Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daya keyi achan baya yadawo masa,A wanchan lokacin yana ganinta cikin kuka ayanzu kuwa cikin tafiyarta irinta ta yara masu wayo yake ganin tana wasarta tana dariyar ta gwanin bugewa,bata ma kulasa duk da yana ganinta tana ganinsa.


Tun mutuwar nora dinsa yace bayason yin karatun likitanci bayan tabbatar da cewa dai tatafi domin dama danta zaiyi,shi burinsa dayatashi dashi shine karatun pilot waton matukin jirgi,wanda shikuma Al Amin nasa burin keman yayi karatun likitanci,wanda sai da mahaifinsa yabashi baki yace yayi yataimaki Al ummah saboda Alllah itama dasu uncle dinsa zasu samu lada wannan kenan.


Kaji dalilin zaman yayanku doctor akasar india, da kuma dalilin dayasa yayan ku yake zama india shida Al Amin har yazamana sun zamo manyan likitota akasar da batasu ba...

**********

*******

****

------------------------------------------------------------------

"Sarki Ali ne yaci gaba da maganarsa D'an uwana sarki umar a wanchan lokacin shine ya mulkar masarautar nan,yana "yaa norah wadda taci sunan kakarku hajiya sai kuma matarsa lailat ina fa'd'a make kawai duk da nasan kasani yadda zakaji komai yadda yake alabarin ne..yakai karshen maganar cikin wani yanayi yana jin komai yadawo masa sabo...



Hawayene Suka zubo a idanun mahir dasu yuhanis,da sumee da zuwansu kenan aka fara bada labarin sai da babu wanda ya lura dasu,sunyi sallama sai dai ba'a amsa musu ba shine dalilin dayasa suka shiga falon kaitsaye,Haka itama unni hawaye take zubarwa mai zafi maimartaba sarki Ali shine mai lallashin su,shine yafara lura dasu Nisa A tsayen dasuke ido jage jage da hawaye kyafato su yyi tahanyar yimusu Alama..


A hankali suka taka inda suka zauna akusa dashi suka sanya sa tsakiya,suna masu cigaba da zubar da hawayen su,domin su ana goyonsu ne lokacin basu san komai akan labarin ba sai yau duk Ammi na yawan furta musu sumusu Addu'a..


Share musu hawayen yayu yana furta musu kudaina kuka kunji "ya "yan Unni,kai suka d'aga masa da alamar toh,suna masu sake share hawayensu,"kara furtamusu yayi kumusu Addu'A kunji ita suke buk'ata agareku..



Yau ansamu long page😎


https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim

💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥


*MASU SON A TALLA TA MASU HAJARSU*

*SHOULD CONTACT ME VIA*

*+2348069059746*


------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

FREE PAGE2️⃣7️⃣


TYPING📲📲📲


Bayan dukkaninsu sun samu natsuwa sai Sarki Ali yatambaye su daga ina suke gida ko schl


YAr bak'ar wadda take kama da Dr.Ammar sosai ce ta furta" Abba muntaso daga school ne shine muka ce driver yakawo mu nan muganku.


Murmushi sarki Ali yayi yana furta" su sumayya uwayen yawo",sumayya datake d'an satar kallon mahir tad'an kawar da kanta gefe cikin jin kunya tana furta


"Allah Abba bana da yawo,Nisa ce tace sai munzo nan kuma gashi bamu ma gaya wa Ummi ba".


mugun duka Nisa takai mata Abaya Bayan jin kazafin da tayi mata, cikin shagwab'a Nisa ta furta Allah ni Abba ba ruwana itace tace muzo zata karbi sako gurin yaya mahir.


