Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basu Yi bincike ba.

Dr.Ammar kuwa sumy ne da Husna da su Ummi suka rungumesa cikin farin ciki.....

...Finally dai sundawo yanzu kallo yadawo Nigeria...sai mu Jira muga ya abun zai kasance...

Allah kabamu iKon kammala wannan book lafiya ya ubangiji๐Ÿคฒ

Maman Abba๐Ÿ’‹
Sis Ayeesha Abdullahi๐Ÿ’‹
naga comment dinku

Ina godiya

Allah yabar k'auna ๐Ÿฅฐ๐Ÿฅฐ๐Ÿ’‹๐ŸŒน

Next page tomorrow in Sha Allah

If you have any suggestions or advice you should contact me via my
Whatsapp&Telegram +2348069059746
Email -faizaalmustapha1940@gmails.comโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

Like share and comment pls ๐Ÿ™



๐Ÿ’ซA MAFARKI NASANTA๐Ÿ’ซ
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalaminโœ๏ธโœ๏ธ
๐Ÿ’ซFa'eeh BG๐Ÿ’ซ

Firstlady ๐Ÿ™Œ


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai๐Ÿ’”

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*

*๐Ÿ’ซP.E.W.A๐Ÿ’ซ*

*Home of perfect essential writer's together we stand๐Ÿค*

*ESSENTIAL WRITER'S๐Ÿ“š๐Ÿ–Š*

*Pen๐Ÿ–Š๏ธ*is migthier than the sword *๐Ÿ—ก๏ธ*


*Free*๐Ÿ“™

*NOTED EDITED*



โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“

EPISODE1๏ธโƒฃ
PAGE4๏ธโƒฃ6๏ธโƒฃ


*Wannan page sadaukarwa ne agareki Auntyna Kuma abokiyar shawarata k'warin gwuiwataMaman Muhammad (haandy)marubuciyar littafin ๐Ÿ“– BAHAR*
*Thanks for the support I really Appreciate it*๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน



TYPING๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ

ยฃยฃยฃยฃยฃ!๐ŸŒน
ยฃยฃยฃยฃ!๐ŸŒน
ยฃยฃยฃ!๐ŸŒน
ยฃยฃ!๐ŸŒน
ยฃ!๐ŸŒน
!!!๐ŸŒน
!!๐ŸŒน
!๐ŸŒน
Mahir ma da hajiya rungumesa sukayi cikin farin ciki,Shima Dr. Aj duk sai da yabisu d'aya bayan D'aya Yana Rungumarsu cikin farin cikin dawowa garesu.

Bayan yagama diramar sa da hajiya Dake ce Masa yazama k'ato ne yarage cin abincin,yaro kamar d'an Dan be kallonta kad'ai yayi tare da yin murmushi Yana Furta bawani nan kedai Kinga santalelen saurayi kyakkyawa Kuma Gani nan bari nan Auren ma da nace zanyi Dake na fasa,dukkaninsu dariya suka Saka ganin yadda hajiya ta kyab'e Bakin.

Unni Dake gefe ma sai data murmusa tana d'an kawar da kanta irin na kunyar nan ta d'an fari ,A hankali ya tako Yana ta faman sakin k'ayataccen murmushinsa Yana dosar inda Unni take tsaye kanta ak'asa Yana zuwa baiyi wata wata ba ya fad'a akan k'irjin mahaifiyartasa ya rungume ta Yana sakin dariyar farin ciki itama Unni dariyar takeyi na farin cikin Jin d'umin jikin yaron nata, Dukkaninsu wani farin ciki ne suka samu kansu ciki Marar misaltuwa Wanda sun Dad'e basu samu kansu ciki ba Marar misaltuwa.

A hankali ya Furta Nurul hayat I 'm back to you kiyi farin ciki Mai yawa,bana son ki k'ara yin Fushi Dani Kona second d'aya kinji..yakai karshen maganar cikin sauke ajiyar zuciya idanunsa na sauyawa daga yanayin daga kalarsu.

