Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uku ne gwada mu gani Sunyi miki dai dai idan basuyi ba a mayar a canja wasu.
Ilham tana murna tace Amma na gode Allah ya biya,Taufeeq ne yace Amma dai ba a kudina kuka sake eba ba,Kuna min fa ta'adin kudi akan wannan yarinyar,Jiya Haka kuka Bata har dubu dari uku ta bawa su Anna a banza,Wai buga kudin nakeyi,ku baza ku bayar a naku ba, Mj yace to ba so ake a samu Nasara ba,Ilham tace kyaleshi Ranar biyan bukata rai ba A bakin komai yake ba, to wannan dai ba Kudin ka bane Tall man ne ya siyo Mata da kudinsa,Better cewar Taufeeq.
Whot Mj ya dauko sabuwa yace kuzo mu Yi Dan cinye ku.

Dariya sukayi sabo da sun San Bai iya ba cinye shi akeyi.
Ilham kuwa tuni ta shige Bedroom zata gwada Kaya, dogayen riguna ne masu kyau da tsada, Daya ta Fara gwadawa wata peach color, ba karamin kyau tayi ba kamar an gwadata, suna ta game dinsu Ilham ta fito ta tsaya a tsakiyar Palon Kamar me sarauniyar kyau tace Mj ya kuka gani,Har Taufeeq sai da ya kalla kadan,tayi kyau sosai Hannu tasa ta rike kugu Babu magana ta koma daki mintuna kadan ta canja wasu kayan ta fito Mj da Saddeeq suka ce Wow kin fa hadu, juyawa ta sake Yi ta sako baka ta karshe ta Fito ta zauna.
Mj Yana cewa sai kace wata balarabiya,Abincin ta bude Fried rice with chicken taci ta koshi ta maida sauran kitchen,Nima zanyi Whot din,hmm zafa a cinyeki har kiyi Mana kuka,Ilham tace Allah na iya sosai wajen su Hamza na koya.

Rabawa Suka sakeyi da ita,Taufeeq yace dawo gabana yanda Zan dura Miki Kaya sai kinyi kuka yau,Fara Yi sukayi da Ilham ba a dade ba Suka fara raina kansu,sai Suka ga ai su Basu iya bama,Ilham duk Yi ita ke cinyewa.
Tambayarta Saddeeq yayi Wai a Ina Kika koya har Kika iya Haka? wajen su Hamza Aji garau frnds Dina na kauye,aikinsu kenan Whot Kuma kusan ko yaushe da Ni akeyi.
Basu tafi ba sai dare,Ilham tayi bacci abinta.

Kwanan Ilham uku Saddeeq ya dakko Mata kayanta dake gidan Yar uwarsa ya dauketa a mota tare da Maidata gidan Anna,Nesa da gidan ya ajiyeta ta Karasa gidan da kafa.
Anna data ga ta dawo ko a jikinta ko Yar fara'a Babu,Bakin da Suka Zo yaran Anna da jikokinta tambaya suke wace wannan Kyakyawa da ita? Anna ta tabe baki tace Yar aiki ce marar daraja daga kauye,Tunda Suka ji ance Yar aiki ce suka Bata fuska ko wacce ta shiga jan tsaki,Azeema Baki ta tabe tace tashi ki bawa mutane waje anji kin dawo Yar wahala.
Ilham ta mike zumbur tayi waje abinta, Su Hannatu suna ganin Ilham ta dawo Suka tareta da fara'a suna cewa barka da zuwa Golden Girl.
Ilham tana dariya tace yawwa ya aiki? Suka ce lfy,Hannatu tace ammafa anyi ba ke an barki a baya, me ya faru Ilham ta tambaya, Taufeeq ya kawo matar da zai Aura,In fada Miki Kinga kuwa kyanta da haduwarta,Kowa sai da ya koka,wannan duk yanda akayi jinsin larabawa ce ko India,Kuna yanayi da ita Ilham Amma ta take ki a kyau da komai, ga Naira,Baki ga Soyayyar da suke zubawa da Taufeeq ba abin kallo,ke Kinga Taufeeq yanda ya zauce a kanta.