Abbah da jin wannan magana ta Nisa sai yayi murmushi irin nasu na manya dan dama dazu yaga yadda Sumy ke satar kallon Mahir Din sai dai bai kawo komai ba aransa,Murmushi yakarayi irin na jin dadi,sannan A hankali ya furta"Sumayya wani irin sako ne halan?sumayya dake cikin zullumi dama tana tsoron hakan tafaru dan tasa halin nisa wani lokacin bakinta baida sayi,shiyasa tun amota sai data kwatse ta,Dan ta girme ma nisa da shekara daya kuma tafita wayau ita nisa surutu ne dai bai wani sha mata kai ba kamar sumy d'in.


Gabanta ne yafad'i da jin tambayar da sarki Ali yayi mata in ina tafara Alamar rashin gaskiya sai kuma ta donar da kanta kasa,tayi danasanin cewa nisa gurin yaya mahir zata karbi sako dama cemata tayi suje sugaida Unni da duk haka bata faru ba,Kwadayin ganin mahir din take shiyasa tace sako zata karba awajensa,saboda yakwana biyu baije gurin Ummi ba saboda schl data rikesa.


Shiko mahir duk da yana kusa kuma yana jin komai dake wakana bai nuna ko a fuskarsa ba Alamar dasunan shi azancen..


'''''''ganin taki basa amsa,sai ya juya akalar tambayar sa ga mahir shiru mahir yayi duk da yaji tambayar da mahaifinsa yamasa "wane sako ne halan zaka bata"itace tambayar da yamasa,da gayya sarki Ali ya furta masa tambayar,kara furta masa yayi cikin raha kodai sakon sirri ne yana d'an kallon sumy dake gefensa,Ai dasauri ta mik'e cikin jin kunya tayi hanyar Babban falo,Dariya sarki Ali yayi irin tasu ta manya yana girgiza kansa.


Shiko mahir tunjin furucin mahaifinsa na karshe ya sunkuyar da kansa yana mai turar labb'ansa yana furta " nifa Abba bawani sakon sirri bane kawai dama yaya Aj ne yace zaiyi magana da ita ne"


"Touh itakuma wayar Umminku fa,ko bata da amfani ne " inji sarki Ali,bakinsa yakara turowa jin k'aryar tasa bata hauva,Amma akarfin hali irin nasa sai ya furta Abbah inaga ta lalace ne,Murmushi Unni tayi kawai ita da sarki Ali suna girgiza kansu ganin soyayyar ta yaran zamani.


Ahankali Unni ta furta tashi kaje Babana kasha magani ka kwanta tunda kaki cin abinci,Hararar Nisa Yayi dake jinhgine da kafad'ar mahaifinsu tana dariya kasa kasa na muguntar da tayiwa Sumy.


Ahankali mahir ya furta " Unni kinganta koh,wallahi yarinyar chan bata jin magana duk Abba da yaya Dr A suka sakanta ta "murmushi Unni tayi tana mai fad'in kyaleta kaji ai kaima unni ta sakantaka koh,Murmushi sarki Ali yayi ganin ydda zuri'ar tashi suke cikin farinciki yana jin ina ma Akwai Ammar dinsa akusa.MganarUnni ce data furta wa mahir ai kai Autan Unni Ne,ta tsayar masa da maganar zucinsa..


Autan Unni din da Unni ta furta ne yasanya yuhanis ta taso da sauri tana ita wallahi bata yadda itace autar Unni har Da Ummi ma tana maganar tana matso hawayen shwagwaba,tana mai zaunawa a d'ayan gefen Unni Sarki Ali murmushi yakarayi yana furta kyaleshi maji dadi na kinji ai ni ke kadaice AUtanah bada yaya dr ba bada yaya mahir ba,kivar Unni chan danata tarkacen kidawo nankinji yakai karshen maganr cikin wani yanayi dalilin saka sunan Dr Ammar,sbd haka suke kiransa yaya dr,Ita kanta Unni wani yanayi tashiga mai dadi jin karo nabiyu yakara sanya nur d'inta cikin zancen sa.


Nisa kuwa da sauri takoma inda Abban tana dariya tare furta yawwa Abbana ni kadai bada yaya rigammenme ba,ganin mahir na kokarin yimata rankwashi akai jin takirasa rigamamme.