Unni kanta kad'ai ta iya d'aga Masa tana taping hannunta akan bayansa alamar lallashinsa Jin ajiyar zuciyar da yasauke,hawayen Daya zubo mata tashare tana Furtawa cikin harshen larabci "marhababika ya Nur",Dan haka take Kiran sa awasu lokuttan,janyesa tayi ajikinta sannan ta d'an d'aga k'afafunta ta sakar Masa kiss a goshinsa cikin farin ciki da murmushi kwance akan fuskarta,kowa Dake kallonsu Unni da Dr.Ammar sun burgesa sosai.

Jikin su Ummi da Nisa yayi sanyi na ganin yanayin da Unni tashiga itada Ammar,A hankali Shima Dr.Aj yatako cikin farin ciki yana rungume Unni barka da zuwa tamasa cikin farinciki itama tana Furta barka da dawowar ka k'asar Haihuwarka Aminullah na,Amsa mata yayi da yawwa Unni cikin farin ciki kamar yadda fuskar ta Unni take wanze da farin ciki,Shima peck ta Masa agoshin sa bayan sa take bubbugawa anatse.

Nisa ce cikin farin ciki ta rungume Dr Ammar tana Furta welcome back Yaya A,cikin farin ciki Shima ya rungume k'anwartasa yana Furta thanks you dear
Cikin farin ciki Mai yawa na ganin junansu.

Dukkaninsu rangama sukayi cikin had'add'un motocin su, mota d'aya suka shiga Dr .Ammar da Aj sai hajiya a front seat wadda mahir ya tuk'o su sai Kuma sauran motocin su Nisa da su Ummi,suka shiga sauran motocin wayenda fadawa suka tuk'o da sauran fadawan da suka zo rakiya.

A motar su Dr.Ammar kuwa hajiyace take ta tsokanar su tunda sun dawo gida sai afara maganar Neman Aure Dan ita Kam duk sun mata tsufa,sai dai Dr Aj ne kad'ai ke tanka mata, cikin Jin haushi ta Furtawa Dr Ammar "wai Kai bak'in likita me ka taka ne waih yau,takai karshen maganar tana rike hab'a, Murmushi kawai Dr.Ammar yayi Yana Furta hajiya mezance Miki , uwar harara ta gallara Masa ta cikin madubi wadda tasanya dukkaninsu dariya har mahir Dake driving,A hankali Dr .Ammar bayan Lumshe idanunsa ya Furta dama danki ta ku rani kikace dole atare zamu koma gida ko,nikam zan k'ara maimaita Miki kin min tsufa sai dai daga nesa, hajiya mere Bakinta tayi tana Furta Allah wadaran naka ya lalace ta cigaba da Jan charbinta batare da ta k'ara Furta masa wani Abu ba, dukkaninsu murmushi sukayi kawai.

Tun dosowar su Babbar masarautar suke Jin tashin busa da algaitu aciikin fadar dan Dr.Ammar ya ce Baya son algaitu su bisa har airport shiyasa aka dakatar dasu cikin masarautar kawai,kid'in gangane ta ko Ina ke tashi,wangale musu k'aton gate din masarautar ne ya basu damar shiga daga cikin Babbar masarautar,jama'ace ta ko Ina fadawa da sauran ma'aikatan ma'ana bayin Dake masarautar,ma'aikatan kowanne Sashe sun fito tundaga sashen Fulani,hajiya,fada,Yaya Mustapha, Muhammad (malan ) da sauran dangi,kowa na tsaitsaye a compound d'in masarautar Jiran dawowar yariman masarautar,shigarsu ciki yabada damar fitowarsu daga cikin motocin su.