Ilham tayi dariya tace wayyo kallo ya barni,ya sunanta? Suna me Dadi Amatullah sunanta,Kai Allah ya bamu arziki,kudi Sunyi Yar Gomna ce,Ilham tace kice Babbar harka ce? Hannatu tace kudi ta bawa su Anna da yawa ga laces da Atamfofi masu tsadar gaske Baki gani ba wajen kala goma aka ce,Hajiya Maryam ta zaba,Haj Zeenatu Haka da masifaffiyar Nan Haj Asmau,ke Kinga yanda suka dinga ji da ita sunga yar Gomna,Har yanzu kullum sai anyi zancen Amatullah Ana fadin kirki da hankalinta,kin San su hankalinki kudinki,Ilham ke Kinga irin takun da takeyi na Isa da gadara, da gani gaba Daya a Turai tayi rayuwa,lokacin ma Wai sauri takeyi zata tafi Germany ko Ina oho dai.
Ilham a ranta tana ta dariya tace kice ya iya zabe hmm ke dai idan Ana Sallah ba a magana ta tafi da Imanin kowa,duk Iyayin Taufeeq sai gashi girman kai Babu an zage Ana nuna kauna.
Ilham tace wai duk girman kan Taufeeq Ina ya kai shi? Cab anga me zafi ya sauke shi tuni, ai kin dawo Zaki dinga Jin labarin Amatullah kullum a gidan Nan yar Gomnan Jigawa state ce.
Ilham tace ai ko Ina son Taufeeq Zan dage kafin Yar Gomna ta aure shi ya aure Ni ko Kuma ya Kara ta biyu da Ni.

Baki Hannatu ta bude tace Baki da hankali me Taufeeq zai ci Dake kina Yar talaka,ke ki tsaya kiji ki daina daukan kanki wata Dan Ana cewa kina da kyau baki Kama kafar Amatullah ba, Ilham Tace ki daina ja da ikon Allah,ai Wallahi Taufeeq bazai aureki ba me zai ci Dake,ko da Wasa su Anna baza su Bari ba kinji na rantse idan kin auri Taufeeq na Mutu kuli kuli wallah kinji na rantse ma Kuma indai kin aureshi to zanyi azumin kaffara na yarda, Dariya Ilham kawai tayi tace to shike Nan ai Allah ya nuna Mana lokacin,Ameen cewar Hannatu tana farrr da ido ita me gaskiya.

Yara maza na Zeenatu,Maryam da Asmau su Ahmad,Fauzan,Fuad,da Jabeer tunda Suka ga Ilham suke gulmar kyanta,Fauzan yace kyan yarinyar Nan gidan kudi da Naira,Ahmad yace ai Ni duk kyan yarinya matukar Yar gidan Malam Shehu ce to ba abinda ya hadani da ita,Kai nifa duk wacce Bata fito daga gidan Naira ba irin Amatullah ta Taufeeq to wlh bazan aurenta ba ko Mai kyanta ,Amma duk munin mace aka ce Yar wani ce to Ina sonta,Fuad yace ko Frnds bani da talaka Kayan wahala komai a taimakesu da kaza kaza.

Bayan Kwana biyar Ana shirye shiryen tura manyan Taufeeq Neman auren Ilham wato Amatullah Yar Gomna,Mujaheed ya Kira Ilham wacce mararta ke ciwo Sama sama Bata San dalili ba Tunda Bata Fara period ba,Ilham ta boye tare da daga wayar yace fito anjima 4pm zan daukeki akwai Wani plan da zamu shirya a Guess House na Taufeeq yana can Yana jiran mu.
Ilham tace to sai na fito.

