Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne A hankali ya tunda kince ita tace kije ki karb'i wankin ki iyar da kanki ko kibawa khadija ko kira almajiran da kewankin.Amsa masa tayi da toh,sannan ta fice daga d'akin tana guna gunai kasa kasa cikin ranta afili kuwa badamar fitarwa,Dai inda Halee ke duk'e cikin rana tana wanki wanda bayan fakon idon na Baba Asabe khady ta taso ta rika mata dan kayan nada yawa,jin motsin fitowar tane daga d'akin Baba Adeen ne yasanya khady runtumawa aguje zuwa d'akinsu wanda har sai da Halee tayi d'an murmushi duk da yanayin da take ciki na kuncin zuciya,domin kuwa khady bata mance da kashedin da tamata ba na inta sanya hannunta cikin wankin sai lakad'amata na jaki.....

ooh ni fa'izatu ke kam wannan Baba Asabe anyi futinanniya,har da yar son taki ma baki ragawa to kenan koni mai kwaso rahoton baza ragawa in ankamani kai aiko bari inyi takaina inkara boye kaina.😝


"ke ta furta bayan tsayuwar ta gaban Haleen ki Aje wankin nan ki kira min su idi suzo su idasa shi takai karshen maganar tana sakar mata harara Kinyi arziki Amma ko yanzu akwai wata rana zamu hadu zaki idasa aikin ki takara furwa Halee kasa kasa,A hankali Haee tajawo dogon hijab d'in blue dake mak'ale a igiya tasanya adan karamin dake jikinta cikin dan yanayin sanyin jiki tafice gidan wanda sai da takai zagayen gidan sannan wasu hawaye masu zafi suka samu damar silalo mata tana sharar zufan data tara acikin ranar mai kyaifi da tasha,share hawayen take da gefen hijab dinta aranta tana Addu,ar Allah yabayyanar da iyayenta in suna raye da ahalinta baki d'aya,sannan tafice bayan tsai da hawayen nata.


Wasu yarane guda biyu daKe zaune achan gefen barandar masallacun dakE unguwar tasu ta kyafato da alamar su zo,biyota sukayi har cikin gidan Alokacin Baba Asabe duk ta hada musu kayan dan fita dasu idi almajiri zasuyi ,direct bohol din unguwar sukayi Domin idasa wankin bayan kwasar kayan.


Halee dakinsu ta wuce achan ta tarar da khady na assignment din da aka basu,dashigar ta d'akin ta fad'a toilet dan yin wanka wanda kuma achan cikin bayin ne ta darji kukanta kamar ranta zai fita gwanin tausayi khady tayi tayi tabud'e kofar ta lallasheta ta yi banza da ita hasalima da ta murd'a handle din arufe kofan yake ansanya sakata dole takyale ta tayi mai isarta..



Wankan ta tadauro tare da dauro alwallar la,asar bayan ta lallashi kanta

'karar bud'e kofa ne yasanya khady bud'e idanunta dake rufe wanda dama tsumayin fitowarta takeyi bare datas

Ji shiru.kyakkyawar Halee ta kalla datayi jawur da ita sosai abun ka da jar fata abun sai yabaka tsoro yadda eyes dinta sukayi luhu luhu dasu,gab gab d'in da jikinta keyi ne da khady tagani yasanya ta mikewa da sauri tana taimaka mata tazaunar da ita kan katifarsu tana rika mata kayan ta da tacire a toilet din,taba goshinta khady tayi rau da zafi taji shi,mai ta d'auko ta shafa mata alallausar fatar ta ganin alamun bata iya komai sannan ta fito mata da kayan da zata saka mata mai dan nauyi wanda zai taimaka wurin rage mata sanyin jikinta,dakyar ta amince ta taimaka mata ta sanya mata kayan jikinta zuwa wata rigar yadi mai d'an nauyi da rigar sanyi mai hula da dan hijab din ta baki.


