Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta wucewarta d'akin su Dan cire kayan kayan jikinta ta sauya wasu Dan Baba Asabe ta Hana ta fita da kaya masu kyau in zata fita in ita kad'ai ce.

Bayan wucewarta d'akin Khady ta tashi dasauri jiki ba kwari ta zube kayan nan ta wuce d'akin Baba Asabe,azaune ta isko ta ta baje manyan kwalayen kan tiles din dakin tana cin chocolate dinta hankali kwance..

Kai Khady ta dafe tare furzar da iska Mai zafi cikin b'acin rai tana furta "Babata hakan Bai dace ba ankawowa yarinya kaya duk kin kwashekke wannan Abun ai Abun kunya ne ma wallahi agareni ,kinsan cewa ko Baki karbi kayan nan ba Halee dole ke zata fara kawowa ki Gani, ko duka kika dauka bazata ce komai ba Babata,kibar hakan yanzu shi wannan cin fuskar duk na mene ne Yan zu duk akaina ne,indai nice banaso wallahi ki barni da yar uwata Kar bakin cikin ki Babata ya kashe mun ita takai karshen maganar kamar zata fashe da kuka..ni wallahi Babata nafison tasamu komai na duniya fiye Dani saboda ita bata San gatan mahaifiya baa ita abar tausayice, meyasa bazaki ji tausayinta tunda Nasan kinsan wacece ita, meyasa bazaki sota kamar ni ba? Meta Miki meta rage Miki wasu hawaye ne masu zafi suka silalo mata...

Wani lafiyayyen Marin da yasauka kan fuskarta ne yasanyata kasa iya furta kowace kalma,Baba Asabe ce ta sauke mata wannan Marin ko tantama batayi Wanda bata tab'a yimata irinsaba domin bata tab'a kwatanta marinta ba sai dai duka saboda yadda takeji da ita,bisa ga Halee da take Shan duka da maruka da tsangwama..

Cikin b'acin rai na maganganun Khady ta furta sakarya kawai tana hararar ta,Khady Dake dafe da kumatun ta tana tsiyayar da hawaye gwanin tausayi...

Cigaba da magana tayi Sha Sha kawai ya za 'ayi ki Had'a kanki da ita eeh takai karshen maganar kamar zata Kara kaimata wani Marin,cigaba da maganar tayi...
Wadda ke yar tsintuwa Kuma Marar asali domin ba,a San asalinta ba, waya sani ma ko yar yar shege ce aka yasar abola Baban ku yakwaso shi Mai zuciyar annabawa,sannan har zaki iya Had'a kanki da ita ke yar halak sannan Zaki Yi mata fatan samun duniya fiye da taki mtssww taja tsaki tana sake furta wawuya kawai,wuce kibani guri ko in tattakaki kinzo kinamun Fada kega uwata,duk zanyi maganin ku Dake har ita sai naga in tare kuka zo DUNIYAR shasha kawai.

Komawa tayi Rai ba'ace na maganganun Khady tacigaba da cin biscuit dinta tana Kara Jan dogon tsaki.

Khady Dake rik'e da kunce ce cikin Rashin kuzari da bakincikin maganganun na mahaifiyarta ta juya tana share hawayenta,Bayan fitowarta ne taci karo da Halee....

Baiwar Allah😥Allah ya kawo Miki mafita✍️✍️

Yau matuk'a HALIMATU SADIYA tabani tausayi wallahi rayuwarta akwai abun tausayi aciki..

Allah muna rok'on ka Kar ka jarabce mu da Abunda zuciyar mu bazata iya d'auka,idan ko ka jarabce mu ya ubangiji kabamu iKon yin tawakkali
Amin✍️✍️✍️✍️✍️


In naga comment da yawa gobe zaku
samu long page...

