Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya dawo min da kai
Lafiya,Allah ya hada
Ka da wacce zaka
Aura ta Gari,Allah
Ya Kare min Kai
Allah ya maka
Albarka, kana
Dawainiya Dani
Allah ya baka kaima
Masu Yi maka.
Idan kaje Text me pls .
Yana karantawa ya rubuta Inshaallah Ummi.
Kiss ta manna Masa a goshinsa shima yayi Mata sannan yaja jakarsa ya tafi Yana daga Mata hannu.

Su Ilham sun Isa Airport din Dubai lafiya,za ayi musu Check in, Guy din da aka hada su dashi Agent shi tuni an buga masa stamp ya wuce ciki Yana jiransu aka karbi passport din su Ana dubawa su biyun fake visa ce Suka Zo da ita,Nana aka Kira securities su rike su,wancen Yana Jin Haka ya maza yayi tafiyarsa ya barsu, sun Dan tsinci turancin za a kamasu suka arce da gudu Ana binsu Amma sunki kamuwa, a wajen Suka bar kayansu Suka fada Toilet.

Ana ta nemansu ko Ina a Airport din har dare yayi Basu fito ba sun kulle bayin, a cikin Toilet Ramcy ta fashe da kuka kasa kasa tana mun shiga Uku Allah ka fitar damu,Wlh idan na kubuta gida zan koma gaban iyayena,Ilham ta dinga dariya tace ke banza ance a prison dinsu kullum kaza ake ci, kiba zamu Yi bul bul.
Wasa Wasa a toilet Suka kwana har rana tayi, Securities sunce a kyalesu zasu fito Dole suna Airport din Dole a kamasu akan sunzo da Visa bogi.
Azabar tsaiwa ce tasa Suka fito da kansu ai kuwa Aka biyo su za a kamasu Suka dinga gudu suna zagawa da securities din sai sun kaisu gaba sai su dawo baya suna ta kwana da su,mutane Ana ta kallonsu wasu ma dariya sukeyi, Ilham ce a gaba,ga wasu jirgi Yana ta sauke su suna shigowa ciki,Da gudu ta taho ba tare data sani ba ta fada Jikin mutum,wani kamshi ya ratsata, da sauri ta kalli mutu min tsoro ya shigeta Taufeeq ne Sanye cikin jallabiyarsa ta Yan gayu,tsoro shima ya kamashi ko Aljana Ce Ilham, duk inda yaje wajen talaka da masu kudi sai yaga Ilham,Tana haki tace ka taimake mu wata Hajiya ce tayi Mana visa Wai zata tura mu Neman kudi Dubai Ashe fake visa ce shine ake so a Kama mu Dan Allah ka fitar damu kayi musu bayani ba wani turanci Muka iya ba.

CSecurities tuni sun cafke Ramcy,Taufeeq ne yayi Magana cike da Izza yace tasar min a jikina,Da sauri taja Baya tana washe Baki tace kamshinka ne sai shegen dadi, wasu securities din ne Suka taho zasu kama Ilham ta samu tayi Tsalle ta dafalfale a jikin Taufeeq tare da sakalo Hannayenta ta wuyansa, aiko police suna zuwa Suka fisgota kasa,ta fisge tana ihu,Taufeeq yayi gaba Amma ta Fisgo gefen rigarsa da karfi ga police suna janta sai Suka hada da Taufeeq Suka jawo su duk karfin Taufeed sai da ya Fadi a kasa yayi flat,Ilham ta fisge da gudu tana kuka da ihu ta fada kan Taufeeq ta makalkaleshi,Ramcy itama ta fisge ta karfi ta taho kawai ta fada kan Ilham ita Kuma Ilham tana kan Taufeeq,daga kwancen ran Taufeeq ya baci ai ko ya gasawa Ilham mari.

