Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta murguda tace ae wlh taci sa'a niyya nayi na rushe Mata hakora,Kai Zubairu Rocket an daina cewa da Kai Baba kaima Ubanka ya daki goshin Uwatas, Zubairu ya hangame Baki yace to wannan sai dai gidan Mari,Bilkisu ce ta cakumi Ilham Wai ta zagi iyayenta,Ilham ta dauki buta ta kwadawa Bilki a kanta,Butar ta fashe Mata a goshi Nan take itama Bilkisu ta Fadi kasa goshi na jini,Halima ta saki Ihu,tace wlh bazan yarda ba Zaki kashe min Ya, dama an kawo min maganar Gidan Almajirantar Mata a Kano Kamar yanda ake Kai maza Almajirai haka yanzu akwai malamai yanzu Ana samu a Kano ance harda na Mata wlh can zan turaki Dan ubanki,Anty Halima tayi zaton Ilham zata ji haushi sai gani tayi ma Ilham ta Fara taka rawa tana murna,harda zuwa ta durkusa tana bawa Anty hakuri,Dan Allah ku yafe min kuyi Hakuri,ban San kuna kaunata ba sai yau,yaushe zan tafi almajirantar? Baki Bude Zubairu yace yo dama gobe ne naji wani malamin zai tafi daku a mota,akwai Mata biyu a garin nan kece ta ukun da Kuma maza sunkai su Goma,Farin ciki ya kama Ilham,tana tsalle tace wayyo Allah birni shike nan na Zama Yar gayu an Gama wlh Dole ma nayi gayu,wow ta turawa ai wlh daga yau na Koma maganar Yan gayu da turanci kawai,Ashe Ni ci gabana yazo,ku yafe min Anty,Nan take Ilham ta dakko dari biyar ta bawa Anty sai ga Anty ta mike ta wanke ciwonta Dana Bilkisu tana murna sabo da kudi.

Zo Ilham dakina muyi sirri kinji cewar Anty,Aiko Ilham ta shige tana wani gayu tana yarfe Hannu ta Zama Yar birni,Anty tace da farko Idan kinje Ilham Ana sana'a a can iri iri,Kuma Kinga a dakin Matan malam din zaku dinga kwana,Dan Allah Ni dai ki dinga Yi Mana aike a Kai a Kai na kudi,kiyi sana'a sosai na sanki da kwazo 'yata ki daure ko yaushe naga kudin Nan,Ilham tace to kawai ita kuwa walaha ce ta isheta ta matsu dama ta bar gidan ko garin gaba Daya ta huta.

Yau an zauna lfy ba masifa,a ranar Ilham ta kaiwa kowa abin kiwonsa gidansa da komai na mutane ta mayar,Washe Gari da Asuba ta shirya Kayanta a jaka Ghana must go sannan tace Kano ce garin gayu yau Doguwar riga tasa Fara tas me dison dison ja me dogon hannu,ta matse sama ta bude kasa,Sosai tayi Masifar kyau ta yafa gyalenta siriri baki a kanta,ta Sa takalmin robarta Baki, Haka Zubairu Rocket ya dinga jajjada Mata akan ta dinga Aiko musu kudi,Su Bilkisu kuwa sai dariya suke wa Ilham suna ce mata Almajira Almajira,ko kulasu Bata Yi ba,cikin Gari taje tayi musu sallama da kawaye Amma Anty tace Wai tace Boarding schl ta Boko za a kaita Haka zance ya cika kauyen Ilham zata tafi Birni karatun Boko makarantar Jwana, Su kuwa Wanda za a Kai almajiranta maza da Mata sai kuka sukeyi suna jin Dama sune Ilham,munafuki Driver motar da Malamin sun hada baki da Anty A babban titi zasu hadu da Ilham su dauketa a Hanya ba Wanda ya Sani.