Comment dinki kamar taki yake agareni Ina godiya 🙏

Ayeesha Abdullahi...🥰

Pls like share and comment...

https://www.wattpad.com/list/1003211273?utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_source=android&utm_content=share_reading_list.

https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim


💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫
Firstlady🙌🙌

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*


*Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣2️⃣


TYPING📲📲📲

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Iftar Mubarak 🍉
May our prayers be acceptedo prayers🤲
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Bayan fitowarta ne taci karo Halee tana shara,Bayan d'ebo ruwan,Dan ta tarar babu Jira tagama da wuri har tafara saharar bayan gama debo ruwan.

hawayenta ta k'ara sharewa gudun Kar Halee ta fahimci wani Abu,bata San kuwa ta makaro ba domin dukkanin maganganun Baba Asabe a kunnenta suka sauka tun lokacin da tamari Khadyn ta fara sharar komai data furta agareta yashiga kunnenta harta yar shegen da ta tsani jin sa abakin Baba Asabe taji.

'cikin sagewar gwiwa ta furta Halee Ashe har kingama kwasar ruwan ta Yi hakan ne Dan ta tabbatar da hasashenta
"Ehh" Halee ta furta cikin son danne kukan Dake cinta arai da k'ololon bakin cikin da take ji har cikin mak'oshinta Yana taso mata ji take Yi kamar ta had'iye zuciya ta mutu....

😥😥😥😥

Khady fahimtar yanayin da Halee ke ciki Wanda take da tabbacin maganganun mahaifiyartane sanadin shigarta hakan domin tasan ta da hakuri Amma gashi ayau takasa b'oye abun da takeji aranta,cikin bakin cikin da bata da maganinsa sai Allah ta wucewarta d'aki batare da ta Kara furtawa Halee komai ba tare da kwasar sauran kayan ta wuce dasu wayenda ke yashe ak'asa.

***Bayan wucewar Khady Wani mugun kuka ne ya taso mata Marar control na ban tausayi,Wanda har saida ta Dad'e bakinta gudun karta k'ara b'allowa kanta wata sabuwar masifar gun Baba Asabe,jikinta har gigirza yakeyi tsananin kukan da take Yi haka takoma da tsintsiya ahannunta tana cigaba da kukanta Wanda Babu mai lallashi...

Cigaba da sharar ta tayi bayan tafara samun natsuwa tana Yi tana sharar hawaye gwanin tausayi kyakkyawar fuskar nan tata tak'ara yin jaaa na kuka kyawawan idanunta masu haske ayanzu sun rikid'a sun sauya sanadin kukan da tayi.

Bayan tagama sharar ne tafara shiryen shiryen d'ora musu abincin dare. Khady ce bayan tayi sallar la'asar ta fito tana Taya ta fira duk da bawani kuzarin firar dukkaninsu Suke dashi ba,musamman Halee firar Khady take mata Amma kwata kwata hankalinta Bai kanta,lura da hakan da kkady tayi tayi ne yasanyata tashi ta d'auko musu chocolate d'aya d'aya Dan dama tana mata firar ne Dan rage mata damuwar da ta Gani kwance akan fuskarta,domin har kukan da tayi Khady ta fito Jin sautinta Amma ganin kukan Shima wata rahamace ta yaye damuwa agurin d'an Adam sai bata lallashe taba, bata Kuma Taya ta aikin ba gudun k'ara b'allo mata wata rigimar datafi wacchan ,Dan duk ranar da tasanya Halee Khady tasanya hannu aciki to dukkanin sai ransu ya b'ace musamman Hale...

Har 'yar son ma BA'A bari ba

Allah ya shirya muna ke gwaggo masifa
Hajiya Laure uwar gidan Baba Adee😹

Kada ku shagala Kuna karatun LITTAFIN AMAFARKI NASANTA
Daga
Alkalamin ✍️✍️
Fa'eehbg
First lady 🙌🙌

🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴

Chocolate din da ta d'auko ta Mik'a ma Halee bayan ta fasa mata shi Dan dawo da ita a tunaninta,kallonta kawai Halee tayi da idanunta masu girma wayenda suka chanja launi tana Mai girgiza kanta tana furta ...

