Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

intayi musu laifi,A hankali ta bangaren Unni ta furta Allah yajikanki da rahama laila da dukkan kulluhin musulmi,Ameen Ummi ta furta cikin yanayin da suka tsinci kansu aciki bayan tunano da yar uwar tasu.

.....cikin farinciki Ummi take furta Alhmdllh Allah mungode maka bayan gama jin maganar ta Unni akan maganar su Ammar,In sha Allah kuwa yaya bazasu sanda komai ba sai lokacin da yadace Ta furta cikin murmushin ta daya kasa tsayuwa, sallama sukayi kowa ya ajiye wayar tasa cikin farinciki.


Unguwa ce Babba tamasu kud'i ana naga motar da ta dauko su Nisa ta shiga inda ta parker a wani tangamemen gida wanda tun daga gate din zaka san naira ta zauna Ma masu gidan,Horn drivern sarki yayi sai ga wani gabjejen soja ya lek'o bayan ya shaida suwaye aciki motocin har yan rakiyarsu,sai

Wangale musu katon gate din,Gida ne na alfarma ko ina tsaf komai atsare tundaga parkinga spqce dake shake da manyan motoci na alfarma ga shuke nan masu kawata gida,sojoji ne birjik kowa datasa kalar suna shawagi acikin babban compound na gidan,D'ai daga cikin sune yataso yana kokarin bud'e musu k'ofar motar,Nisa Dalla masa harara tana kowa ya saka ka ka kicifaffe,shidai sojan nan bai takan taba face komawa sashen da Sumy take ya bud'e mata,Itama Nisa budewa tayi dakanta inda ta fito tana harare hararen sojan nan murmushi yayi kawai yana rigimammiyar tadawo cikin ransa dan ba damar fitowa fili afad'a duk da yasan ba abunda zatayi masa domin bata da matsalarkomai kawai dai rigimarce wadda kuma ba kullum take yintaba.


Juyawa motocin da suka kawo su sukayi suna barin gidaN.


Da gudu fad'a acikin had'adden falon gidan bayan sumy ta gaisa da Sauran sojojin


Ummmi! Ummmi! shine sunan dasuke ta kwalawa kira wata matace ta fito daga wani daki daga chan upstair tana takawa ahankali tana furta har kun iso kenan,Macece kyakkyawa kamar Unni fara tass komai nasu iri d'aya har muryar ma tasu identical twins kenan kafin ka shaida d'aya sai ka d'anyi dogon nazari.


Cikin murmushi dukkaninsu suka rungumeta itama murmushin tasaki tana furta sannun ku da zuwa "ya "yana shine ba sanarwa sai kukayi gidaan Unninku kuka turo mun driver kawai.

Dariua sukayi dukkansu har Ummin.

Nisa na bud'a baki zata furta ai yya mahir....Sumy ta mintsileta gudun karta sakammata layi,fahimtar hakan da Nisa tayi sai tace Ummi yaya mahir yace agaisheki,ina amsawa ta furta tana raba jikinta da nasu itama sumy ta furta Ummi yya Abdallah ma yce agaisheki duka ina amsawa tace duk da sun gujeni kwana biyu...


cigaba da magana tayi yau Ina cikin farinciki yayan Unni da Ummi duk sai suka had'a baki gurin tambayar mene ne yasanki farinciki haka Ummi ko dadyyadawo ne bamu sani ba duk da bamuga motarsa ba acompound girgiza musu kai tayi cikin murmushi tana furta aah,BAi dawo ba Amma karku damu zakuji komai nan gaba,Tana wucewar ta kitchen.


Wanka tace suje suyi suci abinci toh suka ce suna takawa upstair d'in ...


Wata kyakkyawar yarinyace fara kamar ta sak da Alamin da sumy sai dai batayi hasken su ba,da gudu ta taho ta rungume yayyen nata bayan sun idasa take kan step din tana furta shine kuka je gidan Unni yau badani ba koh'tana maganar tana neman bare musu baki tasaka kuka,Nisa ce tajawo ta ta na furta kinason zuwa wurin Unni koh,kai tad'aga mata, toh kibari juma'a tayi sai muje koh har Ummi,ai kinga juma'ar takusa zagayowa koh kai takara d'aga mata,yawwa An Husna ta muje kema inmiki wanka ko,suna wuce wa ta sashen da rooms nasu yake.



