Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shojojin arado baka ga makamanshu ba, shunfi namu arado Kuma anzuba shu gurin da yawa kamar shuna gadin wani agurin..

Cikin b'acin Rai ya da d'aga murya ya Furta " wai su wane ne Suke muna zagon k'as a suwaye,duk wani shiri namu suna kan gaba suna rusa muna shi,suwaye muna zagon k'asa Mai muni agare mu ya iyar da maganar cikin k'araji tare da Yanke Kiran...

My team yayi dialing cikin b'acin Rai... bayan d'aga Kiran ne muryoyin su suka fara Bada sauti cikin tashin Hankalin Jin muryarsa Jin Ya Furta kusameni gidan shak'atawa ta yanzu,oga lafiya dukkanin su Suke tambaya inada ya Yanke Kiran batare da yabasu Amsa ba...

Ko minti ishirin ba'ayi ba,sai ga wasu aranayen jif sun shigo gidan bayan wangale musu da aka Yi,parker motocin sukayi a inda yadace.

Babban falon dukkaninsu suka dosa cikin tashin hankali na Rashin sanin Abunda Yafaru Wanda sak'e sak'e yadabaibaye zuciyarsu na dalilin Kiran gaggawar da yasame su...


Samunsa sukayi tsaye ya rungume hannaye abayansa Yana sabbatu shi kad'ai
Yana Furtawa shin wannan Mai muna zagon k'asa taimakon mu yake Yi ko cutarmu,a iya binciken danayi su wad'annan Yan sandan da muka kashe kosu basu San dalilin dayasa aka sanyasu k'one gidan ministan (S.I.C) ba da iyalansa
Sun dai bi umurnin sane kowaye tabbas akwai Wanda yakeda sirrin mu Bayan (S.I.C) minister,dole muk'ara tsaurara Al amurranmu...

Minister iyaka Muradi ne Dake da mugun tsoro ya Furta cikin d'an tsoro da tashin hankali kardai ace fatalwar minster Umar ce tadawo Dan d'aukar fansa duk da bamu muka k'onasu ba,dukkaninsu dariya suka Sanya duk da tashin hankalin da Suke ciki Banda malan,Dan maganar tabasu dariya

Senator Jamil Babuga ne ya Furta haba kaiko minister aimu ko fatalwarsa tadawo muba Abunda zata Yi muna Kai zata Nema tunda kaine d'an rahoton mu Kai ne Mai yimusu kutse da lamarin su Kai da captain Anas Lemu yakai karshen maganar Yana dariya,Shima Captain Anas dariyar yayi Yana Furtawa senator Jamil ai za,a fara dakai Dan kaima Mai laifine,Emir Kabir Saraki ne yadakatar dasu tahanyar Furta ba wannan ba,yanzu dai oga meye abunda ya faru...

Cikin d'an Yana Yin hasala malan yazayyane musu komai Akan farmakin da yasanya Akaiwa Sarki Ali Da Dr Ammar,inda yasanar musu sojojin da akace anbaza awurin Wanda shikansa abun yad'aure Masa Kai na tunanin ubanda ya turo sojojin,dukkaninsu sunji faduwar gaba sosai musamman captain Anas Lemu Dan basu Yi zaton haka ba,Kuma tabbas da gaskiyar ogan nasu akwai wata ak'asa duk agamata tabbas akwai Wanda yasan da Shirin ogan nasu,duk da kosu bai sanar musu da Shirin ba,Dan bazasu manta da yadda wanchan karon aikin da suka Bada da hannunsu ya chanza ba..



TWENTY TWO YEARS BACK ....
WAIWAYE ADON TAFIYA...

A chan Baya...

K'ungiyar "Yan taadda ce da tayi shura ajihar zamfara dama wajajen zamfara ma'ana k'auyukkan zamfara,wadda kusan kullum sai an watsa labarin sunkashe mutane sun tada k'auye,sun sace dabbobi da dukiyoyin Al umma sannna sunyi kidnapping na bayin Allah,Ako dayaushe fama akeyi dasu har yanzu Allah Bai kawo k'arshen su ba..