"Banaci"

Sai Kuma hawaye Shar suka silalo mata abisa kyakkyawar fuskarta,lallashinta Khady tafarayi da Kai tana girgiza kanta,alamar tadaina kukan.. tana share mata hawayen gudun Kar Baba Asabe Taji..
Bayan tad'an natsu sai Kuma Ahankali ta fara tsakurar chocolate din din da Khady tayi forcing dinta ta karb'a,ya mutsar fuska takeyi Ahankali Wanda duk Khady na lura da ita har takai takasa jurewa ta dafe kanta da sauri tana furta" Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un". Jin wata muguwar sabuwar azabar data kunno mata Kai domin kanta ne yayi wani mugun sarawa Wanda har saida tadauke numfashi na wucen gadi..Hankalin Khady yayi mugun tashi naganin yanayin da 'yar uwarta ke ciki...

Kaico tayi da halin mahaifiyarta Dan tasan duk itace sanadiyyar motsawar matsanancin ciwon kan na Halee Wanda sai da likitota suka gargade su da Kar Arik'a barinta cikin damuwa ko b'acin rai domin zai iya Sanya pressure dinta Hawa sannan ya Sanya yawan jinin yak'ara girma daga inda yake har yakai inda ba'aso..

Dasauri tadauko d'ai daga cikin maganin nikkanta da akayi prescribing Wanda Zata Rika Sha idan ciwon ya motsa kafin ayi mata neuro surgery din domin shi zai taimaka mata tak'ara samun karfin neutrons dinta.

Maganin Tasha da taimakon Khady sannann ta Rika ta suka wuce d'aki ta takwantar da ita domin maganin Yana Sanya bacci,Bayan tayi bacci ne ita Kuma ta fito ta cigaba da kula da girkin nasu..
Duk abunda ke faruwa Baba Asabe bata sani ba,ana chan ansanya zak'i gaba sai ancinye.
Allah yasa d'an kanoma yakamaki Baba Asabe,kuce Amin🤗

Fitowarta kenan taga in Halee Taga ma dukkanin ayyukan da tasaka ta ci karo da Khady na iza murhu cikin madafa

Tsaye tayi rike da k'ugu tana kallon Khady cikin sannan cikin gadara ta furta ke Khadija ! Uban me kikeyi anan ne Ina ita wacchan natattar da bata da zuciya...

Wai nikam bama na hanaki Sanya hannu acikin aikinta ba?Khady Dake kallon Baba Asabe ce cikin Rashin. Jin tsoro da haushin Babar tata ta furta" Ai Babata bata Jin dadin jikinta ne ciwonta kanta ya motsa Kuma kinsan likita ya a da sharudd'a abar yawan sanya mata damuwa da b'ata mata Rai Amma Kuma Kinga Abunda kika janyo yanzu in ba Allah ne ya bata lafiya ba dole inje in Nemo Baba yadawo gida akoma da ita asibiti Allah ma yataimaka tana da maganinta na rage radadi..

Kuma wallahi Baba ta kika Dake ni yanzu sai na fad'a Masa ke kika tado mata da ciwon takai karshen maganar tana turo Baki gaba da hurar hanta..

Khady tamu watan bakin Baya mutuwa duk da Marin da ka Sha dazu🤣


Muje zuwa
🚴🚴🚴🚴🚴

Sak'ake Baba Asabe tayi tana hararar khady dan Tasan tabbas zata iya sanar da Baba Adee komai har Wannan zagin da Bai San tanayi ma Halee ba na aiban tata da d'iyar shege da marar asali da Marin da tamata,Aiko da ranar ta bani Dan zai iya kora ta gida yadda yake Jin wannann yar tsintuwar,Yanke shawarar bari ta kyale ta kawai ahad'u wata Rana Dan tana tsoron komawa kauyen nan ayanzu ..bayan gama tunanin zucinta ne ta buga k'yafci tare uwar harara ga Khady, sannan ta fice daga madafar,cikin Jin haushin Khady .

Hamdala Khady tayi bayan wucewar Baba Asabe Dan tasan tabbas zata iya sanar da Baba Adee ne shiyasanya tabar maganar nan,da sai taje ta tado da Halee dake baccin wahala cikin pain .

