu ba,Taufeeq Yana latsa waya yace Babanta ma Shine ya Kama wajen a Nan Garin inda za ayi Dinner, Mashaallah cewar Asmau da talakawa ne shike Nan a jikinka zasu laru komai miji gayyar na Ayya.
Sun Dade suna tattaunawa.

Ilham kuwa washe Gari ta sanarwa Ramcy a waya,Ramcy ta dinga murna tace saura sati daya bikin zanzo da mu za a Karasa Mission din Zan sanarwa Manager Rabiu shima ya taho ko ya Kika ce? Ae Mana yanzu ma Kinga Ina Guess House dinsa Ni kadai sai abinda Naga dama nakeyi cewar Ilham, Ihu Ramcy ta saki Wanda sai da Kakarta ta Dirka Mata duka a bayanta,Ilham tana ta dariya suna Wayarsu tana ta bawa Ramcy Labari, Ramcy kuwa Manager ta Kira shima a waya ta fesa Masa yace ki Shirya Ramcy Next wk zamu wuce can Jigawar Muna cikin Walliyan Amarya za a Basu kala,wani show zamu yi, Dariya Ilham tayi tace ai Suma Iyayen Next wk Zasu dawo Jigawa sai mu hade a can.
Ramcy tace Kai kaga Haduwar Mijin Ilham Kamar balarabe na taba ganinsa sau Daya,sai ka ganshi kawai, Rabiu yace nafa canja mota sabuwa me tsada Zaku ganta Idan mun Hadu,Allah ya kaimu kace da ita za Basu kala wlh cewar Ramcy.

Ana ta shirye shiryen biki cikin gaggawa har sun bugo Iv Hadadde me tsadar gaske,An Gama Hada Lefe na Alfarma Baffa ya bada kudin,Akwatuna kusan Guda ashirin Suka Yi kusan duk kayan Haj Zeenatu ce taje kasar waje ta Hado su na Alfarma tana can Bata dawo ba sabo da Bata siyi Inner wears ba sai ta tambayi Taufeeq size din Ilham,Kayan Hausawa ne kawai aka siya a Nan Nigeria su Haj Maryam dasu Azeema sune Suka Yi zabi kalar birni,Zeenatu ta Kira Taufeeq akan ya tambayi Amatullah Size dinta na su Bra etc, lokacin Yana Guess House dinsa shi kadai a palo,Ilham tana kitchen tana girki, Fitowa tayi da Dan Bowl dinta ta dafa Indomie zata ci,a kasan carpet ta zauna tana cin abinta,Taufeeq ya kalleta kadan a hankali ya furta Size din Bra dinki fa? Kunya ta kama Ilham ta Kama wani sadda Kai kasa da kyar tace b...bana..Bana sawa Ni,Fuska ya Bata yace ban son Shirmen ki na banza kullum ina ganinta a jikinki Zaki Raina min hankali,Ido Ilham ta zaro tace yaushe ka gani? Harararta yayi yace Ga shatinta Nan a jikinki ta baya ana gani, Kunya ta kamata tace to 36 nake sawa,Baki Bude yace tun kina wannan Yan shekarun kike sa 36? Ilham tace a'a tunda na lefe ne ai maje gaba nasan Zan Kara girma Zan na sa 36 kaga shike Nan Ina da su dama tunda ai Nan gaba ba Haka zasu Yi ta Zama ba, Taufeeq yace Hmmm kina da tabbas Zaki Kara girma kenan? Sosai ma kuwa ai yanzu ni ban cika budurwa ba,sai Nan gaba ku kanku lokacin sai kun koka yanda Zan Zama Big girl,Yanzu fa?Taufeeq ya tambaya, tace kwaila Ce tana zuba Indomie a bakinta,waya ya daga ya Kira Zeenatu,tana dagawa yace 36 take Using, Pant fa da...Kinga Umma Zeena kawai ki kamanta Kamar Azeema ki kwaso kawai kit ya kashe wayarsa.
Ilham tace au har pant akwai size nasa? Ban taba kula ba,banza ya Mata Yana Danna waya,Taci gaba da cewa Pad Kuma gida nawa aka zuba min? Kar a zuba min Kayan jarirai tunda ba Haihuwa zanyi ba, Amma pad afa zuba su da yawa a lefen Nan yanda zanyi ko shekara biyu Bata Kare ba,Kuma kasan ni akwai ta'adinta wacce ka siyo min rannan kaga duk yawanta tashi daya na Karar da Abu ukun du Daya ce tal ta rage a ledar ta karshe,Taufeeq Yana daga kwance Yana Danna waya yace ke kuwa sai kace me jego,Ilham tayi dariya tace lokaci daya guda hudu nake sawa na shiryata gado gado a jikin pant din sai ka ganni Shar Dani bana ko matsala, ban taba ji Ana sawa da pad a lefe ba a duniya tunda nake cewar Taufeeq, daga kaina za'a Fara ai ita ce jigon lefe ma,Hausawa ne basa ganewa Amma tana daga cikin Ilfortan( Important) Abu na rayuwar mace,da kayan jarirai sabo da zamani ya canja ana yin aure wata Tara ake Haihuwa, ance daga kofar daki Amarya kafin ta shiga dakin mijinta take kunsar ciki ta shige ciki da shi, kaga kuwa kayan jariri ma ya kamata a zuba su a lefe.