A bunda ya faru achan Baya......

Cikin k'ungurmin daji ne da ya kasance d'ai daga cikin manyan dazukkan Dake cikin jihar zamafara Wanda Namun Daji kad'ai ke rayuwa agurin ada, Wanda a yanzu Kuma b'arayi suka maidasa mafakarsu,suna rayuwa aciki su wayen nan "Yan ta daddan.
Zazzaune Suke akan wasu kujeru su biyar oga Afarkon layi,sai senator Jamil Babuga da captain Anas akusa dashi,sai emir Kabir Saraki,sai minister Isyaka Muradi,dukkaninsu face mask ne afuskar su sai wasu irin mutane dazasu Kai dubu yawansu kewaye dasu da manyan bindigogi da sark'okin albarushi shigarsu Babu kyan gani kowa yasha uban rawani kamar wasu sarakuna wasu bula wasu bak'i sai warin suke tashi agurin da warin tabar da Suke zuk'a da ya garwaye wurin Babu dadin shak'a..

Shigace dai Dake nuna alamar su tazamansu Fulani da zabarbarbawa,wasun su sun Tara uban gashi kamar ka kitse sa kamar dai yanayin mutanen Mali,gasu nan dai ba maganar kallo biyu saboda in ka kalle su har wani mazari jikinka zai dauka...

Oga ne yake magana,Yana Furta tabbas duk da yake d'an uwana ne zanyi maganin sa tunda har yanemi ya tona mini asiri a idon duniya ta hanyar bincikensa tabbasa bazan tab'a ragama Masa ba, duk abubuwa da na shanye akan gidan mu na wannnan sarautar datake mallakin mu wallahi bazan tab'a rufe idona akan wannan ba,tun lokacin da minister Isyaka Muradi yasanar Dani cewa sunyi akan wannnan k'ungiya binciken su zaizo kanmu Asirin mu Yana Shirin toniwa, Kuma duk Wanda aka bincike sa Asirin sa take yake bankaduwa a idon duniya,nayanke wa kaina da ya tona muna asiri,gara ayo mani kidnapping na D'an wana Umar da iyalansa in kashe da hannu na sannan in hau karagar mulkin dayake tak'ama da ita shida Wansa,wadda nadade Ina mafarkinta tun kafin rasuwar Mahaifina,Dan shiru yayi sannan ya cigaba da magana Yana kallon wayen nan k'azaman mutanen Ina ga sunyi Rabin shekara jikinus baiga ruwa ba saboda tsaabar warinsu... Na Baku damar ku shiga har fada duk yadda zakuyi ku yo kidnapping nasaa shi shida iyalansa,Amsawa sukayi da zaka ga aiki oga angama.

D'ai daga cikin su ne fuska ba annuri ya Furta ya mutsatsiyar hausarsa da ta Had'a da fulatanci "oga Koda Kisha ne ayi ko wayaso yashiga Sha kanin mu da aikin "
Kai malan yad'aga cikin Bada umurni, Bindigoginsu suka d'aga sama suna harbawa suna ihu Mai ban tsoro ...dakatar dasu Emir Saraki yayi ta hanyar Furta sai kunyi shiri Mai kyau Dan Shima minister Umar wayaune dashi,Amsa Masa sukayi da angama..

Buhuhunan kud'ad'en fansar Al umma ne da Suke k'arbo kwana kwanan nan daga gidan tsohon shugaban k'asa Dr Lukman Murtala Mon na fansar yayansa guda hud'u mata biyu mata uku wayenda akayi kidnapping daga zuwa biki ak'auyen Babban nasu da ya tilasta musu zuwa kasancewarsu Mai son sada zumuci Maison zama da Yan uwansa duk da yabar su achan Yana taimakonsu da biyarsu..

