Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakai karshen maganar kamar ya yayi ihu yake ji na jin zafin halin da norah din take ciki.....


Murmushi wanda aka kira da uncle yayi yana share ma Ammar hawayen sa dasuka kasa tsayawa,jawoshi yayi yazaunar agefensa inda D'an uwansa yazauna,A hankali yafurta mai sunan Autan maza yana jin wani abu na taso masa bayan kiran sunan Autan mazan,kayi shiru kadaina kukan nan kaji Halimatu sadiya tayi bacci ma kaga tadaina kukan yakai karshen maganae yana shafa beauty face dinta,


Ajiyar zuciya ammar yasauke mai nauyi kamar wanda waci bakar wahala yasamu hutu,Jin cewa ta hakura, wanda har uncle din saida yaji fitar ta,har Aunty da yanzu tazauna bayan gama bawa ma'aikatan dake cikin kitchen umurnin abunda zasu aiwatar yau domin bazata samu damar shiga kitchen dinba norah ba lafiya...


murmushi mai taushi gimbiya laylat ta sauke tana mai shafa lallausar sumar dake shimfid'e abisa kansa,domin kuwa tana mugun son Ammar musamman yadda yake nuna kulawar ga norah dinta,wadda tun ranar da fad'o duniya yake kokarin daukar dawainiyarta duk da karancin shekarunsa,wannna soyayya dayake ma nora har maamaki take bata ba ita kadai gaba daya a halin ma sun san yadda norah take agurin Ammar ,shiyasa take jin wani kud'uri yana shigarta ahankali ..........


Bayan kwana biyu tun faduwar da norah tayi kullum cikin kuka take ga rashin bacci har saida aka kira family doctor nasu ya duba ta sannaan yatabbatar musu da ciwon kaine ke damunta mai tsanani,tun lokacin tasamu sauki bayan an rubuta mata magungunna,daga baya sai abun yadawo wanda duk bayan kamar watanni sai tayi ciwon kai da zazzabi mai zafi,Ammmar shine mai jinyarta lokacin duk da yarintarsa dan Alokacin yana da shekara shidda itakuma shekara daya da rabi Aduniya, kuma tun alokacin yadau alkawarin zama likita saboda norah ganin yadda take wahala,Domin yakula da ita ita kadai...Wannnan kenan............


*MUKOMA CIKIN LABARI*


Bayine ta ko ina suna gabatar da dukkanin ayyukan dasuka zame musu Al adah wato kai kawo domin gudanar da aikin su,kowa da kalan uniform na sashen da yakewa hidima da masu kula da kofa fada, masu kula duk wani motsi na fadar,masu kula da dawakai,abun gwanin burgewa sai wanda yagani...


Tangamemiyar masarauta ce mai tsaunukkan gine gine masu kyau irin dai yadda kuka san ginin gidajen sarauta suke,tako wanne gefe haskene tar kamar rana na ban mamaki ko lif lif da shuke shuke,ga gurin aje dawakai da motoci na alfarma.


Wata faffadiyar koface wadda zata sadaka da fadar sarki nan na kutsa kaina domin dauko muku rahoto duk da manyan dakarun dake tsaronnata ..


Had'addiyar fada ce mai abun burgewa tako ina fadawa ne atsaitasye ga wata kujera ta alfarma wadda tasha adon gold sai shining take yi ga fadawan dake gefen kujear baibaye da ita sai fifita sukeyi ma wanda ke kan kujerar ta alfarma Ahankali duk da AC din dake huro iska mai dadi wanda yahadu dawani kamshi...


A hankali fadawan suke furta gyara dai sarki Mai dubbanin alkhairai,Allah yakara lafiya,jin tarin dayake yi wanda ke nuna alamar mura ke damun mai yin tarin,Hannunsa yad'aga cikin nuna mulki da Izzah,Alamar ya isa A hankali naji kyakkyawan dattijon da bai haura shekara sittin ba yayi magana da muryarsa mai nuna dattako da manyan taka,yana mai furata "har yanzu yarima baice komai ba ne galadima"?