Kyafci mahir yayi yana mai mikewa tsaye sallama yayi musu,sannan yayi ma Nisa Alamar zamu had'u,yayi fucewarsa yana murmushi.


A b'angaren sumy kuwa bayan ficewarta daga dakin sai tayi zamanta afalon jin zaman y isheta kuma tana jin nauyin komawa ciki ganin tabada kanta,dan taji kunya sosaiii,sai tayi ficewarta daga sashen fitar ta kenan ta hango motarsu Abdallah da yusuf tashigo Jikokin fulani,Abdallah d'an gurun yaya mustapha shikuma yusuf d'an wurin malan,Yayyen su Unni.


A hankali suke firarsu ta yan uwa shida sumy bayan gama parkng motar A chan achan Babban parking space dake a fadar yusuf ya wuce nasu sashen bayan gaisawa da sumy,shiko Abdallah yatsaya domin su gaisa kwana biyu basu had'u ba...



A bangaren Mahir kuwa bayan fitowarsa daga dakin yaduba falo baiga sumy sai yafito gaba d'aya cikin sashen ckin mamakin ina ta tafi kuma,a compound din sashen nasu yahango su ita Abdallah Akan wasu chairs suanat firarsu gwanin burgewa kamar wasu masoya,wani kololon bakin cikin ciki ne ya ziyarci mahir daganin Babban Abokin nasa da sumy zaune sunata raharsu,takawa yayi zuwa inda suke yayi,ya yyi tsaye,Abdallah ne yafara lura da tsayuwarsa Abayan sumy dake ta maganarta hankali kwance,lura da yanayin fusakarsa ne yasanya Abdallah tambayar bros lafiya dai koh?sai alokacin sumy ta gansa dasauri ta mike ta fara kame kamen rashin gaskiya... cikin "sanyin muryarsa ya furta lafiya qlau".Unni ce tace inkira mata wannan yarinyar,ohk Abdallah yafurta yana fadin" big girl sai anjima ko dan nasan dakyar mukara had'uwa kila.. inkoma gida kigayar mun da Ummi da husnat"toh tace tana mai rab'a mahir tawuce cikin gidan..


Abdallah ne yakara furta ma mahir yakannaka bros?kasha magani?eh kawai mahir ya furta wucewarsa cikin jin haushin Abdallah,bai tab'a jin haushin big girl din da Abdallah ke kiran sumy dashi ba sai yau,sauri sauru yacimmata Sumy da har tashiga falon..


Ke yadakatar da ita daga kokarin bude kofar second falon datake kokarin yi A hankali ta juyo suka had'a ido dashi yana mai kafeta da dara daran idanunsa masu yanayi dana da Dr ammar,Saurin duk'arcda kanta ta tayi kasa ganin irin kallon dayake jifarta dashi,wanda bazata iya jurewa bah,muryarshi ce tadaki dodon kunnenta,yana furta "wane sako ne zaki karba hannu na"? rass gabanta yafadi nan tafara kame kame duk da bata furta komai ba,ganin yanayin da tashiga yasanyashi dauke kansa,yana kawar da wanchna zancen ta hanyar tambayar ta maganar me sukeyi da Abdallah?


niko nace mahir kamanta da yan uwata kai ne 😄



Kanta tayi saurin dagowa danjin tambayar da yayi mata ido suka kara had'awa dashi tayi saurin janye nata ganin uwar hararar da ya sakar mata,murmushi ne ya subuce mata wanda ganin irin hararar da yayi mata sai taga yakara yimata kyau,Amsa masa tayi A hankali "yaya mahir gaisawa ce mukayi sai kuma firar school din mu danake basa,"ke uwar bada labari koh"shiru tayi jin abunda abunda yafurta girgiza masa kanta kadai tayi tana kara sakin murmushi a fakaice,Bata san cewa yaganta ba,shima ana bangaren murmushin gefen baki yasaki yana mai furta "meye na murmushi"kai takara girgizawa tana kokarin bud'a bakin ta kenan taji tafi abayanta raff raff ....



