Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wanda ke zaune akan mirror da towel daure akugunsa daya kuma agefen kafadarsa, kwantaccen gashi ne abisa kansa Wanda dagani ya hada da jinin larabawa ko fulani daga bayan sa zaka fahimci yana da faffadan kirji tare da kwantaccen gashi Wanda yake luff gwanin burgewa jikinsa ko ina lui lui dashi daganin sa kaga Dan hutu kafafuwansa da tafin hannun sa wayenda yake ta faman murtsuka mai dasu gwanin burgewa Wanda dagani zasu yi kamar na sabon jariri,chocolate colour fatarsa sai sheki takeyi.inda wannan guy din yake furta ai narantse bazan jiraka ba tafiyata zanyi yana maganar ne kamar ransa abace kasan yau muna da meeting ga tarin patients na jiranmu Amma shine kak'i saurin shiryawa,wadannan maganganun dayake yi su suka dawo Dani daga sumar tsayen Dana yi, inda nakai duba na ga saurayin dake maganar,shima dai hadadden ne kamar Wanda naji ankira Ammar, ashe ma shine wannan fari tass din guy Wanda nagani afalo, yasha

Kyau cikin kananan kaya yadora labcoat akan kayan sa inda naga an rubuta Dr .Al Amin jabir Muhammad soja Wanda mafi yawan colleagues da abokansu suna kiransa da Dr AJ...

Dacin Raine bayyane akan fuskar Dr AJ bayan yagama mganar

Yana batun fita ne yaji anriko hannun sa,yana kucce kuccen ya kwace hannunsa kenan yaji an rungume shi dasauri ya turesa yana furta ji iskanci Kai fa Ammar Dan iska ne mtsww yaja dogon tsaki,jiyayi Ankara riko hannunsa wannan karon .....


Mu hadu next page🙏

Gobe in Allah yakaimu


Comment din ku kadai nake bukata...


💫Fa'eeh Bg💫


💫A MAFARKI NASANTA💫 FANS

INAYINKU OVER💯 MUSAMMAN MASU BIBIYATA FACE BOOK INA GANIN COMMENT DINKU INA GODIYA SOSAI🙏KUMA NA WHATSAPP INA GODYA MASU COMMENT DA WAYEN DA BASAYI


Pls like share and comment...


https://chat.whatsapp.com/HO4hVB1luhXGyRzaOdWy68


💫A MAFARKI

NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍

💫Fa'eeh Bg 💫



Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*

Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*


Dan Allah duk wanda yakaranta wannan page yayi mini Addu,A🙏

Allah yabiya mini da dukkanin bukatu na tare da dukkan kulluhin musulmi🙏


EPISODE1️⃣

FREE PAGE8️⃣



TYPING📲📲📲



+++++++++++++++++++++++++++++++++++


wannan karon daya fisge hannunsa baiji an rungume sa ba sai dai yaji anja hannunsa,anzaunar gefen gado,baice kara cewa uffan ba har ya zauna.

Had'a idon da sukayi daDr. Ammar ne yana sakar masa wani shu'umin murmushi ne yasan ya sa galla masa wata katuwar harara yana mai jan tsaki,shiko Wanda naji ankira Ammar A hankali cikin wata kasalalliyar murya ya furta just give me three minute ohk! yakai karshen maganar yana mai k'ara sakin yalwataccen murmushi a fuskarsa, wanda maganar da yayi iya kar labbansa ta tsaya,maganar da yayi ce bayan barowar sa kan madubin,tasanya ni kara cikin natsuwa ta daga sumar tsayen da na kara yi ganin hadadden guy din da na gani ahoto falo Amma tabbas afili yafi kyau daganinsa kaga ingarman namiji mai ji da kudi,mulki da izzah ga fatar nan tasa sai sheki take yi kamar an mata wankan madara sai narasa tantance shin chocolate colour ne skin nasa ko fari ne mai dan duhu,wanda fuskar sa takara nuna hutun da yake samu....