Har Su Hamza kungiyar su sun bawa Ilham kudi sun hada Mata dubu biyar ta boye Anty Bata sani ba, sannan ta karbo kudinta data Tara a gidan Kawarta Hadiza sannan Anty ta daura ta a machine Hamza ne ya kaita har can babban titi ya ajiye Ilham Suka Yi sallama tace Hamza Dan Allah ku daina shan wiwi,kafin na dawo ya kamata ace kun daina, Inshaallah Ilham zamuyi rashinki Babu Whot dake yau,Hmm karka damu Zan dawo Kunji,kacewa Sagiru ya Tara tattabaru da yawa kafin na dawo,dariya Hamza yayi yace salon ki cinye Masa ko? Uhm ta daga Kai,sallama ya Mata ya koma garin ita Kuma tana gefen titi tana jiran motar Almajirai ta Fito su wuce.

Taufeeq kwanansa daya a Yobe Manager ya dauko shi zai maida shi Airport zai koma garinsu suna hanyar Daji can wajen Gari hanyar daza ta kaisu Airport dai dai kusa da Inda Ilham ke tsaye tana jiran motarsu taga dalleliyar mota ta tsaya da alamar lalacewa tayi,Taufeeq ne ya fara fitowa,Da gudu Ilham ta fada cikin ciyawar dake gefen titin ta boye tana lekowa da kanta kadan tace Alqur'an Balarabe ne zai sace Ni,Kamshinsa ta ji me dadin tsiya,tace Kai ko mutuwa zanyi ne nake jin kamshin Aljanna Aljanna Haka,Kai kamar mutum Normal Bahaushe Kuma,Ganin Manager ya fito baki wuluk dashi Ilham tace Cab Yasin ga Dan Duna can Hausawa ne gashi Nan naji suna hausa sun bude gaban motar da Alama ruwa suke nema zasu zuba,Taufeeq yasan sun taba zuwa Nan Haka Neman sassaken bishiya Amma tsoron wajen yake ji yayi Dani da yawa.

A hankali Ilham ta fito a inda ta boye, a tsorace ta lallaba ta bayan Taudeeq ba zato ta daka tsalle da tafi a hade tace gata Nan kamo shi,wani uban tsalle ya buga yayi gefe harda faduwa a kasa,Dariya Ta Kama Manager da Ilham Suka dinga yiwa Taufeeq dariya,Ilham tace Yar Girl Dani kake jin tsoro Babba da Kai Lallai daga ganinka ba karfi zaka Yi ba,Mikewa yayi tsaye Yana muzurai Yana goge jikinsa,Ilham tace Kai Dan Baki me kuke nema a Nan? Taufeeq Harara ya watsa Mata yarinya mitsila da Iyayin tsiya,Ilham tace Dama idan ruwa ne sai na baku, Da sauri Taufeeq yace bamu pls cikin muryarsa me Dadi,Nan take Ilham taji Kamar tasan me muryar,,Ni tsoron hanyar nakeji Taufeeq ya sake furtawa,Da gudu Ilham ta koma Cikin Jakar kayanta ta ebo wasu Robar faro biyu data ciko da ruwan rijiya, sai pure water guda biyi a gyalenta a zubo gashin kanta Kuma a bude wani yalala har gadon Baya kamar Yar India. manager yace Ina Zaki ne Haka Naga Kuma da ruwa pure Water,Hmm ai Boarding zanje Birni in fada maka kasan Birni garin yan gayu shine Nima Dan ubansu zan shiga da ruwan Yan gayun nan Nima Ina Sha Ina yanga,Manager ya karba yana godiya Yana dariya.

Ilham tace ai wlh bazan yarda su rainani ba turanci kuwa sunzo gidansa Haka zan dinga tsantsaro shi,Ruwan Nan da kuka gani ba duka na Baku ba,hauka nake nayi muku kyautar shiga daka kayi kuka,ai tun a hanya Zan bi titi idan zan tsallaka a birni zan tafi Ina zukar ruwan gayu na Nima,Ina taku dai dai Har zubarwa Zan dinga Yi a titi kadan kadan suga Ni na fisu har zubarwa ma nake yi, Mu za a gayawa burni Saura kadan ma da tuni Ina Sha Wiwi naki Sha kawai banyi niyya ba,Amma ka ganni Kai Dan Baki Ni Ze Golden Girl ko? One In tow (town) kenan, Dande kawai karku ji sirrina ne shi yasa Amma Muguwa Kanwar Mamana sabo da ita na gaji na bar gida.