3:30pm ta shiga Part din Anna lokacin ba kowa daga Anna sai Haj Zeenatu, Durkusawa tayi ta gaishe su,Zeenatu ta daka Mata tsawa ke Dalla matsa daga kusa Dani ku yan kauye Baku da aiki sai Gaishe gaishe na banza,Mene Anna ta tambaya da Hantara,Ilham ta matsa can nesa tace dama maganin Ciwon ciki Zan siyo, Haka aka iya Allah dai yasa ba karuwanci ake Fita Yi ba, Sai kin dawo iya kaci idan kinyi ciki na kai ki kauyenku cewar Anna.
Ilham tace Allah ma ya kiyaye ta fice,Zeenatu tace Iyyeeee kaji Yar Iskar yarinya Lallai Anna kinyi sake wlh ai irin wannan kwashe shegiya zakiyi da mari, Yar Iskar yarinya ce bata jin duka cewar Anna.

Ilham dai Hijab ta daura a saman atamfarta ta fice da sauri bayan tayi Sallar la'asar, Tana fita Mujaheed ya dauke ta zuwa Guess House din Taufeeq, a can ta Iske Taufeeq ya dau wanka cikin farar shadda,yasha kyau a ranta tace guy Nan Yana daukan wanka Yana abinda yake so a kasar Nan, Basu Dade ba Suka shirya abinda zasu shirya,Mujaheed yace Taufeeq ka kaita gida Abba ke nema na zamuje Unguwa dashi,Ok Taufeeq yace,Mj ya wuce abinsa,Taufeeq ya kalli Ilham sama da kasa katon Hijab tasa har kasa Yana hango wando a ciki da Alama kana Nan Kaya ta Sa,a ransa yace tana son English wear, a hankali yace muje,Wajen Wata hadaddiyar motarsa baka Suka nufa katuwar gaske,Gaban motar ta shiga ya zauna a mazaunin Driver,a nutse yayiwa motar key tare da kunna kida ga Ac tana buso sanyi da kamshi,Kawai yaga Ilham yau Bata da walwala ko kadan,Ba tare Daya kalleta ba yace ko akwai damuwa? Kai Ilham ta girgiza alamar a'a kawai dai bana jin dadi,marata ke ciwo tun jiya,Kuma sai in ta Jin masifa kawai Ni yanzu neman Wanda zamuyi fada da shi nake Yi,yau tun safe masifa nake ji,Taufeeq ba kunya yace period kikeyi ko Zaki Yi? Ilham ta San me yake nufi kunya ta kamata ta boye Fuskarta gefe can, tace Mene Haka Kuma? Taufeeq yasan ta sani ko tunaninta bazai iya fada ba sai kawai yace Jinin Haila kike Yi? Ilham a fili tace yau na shiga uku ta Daura Hannaye a kanta, Baki Bude Taufeeq yake kallonta Yana tukinsa, Kai baka jin kunya ta? Tsaki Taufeeq yaja yaci gaba da tukinsa cikin nutsuwa.










AsmaBaffa
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰







NA KUDI NE







41-45







'YAR KWANGILA IS DEDICATED TO
MAI DARAJA
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.







Official







By
AsmaBaffa



FREE PAGE







RASHIN SA'A COMPLT
Naira dari Uku 300 ne

TA GYARU CMPLT
Naira dari Uku 300 ne

'YAR KWANGILA
Naira dari biyu 200 ne
Ga me so a sata group.

Zaku iya Siye ta wannan Hanyoyi kamar Haka...

Accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, Zenith Bank.

Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
09032409668.

Tura katin waya Mtn ta WhatsApp ga number ta
08033933642.

'YAN NIGER ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.





Free page.