had'add'iyar carpet ce Mai taushi aka shimfid'a wadda zata sadaka da sashen Unni,wadda yarima zai hau aka rubuta ur welcome ce shimfid'e agurin, a hankali Dr.Ammar ya d'aura had'add'iyar k'afarsa akan carpet din shida Dr.Aj ma'aikata ne ketayi musu gaisuwa ta hanyar bow,ta hanyar sunkuyar da kansu su d'ora hannayensu akan goshin su hannu d'aya bisa d'aya irin yadda Yan Korea Suke Yi a historical films nasu,hannu kad'ai Dr.Ammar ke d'aga musu shida Aj Har suka shiga Babban falon Unni gaba D'ayan su har su hajiya dasu Nisa,sarki Ali Dake tsaye a Babban falon shida Dady soja ne suka mik'e suka rungume "Ya "yan nasu cikin wani farin ciki sarki Ali ne ya furtawa Ammar Barka da dawowa k'asarka ta haihuwa nayi farin cikin ganin ka Kai da d'an uwanka...Kai Dr Ammar ya d'aga cikin farinciki a hankali Kuma ya furta I 'm sorry Yaya Dady cikin farin ciki sarki ya Furta shiii alamar yayi shiru su. Sun Dade rungume da junansu cikin shauk'in soyayyar D'a da mahaifi,sarki Ali ne ya fara jaye jikinsa daga na Dr Ammar Yana komawa yayi kissing din hannun Ammar din,haka yakoma ya rungume Dr.Aj cikin farin ciki,Shima Dady soja rungume Dr Ammar yayi cikin farin ciki bayan sakin aj Yana Masa barka da zuwa.

Bayan dukkaninsu sungama gaggaisawa aka d'unguma ga gaba d'aya zuwa babban dining Area Dake falon,Nisa ce agefen hajiya tana facing chair din Dr Aj ita Kuma sumy tana a kusa da masoyinta Yaya mahir,sarki Ali da Dady soja suna akusa da juna Unni da Ummi sun Saka Husna atsakiyarsu,sai Dr.Ammar Akusa da Dr Aj Yaya Yusuf da Abdallah ma suna agefen hagun hajiya, dukkaninsu Bismillah sukayi bayan kowa yazab'i Abunda yake so ma'aikatan sunyi saving dinsa.


A hankali Suke cin abincinsa Babu motsin da Kake Jin sai na k'arar cokulla da sautin fillet,Dr.Ammar ne Dake cin had'add'iyar basmatic rice wadda taji had'i na musamman,Wanda Unni ce tayi kokarin Had'a Masa ita kasancewarta d'ai daga cikin favorite dinsa, kamar ance ya d'aga idonsa yahango k'anwartasa Abar k'aunar sa Nisa ta Tsurawa sashen da Suke da ido Ahankali ya bi inda take kallo da ido Dan yasan dai bashi take kallo ba dan ya tab'a Jin sumayya nagayawa Aj n irin son da yuhanis din ke Masa Kuma agaban sa ma yasha Furtawa sumyn baijin komai akanta tunano da maganar da Aj yayi suna India ,ya yarda cewa k'ila jarabawar k'anwarsa ce kenan kamar yadda Dr.malini take ta wahala da soyayyarsa,Amma shi ko kad'an bayajin soyayyar ta aransa,sunan Dr.malini ne da yashigo kansa yaji tausayinta ya kamashi abin cin ne ya gunduresa na tausayin k'anwarsa,A hankali yazare hannunsa dake rik'e da spoon,Lemu ya tsiyaya A hankali kurb'a biyu yayi Yana mik'ewa,mik'ewar sa tsaye ce tasanya Aj kallon sa da mamaki Dan yasan badai k'oshi yayi ba,cikin yaren India ya Furtamasa "wai harka k'oshi ne "kai kad'ai Dr Ammar yad'aga Masa ya juwarsa Yana furtawa Unni "Nurul hayat natafi inyi fresh up,tambayar sa tak'arayi ya k'oshine ko Akai Masa d'aki dan batasan tambayar ce Aj yamasa ba,eh" ya furtamata atakaice cikin tattausar murya wadda mahaifiyarsa kad'ai kesamun irin wannnan sautin,juyawa yayi yaci gaba da tafiyarsa batare da ya tamkawa hajiya Dake jansa da wasa ba,har ya b'acewa ganinsu yanajin sautin Muryar hajiyar na fad'in kayiwa ubanka Mustapha Dan murmushi kad'ai yayi Yana girgiza kansa,Yaya Mustapha da shigowarsa falon kenan cikin yar dariya ya Furta hajiya me Kuma muka aikata daga dawowarmu yau,kawar da kanta tayi gefe irin Jin haushin nan tana Furta barni da ja 'irin wai ni zai kyale Ina magana Dan shegantaka to ni nama fasa Auren,dukkaninsu dariya suka Sanya,rigimar hajiya da Ammar akwai abun dariya aciki,duk da Baya kula ta ma.