Mutumin da naji ankira da galadima ne naga yaduk'ar dakansa yana furta Allah yataimaki sarki,ehh haryanzu bai nuna yaga sak'on mubah,yau wata takwas kenan,ni anawa ganin Allah yataimaka sarki kawai akyale sa sannan Ku gyara tsakaninku....


Wani murmushi mutumin yasaki Wanda yatsaya iyakar labbansa,zaka gane hakan inka kura mai ido duk da yana cikin rawani ,shiru baiba galadima amsa ba,saima mikewa da yayi,Dan danan fadawa suka fara karesa suna furta gyara dai sarki mai dubbanin alkhairi,gyara dai sarki mai masarautar gado mai garin na sambo,,,


Mai garin na sambo zai fito,wata murya CE ke d'aga wannnaa sauti a waje,kirari suka cigaba da yimasa tare da kara gyara masa alkyabbar sa ta alfarma sai walkiya take na duwatsun gold,A hankali yake takawa harsuka fito daga babbar fadar tasa sai dai yau baibi ta kofar dazata sadashi da sashen UNNI ba

Yafito ne ta kofar dazaka iya ganin komai dake gudana atsakiyar masarautar,tafiya yake yi Ahankali inda duk inda sukabi ma'aikata bayi sai sun masa irin gaisuwar nan da yan Korea suke yi a series dinsu na sarauta ga shuwagabannisu gamasu kallon su zaku gane yadda nake nufi Niko vow suke cemishi....

( Adan sunkuyar dakai kadan sai alankwasa hannu biyu ahade su guri daya kamar mai daidaton sallah,sai a saita shi akan tsakiyar goshi)Allah yasa kunhgane😜


Kansa kawai yake d'agawa alamar karba gaisuwar tasu acikin lemar da suka ware masa ta alfarma, har ya isa inda manyan motocin suke aparkey na alfarma,Isar sa wurin d'ai daga cikin fadawan da ke lullube dashi ya bude masa wata arniyyar parado new design bak'a wulik mai tinted glass irin yan 57billion dake parkey agefe cikin wata had'addiyar rumfa inda dagani nan ne mazaunin aje wasu motocin na musamman😱 kai FA'EEH wannan karya...koda yake abunda nagani ne ai😇



Ahankali yashiga cikin motar dai dai Wanda ke rike da dai Wanda ke rik'e da had'addiyar umbrellan da suka kara masa tun lokacinda aka shimfida masa bugaggiyar carpet ta alfarma an rubuta MURAI'S PALACE akanta cikin tsari mai kyau....



Bayan shigarsa motar tafiya kad'an sukayi da direban da yatuk'osa da sauran fadawan sa dasuka k'asa da algaitu da busa suna masa kirari,motar drivern yafaka A wani tangamemen gida dake d'ai daga cikin gidajen masarautar na alfarma,take fadawa suka zagaye motar suna masu kakkaresa bayan yafito a lokacin har an kara shimfida masa carpet tare da bud'e masa umbrella ta alfarma abun gwanin burgewa sai Wanda yagani wollah in maku hausar mu ta sakkwato😀.



Tafiya kad'an yayi ya Iso kofar shiga mai rike da had'addiyar kofar ce wadda zata sadaka da falo, ya wangale masa bayan ya rusuna masa alamar gaisuwa


Shigarsa had'adden falon na alfarma yabani damar debe keyar ido nah masha Allah nake furtawa tsayawa kwatantamuku tsaruwarsa bata lokacin ne,falon yaji komai na more rayuwa....