MEENAL PAGE NAKU NE.
Rukiey Muaz
Reemart
Sarauniya Hairat







Suna motar Ilham ta dafe Mara tace Wayyo..wayyo...ji tayi kamar Abu yana zubo Mata a kasanta,Ta cikin Hijab ba tare da Taufeeq ya gane ba tasa Hannu ta tabo taji Laima ta zaro Hannun ta cikin Hijab ta Dan leka taga jini,Ai sai ta saki Ihu tana wayyo dazu a gidanka a Kan Reza na zauna ta yanke min jiki jini yake ta Yi,Taufeeq Yana Jin haka ya taka wawan Birki tare da gangarewa kasa,yace maza mike tsaye,Ilham tana Jin Haka ta fashe da kuka tayi zaton wani Abu ne Babba,bayanta ya duba yaga motarsa Bata baci ba,ajiyar zuciya ya sauke, yace karki sake ki zauna a tsaye Zaki je gida,Ilham tace to wani Abu ne idan na zauna? Ai kina zama zai ta zuba,Allah sarki Ilham ta Dan mike tsaye ta Dan duka ta rike saman Kujera Haka ya figi mota Yana uban gudu Kamar zai tashi Sama zata Bata masa mota Wai,wani chemist ya tsaya yace fito ki tsaya a waje karki zauna,Ilham ta fito ta tsaya a jikin Mota,har Taufeeq ya dawo dauke da Leda a hannunsa yace shiga mota kici gaba da tsayawa, a Haka Suka karasa gaf da gidan Anna,Ilham tace kaji Yana ta zubowa wallahi, ta gama gigicewa tayi zuru zuru sabo da ta manta Mata suna period Allah Bai Sa ta Fara nata da wuri ba, ta manne kafafu, Taufeeq dariya ma ta bashi duk ta cika masa kunne tana ta faman kuka,Taufeeq yace ga pad Nan da magani ki Sha ita Kuma ai kin San yanda ake sawa ko? Ae na gani Ramcy tana sawa,Good to al'ada ce Kika fara kema in kin Gama kiyi wankan tsarki nayi mamaki da girmanki Haka bakya Yi.

Ilham tace na gane malam ya koya Mana a makarantar allonmu ai mantawa nayi, yanzu nima na Fara? Kai Taufeeq ya daga Mata kawai,Sai ko yaga Ilham ta Kyalkyale da dariya tana Alhmdllh dama Ana ta Yi min iyayi an rainani Wai Ni yarinya ce to Gashi mahakurci mawadaci nima Allah ya azurtani dashi,Kai yau sai na kwana Ina murna,tace Kuma bazan Yi Sallah ba ko sai na Gama an yafe min Sallah? Taufeeq yace ae Ilham ta Kyalkyale da dariya tace kace wayata yau ta shiga uku zan ta dannawa ba Sallah zan huta in ta shanawa ta,to Azumi ma in yazo Zan Sha Bayan watan sai na rama? Taufeeq yace ae,Ilham tace wooo ni Za aga girki wlh iri iri da Azumi har gwalo zanyiwa su Anna zasu gani ai an kusa azumin Ramadan zan musu gwalo,Fita to kije Ni karki Bata min mota,Kai Ya Taufeeq nawa kamshi zaiyi ta furta tare da ficewa tana wani Kunya.

Tana zuwa gida ko Toilet Bata shiga ba aka ce Ilham taje inji Anna ta wanke Mata Toilet,Ilham tace yawwa ga dama tazo wacce zan kuntatawa Anna,Pad daya ta dauka da pant ta tafi da sauri, Anna tace yawwa maza ki wanke min su Azeema sun kusa dawowa daga yawo nasan wasu a Toilet Dina zasu Yi wanka.
Ilham tana murna tace an Gama Anna ta fada toilet, ko taba toilet din Bata Yi ba bare ta wanke kawai wanka tayi tare da wanke pant dinta,Dan Iya shegen Ilham ko ruwa Bata Kora ba kawai tayi faca faca da toilet din da jini da zatayi wankan ma Gefe ta matsa can Dan kar ruwa ya tafi da shi.
Tsaf ta shirya ta boye pant din data wanke a jikinta tace Anna an wanke shi fess Yana Nan ragas yanda jikokinki zasu ji dadin wanka a ciki,tayi waje abinta.