Waye kuke tunani kenan ya musu kutse suna tsaka da shan love 😍?shin ko dai mahir ya fad'a ne?


Like,share and comment pls.


Idan kina bukatar daga farko zaki iya tuntuba ta....

https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim

💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥

*masu son a tallata musu hajarsu should contact me via*

*call +2348069059746*

*chat +2348066995473*


------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

FREE PAGE2️⃣8️⃣



TYPING📲📲📲


Duk da bata juyo ba tasan aikin waye,Nisa ce ke sakin karamar dariyarta tana tare da tafa hannayen ta a hankali bayan isowarta kusa da sumy ta furta acikin kunnenta "me kika gayawa yaya mahir naga yana sakin murmushi"



Aiko da jin maganar ta Nisa sumy ta kai mata d'an karamin dundu abayanta,da sauri ta Nisa ta juya dagudu bayan jin dundun da takai mata tana furta sai nagayawa Unni da Abba soyayya kukeyi,ai kafin takai ga bude kofar Second falon na Unni har mahir ya chafko hannunta ido ya raina fata Nisa A hannun mahir dan tasan bawai wani raga mata yakeyi ba take ta raina kanta hawayen karya tafara matsowa tana bashi hakuri tun kan ya kai ga hukunta ta ta.



Kansa kawai ya girgiza yana mai furta "mai kikace zaki fadawa su Unni ne "?

Shiru tayi sai dai faman girgiza kanta kawai takeyi tana cigaba da kakalo hawaye,warning ya buga mata akan kar ta yadda tasanarwa da kowa tagansa tsaye da sumy,Sannan yasake hannunta yana furta stubborn girl.


,,,,,,sai da ta bud'a kofar shiga falon sannna ta juyo ta murgud'a masa baki.


Itakam sumy dariyar ta kawai takeyi kasa kasa.


Bayan wucewar Nisa ya kalli sumy kallo irin na zamu had'u,ya juya ya yayi hanyar nashi dakin wanda yake chan jere shidasu dr Ammar A wani lungu da yashiga ta falon unnin.


Bayan wucewarsa itama sumy ta taka afalon na unni da tunani barkatai aranta.


A bangaren Abdallah kuwa yanayin yadda mahir ya amsa masa ne bai masa ba,Amma sai bai kawo komai aransa ba,face tunanin kila ciwon kannasa ne ya sanya sa zama haka


*BUG*

Abangaren su halee kuwa wallahi mijin ki zaiyi faman da khady ta furta ne,yasanya Halee data debo yar madaidiciyar loma a spoon tagaza kai ta kan d'an karamin bakinta wanda yake d'auke da pink lips,dasuke shekin maik'o dan maganar ta Khady ita dariya tabata,sai da takai lomar abakinta tana tauna a hankaali sannan cikin sanyin muryar da zame maata jiki ta furta"meya sa kikace haka"?


Cikin zakuwa khady tafara jero mata halayenta wayenda suka zame mata jiki ko ince wayenda aka halicceta da su ,"kinga na farko ni ban masan yadda zaiyi dake ba mutun kullum ciki hijab tafurta cikin dariya ni na namatsu in ganki gidan mijinki inga yadda zaki yi"

A bangaren Halee murmushi kadai ke wanzuwa akan kyakkyawar fuskarta tana cigaba da cin abincnta hankali kwance,khady ce ta cigaba da maganar ta"mutun inkayi magana bai baka amsa ina lafiya" wannan karon Halee sai da tadara harda rike ciki,wanda sai da fararen hakoranta suka bayyana, itama khady dariyar takeyi ganin yar uwarta na farin ciki.