Mik'ewa hajiya tayi Dan dama tagama cin abin cin ne ta k'oshi tare da barin gurin.

Aj da tun d'azu yake lura da irin kallon da Nisa ke Masa ne yad'an kawar da kansa bayan d'an k'ara nazartar ta da tabbatar da zarginsa arai akan tabbas wannan shine dalilin da yasanya Dr Ammar Barin wurin Dan ya tabbatar ba k'oshine ya tadashi ba yasan yadda yake Baya wasa da cikinsa musamman Abunda yake favorite nasa,k'ara d'ago kansa yayi inda karaf idanunsa sai a cikin na Nisa da duk Rabin hankalinta nagunsa,kasa dauke idanunsa yayi sai dai suka cigaba da kallon junansu Babu d'auke ido,Nisa ce ta Yi karfin halin sauke nata Idanun k'asa cikin yar kunyar data kamata,duk abun nan da ke faruwa atsakaninsu Babu Wanda Bai luraba duk su Unni sungani dasu Dady soja,sumy murmushi kad'ai tayi tana fatan Allah ya karkatowa Nisa Hankalin yya Aj,Dama tasan dole zai so Nisar Dan ayanzu kosu kansu sunsan suncika manyan 'yan mata dan duk wata halitta Dake jikiinsu tak'ara Bayyana tasan duk chan Baya fad'e yake Yi bata cikin tsarinsa tasan cewa Dan baiganta bane ayanzu....

Shima Dr Aj kawar da idonsa yayi yanajin nauyin Had'a idon da sukayi da sarki Ali Lemu ya kurb'a a hankali sannan ya mik'e Shima yabar kan dining zuwa sashen su,Murmushi kad'ai sarki Ali yayi bayan wucewar Aj din tare da girgiza kansa.

Nisa da keta ya mutsar abincin Dake gabanta da cokali na Rashin jinta comportable tun lokacin da Dr Aj yakamata tana kallonsa,itama tayi tsam ta bar kan dinning din, sumy dake k'unshe dariyarta ce ta furta jirani Nisa,isko ta tayi inda take tsaye Sannan suka cigaba da tafiya tana tsokanarta da Mrs Al Amin, Murmushi Nisa keta saki Jin sunan da Sumy ta Kira ta dashi bayan isarsu d'akin Nisa ne sumy keta sakin dariyar da take k'unshewa abakinta tana Furta" wai Nisa Kinga irin kallon da Yaya Aj yake Miki duka fa su Ummi sungani Allah ma ya rufa muku asiri hajiya tabar kan dinning yau da sai kunji kunya ba yar kad'an ba Dan Nasan intafara tsoakanar ku takai karshen maganar cikin sakin karamar dariya......

'Nabani Nisa ta Furta tana d'ora hannayenta biyu akanta sai hawaye yanzu kenan duk su Unni da Abbah sun ganemu hawaye kuwa sai k'ara kwaranya Suke Yi A idonta,lallashinta sumy farayi tana Furta mata "aikin ma jidadi Nisa hakan komai zai zo dasauki bakyaso kowa yasani ne kamar nida Yaya mahir,Kinga hakan cikin sauk'i sai a Aura Miki Yaya Aj sai ki zama Mrs Al AMIN JM SOJA dariya ce ta sub'ucewa Nisa wadda tasanya kyawawan dimples dinta bayyana masu yanayi da na Dr Ammar cikin murmushi da yar k'aramar dariya kamar wata yarinyar yar Sha uku ta Furta wa sumy " hakane Kuma fa Aunty sumy"

K'aramar harara sumy ta sakarmata tana Furta yau Kuma nak'ara samun auntyn dariya suka Sanya. sannan suka cigaba da hirar su sumy nabata shawara yadda zata janyo Hankalin Yaya Aj kanta asauk'ak'e.