To Ni dai Kar a sa min na jariri sabo da Inshaallah bazan samu ciki a kofar dakinka ba,Idan watarana na Gama aikina na tafi kaga shike Nan har a bada baza mu sake Haduwa ba.
Suna Haka Su Mujaheed suka shigo da Iv da yawa a hannunsu,Ilham ta Karba tare da karantawa taga nasu ne guda Biyar ta eba kacal tace Daya na Ramcy Daya na Manager guda uku Kuma Zan ajiye Tarihi a wajena,dariya sukayi gaba daya.

Biki Yana ta matsowa Ana ta Shirye Shirye ta ko wanne bangare,Har Dangin Ilham na karya,har kudin gyaran Skin su Taufeeq suka biyawa Ilham Saddeeq Yana kaita Ana gyarata,Tayi wani irin kyau fatarta tana sheki da kamshi, Saura sati daya biki Ramcy da Rabiu manager Suka Isa Jigawa gidan kanin Gomna na karya suna ta shiri Suma,dinkunan da zasu sa gaba Daya su Taufeeq ne suka dinka na Alfarma, Bangaren su Anna da Iyalanta sai abinda aka gani shiri iya shiri Sunyi shi, Su Taufeeq gayyata sukayi ta gaske har kasashen waje,Bangaren Baffa ma haka ya Sha shiri da gayyata,Iv dinsa daban ne shima, Ummi ma Haka Taufeeq ya Gama Mata Dinkuna da komai sai murna takeyi,Ga gidan Taufeeq ya canja komai na ciki etc ya dawo wani fasali daban Na haduwa.
Ilham Dinkuna anyi Mata na musamman,Suma su Taufeeq da frnds haka,Saddeeq yayo hayar Yan Mata masu shegen kyau da gayu wajen su Talatin sune Zasu Zama Frnds din Ilham,an shirya biki,Ramcy itace close Frnd,Rabiu manager Drivern Ilham zai koma.
Biki saura kwana Biyar Taufeeq yace akai lefe Amma su a tsarinsu Mata basa Kai lefe sai maza manya,sabo da Gudun gulmar Mata yasa Maza Dattijai Yan Uwan Baffa aka kaisu Suka Kai Lefe still ba gidan Gomna ba gidan Kaninsa Alhj Suleiman da Haj Rakiya tare da yaransu,sai Karin Manager da Ramcy sai Kuma wasu Yan Matan da manyan Mata su Shida da maza mutum biyar su Suka karbi Lefe aka Gama komai na al'ada sannan Dattijai aka maida su kauye Basu San komai ba,Basu da wayewar da zasu gane.