*HOSPITALISED*

-----------------------------------------------------------------

*INDIA*

*Maharastra 24hrs Hospital mumbai*

Zaune yake akan chair dinsa mai juyawa acikin kayataccen office d'insa mai kyau bayan ya cire labcoat dinsa yasargafe ta a had'addiyar hangern office din nasa, bayan yagama duba outpatient.

Katon office ne kamar wani falo guda komai yaji komai na kawa, windows dinsa gaba daya gilas ne ga katuwar lockern sa ta ajiyar takardu da document,da haddaen fridge d'an karami wanda yakarawa office din ado, sai d'an madaidaicin gado na duba marar lafiya tareda sauran kayan amfani irin su spring cover d.S,sai kofar toilet da wata kofa danake tunanin bedroom ne,komai masha Allah ba wani tarkace.



,,,,,,game Yake bugawa a had'addiyar wayartasa kirara 15promax( iphone) sanyin A.C na office d'in yahad'e da k'amshin turaren sa mai dadi BETTER MAN na kamfanin "yosen"domin kowa yasan dr Ammar ma'abocin sanya turare ne.

Had'adden table din dake gaban sa yana dauke da wani tambarin na kwalbar zinari kamar na award an rubuta Dr.Abdul rashid Aliyu Ahmad,cikin tsari mai kyau,ga kayan aikinan masu quality da kyau na aikin su irin su Bp apparatus,spygmanometer...Thermometer abun awon pulse da dai sauransu sai wasu yan d'ai d'ai kun takardu na amfani wayenda bukatar su kan taso ga patient...


K'arar door bell ce tasanyasa Ahankali cikin tak'ama ya furta come in,Kyakkyawr budurwace tabayyana acikin office din nasa,Dr.Malini kenan kyakkyawar ba indiya ruwa biyu jinin larabawa da indiyawa,kykkywace ajin karshe sanye take da sari ja da labcoat ajikin ta inda naga anrubuta dr malini arorah,takowa tayi Ahankali tazauna akujerar da taje gefen table din tana mai furta masa barka cikin harshen india tare k'awata fuskarta da murmushi....


kamar bazai tanka ba sai kuma ya furta yawwa Atakaice cikin yaren idia shima, yana cigaba da buga game dinshi,tun shigowarta da yamata kallo d'aya yani itace bai ka'ara kallon taba,koda sashen datake.


A hankali ta k'ara furta masa cikin harshne nasu,yazo sufita cin abinci suje bakin ruwa,,,,Bakin ruwan da furta ne yasanya gabansa muguwar fad'uwa daya tunano mafarkinsa da yayi jiya wanda har yau baisanarwa da kowa ba.


A hankali cikin tak'ama da izza irinta jinin sarauta masu ji da ita ajikinsu Bayan tsai da tunaninsa akan mafarkinda yatsaya masa arai,ya mayar mata da Amsa ''I am not interested"

atakaice maganar ta kona wa dr malini zuciya sai dai sanin halinsa sai ta basar bata k'ara furta masa komai ba domin inda sabo tasaba da irin cin kashin da yake mata,wanda ita taja wa kanta,wanda su achan kasar su ba komai bane is nrml thing.

*daMa mazan yanzu ya aka kare koshi yace yana sonki bare ke kika kai kanki,abun sai anrika had'awa da Addua,inkin zurfafa yar uwa,sannan karki bayyanar da soyyayr nan har yagane kina iya vada ranki saboda shi,domin wasun su suna amfani da wannan damar su cutar da mu,Allah yabamu masoya nagari*🙏


Ganin da yayi bata k'ara yin magana ba kuma bta fice ba yasanyasa d'ago dara daran idanunsa yayi duba na second daya agareta,yana dauke kansa cikin cije leb'ensa na kasa,yayi danasanin d'agowa yakalleta harsuka had'a ido,domin hawayene yagani suna a idanunta wasu na turereniya da wasu,D'an karamin bakinsa yakara tsukewa dan yatsani ganin hawayen mace domin take yake rikicewa,Tabbas a wannan gab'ar dr malini tayi nasara domin zata janye hankalinsa in har tagano lagon.