Buhu shida suka jawo na Yan dubu dubu b'arayin suka jawo suka ajiye atsakiyarsu oga Anan take aka zazzage kud'ad'en ana n gurin oga yakasa Kashi bakwai su Kashi d'ai d'aya Yan dabar Kashi biyu,sai na sayen sababbin makamai Kashi d'aya na informer Kashi d'aya ak'alla kowannen su yatashi da million ishirin ishirin,Sauran tumaki da dabbobi suka bar musu amatsayin k'arin ganima agare su murna sukayi sosai ganin tarin dukiyar da aka bar musu..

Bayan watsewar Taron ya ta addan suka fara shirye shiryen shiga fada Banda gobe...

Sai dai Abunda basu sani ba duk wani Abu dasuka tattauna ayanzu Yana recording awata "yar k'aramar na'ura Dake mak'ale a cikin agogon MALAN da matar sa tamasa kyautarshi...

Geng geng
Taufa Al amarin nan yafara rikicewa
Kaji wata sabuwa✍️✍️✍️

Mudai Allah ya Yi muna tsari da wayen na. Ya taaddan Allah karka basu iKon Had'a hanya damu ka Kara kare mu🤲🤲

Mu had'u gobe in Allah yakaimu Dan Jin yadda zata kaya...


Kuyi hakuri ba editing cos am tired Kuma bana da lafiya Ina maneji ne kawai...

Like share pls and comment ✍️✍️✍️✍️


💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Firstlady 🙌🙌


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️is migthier than the sword 🗡️*


*Free*📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣8️⃣


*Kuyi following D'ina A*
*Arewa books,@Fa'izatou*
*Wattpad @Fa'iza murai*🙏🙏🙏


TYPING📲📲📲


••••••••••∆••••••••••••∆••••••••••∆•••••••••••∆
×××××××××××××××××××××××××××××××××
<<<<<>>><<<<<<<<<<<<<<<<<<<>>>>>>

......sun shirya tsaf Dan Kai farmaki a fada,sai dai sunyi Rashin sa,a domin a safiyar data kasance saura kwana d'aya su shiga fadar,suka samu labarin gobara ta tashi agidan minister Umar Wanda agidan babu Abunda aka fitar agidan harsu kansu sai dai gawawwakinsu da duk suka cinye da wuta.

Labarin ya riski oga agidan shak'ata warsa yashiga tashin hankali ma tuk'a domin yasan wannan ba aikin su bane ba shine Abunda suka shirya ba dan k'ara tabbatar wane yayi Kiran sauran Dan Jin yadda akayi,in su suka cinnawa gidan wuta tunda yabasu umurnin kisa,..

Bayan gama sauraren sa Babban b'arawon yasanar Masa da basu chanza komai ba hasalima su yau ko cikin gari basu shigo ba sun tsaya shirye shirye ne,yanzu Suma suka samu labarin wutar daga d'ai daga cikin informers nasu Dake cikin garin, daga nan ne suka Sanya dogon bincike harsuka gano wayen nan "Yan sandan nan guda biyar nada Sanya hannu acikin k'ona gidan sarki Ali Umar murai,minister of security and investigation crimes,har sukayi nasarar kamo Yan San Dan nan suka wahalar dasu ta hanyoyi masu yawa dan duk suyi bayanin dalilin Wanda yasanya su cinnawa gidan wuta dakuma wane ne shi,duk wahalar dasuka Sha kuwa basu sanar musu Wanda yasanya su ba da dalilinsa inda hakan ne yabawa oga damar kashe su duka wannnan kenan.


Emir Saraki ne bayan gama tunanin sa yasauke ajiyar zuciya Yana Furta yanzu dai muk'ara shiri Akan wannan mission d'in na gidan tsohon gwamna Alhaji mukhtar,cigaba da tattaunawa sukayi yadda zasu k'ara b'oye kansu wa duk wani Wanda yake Shirin Yi musu shigo shigo na shigo ba zurfi a alamurransu


*A MAFARKI NASANTA 📚 DABAN YAKE DA SAURA*

••••••••∆••••••••••∆•••••••••••∆•••••••••••••∆••••

*BUG*

A b'angaren su Halee kuwa, A Ayau ne suka gama zana jarabawar karshe a secondary schl,ta fannin soyayyarsu da Dr.yusuf sai Abunda yak'ara yin gaba,Baba Asabe kuwa har yanzu tana nan tana cigaba yad'awa Halee maganganu tare da wahalarda ita da musguna mata cikin ruwan sanyi.