Bayan sallar magrib ne har Halee ta tashi barcin ta garass kamar bata tab'a Jin ciwon Kai ba,Abincin su sukeci hankali kwance musamman Halee wadda bata son cin abin ci Mai nauyi da dare Kuma bata cin abincin dayawa Wanda dama dabi'arta ce, taliya ce Suke ci yar Hausa wadda taji daddawa da kayan Had'i wadda Halee ta d'ora Khady ta iyarr ...

Bayan gama cin abincin nasu ne suka d'an tab'a fira kad'an
Kiran sallar isha'i ne ya tsayar musu da firarsu inda bayan sun gabatar da sallar ne Halee tadauro wanka tare da yin brush ..towel ne Babba tad'auro ajikinta Wanda duk da girman sa sai da yad'an bayyanar da fararen santala santalan
Cinyoyinta masu d'auke da kwantaccen gashin irin na mata sai guntun hijab dinta red domin tana mugun son jar kala itace favorite dinta,hijab ne Wanda tasaba sakawa inzatayi wanka Wanda tadauke sa al'adarta ce ko ince dabi'arta zama da hijabi Ako Ina shiyasa ma ta nemi k'ana nan domin sakawa cikin gida saboda bata iya zama hakanan kunya take ji..

Kyawawan legs dinta take takowa dasu masu taushi kamar na jariri kamar basu taka k'asa ba Ahankali bayan fitowarta gurin wanka,Wanda duk wahalar da take Sha baisanya wani halitta nata chanzawa ba domin haka Allah yayi ta.

Mai tashafa da turare da man Baki sannan tasanya kayan barcinta wayen da tariga ta fiddo su tare da wani farin hijab din fari Wanda yakara haska kyakkyawar fuskarta ya bayyanar da kyawon asalinta na jinin larabawa za ce Kona fulanin Sudan,inda hijab din zai Kai yadi uku haka.

Khady da ta Dan fara bacci ne taji kwanciyar Halee abayanta..

gyara kwanciyarta tayi Bayan tahau katifar bayan ta tofa musu Addu'a itada ita khady dan yau Khady tace Agajiye take ko wanka batayi ba,to ko tana da tabbacin dakyar in tayi Addu,o'in kwanciya barci....

Asuba tagari Khady.

'Juye juye take akan katifar takasa runtsawa tun kwanciyarta kan katifarta tayaki tunanin da yake Shirin shigo mata ta kasa,sai ayanzu maganar Dr Yusuf yayi mata da dukkanin firar da sukayi take dawo mata sabuwa..
'murmushi take ta saki ita kad'ai tana tunano da kyawawan kalaman sa da yanayinsa da murmushin da yayi mata na karshe,murmushi tak'ara saki tunano furucinsa da yace taso shi har har k'arshen rayuwarta ma'ana har abada,Kuma tarik'a yimasa murmushinta Mai narke zuciya,Samun kanta tayi da sakin wani narkakken murmushi Mai harzuk'a zuciya Wanda bata San yaushe yafito ba..

Khady da tun d'azu ta farko inda take jin motsin Halee Wanda shi farkar da ita inda har ta juyo gabanta batasani ba ta zurfafa atunani..

Khady cikin mamakin murmushin Da Halee ke ta saki a tsakiyar Daren nan kamar Mai aljanu ta furta "ke Koh lafiya kika kasa bacci sai faman sakin murmushi kikeyi ke kad'ai kamar Mai shafar aljannu .....