A b'angaren Dr Ammar kuwa tun bayan shigarsa had'add'en d'akin nasa da yaji kayan more rayuwa Wanda yaji white paint da pink k'aton falo ne Wanda yakusa girman falon su na India acikinsa akwai kitchen,da store sannan akwai d'aki biyu Jere da juna Babbar Tv ce ta kamfanin Apple jingine a bangon falon wadda takusa cinye Rabin bangon sai kujeru na Alfarma farare k'ar sabbin zubi da akayi musu,sai labulayye pink colour, sai d'an karamin fridge Shima agefe,
d'akin batarkace ko Ina sai k'amshi ke tashi ko Ina musamman turaren mamallakin d'akin Wanda yakasance kamar dashi aka Gina d'akin sabo da yadda ya kamsashe d'akin da kamshi Mai dad'i, ga sanyin a.c da yak'ara wa d'akin yanayi Mai dad'i.โœ๏ธ

๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšด

A hankali yake takonsa har yakai k'ofar bedroom nasa d'ai daga cikin k'ofofin Dake ajere yabud'e inda wani daddan d'an k'amshi yaziyarci hancinsa da yasanyasa Lumshe manyan idanunsa Yana sauke su acikin had'add'en bedroom din nasa,Bedroom nasa Shima babbane d'aki ne Wanda yak'unshi makeken gadonsa da wardrobe Mai aiki da controller da taji madubayye ta ko Ina sai walk'iya takeyi kayan d'akin milk ne Shar har labulayye d'akin Masha Allah komai yaji zam zam.

Da shigarsa d'akin ya fara rage kayan jikin sa guntun wandon sa kad'ai yabari.

wani lafiyayyen towel fari k'ar Mai taushi ya jawo bayan bud'e sip din tasa ta hanyar yin amfani da controller nata,A K'ugunsa yadaura inda towel din yakara haskaka surar jikin sa wadda ta Bayyana ta k'ak'k'arfan namiji Mai jini ajika dogo Mai siffar k'arfi kamar d'an wrestling six spacks dinsa sun Bayyana irin na tiger shroff,kayan da yacire ne direct ya wuce dasu toilet,toilet din Masha Allah Shima ya had'u ba kad'an ba fankacece guda,Dan Yana yanayi da na gidan su na India. Kayan yasanya acikin washing machine nasa k'irar k'asar Chinese,busar dasu yayi bayan sunyi tass Dama bawata daud'a ce dasu ba,wankansa yayi acikin had'add'iyar shower dinsa wadda ko Ina tana iya isko ka tare da wanke kwantacciyar sumar sa Mai laushi, wadda gyara ya ratsa ta da sabulu Mai Sanya k'amshi,sannan yak'ara d'auro wani Sabon towel pink Dake mak'ale a hanger d'in toilet d'in,cikin d'ai daga cikin had'add'un towel d'in Dake mak'ale agurin tare da d'an k'aramin towel Wanda yake Dan goge kansa.


Kayan da ya wanke yad'auko a hannunsa da'ya,d'aya Kuma rik'e da towel din da yake goge kansa dashi,Bayan ya fito ne ya a je kayan akan had'add'en gadonsa k'irar Italy.