Ayanzu haka ma yakar zuciyarsa yakeyi data fara darsa tausayin Dr malini wanda kuma shi haknne bayaso yafaru.....


Karaamar tsuka yaja wadda iyakarta kan labbansa yana ajiye wayartasa akan desk,handkerchief dinsa fari k'ar dora mata agefen da ta kife kanta tun bayan had'a idon da sukayi tana cigaba da kukan ta kasa kasa,Saurin Dagowa tayi A hankli ta kallesa cikin wani yanayi ganin ya ajiye mata hanky kallonsa take da mamaki da alajabi domin yauce rana ta farko da yafara nuna mata kulawa,take ta tsinci kanta acikin farin ciki marar misaltuwa ita a tunanin ta yafara sonta,tunda su dab'iar su ce in har saurayi yabawa budurwa handky tashare hawayenta kamar alamar soyayya ce tunda shima wannan kulawa ce.....

Hmmmm Nikam nace DR.MALINI Kenan.




💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

FREE PAGE3️⃣1️⃣



TYPING📲📲📲



"Sorry" ya furta mata ayangance,duk da yadda Kalmar kemasa nauyi ahankali ganin tana share hawayenta Wanda har fuskarta tad'anyi jaa fuskar ta chanza alamar kuka abunka da farar Fata.kai kad'ai Dr.malini tad'aga masa,Bayan share hawayenta da kyakkyawan handkerchief Nasa fari kar mai kamshi.

A hankali ya buda bakin sa dakyar cikin tattausan lafazi da muryar mai sanyi da nuna izzarsa ya furta mata acikin harshen turanci, I have a lot of appointment today,so thats why I have told u I can't go with you,ya furta mata hakan ne kawai ganin hawayenta, yanaso tasaki fuskarta bazai so ace kullum cikin kuntata mata yakeyi ba yasan cewa soyayyar gaskiya take masa sai dai shi bata cikin Ra,ayinsa har yanzu.

Shiru yayi bayan gama maganar jin bata CE komai ba yakara furta i'm sorry ohk!


D'aga masa kanta tayi tana tashi tsaye da lab coat d'inta da tacire kafin ta zauna,hanky d'insa ta ajiyemasa No,

Ya furta da ita "you can go with it"murmushi tayi har cikin ranta jin furucinsa taji dad'in kulawar da ya bata yau kad'ai akaro na farko wadda tadauke ta amatsayin wata nasara ta ta.

Bye tamasa Tana takonta d'ai d'ai na big ladies masu ji da Kansu tako wanne fanni k'arar high hill dinta ne kad'ai yake tashi duk inda ta wulga sai an mata kallo uku saboda haduwarta.


Dr.Am dayaga wucewar Dr malini tana ta faman sakin murmushi ne abunta,kansa yad'aure masa kai,dama ga office d'insa ganasa,yana bud'o k'ofa yaga wulgawar ta sai dai bata lura dashi ba. ida rufe kofar tasa yayi ya doshi kofar ta Dr.Ammar ko neman iso baiyi ba ya bud'e door d'in yashiga ciki,ko ba,a fad'a ba yasan Al amin ne yashigo saboda shi kad'aine Wanda baya tsayawa Neman iso ta hanyar danna door bell.


Idanunsa a rufe ya furta wai lafiya kamun tsaye akai, Dr.Am bai ce masa komai ba duk da yaji furucinsa,sai ma kara gyara tsayuwarsa da yayi yana mai rungume hannyensa akirji,tsawuyar minti uku yayi babu Wanda ya furta k'ala ga dan uwansa,Dr aj sai ma karantarsa da yake yi.Aj ne yakatse Shirun nasu ta hanyar furta ma Dr.ammar" meye damuwarka na fahimce ka tun safe kamar kawai Abunda ke damunka azuciya,kuma inada yakinin bazai wuce mafarkin da kasaba yine kayi sai dai ban sani ba,ko wannan ya chanza daga Wanda suka sani ganin kamar yana kokarin boyesa ne.