A sace Taufeeq ya kalleta tunaninsa ma kawai Shirme take Yi tunda yarinya ce ko kulasu baiyi ba da manager suke ta magana ta Sa Masa Dan Baki,Yana Gama Zuba ruwan motar ta tashi,tace Allah yasa mu hadu watarana a City Dan Baki Kai fa nake nufi ba wannan ba,Allah dazu Dana ji kamshim wannan na zata mutuwa zanyi na Fara jin kamshin Aljanna,Shi kanshi Taufeeq Jin yanda take magana ba tsoro gata Karama da ita ta bashi mamaki,Kamar tasan me yake cewa a ransa tace karfa ka ganni Yar karama,girman kauye ce tumburewa nayi,cutar shanu ce ta kamani na dade a duniya tumburewa nayi kawai karku rainani, cutar koshioko nayi, Taufeeq a Nan ta bashi dariya Wai Tumburewa tayi yarinya lafiyayya tace tumburariya ce ita,zasu shiga mota kenan motar Almajiran ta Fito daga kauye totse da Yara Maza Mata biyu a gefe duk da tarkacen Kayansu a saman mota,Ilham tace ga motar mu tazo sai birni,Tunda Taufeeq yake a duniya Bai taba ganin Mota Bus da paint na Light blue ba sai a motar almajiran ta Gama jinjiki motar,Suna kallon Ilham ta tafi da gudu motar ta tsaya,malamin da kansa ya dauki kayanta ya daura saman motar tare da Daurewa Ita Kuma ta daka tsalle ta shige ciki da pure water guda a hannunta.

Taufeeq yace Manager wannan ai Almajirai ne? Yes kasan yanzu ance wlh an Fara kai Mata wajen wasu malaman a gidansu dakin matan malaman Matan suke Zama, maybe can za a kaisu tunda kaga Haka,Allah ya kyauta Amma a Arewa suna Shirme wlh Sabo da wannan ganin bacin Rai irin wannan bana son Zama a kasar Nan,Yara kana na,kuma Bauta zasu yiwa Matan malaman cewar Manager Suka ja motarsu suka wuce Suma.
Cikin lokaci kadan Taufeeq ya koma Rivers State gida.
Suma su Ilham sun Isa Kano Lafiya aka saukesu a unguwar da Malamin yake wato Gwammaja.














AsmaBaffa.
[8/6, 12:44 AM] Sis Asma: 🔰🔰'YAR KWANGILA🔰🔰









NA KUDI






4









'YAR KWANGILA
IS DEDICATED TO
DR RABIU MUSA KWANKWASO.










Official






By
AsmaBaffa.












RASHIN SA'A COMPLT
DARI UKU NE 300.

TA GYARU COMPLT
DARI UKU NE 300.

'YAR KWANGILA DARI BIYU NE 200 GA MASU BUKAR SIYE...

Accnt number 2177560408, Yahaya Garba Muhammad,Zenith Bank.

Zaku iya tura numbibin katin MTN ta Sms ko WhatsApp ta Nan
08033933642.

Ga masu bukatar Transfer kati ko Vtu ga number da zaku Yi
09032409668.

'Yan Niger masu bukata ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39.








Page naku ne
Jikarkulu
Jameela Abdullahi
Rukayyatu










Taufeeq Yana komawa gida Amminsa kawai ya duba,Wanka ya fesa ya shirya cikin 3qtr da Riga T-shirt yasha kyau komai Daya Sa Silver and White har takalminsa,Abinci yaci ya dauki Key da kansa ya tuka kansa zuwa gidansu Mujaheed, Maman Mujaheed ya iske a kitchen tana Hada Abinci tare da Yan aiki, Gidane na gaske Hadadde na masu kudi Amma Bai Kama kafar na Taufeeq ba, Mama ce tace Yana side dinsa fa tare da su Sadeeq suna sana'ar taku ta Game,Murmushi yayi ya wuce part din Mujaheed, ya iske Su saddeeq da Mujaheed suna game a Tv sun hada,Yana Zuwa ya kashe game din,Tsaki Mujaheed ya ja yace wannan wanne wulakanci ne pls? Saddeeq yace yaushe ka dawo ne Man? Tun dazu na dawo,Magana zamuyi da ku fa akan Aure na da irin matar da nake so Kai Mujaheed zaka Nemo ta.