Zumbur ta mike a gigice ta hantsalar da Ramcy ta Fadi gefe can,Taufeeq ya mike cikin fushi yaja akwatinsa zai tafi kawai Ilhama ta tafi da Rarrafe ta riko kafarsa tana kuka tana Dan Girman Allah ka taimaka Mana,Yana gani police suka kamasu gaba Daya.
Har yayi niyyar tafiya sai ya fasa ya tsaya wajen Securities yayi musu bayani akan matar data turo su Basu San komai ba,da kyar ya ganar dasu sannan Suka amince bayan ya biya makudan kudade aka saki su Ilham aka kaisu zasu shiga jirgi a maida su gida Nigeria, Ana cewa Haka Ilham ta kyalkyale da wata dariya me style tace ko banza mun shiga jirgi munzo Dubai kasar waje woooo mu woooo mu, Taufeeq Yana kallonta Murmushi kawai yayi tace sai mun sake haduwa Arab Man Bye Allah ya Kara budi.
A jirgi aka sa su sai Nigeria aka sauke su a Kano state,mota Suka shiga zuwa Kaduna zasu koma gidan Hajiya Uwani,Ilham tace Hajiya Uwani Ashe ba mutuniyar kirki bace to Lallai sai munyi maganinta,Ramcy tace sosai ma ya kamata a koya Mata darasi.

Hajiya Uwani tana gida sai ganin su Ilham tayi sun shugo, zumbur ta mike tsaye tana cewa lafiya? Ilham tace fake visa ce saura kadan ya rage a kaimu prison Allah yasa wani bawan Allah ya taimaka Mana,Hajiya Uwani tace toh ikon Allah ku ajiye kayan naku Bari Zan Kira Hajiya Baturiya a canja muku visa me kyau ku tafi ko Sudan ne,Ilham tace to Allah ya kaimu,Suka koma dakinsu,Ramcy tace kinji muguwa bafa zata saduda ba kawai mu dage mu nemi wajen guduwa tun kafin ta Nemo wata visar mu kyaleta da halinta kawai.
Kwanan su Ilham Uku ba inda suke Fita sai dai Hajiya ta Basu me kyau suci su Sha,daga Haka suka ce zasu koma gidan kaji da aiki kafin a samo Visa Hajiya tace Baku da matsala.
Bayan sun koma aiki Haka Suka dinga ta cinye kaji kullum,Suka Yi wata kiba bul bul, akwai wani me kula da kayan marmari Shehu, Ilham ta same shi Yana aikinsa tace Baba Shehu ba inda ka sani ne a kasar Nan da zamu iya aikin Wanke wanke da shara Banda Kaduna a wasu state din,Shehu ya washe Baki yace gaskiya ban sani ba Amma naji abokina dake aiki a Gidan gona can rivers garin patakwal wasu suna neman mace me iya kiwo Idan Kuna so nayi Masa waya kuje can,Ramcy tace Ni dai wlh na gaji da yawon duniya Ina da gata na,gida zan koma kauyenmu, Ilham tace a dawo lafiya dama a hanya Muka hadu Baki San tarihina ba Ni ko na San naki baki da matsala Ramcy wlh na yarda dake ki koma garinku,Nima da ace Ina da gata da gida zan koma Amma ni wannan yafiye min rayuwa cikin dangina.

Ramcy tace Ni dai tafiya zanyi Ina da Number ki zan na kiranki Muna gaisawa,Ilham tace ba damuwa, Yau ma mun gaisa da Rabiu Manager yace na gaishe ki,Murmushi Ramcy tayi tace Zan kirashi Nima,Shehu tuni ya bugawa abokinsa waya yace an samo macen me kula da kiwon,gobe zata taho Inshaallah,.