A hankli dukkanin bayin dake kai kawo suna hidima asashen suke rusunawa suna gaidashi hannu kadai yake iya d'aga musu har ya isa wata kofar inda naga wata dattijiwa mai uniform wasu colour masu kyau tafito,Ashe Babbar Amintacciyar masarauta ce tun lokacinsu Ammi take hidima dasu,

Inda yanzu ma ita keyiwa sarauniya hassaana da sarki duk da bawata hidimar bace kawai dan duba sauran ma,aikata ne sai yin iso ga sarauniya,

Iso tayi ma sarki ga sarauniya bayan tagama yimasa kirari nuna gasuwarta bayan ya karba tawucewar Alokacin duka ma,aikatan kowa yacigaba da aaikinsa....



Sallamar ce acikin uwar dakin tasanya kyakkyawar matar dabazata wuce shekara Arba'in wadda daka ganta kaga zubin larabawa, in kallo daya zaka mata kagane wacece ita idan har kasan gwarzon d'anta,Amsa sallamr tayi atsanake cikin murya mai nuna farinciki,furtamasa tayi "marhaba biki shugaba adili ya zaujaty ,Abul mahir Abul yuhanis,Abul Abdul rashid " takai karshen maganar ciki. Kara kawata fuskarta da murmushi,Murmushi yake ta saki Wanda yake kara kawata fuskarsa dan yana mugun son wannan kirarin Nata murmushinsa ne yafara gushewa jin furucinta nakarshe Wanda dama tasan hakan zata faru shiyasa bakasafai take yimasa shiba,Wanda aduk lokacin da tamasa kirarin ta ambaci sunan Abdul rashid,Abu uku ne ayanzu ke zomasa arai damuwar d'an yarima,dakuma k'anensa daya b'ata shekara talatin da suka wuce dakuma dakuma babban rashi dasuka yi na dan uwansa da iyalansa a shekarun baya,b'at murmushin dake kan fuskarsa yakyau zuwa hawaye bayan jin komaai yadawo masa sabo arai.......



Chakwakiya to ko meyasamu dan uwan nasa da iyalansa?wane kalar rashine ne wannan


Shin wanene kuna d'ayan d'an uwansa daya b'ata kuma ashekarun baya?


Ko suwaye wayen yan uwan NASA?

Gaskiya yabani TAUSAYI dattijon nan 😢nima kamar inzubda masa da hawaye

Shin ko kungane wane yarima ake

magana ?


Duka zaku samu cikon amsoshinku anan gaba kadan

Kucigaba da bibiyata duk zan warwaremuku in sha Allah In Allah yamauna aron rai


💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥


*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*

*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........

*+2348069059746*

*+2348084504630*

----------------------------------------------------------------

*💫A MAFARKI NASANTA💫*

*2023 novel is the story of an innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA*KO MASU MUKAMIN *MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....

*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*

--------------------------------------------------------------------

https://chat.whatsapp.com/GNSky8tcQT72iE1IVm7Vpt


💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥


*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*

*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........

+2348069059746

+2348084504630

---------------------------------------------------------------

*💫A MAFARKI NASANTA💫*

*💫In my dream i know her💫*


*2023 novel is the story of aninnocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA KO MASU MUKAMIN MENE DASU DA HAR ALKALAMINA YA KIRA SU MANYA KASA*....

*DUK AMSOSHINKU ZAKUJI SU ACIKI WANNAN BOOK KUCIGABA DA BIBIYATA*

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

FREE PAGE2️⃣2️⃣



TYPING📲📲📲


A hankali tataso daga kishingid'en da take zuwa wurin mijinta cikin had'addiyar alkyabbarta


Hannunsa talakamo acikin nata sannan ta zaunar dashi akan hadaddun rugs din dake cikin bedroom din nata mai had'e da tafkekiyar tv da wankacecen gado na alfarma da tintimi irin na gidan sarauta mai taushi akan tattausar turkish carpet dake malale adakin


......Hawayen sa share masa tana mai kwance masa rawanin da yarufe rabi da kwatar fuskarsa,nan da nan fuskar Ammar ta bayyana agaresa hatta yanayin chocolate colour skin dinsu iri daya ne,duk da yafi kama da mahaifiyarsa ta idanunta da lips dinta ammar hatta girarsa irin ta mahaifinsa ce da tsawon,inbaku manta ba mahaifiyarsa da mahaifinsa tsatso daya ne Diyan wa da k'ane ne shiyasa zaka ga kamar dukkansu kamar su d'aya iayayen nasu da.....


