Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da dariya yace Allah sarki ai Muna tare da mutanena nifa yanzu jinsu nake kamar Yan Uwana na jini,mun rigada mun shaku.

Tsawa Iya ta daka Masa Kai Dan Ubanka ka daina cewa kun shaku wannan badala ce,Dariya Suka Yi gaba Daya Suka maida Iya wata shashasha, Rabiu ya zubo karyarsa Daya saba yace Ni da nake so na Gina Mana gida a Abuja mu koma gaba Daya dasu Golden girl Amma Iya sai yawa kike Yi.
Ilham tayi tafi tace ai jiya in fada maka nayi mafarkinmu a wani katon gida gaba Daya Muna tare,Da sauri Rabiu yace gida na Kika gani to ai gida nane, kin ga Office Dina ko a mafarkin? Ramcy tace wannan nice nayi mafarkinsa Wai naje da jakata na Zama Yar gayu kana saman Kujera tana juyaka kawai kudi kake Irgawa fal fal fal, cikin jin Dadi Suka Yi tafi gaba Daya Ana murna,Ilham tace Allah ya baka Manager,Manager Alhaji Rabiu zubata ka tashi na Amiru watande ikon Allah, kaji dadinka kayi banza da ranka mun ga gidanka da Office dinka,Iya akwai shanawa nan gaba,Rabiu ya Mika musu Hannu Suka tafa,Iya da sauri ta rufe idonta Wai kunya baza ta iya gani ba.

Ilham tace wancen satin Har mafarkin motarka nayi Manager, Dan manzon Allah? Rabiu ya tambaya,Ramcy tace ai Ilham ta bani labarin motar taka kala Uku ta gani akwai baka wuluk ,akwai ja dau sai wata Fara Kal malam ka fito cikin Kaya farare kaima na gayu,Rabiu ya saki Ihu tare da Mikewa tsaye ya shiga cashewa Yana takawa sosai Kamar Ana shooting film suna Masa Waka da Baki da tafi, Iya ta dinga dariya Dadi yasa Iya tace na fasa korar ku kuci gaba da zamanku Kamar gidan Babanku sai abinda kuke so,Kuna sani Nishadi jikokina,da nayi niyyar korarku Amma na fasa Dan uban mutanen sun Dade Basu Yi munafunci ba, Zanku Rabiu yaci gaba da takawa Yana girgiza,a wayarsa Ramcy ta Danna Masa wakar Zlatan,Yana gamawa Yace Ramcy Yi Taki mu gani kin iya,Ramcy ta mike ta cashe ta Iya sosai,Sai Ilham itama tace Ni da Baki zanyi wakata bana son wakar wani,Nan Iya tace a kashe Mata wakar to Muji tata,.

Ilham ta Fara cashewa tana wakarta
Zu..zu..zu...Zubairu
Antyty...Ant...Anty
Makiraaaaaa
Ta hada da kidan bakinta sai ta dinga rawarta,Iya harda tafa mata.
Ranar da yamma Manager ya siyo musu waya karama me memory wacce zasu iya kallo da jin kida ya Sa musu layi ya Basu,wayar ma sai da aka Yi Mata rawar murna anyi waya.
Zamansu suke lafiya cike da nishadi,Basu Zama fetsararru ba sai da Suka shigo birni,sun Kara gogewa baza kace su Ilham bane.