Cikin dare 10pm Hajiya Uwani lokacin tayi bacci tuni su Ilham suka kwashe kayansu Suka bar gidan,a gidan kajin Suka kwana washe Gari da safe Ilham ta tattara har Gas din da tukunya Suka tafi Tasha Ilham ta shige Motar Rivers ita Kuma Ramcy tana kukan sabo da sukayi itama ta shiga Motar Kano Sumaila, Ilham kuwa Yar kwalla tayi Suka rabu Ramcy tana shesheka tace s...sai...m...munyi...wa..waya, ba damuwa.
Ilham ta shige katuwar mota Shehu ya Bata number abokinsa Saluhu ta kirashi tace tana hanya sun taho.
Tun Basu Yi nisa ba Ilham ta kwadawa Ramcy Kira a waya,Ramcy tana ganin Golden girl ta saki Murmushi tare da dagawa Hello Golden Girl Naam ya akayi Ramcy tunaninki nakeyi Ina kewarki,ta turawa Suka ce I miss you, Golden har kin San na tuno muguntar da Muka hadawa Hajiya Uwani Allah sarki hhhh dariya sukayi Ilham tace ai yanzu taji azaba na sani sun Dade suna surutu sannan Suka kashe wayar,Ko minti Goma ba ayi ba Ramcy ta sake kiran Ilham,Ilham tana dagawa tace yanzu muka wuce wajen wani gashin kaza da gani zata Yi Dadi irin Taki ce kin San ke ba komai kike ci ba,Ilham da sauri tace Dan Allah jefa kanki ta window ki shakar min Kamshinta Aiko Sai gani akayi Ramcy ta zuge glass din mota da sauri ta tura kanta waje ta Dade tana shako kamshi da iska sannan wani mutum yace Dan Allah Hajiya ki rufe Mana iska ta Dame mu,To Tsinau an rufe Ramcy ta furta tare da zuge window.

Ilham kuwa Bata kira ba sai da aka tsaya daf da Rivers akace masu fitsari da Sallah su fita an Basu 30 mnt, sun firfita Ilham ta shige Toilet na Mata zata Yi fitsari Amma sai da ta Kira Ramcy tana dagawa ta Fara fitsari tsuuuuuuuu tare da Kara wayar Ramcy taji Tsuuuuuu kawai take ji Kamar ruwa Yana zuba tana ta Hello Hello, sai Ilham tayi tsarki sannan tace ya kikaji fitsari muka Fita Yi,naji zahiri cewar Ramcy tace Ni ai har Naje gida kin ganni a kauyenmu Dangi sai Murna akeyi tunaninsu sace ni akeyi sunce baza su Kara bari na fita ba,Ilham tace na tayaki murna Dan Allah karki Yi aure ki Bari muyi aure a Gari Daya mu auri yan birni, ai wlh Inshaallah muna kusa da juna cewar Ramcy,Kinga yan gidanmu duk sun san labarinki Ilham suna ta son ganinki,Ilham tayi dariya tace sai mun sake Haduwa Ramcy zan baki Tarihin Rayuwata kaf,Allah ya kaimu.

Ilham Yogourt da ruwa ta siya sai balangu ta koma mota bayan tayi Sallolinta.
Bata Dade da shiga ba mota ta tashi,sun dauki kusan 2hrs suna tafiya sannan Suka Isa Rivers State garin da Hausawa ke kira da Patakwal Porthacourt.
Yamma likis Suka sauka ta Kira number abokin Baba shehu,30mnt ya Iso a cikin Taxi ya dauki Ilham Suka wuce bayan ya Kira Baba Shehu ya sanar Masa Ilham ta Iso lafiya.