Yau takasance Lahadi Halee ce Gaban murhu cikin madafa sai faman hura wuta takeyi inda wutar tak'i kamawa saboda kasancewar makamanshin wutar d'anyu ma,ana itace,lu lu eyes dinta sunyi jawur na hayak'in da ke shiga cikin su.

Inna Asabe ce cikin d'aga murya take Furta ke Halimatu wai Dan Rashin mutunci har yanzu kina nan kina iskancin naki da son jiki tun d'azu hura wuta ya gagara eh! Yar iskar yarinya ke komai nasa ka ki sai kin mini shashan ci aciki..

Cikin sanyin jiki da sagewar gwiwa Halee ta Furta"Baba Itacen ne Basa ci"k'aton tsaki Baba Asabe tasaki tana Furta nabaki nan da minti goma ki Had'a ta inba haka ba wallahi sai na lakad'a Miki dukan tsiya agidan nan sakarya kawai Sha Sha tsintacciya yar gaba da fatiha ...har tagama zage zagen ta da fad'anta Halee bata d'ago Kai ta kalle taba,sai dai cikin ranta tana Jin zafin duk wata kalma ta b'atanci agare ta domin dukkanin kalaman da ta Furta mata ayanzu kalamai ne da ta Saba dasu in dasabo sai dai haryanzu sune abubuwan da takasa sanyawa zuciyar hakuri akansu takanji matsanancin zafi aranta aduk ranar da Baba Asabe ta Furta mata su wasu lokuttan ko baccin kirki bata iyayi take Kuma nan ciwon ta sai ya tashi..

Bayan wucewar Baba Asabe ne tasanya kyawawan yatsunta tashare hawayen fuskarta na bak'inciki da Kunar Rai tana cigaba da huraa wutar har tasamu cikin Ikon Allah wutar ta ruru duk da Itacen yanayi Yana mutuwa inka kalle ta gwanin tausayi kyakkyawar fuskar nan tata duk ta yamutse,ga kwanciyar busashen hawaye nan afuskarta sai dai natsuwar ta da bata gushe ba in ka kalleta zaka ganta so calm kamar babu Abunda ke damunta arai ko yake ci mata Rai..

Khady da tashin ta kenan daga bacci ganin bata ga Halee a gafen ta ba yasanyata fitowa daga cikin d'akin Dan tasan tabbas tana nan tana yin bautar da ta Saba,tasan ko yau Baba Asabe sand'o tayi ta tada Halee d'in.

A hankali ta zauna gefen Halee a Cikin kitchen din wadda ta buga tagumi da a alama bata ma San da zuwan ta gurin ba,Halee Dake cikin dogon tunani Jin anjanye mata hannun a hab'arta yasanyata Duban gefen da Khady take zaune akusa da ita, Had'a idon da sukayi da Halee ne ya bawa hawayen Dake mak'ale a idonta damar fitowa na tausayin yar uwarta naganin yadda fararen kyawawan idanunta suka rune sukayi jaa kamar garwashe,hannu tasanya da sauri ta goge su gudun Kar Halee tagani,sai dai Ina ta makaro domin Halee ta lura da hawayen itama nata hawayen tashare a kaikace,cikin dauriya ta furtawa Khady
" har kin tashi " tausayinta ne ya K'ara kama Khady Kai kawai ta iya d'aga mata b tare da Furta mata komai ba.
Cigaba da hura murhun sukayi atare,Inna Asabe Dake tsaye tana kallonsu ne taja wani mugun tsaki Mtsww Wanda yasanyasu duban inda take tsaye Dan basu San da tsayuwarta gurin ba.