Bayan kwanaki Masu zuga Suka yiwa Iya yawa,har Yan Uwan Rabiu Suka ce Basu Yarda ba Sam,zugar da tayi tasiri Sosai wajen Iya, wannan Dalilin yasa ta Kira su Ramcy Babu kwayar fara'a a Fuskarta lokacin Rabiu ya tafi unguwa da yamma tace ku dauko kayanku ku bar min gida,Ina sonku Kuma naji Dadin Zama daku Amma ban Amince tarayyarku da jikana ba,ku tattara ku koma gidan ubanku, Ilham tace Iya kiyi hakuri idan laifi Muka Yi Miki wallahi mun tuba baza mu sake ba,Baku Yi min komai ba kawai ku tafi tun kafin na Kira muku hukuma,Ilham tace Haba Iya to ki Bari mu samu wajen Zama sai mu koma,wlh Baku Isa ba a yanzu Zaku kwashe kayanku ku tafi.
Ramcy tace Haba....Baki Ilham ta rufewa Ramcy tace ya Isa Allah ne ya hadamu da Rabiu ba tare da mun sani ba,muje Allah ne ya kawo karshen zamanmu,sannan Allah zai hada mu da wasu muje kawai, Tausayinsu ya cika zuciyar Iya tace kuyi hakuri wlh Ina sonku ko Dan Addininku duk shirmenku bakwa Wasa da Sallah ga Azhkar, Ba komai Iya Muma Muna sonki cewar Ramcy,kayansu suka kwaso tas Suka shirya komai, Suka canja Kaya jikinsu zuwa atamfa riga da skert Suka sa Hijab,sun fito suka ce to Iya ki gaishe Mana da manager kice duk sanda muka samu dama zamu Zo mu gaishe shi,Kar ya damu.
Iya tace ko Zaku zauna ya dawo kuyi sallama,Kai Ilham ta girgiza tare da goge hawayenta tace Iya idan naga manager zanyi kuka Sosai na Saba dashi shima ya Saba damu zai Hana mu tafiya tana fadin Haka ta saki kukan rabuwa da Manager dinsu,Ramcy ma tana shesheka tace Allah sarki na tuna sanda muke haduwa da abokan aikinmu masu bada mai da manager muyi ta Hira ana dariya,Manager yayi ta zubo karya,Ilham tana shesheka tace na tuna sanda kullum Yake siyo Mana Dan tsiren Nan me yaji ,Ramcy tace da Madara me sanyi, Iya tace Iyeeeee kaji munafuki Amma Ni ko tantani baya siyo min sai ku Yan Mata zai ci ubansa zaizo gidan Nan ya same ni Allah ya tona asirinsa.

Ilham tace to har kwai a cikin kwai yake siyo Mana,Iya tana salati tace daga jin sunansa zaiyi Dadi kwai cikin kwai,Ramcy ta goge guntun hawayenta tace kin tuna dazu Kamar yasan zamu bar gidan Nan ya rungumeki Nima ya rungumeni,Iya tace Allah ya taimakeni Dana Kore ku dama abinda kukeyi kenan ku fice ku bani waje,ta mike tare da dakko sandarta ta biyo su Ilham da ita,Amma Ilham sai da ta tsaya ta rike kugu tayi fari da Ido tana tafi,Iya tace kuje can wajen danginku kuyi a gabansu,Iya aini na shaki Hayakin Wiwi yafi Sau dubu,Dana zauna wajen dan Uwa na gwara na zauna wajen masu shan Wiwi su fesa min hayakinta, Dariya Ramcy tayi tace yeer ayyiriri Nanaye Iya ta jefe su da sandar sai lokacin Suka dauki Ghana must go Suka fice.
Napep Suka shiga Ramcy tace to yanzu Ilham Ina zamu tafi? Iya wuya baza mu bar birni ba mu koma Kaduna state sai mu nemi aiki a Gidan masu kudi.