Wacce Ilham zata yiwa aiki ba kowa bace face Anna kakar Taufeeq, Uba Salihu abokin Baba shehu har gidan Anna ya Kai Ilham, Anna tana zaune tana kallon TV ba wata tsohuwa bace can,Ilham Da Uba Suka shigo dauke da Sallama, Anna da kyar ta Amsa musu gaisuwa Sabo da ita talaka ba komai bane a wajenta, a kasa Ilham ta tsuguna,wata mahaukaciyar tsawa Anna ta daka Mata Wanda ba shiri ta mike tsaye,Anna a fusace tace ba a aikata komai a gidana face na bawa mutum Dama,wannan uban shirgin kayan duk nakine? Ilham tace ae nawa ne,makarantar kwana Zaki je ko Kuma Ina Zaki? Uba kwashe wannan kayi waje dasu can dakin Shirgi,Ilham a ranta tace cab Ashe za ayita tsohuwa,Bari na goge na gane Kan garin Zaki san wace Ilham.
A Fili kuwa Ilham cewa tayi kiyi hakuri Iya, ba sunana Iya ba Anna nake, to Anna cewar Ilham.
Jeka Uba ka Gama aikinka,Ilham tana Shan kallon Yan aiki sai zagade sukeyi a gidan,Anna ta Kira wata Budurwa me dafa Mata abinci tace Harira Kai wannan part dinku a Bata abinci a tabbata tayi wanka,To Anna taso muje,Ilham ta mike tace Bilmillah a hankali Kamar me rada tace Anna Uwaki...Uwaki...Anna Bata ji sosai ba tace Ke uban me Kika ce?Ilham tace cewa nayi Bilmillahi Anna Uwarmu me karamci,Oho to jeki Amma nayi zaton zagina Kika yi,Ilham tace Allah ya kiyaye ai ko ba komai ke Kakata ce,tsawa Anna ta buga Mata Allah ya kiyaye ki Zama Jikata,duk zuria ta babu talaka me Bauta.
Ido Ilham ta zaro ba tare da tace komai ba tabi bayan Harira bakinta alaikum.










AsmaBaffa.
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰








NA KUDI NE




21-25







'YAR KWANGILA IS
DEDICATED TO MAI
DARAJA
🚨DR RABIU MUSA KWANKWASO.









Official






By
AsmaBaffa







RASHIN SA'A COMPLT AND
TA GYARU COMPLT
Naira dari Uku ne 300.

YAR KWANGILA
Dari biyu ne 200 ga me so a sata a group.

Zaku iya siya ta wannan hanyoyi..

Accnt number
2177560408,Yahaya Garba Muhammad, zenith Bank.

Transfer ko Vtu ga number da zaku tura
0903240966.

Wanda Zaku tura katin MTN ta WhatsApp ga Number.
08033933642.

'Yan Niger ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.





Ga page naku mutanena









'yar aikin me suna Harira ita ta Kai Ilham part din masu aiki,gaskiya gidan Anna ma ya hadu sosai Madaidaici me tsananin kyau Babu abinda Babu na more Rayuwa,Wani karamin Dakin aka Kai Ilham da katifa Yar madaidaiciya Sai Toilet a ciki Karami,Ilham tasan komai sabo da Zama a gidan Hajiya Uwani, Ilham dai gefen Katifarta ta zauna,window dakinta Yana kallon Compound zuwa Bakin gate, Kayanta taga wani katon Namiji Arne ya kawo Mata Babu tunanin wani dakin mace ne sabo da garin arna ne, Abinci Harira ta kawo Mata shinkafa da wake da Mai da yaji,Ilham baki bude ta kalli plate din tace Harira kike ko gida kamar wannan dama Ana cin shinkafa da wake? Baki Harira ta tabe tace ai Anna indai ke talaka ce Yar Aiki to baza kici Abinci me Dadi ba,tace talaka abinda ya Saba ci a kauyensu shi zai ci a gidanta.

Ilham tace to ita Kuma Haka take? Hmm kiyi taka tsantsan kawai cewar Harira,To Ni kuma gashi bana cin shinkafa da wake ko a kauye Haka nake,Cab Aiko karki sake Anna taji don Wallahi sai ta Kare Miki cin mutunci,Idan Kuma Kika yi Mata rashin kunya kartai maza zata sa wallahi su zaneki tas sai sun Miki dukan kawo wuka, sannan akwai wani jikanta sunansa Taufeeq tana Masifar sonsa,ko kallo Bata so me aiki tayi Masa,Allah ma ya taimakeki gidan kiwon Dabbobinta naji Tace Zaki dinga kula dasu, to wallahi ki kula ko kaza ce akan a yanka ta gwara a barta ta mutu haka Anna take,Kuma jikanta shima Yana zuwa ganin dabbobin nata,yaga ya aikinsu yake, a can akwai ma'aikata maza da tsofaffi su biyu Amma Anna tace cutarta suke Yi shi yasa tasa aka Nemo Mata wata Yar aikin wato ke, ki kiyaye Zama da ita duk mutuncin da kike Mata Rana Daya Kika kuskure to wlh sai kin Gane kurenki,gwauron numfashi Ilham taja tace to Gashi Kuma Ni bana jin magana ba mutunci ne Dani ba ya za ayi kenan?
Harira tace Ni dai na fada miki gaskiya ba ruwana Zaki ci shinkafar ko a'a? Ilham tace bana ci fa na fada miki, Haka Harira ta dauke abincinta tayi gaba.

