Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga falon yadosa,sukuma sauran yaran suka gyara parking nasu...Sallamar da yayi ce tadawo dr ammar tunanin zucin daya kasance masa dole akullum inyayi mafarkin nan nasa to duk yinin ranar zai kasance acikin tunanin sa ne,badai natsuwar zuciya,

A hankali ya bud'e manyan idanunsa da suka dan fara sauyawa na damuwa,ya dora su akan,Dr al amin aj,dake gefen sa wanda har yazauna ma,A hankali kuma yadauke idanunsa kan aj din wanda shima kallonsa nasa yake yi dan ya fahimci kamar akwai damuwa a fuskar dan uwan nasa.......


A hankali dr.Aj yafurta masa meye matsalar dude,shirun daya masa shi yakara tabbatar masa da zarginsa na cewa tunanin dake kezo masa arai bazasu wuce mafarkinsa ba da kuma mahaifinsa, sai mahaifiyar wadda ke yawan yin fushi dashi akan sarautar da baida ra,ayi kanta...

Bayan ya k'ara k'are masa kallo sai kuma yadafashi ahankali yana furta calm down man anything will be fine ohk!yakai karshen maganar cikin tausayin dan uwan nasa....

-----------------------------------------------------------

A hankali kuwa Dr.Ammar yaware manyan idanunsa kan dr aj sannan yacire hannunsa da ke kan kafadarsa ya mik'e a hankali ya doshi upstair har yafara taka step na daya na biyu sai ya juyo a hankali yadan kalli aj dake zaune kan rugs yana kallonsa,A hankali kamar bai son yin maganar irin an masa dole cikin zazzakar muryar sa mai yanayin natsuwa ya furta wa dr aj thanks,wanda koshi dan saboda hankalin sa nagaresa ne da bazai ji abunda ya furta ba da iya labbansa ....


Yana gama maganar ya cigaba da tafiyarsa,shiko dr aj murmushi kad'ai yayi yana girgiza kansa,dan hangosa da yayi ya lakaci tsinin hancin wanda alamace dake nuna yana cikin yanayi mai dad'i,Shigar sa haddadden falon nasa wanda yake ko ina tsaf ank'ara gyarashi bayan fitarshi,takalmin sa ya fara cire da safarsa bayan yazauna akan rugs dake dakin masu taushi bayan kamar minti biyar ya bude idanunsa dake alumshe bayansa najingine da kujerar ya mike ahankali ya wuce yashige had'adden bedroom nasa,yana maida takalimin a inda suke,Kayan jikin sa ya fara cirewa a hankali komai yana yinsa atsare kamar wata mace yana gamawa yajawo d'ai daga cikin towel nashi dake cikin sip sabbin kal yad'aura nan take hadaddiyar surar shi takara bayyanar da kanta ga lallausar cholcolate skin din sa sai kyalli takeyi....

Toilet yayi shigewar sa cikin takun kasaita,kansa yasakarwa shower ruwan masu dan dimi suna dukan sa atsaye idanunsa alumshe,bayan ruwan sun duke sa sosai sai yadannan wani abu take shower din yatsaya,kan hadadden katon bahon wankansa na kwalba wanda kana iya hango na waje daga ciki amma shi bazai iya ganin ka ba,yashige bayan ya cire towel nasa yajefa shi a cikin haddaden washing machine na cikin toilet din..

ya dade acikin bahon wanka inda yayi nutse,sannna ya dauro wanka sa da turarrukansa da shower gel mai kamshi,a natse yafito yana takawa in da jerin towel din sa suke da bathrobe,wata farar batherobe yajawo fara kar gwanin burgewa domin shi Allah yamishi son farar kala shiyasa zaka mafi yawan komai nasa farine,bayan yasanya ta ne yajawo dai daga cikin kananan towel dake wurin ya daura akansa bayan yagoge kansa dashi,kansa yake karewa kallo amadubi dake cikin toilet din....

Ficewa yayi ahankali cikin toilet din bayan yagama tsayuwar sa abakin mirror din yana karema kansa kallo...


Stool din dake gaban kamfacecen madubinsa dake shake da kayan gyara jere gwanin burgewa...