Shiru Dr.Ammar yayi kamar baiji Abunda da Dr aj yafad'a ba saima kara tsumewarsa da yayi akan had'addiyar kujerar tasa mai rotating ,ganin baida niyyar magana yasanya Dr aj kawar da shirun ta hanyar furta...

"Mekasanar wa Dr.malini ne naga ta fita tana tasakin murmushi kodai kabar hak'ar ta ta cimma ruwa ne duk suna maganar ne da yaren India din.



Murmushin da bai shirya yinsa bane ya subuce masa akan kyakkyawar fuskarsa jin abunda Dr aj ya furta idanunsa ya bud'e ahankali tar akan Dr aj yana kallonsa da murmushi a fuskarshi,sai kuma yakawar da idanun nasa masu kaifi ganin Dr aj ya daure fuska ta Yar dariyar da ta fito masa ta rainin hankali duk da bai tsawaita ba.




A hankali ya mike daga zaunen da yake yatako A hankali dai dai inda aj yake tsaye nan ya tsaya suka jera gwanin burgewa sunsha fararen riguna da maroon colour trouser kowa ya tsuke da belt maroon sai kuma hadaddun boat dinsu masu kyau far are kar dagani dai sunji naira,yau anko sukayi dama mafiyawancin lokutta anko sukayi domin duka Rabin kayansu iri daya ne da juna sai dai kala CE wani lokacin take banbanta,tsayuwarsa data Dr.Aj gwanin burgewa ne Daya yafi daya tsawo,Dr ammar shine mai tsawon,duk sun saka hannayensu a aljihu Wanda ke facing bangon da yake na gilas Wanda dukkan abun hawan dake wuce wa a express way dama mutane suna gani tar.



Tsayuwarsa da minti ya juyo ya dafa aj akafad'a Wanda har yanzu fuskar nan take mur,tsulum yayi yakoma gaban sa suna fuskantar juna, cikin izza da yanga.



Wani killer smile yake ta sakarmasa Wanda ke iya haddasa gubar soyayyarsa acikin second daya acikin zuciyar yan mata,shiko aj ganin sa a gabansa yasanyasa ja da baya yana sakarmasa katuwar harara wadda tasanya Dr.ammar sakin kayataccen murmushi Wanda har sai da fararen tass jerararrun hakoransa suka bayyana.Aj ne ya furta Dan iska kawai haka kakayi wa yan yayan mutane suna fad'awa daga kallon daya cikin kara sakar masa harara.Dr ammar kuwa murmushin sa yakara fad'ad'awa jin abunda aj ya furta masa.



Ahankali ya mayar masa da amsa cikin kasallaliyar muryasa ta gwarazan maza,kar damu likita yanzu duk zan baka amsar tambayoyinka duk da bayanzu naso kaji wasu daga amsoshinka ba,yana mai kara gyara tsayuwarsa,Kwantacciyar sumar kansa yashafo sannan ya cigaba da magana a hankali "tabbas mafarki na ya chanza kamar yadda kayi hasashe ......labari yabasa na yadda mafarkin ya wakana domin dama tin asali basa boyewa juna sirri duk da dama shi aj yasan mafarkin saboda some time lokacin suna kwana daki d'aya yakan ji shi yana magana k'asa kasa cikin baccinsa,Wanda dama yasan yana yin wannan mafarkin.



Ta gwayen ajiyar zuciya yake sauke wa,Wanda har sai da Aj yaji,bayan yagama basa labarin.


Tausayinsa ne Yakama Aj ruwan sanyi yadauko a fridge dake a office din tsiya ya masa yayi acikin glass cup mai kyau dake jere awata locker daga gafen fridge din.