(hijabban gado)😜hijaban gado mana kullum mutun cikin hijab bawani shan iska Allah ni masu wannan dabi'ar tausayi suke bani da dariya kai bawa kullum kamar matar liman ko matan malan ai suna cirewa agaban malan bare ke da ba matar mai sittin ba😂su Halee araga wa kai sako 💬ne sako ne fans nata ku isar dashi koma samu hasken💡💡


💫FA'EEH BG💫

FIRSTLADY🙌




ALLAH YA JIKAN IYAYENMU DA RAHAMARKA YAA ALLAH WAYENDA MUKA RASA🙏😭 DA WAYENDA KE A RAYE🙏


turare tasanya mata sannan tabata paracetamol dan tasamu relief dawuri da kuma bacci,Bayan sunyi rigima gurin shan maganin dan bata son ganin ko kwalin kwayar magani ne Ko allura,tamata dolene wurin shansa ta hanyar furta mata zata sanarwa da (daddy)Baba Adee dakyar ta karba tasha tana ya mutsar fuska.


Allah sarki Ashe muna😩 da yawa Halee shan magani ko wahala😾Allurar ma basauki kai Allah yakara muna lafiya mai inganci🙏


Bargo khady ta lullub'a mata tana mata Addu'ar samun waraka kamar yadda annabi saw💙ya yadda sahabbai suka samodaga garesa idan kaje ganin mara lafiya idan har ciwon bana ajali bane to za,a warke da yardar ubangiji bayan Ankaranta ta sau bakwai akusa da marar lafiyar wannan Addu,a sahihiyace domin tazo alittafan hadisi da dama irin su umdatul ahkam,hakkul mubin,gulubul mara .Da dai sauransu...

Ga Addu,ar kamar haka ..............


*"AS ALUL HAHUL AZIM RABBAL ARSHIL AZIM,AN YASFI YAKA*"Face sai Allah ya yayema masa,sahih ne abu dawud ya ruwaito sa..


wannan lamirin namiji ne in macece za,a ce anyash fiyaki...


kiduba acikin kitabul hakkul mubin na hud'u hadith no.100:cif

a page 10.

zaki samu dayar addu'ar ma wadda annabin yakasance yanayi in yaje ganin mara lafiya apage din..

Allah ne mafi sanin daidai

Allah yasa mudace🙏


Sannan tacigaba da solving din assignment dinda aka basu yau inji malamin maths,A hankali dake kwance tana kallon yar uwar tata cikin so da kauna, cikin yanayin zazzabinta bacci yakwashe ta


*WACECE HALEE*

cikakken sunanta halimatu sadiya umar,tana zama garin bungud'u ita kamar Amana ce a gidan Baba Adee domin kuwa halee yar tsintuwa ce tsintuwa mafi daraja agaresa shiyasa kullum yake jin tausayinta na rashin bayyanar iyayenta,Halee dai kyakkyawa ce takarshe ga shagwab'a da saurin kuka.Halee tasamu gwargwadon karatun arabia duk da yadda Baba Asabe ke addabar ta duk da wani lokcin bata samun damar tafiya islamiyar ma bare boko,ta haddace wani kaso acikin alqur,ani mai girma,kuma tayi manyan littafan fiquhi da hadisai da sauran su domin Halee akwai hazak'a tako ina da ace tasamu bground na kwarai da sai ta fi haka.Halee takasance bata da yawan son magana shiru shiru ce inkaga maganar ta mai tsawo da to Baba Adee ne ko khady,tana musgunawa sosai agurin Baba Asabe sai kuma Allah yasanya mata wani irin hakuri na ban mamaki da tausayi,Baba Adee yanason ta sosai shiyasa komai zai musu ita da khady yakeyi shiyasa har a makarantarsu ma kawayen su da wasu daga cikin malanmansu yan biyu suke kiran su duk da jin ba sunan uba d'ay suke amfani dashi ba amma ganin yar kamar dasuke da juna da kuma shakuwar da tsakaninsu sai ba,a dauki Banbancin sunan uban da komai ba sai suka barshi amatsayin may be sunan wani ne na familynsu take amfani dashi,suma halee su sun san suna kamar dan wasu lokuttan sukan tsaya gaban madubi sudubi kansu tun lokacin da aka fara furta musu suna kama amakaranatar dan kara tabbatarwa dakansu sai dai suma basu daukesa komaiba,Suna kama kam tabbas sai dai banbancin dake tsakanisu na fata ita Halee fara ce tass kamar farin nan na larabawa mai kyau kamar ka k'wanta jini ya fito sabanin itakuma khady black ce ko ince chocolate irin mai kyau d'in nan,khady bata da bata wani saurayi agefe duk da yadda samarin ke musu turu turuwa saidai suna bin umurnin Baba Adee ne da yace sai sungama secondry sannan zasu fara tsayawa da wani wanda itakam dama halee bata tab'a tunanin tasamu damar tsayawa da kowa ba domin acewar basu ne gabanta ba,iyayenta sune abu nagaba da takeson ganawa dasu idan har suna raye awannan duniyar.