Anna har Dare Bata shiga Toilet ba bare ta gani,Har su Azeema Suka dawo basuyi amfani da toilet din ba,Hajiya Asmau ce kadai ta bude toilet din da niyyar yin wanka,da sauri ta saki Salati ta banke kofa ta wuce wajen Anna,tana Anna shiga kiga Toilet Kamar anyi barin ciki, Anna ta mike tace dazu fa Ilham ta wanke toilet ras to sai dai idan su Azeema ne Suka Bata toilet din da Hailar su dama sangartattu ne su,Anna tana bude Toilet da karfi tace me zan gani Ni yau na Shige su ko kisan Kai aka Yi a toilet Dina,sai kace mahauta ko gidan yan Mafiya ai sai Haka,Aiko wlh su Azeema ne suzo su Gyara da kansu na gaji da Kiran Yan aiki,Su Azeema duk Suka ki yi Mujaheeda tace wlh bana period yau bazan gyara jinin katuwa ba,ko a gida bana cas bare as,Azeema tace bare Kuma Ni,Anna ta dinga masifa,Haj Zeenatu Bata son Ana yiwa yaranta fada akwaita da son Yara Haka ta hakura ta shiga toilet din ta wanke ta da kanta tana toshe Hanci.

Bayan sati biyu Ana saura kwana biyu za a Kai kudin auren Ilham,tasan Ana Kai kudi bikin ko wata daya baza ayi ba za ayi bikinta da Taufeeq,sabo da Haka Ilham tace ya Zama Dole nayi abinda Anna zata koreni daga gidanta Baki daya,tana sani cikin dare ta lallaba ta saci sarkar Gold din Anna manya Kala uku, ta kai dakinta,Anna da son kudi kullum sai ta duba dukiyarta da kadarorinta,tana tashi ta duba taga Babu guda uku,Ihu ta kurma Wanda yaja hankalin su Hajiya Zeenatu Suka Fito da gudu,Anna tace wlh bazan lamunta ba,barayin yaranku sun min sata Babu Wanda ya taba Yi min sata ko a Yan aikina sai da kuka Zo to wlh duk Wanda ya dauka ya Fito da ita ko nayi caje da kaina,kowa yace Bai dauka ba,Nan Anna tabi jikokinta da yaranta ta caje kayansu da jikinsu ba komai,tasa aka Tara Yan aiki kaf zata Fara caje su Taufeeq ya shigo gidan da wata tsaleliyar motarsa sabuwa marcedes dama yasan plan din da Ilham zata hada dasu aka tsara komai.

Azeema da Sauri ta Karasa Inda Taufeeq yake Fitowa daga Mota yasha wankan wani yard dark Brown, Azeema tana kuka ta bashi labarin satar da akayi,Taufeeq ya nuna Bai San komai ba Yana ta Basu hakuri Yana abi a hankali za a gansu Inshaallah,Azeema tace Ya Taufeeq Babynka Amatullah tana Kama da waccen Ilham din kasan na kalleta sosai, Taufeeq yayi Murmushi yace haka ma Su Mujaheed suka ce suna Kama,ai naso ma na hada Honey da waccen taga mai Kama da ita,Baki Azeema ta tabe tace me zata kulata tayi ta shafa Mata Hamamin Talauci,Amma Ya Taufeeq zaka aure Ni a ta biyu kaga nayi hakuri sosai Ina sonka wlh,Kici gaba da Addua cewar Taufeeq ya wuce gaba abinsa,a baya ta bishi tana shagwaba har suka karasa inda yan aiki suke su Ilham za a caje su.

Taufeeq har masifa Yana fada yana cewa ku Fito da shi wlh tun kafin na dauki mataki a kanku, Anna tace Kar ma su Fito dashi ta mike tare da Fara caje su Daya bayan daya,har dukiyar fulani Anna sai ta Lagutse Wai ko an boye a Bra.
Kan Ilham aka zo sai Nokewa takeyi Anna cike da masifa tace saki jikinki munafuka tabi ko Ina tana shafawa a jikin Ilham,Ilham tana Jin kunya tana zamewa,tazo gaban Ilham ta shafo tace ya naji tudu,Ilham tace kin San girma yazo Jiya na Karasa Balaga,Su Azeema da Taufeeq du sai da sukayi dariya,Anna tashafo Yan dukiyar Fulanin Ilham Anna ta shafo,Ilham tace ah...Kai...ban gane ba Anna kice ke Yar lesbian ce kawai,ya Zaki dinga shafe min Abu ba sadaki ba komai,Duka Anna ta dirkawa Ilham,Ilham ta saki Kara tana zamewa Anna tana kamota ta matse dukiyar fulani da yanzu ma suke tasowa Ilham taji zafi tace Wai ni ya Haka ne da girma na a dinga....katseta Anna tayi tace Dan ubanki Mene kike dashi bani da bani dashi ae? Gani Ni na tsaya shafa ko Ina a jikina Ina ruwana Mene a ciki,da sauri Ilham tace a'a wallahi ke kinyi Expired Ni kuwa sabuwa ce gadagal yanzu nake tasowa kice in taba naki me zanji jiki duk yaushi an tamushe,Dariya aka dingayi Anna sai masifa take Yi ance ta tsufa Bata da amfani.