Ahankali yakai cup din saiti dan karami bakinsa kurb'a d'aya yayi yasauke gilas d'in ya rike a ahnnunsa yana sakin nannauyar ajiyar zuciya cikin wani yanayi marar fassaruwa, jin yadda sanyin ruwan ya ratsa Dukkanin sassa na jikinsa,Bayan kamar minti Uku yacigaba da maganarsa yana furtawa Aj" Dr.malini Arorah bata isa tasamu gurbi acikin kirjina ba ko yanzu kawai Dan tausayi tabani ne ganin hawayenta na zuba abanza,saboda ni kai kanka kasan bana son ganin hawayen mace bare ma ace ta sanadi na suke zuba.


*wato abanza Dr😰😢*.Hmmm maza

wasu wallahi tausayinsu ragagge ne *baiwar Allah nata wahala shekaru araru amma ayanzu hawayenta ma na banza nesabd haba dr.Namu,*

*Dr.AMMAR FANS nidai gaskiya mutumenku yafara wuce gona da iri dan bazan dauki wulakanci ga miss malini ba baiwar Allah😢Allah karabamu da son maso wani,da soyyayar bangare d'aya.*🙏🙏


"Tabbas da badan kwallar da nagani ba babu abunda zaisa inkula ta har inbata abunda zatay wiping na tears nata,saboda bata cikin tsarin matan da nakeso and kuma she's too young for me yana kai karshen maganars da yatsinar fuska yana kara furta bama kuma Aladun mu d'aya kuma ba Addinin mu d'aya nasan kasan da haka maganar hak'ar ta ta cimma ruwa har abada yana lumshe idanunsa s ai kuma a hankali ya na bude su.

Dr Aj ikon Allah kad'ai yake kallo atare Dr Ammar yana mai yana mai mamakin hali da da taurin zuciyh irin na d'an uwansa ace mutun kaifi d'aya ne ba chanji domin yakamata ace yanzu ya fara kula al amarin Dr.Malini saboda shekarun da tadauka tana bibiyarsa da soyayyarta,.''kaji tsoron Allah Dude,bayan yagma maganar zucinsa, na jin zantukan Dr Ammar d'in. yar karamar harara yasakar masa yana mai kau da kansa gefe,Aj ne yaci gaba da magana yanzu ita Dr malini d'ince yarinya just bai wuce kabata shekaru uku ba fa domin bazan manta ba when last birthday nata danaje ishirin da biyar tayi celebrating Amma shine kake kiranta da yarinya sannan bata cikin tsarin matan da kake so kake iya aure koh !!! hmm Dude kenan inbanda so yana haka me Dr.Malini zatayi dakai dubeka skin dinka kamar zumar dataji wuta ta kone,yakai karshen maganar cikin dan yin dariyar mugunta domin yasan Ammar yatsani wannan furucin.


Karamar harara Ammmar yasakar wa dr aj dan dagaske yatsani kalmar nan dan aj nayawan furtamasa ita duk da yasan wasa yakeyi masa fatarsa normal take kuma ahakan mugun sonta yakeyi.

Murmushi Dr.AJ yayi yana cigaba da maganar sa,"ga mace har mace Amma so na walagigiya da ita gaskiya Dude da zakaji shawarata da ka karb'i Dr.Malini saboda kaima shaida ne tayi maka son gaskiya kuma bugu da kari ta had'a duKkanin Abunda Daaa namiji zai bukata ga mace,kuma duk jarabarka nasan malini zata iya dauka domin nasan halinka inaga ka raina girmanta ne,ina kara baka shawara karkayi watsi da damarka toh!!!!!!yakai karshen maganar tasa yana dariya tare da kanne masa ido d'aya.


Dr.Ammar da ke kallonsa k'uri da ido ne Yayi D'an murmushin gefen baki sai kuma ya murtuke kyakyawar fuskarsa jin furucin aj d'in na karshe domin nafarkon bai bashi haushi ba face ma mere baki da yayi.