Saddeeq ya furta Muna jinka Muji irin Hadaddiyar da kake so a samo maka ita ko wacece wacce Ummi Zata kaunace ta,Dariya Taufeeq yayi yace Yan Iskan banza Bari kuji Ni yanzu na fasa auren burin raina, Kun san irin matar Dana ke so Amma yanzu na janye na fasa,zanyi aure ne a bisa dole, zabin Ummi wacce Zata yiwa Ummina abinda ta ke so ta kula da ita da komai shine kawai,na fada muku Ni wlh ko Bed bazan iya hadawa da wacce bana so ba.
Sabo da Haka Idan kun tashi Nemo min matar Nan a Nemo katuwa,kafceciya,Kamar basamudiya me karfi kirar maza,wacce Zata iya Daukan Ummi na me hankali Kuma wacce ta Saba da wahalar rayuwa,ba ruwana da kyanta ni,Dariya Mujaheed ya dinga yi Suna tsokanar Taufeeq.

Ilham tana ta kallon Birni tare da Matan da Suka Zo su biyu Binto da Ummi,sai maza da yawa an kaisu can wajen Malam an hada su a cikin Yara almajirai,kallona Binto tayi tace dama kema almajiranta Kika Zo ba makarantar kwana ba? Ae Mana yan garinmu ne Anty Bata so su sani, Ummi tace cab yo ni Ina ruwana da zan boye boye,Muna tsaye Malam yazo ba fara'a a fuskarsa ya daga Mana tsawa Kai kuzo muje gidan Matana a can zaku zauna, kayanmu muka dauka tare da binsa a baya,na dakko pure water na,Muna tafiya Ina zuka kadan kadan har Dan zubarwa nakeyi ni Dole na birge yan birni,Bulala naji malamin ya tsula min Wanda nayi zullo tare da sakin Kara yana magana yawu Yana fallatsowa daga Bakinsa Dan ubanki asarar ruwa kikeyi ba kyau Allah ya Hana Haramun ne, Aradun Allah Kika sake sai kin Sha doruna.
Shuru mukayi da mamakin zaluncin Malaman Allo.

Wace ce Ilham?

Ilham Abubakar 'yan Asalin Fulanin Yobe ne,Abubakar Iyayensa sun Haifi Yara da yawa Amma sai sun girma sannan suke mutuwa Abubakar shine na farko Kuma shi kadai Allah ya barwa Iyayensa,Yayi karatun Allo ya girma ya taso da arzikin kasuwancin Noma a kauyen Fulaninsu Rigar Dukko ganin Yana samu sosai Babansa Abdullahi ya siyar da Shanunsu kaf ya tattara ya siya musu gida a birni cikin Garin Yobe Suka koma can da Zama,Sannan ya bawa Abubakar jari ya fara sana'ar Siyar da robobi, Sosai ya fara samun arziki,Maman Abubakar Fatima ta damu akan yayi aure.

Abubakar Yana shagonsa na siyar da Robobi Hafsatu tazo siyen Kayan Azumi ita da kanwarta Anty Halimatu a Nan Abubakar ya ganta yaji Yana kaunar Hafsatu sabo da ba laifi akwai hakuri,hankali da nutsuwa a tare da ita,gata Kyakyawar gaske Fara tas duk da shima Abubakar fari ne Amma ta fishi hasken fata,Halimatu kuwa kanwarta wankan tarwada ce ita,a Nan Abubakar ya dage ya Kulla alaka da Hafsatu har ta bashi Address na gidansu.

Bayan sun Shaku da son juna Abubakar Abdullahi ya auri Hafsatu ,wacce Hafsatu Marainiya ce ba Uwa ba uba su biyu ne iyayensu Suka Haifa a hannun matar Babansu Suka girma sai Bayan anyi auren Hafsatu Babansu shima ya rasu.
Hafsatu tana dakin mijinta Da wata uku Anty Halima ta Hadu da Zubairu Rocket,Zubairu Rocket ya kware Wajen iya karya sabo da Yana zuwa birni kawo amfanin gonar Babansa,Haka ya tsara Anty Halimatu har sonsa ya kamata Ta Amince ta Aureshi Wanda Kayan daki ma Abubakar Baban Ilham ne yayiwa Anty da komai.