tsaye yake akan Babban mirror n Nasa Yana goge sumar kansa wadda take Shan gyara Ako da yaushe,Bayan yagama shafe kannasa yasanya Masa mayukkan Dake Jere birjik akan madubin nasa na gyaran Kai masu tsada bayan taje sumar inda take kuwa tad'au shekiyi gwanin burgewa Bayan ya gyara kan nasa yajawo mayukkansa na jiki masu tsada wayenda ke k'ara haskaka chocolate colour skin d'insa,yashafa adukkanin sassan jikin sa, kyakkyawar fatar sa sai shek'i takeyi gwanin burgewa ko Ina lui lui Masha Allah tafen hannayen sa da k'afafun sa sai walk'iya sukeyi,tsadaddun turarrukansa yajawo ya feffesa na body spray masu dad'in k'amshi,man bakinsa ya shafa (lipsbalm)Wanda ya K'ara haskaka kyakkyawan pink lips dinsa,tare da kyakkyawar fuskarsa Mai cike da kwarjini gwanin burgewa.
Bayan yagama'yan gyare gyarensa da yan shafe shafensa,Ya Sanya kayan da ya wanke acikin sip din sa bayan ya bud'e ta,domin shi mutun ne Mai tsafta Baya son ganin kowane irin tarkace a inda yake,yasansu agefen da ake mak'ale kayan da ba ayi ironing nasu ba.

kayane birjik a cikin wardrobe d'in tun daga kansu vest da panties na maza da short trouser,jeans da t-shirt da suit sai, harda sashen da towel Suke da handkerchief,sai kayan mu na Hausa tundaga kan kaftani shaddodi kala kala irin su gizner,meter d.s ,da yadudduka zubin k'asar Morocco,dakuma had'add'un huluna kala kala duk Wanda kuka San maza na sakawa Babu Wanda babu agurin komai atsare gwanin burgewa abun ba,a cewa komai sai Wanda ya Gani.

Wani tattausan yadi ash colour ya Ciro mara kauri da farar vest da short din sa black..shirinsa yake Yi Ahankali cikin yadin inda ya fito tsaf kamar kasace sa ka gudu dashi kyakkyawar fuskar nan tak'ara haske kamar tauraro acikin taurari idan ka kalle sa Sau d'aya sai k'ara saboda yadda yadin ya k'arbe sa yayi fitting din sa sosai kamar wani ango.

Towels d'in da yayi amfani dasu ya Sanyo acikin washing machine bayan ya ciresu.

Turarrukansa masu k'amshi yak'ara fesawa ajikinsa Yana k'ara Duba kyakkyawar fuskar sa Dake ta shek'i acikin madubi ganin yadda yadin yazauna ajikinsa kasancewar baicika Saka irin wayen nan kayan ba,lakace tsinin hancin sa yayi da dogon ya tsarsa najin wani yanayi Dake shigarsa na farin cikin dawowar sa ga ahalinsa gaba d'aya Yana sakin wani narkakken murmushin da yakusa sumar dani.๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ


*Kai fa'eeh Arage k'arya haka*๐Ÿฅต๐Ÿฅต

Ai shi gida na da banne..โœ๏ธโœ๏ธ
Yo dama ai kowa yabar gida gida yabarsa
A halinka sune komai naka malan a duk inda kaje ka dawo sune dai...

Nigeria k'asar mu tagado muna cikin ta har ......๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšดyau da Banda gobe but wani sati zamu koma india๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚

Allah kayafe muna๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ

# Maman Abbah
# Maman Muhammad
# sis Ayeesha Abdullahi
Ina godiya da kulawar ku Allah ya bar k'auna โœ๏ธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒนโค๏ธ


*If you have any questions*
*U can chat me on my telegram account*
*Via dis number*
*0806905946*


Kuyi comment please
Kuyi sharing
Kuyi like.๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™


๐Ÿ’ซA MAFARKI NASANTA๐Ÿ’ซ
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalaminโœ๏ธโœ๏ธ
๐Ÿ’ซFa'eeh BG๐Ÿ’ซ

Firstlady ๐Ÿ™Œ๐Ÿ™Œ


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai๐Ÿ’”

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------
*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*