Zazzak'ar muryar sa kuwa kamar ana kad'a sarewa inyana magana kmar kayi bacci saboda dadin ta,saboda zakin ta da taushinta in yayi magana kamar ba,a bakinsa tafito ba,daga yanayin Kallon da masa na fahimci akwai jan aji da izzah da yanga kamar mace kuma baida son magana,Ammar dai daga ni miskili ne na karshe...


Bayan ya gama maganar da iyakar labbansa ta fito inba ka kalli bakinsa ba ba zaka san dakai yakeyin maganar ba,juyawa yayi ahankali yataka kamar yana tsoron carpet din dake kwance male2 ad'akin ta huda masa k'afa,har ya isa inda doguwar sip dinsa take wadda ake bud'ewa da thumbprint inda yasanya dai daga cikin zara zaran yatsun sa na hannu take hadadden sip din tashiga budewa da kanta har ta kai karshe wow! bansan lokacin da baki na ya furta hakan ba,Allah yasa ba wanda yajini...

Kayane birjik kamar botique wasu asama wasu ak'asa,sashen ko wanne daban su trouser,men panties,t shirt ,necktie suma gasu nan atsare ta ko ina sip din kayane atsare chan daga karshe suit ne jere kala kala sai walkiya sukeyi,sai sashen shaddodi,yadukka da huluna irinsu mu hadu banki ,su ku'be, har da irin su tadara mai irin na gidan sarauta kamar yanayin na(raba gardama) labarina...sai dai na wannan likitan sunfi na (raba gardama) kyau kuma design dinsu ba,a irin na nigeria bane daga ganin su kaga bugu turai sun sha kari har sun gaji,sai daga chan sama wata hanger ce rataye da wasu fararen riguna masu kama da labcoat,dasu long sleeve,under wears,short nikers da vest,handkerchief, kowanne da gefensa akan hanger din.


................

Hannunsa ne yana jawo d'aya daya daga cikin fararen rigunan labcaot,

Shi kam Dr.Alamin Aj murmushin bakin ciki kad'ai yake yi yana jan tsaki yana mai duba hadadden agogon da ke hannunsa kamfanin apple,dogon yakara ganin har minti uku ya wuce har yakara biyar akai,Dr.Ammar kuwa duk da yaji jerin tsakin dayake ta faman saki kuma yana ganin hararar da yake ta sakar masa bai tanka saba

.....Komawa yayi yadauko wani had'dden wandon jeans bak'i,bayan ya aje labcoat din,ya juyo kenan Dan ya ajesa kan gado yaji Dr Aj yakara jan wani mugun tsaki wanda sai da Dr. Ammar ya rufe kunnuwansa yana mai yamutsar beautiful face dinsa D'an kallon Dr.Aj yayi wanda yayi tik'in tik'in da fuska,Dauke kansa yayi,A hankali yajuya gurin sip din yana sakin kayataccen murmushi a fuskarsa wanda ya bayyanar da dimple dinsa na gefe daya yatsan sa yasanya cikin kwarewa kamar wani jarumin ya lalaci tsinin hancinsa,wannan dabi'ar sa ce ta lakarta tsinin hanci in yana cikin yanayi mai dadi dakuma yan maganar sa nakai.

Dama haka yake Idan yana jin shirmen sa haka yakeyi da d'ai dai yake zabo kayan da zai saka acewar sa suna masa nauyi ne ahannu,wani lokacin ma in Dr Aj ya ga zai tsayar dasu shike zab'o masa kayan kamar wani karamin yaro

Abun da yasa yajuya ya fahimci Dr Aj yakai kololuwar b'acin rai yanajin uwar hararar da yake sakar masa,ga tsukkin da yake ta faman ja suna neman jaza masa light headache,shiyasa kawai ya juya batare da ya aje trouser dinba yakoma domin ya hado kayan baki d'aya,da isarshi bakin sip din yasanya kyakkyawan hannunsa yazaro farar vest da long sleeve fara kar mai dogon hannu,da handkerchief fari, yana gama zab'ar kayan yadanna wani madanni kamar na ura daga kasan inda ake thumprint,A hankali katuwar sip din tarufe ruff kamar dai yadda take farko.