Taufeeq karya sukayi sukace Ranar da aka daura aure ranar za a kawo Amarya Kuma washe gari sai ayi wedding Dinner shike nan Mata ba sai sunje ba Wanda zasu dakko Amarya kawai za a tafi dasu,Ciki sai ya zabi wasu manyan Mata na kauye Yan uwan su Anna yace da su zasu tafi ranar Daurin Aure.

Dan Kar Danginsa suje da yawa sai Taufeeq ya takalo fada Haka kawai ya dinga fushi Yana masifa,cikin Yaran Anna da jikoki ya Fara gaba dasu ya daina yiwa kowa magana,Taufeeq Yana hakan Haj Zeenatu ta zazzage tas a gidan Anna bayan sun Kira shi gabansu, tace Aysha uwarka mu tun yaushe muka manta da ita,Mene amfaninta a duniya,ran Taufeeq ya baci dama kadan yake jira yace ai sai kuce Nima bakwa so na tunda ita ta Haifa muku Ni har kuke wani daukin zuwa bikina waye waye ai da sai kuce baza kuje ba ku tsame hannuku,ku sani Ummi na tafi min ku sau dubu Kuma wlh Kar Wanda yaje Daurin aurena Cikinku Dangin Baffa na kauye sun Isheni ku ba yan Uwana bane,Baki Suka saki har Anna suna kallon Taufeeq ya Gama zazzaga musu rashin mutunci ya fice abinsa,Anna tace to gaba dayanku yaran cikina da ku jikokina Idan Kuna da zuciya karku je bikin ko me zaiyi yayi daga shi sai Uwar tasa da Ubansa,da kansa zai dawo ya neme mu,ku kyaleshi yayi abinsa,Nan take Anna ta daga waya ta Kira Baffan Taufeeq ta fada Masa irin cin mutuncin da Taufeeq yazo har gida yayi musu harda Karin karya Wai ya zazzagesu ta Uwa ta uba,Nan take Baffa yace tunda ya iya zagin Yan Uwana Nima zai zageni,Nima Banga amfanin zuwa Daurin aurensa ba,ga wakili Nan zan tura Masa da walliyansa su dauro auran su dawo Amma Nima bazan je ba,walliyai suje tunda su ya zaba.
Anna tace to kunji Shima ya fasa ya tura Masa Waliyansa su daura kawai Kuma yace Ummi sai ta Gane kurenta Ana Gama biki da kwana Bakwai zai dawo yaci ubanta,murna su Zeenatu Suka dingayi suna ta zagin Taufeeq da Ummi.

Taufeeq dayaji duk sun fasa zuwa sai Yan uwansu na kauye,ai sai Suka dinga murna suna dariya,Ilham tace Kunga Idea ta tayi kyau ko,Taufeeq Yana murna yace Kinga yanzu babu me kure karyar mu, tunda anbar na kauyen shike nan.
Bikin gidan Radio da Tv Ana ta sanarwa Taufeeq Abdulaziz Rariya da Amatullah kawai ba Sunan Uba Haka ake ta sanarwa,kowa sai yaji Amarya an manta ba a Fadi sunan Ubanta ba, sannan wajen Daurin aure sai akace Babban masallacin juma'a Dake kan titin gidan Gomanti,an kasa Gane Kan bikin Taufeeq,
Ba karamin Gayya Su Taufeeq sukayi ba ga Baffa ma yayi.