Hafsatu Allah ya yita me Neman kudi da Business kala kala Bata Zama,Haka tasa Yar Uwarta Anty Halima a ciki suna Yi tare kullum Anty tana hanyar Yobe harkar Business nasu iri iri.
Bayan shekara Daya Hafsatu Ta Haifo Yarta zukekiyar gaske kasancewar Hafsatu tayi makaranta har Secondary schl Abubakar yace ta zabi sunan da za a sawa yarta sai ta zabi Ilham a lokacin Sabo da su Fulanine Amma birni aka haife su.
An Haifi Ilham da wata Biyu Anty Halimatu dake aure a kauyen Rigar Arma ta haifo Yarta Bilkisu itama, daga lokacin Kuma iyayen Abubakar Suka rasu gaba Daya sai Yan uwansa da suke Kauyen Dukko Wanda Ilham ta rigada tasan kowa cikin Dangin Mahaifiyarta da Kuma na Babanta, bayan Ilham ta cika shekara hudu ta taso cikin gata aka samu wasu Yan fashi Suka shiga kasuwar da Abubakar suke siyar da kayan robobi Suka bude musu wuta Nan take Abubakar bullet biyar Suka shiga cikinsa ya mutu.
Hafsatu Tasha kuka Kamar ranta zai fita sanadin Damuwar ko sadakar arba'in ba ayi ba Hawan jini da Ciwon zuciya ya Kama Hafsatu ko kwana Uku ba ayi ba itama zuciyarta ta buga ta rasu.
Mutane sun Tausayawa Ilham.

Bayan Rasuwar Dangin Abubakar Suka ce zasu tafi Da Ilham,Haka wasu a Dangin Mama Suka ce suna son Ilham a Basu Amma Anty Halimatu tayi ruwa tayi tsaki tace ai tafi kowa kusanci da Hafsatu ita zata tafi Da Ilham, ta dinga Bala'i Dole aka hakura,Babu rabon gado ba komai ko malamai Bata Nemo ba,Bata Kira ko Yan Uwa ba ita da mijinta Zubairu Rocket Suka Tattara duk wata dukiya ta Hafsatu na Business da masu bashi da Suka kawo wasu dubu ashirin,wasu dubu Hamsim,wasu goma etc gaba Daya Anty Halima ta tattara ta kwashe komai ko Handkerchief Bata Bari ba na Hafsatu, Bayan ta maidani kauyen Arma garin mijinta Zubairu Rocket sai ta dawo ita da Zubairu Suka siyar da kadarar Abubakar har gonakin kauye tace Wai zata dinga juya kudin gadon Ilham idan ta girma zata bata abinta,ganin tana business sai aka yarda Aiko Ashe karfin Business na Hafsatu ne,lokaci kadan Zubairu Rocket ya tsara Anty Halimatu ya cinye kudin Nan tas,itama ta cinye wasu Suka Kare Amma kullum sai ta dinga dukan Ilham tana cewa Ubanki Bai mutu ya bar komai ba shegiya.

Anty Halimatu masifaffiya ce,Azzaluma,Bata da Imani ko kadan Kamar mijinta Zubairu Rocket ga karya ga cin amana,Rocket Yana Shan taba sosai ga rashin tausayi, Zubairu Dan Fulani ne Kuma Iyayensa suna raye da Kannensa Sune Suka lalata dansu Basu bashi wata tarbiya ba,tun Yana yaro abinda yaga dama yakeyi,gashi yanzu Iyayen nasa basa jin dadinsa ko kadan.
Tunda Ilham ta taso a hannunsu suke zaluntarta,duka kullum safe da Rana,tun tana Yar karama ake sata aiki,debo ruwa da aiki har ta girma a Haka.