💫Fa'eeh Bg💫


A hankali yataka zuwa bakin gadon ya aje su anan gefen labcoat din a kusa da Dr.AJ din

Wanda kallo daya yayiwa Al amin Aj ya dauke kansa, yana cigaba shirinsa cikin natsuwa wandon yafara jawowa zai sanya wanda yayi dai dai da d'ago idon Dr Aj,ganin abunda Dr yake kokarin yi ne na sakin towel d'insa kasa yasanya sa dasauri yadauke kansa yana fadin marar kunya kawai yana jan karamin tsaki,bai san cewa Dr motsinsa Dr.Ammar na ankare dashi ba har dauke kan da yayi,shi atunaninsa babu short ajikin sa shiyasa yayi saurin dauke kan nasa duk da yasan ba halin shi bane sakin tsaraici tun suna yara shi ba ya yadda wani ya gane masa jiki in za,a musu wanka dakyar yake yadda wata rana sai dai akai shi gurin Aunty....



Murmushi kawai Dr Ammar yayi yana cigaba da sanya wandon sa acikin dan short din da ya chanza tun atoilet cikin wayen da ke a lakkame a hanger,vest dinsa yasanya da long sleeve dinsa masha Allah na iya furtawa takawaa yayi zuwa kan madubi yana kara gyara lallausan gashin sa da sajensa tare da kara taje sa da murtsuka masa kalolin mayukka bayan wanda yashafa acikin toilet,sannan ya fefesa turare kusan kala biyar oud masu bala'in kamshi,man bakin sa ya shafa :lips balm: wanda yakara kawata kyakkayawar fuskar sa da aina hin kyawonsa da shekin fatar sa,dama bakin sa bai rabo da maskin lips balm domin wannan dabi'ar yasaba da ita tasha man baki kamar mace,shidai Dr Aj kallon ikon Allah kadai yakeyi yabuga tagumi yana yi yakai duban sa ga agogo,ace katon saurayi yazauna ya dinga shafe shafe kamar mace, azuciyarsa yayi furucin.

Dan yin murmushi DR .AMMAR yayi jin maganar da Dr. AJ yafurta wadda yayi kasa kasa,tsinkayar muryarsa Dr Aj yayi yana furta nagode ma Allah da ba maccen nake ba kamace kagani yakai karshen maganar cikin yin dan karamin murmushi Dr aj da yaji abunda ya furta duk da baiyi tsammani yajisa ba dan ciki ciki yayi maganar,sai bai yi mamaki ba dan yasan yadda dan uwan nasa yake da mugun ji kamar kunnen maciji..

sai bai bai basa amsa ba yashare sa .

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

©💫Fa'eeh Bg💫

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

cikin dan kan kanin lokaci dakin yakara gauraye da kamshin turarrukkansa

A Hankali yajawo labcoat dinsa irinta ta Dr. Aj samfurin ta likitota fara tass sai shekin sabon taka takeyi kamar ma sabuwa ce akan kayan sa yadaura irin da yadda kuka san likitota nayi masha kawai zamu ce domin tsaya wa rubuta kyawon da yayi page din bazai dauka ba,stethoscope dinsa dake akan hadadden gadon sa ya sargafa abisa wuyan rigar sa dan danan yakara fitowa likitan sa sak,ga sunan shi nan ya bayyana radam agefen rigar tasa cikin tsari mai kyau inda aka rubuta DR. ABDUL RASHID A ALIYU da manyan baki Amma colleques nasu nasu da childhood friends na kiransa da DR.AA

wasun ma cikin colleques nasu suna kiransa Dr. Ammar a gida kuwa suna kiransa Ammar Saboda sunan kanen mahaifinshi da yaci shiyasa aka masa lakani da Ammar.


A hankali ya juyo inda Dr aj yake sannan ya kalli hadadden agogon zinarin dake daure a tsintsiyar hannunsa kirar kamfanin rolex wanda yadaura bayan tsayuwar sa kan madubin wanda yakara kawata shigar tasa skin din sa sai sheki takeyi.