Cigaba da goge gashin kansa yayi mai taushi da walkiya,bayan yazauna,bayan kamar minti uku ya goge gashin kan nasa da sauran danshin ruwan dake jikinsa,yafara murza mansa na fata mai sanyayyen kamshi kamar turare lungu da sako haka yake murza man nasa akan fatar sa,bayan yagama neyajawo hair cream nasa mai kyau mai kara ma gashin sa sheki ya murzasa tare da taje sa,dan danan kyawon sa yakara bayyana sumar kansa sai sheki takeyi,lipsbalm din sa yashafa akan kyakkyawan labban sa pink colour masu laushi,turarukkansa ya fesa tunda kan body spray oud masu kamshi,kala kala wanada akalla zasu kai guda biyar,kan sipdinsa yakoma inda yadan thumprint take kuwa sipdin ya shiga bude kansa,sashen da yake na under wears da short trouser yamatsa,jawo dai daga cikin short trousers din yayi sky blue color da short fari da kuma best fara sai yakoma sashen armless yazaro mai layin blue ajikin yana gamawa yadanna abun rufewa take ta rufe ruf,cikin natsuwa yafara shirinsa.


💫Fa'eeh Bg💫

A b'angaren dr. aj shima bayan wucewar dr ammar ya wuce shi dake kusa da na Ammar din daga gefen damar shi dakin yaji komai na more rayuwa,banbancin dakin shine cusion shi nashi maroon color ne dan shi kalar na matukar burgesa da fari kamar dr ammar din.....

-----------------------------------------------------------------

* Nikam ban ga laifin ku ba domin farar kala tayi,ko mala'ku kagani masu farin kaya tokai kawuce wurin,a kabarin mu ma sune suturar mu domin sune suturar mu takarshe a duniya,Annabi muhammad s a w farin kaya yake sakawa duk ranar idi,haka ma ranar juma,a wannan yana dai daga cikin sunnoninsa...Allah yasa mudace yasa muyi kyakkyawan karshe,Yasa da mu da mala'kun rahama🙏🙏*

------------------------------------------------------------------

shima dai yashityawr sa tsaf cikin irin kayan dr ammar.


A hankali yake taka step step din da wayar sa a hannusa dayan hannun kuma acikin aljihun wandonsa yana tafiya dai dai cikin izza daga yanayin tafiyar kasan ta zaratan maza ce wadanda suka da mulki iko...

Kamshin turarensa ne yasanya dr aj dagowa daga kan wayar sa dayake kan preesing,wanda ke zaune akan dining table wanda shima bai dade da fitowa ba....

A hankali yatako izuwa kan dining har ya iso inda aj yake,cikin sanyin murya ta gwarazan maza ya furtawa aj lafiya?yana mai jan kujerar dake facing dr aj,ganin ya tsare sa da idanu,zama yayi yana ajiye wayar tasa agefensa.

Murmushi kawai dr aj yayi yana furta dude dole dr malini ta zauce wannan madarar kyau haka,ya k'une kyakkyawar fuskar sa yayi jin furucin dr aj din yana sakin karamar tsuka wadda aj kadai yajita shida yake kusa dashi " mts",murmushi kawai aj yayi yana aje wayar tasa agefe...

kukunsu ne sajid khan yakaraso yana fadin afternoon sir yana mai kokarin yin serve na dr ammar,dakatar dashi yayi,da hannu,sai kuma ahankali yajawo dai daga cikin haddadun filet din dake kan dining din yafara saving kanshi,farar shimkafa da miyar da taji na man sa yadiba sannan yajawo wani filet din ya debi hadadden farfesun kaji wanda yaji hadi sai tashin kamshi yake yi.

A hankali cin abincinsa dan shi kam ingurin ci ne bai wasa da cikin...

Aj dayake ganin duk abunda ke faruwa murmusawa kadai yayi dan dama yasan abunda zai faru kenan,kusan kullum haka suke shida sajidkhan indai yazo zai zuba masa abinci cewa yakeyi baiso duk da zaman kukun nasu musulmi,dan shi mutun ne mai bakar tsandar tsiya,ansha chanja musu masu dafa abinci saboda shi,sai akan wannan ne haryanzu baiyi complain ba,shi abun ma dariya yake basa da haushi mutun ya girka abinci amma kace baka son yayi serve naka saboda bak'ar rigima,kara girgiza kansa yayi yana cigaba da cin abincinsa da sajidkhan ya zuba masa....