Ana saura kwana biyu Daurin aure Driver ya dauki Ilham da kayan da zata saka da Sassafe sai gasu a Jigawa state,Tana zuwa Suka gaisa dasu Hajiya Rakiya,sai Yan mata take gani sunfi Talatin Yan gayun gaske suna sha'aninsu,Ramcy ce ta fito da gudu Suka rungume da Ilham,Ramcy tace shegiya kin ganki kuwa yanda kikayi wani uban kyau da haske sai sheki kike Yi,ga Frnds fa An tanada,Dariya Ilham tayi taje Suka gaisa da kawaye Ana shewa ga Amarya ta iso,Ramcy sama ta ja Ilham Suka fara zuba Hira sai dariya sukeyi suna tafawa,Ramcy tace Ilham ke kam kinyi dace wlh karki Bari ya sake ki,karki sake kwangilar nan ta Kare Allah ya rufa Miki asiri ki kameshi ya fada sonki ya kasa sakinki,Baki Ilham ta tabe tace akan me? Wlh Ni Bai dameni ba ko a jikina ba ruwana kin San fa Halina,watsar da Zancen Ilham tayi tace Ina manager Driver na,Ya shiga Gari nayi nayi ya tafi Dani yace Wai sabuwar Budurwa yayi,Dariya sukayi gaba Daya Sannan Ilham taci abinci ta huta daga bisani ta Fita wajen yan matan suna ta hirar duniya ana shewa.

Sai Dare Ilham suka hadu da Manager ansha hira da labarin duniya tare da harkar gayu,Manager dubu ashirin ya bawa Ilham sababbi na liki Yan dari biyar biyar Wai gudun muwarsa,Ramcy Kuma dubu biyar ta bawa Ilham,Ilham sai godiya da farin ciki dama Bata da kudi.

Ana Gobe Daurin Aure Saloon Suka je dukka kawayen,Amarya wajen da Manager ya kaita daban ita da Ramcy yace ai naku na musamman ne na yan gayu, a Nan aka zana musu Lalle me shegen kyau da Gyaran gashi sai dare Suka dawo gida har kawayen,Ga yan aiki a gidan sai abinda kake so zaka ci su Taufeeq sun Gama shirya karya.

Haka kawayen Nan wani dakin kaga mutum biyar Ana zuba Hira,can aga mutum Bakwai Haka Suka rabu, Ilham da wasu Yan matan Su Samahir,Zeena,Teemah,zee zee,Sakina,Merry,Sady sai Ramcy da Ilham suna ta Hirar su Ana shewa,Taufeeq ya Kira wayar Ilham,Ramcy ce ta daga wayar tare da lankwashe Murya Wai zata tsokaneshi ko ba zai Gane Muryar Ilham ba,tace

Hello Sweetheart,ka kyaleni duk na gaji ga missing naka Ina Yi yau ko nemana bakayi ta furta tana lankwashe Murya Murmushi Taufeeq yayi yace to bawa me wayar wayarta baki canka ba, Dariya Ramcy tayi ta mikawa Ilham,Ilham ba wani iyayi ko wani lankwashe Murya tace Hello ya akayi to? Kaji magana ta gaskiya cewar Taufeeq, gobe 10am Muna Nan zuwa so bayan an daura za ayi pics sabo da su Baffa,ba damuwa Allah ya kaimu,Kaci abinci kuwa? Ina ruwanki da cikina,Muryarka naji ne wani kasa kasa,kitttt ya datse wayarsa ya bar Ilham rike da waya tayi galala.
Frnds suna Ango ya fada Mata kalamai masu zafi jiba yanda ta wani washe Baki to rufe bakin, Ilham dariya tayi ta zugo karya tace hmm maza Basu da kunya Wai gobe Ana daura aure zai Zo nayi Masa Kiss har sai na tabo tantanin makwallaton sa,Heeeeeee Yan Mata Suka saki dariya Banda Ramcy tasan karyar Ilham ce kawai.