A hankali bayan yataka ya zabi dai daga cikin shoerock din dake dauke da takalma iri iri masu kyau wanda sai da yafara saka sock baka aciki sannna yasanya takalman nasa masu kyau bakake rufaffi sai walkiya sukai gwanin burgewa

A gogon nasa yakara dan kallo ganin lokacin da yadiba har ya wuce wani ya zo wani yakaru, sannan cikin izza ya furta man katashi mutafi karmuyi late...

wani ...

Kallo da Dr aj yamasa ne yasa sakin wani killer smile wanda ya tsaya iya labban sa,dama da gayya yayi maganar dan yasan mutumen nasa acike yake kamar ya fashe wanda kuma yasan fushin nadan lokaci ne zai sauko ......


Shiko Dr aj dayake kan pressing phone dinsa baice masa komaiba yadauki nashi stethoscope din ya sargafa,wanda dama sargafe yake awuyansa ne,gajiyar jiran Dr Ammar ce tasa ya cire ya ajiye shi gefe,duba kansa yafara yi agaban madubin dan tabbatar da komai normal sannan ya fice daga dakin shima uban gayyar dake tsaye yana kallon sa A hankali ya matsa gefen gadon yadauki wayar sa dake chaji abisa bed side drower sannan ya fice daga cikin dakin cikin tafiyar takama da izzah yana ta faman zuba uban kamshi kamar sabon ango........


Fitar su dakin ce tabani damar

Karewa da Katon bedroom din kallo fari ne tass mai kyau wanda yake katone ne nagaske ashe ma Ciki da falo ne ban lura ba wurin uban sauri,bedroom din tana da fadi sosai gadon ya hadu iya haduwa,da sip din sa wadda take lafe abango kamar babu ta sai gefen hagu ga katon mirror mai dauke da kayan gyaran jiki irinsu mayukka masu tsada manyan manyan turarukka da man gyaran gashi da sauran kayan amfani,sai wata kofa dake gefe wadda nafi tunanin toilet ne inda na lek'a sa ya hadu iya had'uwa dukkaninsa glass ne aciki ga katon bahon wanka nan irin na turawa mai kyau da katon madubi da yaji kayan amfani irins sabulu shower gel da turarukkan wanka,toothpaste, brush komai akwai ga tsakiyar toilet din gudan fankacece komai akwai aciki na bukata ya tsaru iya tsaruwa,curtain din kuma milk ne masu kyau.


Falo na dawo bayan na fito daga toilet din inda falon ya hadu shima ya hadu komai na cikin sa yakasance lite blue and white har cusions da labulayye komai agyare gwanin burgewa kamar ba dakin men ba.


Sawun tafiyarda naji ne yasani waigawa dan ganin wanda ke tafowar

Dr Ammar ne yana shigowa direct bedroom nasa ya yi tsinke

Cikin sanda nima nabi bayansa


Gurin aje takalmi yanufa shoe rock wadda ke cike da takalma na alfarma masu kyau,wadda ke akusa da sip dinsa takalmin dake kafarsa yacire ahankali tare da ciro wasu masu masu kyau sai walkiya suke yi suma cover shoes ne kamar na farkon sai dai kalace ta banbanta wadanchan baki ne a kala su kuma waddan nan fari,bayan yachanza su ne ya dauki yar madaidaiciyar bag tasa kamar ta school mai kyau yasar gafa agefen kafadarsa yana ficewa.

Ahankali yake takonsa har ya fito falo sannan ya isa inda wata dankararriyar mota take fake kirar benz a tsakiyar compound din gidan ,dama Dr aj yayi ya kunnata har sun yi reverse, Ammar yace yayi mantuwa cikin jin haushi Aj ya tsayar da motar anan tsakar gidan.