Haka kuwa aka kaisu Tasha cikin kudinsu da Suka samu Suka biya kudin mota zuwa Kd,Sai 4pm suka Isa Kaduna,a tashar suka Yi Sallah tare da cin Abinci sannan Suka ja jakarsu Suka fito tare da shiga Gari,gidajen Masu kudi Suka fara shiga suna tambayar aikin Wanke wanke da shara etc.
Har dare yayi Basu samu ba,a jikin wata bishiya suka zauna suna hutawa,Ramcy duk ta Fita Daga hayyacinta kasancewar ita Bata Saba da wahala ba ko a kauyensu yar gata ce, Ramcy ta fashe da kukan wahala ga Hadari ya Hado Taga Ilham ko a jikinta,tace ni gidan iyayena Zan koma gaskiya bazan iya ba,Dariya Ilham ta dingayi tace a dawo lfy ta dauke Jakarta ta kaita jikin wani gida inda ruwa bazai taba su ba,Ramcy tace to Ni baza ki Kai min jakata ba Ilham? Ilham tace nawa Zaki biya? Ba wani Maganar tausayi malama ki tashi ki San duniya Kika shigo, Ramcy taja kwafa ta mike ta dauki kayanta itama ta Kai can ta ajiye,Ta dawo tace to na Kai sai ki mutu Yar bakin ciki banza jaka,Ilham tace gaki Nan bakar akuya Tinkiya, Suna zage zage ruwa ya tsuge ya Fara dukansu lokacin Kuma fada Sosai ya barke a tsakaninsu Suka rukuma kokawa ga ruwa Yana casa su Amma kokawa suke sosai, Ilham ta dauki Ramcy ta dagata sama zata saketa a kasa sai ta fasa ta sauketa a hankali tun suna zage zage da Hararar juna har suka hakura ga dukan ruwa sun Sha.

A inda Suka ajiye kayansu a Nan suka koma Suka tsuguna, sai cikin dare wani tsohon Dattijo yazo wucewa a kekensa ya tsaya a wajensu tare da haska su da touchlight,hango su yayi a takure sun kankame junansu sabo da Sanyin da suke ji,Dattijon yace Kai Yara lafiya? A hankali Ilham tayi magana cikin muryarta wacce daga ji kasan mura ta Mata mugun kamu tace lfy Baki ne mu,almajiranta aka kaimu shine Muka gudu,Dattijon yayi Murmushi tare da Furta haba yarinya sake magana Amma ace Mata da almajiranta a Ina Kika taba gani? Da Allah ku dinga fadar gaskiya ko zaku samu masu taimaka muku, Ramcy ce ta karbe zancen tace wlh Baba yanzu dai dai ku suna Almajiranta Mata da maza ka tambaya kaji,Allah ya kyauta tunda nayi Niyyar taimaka muku kuzo muje gidana Amma kwana Daya kacal zuwa gobe zan kaiku gidan Wata Mata Uwani ita naji Tace tana bukatar masu kular Mata da gidan gonarta na kaji tana son daukan Mata ma'aikata zata Kara tare da mazan,Baki Ilham ta washe tace kaji inda Muka Fi kauri ai Baba anzo bangarena tun a kauye na iya kiwo Iri iri za a Sha mamaki na kuwa.

Baba dai Bai ce komai ba yana gaba Yana tura kekensa suna bayansa da kayansu Babu nisa da gidan nasa na talaka me rufin Asiri,Jin sallamarsa Matarsa ta Fito tana Masa sannu da zuwa,yace yawwa Talatu ga Yara Nan zasu kwana zuwa gobe zan kaisu gidan Hajiya uwani zasu Yi Mata aiki,wacce aka Kira da Talatu me kirki su Ilham ta Kai wani daki yasha gyara da Tsafta,Ruwan wanka me zafi ta hada musu Suka Yi wanka tare da canja kayan jikinsu Suka shanya Wanda Suka jike,ko da Talatu ta kawo musu tuwo Haka Suka Fara ci suna yabon halin Talatu da Baba,Ramcy a hankali ta radawa Ilham kaga tsofaffi da iya soyayya ga mutunci,Ilham ma ta karkata ta radawa Ramcy tace wlh kuwa ga Iya girki kinji miya Kamar ansa zabo,au dama ba Nama? Ramcy ta tambaya da sigar rada,Ilham tace hmm ai tsabar iya girki ne,ga gidan ko Ina kamshi, dariya sukayi kasa kasa tare da tafawa,Ilham tace har fari naga tana yiwa Baba,harda cire masa babbar Riga cewar Ramcy itama,Heeee Suka Yi shewa kasa kasa yanda baza a ji su ba.
Bayan sun Gama Hannu da Baki Suka wanke sannan Suka kwanta bacci me Dadi ya kwashe su.