wannan kenan agaba zan warware muku komai munma kusa kaiwa inda yadace kuji asalinta da yadda akayi tazamo yar ysintuwa mafi daraja agurin Baba Adee har yake kiranta da Amana agaresa.


©°•••••••••••••••••••••••••••••••••°©

©°•••••••••••••••••••••••••••••••••°©

💫FA'EEH BG💫

FIRST LADY 🙌

IN THE BUILDING👓 EYYH DJ KARAMUN VOLUME💃💃

au ashe typing 📲nakeyi Allah yashiyeni🚲🚲

Allah ya muku Albarka fans💋👏👏


*KHADY*

itama yakamata mubata nata shafin,ko dan yadda tadamu da Haleen mu.


Khadija Abdul rashid shine cikkaken sunanta Haifaffiyar garin bungud'u lg a unguwar sarki mahaifin khadija Abdul rashid ana kiransa da Da Baba Adee inji mutanen unguwar yara da samari yana aiki a talatar mafara wanda duk kwanakki yake dawo wa gida yana aikin taimakon likitoci a chan wanda ada kawai matsayin warda servant security ne mai tsaron kofa sai kuma aka fahimci yana da wani talent kan abunda yashafi tiyata da dai sauran ayyukan likitota sai suka dawo dashi cikin ward din yana taimaka musu da wasu ayyukan,sannan yana d'an madaidaicin kanti achan na saida provision.


Khady ita kad'ai Allah yabawa su Baba Adee da Baba Asabe wadda sunanta na asali yake Lauratu sunyi Auren soyayya da Baba Adee Alokacin yaje yin aikin noma agonar mahaifinsu a kauyen na bungud'u mai suna (gada) gada gadajen Allah kauyen akwai dadi arado.


Ya had'u da ita ne achan lokacin takawo musu tallan fura tun alokacin soyayya mai zafi ta shiga tsakaninsu wanda dan danan manya suka shiga maganar tasu.

Anyi Aure Amarya ta tare agidan da mahaifinsa yabasu wanda sai bayan kusan shekara biyar Allah yabasu haihuwa ta ya mace inda yarinya taci suna khadija,dan shine sunanda Baba Adee ya zab'a duk da saida akayi rigima da mutuniyar fafur bata son sunan,tun alokacin Baba Adee yafara takawa abun burki yakuma san Lauratu bata mutunci dama lunbu lumbu tamasa,take kuwa shima ya bure mata.

Khady itama dai kyakkyawa ce yar black beauty kamar yadda nasanar muku alabarin Halee sai dai kuma ta d'an d'ara Halee girman jiki, A yanzu shekarar ta goma sha takwas a duniya da yan watanni sabanin halee mai shekara goma sha tara cif da wata biyar.

Khady takasance tana mugun son HAlee tana jinta kamar yar uwar ta tajini tasha furta ma Halee ni inajifa kamar tsatso d'aya muke dake inaji jininki na yawo ajiki na sai dai kawai Halee tayi murmushi tace nima haka. duk wata Damuwar halee tasani sai dai bata yadda zatayi,dan lokacinda ta fahimci itama Halee ba innarta ta haifetaba sai tausayin ta yadarsu azuciyarta mai girma wanda shine yake tasiri haryanzu.

itama gwargwado tasamu ilimin arabiya dana boko dan kamar ma komai d'aya sukeyi da Haleen duk da yadda Baba Asabe ke son sakanta ta hakan ya faskara itama tasamu gwargwadon tarbiyya awurin Baba Adee.ta fannin samari babu dokar dai ta mahaifinsu na aiki.