A hankali ta furta bayan gama dariyarta "to me kike so ince ne yar karamar harara khady ta watsa mata chan takara furtawa "bari kiji mama dije cikin d'an murmushi wanda ya fito da side dimple dinta da ya lob'a gwanin burgewa ta ce ni bari kiji koda nayi Aure babu wanda ya isa ya hana ni sanya hijab dina,sai maganar dake cinki ta biyu dan naga kina kalllon filet dina,kinfi kowa sanin ban cika son cin abinci mai nauyi ba saboda bana son inyi kiba inkoma mama dije tulluka gaki nan kina ta zama lukutarki takai karshen maganar cikin sakin karamar dariya,itama khady dariyar tayi tana furta nice yar lukuta,zan rama ,ai gashi nan ke kuma kina ta zama iccen kara mutun kamar iska yakwashesa inbanda wannann abun da wannana abun da bakomai cikin ki tana nuna breast dinta da hips dariya dukkan su suka kwashe da ita musamman Halee da maganar ta bata dariya...


Bayan gama cin abincinsu ne, Khady tafara yiwa Halee kalabar dogon gashinta mai santsi da dubara,ana take shaida mata....


Ai Baba Asabe ta fita tun karfe takwas tayi wurin zaman makoki mamaar Babar Aminiyarta larai,sai maraice tace mata zata dawo.


*Niko nace kaga su Baba Asabe an zake dayawa sai kace masu wata hidima ta biki tun safe sai maraice,ko da yake yanzu haka nan akeyi musamman ingidan mutuwar akwai maiko Allah yasa mudace muyi kyakkyawan karshe.*


Hamdala Halee tayi A zuciyarta na farinciki jin wannnan labari na Khady ganin yau zata wala,Tambayar khady tayi cikin yanayin farin ciki "to amma meyasa baki tada ni ba nayi ayyukka na"

"yau ni tace in yi Ayyukkan bake ba" khady tace mata hakan ne kawai.


Halee dai tasan sarai karya khady ta fad'a mata dan tasan wacece baba Asabe,Tunano yadda sukayi da Bba Asabe tayi ajiya kan kawai ta dade ba kawo ko sawu daya na ruwa ba domin harda marinta tayi wanda ita kuma jira ta tarar a bohol din....


Hawaye ne shar suka silalo mata a ido tayi saurin gogewa gudun kar khady ta gani,sai dai khady ta riga taganta kai kawai ta iya girgizawa tare da share nata hawayen daya zubo mata na tausayin yar uwarta.



........Mganar Baba Asabe ce ta fad'o mata arai kafin fitar ta zuwa gidan gaisuwa Halimatu!Halimatu shine sunan da BAba Asabe take ta kwad'a kira,wanda sautin neya farkar da Khady jin Bba Asabe na doso d'akin nasu ta mike da sauri bayan bude idanun nata kazazam ta yi saurin lullub'awa Halee bed sheet dake tsakanin filonta da na Haee Sannan ta isa bakin kofar da sauri alokacin itama Baba asabe takawo bakin kofar....


Gaidata ta Amsa mata cikin sakin fuska

Sannnan ta furta" ina yar iskar yarinyar nan take bataji ina kiran sunan ta bane ko wani sabon iskan ci ne ta tsiro dashi ehh"?takai karshen maganar tana kokarin yaye labulen dakin sai dai Khady ta hanata ta hanyar kara kare bakin kofar tana ta faman susar kai na rashin gaskiya Baba asabe kuwa kafeta da idanu kawai tayi ganin wani sabon iskancin gun yarta furta wa Baba Asabe tayi innata tashiga toilet ne,Uhm meye na kare mun kofa eh sannan uban mi takeyi acikin toilet din tabarni inata turar labb'a ga yar iska,Ganin tana neman tada HAlee da hayaniyar ta yasanya ta marairaicewa tana furta innata kaina ke ciwo gashi kinata d'aga mun murya aka.