Motsin chokulla kadai ke tashi a falon sai karar ac,dr aj ne yayi ma kukun alama da ya wuce kawai,a hankali ya dago kansa ya kallesu duk su biyun cikin second guda yamayar da kansa kasa yacigaba da cin abincinsa.....

Bayan wucewar sajidkhan kitchen suka cigaba da cin abincinsu hankali kwance.


Karar shigowar sako ne a wayan dr ammar yasaka dr aj dago kansa yakallesa,a lokacin shima yadagi nasa,ido daya dr aj yakashe masa yana sakin kayataccen murmushi dan tabbas yasan sak'on wayene yashigo wayar ammar din,shikam dr ammar duk da yaga abunda Aj din yamasa bai nuna ba sai ma cigaba da cin abincinsa da yayi hankali kwance yana mai kara tamke fuskar sa.


Aj yana gama cin abincinsa ya mike tare da daukar wayar yana barin kan dining table din ...............................

A hankli dr ammar shima ya mike yabar kan dining a hankali fuskar nan a tamke,a falo shima yazauna kan 3 sitter wanda shikuma aj yana kan 2sitter yana pressing phonedinsa.

kyawawan kafafunsa ya mike yana mai daura hadadden throwpillow akan dan shafafen cikin sa,har yakwanta kuma meya tuna sai ya mike zaune yana jawo wayarsa dake gefen kafens,thumprint yadanna wanda take takawo haske har yayi niyyar ya wuce sakon da yaga anturo da private number ,sai kuma yaji yana kwad'ayin bud'esa,abunda yaci karo dashi ne ybasa mamaki dan shi baiji alamar shigowar sakon ba dan yaga sako biyu ne suka bayyana na biyunne wanda yaji shigowar sa shine na dr malini nafarkon baiji shigowar sa ba,ya karanta sakon ya fi akirga har private number din yake karantawa,inda na leka kan wayar dan ganin abunda aka basa mamaki dan shi baiji alamar shigowar sakon ba dan yaga sako biyu ne suka bayyana na biyun ne wanda yaji shigowar sa shine na dr. malini na farkon baiji shigowar sa ba,ya karanta sakon ya fi akirga har private number din Da yabayyana yake karantawa,inda na lek'a kan wayar dan ganin abunda sakon ya k'unsa nan naci karo da rubutu kamar haka da manyan haruffa da yaren mu na hausa "¿KA NEMI YAR UWARKA TANA RAYE¿?"

..............Tambayar kansa yake yi waya turo sak'on ?…ba amsa ¿

Nima dai kaina yad'aure kowa cece wannan yar uwartasa oho?kuma a waya turo sak'on ????????nima dai ana n alkalamina ya fadi......,kucigaba da bibiyar akalamin✍️✍️💫 Fa'eeh Bg💫domin warware muku duk wani abun da yashige muku duhu acikin littafin a mafarki nasanta........... Kuyi hakuri da

rashin samun update jiya hakan yazo sanadiyyar rashin chaji da banida.......

Shiyasa ma na had'a muku page biyu..


Comment kadai nake bukata ko like

Sannan plskutayani sharing🙏


inayin ku 💯 percent a mafarki nasanta fans💋💋💔 over Allah yabark kauna



💫A MAFARKI

NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍

💫Fa'eeh Bg 💫



Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha

Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*

Pen 🖊️is mightier than the sword


EPISODE1️⃣

FREE PAGE1️⃣5️⃣




TYPING📲📲📲


**************

**********

*******

****

***

**

*

Ina mai kara baku hakuri akan abunda yafaru in sha Allah hakan bazata sake faruwa ba domin mun dau kwakkwaran mataki na farko link dinmu na wannan sabon group bazai fita ko ina ba,sai wanda muka ga dama muka saka..