Taufeeq Yana Office wayarsa ta shiga Ringing, Mujaheed ne ke kiransa Yana dagawa zaginsa ya Fara Yi Yan aikin banza Ana ta kiranka baka dagawa to dama fada maka zanyi na samo maka wata matar Auren sunanta Safiyya,yar Asalin Jigawa ce Cirani Babanta yazo nan garin ya haife su talakawa sun Saba da wahala Amma wlh Nutsatsiya ce,Ba damuwa Zan aureta haka a shirya ranar da Ummi zata ganta Idan tayi mata sai a aura kawai,Kawai ka shirya jibi zan kawo ta wajen Ummi ka fada Mata, Alright cewar Taufeeq.
Bayan Kwana biyu Mujaheed ya kaiwa Safiyya Kaya masu tsada kala biyu Wanda zata sa,Iyayen Safiyya sai Murna sukeyi yarsu ta samu miji Wanda Kuma Kwangila zata Yi a biyata kudi, Baban Safiyya yafi kowa Murnar auren sabo da idan ta samo kudin jari zaiyi dashi,matukar zai samu kudi haka to ko yau aka daura aure gobe aka sako ta bashi da damuwa.

Lokacin da taci kwalliya cikin wata shadda pink Yar gaske Mujaheed yazo ya tafi da ita a motarsa, Safiyya tana da nutsuwa sai Suffarta ba kyan fasali jikinta siriri, kirjinta Dam ya cika ya batse duk kayan data Sa Bata yin kyau, saman Kirjinta dam kasa siriri, idonta Dara Dara Amma jajir dasu sakamakon tana da lalurar Ido idon nan Kamar jan gauta, ganin irin mahaukacin gidan Su Taufeeq Safiyya ta rude nan take taji wannan gida ya shige ranta, a ranta tace ko Dan wannan gida ai kaso mutum, Da sauri Mujaheed ya kalleta sabo da Zancen zucinta ne ya fito fili Bata sani ba, ci gaba da magana tayi kalli motoci a Nan sai wacce na zaba,wayyo ayi sauri aje Naga Angon nawa,Baki Bude Mujaheed ke kallonta Bai ce komai ba yayi Mata Iso Palon Ummi inda Taufeeq da Saddeeq ke zaune suna Hira Mujaheed yayi Sallama,Safiyya na binsa a baya,Jan idon Safiyya kadai sai da ya firgita Ummi, itama a kasa ta duka ta gaida Ummi,Saddeeq yace zamu sanar Mata ita ce wacce Zaki kula da ita,Cikin zumudi Safiyya tace Inshaallah wayyo Allah wannan Farin ne Mijin nawa? Dadi kashe ni Allah na gode maka ta furta tana washe baki tare da daga Hannaye sama, a rubuce Taufeeq ya tambayi Ummi Tayi? Ummi ba a son ranta ba Amma Dan Kar ta wahalar da Dan nata tace tayi kawai ba damuwa Amma ku tashi ku tafi gidan Anna ku kaita ta ganta kasan idan Anna Bata sonta baza ta Bari ka aure ta ba.
Taufeeq ya Bata Rai zaiyi Musu Ummi ta kwace bironta ta korasu,Ita kuwa Safiyya gani takeyi ta cinye zabe kawai sai wani dariya takeyi tana washe hakora gaftara gaftara.

Taufeeq can nesa da Safiyya ya Fara tafiya su Mujaheed suna gaba,Safiyya harda dawowa kusa da Taufeeq duk kudi ya rudata, Motar Saddeeq Taufeeq ya shiga, Mujaheed Kuma ya dauki Safiyya Suka tafi gidan.