WAZAI MINI TYPING💂


muje zuwa🚲🚲


*GUSAU*


A bangaren sarki Ali yasanarwa da Unni game da dawowar Hajiyar safkare tayi farinciki sosai dan danan takira Ummi tasanar mata farincikin su bai b'oyuwa awannan rana take aka fara shirye shiryen gyara mata sashenta da yakasance arufe duk da duk bayan dan lokaci ana gyaransa,ayanzu ankara kimtsa komai dan jiran dawowarta wanda dama shine kowa ke tsumayi domin hajiya mutunce mai kima a idon Al ummar masarautar don macece mai son mutane.Duk wanda yaga irin gyaran da akeyiwa sai yaji fariciki domin kuwa sun san tabbas dawowa zatayi.UMMI ce takira Ammie dake k'asar jidda tasanar mata,Ammie tayi farinciki sosai jin wannan abun farinciki take itama anan tasanarwa da Ummi zata dawo itama karshen wata sai dai ta gargad'i Ummi da kar tagayawa kowa tanason basu suprise ne,farin cikin da Ummi tashiga baya faduwa yanke wayar sukayi cikin farinciki..


labarin dawowar hajiyar safkare ya karade masarauta har ya isa kunnen gimbiya fulani matar tsohon sarki mai rasuwa wanda itama yanzu mustapha Yashigo yake sanarmata bata wani nuna jin dadinta face Addu,ar sauka lafiya datamata,tana mai furta ita taje ita tadawo bayan fitar mustapha daga gidan,tana mai kyab'e baki irin yadda tsofaffin masifaffun nan keyi Wayenda suka ga jiya sukaga yau.


FULANI TAMU••••••••


Shima muhammad( malan) dayaga irin gyaran da akeyiwa sashen bakinsa yashiga tabewa yana wucewa sashen fulani da shigarsa ko sallama babu ya furta Fulani ki tsaida khairyya daga zuwa gidan nan bansan ubanda zatazo yi ba kawai dan hajiya zata dawo shine itama zata wani kwaso kafafu,kallonsa kadai takeyi tana taunar goronta,cigaba da magana yayi jin bata tanka masa ba.ta kirani fa wai inturo mata kud'in mota saboda bata dasu kuma mijinta baya nan,tafiya kamar ta dole natambayeta mezatayi da kud'in wai mota zata shigo tazo tarbon hajiya,tunda hajiya uwar tace yakai karshen maganar cikin jan guntun tsaki,nace bazan turamata ba indai dan hajiya zatazo shine dan iskanci takira yaya mustapha dan tasan dole ma ya tura mata yakai karshen maganar cikin b'acin rai.

Kallon sa kadai keyi bayan gama jin zancen sa rai b'ace.


Mikomun wayata gata chan kan madubi ta furta cikin wani bacin ran da yakara taso mata,wayar ya mika mata tasanya gilass dinta tana mai dialing numban da aka saving da Auta,ringing biyu ana uku tad'aga cikin shesshekar kuka khairiyyah ke furta na shiga uku fulani abun na alhj har ya kai yafara shigo mini da karuwai cikin gida kuka take kasharban har tana shid'ewa saboda bak'incikin dake cin zuciyarta,fulani ma data kira da niyyar masifa dakarfi take raunar goronta cikin bakincikin da ke turneke ta,sai kuma tasamu kanta da yin shiru, dan tun Auren khairiyya shekara talatin yanzu da yan kai babu cigaba,kuma shegen mijin yaki sakar mata "yaa wanda kuma ita dakanta ta had'a auren rayi danasani marar iyaka ga rashin haihuwa da bayayi ga kashin da yake bata da rashin kula domin ko abinci wannann dakyar khairiyya take samu duk da kasancewar alhjin mai tarin dukiya.