tana Fara girma Anty take Daura Mata Talla da yamma da safe Kuma taje makarantar Allo,da kyar aka samu Babar Zubairu tasa Dole aka sa Ilham a makarantar boko itama Kamar yaran Anty Halimatu,Amma duk da Haka ba a sa Ilham a makarantar su Bilkisu ba sabo da tasu tafi tasu Ilham karatu.
Yaran Halimatu hudu ne Allah ya bata Bilkisu,Firdausi,Sa'adatu sai Auta Rukayyat.
Sune Suka taso Yan gata har girmansu,ba abinda suke Yi sai dai suci su koshi suje makarantar boko da yamma suje Islamiyya,Ilham kuwa komai na aikin ita keyi,ga duka,zagi,Talla da aikin gida sannan Bata zuwa Islamiyya sai ta Allo da safe kafin ta tafi ta boko, Ilham tana girma Suna Kara takura Mata,daga Nan Suka Fara dukanta da korarta kwana a kango ko gidajen makwafta,ko su hanata Abinci Amma sai ta gano Idan ta Basu kudi ko Naira Hamsim ce sai su barta ta kwana su Bata Abinci,hakan yasa ta Fara sana'a a kasuwarsu ta kauyen,tana karbar Kaya ta zaga a kasuwar idan ta siyar su Bata Lada,tana tallan Nama,kitse,Kashi tantakwashi,Zaren dinki,cashew,Mango etc,a Gari Kuma idan ba kasuwa tana sana'a iri iri har ta Fara karbar kiwon dabbobi Ana biyanta, Amma duk ranar da Bata samo kudi ba to Anty zata koreta ta kwana a waje,Hakan yasa ta yanke idan an koreta tana Jin tsoro sai ta tafi wajen su Hamza Yan shaye shaye ta zauna a wajensu daga Haka ta Zama kawar su Hamza,suna yawan taimaka Mata sosai Kuma ta kwana a wajensu suyi Mata Shimfida a gefe basa taba kawo Mata ko Zancen banza,anan ta koyi Whot sosai da game iri iri.

Ilham sabo da wahalar da take Sha kullum ta taso Bata da tsoro sannan Bata rashin kunya Amma duk Wanda yayi Mata sai ta Rama,ga Surutun tsiya, sabo da yawan zuwa birni wajen Dangin mamansu ta Dan waye ta Fita daban a kauyen,gata da basira ko me ta gani sai ta iya, girki ma ta iya sosai Sabo da yanda kullum ita ke yiwa Anty.
Ga Ilham da farin jini, su kuwa su Bilkisu ba wani da yake cewa Yana sonsu ko kadan,Basu da tarbiyya ko kadan.
Suma sun tsani Ilham bayan Ilham da kudin wahalarta ake musu komai Kuma tana Basu kudi sosai Amma basa gani ko kadan murna ma sukeyi an kaita Almajiranta.

Ilham Kyakyawar gaske ce Fara ce Amma ba irin fari fau ba, Round face ce da ita dauke da hancinta ba me tsayi sosai ba, ba Kuma ba gajere ba Hanci ne da ita me kyau,ga Ido Dara Dara farare Kamar Madara,gata da yalwal gashi har gadon Baya wani Kuma ya kwanto a goshinta,jikinta lumi ita ba me kiba ba Kuma ba ramammiya ba,ga diri me kyau,hips da tuwon mazaune,Cinyoyinta zuwa kafafunta mulmul dasu manya,lips dinta Pink Dasu,Bakin Nan Dan Karami dashi,Harda dimple dinta a kumatu idan tayi dariya,duk inda kake Neman zankadediyar yarinya matashiya Yar 17 to to Ilham ta Kai,kowa ya kalleta sai ya Kara Dan ma a kauye take ne.
Shine Tarihin Ilham Abubakar Abdullahi wacce taga rayuwa a kauye ta taso cikin wahalar rayuwa wacce aka santa da Ze Golden girl a kauyen.

Waye Taufeeq?

Taufeeq Abdul'aziz Rariya kenan.
Abdulaziz Dan Asalin zamfara state ne,Fulanin zamfara ne, su Hudu Mahaifansu Suka Haifa Abdulaziz shine Babba,sai Mata uku Haj Zeenatu,Haj Maryam ta biyu sai Haj Asmau.
Babansu ya rasu ya bar musu tarin dukiyar,gadon arziki sukayi tun Asalin danginsu a dukiya Suka taso,gaba Daya Matan suna aure a Abuja suna auren hamshakan masu kudi a Abuja,Suma masu Arziki ne da yaransu manya Mata da maza,Taufeeq baya wani zuwa wajensu sabo da basa kaunar Mahaifiyarsa ko digo.
Babarsu Hajiya Rahinatu wacce suke Kira da Anna tana jin dadin yaranta suna kula da ita.