Bayan an Gama cajesu ba a samu ba Taufeeq yace Anna ki duba dakunansu,Anna tace yanzu kuwa,suka wuce kuwa bedroom din ko wacce aka duba Babu ana zuwa na Ilham aka samo su a Kasan katifarta,Anna ta jawota tace yau kafin na koreki sai na Sa kowa ya zaneki a gidan Nan, Finciko Ilham sukayi da kayanta Baki daya aka watso Mata tsakar gida,Ilham idonta ya cika da Hawaye yanda kowa a cikin iyalan Anna ke dungureta suna rankwashinta suna zaginta,Yan aiki ma Haka an hadu a kanta,Anna ta finciko ta tare da jefar da ita ta Fadi a kasa gwiwarta ta kuje,Anna zata sa a Zane Ilham kafin su koreta,Taufeeq ya hade rai Ya Karaso Inda Ilham take yace Barauniya,Anna zata sa a fara dukan Ilham Taufeeq yace Anna yaushe Zaki Bata lokacinki akan wannan Yar kauyen talaka ai ku sallameta kawai ta tafi zata fi jin zafin hakan ta rasa aikinta ba samun kudi,Haj Zeenatu tace hakane wlh ta karata yar tsiya tunda an ga sarkokin ai shike Nan tashi ki bar Mana gida,da gudu Ilham ta kinkimi Ghana Must go Dinta tayi waje da gudu Yan aiki suna Mata ihun barauniya.

Tana fita Taufeeq yace wlh ta bani haushi bana, son mutum barawo gida zanje na huta gobe na dawo kawai,Anna tace jeka ka huta kar ta sa maka Ciwon Kai,Taufeeq mota ya shiga da sauri ya bar gidan Anna, Hanya Taufeeq ya mike Yana kallon Hanya sai da yayi Nisa ya hango Ilham tana Jiransa jikin wata bishiya,Glass ya sauke tare da yin slow da motar ya gangare ta zaga da sauri tasa Jakarta a baya ta shige gaba da sauri yaja Suka tafi sai Dariya Suke shekawa Plan ya hau dai dai,Su Mujaheed suna Guess House suna jiransu sai duba agogo suke Yi, suna ganin me gadi ya bude gate Suka hau murna da tafi.

Saddeeq ne ya dauki Jakar Ilham yace Bauta ta Kare an shaki iskar yanci,Dariya sukayi gaba Daya,Taufeeq yace saura kadan ta taci duka,Wlh nafa kusa kuka Kunga yanda Suka yanyame Ni me rankwashi me Masga yana Yi,Dariya sukayi, Su Mujaheed tafiya sukayi guda sunce sai dare zasu dawo daga Ni sai Taufeeq a Palo, First aid Box ya dakko yace muga gwiwar Taki.