A hankali yasanya zara zaran yatsunsa yabude front sit yazauna Dr .Aj bai cemasa uffanba duk da yaga chanjin takalmin da yayi cikin ranshi kuwa kuwa fadi yake mutun sai shegen kichifi kamar mace,kai kam Ammar matar ka tabani mtssw yana jan tsaki abayyane, Dr Ammar kuwa bayan ya gyara zaman sa har ya maida karamar jakarshi sit din baya yana jiran Dr aj yatada motar shiru sai dai yaji tsakin da yayi,murmushin mai kyau kawai yayi yana furta man gulma ta kakeyi azuciya koh yakai karshen maganar yana kafesa da manya idanunsa ......Shiko Dr.Aj harar wasa yasakar masa yana furta abunda ma yafi gulmar ka za,ayi,yafigi motarsuka fice daga gidan bayan sun sanya belt mai gadi na wangale musu katon gate din.......



💫Fa'eeh Bg💫



next page tommorrow in sha Allah


Comment dinku kadai nake bukata FANS 💔💋💋 domin shine kwarin gwiwata 🙏🙏


godiya agare ku ta musamman

..........................

fiddausi dan galadima

siddiqerh muhammad

halima bashar bello

ukuteey

anty zee

oum amjad

sha'awa hamis

Oum sudais

Umma

Da ma wayenda ban ambata ba

wannan page naku ne

💋💋💋💋💋💋

Allah yabar kauna💔💔

ina ganiin comment dinku ina jin dadi sosai🙏🙏🙏



Allah yakai haske acikin kabarin ka

Baba Bello ya yalwanta kabarin ka dana dukkan kulluhin musulmi,🙏🙏

Mukuma kasa mucika da imani ya Allah 🙏🙏pls say amin !


* Allah yasa mudace*🙏🙏

Pls like share and comment



💫A MAFARKI NASANTA💫

in my dream i know her

By

Pha'eezah Almstapha

Daga Alkalamin ✍️✍️

💫Fa'eeh Bg💫


Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand 🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*

pen🖊️ is mightier than the sword🗡️*


Group na whatsapp ina mai kara baku hakuri akan abunda ya faru🙏


`´`´`´`´`´`´`´`´`´`´`´`´`´

EPISODE1️⃣

FREE PAGE9️⃣


TYPING 📲📲📲


Tafiya suke yi ahankali kan katon titin dayake da abun burgewa ta yadda aka tsara shi,ba,abun da ke tashi a cikin motar face sautin sanyayyiyar wakar rihana mai taken my umbrella 🌂

Uban gayyar yayi shiru ya jingina da sit din sa yana sauraren wakar idanunsa alumshe fuskar nan sai sa,sai sa ba murmushi ba dariya,karar wayar sane da aka kirane dake ringing waka mai sanyi ta mahaifiya ne yasanya sa bude manyan idanunsa a hankali tare da daura su akan screen din wayar wanda sunan nurul hayat ya bayyana b'aro b'aro b'aro akan wayar da numban nigeria + 234......A hankali bayan ya gama karewa wayar kallo wanda har kira na biyu ya shigo yasanya kyakkyawan hannnunsa ya dauki wayar tasa dake gefensa aje kirar iphone latest one 15 pro max picking din call din yayi yana mai kara wayar akunnen sa akunnensa tare da sakin kayataccen murmushi yana furta Assalamu alaiki nurul hayat,daga chan dayan bangaren,murmushi aka saki wanda yakara sanya masa natsuwa,wslm kyakkyawan likita na takai karshen maganar cikin nuna farincikinta,murmushi ya mayar mata dashi tare da furta fatan kina lafiya nurul hayat? daga chan bangaren ta amsa da lafiya lau ya aiki?Alhamdulillah,ya furta mata cikin kulawa kamar yadda tayi masa tambayar,A hankali yakara furta inasu maheer da nisa,maheer na school kasan suna shirye shiryen graduation ne oh hakane fa jiya ma munyi magana dashi yasanar mun,Nisa fa?ya kara tambayawa cikin kulawa da ladabi amsa tabashi da dama ai nida maher kadai ne agidan sai sarki,yuhanis tana gurin sister Husaina tatare gurin sumy,A hankali bayan gama saurarenta ya furta meyasa kika barta kinsan bata son karatu ga sumayya ma duka daya suke,yakai karshen maganar kamar yana jin tsoron yin maganar yana kokarin danne wani abunda ke shirin taso masa na jin sunan sarki da ta ambata,murmushinta ne yaji tana furta nur yanzu fa ba yarda bace sun girma kowa censu tayi hankali 18+ suke fa kaga kuwa sunyi hankali da channe dai basa son zuwa makarantar kuma lokacin babu Wayo ne gashi ma yanzu suna gab da yin ss.c e.graduation Uhmm kawai yace,bawai dan ya yadda da karatun nasu ba shi atunanin sa mahaifiyar tasu tana kokarin kare su ne kawai dan yasan yadda yake fama dasu in sunje nigeria dakyar da lallashi suke samu suje school...Kuma ehh dagaskiyar ta yanzu sun girma da daine yake tilasta musu zuwa makarantar itada sumy amma ayanzu su da kansu suke zuwa dan sun mahimmancin karatun,wannan kenan......