Haj Zeenatu yaranta biyar ta tsaida Haihuwa biyu maza uku Yan Mata manya,samarin Kuma Daya ya girmi Taufeeq Daya Kuma Mate din Taufeeq,Yan Matan ma Daya tayi aure sai biyu suna karatu a Dubai.
Yaran Haj Maryam Biyu rak duka maza su ma mate din Taufeeq ne kusan,Haj Asmau kuwa yaranta Hudu Daya Namiji Dan 26yrs sai matanta uku Daya 17yrs sai kannenta.
Gaba dayansu Yan Boko ne na karshe cikin su Haj Zeenatu Babu me Degree Daya daga me masters sai me PHD,Yan gayu ne na gaske masu takama da Naira,ga Mulki da gadara,basa kaunar talaka ko kadan Haka jininsu yake har Abdulaziz Baban Taufeeq, tsakaninsu Da talaka suyi musu Aiki,Haka yaransu ma,Taufeeq ne kawai daban shi ba ruwansa harkarsa yakeyi da kowa idan ta Kama.
Anna ma Bata kaunar wani ya rabi jikinta sai Wanda ya fisu arziki ko ya kamo kafar yaranta a kudi.
Abdulaziz ne kadai Allah ya bashi da Daya tilo Taufeeq.

Abdulaziz Dan siyasa ne na gaske yayi senator sau uku a zamfara state,daga Nan ya Zama ambassador,ya rike secretary Gomnati na kasa,ga Business yanayi Kamar hauka,Neman kudi a wajensa Kamar zaiyi sata Baya koshi,daga Nan yanzu aka bashi babban mukami a majalisar dinkin duniya,ya Tara dukiya me yawan gaske,da Kadarori ga company iri iri da abubuwan Business kasar waje da gida Nigeria.
Tunda ya taso a duniya yake da Jarabar son Mata,Neman Mata Arna da musulmai,indai kina da kyau to kin Gama dashi,Anna tana Masa fada Sosai tasan halinsa Amma da yaga Haka sai ya Fara auri saki,duk wacce ya gani Fara me kyau sai ya auro ta daga ya shanye zakinta zai saketa,Gashi Bai taba samun Haihuwa ba,yaje asibiti da dama a kasar turai akace kwansa guda Daya ne a duniya da zai iya haifa.
Haka ya dinga auren Mata Yana sakinsu Yan uwansa kuwa su Zeenatu ba ruwansu su sai abinda yayi sabo da Yana da kudi.

Yana Haka watarana aiki ya kaishi kasar Isra'el,sunje wani kauye duba Yan gudun Hijira Wanda aka kashe iyayensu da danginsu,da yaran da basu ma san Iyayensu ba a Nan yanki Na Larabawan Isra'el ya hadu da Marainiya Aysha Ummin Taufeeq,Ya ganta kyakyawar gaske Bai taba samun mace irinta ba,gata Yar Talakawa Bata da kowa an kashe su a yaki, ganin farar fatar Balarabiya usul da kyau ya hakura ganin Bata da gata Iyayenta da danginta duk an kashe su a yaki ita kanta cikin Yan Hijirar ta taso har ta girma.
A Nan yace Yana sonta Nan take taga zata kubuta daga wahala ta amince ko ba komai Nigeria munfi su Zaman lafiya, a Nan aka taru da ma'aikatan da Suka zo a masallaci aka nada Mata waliyyar ya bada kudin sadaki Milliyan Daya In doller a aka daura musu Aure.
Anna tana gida sai ganin Abdulaziz tayi da mace balarabiya yar budurwa 20yrs yazo da ita, a Nan ya bawa Anna labarin Aysha,Jin talaka ce ba a San Asalinta ba suka taru dasu Zeenatu Suka tsani Aysha, a zamfara burunsu suzo su ci Mata mutunci iri iri,Aysha ga hakuri Bata kulasu ko kadan.
Tun Bata Jin Hausa har ta Fara koya.

Suna zaune a katafaren gidan mijinta Dake zamfara,Anna ta addabi rayuwar Aysha Baki daya sharri kala kala take hada Mata wajen Abdulaziz shi

Please Login or Register in order to submit comment