Washe Gari ranar Daurin aure wanka ake zubabawa ta ko wanne bangare, masallacin da aka saka tuni mutanen Baffa da su Taufeeq sun cika sun batse, Ilham ba danginta ko Daya sai waliyyanta data zaba su Alhaji Sulaiman, ta Gama shirinta me kwalliya tazo ta sauya Mata kamanni Baki daya Tasha uban kyau cikin wani lace Hadadden gaske Fari da ratsin Sea blue,Duk yan matan Nan sun hade,Taufeeq Babu Danginsa na kusa sai abokansa da Suka san Ilham ba yar Gomna bace sai Wanda ma Basu San komai akai ba,sai walliyansa na kauye da Mata su Hudu na kauyensu dasu kawai Suka taho , masallacin Daurin aure ya cika makil ta ko Ina har waje iya kallonka matasa ne da manyan masu hannu da shuni ne, harda gayyato makada da masu roko etc Wannan aikin su Mujaheed ne,Taufeeq suna zuwa Allah Allah suke a daura kowa ya watse Kar asirinsu ya tonu,Walliya Suka hadu Dana Ilham Dana Taufeeq aka bada sigar Daurin Aure babu jira Na Ilham Suka ce ayi sauri mutane suna da Uzuri, Nan take akayi Khuduba sannan aka bada sanarwar an daura Auren Taufeeq Abdulaziz Rariya da Ilham Abubakar, akan sadaki dubu dari, Nan fa wasu suka ce ai Amatullah ce a Iv, Su Mujaheed suka ce ai a gidansu ake ce Mata Haka shi yasa,Ana ta Kade kade Bayan an daura aka tafi Reception a garin Jigawa an Fara watsewa Baffa yaga Bai kyauta ba Daurin auren dansa guda yabi jirgi sharp sharp sai gashi ya iske har an daura yasha shiga ta Alfarma,suna haduwa da Taufeeq Yace Baffa kazo nasan zaka Zo Baffa na Nan take Taufeeq ya saki kukan karya Yana cewa a daura aurena guda babu Mahaifina Babu yan uwanka da Yayan Yan uwanka sai waliyyai kawai ka Bari Suka Zo Haba Baffa,Rungumeshi Baffa yayi Yana Lallashinsa kamar jariri yace I'm sorry my son,Kaine da laifi baka ji ai gashi nazo to,Taufeeq ya Kama murna Yace muje gidan Kanin Babanta ka ganta ku gaisa,tun dazu Me girma Gomna yake ta jiranka kazo ku gaisa zai wuce Abuja Yana da Meeting Amma ka nuna ni bani da gata,Baffa yace It's ok my son muje ai shi da Kaninsa duk Daya ne,Su Mujaheed suna ta dariya a boye.

Abokan Taufeeq sunfi su ashirin da Baffa tare da Securities dinsa su Mujaheed ansha Shadda,gidan Suka Isa gaba Daya,Yan Matan Amarya ko Ina,Baffa sarkin son Mata sai kallon Yan Mata yakeyi kamar idonsa zai Fado, Kai tsaye Suka shiga Main Palon nan ma duk Yan Matan ne,Hajiya Rakiya tana zaune Taga angwaye harda Baban Ango nan ta mike ta Kira su Alhaji Sulaiman su Hudu manyan maza cikin shiga ta Alfarma Suka karaso Suka gaigaisa Baffa yayi musu godiya sosai, Alhaji Sulaiman ya kirawo wata tsohuwa tukuf Tasha gayu ya nuna ta yace wannan itace Mahaifiyarmu nida Yayana Me girma Gomna,Baffa yace Allah sarki Suka gaisa Yana girmamata, Sai ga Ilham tana sakkowa daga Sama tafi dukkan Matan kyau,tana Hawaye ta fito irin anyi mata aure tana jimamin farin ciki,yan Matan da tsofaffin karya da aka gayyato suna ta Tsokanarta.