Sassauta murya Baba asabe tayi tana furta inta fito kigaya mata tadaura miki abun karin kumallo da ruwan zafi sannan ta gyara mini d'akina na Alhaji nasan basai nace ba ashare agoge ko ina ,harda toilet,sannan intagama acika kwannan gidann nan kuma akaimani ruwa makewayi na,saura kuma ki sanya mata hannu tunda nasaka ki tana gama maganar ta fuuu ta fice daga gidan har ta kusa ficewa khady ta furta inna ta inazaki tunda safen nan,gidan larai zani mahaifiyarta tsohuwa ta cika dazu anfada amasallaci,Ayyah khady ta furta" Allah yajikanta da rahama" Amin Ta furta tasa kai ta fice gidan.


KAI BABA ASABE AJI TSORON ALLAH WANNAN SONKAI YAYI YAWA.


Bayan fitar ta ne khady tayi dukanin ayyukan da Baba asabe yar sonkai ta lissafawa Halee domin tasamu koda hutu yaune kafun dawowar Baba

Adee.




Bayan Gama wannan tunanin sai ta fara jan Halee da fira duk da ba duka take amsawa ba domin har yanzu akwai sauran tunanin mafarkin nan aranta dakuma zaginta da Baba asabe ke yi.


*GUSAU*

A Bangaren sarki Ali kuwa bayan ficewar Nisa A dakin ne ya furtawa Unni "ya "yanki fa kamar akwai wani al amari atattare dasu ni gashi tuni har nafarawa ba indiyen yaronki kame,sai kuma naci karo da wannan sabon al amari yakai karshen maganr yana murmushi,murmushi Unni tasaki itama tana furta to dad'a yaran yanzu ba,a gane cikin su ta yuyu akwai wani abun atsakanin su amma suna boye wa ne duk da nasan Baaba na baida nuk'u nuk'u a irin wannan maganar kamar Ammar wanda har yanzu ko budurwa baida ita gasu girma nata zuwar musu gaskiya insuka dawo ka nema musu mata ko cikin ya yan kawayenka ne na matsu inga jikokinmu takai karshen maganar cikin dan murmushi najinin larabawa da fulanida ke yawo ajikinta,shikansa sarki Ali murmushi yayi yana furta gaskiya kam dole in nemo musu mata tunda har gimbiya sarautar mata tafara maganar jikoki agabana yakai karshen maganar yana leken fuskar Unni data sunnar kasa na kunya.


Wallahi soyayyar tsofaffin nan na burgeni...😄


Sai da taga yajanye daga kallon ta dayake yi sannan tacigaba da magana,maganar Ammaar mu kyaleta kawai Adili kabar ta bamusan Alkhairin da ke shirin shiga atsakaninsu ba wanda Allah ne kadai yabar wa kansa sani.


Hakane sarki Ali ya furta sannan yakara furtawa su mutanen india mubarsu sudawo muga inbasu fitar ba sai anema musu, shi yarima inbanda kaddara ai dayanzu da matar shi ahannu Allah ya jikanki norah keda mahaifanki,Ameeen suka amsa su duka cikin wani yanayi shikuma Al amin Auta ta zan bashi inyanaso..Yakai karshen maganar yana murmushi,itama Unni murmushin kadai tayi tana furta Allah yatabbatar da Alkhairi,Ameen sarki Ali ya Amsa.


yana mai Mikewa tsaye rawaninsa yanad'a wanda da taimakon Unni yadaurasa sannan ya sanya alkyabbarsa wata colour maroon mai stone da wata zaiba abun sai wanda yagani.


Shigowar Nisa da minti kusan Uku sai ga Sumy tashigo,A hankali sarki dake gyaran Alkyabbarsa yabfurta y"a yan ummi nizan koma fada,yaushe zaku wuce ne,cikin sauri Nisa ta Amsa da Abban Yanzu tana zunburarar baki dan duk gidan ya gundureta tunda mahir yayi mata rankwashi akai,



Murmushi kawai Unni tayi tana fadin har angaji damu kenan?kai ta girgizawa unni tana mai kara turo d'an karamin bakinta gaba.