"cikin tsuke fuska ya furta Wai yaushe ka koma hakane bansani ba naga alamar idanunka sun bud'e fa,murmushi ne ya subuce masa tuna furucin wai malini zata iya daukar sa abu na kayan wanki,dakuma amsar datazo kansa kan maganar malinin wadda zai mayarwa da aj d'in wadda zaiji zafin ta domin tabbas yaji haushin furucinsa na karshe wai zata iya d....Kasa ida karasa tunanin yayi ta sanadiyyar zuciyarsa da tafara hasaso masa yadda komai na malini yake duk da ba wani kallon tsaf yakemata,subhanallah ya furta azuciyarsa yana lumshe idanunsa tare da bud'esu


yana cigaba da magana kace Dr.Malini Dr.Malini tacika mace ;Am nace ko zaka gwada sa,a ba ko zaka samu cikakkiyar macen tunda naga har ka hango cikarta yakai karshen maganar tasa cikin yana kanne ma Dr.Aj ido Daya kamar yadda yamasa,tare da sakin wani killer smile, aj wqnda daga farkon maganar ta Dr.Ammar murmushi yakeyi sai wannan furucin na karshe yasanyasa turb'ene fuska wata katuwar harara Dr.Aj yasakar masa wadda sai da tasanya Dr .A murmushi wanda yasanya two side dimple dinsa bayyana gwanin burgewa,tsinin hancinsa ya lakata yana mai k'ara sakin murmushi ganin shan tokar da Aj d'in.



A bangaren aj maganar ta bashi haushi matuka domin yadda suke da ammar soyayyar dayake masa bazai iya son abunda yakeson dr .Ammar dinba koda shi bayaso kamar dr malini haka..

Ya bud'a baki da niyyar yin magana sai yayi shiru, karar wayarsa da yaji tadakatar dashi daga abunda abunda yake niyyar furtawa,cirota yayi daga aljihun wandonsa na baya dan ganin wanda ke kiran nasa wanda alokacin har wani sabon kiran yashigo nafarkon yakatse saurin d'agawa kiran yayi Bayan duba sunan mai kiran nasa UNNI

sunan da ya fito baro baro da manyan rubutu.......




💫A MAFARKI NASANTA💫

In my dream I know her

By

Pha'eezah Almustapha

Daga Alkalamin✍️✍️

💫Fa'eeh BG💫


Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔


💫A MAFARKI NASANTA💫


YAZAMA FREE BOOK

Nama mayar muku dashi free book akan wani dalili nawa inason duk Wanda yaji dad'i yamun Addu'a,Allah ya biya mini da dukkanin buk'atuna🙏


Ina godiya da hakurin da kukayi dani har na tsawon sati biyu koma fiye🙏

Ina alfahari daku masoyan Amafarki nasanta,kud'in na daban ne agareni💋



------------------------------------------------------------------

--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️



💫P.E.W.A💫


Home of perfect essential writer's together we stand🤝


ESSENTIAL WRITER'S📚🖊


Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️


EPISODE1️⃣

PAGE3️⃣2️⃣


TYPING📲📲📲


©°••••••••••••••••••••••••••••••°©

Sallamar da akayi A dayan b'angaren ce ya amsa yana sakin murmushi,Unni yakike?ya gida?'sunan da aj ya furtane yasanya gaban Dr.Ammar fad'uwa idanu ya tsurawa Aj dake wayarsa da unni a tsanake cikin girmamawa cikin ladabi.A d'ayan b'angaren Unni ta tambayi Aj ya aiki ? bayan ta amsa masa duka gaisuwarsa,Alhmdllh ta furta ya furta yana mai sake fad'in Unni ai yanzu haka ma muna hospital d'in yau bamu tashi da wuri ba...


Ohk tau Allah yataimaka"ta furta masa,A hankali ta furta" Nur na kusa"ehh ya bata amsa atakaice yana mai d'aga idanunsa ya kalli Dr. Ammar da ya tsuramasa idanunsa masu kaifi Ba ko kyaftawa tunda yaji sunan Unni ya fito bakin dr aj gaban shi ke k'ara faduwa.

Unni ce ta juye harshen ta a yaren fulatanci,tana tambayarsa har yanzu Ammar yana nan kan bakansa ne?bazai karb'i sarautar ba,fahimtar da yayi bata son Dr Ammar d'in yagane zancen da suke yi yasanya sa shima chanja shima zuwa fulatanci,dan duk sun san Dr.Ammar baijin sa tun suna yara akayi koya musu yaren inji kakarsu Ammie gimbiya fatima,wanda itama ga mijinta margayi sarki Hamza ta iya sa da kuma kawar tata HAjiya,har ya" yan ta ma,shi yak'i maida hankali ya iya ne shiyasa bai iya yaren ba.