Washe Gari Haka sukayi Kari me kyau tare da wanka Suka saka lace dinsu iri Daya da Rabiu ya dinka musu, bayan sun Gama komai Baba ya tasa keyarsu da kayansu bayan sun yiwa Talatu sallama,Gidan Hajiya Uwani ya kaisu gidane Hadadde na masu kudi ba sai an fada maka ba,Ramcy tana shiga ta faki idon Baba tayi rawar Michael Jackson data fara koya wajen Rabiu,a kunne ta radawa Ilham da tuni ansha Ni basilla na tafi kauye, Na gode kawata da Kika hanani tafiya, Ilham tace ban taba shiga Gida irin wannan ba,Nima Ina fakar idon Baba zan cashe.

Cikin katafaren Palon Uwani Suka Shiga wani Kamshi da sanyi ya bigi Hancinsu,Ilham taja munsharinta data saba na shinshinar kamshi kwarrrrrr Baba ya kalle ta da sauri sai yaga ta fuske kamar ba ita tayi ba,sai ya Rasa a Ina aka Yi abin, ku zauna Bari na sa a Kira Hajiya,Ficewa Baba yayi,Nan take Ilham take Bari na bada hakkin rawa, nan ta Fara takawa harda girgiza da kafada da kirji,Ramcy tace baza a Barni a baya ba, ta mike suna ta Yi iri Daya ba banbanci, Motsi Suka ji da sauri Suka zauna kamar ba su ba,Baba ne ya dawo ya kallesu yanda Suka nutsu,yace wlh hankalinku da nutsuwarku yasa zan taimaka muku, mun gode Suka furta.

Hajiya ce ta sakko daga sama sanye cikin Wani Lace me tsada Tasha kwalliya ga uban gashin atach ta Sha,Zama tayi su Ilham suka gaida ta,amsawa tayi da fara'a tace Baba sune masu aikin,Kuma zasu iya a gidan gonar? Ilham tace Ni dama aiki na ne kiwo, Murmushi Hajiya tayi tace a Nan zaku dinga kwana kullum da safe zaku je gidan gonar ku dawo 5pm akwai maza ma'aikata Ina so ne kawai na Kara da Mata Sabo da sun Dan Fi Amana,Idan gaba Naga aiki na kyau ba abin mamaki bane na kaiku kasar waje Neman kudi ku dogara da kanku yanda danginku zasu Yi Alfahari daku.
Gama Fadar Haka da Hajiya tayi Ilham da Ramcy Suka kalli juna da sauri.

Kudi Hajiya ta bawa Baba tayi masa Godiya tare da sallamarsa ya tafi, dakinsu Hajiya ta nuna musu Hadadde,aka kawo musu abinci bayan sun koshi Zama Suka Yi suna ta Hira suna jira gobe tayi suga gidan gonar da ake ta wani yabon girmana.
Hajiya kuwa ganin irin Kyawun Ilham tace wannan ai tafi karfin aiki a Gidan gona, itama dayar tana da kyau,amfaninsu nayi musu Visa nan gaba na tura su Egift su Nemo min kudi a bariki kawai Amma sai Nan gaba idan sun Saba Dani yanda duk abinda nace zasu yarda.

Rabiu Manager tunda ya dawo ya Iske Babu su Ilham ya tambaya Iya tace ta Kore su,Kuka kawai ya saki da gudu ya fada motarsa ya dinga duba Inda su Ilham dinsa suka tafi Amma Bai gansu ba har ya gaji ya dawo gida kwana yayi Yana Bakin ciki ko aiki Bai fita ba Ranar.