💫Fa'eeh Bg💫


Shirun da taji yamata ne yasanyata ta A hankali furta YARIMA, gaban sa ne yayi muguwar fad'uwa jin furucin nata yanzun ma shiru yamata dama tasan abunda zai faru kenan, dama irin hakan tana yawan faruwa duk ta kirasa da sunan bakin sa yana masa nauyin amsa sunan, dalili kuwa shine takirasa da sunan ne ko zai nuna alamar cewa yasauko daga fushin da yake ne da mahaifinsa,da kuma jin in yanzu ko yana son sarautar da yake gudu wadda mahaifinsa yake son lakaba masa shima yasamu ya huta wanda kuma shine yasanya sabani atsakaninsu domin kowa kafaffe ne like father like son ,da dai taga alamun bazai ce komai ba,ta furta cikin sanyin murya ABDUL RASHID har yanzu kana nan kan bakan ka ?takai karshen maganar cikin yanayin da bazai iya juraba,wannna karon faduwar da gabansa yayi sai da yadafe kirjinsa wanda ko Dr aj dake tuk'i a hankali sai da yajuyo ya kallesa dan ganin alamar razana atattare dashi ga kuma hannunsa dafe da kirjin sa,A hankali yaji shima jikin nasa yayi sanyi ganin d'an uwan nasa cikin wannan yanayi,Dayan Hannunsa kawai ya riko da hannun da baya driving dashi ya damk'e acikin nasa, yasan cewa tabbas ko ba,a fada ba maganar sarauta ce, akayi masa,wanda ya rasa wace irin kiyayya ce tsakanin Ammar da sarauta da har baison mulkin wanda kuma yake tunanin shine abunda yasanya sa rashin son komawa kasarsu,idanu suka had'a dashi ya girgiza masa kai da alamar be strong man shikuwa Dr.Ammar dauke kansa kawai yayi batare da ya nuna wani abu afuskarsa ba .

Achan bangaren mahaifiyarsa dataji shiru ne yasanyata duba wayar dan tabbatar wa inyana online,,,,,,,,,,,,,,,,,,kuma dama akan sarautar ne yakarbi aikin da kasar india tabasu bayan kammala karatunsu,wanda shikuma Dr Aj yana da burin dawowa k'asar sa ta haihuwa domin yin aiki acikinta dan su taimaki kasarmu ta nijeriya,Amma saboda Dr. Ammar yasadaukar da nashi burin suka fara aikin tare anan kasarta india wanda izuwa wannan lokaci sunansu yayi shura a india dama fadin duniya baki daya,kowa yasan Dr.Abdul rashid Aliyu Ahmad da Dr.Al Amin Muhammad soja,inda kowace k'asa masu dauke da manyan asibitoci suke son su samu damar gayyatar su sumusu aiki koda na dan lokaci ne amma basu samun wannan damar saboda shidai Dr.Ammar kaifi daya ne acewar sa kasar india su suka fara daukarsu aiki har suka yi suna a ko ina to ayanzu bazai iya barin kasar ba dan yaje wata kasar da sunan aiki ba,haka shima Dr. aj duk da yana da burirrika,inda kawai zai iya yin aiki yabar india shine kasarsa ta nigeria ko shi dan saboda nan ne cibiyarsa take,kuma yana son taci amfanin ilimin suwannan kenann......


mukoma inda muke ......