A hankali ta Dan kwaye skert Dinta zuwa cinya tana Zaune a saman Kujera,kasa ya dawo gabanta wajen Yana Dan fitar da jini kadan, wani ruwan spirit ya kwara Nan take zafi da radadi yasa tace ouch...kallon fuskar ta yayi kadan ya wanke mata wajen sannan ya manna plaster a wajen Bayan ya shafa mata wani gel, Gashin kansa da fuskarsa kawai take karewa kallo Yana birgeta,Bayan ya Gama ya maida box din sannan ya dawo zai tafi shima Yace karki manta Banda Fita ko da Wasa Sabo da Kar a samu matsala, Inshaallah ta furta,Fita yayi yana cewa Mujaheed zai kawo Miki Abinci, ok to na gode.
A saman Kujerar ta kwanta Bacci ya kwashe ta, baccin da tayi ba shiri bata kwanta dai dai ba, wuyanta kamar zai karye, Yamma Likis bata tashi ba tunda ba Sallah takeyi ba,Taufeeq ne ya shigo gidan,ya dinga buga Mata kofa ta bude Shuru,kawai ya bude da Kansa ya shiga,ya hangota a saman Kujera tana bacci kanta ya lankwashe, sai bacci takeyi.

Taufeeq Daukanta yayi kamar jaririya ya kaita Bedroom tare da kwantar da ita,Ilham taji sanda ya dauketa Amma kunya tasa ta kasa bude idonta,Sai da ya dawo Palo ya zauna Yana kallo Sannan ta mike tare da Shiga toilet wanka tayi kawai ta fito ta shafa lotion dinta cikin Wanda Hajiya Maryam ta Hado mata a matsayin Amatullah Yar Gomna, cikin dogayen rigunan da Su Saddeeq Suka siya Mata tasa Peach din ta daura dankwalin na zamani yanda ake yayi a yanzu,jikinta tabi da turaruka ta fito Palo cike da nutsuwa.
Mj ta Iske shi da Taufeeq suna ta cin Abinci Take away Suka Yi, Mj yace wannan sai kace yau aka daura Auren irin kyau Haka,Dariya Ilham tayi kawai ta zauna a gefen Taufeeq kusa da shi tayi Shuru tana kallonsu suna game iri iri bayan sun Gama cin Abinci, Ga abincinki fa kinyi Shuru yau lafiya? Kamar baki da lafiya Mujaheed ya tambaya.
Murmushi tayi kadan tace ba komai kawai bana jin dadi ne sosai, Taufeeq kuwa yasan meke damunta period ne da bata Saba ba ya dame ta.
Shuru Ilham tayi Kamar ba ita ba akan tana period duk ta damu kanta,Maman Mj ce ta Kira shi a waya ya tafi ya bar Taufeeq da Ilham,Kallon Ilham yayi kadan yaga ta sake kwanciya again Bai ce mata komai ba.

Zubairu Rocket Yana tsaye Anty Halima tana ta faman zaginsa tana zazzaga Masa Bala'i kamar zata cinye shi,In ba kaddara ba me zai sa na auri miji irinka,Lusari me Ka taba tsinana min,idan an haifeka da jini ka sakeni,Murmushi takaici Zubairu ya saki yace ai Ni bana sakin mace indai akan na Sakeki ne to sai dai kiyi abinda zakiyi Halima,me kike so nayi Miki iya karfina Ina kawo Muku abinda Zaku dafa,Garau Garau kullum zamuci, Anty Baki na kumfa tace ni da yarana wlh kasan da gata na ka auro ni,ban San kaddarar data Sa na Aure ka ba,Zubairu yace to ya zakiyi Kinga santalelen saurayi Dan gayu ga iya tsari, yaro Dan Fulani Kika rude a kaina,har kuka kike min akan Lallai na turo dangina ayi auren kin matsu ki ganki a gidana,Halima taja tsaki wannan har gida ne? Gidan kasar,Yan kauye kawai Ina birni nazo wannan rugar Tirrr na cuci kaina,Kuma Bari kaji da kake cewa wai na mato a kanka har kuka nayi ayi a Mana aure to Rocket din karya ka harbo, Ni wlh farkon ganina da Kai wani Dan yaro na ganka duk yunwa ta Gama maka Illa, ni da Wasa Muka gaisa a kasuwa,abokinka Ya'u shine Dan Iskan domin shi ya hada mu,Ina Yar birni Ina ni Ina Kai, yanzu ne fa ka girma,Zubairu yace to sai ki koma baya ki duba ke Yaya kike a lokacin? Gefensa da gefensa ya kalla yaga su Bilkisu

Please Login or Register in order to submit comment