Baban Taufeeq Yana ganin Ilham Kirjinsa ya buga dam Nan take yaji ta wani birgeshi,yaji wata muguwar kaunarta da Sha'awarta tana taso masa,dare Daya yaji wani son Ilham Yana ratsa shi,Ido ya kafeta dashi ba ko kyaftawa Kamar shine Angon, gumine ya Fara keto masa jin ance itace matar Taufeeq ta durkusa a gabansa tana gaida shi,Da kyar ya Nemo Hankalinsa ya amsa Mata da sakin fuska Yana Kare Mata kallo,kunya tasa Ilham ta koma bayan Rakiya ta boye,a Nan Baffa ya musu Sallama Securities suna take Masa baya ya tafi Rivers State.
Taufeeq kuwa Allah Allah yake a Gama ya koma shima tunda yasan Baffa gida zai koma wajen Umminsa Kar yaje ya cutar Masa da Umminsa,hankalin Taufeeq Sam Baya jikinsa.

Farar Shadda Taufeeq yasa ya hadu iya haduwa Wanda fadi ma Bata baki ne, ita kanta Ilham Bata taba gani yayi kyau haka ba,Yan matan Amarya Kamar zasu cinyeshi da kallo.
Allah sarki Walliyai Yan kauye sun tafi tuni Taufeeq yasa a maida su ya Basu kudade masu zafi,Matan kuwa da aka zo dasu masu daukan Amarya Allah sarki yan kauye suna daki sun makale sun kasa ko Fitowa an kai musu abinci Iri iri sai Murna sukeyi, Ilham Kuma taje wajensu ta Dade Sunyi Hira sosai sai kaunarta sukeyi ba girman kai duk da irin kudinsu da suke gani, Daya a cikin Matan laraba tace Kai jama'a dama a duniya akwai gida irin wannan? Shawai tace yo ke ba Dole Kika ga gida Haka ba Yar gidan Gomna ce fa ance,cab Dole aga gida Haka,Allah sarki tuni an ninke su musamman da Ilham ta Basu dubu biyar biyar ta sake rufe bakinsu.

Su Mujaheed sai kallon Ilham sukeyi suma yanda tayi kyau abin kallo ce,Masu hotuna da video ne suke ta Haska angwaye da Amarya da Yan Matan Amarya ga Dj ya saki kida Ana ta rawa da Hotuna,Ilham ta fito sai ga Rabiu manager Yana Mata kirari tana ta dariya ta tsaya da me hoto aka daukesu Ramcy Tasha shadda tayi mugun kyau kamar a saceta sai gata ta Fado da sauri tace Haba Amarya an manta da Best frnd ta tsaya Ana ta pics, Mujaheed tunda yazo Suka Saba da Ramcy sosai kamar sun san Juna anyi hotuna har an gaji, Saddeeq yace Amarya da Ango fa Kala Daya akayi musu kacal gaskiya bamu yarda ba,Taufeeq hankalinsa Yana wajen Umminsa, Haka Ramcy ta jawo Ilham kusa da Taufeeq,Ilham ta saci kallonsa kadan duk hankalinsa baya jikinsa a hankali Ilham ta Kara bakinta a kunnensa tana tambayarsa a hankali meke faruwa ne?
Sai masu pics da Video Suka shiga dauka kyaras kyas, Shima Taufeeq rada mata yayi Ummina...Ummina...Nan ma aka ta dauka,sai Kuma Ilham ta dage kafafu sannan hannunta ya iya kaiwa kafadarsa ta dafa shi,dariya aka dinga Yi Har Taufeeq yanda ta dage kafafu sosai.
Sun Dade sannan Taufeeq ya tafi ya bar Su Mujaheed zasu taho a Suma tare da Amarya.

Zuwa Yamma aka tafi da Amarya da lefe da sauran kayanta da tazo dashi da Yan Uwan Baffa da wasu Kawayen,Rabiu tuni yayi musu sallama ya tafi Kano, Sauran mazan Dattijai yan Kwangila duk an sallamesu da kudade masu yawa sun tafi Suna murna haka Yan aiki ma,Wanda Suka rage kawayen Amarya Hajiya Rakiya da yaranta sai Dattijai su Biyar a matsayin Dangin Amarya dasu aka tafi Rivers State Kai Amarya.



Ayi hakuri da wannan.






An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya

Please Login or Register in order to submit comment