Muryar khairiyya ce tadawo da da ita daga maganr zucin da takeyi i nda take furta Fulani zuciya cikin kara fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai saurare..✍️✍️


Wayyoh khairiyyar fulani ke kuma taki kaddarar kenan😫


Nasan dai kungane wannan khairiyyar koh..Domin sai da namuku kwatta kwatta na labarin tundaga kakanni.Kuma nayi haka ne don kugane dakyau.✍️


ko zai faru da khairiyya Allah dai yasa ba zuciyarta ce take shirin bugawa....


Yawan likes yawan comment yawan page....✍️


Like,share and comment pls


[3/27, 10:05 PM] Fa'eehbg writer: 💫A MAFARKI NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

IDAN KINA BUK'ATAR UPDATE DINA DA ZARAN NAYI TO KIYI JOINNING GROUP DINA MATA KAWAI✍️

https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim
FIRSTLADY 🙌
------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*

*Free book*📙

EPISODE1️⃣
PAGE3️⃣5️⃣


TYPING📲📲📲

••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
not edited..🙏

A hankali ta lallasheta tana mai tambayar ta ya bata umurnin zuwan da zatayi duk "A ah"ta bata amsa bayan ta tsaida kukan nata,kara tambayarta tayi kudin na isar ta eh ta furta tare da kara furta ai dubu hamsin ne ya turo mini cikin mutuwar jiki,umurtar ta tayi da tabishi a alalama dan tasamu gobe yabarta ko jibi tazo,touh tace sukayi sallama.

Fulani ce ta umurci malan cikin wani yanayi da yabata maganinta na hawan jini dake cikin lockern drowern ta na gado dauko mata yayyi tare da jarkar swan mara sanyi yana furta ai duk ke kika ja mata tunda tun farko sai da nace karki had'ata da wanchan tsohon kika kika k'iji tun kafin murabata da Abdul rashid nace miki kibari tasamu wani kika k'i ke ga d'an uwan k'awarki mai kud'i alhaji ai ga irinta nan,Bayan tasha maganin kallonsa take da mamaki jin furucinsa wai duk laifintane,kamar ba dashi da ita sukayi komai ba yanzu kenan ita zai bari ciki tasan idan har khairiyya taji ai tasan ta rasa ta dan zata iya barinta har abada gashi Allah yadora mata son khairiyya kasancewarta itakad'ai mace agareta da kuma Auta,da maln shima tana son sa saboda tasu tazo d'aya shine abokin shawararta amma yanzu jibi yadda yake mata fad'a kamar baisan komai ba kamar kuma ba ita ta haifesa ba.

YAA ALLAH KAR KA BAMU IKON HAIFA "YA "YAN DA ZASU RIKA YIMUNA FAD'A KAMAR SU SUKA HAIFEMU AMEEN🙏

Uffan batace masa ba har ya gama yimata fad'ansa yafice.
Take nadamar da ta dade tana tare da ita ta taso mata na raba Ummulkhairi da Abdul rashid a yanzu da komai ya chabe,hawayenta ta share na tausayin khairiyyah.

A kano kuwa b'angaren Hajiyar safkare sun taso daga kano lafiya tun safe cikin jahar zamfara wuraren karfe sha biyu da rabi na ranar Alhamis,sun samu tarba ta musamman dan duka ahalin babu wanda baizo ba sai mutanen india, girke girke kala kala aka musu da sanya hannun Unni da Ummi.

Farincikin su Nisa da Sumy bai Fad'uwa lokacin da suka hajiyar dan basu san da zuwanta ba Ummi tadai ce su shirya yau zasu je Wurin Unni,Dad'i biyu kuma Inayah tare da ita dan sun saba da Inayah sosai a lokutta da dama su mama dije kan kawo musu ziyara itada hajiya,kuma suna waya da ita awayar Unni ko Ummi.

Janye Inayah sukayi zuwa d'akin Nisa dake chan akusa dana sarki Ali fira sukeyimata kala kala duk rabi ta yaya Abdallah ce dan sun san lokacin baya bata da wani wayau Allah yadaura mata sonsa sai dai shi besani ba har kawo wa yanzu.