----------------------------------------------------------------


....Rasa mai basa amsa ne,da kuma wanda zai warware masa sakon ne yasanya shi goge sa gaba d'aya.


Sai sak'o na biyu wanda atak'aice yabud'esa ya karanta inda sak'on yak'unshi kalaman soyayya masu zafi da tsayawa arai da yanayin tausayi acikin kalmomin,ko k'ir baiji ba alokacin da yake karan ta wannan sak'on na Dr.Malini yana gama karanta wannan sak'o na dr.Malini ya gogeshi yana jan k'aramaar tsuka...


Tare da jawo tv control yana kara volume da bayan chanza tasha izuwa ta labarai,cigaba da kallon labaran sa yayi hankali kwance duk da tunanin wannan sak'o da yad'an tsaya masa arai,shidai aj duk da yaga yadda dr ammar yake ta kallon screen d'in wayar sa da alamun mamaki da rud'u bai bai matsa wa kansa da son tambayar sa ba,dan ya fahimci akwai abunda dr AA yake b'oye masa ayanzu k'ila sak'on sirrine duk da baisan ta ina sak'on zai fitoba,to wane kalan sirri ne wanda Dr.Ammar zai b'oye masa oho?ba amsa yakice tunanin da yake aran sa yayi jin sallamar d'ai daga cikin yaran nasu yana neman izinin shigowa.....



Gate man ne yashigo dama shi musulmi ne daga cikinsu kuma yagirme musu...


Hannu dr.ammar yad'aga masa yana basa izinin shigowa bayan amsa sallamar sa dasuka yi, A bangaren dr aj tunani yake aransa meya tado da gate man yanzu...


Bai gama tunanin sa ba yaji gate man din wanda yake da kagansa kaga tsufa atattare dashi yana furta sir gani naga kiran dakamun,aj ya furta wa kansa ohh ashe ammar ne yakirasa ko saboda me,?rasa mai basa amsa yasanya shi zubamusu idanu su biyun....


A hankali Dr.Ammar yad'ago kansa suka had'a ido da dr.aj saurin d'auke kansa yayi tare da lumshe idanunsa,yana mai bud'e bakinsa a hankali ya ce da wannnan tsohon mai gadi "hv a seat father"murmushi kawai tsohon yayi mai suna sabirkhan cikakken ba indiye,yana furta aa'ah sir nagode,aj dai kallon su kawai yake suka gaisa da tsohon baik'ara cemasa komai ba.......


A hankali dr Ammar yak'ara maida kansa k'asa bayan jin amsar da tsohon ya basa ya yi rejecting request nasa,bayan ya bud'e idanunsa dake lumshe,sai yaji duk baiji dad'i ba danshi kam yana darajja tsofaffi kuma yana tausayinsu,har yanajin hukuncin da yake son ya yanke kamar yafasa na korarsu gaba d'ayansu da nufin akawo musu wasu sabbi tunda wad'annan basa aikin su yadda yadace danshi baisan kuskure ba,cewa yake gangancine,duk da baiso aka basu suba tun farko........



Bayan gama zancen zucinsa ne ya bud'e dan k'aramin bakin dan karamin bakin sa mai dauke da pink lips da suka sha lipsbalm sai glowing suke,father

Could I ask you to move a little?you and your colleques sannan ya cigaba da maganar sa da yaren india ga tsohon tunawa da yayi baijin english cikin kwarewa da yaren ,har yagama maganar sa sabirkhan bai ce komai ba face murmushin da yake ta saki,sai da yagama ya furta masa sorry sir,ya juya yayi wucewarsa ......


Bayan fitar sa shikam aj da yacika da mamaki dan wannan ne karo na farko da yaji aj ya yanke game dasu batare da shawararshi ba,cikin kafe ammar da idanu ya furta saboda me ?zaka nemi su matsa daga nan gidan kuma har da suspension na wata daya eh?

yana mai cigaba da tuhumarsa da idanu,Cikin halin ko inkula kamar bazai amsa ba sai kuma ya furtamasa ra,ayi yana gama fad'in maganar sa yatashi da wayar sa ahannu yayi wucewrsa upstair zuwa bedroom nasa,da ido kad'ai aj yabisa yana girgiza kansa,shima yana mik'ewa ya fice compound din su domin dakatar dasu,bayan yafito ne yatarar dasu cirko cirko atsakiyar compound d'in atsaye suna jimamin umurnin ogan nasu,bayan ya gama kallon gaba daya tare da karantar yanayinsu,yayi gyaran murya,duk suka hankalta dashi suka fara mik'a masa gaisuwa yana amsawa musu cikin sakin fuska....


a hankali ya furta musu kar wanda yaje ko ina nasan ko mene zuwa anjima zai bar maganar zan shawo kansa..