'cikin masifa ta Furta Khady "ke shalele uban wa yakawo ki nan eh"

Cikin tun zurar Baki Khady ta Furta "bakowa" tsaki Baba Asabe tak'ara ja sannan kamar an janyeta tabar wurin fuu tare da yiwa Halee mugun kallo.

•••••••••••••∆••••••••••∆••••••••••∆•••••••••••••∆

*Few minute later in the moment*

Baya sungama cin abincin su ne wayarta tayi k'ara
D'agawa tayi cikin yin sallama da zazzak'ar Muryar ta,A D'ayan b'an garen Dr.yusuf Shima k'arba mata yayi cikin farin ciki inda ya Furta " wa ailaiki Salam zaujati " wani kyakkyawan murmushi ta saki Wanda duka gab'b'ansa sai da suka Amsa,Dan tana mugun son ya kirata da wannan sunan,gaisawa sukayi irin ta masoyan nan da suka mutu cikin kaunar junan su,shiru ne ya biyo Baya bayan gama gaisawar tasu inda Ahankali ta tsinkayi muryarsa yana k'ara Furta

" Nurul Qalb na matsu lokacin Auren mu ya zo inganki Gani ga ki kina mun kallon soyayya da kyawawan idanun na naki,nikuma na Miki kallon k'auna" yakai karshen maganar Yana sakin murmushi Mai had'e da dariya.

Murmushi tasaki itama tare da Jin kunya ta Furta " ai lokacin Yana kan hanya ya kusa isowa"
dariyar yayi sosai na furucinta sannan cikin murmushi ya Furta Allah ? Dagaske

"tabasa" Amsa

Cikin sakin yar karamar dariyar itama.

Cigaba da maganar sa yayi "Kinga yanzu in muka Yi Aure Hankalin ki zai k'wanta domin daga lokacin ko spoon bazaki k'ara d'auka ba nizan dinga girka Miki Abinci in rik'a ciyar Dake in shayar Dake da hannuna ,sannan in Miki wanka in shimfid'ar Dake kamar jaririn k'wai ke komai ma nizan rik'a yimiki sai dai kizamo miji na zamo mata Arik'a Kirana da Mijin Hajiya ....

Duk da kunyar da maganar ta Saka ta ji Bai Hana ta darawa ba saboda sabon da ke tsakaninsu domin kyalkyalewa tayi da dariya kamar ba Halee ba Dan ba kasafai takeyin irin dariyar ba,sai ayanzu da Allah ya jefo Dr .Yusuf cikin rayuwarta.

Firarsu suka cigaba dayi cikin nunawa junansu kulawa da soyayyar junansu gwanin burgewa.

Khady Dake kallon su Halee cikin burgewa ta Furta Azuciyarta itama Allah yabata Miji irin Dr yusuf Wanda zai rik'a nuna mata soyayya irin haka Dan su Halee Soyayyar su na burgeta.


*GUSAU*
Ayaune za'a yi Taron bud'e Babbar Asibitin .
Shiri na musamman akayi domin bud'e katafariyar Asibitin.
Dukkanin familyn sun hallara a masarautar don Taya murnar bud'eta,kowa kagani yaci ado na musamman tundaga k'anana har manya,girke girke akayi masu Rai da lafiya.

A b'angaren uwayen taro kuwa sun shirya tsaf,dukkaninsu sunyi kyau cikin wasu aranayen suit farare,musamman Ammar sai yazamo kamar wani tauraro acikin taurari duk inda ya wulga sai Anmasa kallo biyu,kyawonsa yak'ara bayyana kyakkyawar fuskar nan ta karayin wani kyau na musamman dogon hancin nan nasa yak'ara tsawo kamar biro chocolate skin d'insa tak'ara yin glowing na musamman,pink lips nasa Suma sai shek'i sukeyi na mask'in man Bakinsa,manyan idanunsa sun k'ara kyau sunyi wani haske kamar an musu wankan Madara sai k'yalli sukeyi acikin su kamar anshafa musu Mai Zara Zaran eyelashes dinsa sun k'ara k'awata idanun nasa kasancewarsu cikakku masu tsawo tare gyarar sa da take kamar anyi shaping nata, mai yawa da ita atsare,Masha Allah kad'ai zamu ce.