Anty Halima kuwa da Zubairu Rocket bashin kudin mota Suka ci zuwa Kano zasu tafi da Ilham taci gaba da wahala a kansu tana ciyar dasu .
Da Sassafe Suka sauka a gidan Malam.
Bayan an Kira malam sun gaisa Zubairu yace Ilham Muka Zo tafiya da ita gafarta malam aure za ayi Mata.
Malam ya kallesu yace to Yara dai sun gudu,Ni da ta kusa hallaka mu,Sam Baku iya tarbiya ba Kun kyankyashe jaraba duk Almajirai na wannan Ilham sai da ta tarwatsa min su yanzu duk kusan Matan sun arce saura Bai Fi biyu ba Suka rage,Ni ban San inda sukayi ba,Rannan dai na gansu a wani gidan Mai suna aiki,kuzo muje na rakaku ko zaku Dace.

Salati Anty ta saki tace muje Malam Dan ya rasulillahi ka taimake mu,a motar malam Suka je gidan Man Amiru watande Babu su Ilham,Wani cikin Maaikatan shi ya rakasu gidan Su Manager,Allah yasa manager yasan labarin Ilham kallon banza yabi su Anty dashi yace basa Nan sun tafi gida, ko fuska Basu samu ba Dole Suka hakura tare da komawa kauye cike da bacin Rai.
Haka Malam ya Kira Iyayen Ramcy ya sanar musu ta bace, hankalinsu ya tashi musamman Kakarta da ta taso a hannunta,Nan fa Suka shiga neman Ramcy Ido rufe Amma ba a ganta ba.







AsmaBaffa
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰








NA KUDI NE







16-20







'YAR KWANGILA IS
DEDICATED TO ME
DARAJA
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.








Official







By


AsmaBaffa








RASHIN SA'A COMPLT
TA GYARU CMPLT
Dari uku ne 300

'YAR KWANGILA
Dari biyu ne 200 ga me so a sata a group.


Masu bukatar siye ga hanya..

Accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, Zenith Bank.

Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
0903240966.

Wanda zasu tura katin waya Mtn ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number ga masu siye.
+227 90 79 59 39.





Page naki ne ke Daya
Mrs A
Allah ya bar kauna.









Iyayen Ramcy Addua Suka dukufa Yi kullum ba dare ba Rana Allah ya bayyana ta.
Allah sarki Su Ilham washe Gari Hajiya Uwani da kanta ta sasu a motarta ta kaisu har katon gidan gonar ta na kiwon kaji maza ne ma'aikata a ko ina, sai kallon su mazan keyi musamman Ilham,Kudin Napep Hajiya ta Basu tace gashi ga Adrees na gidan a wannan paper karku manta,ku kula da masu aikin sabo da suna cucutata,Ok an Gama Hajiya cewar Ilham.
Tunda Hajiya ta tafi Suka karasa wajen mazan Suka gaisa da kowa suna duba kajin, Ilham ce tayi wa Ramcy Rada tace gobe sabuwar gas cooker zamu siyo karama da tukunya kullum sai munci kaza,da ragowar kudin mu zamu siyo komai,Ramcy tace Ashe kin Gane.
Ilham ta Iya kiwo sosai ta tsaya tayi aikin ba abin da yasha kanta,mazan gaba Daya har Kar manage sukeyi basa ciyar da kajin yanda ya kamata sai da Ilham ta gyara musu.

Basu tashi ba sai karfe biyar lokacin sun Saba da mazan ciki,Ramcy ce tace Kar mu shiga Napep yanzu mu tafi a hankali muga garin kd,a hankali suke tafiya suna Hira kowaccensu sanye da Hijab Kato har kasa,wata Unguwa Suka Zo ta talakawa sosai wasu motoci Suka hango a kalla zasu Kai guda Bakwai gaba Daya matakan tsaro ne a ciki,guda Daya motar tana tsakiya me arnen kyau da tsada,Ga wasu Mota Kuma Kurkura sun Kai guda goma shake da kayan abinci guards suna rabawa talakawa kyauta na taimako.

Ilham tace muje muga wanne Dan Iyayi ne yake gadara da kudi Yana rabo? Haka muke ratsa cikin talakawan ,Ramcy tace wani Dattijo ne maybe ya Tara kudi yaje tallafi ko zakka.