Duk sai sukayi na,am da maganarsa,yacigaba da magana nasan abunda kuke tsoro kar gwamnati taji abunda yafaru na suspension din da yabaku,namuku alkawaro bawanda zaiji,nasan cewa incident din da yafaru d'azu da safe ne yasanya sa baku wnnnan hukuncin duk da banga alamar fushi afuskarsa ba,dan shi mutun mutune wanda baicika bayyyanar da fushinsa ba...


Godiya duk suka masu nuna jin dad'i har ya juya sai sabirkhan ya tsaidashi ta hanyar fad'in sir,juyowa yayi dan ga tsoho sabirkhan yace da aj yallab'ai ban tari numafashinka ba,amma inaga da kabar hukuncin yadda yake saboda ina da tabbacin duk wannnan abun akan ka yayasa saboda fahimtaar da yayi ranka ya sosu alokacin da aya aika akaima maka mota,kuma ba,aje da wuri ba,shiyasa,dan nima na fahimci bada son ransa ya furta musu maganar suspension ba ,shiyasa tunda yafara maganar sa ban nuna alamun b'acin rai afuskata ba sai dai murmushi da ya wanzu akanta,inda ka lura ko d'ago kansa baison yi gudun had'a ido dani,kabarshi kawai dan inyaga katsaidamu zaiga kamar ka kwatse sane.....................


Murmushi kawai aj keyi har zuwa lokacin da tsohon nan yagama maganar sa,yak'ara da cewa kuma inada tabbacin ransa ya b'aci matuk'a dan naga alamar hakan alokacin da zai fita suka biyosa ya furta bai bukatar kowa ya bisa acikinsu....Kuma kasan halinsa baison ya sanya doka atake,nasan wani laifin ne kuma binsa da sukayi,mukuma yallabai kasan munyi rantsuwa akan zamu kare ku ta ko wanne yanayi kuma nasan kasan mahimmancin rantsuwa.


Uhmm aj ya furta yana mai girgiza kansa tare da sakin murmushi a fuskarsa,toh shikenan father dan haka suke kiran tsoho sabirkhan,kuje amma nan da kwana uku ku dawo nasan zuwa lokacin ya sauka ya furta musu,touh suka amsa masa dashi.Suka fara watseqa suna shisshiga motocinsu domin zuwa quaters nasu dake chan gaba da gidan su aj,bayan sun mimmika car keys ga aj dakuma gate controller...

Dr.Ammmar dake chan tsaye kan windown din dakinsa ne ya furzar da iska mai zafi abakinsa yana mai jin ba dad'i aransa duk da yasan yayi ne dan ya farantaran dan uwansa,A hankali yabar bakin window din yana komawa kan hadadden gadonsa ya kwanta flat yana kallon ceilling daga shi sai towel dama fitowar sa daga wanka kenan....


Aj nashiga shima ya wuce nasa dakin wanda izuwa lokacin har ankara gyara falon sai tashin kamshi yakeyi ankwshe food flask din dasuka ci abinci angyara lungu da sako sai sanyin ac daya kara ma falon natsuwa ko ina masha Allah.


💫💫Fa'eeh BG💫💫


Aj ne bayan shigarsa nasa dakin ya aje car keys din da gate controller din ya jawo wayar sa yana dialing numban sabirkhan gate man....

Bayan yad'aga kiran sun gaisa cikin mutunci,tambayar sa yayi daya turo mai dai daga cikin yaransu wanda zai kula da gate din kafin su dawo aiki to kawai yace sannan sukayi sallama...