Su Nisa da sumy da Inayah sun Sha wani bugaggen less Mai shegen taushi Wanda yaji duwatsu ta ko Ina,su Unni ma less ne sukayi anko dashi su uku Ummi,Mama dije,Dady soja Shima ansha kyau cikin wani had'add'en yadi,sarki Ali Shima yadin ne ajikin sa sai wata had'add'iyar alkyabba da ya d'ora akan yadin sai walk'iya takeyi,su hajiya ma ba,a barsu abaya bah,dasu Yaya mahir,Abdallah da Yusuf kowa kagani yasha kyau.

Zazzaune Suke acikin katafaren filin Asibitin Bayan isowarsu ,komai atsare afilin da aka k'awata musamman yadda kasan wata sabuwar duniya.. sashen maza daban sashen mata da ban kowa an ware Masa gefen sa.

Manyan bak'i ne aka gayyata tundaga
Tunda sarakuna, shugaban k'asar mu na yanzu Mai ci Babanku😁Bola Ahmad tinubu,da Sabon Gwamna Dr.Bello Muhammad matawallen maradon da wasu daga cikin manyan manyan gwamnonin Arewa, da sauran masu rik'e da muk'aman gwamnati tundaga tundaga kan Yan majalisa da ministota d.s.

Sai shuwagabannin Airforce duk sun halarta gurin Babu kakin da Babu agurin tun daga Sojoji, custom...

Sai shuwagabannin k'asashen waje America, London, China,Korea musamman sunzo Taya wayen nan gwarazan likitota murnar samuwar wannan Babbar Asibiti.

Sai Kuma abokan kasuwancin sarki Ali Dukkaninsu sun hallara A gurin na kasashe da dama Dan Taya sarki Ali Murnar Bude wannan Asibitin, Dukkanin wasu shuwagabannin na manyan asibitotan Dake k'asahen waje sunzo dakuma colleques dinsu Dr.Ammar na India dama na sauran k'asashe,k'ungiyar UNICEF itama takawo jiki Dan tayasu murna.

A b'angaren Dr.Malini bata samu damar halartar Taron ba,sai dai ta turo da sak'on Taya murna inda tasanar Mrs Arorah sigh ce bata da lafiya
Ma'ana matar Babanta.


A b'angaren mata kuwa manyan mata sun halarta,tundaga matar shugaban k'asa,matar gwamna,Mrs Bello Muhammad Matawallen maradon (Mon) Hajiya Hajiya Balkisu Muhammad da sauran matan gwamnonin Mak'otan zamfara kowa kagani agurin sai ka k'ara kallawa,K'ungiyar marubutan Arewa takawo jiki...Chan na hango *Perfect essential writers association*sun kawo jiki,su sister bareemat( Yan biyu macizai),oum Amjad,(Yan biyu)oum Maryam (Ina izzar take),Anty moon(Mijin bahijja),Dr teema,maman Abdallah( Yan kance ) Autar Ammi (Aljannar ruwa ce) d.s.
Itama Haandy takawo jiki marubuciyar *Bahaar*
Chan Kuma na hango Boss bature (Abba Sojoji) itama ta kawo jiki tana gaisawa da fans dinta, Yan group na *NOVEL'S KINGDOMS* ma sunzo kungiya guda Dan Taya murna sun Sha Anko,Mai kyau,su sis Ayeesha Abdullahi,Maman Muhammad,Maman Abba,Zarah ibrahim,Jibril,ummu-Salma kabir gagara,Amina janyau,sahura Kabir gagara,Umaima Halliru,baby birnin gwari,Asama'u ibrahim,Halima Bashar da sauran su..in nace duka zan lissafo sunayen ku zan cika page din ne.