Ilham Har yanzu Anna Bata Turata gidan gonar ba sai wahala Anna take sa Ilham Iri iri,Yau ma da yamma ta kira Ilham, sanye take cikin kana nan Kaya Jean pencil black da t-shirt red sai Hijab da ta Sa Kato, Ilham tana gabanta a durkushe Amma har yau Bata ce me zatayi Mata ba,Dai dai lokacin Suka ji motoci sun tsaya cikin gidan, Anna da kyar tace da Ilham Yi min tausa Mazari, naji ance har rawa Kika samu dama kina Yi a gidan Nan ko? Nishadi ne ai Expire lady cewar Ilham,Anna tace ke turanci Zaki Yi min ai nufina Sunan matar kirki shine Expire lady,Anna taji Dadi tayi zaton Ilham yabonta tayi,a boye Ilham tayiwa Anna gwalo, dai dai lokacin su Taufeeq suka shigo dauke da Sallama a bakinsu,Ilham a hankali ta Dago kanta sama tana yiwa Anna tausa,har zata saki ihun murna ganin Wanda ya taimakesu Amma sai ta fasa tunawa da tayi da halin Anna Sai ma nunawa tayi Bata san Taufeeq ba taci gaba da yiwa Anna tausa.

Anna sabo da gadara tana ganin su Taufeeq da bakuwa Amma ko kulasu Bata Yi ba,gaisuwar ma da kyar ta amsa musu,Ita kuwa Safiyya ko gaisuwarta Anna Bata amsa ba,sai ma Ilham da tacewa ke naji ance Rawa kike min a gida? Gidan shedanu ne,?

Ilham tace Haba Expire lady kiyi hakuri da sauri su Mujaheed Suka kalli Ilham,Anna Suka gani tana wani jin Dadi ta kalli Taufeeq tace Kai yaro kaji inda aka iya yabo da turanci ba uwar da ka Iya,dariya sukayi gaba Daya Basu ce komai ba Dan sunga An Gama da Anna Bata sani ba,Haka Anna ta dakawa Ilham tsawa ke dauke Ni cak ki maidani saman 3seater Zan mike, Su Taufeeq suna kallon ikon Allah taya wannan yarinyar Ilham ta iya Daukan Anna wacce take da kiba, Ilham tace an Gama tasa Hannu tayiwa Anna daukan jaririya cak ta dauketa tare da Maidata inda take so,Anna tace saura rawar da akace kina Yi a gidan Nan wlh idan bakiyi ba sai nasa an zaneki Dan Nan ba gidan ubanki bane da Zaki min rawa a gida ba Izini na, Kallon Taufeeq Ilham tayi kwarjininsa da kunyarsa yasa taji baza ta iya Rawa a gaban su ba,a nutse tace na zabi a Zane Ni akan nayi rawar.

Safiyya tana gefe har wani yanga takeyi ita a Dole ta Dace,Mujaheed ne yayiwa Anna magana yace dama Matar da Taufeeq zai aura muka kawo Miki zata gaida ki,Da sauri Ilham ta kalli Taufeeq Suka hada Ido lokaci guda kowa ya janye idonsa,Anna kuwa waige waige ta Fara tana tambaya Ina matar? Tana Ina,Safiyya tana kallon ikon Allah wato ma Bata ganta ba,Saddeeq yace gata fa Anna,Tsaki Anna taja tace Wasa kakeyi Taufeeq Dan Allah ku tashi ku bani waje,baza a aureta ba,ka Rasa wacce zaka kwaso sai wannan kirar talakawa,Wlh ban Amince ba,dama Taufeeq shima ba damuwa yayi ba sai ya kalli Safiyya yace to kinji ba laifi na bane Kiyi Hakuri,Tsawa Anna ta daka Mata tashi ki Kama gabanki,da sauri Safiyya ta mike tayi waje,Mujaheed ya bi bayanta da sauri Yana Bata hakuri Amma kafin kace me Safiyya ta fada Napep ta bar Layin ma gaba Daya.
Taufeeq ma da Sadeeq barin gidan sukayi baki Daya.