Sauraren su take kawai insun fadi abun dariya tayi dariya na murmushi ta murmusa babu wadda ke bata dariya Irin Nisa,Dan Harda Gulmar sumy ta kawo mata a kunne kuma agaban sumy d'in akan mahir inda take shaida mata wai har iyaye sun shiga ciki da sungama karatu za'ayi bikin,k'aton rank'washi sumy tayi mata tana furta wallahi Inayah k'arya take miki,sai kuma suka koma dariyar Nisa dake zubar da hawayen rankwashin da Sumy tayi mata,Inayah ce tajawo ta tana lallashi,sai kuma ta warware jin tambayar da Inayah tama ta na " ina Yah Al amin??

Amsa tabata yana india man sai kuma ta dafe kanta tana furta gosh! tare da rufe bakinta tana furta Nabani Amma dai Aunty Sumy Munafuka kike badai kingaya mata bah,tana k'ara b'are baki zatayi kuka Inayah ce ta jawota ta rungume tana lallashi sannan ta rad'a wata magana akunne da bansan ko ta mece ce ba,dukkaninsu suka sanya dariya.

K'wank'wasa k'ofar da akayi ce tasanya su yin shiru,"waye"cewar Sumy, Muryar Husna ce tasanya su yin shiru inda ta furta nice fa Anty tana turo k'ofar tayi jin ance tashigo,da gudu tashigo bako sallama sumy ce tadakatar da ita ta hanyar furta sallamar fa tana hararar ta komawa tayi da baya tayi sallamar suka amsa mata atare,ya akayi ne Husna ta Halan?inji inayah,hajiya ce take kiran ku,kuzo kuci abinci tabasu Amsa,mik'ewa dukkaninsu sukayi suka fice daga d'akin.

FIRST LADY🙌

A had'adden dinning table d'in dake part d'in Unni dukkaninsu suka iske iyayen nasu,tundaga Su Unni da su mahir har kan sarki Ali da sauran su Abdallah dasu yusuf,isowar su wurin yasanya dukkaninsu suka ja kujeru akusa da hajiya suna saka ta a tsakiya itakuma inaya tana akusa da Abdallah da Husnat,kowa shi yake zab'ar abun da za'a zuba masa..
Had'addiyar fried rice jallof ce da taji naman hanta da kuma white rice da stew ta chicken mai hade da cos low da yaji kayan had'i,sai kuma wainar shinkafa da taji had'i,hajiya ce mai son waina itada nisa saboda ita kayita musamman.drinks ne kala kala.

Bayan hajiya Dukkanin su daga mai fried rice sai mai coslow suka zab'a.
Ahankali suke cin abincin su tun bayan saving dinsu da masu aikin na Unni sukayi,sai su Nisa ne dake k'us k'us din zaman zaman Inayah kusada Abdallah sukeyi kasa kasa Bayan Hajiya duk da hajiya tanaji bata tanka musu ba.

A hankali dukkaninsu suka fara watsewa suna komawa falo sai yarage daga Nisa sai Sumy suka rage da suka tsaya gulma sai inayah dake tsakurar Abincinta saboda jin ta uncomfortable a wurin,Abdallah ne ya furta mata Ahankali Inayah lafiya kuwa?Dasauri tad'ago manyan dara daran idanunta tana sauke su kansa arazane jin yadda yakira sunan nata ba yadda tasaba ji ba,Murmushi ne ya sub'ucewa masa abazata sai kuma ya d'an sauya murmshin ta hanyar furta Allah yasa dai ba tsoro nabaki ba kai ta girgiza masa tana mai sauke idanunta k'asa,Muryar shi ta tsinkayo yana furta bari inbarki kici Abincin ki koh madamm!
Yabar wajen dinning din yana sakin murmushi ya wuce dakin mahir inda suka dosa suma shida Yusuf.