An gabatar da taro lafiya bayan bud'e taro da Addu,a tare da national Anthem,anyi jawabai na Bada shawara daga nan aka tashi aka bud'e Asibitin Mai Suna
*NORA SPECIALIST HOSPITAL*
Wadda Mai girma gwamna Dr BELLO MUHAMMAD MATAWALLEN MARADUN bayan gama Kaddamar da ita daga nan aka d'unguma had'add'en *HALL *Dake cikin *TAULA ARENA*Dake cikin Gusau d'in Dan gabatar da Dinner wadda k'ungiyar likitota ta duniya ta shirya musu Dan tayasu murna Gina wannan katafariyar Asibitin Mai kusan cin gari guda,Asibiti ce da ta k'unshi sassa daban daban tundaga sashen zuciya,sashen k'oda ,sashen kwakwalwa,sashen kula da fata,da dai sauran manyan sassa dama k'ana nan,sannann ta zak'ulo manyan kwararrun ma'aikata dga cikin jiha dama wajen jiha har ma da k'asashen waje,tundaga Doctors,Nurses, Pharmacist, Lab scientist,Public health practitioners da dai sauransu.

An k'awata gurin k'awa ta musamman inda aka manna k'aton hoton Dr.Ammar Da Dr.Al Amin (Aj )sun Sha kyau cikin kayan tiyata na likitota sun sargafe stethoscope awuyansu kowannesu yayi murmushi ya rungume hannayen sa ak'irji sun bawa juna baya,ku kwatan ta kyawon Da Dr.Ammar acikin kayan nan dan bansan yadda zan fasalta muku Shiba,b'ata biro ne ma zayyano muku domin kuwa yayi wata kalar had'uwa ta musamman...

K'aton cake ne ne Mai d'auke hotunan su Dr Ammar aka yanka inda da taimakawar gwamnan jahar zamfara Dr Bello Muhammad Matawallen maradon..anyankansa lafiya inda duk wani ruwa da tsaki sai da yakai bakinsa.
Nima dai na laso yar madarar sa d'in Dana Gani ta mak'ale agefen wata Leda..🥱🥱


Anci ansha Agurin Taron,komai gashi nan save your self sai ka zab'a abun da kake so ,agurin Babu kalar Abunda babu sai Abunda Allah yaharamta ci da Sha,Abinci ne kala kala tunda ga kan snack har zuwa sauran girke girke.fannnin lemuka ma gasu nan zube a fridges ba,a cewa komai sai ka zab'a ka darje
,Chan na hango muku Sis Ayeesha Abdullahi Ana ta fisgar nama ansamu Banza...😀
"Yan *GIDAN NOVELS KINGDOM*
Suma ana ta faman ya mutsar hak'ora kowa nata bawa ciki hakkinsa wasu harda Sakawa acikin jaka😂😂 irin su oyi..✍️✍️

Nima Kam Mai d'aukar rahoton Dana Kai kaice idanun jama'a na Yi maza na cika jaka ta,yo waga banza yak'ita💃💃💃💃💃😂

Kowa kagani agurin cikin farin ciki yake musamman wannan family Unni Da Ummi dasu hajiya bakin su yakasa rufuwa.