A b'angaren dr.Ammar nan bacci yakwasheshi bai farka ba sai dayaji ana kiraye kirayen sallar la,asar,A hankali kiran sallar ke shiga kunnuwansa mikewa yayi a hankali yana addu,ar tashi daga bacci tare da ambaton kalmatu shahada.....fuskarsa yake yamutsa wa bayan duba hadadden agogon dake kan bedsite drowernsa hud'u dai dai ya gani ta buga shi yasanya sa tashi da hanzari dan yaga lokacin yayi kusa,ankusa tada sallah,shaf shaf yashiga wanka bayan yayi brush yayi wankansa tare da dauro alwallah,bayan yafito tsane jikinsa dayayi turare kadai ya fesa sannnan ya bude sip din sa yazaro dai daga cikin jallabiyoyinsa da short,da vest baka dasauri yazura jallabiyar bayan sanya underwears din yasauka kasa yana ta sakin kamshi,koda yasauko kasa yatarar da aj tsaye yana jiransa,shima cikin shirin jallabiya irinta dr ammar sai dai banbancin colour shi aj tashi fara shikuma ammar dark maroon wadda ta karbi fatarsa,ba wanda yaceda dan uwansa kala har suka fita falon suka shigamota aj yajasu zuwa masallaci....Dama mai gadin ya iso yakarb'i gate controller din suna zuwa ya wanagale musu gate din ta hanyar danna remote din,yau da mota suka fita ganin sun makara ,duk da masallacin basu da nisa dashi cikin unguwar tasu ta manyan masu naira maisuna gujarat 105 estate.......


Next page monday in sha Allah

Like pls...Nd comment




* Allah yasa mudace*🙏🙏

Pls like share and comment




💫 A MAFARKI NASANTA💫

In my dream i know her

By

pha,eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫



Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION📚🖊️


💫 P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝



ESSENTIAL WRITER'S 📚🖊️

Pen*🖊️is mightier than the sword🗡️*


EPISODE1️⃣

FREE PAGE1️⃣6️⃣


TYPING 📲📲📲


--------------------------------------------------------------*DRUG ABUSE

🚭❌❌❌

SHAYE SHAYE ILLANE GA RAYUWARMU,INA SAMARI, INA YAN MATA KU GUJI TA AMMALI DA MIYAGUN K'WAYOYI DOMIN SUNE ABU MAFI SAURIN HALLAKAR DA RAYUWAR MU....MUNA📢📢📢 KIRA DA BABBAR MURYA,DAKUMA BADA SHAWARA A GUJEWA DUK WANI KAYAN MAYE DAN SAMUN INGANTACCIYAR RAYUWA MAI AMFANI*

-------------------------------------

HANYOYIN DA ZAKA KARE KANKA💁 DAGA AIKATA WANNAN DABI'A SUNE

*KAUCEWA ABOKAN BANZA

*ZAMA DA MUTANE NA GARI

*SANYA TSORON ALLAH AZUCIYAH

*BADA SHAWARA TA KWARAI GAMASU AIKATAWA

*CIRE KWOKWANTO GA AL AMURRANKA

*KAUCEWA MASU AIKATAWA

*YADDA DA KADDARA KO WACE IRI CE ILLA MAI KYAU CE KO MARA KYAU CE.


🙋🙋MU KIYAYE DOMIN RAYUWAR MU ABA CE MAI AMFANI ATATTATARE DAMU,DOMIN AMANA CE UBANGIJI YA BAMU....ALLAH KAYIMUNA MUWAFAK'A🙏🙏

----------------------------------------------------------------

**********

*****

***

**

*Bayan sun dawo daga masallaci suka cigaba da kallonsu afalo a tashar da ake hasko wasan ball, har magriba ta gabato suka dunguma akafa sukaje a wannnan karon domin sauke farali...



"kowannen su dakin sa yawuce direct bayan bayan dawowar daga sallar dan fresh up,AA ne fara fitowa Dan bakar yunwar dayake ji shiyasa bai tsaya shiriritar sa ta shiryawa ba,dama yunwa ce kadai kesanta sa yayi gaggawar yin abu sa dasauri sai kuma in yasan suna da tarin patient da zasu gani ko kuma akwai emergency case a hospital din....