'Su Nisa dake kallon su kamar status gulma ta yi dad'i A hankali suka shek'e da dariya wadda sai da duka su Unni dake firar yaushe gamo suka juyo suna kallonsu,kai kawai Ummi ta girgiza itada hajiya suna masu fad'in Aikin ku kenan Haijya ce ta furta waisu wayen nan yaran yaushe zasu gama boko ne,Murmushi Unni tayi tana furta Hajiya boko ai ba,a gama sa sai dai kai iya yinka, kyab'e baki hajiya tayi,Ganin reaction d'inta sai Unni tayi murmushi ta furta shekarar nan ne ai Hajiya,to ai kam dasun gama makaranta zan zauna da iyayensu amusu Auren sai ahade da inaya itama,kallon hajiya kawai su Unni keyi dan sun san su nisa ko samarin basu dasu bare akai ga fira duk da basu sani ba ko duk suna da wayenda suke so,Dan D'an yau ba'a shaidar shi...

Unni ce ta furta to ai shikenan hajiya ita sumayya yar gida ma za,ayi inaga tana dariyar jin kunyar maganar tata,basu dai tambayeta dawa ba,Amma ita kam Ummi tagane tunda har Unni kejin kunyar maganar toh da mahir take nufin za,ayi yar gidan Murmushi ne yasubuce mata cikin farin ciki sai ta girgiza kai kawai. Muryar Hajiya ce ke furta itama Inaya kamar akwai nata hadin anan dan naji wadanchan ja'iran na maganar wai akalli Inayah da Abdullahi sun dace sun zata banji su ba murmushi dukkaninsu sukayi suna furta Allah yatabbatar da Alkhairi acikin wannan zur'i a tasu Ameeen nikam nace harda mu...

Muryar hajiya ce takara furta da yanzu takwarata NORAH tana duniya da harda ita sai a had'ata da bak'in likitan turai Ammar take nufi haka take cemasa Shikuma Aj bak'in likita.

A hankali takara furtawa cikin sanyin jikin da yasameta Allah yajik'anki da rahama Sadiyaa keda iyayenki,Dukkaninsu suka Amsa cikin yanayin damuwa,sannan suka cigaba da Firarsu har zuwa lokacin da sarki Ali yadawo shida Husnat bayan fitar su falon.
"Inayah ce ke harara su Sumy taana furta gulmaAjali in ba'ayiba a mutu tana mik'ewa daga zaunen datake kan dinning suma mikewar sukayi suna dariya k'asa k'asa suna mata gwalo,falon dukkaninsu sukayi suka jone dasu hajiya aka cigaba da firar yaushe gamo wanda hardasu mahir dasuka fito yanzu aka cigaba dasu.


💫 A Mafarki Nasanta💫
Daga Alkalamin Fa'eeh BG
FIRSTLADY🙌

©️°•••••••••••••••••••••••••••••••••••°©️

*INDIA MUMBAI*
*AMDAVAD*

Amdavad unguwace Babba tana d'ai daga cikin manyan unguwanni agarin mumbai kasancewar ta tara manyan masu muk'aman gwamnati masu fd'a aji.Babban gida ne wanda yake flat katon gate ne golden inda naga wata mota ta shara ro da gudu tana buga horn mai gadin dake gadin gate d'in ne ya wangale mata gate din inda motar batayi tsinke ako ina ba sai a parking space na gidan ko dai daita parking d'in motar ba'ayi ba wata kyakkyawar yarinya ce yar kimanin shekara goma cikin shigar jeans da t shirt masu kyau ta fito da gudu a bayan motar tana kuka,tana nufar kofar dazata sadaka da babban falon gidan dasauri itama wata yar matashiyar budurwa wadda bazata wuce 16yrs ba ta gaban motar a extra seat tana k'wala kiran Lubna! Lubna! Amma ina yarinyar tuni yarinyar ta shige cikin falon.

"Ziyadah k'yaleta kawai naji an fad'a daga bayanta inji yaron da yafito a driver seat shima dai kyakkyawan yarone fari tasa kamar dai yarinyar da aka kira da ziyadah da kuma Lubna,shima dai

Please Login or Register in order to submit comment