Daga nan aka fara basu gifts na musamman sun samu kyauta Mai yawa wayenda bazasu lissafu ba,tundaga kan manya motoci, gidaje,inda Shima shugaban k'asa kafin tafiyarsa yayi announcement ta hannun protocol nashi,inda yayi Alkawarin zai Sanya hannu gurin Biyan ma'aikata,tafi ne ya tashi cikin hall din raf raf da sound na wooww na farin ciki,inda daga nan UNCEF
Itama tayi nata announcing na mak'udan kudaden data zube da K'ara taimakawa mata da k'ana nan Yara da sauran marasa lafiya,Kuma ta tabbatar zata kafa nata reshe na k'ungiyar ta acikin Asibitin dan k'ara kulawa da Yara da mata..tafi aka Kara d'auka bayan koma Jin wannan abun alkahirin,wata sanarwar ce tak'ara dakatar da mutane daga yayar dasukeyi na wayen nan kyaututtuka ta His excellency Bello Muhammad Matawallen maradon inda yayi Alkawarin Gina sashen marayu da kula dasu acikin Asibitin wowwww Allahu Akbar shine Abunda ke tashi a hall din tare da tafi,A hankali Suma manyan masu kudin dasuka halarta sukayita kawo tasu gudun muwa..
Sarki Ali Da Dr.Ammar Da Dr Aj sun tsinci kansu cikin farin ciki Marar misaltuwa domin ayau idan kaga Dr.Ammar baza kace shine ba yakara yin wani kyau na musamman kasancewar yau fuskar tasa asake take tana ta wanzar da murmushi Mai Kara k'awata fuskarsa,inda Yan mata kuwa kamar su zubda eyes nasu wurin Kallonsa inda shi ko d'aya Bai Gani ba acikin su,ko ince Basa gabansa..cikin su Harda Sis Ayeesha Abdullahi da ta mace kansa.😂💃💃🚴🚴🚴🚴🤗

Subhanallah zoku ga hajiya bakinta kamar gonar auduga harda Yan guntun hawayenta,Unni da Ummi sai hamdala sukeyi azukatansu,su Nisa ba'a magana.


Daga nan aka Sanya kid'a Mai taushi Wanda ko baka Yi niyyar takawa ba sai motsa Koda kafar kace yadda kid'in ke ratsa jiki,chan na hango Anty Moon Ana d'an Rausaya Kai kamar k'adan garuwa...
Musamman Aka Kira *A MAFARKI NASANTA FANs*ma'ana *NOVELS KINGDOM* Suma suka baje suna ta bankan rawayar su,Nima dai na D'an motsa k'afata daga gefe..


Bayan and'an chashe sannan aka rufe taro da Addu'a tare da yin jawabin godiya,taro yawatse lafiya Lau,manyan bak'i Already dama dare yayi an kama musu Hotel anan zasu kwana zuwa gobe su wuce.


A wannan Rana dukkanin kafafen watsa labarai da gidajen telebijin Babu Abunda sukeyi sai haska wannan gagarumin taro domin dukkanin wasu masu yad'ai labari sun halarci gurin, tundaga BBC ,FMs State radio and television,social medias,irinsu tiktokers, Instagram etc,inda take duniya tadauka,masu kud'i nata turo da tasu gudun muwa inda Suma sauran Alumma suka bi Asibitin da Addu,a ta fatan alkhairi da kawo cigaba ga k'asarmu ta Nigeria Baki d'aya dama kewayenta,da fatan wasu masu kud'i ma suyi Koyi da Sarki Ali dasu Dr Ammar wajen Gina Asibitota irin wayen nan da ake zube kud'i Dan taimakon Alumma.🤲

Ayau farin cikin wannan Ahali a wannan Rana Bai b'oyuwa..


Masha Allah
Allah ka yawaita muna irin su Sarki Ali acikin Al ummar mu🤲🤲🤲


Finally dai ankusa had'uwa
Masu son ayi rushing ku k'ara hakuri kad'an ne ya rage...🚴🚴🚴🚴🚴🚴


*FA'EEH BG*✍️✍️✍️✍️✍️

Idan kina da shawara ko tambaya Zaki/ka iya tuntub'ar wannan lambar.
*Telegram,Whatsapp*
*08069059746*

Follow my accounts
*Wattpad @faiza murai*
*Arewabooks @faizatou*
*Facebook Pha'eezah Almustapha*

Like share pls and comment...✍️✍️✍️✍️✍️


```https://whatsapp.com/channel/0029VaZmQcv4yltXZ8zJiD3y


https://chat.whatsapp.com/L42Op0Ya7YPDsMhkJtVRbI

💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams


Please Login or Register in order to submit comment