Halee da taji maganar daga samane ta furta cikin dakewa "murmushi Kuma ni Kam ba daini ba tana maganar tana kokarin controlling kanta daga yanayin da take ciki domin har yanzu takasa dauke murmushin a fuskar ta sai blushing takeyi,tare da waskewa gudun Kar Khady ta ishe ta da tambayoyi ko tagane yanayinda take ciki domin tasan ta da kwakkwafi,ita kuwa Khady tun lokacin da Halee ta fara magana khady take murmushi Wanda ita Halee bata lura ba sabd bata son ta Had'a da ita tayi saurin ganota hmmm Khady tayi tana furta "Ur in love sisi" nagane Mai kike yiwa murmushin nan ai dama Baki b'oyemun ba domin dole zan gane,cikin son kawar da zancen Halee ta furta " Love " she pretend as she doesn't know whats love means..meye love ne halan da kike Had'a ni da shi ta Kai karshen maganar tana yatsinar fuska..k'wantar ta Khady tayi wadda sai da ta mik'e daga kwancen tana Sosa gurin domin taji zafi 'yar k'aramar fitilar da Suke ajiyewa ad'akin da daddare saboda Halee da bata iya kwanciya aduhu sai da haske ko kad'an ne ,tajawo ta haska gurin da har yayi jaa abunka ga farar fata hawaye tafara k'ak'alowa na Jin zafi tana furta Allah sai na rama cikin sakuwa da tab'e d'an k'aramin bakinta kamar wata karamar yarinya yar shekara shidaa, cikin k'aramar dariya Khady Khady ta furta In nabarki kika rama Zaki sanar Dani Abunda kikewa murmushi Dan Khady ta fahimci maganar take so awatsar,Kai ta d'aga wa Khady cikin turo Dan karamin bakinta sai Kuma tasaki murmushin k'eta irin zata d'ibo rabon ta Dan har ta hango yadda zata yiwa Khady.
Hannnu Khady ta mik'o mata dai dai gurin da tasan ta k'wanta,kallon hannun tayi cikiin turo Baki sai Kuma ta dungure hannun dukkaninsu dariya suka Sanya dama Khady tasan ba ramawar Halee zatayi ba rigima ce kawai.bayan sun gama dariyar Khady ta furta "inajin ki Mrs Yusuf,ko dai kin fad'a ne " idanu Halee ta rufe najin kunya maganar,sai Kuma A hankali abunka ga Sabon shiga bazata iya boyewa ba tad'agawa Khady Kai
Alhamdulillah Khady ta furta,domin dama Abunda take sonji kenan,Amma ba kwanciyar hankali a tare dasu,dan tunda Halee zata Raka Halee sai da ta tabata Baki kamar ta Masa wulakanci ko taki amincewa dashi domin mutumin kirki ne k'ila Allah yakawo sa cikin rayuwarta ne domin yazame mata jigo Kuma yacika mata gurabun da ta rasa.
Cikin farinciki Khady ta furta "Allah ya tabbatar da Alkhairi can't wait to see your weeding Mr & Mrs Yusuf janyau dariya dukkanin su suka Sanya harda Halee cikin Jin kunya.
Anan Khady tad'an Kara bata wasu shawarwari Dan itama duk da ba soyayyar takeyi ba duk sune,Amma tana d'an tab'a karatun novel a makaranta in class mate nasu sunzo dasu sab'anin Halee da ba wannan ne agabanta ba..
Daga nan suka sakeyin Addu'ar Bacci bayan gama firar tasu suka k'wanta.

Sai muce Asuba tagari.
Amaryar Dr Yusuf
# Team Dr Yusuf Ina kuke ne ?✍️🤗🤗🤗
Nidai nice ta d'aya 🙌🙌

*NIGERIA*

K'ungurmin dajine da yake cikin jahar zamfara.
Wata had'add'iyar mota ce k'irar jif bak'a wulik Mai tinted glass ta faka a chan wani gefe, inda duhun itace ya rufe da dajin,wani Babban mutun ne da ak'alla zai Kai shekara hamsin da Yan Kai ya fito acikin motar da mask na fuska Wanda ya rufe dukkanin ilahirin fuskarsa sai idanunsa da Baki ta yadda baza'a iya shaidasa ba.

Tafiya yayi Mai tsawo Wanda har numfashi yake saukowa kasancewarta Mai Dan jiki..

Taron Dan dazon wasu kalar mutane kake hangowa shigarsu Babu kyan Gani wasun su sun Sha bak'in kaya da rawani kamar irin na buzaye sun rik'e manyan bindigogi masu sarkuna na albarussai a wuyansu gwanin ban tsoro Taron nasu a lissafin kiyasi zasu Kai d'ari uku kowa ya jingina da Babur dinsa Yara da manyan wayenda iyakar su shekara Tara zuwa goma,Bayan isowar sa inda Suke ne suka fara gaggaisawa cikin sanin juna suna Basa girma kamar wani shugabansu ..