Bayan ta cire masa rawanin ta taimaka masa yacire alkyabbarsa tare da taimakon sa,A hankali ta bd'a fridge din dake chan gefen wata kofa da nafi tunanin store ne da karamin kichenn,dauko filet da glss cup mai kyau tayi na alfarma tadauro ruwan da juice masu sanyi

Tsiyaya masa tayi tana mai kara masa abakinsa kurb'a guda yayi yajanye bakinsa yana mai sauke ajiyar zuciyah,A hankali ta bud'a bakinta ta ambaci sunansa "Ya Aliyu"haka take cemasa idan suna keb'ance ko zaujy , agaban al umma kuwa tana kiransa da maimartaba wannnan kenan.



jin Bai amsa mata ba, sai tayi Murmushi tana furtawa aranta yau kenan sarautar takaara motsawa,murmushi takara saki tunowa da duka rabin halayen Ammar shiya kwaso komai nasu duka d'aya tafannin halayya...


Magana ta cigaba da yi cikin natsuwa "kayi hakuri yaa Aliyu nasan dukkanin damuwar ka,In sha Allah Hamma Abdul zai bayyanah"

' sai ga hawaye shar a idanunta gefen hannunta tasanya tashafe cikin jin wani zafi yana taso mata acikin ranta,


"Tabbas ina ji ajiki nah laila da hamma umar suna acikin ni'imar Allah,kabar sanyawa kanka damuwa kuma in sha Allah ko wanene sila asirinsa zai tonu duk da bamu da wata shaidar cewa ga yadda abun yafaru Amma inaji ajiki nah komai yafaru ne akarkashin sharrin wasu kuka ne ya kubce mata mai karfi,bai hana ta ba,sai da tayi mai isarta sannnan ta tsagaita dan shima kanshi hakuri kadai yake yi yana ji kamar ya fasa nasa kukan ne...


Jawota jikinsa yayi ya rungume ta yana cigaba da lallashinta,A hankali sarki Ai ya furtawa gimbiya hassana "bansan abunda yasanya zuciyatah takasa gasgata cewa emir da layla sun mutu ba

Ako dayaushe inaji kamar zasu dawo garemu ne,inaji ajikina dukkaninsu har Autan maza zasu dawo garemu nan bada jimawa ba,Bayan sauraren maganar mijin nata sai tayi murmushi wanda yafi kuka ciwo.....


ta furta" yayah Aliyu sai dai mujira dawowar hamma Abdul...shida kawai mun wayi gari babu sa,kamanta Cewa Ansamu gawawwakinsu bbu kyan gani norah ce kadai ba,asamu koda kashinta ba,sai hawaye shar aidonta cigaba da maganar ta tayi kagakuwa Kuwa babu yadda za,ayi su dawo garemu.....Ta idar da maganar cikin wani yanayi mai radadi da ciwo..


Murmushi yak'e yayi bayan jin zancenta,danshi sai yanzu ma yake kara tuna wasu abubuwan a lkacin da yarasa d'an uwan nasa da iyalansa,


Tambayar kansa yayi tabbas akwai zoben azurfa wanda mahaifinsu yasamusu duk su duka kuma alokacin da yasanya musu shi yasanar musu da cewa azurfar zinari ce mai kyau wadda ko wuta baza ta iya k'onata ba,ko da ace wutar ta tab'a ta zaiyi wuya ta fita hannun mai ita inbashi yacire ba,


K'ara tuno lokacin da za,a wuce da gawawakin su kushewa bayan yimusu yar dubar domin ruwa bazai sanyu ajikinsu saboda yadda suka chanza kamanni,sai dai gwargwado abunda gawar zata iya dauka,riko hannun d'an uwan nasa yayi mai kama da kwarangwal yana hawaye yana tofa masa Addu,a,A lokacin baiga zoben a hannun sa ba,sai maganar mahaifinsu tafad'o mai arai.......Zoben baijin wuta...