A hankali Suka karasa wajen su kawai kokari suke suga waye a shegiyar motar tsakiya,Ilham tana sani ta zagi wani cikin securities tace talakawa ku dakawa abincin wawa Dan uban me kudin, Kurkura Daya ta Kama ta hau saman kayan abincin tana musu abu Kamar Yar jagaliya, ta dakko carton din Taliya tace Ramcy Cafe ta wullowa Ramcy ta cafe,Magana suke da karfi duk sun Hana kowa magana, motar me kyan gaske wacce Ogansu ke ciki Suka kwankasa ya sauke bakin Tint glass dinsa, securities ne suka fada Masa oga zamu dau mataki akan Waccen yarinyar,Kansa ya daga sama ya hango Ilham a saman mota ta rike kugu tana ta rashin kunya, Ramcy ce ta kwala Mata Kira Golden girl ya sauke glass Ashe Bature ne ko balarabe kalle shi, juyowa Ilham tayi da sauri Karaf suka hada ido da Taufeeq,Mamaki ya Kama Taufeeq ko Aljanna ce duk State din Daya je sai ya ganta,Itama Ilham tace Kamar Aljani a ranta a fili kuwa Hannu ta daga masa tana washe Baki,tace ashe ma Kaine buhu nawa zan dauka nawa? A matsayi na na kawarka? Baki ya tabe yace da security din a Bata ta tafi, Security yace to yace ki dauki abinda Kike so, Ilham tace bana bukata a karkashin wasu nake Ana ciyar Dani Alhmdllh,dama zuwa nayi Naga waye,tana fadar haka ta sauka a saman motar Suka tafi.

Ramcy kuwa sai zagin Ilham takeyi Bata dakko musu sun siyar sun samu kudi ba.
Ilham tace ke banza ce baki da wadatar zuci me zamuyi da ita Hajiya Uwani tana bamu abinda muke so gashi zamu Fara cin kajin gidan gona kullum, Harshe Ramcy ta zaro tace Shuuuuuu Dadi zamu sharbi Dadi,Dariya sukayi Ilham tace Kinji wani sabon Turanci da na ji a gidan kaji, ai Kd gaskiya akwai turanci,Ramcy tace kinji Ashe kema Wai muje mu Duba layin Fruits,Dariya sukayi Wai Ashe Kayan marmari ne Fruits Kinga Idan aka cika Sha da yawa Sai Zawo sai ka shiga Toilet kana Kwaratsatsi kawai Ana jinka a toilet wani Frut ai Bature ya iya sa suna ya Dace.
Suna ta Hira har suka gaji da tafiya sannan Suka Shiga Napep zuwa gida.

Suna Isa gida Hajiya Uwani sai fara'ar Dole takeyi tana wani lallaba su,zatonsu da gaske kaunarsu take Yi tsaka Ni da Allah, wannan Bai Hana su Ilham Siyen karamar gas ba Yar 7k da tukunya harda su Maggi da gishiri sai kayan Miya da wuka.
Gidan kaji suka Kai ba tare Hajiya Uwani ta sani ba, Sauran ma'aikatan kuwa Sunyi zaton da sanin Hajiya Uwani tunda Yanzu su Ilham sune masu kula da gidan gonar.
2pm yunwa tana damun su Ilham,Suka duba lafiyayyar kaza a ciki Suka dakko ta, Ramcy tasa kan kaza gabas da Bismillah ta yanka kaza,ruwan zafi Suka tafasa a ciki Suka saka yankakkar kazar Suka figeta tas sannan Suka fede ta Suka gyara komai har Hanjin Basu Bari ba sai da Suka tatse shi, a pampon bangaren fruits suka wanke Naman sannan suka yanka mata Attaruhu da tattasai,Albasa da Dan ruwa,Suka Fara girki kamshi Yana tashi sannan Suka sa Maggi da gishiri,lokaci Kankani ta dahu ligif Suka Yi farfesunsu, sai da Suka koshi sannan Suka bawa sauran ma'aikatan Suka raba,Haka Fruits ma abinda suke so suke Sha.
Tun daga Wannan Rana Kuma kullum sai su kamo kaza lafiyayya suce Bata da lafiya mutuwa zata Yi su yankata,ko Kuma su ebi kwai su dafa suci ko su soya aikin su kenan kullum idan Kuma sun koma gida sai su fadawa Hajiya sun yanka kaza marar lafiya sun gasa ta,Hajiya Bata cewa komai sai tace ba komai ai kuci kullum.