*๐Ÿ’ซP.E.W.A๐Ÿ’ซ*

*Home of perfect essential writer's together we stand๐Ÿค*

*ESSENTIAL WRITER'S๐Ÿ“š๐Ÿ–Š*

*Pen๐Ÿ–Š๏ธ*is migthier than the sword *๐Ÿ—ก๏ธ*


*Free* ๐Ÿ“™

EPISODE1๏ธโƒฃ
PAGE4๏ธโƒฃ7๏ธโƒฃ


Idan Baki karantaba ki fara kar abaki Iabari yar uwa,littafin ๐Ÿ“š๐Ÿ“š๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซAMAFARKI NASANTA ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซnadabanne Dan haka nake k'aunar wannan book d'in kasancewarsa haka da yanayin siffar littafin da yadda yazo mini nida masoyansa...โœ๏ธโœ๏ธ
Inkimason ki tabbar da zancena kawai ki fara bibiyar alkalaminaโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ
โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“โœ“


TYPING๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ๐Ÿ“ฒ


\\\\\\=\\\\\\\=\\\\\\=\\\\\=\\\\\\=\\\\\=\\\\=\\\\\

A b'angaren Aj Shima Bai zarce ko Ina ba sai A bedroom dinsa D'ayan d'akin Dake kusa Dana Dr.Ammar...
Duka yanayin d'akin nasu d'aya ne sai dai kala ce ta banbanta,nasa kayan d'akin purple n lighte da labulayye purple masu haske,wankansa Shima yadauro tare da Alwallar sallar azahar.


Dr.Ammar ne ya fito cikin Shirinsa anan falo ya tarar da Dr.Aj da har ya yashirya cikin blue yadi,da hula jaddara black Mai kyau, da takalmi bak'ake irin na Dr.Ammar.

Kallonsa Dr.Aj yayi Yana tab'e Baki na Rashin ganinsa da hula Bai Yi mamaki ba Dan yasan dama tun suna k'ana bayason Sanya hula akansa acewarsa takurasa takeyi wai.

Cikin tafiyarsa ta mazan jiya ya Furta"kataso muje ko in wuce in barka nan Yana maganar bisa ga har yakai bakin k'ofar fita falon,Aj Dake zaune akan cussion speechless ya Furta "tafiyarka cikin Jin haushin sa,Dan tun d'azu yake jiransa duk da yasan cewa Yana chan Yana shiriritarsa,ganin cewa ya rigasa tasowa dining amma har yanzu Bai shiryo ba.

Hararar bayan sa Dr.Aj yayi tare da tasowa ya biyo bayansa.

Shikuwa Ammar murmushi kad'ai yayi Yana Ida ficewa daga falon,fitowar Aj tasanya Dr Ammar Dake jiransa su wuce tare abakin k'ofa.

Dr.Aj da ya fito ne yayi kamar baiga Ammar ba yacigaba da tafiyarsa,murmushi Dr.Ammar yak'ara saki ganin Abunda Aj yayi Masa,Shima Bai kulasa ba kawai yacigaba da tafiyarsa,har suka jera atare suka Isa Babban falo.

Koda Suka iso falon sun tarar da su Hajiya dasu Unni zazzaune su Dady soja dasu Mahir,Abadallah duk sun wuce masallacin
Gaida su sukayi,sannan suka wuce masallacin fada inda dama already kowannen su yad'auro alwallar sa Dan gabatar da sallar azahar.



Bayan dawowar su daga masallacin sun tarar da mama dije ta iso daga garin Kano itada Inayah,su Nisa sunyi farin ciki sosai da zuwansu.

Mama dije ce bayan tayi masu Ammar Barka da zuwa take tsokanarsu,yanzu Kam tunda andawo gida samarin Aunty sai afito da matayen Aure tunda Allah yakoro muna ku,Dan haka take kiransu dashi inzatayi musu irin wannan wasar sbd gimbiya Laila..,takai karshen maganar tana sakin yar dariya..

Cikin yar dariya Dr Aj ya Furta Aunty dije kizab'o mana matayen kawai Dan duk cikin mu nan babu mai budurwar bare Akai ga mag...yakai k'arshen maganar Yana susar kansa bayan yad'aga hularsa irin na Jin kunya tare da sakin yar dariya...