Tou Amma ina zoben yashiga da suka k'one k'ila yafita tare da naman jikinsa,touh ina zoben yashiga acikin gidan?sai maganar mahaifin su ta fado masa arai inda yace "koda wuta ta tab'a zoben zai zauna hannun maishi ne,sai idan ancire sa da dubara",Alokacin tunani barkatai ne sukayi ta zomasa arai,duk sai ya watsar dasu saboda tashin hankalin da suke ciki alokacin.....



Abu daya ne yatsaya masa arai maganar rashin samun gawar norah ko wata alama ta nuna akwai ta awurin....


Maganar gimbiya hassanat ce tadawo dashi daga firar zuci ko ince tunanin dayake "Cin abinci ko wanka zaka fara ?sannan insa Akawo ma nan?ganin yafada duniyar tunani....


Murmushi ya dajin jerun tambayoyin da ta jero masa,Cikin kara yin murmushi " har yanzu yarinya kike komawa,hassnat duk wayenn nan tambayoyi yanzu amsa suke nema,murmushi tasaki tana mai d'aga masa kai tare da gyara daya,murmushin yakara saki mai hade da dariya ganin yau rigima take ji,itama karamar dariyar tayi,furta mata ya afara hada mun ruwan wanka,nabiyu abinci da adining zanci tareda "ya "yana...



Murmushi tayi tana furta kamanta yau akwai school mahir yatafi itakuma yuhanis taana gurin husaina,murmushi yasaki yana shafa gemunsa wanda yafara tara yar furfura ooh hakane fa kinga na manta da auta na kusa yau da anga rigima cewa zatayi namanta ta ta baki daya tunda har namanta cewa tana gidan husaina...



Murmushi unni tayi tana furta aiko dai sarkin rigimar ka sai kai


Murmushi yakaryi yana furta toh akawo mun nan gimbiyata,murmushi tasaki jin furicinsa,har tajuya ta tsinkayi muryar sa yana furta shin kunyi waya da mai sunan Autan maza?


Chak ta tsaya domin abazata taji domin anyi shekara bai mata magaanarsaba saboda fushin da yake yi dashi,Akan kafewar sa,wanda har ita sai da abun yashafa sarki yashareta nawata daya kanta saka bakinta ya bar mganar tunda baiso wanda kuma kullum cikin bincikar yaron nata take koza'a dace tunda shima kaifi daya ne kamar mahaifinsa....


Idan bazata manta ba yau shekara da wata takwas ko ma tara za,ace da sarki Ali baiyi maganar Ammar din agabanta ba duk da abaynta yana bibiyarsa,ta email wanda kosun tura sakon baya dubawa,yana boye mata ne gudun kar ta ga kamar ya karaya shiyasa bai bata damar yimasa maganar sa agabansa ba...


Murmushi ne yasubuce mata.....



Nima anan zan dakata sai gobe in Allah yakaimu

Inkunyi comment da yawa zaku samu long page gobe ,zanbiyaku bashi ne kawai na jiya alhamis da bakusamu ba



Kunsan weekend bana typing ranar hutu ce

Like pls comment share



DAGA ALKALAMIN ✍️

💫FA'EEH BG💫


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

FREE PAGE2️⃣3️⃣




TYPING📲📲📲


Juyo wa tayi a hankali tataka inda yake zaune ta kafesa da idanunta,jin idanunta akansa yasanya sa kawar da kansa Yana mai lakace tsinin hancinsa,irin yadda Ammar yakeyi inyana cikin yanayi mai kyau



Hannayensa ta rik'o tana furta Alhamdulillah aranta,A hankali ta bud'a bakinta tafurta nayi magana dashi shekaranjiya,yana lafiya shida d'an uwansa,tambayar ta yak'ara yi har yanzu yana kanbakansa duk da yana da labarinsa,Amsa tabashi cikin d'ar d'ar "eh amma ina nan ina kokarin janyo tunaninsa izuwa garemu da fushina...