A hankali ya doshi kan dinning din nasu yana baza kamshi cikin shigar short trouser fari da kuma vest blue wadda takara haska fatar sa ...


''zaman shi keda wuya sai ga sajidkhan dan dama yaga fitowar ogannasa daga tagar kitchen ta chan mai kallon dining,


"barka da dare yamasa sannnan yajawo pilet yana mai bud'e manyan food flask dake kan dining din masu kyau,duk da yaji bai amsa masa maganar sa sai ya furta sir mai za,a zuba maka,"Anything" ya furta atakaice

Tuwon semo ya zuba masa da miyar egusi da taji busasshen kifi,ya dora masa agabansa tare sa sanya masa spoon a ciki da zuba masa ruwa a karamin cup na glass da lemu,A hankali ya fara cin abincinsa,Aj da tun d'azu ya iso wurin yaga abunda yafaru yau Dr AA ne ya bari kuku ya zubamasa abunci...Yasan cewa bak'ar yinwa ce nanake da cikin sa shiyasa ya yadda amma da ba haka ba da kai tsaye zai dakatar dashi....


"Kansa kawai ya girgiza yana mamakin halin dan uwan nasa


"shima dai tuwon shinkafa da miyar wadda taji naman sa rago ya zaba,bismillah yayi cin abincinsa hankali kwance kamar ammar din,Muryar Dr ammar ce ta karad'e gurin yana mai furtawa sajidkhan "have me some water in a rubber"cikin calmly voice dinsa,ohk sir!ya furta, ruwan ya kawo masa aroba mai dan fadi


"hannunsa yacire dake kan spoon ya kada sa acikin robar ya ya wanke hannunsa sannna yasanya acikin filet din tuwonsa,Yunwar da yake ji bazata bar sa cin abin da spoon gani yake kamar yana bata masa time,domin shi mutunne da baya wasa da cikin sa,shiyasa ya cire spoon din yasanya tattausan hannunsa,mai da robar sajidkhan yayi kitchen ya maida robar ma,ajinta bayan yayi discard din ruwan..



Abincinsu suke ci hankali kwance,musamman dr.Ammar wanda kaikayi zaton manyan lomomi zaiyi daya sanya hannu sai dai ahanklai yake saka abincin adan karamin bakinsa cikin natsuwa kamar ma bai tauna tuwon..Yana gama cin semo dinsa yayima sajidkhan alamar akara masa,Sai yanuna masa na shinkafa,a wani sabon filet din ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance..


Shikam Aj tuni yabar kan dining din yana waya wanda daga ji macece ta hanyar yadda yake mayar mata martani......


Shima dr ammar nagama cin abincinsa ya mik'e ahankali ya wanke hannunsa a sink din dake gefen dining din,lura da akwai aikin da mai aikin nasu yake yi akitchen din....



Wayar sa yadauka kawai yawuce warsa falo cikin tafiyar kasaita wadda sarauta tagama ratsa jikinsa,da zuwan sa yazube akan 2 sitter yana lumshe idanunsa jinsa yafara dawowa nrml da yunwar da ta dibesa, bayan kamar minti biyu ya lura da wayar sa aj din keyi,wanda koba,a fad'a ba yasan sumayya ce yake waya da ita wadda ke bima aj din,Amma anfi kiranta da sumy .....................................................………………


💫 Fa'eeh BG💫


Jin tambayar da yayima nacewa ina Auta husna ne yasanya sa kara tabbatarwa.


Ahankali ya kunna piano game yana bugawa cikin kwarewa da natsuwa,Maganar da aj yayi ce tasanyasa dakatar da game din,inda aj din ke furta wa sumy din kin raina ni ko sumayya tun yaushe nace kibar min wannna maganar amma bakya ji koh,yakai karshen maganar da yanayin hasala,cigaba da maganar yayi yana furta ki sani matsayi daya na dauke ku da ita,nace kibar mun maganar NISA domin kuwa itama kanwa ce agurina bayan wannnan babu komai,daga chan dayan bangaren naji ana furta sorry

Please Login or Register in order to submit comment