A hankali ta furta karka damu kaji tana mai sakin murmushi,Ina d'ana yake takara furtawa,cikin sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya wadda har sai da taji sautin ta,Wanda shi yakara tabbatar mata da Dr ammar har yanzu yana nan kan bakansa nak'in son sarautar, da wata murya mai sanyi ya furtama ta gashi nan,to basa wayar ta furta masa,Dr aj dake driving yakarbi wayar bayan ya saki hannun na dr ammar a hankali yakara ta akunnen sa yana furta momy yakike cikin murmushi ?lafiya lau my son ta furta kuntashi lafiya,lafiya lau yabata amsa kara furta masa tayi ya aiki Alhmdllh yakara bata amsa toh masha Allah!A hankali takara furta naji kamar a hanya kuke koh?ehh momy,sai ina halan ? dan naga kunfita da wuri yau,ehh momy muna da meeting ne kuma kinga yau monday akwai tarin patients, eh hakane fa toh Allah ya kaiku lafiya akula da titi,in sha Allah yafurta mata,sannan takara furta in kun gama abunda kukeyi anjima inkana freee ka kirani akwai maganar da nake so inyi dakai,cikin girmamawa yace in sha Allah momy i will contact you A hankali takara furta asauka lafiya,Allah yasa ya furta sannan sukayi sallama tare da yanke kiran..........


Kuyi manage da wannan ba yawa...Naso inbaku page biyu but abunda yafaru dazu yadan taba ni,kaina ke ciwo ko typing din nadan yishi sai ahankali.


Allah yasa mudace,Abunda ya tsanan ta agaremu Allah ya yayemuna 🙏


pls like share and comment 🙏🙏🙏🙏


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HO4hVB1luhXGyRzaOdWy68

💫A MAFARKI NASANTA💫

in my dream i know her

By

Pha'eezah Almstapha

Daga Alkalamin ✍️✍️

💫Fa'eeh Bg💫


Dedicated to my lovely sis laila Almustapha Murai💔


*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCIATION

💫P.E.W.A💫

Home of perfect essential writer's together we stand 🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊️*

pen🖊️ is mightier than the sword🗡️*



EPISODE1️⃣

FREE PAGE🔟


TYPING 📲📲📲


Dora wayar,yayi abisa laps din Dr Ammar a hankali Wanda ke jingine da sit dinsa ya lumshe da idanunsa yayi tsif kamar Wanda ruwa yaci ko kwakkwaran motsi,ba abunda yake tunani face maganar da mahaifiyarsa tamasa wadda kusan bayan dan lokaci takan yimasa maganar taji ta bakinsa ko yajanye nasa Ra,ayin bisa ga na mahaifinsa,fatan Sa kawai A wannan karon Allah yasa batayi fushi dashi ba,dan bazai iya jure fushinta ko na second ne abun yawa zai masa azuciya


Wayar Sa da Dr Aj ya aje masa ce tadawo dashi daga tunanin zucin da yaje a hankali yasa hannu yadauki wayar ya tsura mata lumsasaun idanunta kamar mahaifiyar tasa ce agaban sa,Ajiyar zuciya yasauke mai nauyi,yana kara lumshe idanunsa tare da budesu



Maganar da Dr Aj yayi ce tasa yadago idonsa daga kallon da yake yi ma wayar tasa,inda yake furta masa kar ka sanya damuwa aranka nasan awannnan karon batayi fushi mai zaifi ba kai inaji bazata tayi fushi dakaiba saboda daga yanayin yadda muka yi magana da

Please Login or Register in order to submit comment