" Dan duk lokacin da mukayi waya dashi ina nuna masa fushi na inbarsa cikin zullumi nasan cewa baison damuwar d'ai daga Cikin mu,ko sharekan da yayi nasan kai kafara nuna masa taurin kai irinka naka,Allah kad'ai yasan yanayin dayake ciki ayanzu,zuciyarsa akar ye take,ni nasan waye Ammar cikin sa da bayansa,kuma nasan waye mahaifinsa...takai karshen maganar cikin jin tausayin yaron nata wasu hawaye ne suka zubo a idonta..


Murmushi sarki Ali yasaki jin kalamin ta na k'arshe..


"A hankali ya furta na janye maganar bashi sarautar,ayanzu inaso su dawo kusadamu gaba d'aya


Ayanzu haka nakusa kammalla Gina masu babbar asibitinsa domin sudawo su rik'e ta shida d'an uwansa su kula da ita....


Farinciki ne mai yawa ya bayyana A fuskar gimbiya hassana,rungume sa tayi tana zubarda hawayen farin ciki da godiya ga Allah,daya nuna mata wannnan rana data dad'e tana mafarki


Shima rungume ta yayi cikin farin cikin dayasamu kansa a cikin cigaba da maganar sa yayi " nasan cewa Ammar yana da kud'in da zai Gina wannan Asibitin,Amma na zab'i inginata masa ita dakaina saboda inason yarike ta da mahimmanci idan yatuna wannann kyautar mahaifinsa ce a garesa,kuma A duk lokacin da akayi ceton rai acikin Asibitin nasan cewa ladar zata je garemu kobama Raye muda sauran iyayenmu...


In sha Allah wannnan Asibiti zata zamo Abin Alfahari acikin wannna kasar mu tana Nigeria dama sauran kasashen...


'Murmushi da dariya ne yake fita akan fuskar gimbiya hassana a lokaci d'aya k'ara rungume sa tayi acikin jikinta,


Murmushin ne shima yake yi na farincikin ganin yalwataccen farinciki a akan fuskar matar tasa,Wanda tada d'e batayi ba, Wanda tun bayan da yafara maganar murabus,juya mulki ga Ammar d'in,Wanda alokacin anti tak'addama sosai dan yakafe yace baiso mulkin shiyasa mai bai cika kawo musu ziyara tun da yaji anfara maganar,sai dai tawaya su gaisa shida mahaifiyarshi da "yan uwansa,Dan har wayar sarki yabar kira tun lokacin da akayi rigimar yakira mahaifin nasa yafi missed call ishirin bai d'aga ba,domin alokacin yana fushi dashi mai tsanani,saboda maganar da sukayi inda yake sanar masa kar yak'ara kiransa da mahaifinsa indai bazai karb'a ba,shiyasa daya kirasa bai d'aga ba domin yasan ba maganar da yakeson ji d'aga bakin sa bace zai furta masa...shiyasa shima sai yasharesa bai k'ara Neman saba tun lokacin duk da dukkansu suna azabtuwa,Amma zuciyar d'ayace,kowa kafiya da taurin rai..



Sarki Ali yatsinci kansa sosai cikin farinciki sanin da yayi Ammar d'nsa zaiyi farinciki fiye da nasa jin wannan labari....