Dukkani dariyan sukayi ta maganar Dr.Aj,shiko Dr Ammar ko tankamata baiyi ba Bai nuna yasan abun da ake magana ba afalon ko mama dije tayi magana, Hajiya ce ta Furta"Kai kafi k'arfin ka amsawa uwar taka,shegantakar taka har ta shafi uwayenka takai karshen maganar tana harararsa ..

Murmushi kad'ai yayi daga jinginen da yake akan hannun kujera batare da yabawa hajiya Amsa ba sannan A hankali ya Furta "Aunty dije kibar hajiya lokaci na zuwa"
To Allah ya nuna munashi lafiya ta Basa Amsa,Amin dukkaninsu suka Amsa. murmushi tayi Jin ya Furta tabar hajiya..
Hajiya kuwa wata uwar harara tasakar masa tare da kyab'e Baki tana cigaba da Jan charbin ta murmushi dukkanin su sukayi na hararar.



Inayah ce da yanzu ne fitowarsu daga d'akin Nisa ta rugo da gudu ta rungume Ammar cikin farin ciki tana Furta sannu da zuwa Yaya A,Amsa mata yayi da yawwa cikin sakin fuska har da yimata Yan tambayoyin kulawa.
Gurin Dr Aj takoma Shima ta rungumesa tana Masa sannu da zuwa cikin farin ciki kamar yadda tayiwa Ammar shima Yan tambayoyin yayi mata na nuna kulawa agareta.

Bayan takoma tazauna ne inda su sumy Suke ne yad'aga idonta sai acikin na Abdallah wani irin mugun kallo yabita dashi na kishin rungumar da tayiwa yayyen nata,kawar da kanta kawai tayi fahimtar kallon da tayi mata.

Aj ne ke kallon sashen da su Nisa Suke,shi har mamaki yake,magana yake azuciyarsa shin wai har yaushe sukayi wannan girman,girman su yabasa mamaki Dan sun Dad'e basu lek'o Nigeria ba, duk da suna video call dasu Amma ganinsu azahirin girman da sukayi na Fili yabasa mamaki matuk'a....

To kabasu mamakin su man๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿšด๐Ÿ˜‚da tsegumi๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿฅต


Saurin kawar da kansa yayi Bayan kallo ma kansa da yayi tudun Yan madaidaitan breast din Nisa da suka taso akan akan doguwar rigar tata ...

Dr Ammar Dake kalle dashi ne ya girgiza kansa kawai Yana sakin murmushi Akai kaice tare da yiwa k'anwarsa fatan samun soyayyar Abokin nasa Kuma d'an uwansa.

Firar yaushe Gamo suka cigaba da ita ga ba d'ayansu,Anan sarki Ali yasanar da ginin Babbar Asibitin da ya gimawa su Ammar D'in dukkaninsu sunyi farin ciki sosai,har su Unni da suka San da maganar yasanar musu wani sati za'a bud'e Asibiti..

>>>>>>>>>>>><<<<<<<>>>>>>>>>>>>>>>> Ranshi ab'ace yake magana ta waya da Wanda ke akan layin Kiran..ya akayi Baku same su ba kuka bari suka sub'uce muna, wannan maganar banza ce ace operation bai yuyu ba,tun farko sai da nasanar muku tun A Airport ku farmaki Yan banzan ku kashe min su shida Mahaifin nasa,ta D'ayan b'angaren ne aka Furta masa Ai uban nasa Bai je hililln jirgin ba,inda Muryar wani bafullace ke fidda wannan sauti cikin yar damuwa da b'acin Rai..
Ta D'ayan B'angaren malan ne yak'ara furta yanzu kenan wannan damar ta sub'uce muna mun Rasa wannan Babbar damar yakai karshen maganar cikin kunar Rai kamar kamar zaiyi aman wuta.

Shima bafullacen ta b'angaren sa yak'ara Furta "arado oga baka ga manya manyan shojojin Dake a Airhort ba, ๐Ÿ˜‚wai Airhot
Kashan bamuje da yawa ba mu biyar kad'ai muka she dagani shai k'ira da jan maje da Mai Adda,da zarto,Dan bamuyi jaton zashu mana haka

Please Login or Register in order to submit comment