Sarki Ali kuwa yar dariyah yayi yana furta waya tab'a mun Auta nah yana murmush,ai kamar jiran tambayar tasa takeyi sai ta fashe masa da kuka,jawota yayi yana lallashi yana kara tambayar ta meya faru?.



In sha Allah ayanzu har weekend zaku rika samun update domin namatsu mu gama book one.


DAGA ALKALAMIN✍️

💫FA'EEH BG💫


Pls like,share and



comme



💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥


*masu son a tallata musu hajarsu should contact me via*


*Call+2348069059746*

*chat+2348066995743*


------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*



*💫P.E.W.A💫*


*Home of perfect essential writer's* together we stand🤝


*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*


*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*


EPISODE1️⃣

FREE PAGE2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣



TYPING📲📲📲



Shiru tamasa tana mai share guntun hawayenta dake d'iga a bisa beautiful face dinta,Auta meya faru halan waya tab'aki?shiru tamasa.


Abangaren sumy kuwa cikinta har ya d'uri ruwa tsoron guda kar Nisa tamata b'anbarma a gurin,


Ido suka had'a da nisa sai ta marairaice mata,ita nisa abun ma dariya yabata sai ta dauke knta kamar bata ga rokon datake mata ba ba ido.

A hankali Nisa ta furtawa sarki Ali cewa"Abba ni Ummi kawai nake son gani ni ba'a mun komai ba.

to yar Ummi ku dauko jakunkunanku driver yakaiku sai in saka fadawa su raka ku basai kun kira drivern ku yazo ba,toh sukace,sallama sukayi wa Unni bayan sun dauki jakunkunansu,suna fice dga sashen D'ai daga cikin manyan motocin masarautar suka shiga tare da mota biyu wadda taraka su,shima sarki Ali bayan wucewarsu masallaci yanufa dan gabatar da sallar la'asar data gabato.


Bayan fitar su dakin na Unni sai ta d'aga waya ta kira Ummi bayan ta bada Umurnin gyara inda sarki Ali ya ci Abinci da tattatare kayan da akayi amfani dasu.


Dialing numban da akayi saving da sister tayi,ringing biyu ba'a d'aga ba ana ukun ne aka daga muryace irin ta Unni sak tayi sallama Bayan Unni ta amsa mata ta dayan b'angaren aka kara furta yaya yakike?Lfy lau! yagida daga bangaren Unni,Lfylau Ummi ta furta Ya Hamma Aliyu yake? lafiya kalau yake yanzu ma yagama ji da rigimar ta gidanki'Murmushi Bangaren Ummi tayi bayan jin maganar da Unni d'in tayi tana furta ai yuhanis rigimar ta sai ita yaya.

Murmushi ta d'ayan b'angaren Unni tayi tana furta ai gasu nan ma sun kamo hanyar dawowa.

ohk! da har sunce ma driver yadawo bayan isha'i Ashe ba dadewa zasuyi ba.

Unni ce tace wallahi sister yar kice tasaka rigima tana son taganki,dariya dukkaninsu sukayi na sakalcin Nisa shekara goma sha tara Amma har yanzu kamar yar goye intana wasu abubuwan.

Tsaigaita dariyar tasu sukayi Bayan Unni ta katse firar tasu ta Nisa ta hanyar furta Albishirinki sister tana murmushi ta d'ayan bangaren Ummi ma murmushin tayi tana furta goro fari,kuma na bawa Ammie ta cinye,tana dariya, itama Unni dariya tayi tana furta kinma kankuwa huta bari inkoma da labarina takai karshen maganar ckin murmushi...


Yayah!yayah!tawa yi hak'uri Ta b'angaren Ummi ta furta.

furucinta duk sai yasaka su yin shiru saboda wadannan kalmomin sune kanwarsu laila ke yawan furta ta agaresu musamman

Please Login or Register in order to submit comment