Wayarta tadauko dasauri bayan mik'ewarta d'aga jikinsa,muryarsa ta tsinkaya yana furta karki sanar masa sai ankammala komai har janye maganar basa mulkin,b'ata fuska tayi,tana furta "saboda me adili"? "

Murmushi yayi ganin yadda tayi kamar wata k'aramar yarinyar,yana furta inaso ne kawai yazame masa Abun kamar A MAFARKI ne murmushi tasaki,tana furta hakan yayi, Amma dai bari insanar wa sister wannan abun farincikin sai muyi farincikin tareπ



"Murmushi yayi yana furta to ki kwatse ta koh kar ta kirasu ta sanar da Al Amin,Amsawa tayi cikin k'aramar dariya ai ko haka za,ayi......



Ruwan wanka ta had'a masa a cikin k'aton bahon wankan na silver mai kyau,dake a cikin had'ad'den k'aton toilet din dak'in nata Wanda yaji kayan k'yalk'yali ta ko ina......

Bayan yashiga yayi wanka tafito masa ta da kayan da zai sanya,sannan ta fita domin Bada umurnin akawowa abinci a turakarta,A falon da na biyu kamin kashiga uwar dakin nata,Abincin suka jera cikin tsari mai kyau akan wata had'addiyar carpet din dake malale afalon,Alokacin duka ma'aikata sun gama ayyukansu na rana...


Kuyi hakuri da wannan ba nida isashen chaji ne


Shinko kuna ganin Dr.Ammar zaiyi farinciki?

Kuma zai baro k'asar India?


Shin ko akwai sanadin da yakai sa k'asar India karatu,ko ko dai Ra,ayin kansa ne?.......


Jama'a ina labarin Halee nasan wasu harsun manta da ita ......



A gobe in sha Allah zamu lek'a rayuwar Halee baiwar Muji a wani hali take sannan wace irin rayuwa take fuskanta ne ayanzu shinko Baba Asabe ta shafa mata lafiya ganin idanun Baba Asabe ko kodai tacigaba da muzguna mata......


Wacece ita?


Mekuke tunani game da rayuwar Halee?

Mu had'u a comment section dan jin hasashen kowannenku.......✍️✍️


Shin tsintacciyar ce dagaske kamar yadda Baba Asabe ke yawan furtama taa?


Shin waya bada Amanar Halee da har Baba Adee yakirata da Amana?

Sannan waya bada Amanar ?

Waih........🤭



Nima fa kaina ya kulle 🤔

Kudai kawai kucigaba da bibiyar Alkalamina✍️✍️domin Warware muku wannan labari mai cike da darussa...


Kuyi sharing kuyi comment

💫 FA'EEH BG💫



💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


*Mun kusa gama free pages in sha Allah,Da mungama book one📖,Episode one kenan za,a fara payment,na episode two*!!!✌️✌️💥💥


*TALLA!!! TALLAH!!! TALLAH*

*ina yan kasuwa masu son tallata hajarsu,toh ga dama tasamu domin muna tallata kowace irin hajace daga jihohi daban daban harma da k'asashe,akan farashe mai sauk'i,zaku iya tuntub'armu ta lambobin waya kamar haka*........

*+2348069059746*

*+2348084504630*

----------------------------------------------------------------

*💫A MAFARKI NASANTA*💫

*2023 novel is the story of an innocent girl call Halee yarinyar da* *tataso cikin rashin iyaye sannan ta* *had'u da kalubalin rayuwa mai matukar* *girgizawa inda bayan haduwar ta da* *iyayenta,wayenda suke nesa da* *rayuwarta tasamu loosing memory,sai* *kuma takara samun "psycho" tab'n* *hankali kenan shin ko meye silar* *faruwar hakan?ya ALAMARI AKWAI* *RIKITARWA,SOYAYYA KAM ZAKU* *SHATA,SANNAN YAR UWA ZUCIYARKI* *ZATA TABU*.....*SHIN KO WAD'ANNAN YAN TA'DDA* *ALKALAMINA ZAIYI AIKI KANSU?SU WANENE ABAYANSU ?SHINSUMA ZASU IYA KARBAR HUKUNCI ?DUK DA KASANSEWARSU MANYAN KASA KO MASU MUKAMIN *MENE DASU

Please Login or Register in order to submit comment