Mashin d'in dai daga cikin su yahau bayan sun gama gaisawa dashi suka kama hanya inda sai da suka Yi tafiyar awa uku sannann suka kawo inda wasu manyan manyan bukkoki Suke da wasu mutanen masu irin shigarsu su gasu nan birjik kamar wata kasuwa da guns rike a hannunsu,ga wasu mutanen nan ad'add'aure da da vest ajikin su wacce ta chanza kala a gefe sun ci wuya har sun chanja kamannin fatar su.

Saukowa sukayi suka hade da wayenda ke gurin wayenda Suma a kiyasi zasu Kai su d'ari bakwai ,suka fara shewa da kuwwa suna murna ga oga ga oga tare da harba bindigoginginsu sama irin na karramawarnan,wani ne cikin hausar da Had'a fulatanci ya furta cikin yin shewa oga yazo oga yazo inda duk sauran Suma suka k'ara dauka ...

Cikin zak'uwa yadakatar dasu ta hanyar furta,su senator Jamil da captain Anas da emir Kabir kurya,minister isyaka muradi sunzo jiya ???
D'ai daga cikin sune ya furta cikin gurb'atacciyar hausar sa" aaah oga Amma munyi waya dashu
Har sun bamu wani aiki Mai "wane kalar aiki kenan? Ya Kara TAMBAYA cikin gadara...

Ehh oga shun bamu damar mu shiga cikin Babban Daji lecal gaimen😹

Ba,a ma iya fad'in local government dinba😂😂 .

Muyo kidmashin d'in yar gidan tsohon gwamna Alhaji mukhtar Maja yanzu ma haka munfara shiri shikin shatin nan jamu tafi,sannan anjima Emir Kabir zai Aiko muna da shabbin bindigogi da makamai wayenda kukai shiyo daga kashar Amirierca wasu shanfurin masu kyau yace ma Ba'a cshika shamunsu a nan kusha ba.duk Yana maganar ne acikin Hausar sa Mai garwaye da fulatanci irin fulatancin nan na kasar Mali,Kenya...

Kai mutumen da suka Kira oga yajinjina

Kana ya furta tabbas aikine Mai kyau suka samo Ashe kamar ansani akayo ordern shabbin makamai ,domin tsohon gwamna Alhaji mukhtar Maja ya saci kud'i sosai Dan za'a samu babban kaso agurinsa ,shewa dukkaninsu suka dauka suna had'awa da kabbara kamar awurin yakin jahadi..

A hankali ya taka iZuwa gurinda mutanen Dake d'aure kamar kayan wanki sun fita hayyacinsu ya furta cikin kwanciyar hankali su wayen na kangararrun har yanzu basu fad'i dalilinsu na k'one gidan ba dakuma Wanda yasanya su ba ,zagaye su Yan ta addan sukayi da manyan bindigogin su Abun tsoro har suna Had'a Baki gurin furta shunk'i magana kangararru ne ai dai kaga yadda shukaci wuya tun lokacin da aka kwasosu nan Amma shunki shewa komai,Dariyar k'eta mutumen da aka Kira oga yayi bayan yagama sauraransu sai Kuma cikin dakewa da Rashin tausayi ya furta ku kawar dasu tunda basu iya magana basu da amfani agare mu... dukkanin wayen nan bayin Allah sai da suka razana cikin tashin hankali Jin furucinsa ,cikin tashin hankali suka shiga rokonsu,Amma Ina Basa ji sharri da mugunta ya Riga ya cika zuciyarsu irinta fir auna,Anan take suka Sanya kan bindigoginsu suka bubbugesu Akai sannan suka jera su layi su biyar jina jina Babu kyan Gani sannan suka bisu da harbi tako Ina ,WAl IYAZUBILLAH 😥
Kashin wulakanci suka musu sannan suka jefa gawawwakinsu ga Namun Daji suka cinye Cikin Rashin Imani da debewar albarka .
Rigunane suka d'auko da ke da baje na kayan police suka cinna Masu wuta ,kayan na ci da wuta suna shewa suna zagayar rigunann Dake ci da wutar ..dukkanin wayen nan bayin Allah basu cika ba sai da sukayi Kalmar shahada sannan suka bar duniya ciki rad'adin uk'uba da zak'in Azaba....

Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un🤲🤲Allah ka kawo muna mafita acikin wannan k'asa tamu tabbas wannan page yasaka ni zubarda hawaye domin ire iren wannan kisan na wulakanci shine alummar mu Suke fuskanta ayanzu.
Wayen nan bayin Allah sun bani tausayi sosai inajin abun kamar gaske 😭😭😭
Allah yajikan kulluhin musulmi Allah ka Kara yimuna kariya 🤲🤲

Allah ka kawo muna karshen wannan Rashin tsaro da muke fama dashi acikin jihar mu ta zamfara da ma k'asa Baki daya🤲,Allah Kuma ka rabam da wayen Azzalumman bayinka,Kar ka basu iKon Had'a hanya damu🤲🤲
Allah yajikan wayen nan bayin Allah🤲

😭😭😭😭Naji mutuwarsu wallahi duk da bansan suba Kuma bagaske bane Amma abun akwai tausayi .....😭

Tambayoyinku
????????????????
...su wayen na nan bayin Allah su waye ne kidnapping boko haram ?

Su waye sukuma wayen nan polisawan meye sanadin zuwan su gurin Azzalumman mutanen nan?
meke tsakaninsu da wayen nan Azzalumman ko ince meya Had'a su mesuke son sani ne,??
Sannan su waye ne wayen nan mutane da mask man ya ambato ajere ,captain Anas ,emir Kabir d.s ???
Zaku samu amsar ku
Ku dai inmuku ta bature yace just follow me.✍️✍️

Yau naji tausayin Halee
Sai dai nataya ta farincikin sosai...fadawarta asoyayya😂🤗

Finally dai da alama Halee tagama zurmawa duka,sai Shirin buki💃💃💃munyi nasara mu Dr.yusuf's team🥱🥱
Sai dai muce Allahyabaki lafiya Halee

Ina labarin mutanen India???

Amsar tambayoyinku duk zaku same su a gaba in Sha Allah,idan Allah yabamu Aron Rai duk zan warware muku Saka sala✍️✍️✍️

Kudai kucigaba da bibibiyata.✍️✍️✍️

Kuyi comment
Kuyi like
Kuyi sharing Don Allah🙏🙏🙏

Akwai darasi Mai yawa cikin book din shiyasa nake so ku tayani sharing dinsa,Dan Al umma su Amfana ✍️✍️✍️

First lady 🙌🙌🙌🙌




💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Firstlady🙌🙌


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*


*Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣3️⃣


TYPING📲📲📲

Bayan rigunann sun ciye da wuta ne ogan yace su rubuta sak'o su turawa duniya cewa sun kashe 'yan sandan nan da ake ta Nema ruwa ajallo wayenda ake Nema tun watanni uku da suka wuce,take Anan kuwa suka watsa hotunan Yan sandan nan da yadda suka kashe su har yadda Namun Daji suka lamushe su suka musu cin gilla Wanda Dama sun Riga da sun Yi d'auka.

Hasbunallu wa ni'imal wakil..

Ogane yaciro wayarsa k'irar iphone 14promax yayi dialing numban din da akayi saving da MY TEAM yakira,Senator Jamil Babuga ne yafara yin magana bayan receiving call din cikin yanayin kamar na maye ya furta "yane oga",Shima Captain Anas Lemu Dake cikin Taron Dan dazon manyan Sojoji ne ya mik'e tsulum ya fice daga d'akin Taron bayan Bada uzurin sa na k'arya,A b'angaren Emir Kabir Saraki ne yad'aga Kiran yanayin sallama bayan tashi da yayi daga cikin iyalan sa,sai Kuma minister Isyaka Muradi da yad'aga nasa Kiran Bayan korar 'yan matan Dake

Please Login or Register in order to submit comment