Hajiya Uwani ce ta Kira Su Ilham,a palonta Suka Iske ta,Hajiya gamu Ramcy ta Furta,Hajiya tayi Murmushi na munafunci tace ba komai bane yasa na Kira ku sai Dan na yaba da hankalinku gaku kyawawa daku abin mamakin yanda kuka iya kwalliya Kamar ba Yan kauye ba,wannan yasa na yanke Hukunci Zan fitar daku kasar waje Dubai kuje can ku Nemo Mana kudi muji dadin Duniya ko bakwa so ku Zama Attajirai,Muna so Mana suka hada baki wajen furtawa,Yawwa to zan muku E passport da visa Zan turaku wajen Wata kawata a can Dubai ita zata koya muku Neman kudin,Hajiya a ranta tana dariya Tace kwana Nan Zaku Zama Karuwai a Dubai,Karuwanci take son turasu suna Bata nata kason, su Ilham Basu gane ba sai godiya sukeyi da murna Nan take Suka Amince.

A gaban Hajiyar Suka fara rawar kasar waje suna dariya har Hajiya,Hajiya a ranta tace Zaku yi bayani tunaninku banza ta fadi Kun bi Kun cinye min kaji Ina da labarin komai.
Cikin sati daya aka yiwa su Ilham passport da Kuma Kai passport din Lagos za ayo musu Visa.
Hajiya harda Kara dinka musu Kaya Hausawa kala uku uku masu kyau da Kuma kana Nan Kaya Suma kala uku.

Bayan sati Biyu Aka kawo passport din su Ilham dauke da visar Dubai, Ticket ta siya musu Ranar Saturday da kanta ta shirya su kowacce cikin riga da wando matsatsu da Dan mayafi,Ilham tace Hijab dinfa Haka zamu Fita Ana kallonmu ba mutunci? Ba wani Abu yan kauye wannan shi ake yayi, Kayan Ramcy pupple ita Kuma Ilham farare da blue sunsha kyau,gashi yaci gyara na gaske, Hajiya da wani ta hada su zai tafi dasu Dubai, da kanta a motarta ta kaisu Airport, Ana Gama musu screening da safe jirginsu ya daga zuwa kasar Dubai,burin Hajiya Uwani ya cika a Kan su Ilham dama ta tura wasu yaran Amma Daga baya da Suka waye sai Suka daina Bata percentage nata.

Masu aiki Sababbi sun Kai su Biyar Taufeeq ya sake kawowa Umminsa tare da Yi musu zazzafan warning akan duk abinda ya samu Umminsa Idan ya dawo daga tafiya to tabbas sai ya dauki mataki, yau Sunday ya fito cikin wata arniyar Jallabiya Fitted Fara Kal ka rantse balarabe ne sak Bai hada jinsi da Dan Nja ba,Karamar Trolley dinsa Yana ja a hannunsa,Palon Ummi ya shigo Sumar Nan me yawa taci uban gyara,Ummi tana saman kujerarta zaa kaita Garden ta shakata, yazo da sauri tana tare da Durkusawa a gabanta ya sauke gwiwoyinsa a kasa tare da daura kansa a saman Cinyarta,Murmushi ta saki tare da shafa gashin kansa, Biro ta Mika Masa da Littafinta ya karba Yana kallon Umminsa ya rubuta Mata Kamar Haka
Ummina zan wuce
1wk zanyi Inshaallah
Zan dawo, ki kular
Min da kanki,Ina
Sonki Ummina.
Tana karantawa itama ta rubuta Masa amsa
A dawo lafiya,Allah


Please Login or Register in order to submit comment