Hajiya Uwani washe Gari da Asuba ta farka bayan su Ilham sun tafiyar su ,ba tare data kalli wajen ba tasa hannu cikin duhun dakinta zata jawo Touchlight zata Haska,daura Hannunta ke da wuya ta kwala wani uban razanannan Ihu, Nan fa Hannunta ya makale ita kadai ta Fara Vibrating tana jijjiga,Jin kararta Yan aikinta mutum biyu suka shigo da gudu suna tambaya Hajiya lafiya,light suka kunna haske ya gauraye dakin suka hango Hajiya hannunta saman Drower kan Touchlight tana ta jijjiga,Daya cikin Yan aikin tace kalli wayace aka hada Shocking hajiya ta dakuma, Katuwar Sanda Suka dakko tare da make Toch din ta Fadi gefe gaba Daya,Lokacin Hajiya ma ta Fadi kasa shame shame tana jan numfashi da kyar motsi ta kasa Yi, Nan take Suka Nemo Driver Suka tafi da Hajiya Asibiti.

Ramcy Tunda ta koma Suka kasa Gane kanta Wai ta waye ita, komai na Yan Birni takeyi,ga Jarabar sa kana Nan Kaya,gashi da kyar suka samu ta dawo gida da Addua yanzu basa son abinda zai sa ta Kara barin gida,shi yasa basa takura Mata sai abinda take so,ga wayar jaraba ta Kira Manager ta kira Ilham ko su kirata suyi ta waya ko gajiya basa Yi.

Zubairu Rocket da Anty Halima Talauci ya sasu a gaba,Kullum yanzu soyayya ta Kare sai Fada da zagin juna da sukeyi,gida ya kazance dama Ilham ke gyarawa su Bilkisu basa dauke ko tsinke.
Zubairu ne a saman machine Ana figa gudu dashi ya dawo daga kasuwa yayo cefanen miyar Taushe,Alayyahu a cikin Leda Rabi yayo waje Iska tasa Yana Falau...Falau...a kofar gidansa aka saukeshi ya shiga Gida da murna yau yayo cefane,Yana murna ya shiga kwalawa Anty Kira Halima.. Halima fito maza ga cefane,Anty tana Fitowa ta karba da murna ta bude nan take ta fatalar da ledar tace Amma anyi sakarai ragon Namiji wannan ne zai ishe mu? Haka kaga Ilham tana siyo Mana da kudinta,Kalli fa kabewa guda goma,Attaruhu kawai guda biyar sai Dan Alayyahu kamar gemun Malam Liman,wlh ba abinda zanyi da shi kowa ya kwana da yunwa lusarin miji, Zubairu ya mike tsaye yace Halima wlh ki kiyayeni na gaji da Halinki,Ubanki ne ya fito daga lahira ya bani kudin,kin San wahalar Dana Sha? Tsaki Anty ta ja,kafin ta rufe baki Zubairu ya kifeta da Mari me azaba, tana dagowa ya Kara kantsameta da wani,Kururuwa ta saki da Ihu ta fada daki da gudu Amma ya bita ciki kamar ya samu katon Gardi Haka ya shiga jibgar Halima Su Bilkisu suka rike Zubairu ta ko Ina suna jansa suna bashi hakuri,Amma yaki hakura sai da ya yiwa Halima lilis sannan ya hakura ya fita, Anty Halima tana kuka tace zaka dawo wlh zaka dawo wlh akanka sai na Sha maganin Tauri,fuuu ta suri Gyalenta sai gidan Sarkin Yan Tauri na Garin wato Kaura goje .

Bako Sallama ta fada gidan Kaura Goje tana kuka,Ya fito da Adda da takobi ga gariyo,jikinsa duk guru da layoyi ya iske Halima tana kuka tana Kokawa Matar kaura matsalatar, tace gwara na Sha magin karfe wlh yanda zamu dinga kafsawa dashi Dan bazan kyaleshi ba.
Hhhhh Goje ya saki mahaukaciyar Dariya yace zauna na Baki magani Haka nake son mace me Kamar

Please Login or Register in order to submit comment