"Amsawa unni yayi da tabbas dai kam Unni yana nan kan bakansa,Unni bata nuna komai ba duk da amsar tasa tad'anji ba dadi ganin kafiyar yaron nata duk da tasan baizubar bane haka mahaifinsa yake da kafiya.furta masa tayi " kyalesa kar ka k'ara masa maganar komai yazo karshe in sha Allah.Sosai Aj yayi mamkin sosai da jin maganar da unni tayi dakuma rashin nuna damuwa da batayi ba kamar sauran lokutta,sai dai bai tambaye ta dalili ba saboda yanajin nauyin ya yar ta mahaifiyarsa fiye da mahaifiyartasa.Tambayar da ta masa ce ta katse tunanin zucin nasa"•••••••••


Ranar nace ka kirani inkazama less busy Amma Aminullah shiru babu kiranka,da yake haka take kiransa some times itada Sarki Ali ko son,shiru yayi na rashin gaskiya dan tabbas yana sane yak'i kiran nata gudun tambayoyin nata game da Dr.Ammar d'in akan rigimarsa da mahaifinsa,saboda kuma bayaso ya rik'a yawan yiwa Ammar maganar dan duk lokacinda ya masa magaanar sai yaga damuwa karara akan fuskar d'an uwannasa shikuma hakanne bayaso duk da yasan cewa yana cikin damuwar da shi kansa bazai iya boyeta ba a wasu lokuttan ba duk da jarumtar da yakeyi,shiyasa tun ranar da suka fito meeting d'in bai kirata ba,A yanzu ma koda yad'aga kiran yana d'ar darr ne a zuciyarsa duk da yasan unni mace ce marar daukar zafi,sai kuma yaji akasin Abunda yake tunani,yazata yaga ta nuna damuwa ko b'acin rai ko tayi fushi ma dasu.

A hankali ya furtama sorry unni kinsan aikin namu ne,shiyasa bansamu na kiraki ba,Murmushi kad'ai Unni tayi dan tasan tabbas gan gan yaki kiran nata domin baison takurawa AMmar d'in dan tana basa umurni ya tambayesa in yajanye domin ita ko takirasa shiru yake mata,DA kuma yarika convincing nasa har yajanye ra'ayinsa duk da tassan abu ne mai wuya.Shima Aj murmushin kad'ai yayi

dan yagane dalilin murmushin na unni akan maganarsa.


°©•••••••••••••••••••••©°


Bayan minti biyu dukkaninsu suka yi shiru,Unni ce ta takatse shirun nasu ta hanyar tambayarsa game da mafarkin da Ammar yasabayi tun yana k'arami wanda anyi neman taimako akai Amma ba,a dace ba kusan shekara ishirin da yan kai.



Amsa mata yayi da ehh yanayi Unni ma a wasu lokuttan kad'ai dan yasan Ammar bazai masa karyaba in yayi saboda shak'uwar dake tsakaninsu.

labarin last mafarkinn nasa yabata wanda ya banbanta da saura duk a harshenn na fulatanci suke maganar.


Ta B'angaren Ammar ido kad'ai ne ya zubama Aj din dan dukkanin abunda suke fad'a baya fahimtar komai inbanda gaisuwar daga cikin yaren,kuma tabbas yaji ajikinsa duk akansa ne suke magana sai dai bai gane kan zancenba,A hankali Ya lumshe idanunsa tare budesu wadanda suka d'an sauya daga farin madararsu yanayin nasa kamar mai jin bacci wanda haka kawai yake jin kasala na saukarmasa ta rashiin dalili.


'Ta B'angaren Unni ta razana sosai da jin labarin mafarkin da dr Ammar yayi,sosai hankalinta yatashi,Kwantar mata hankali Aj Yayi yana furta "unni karki manta fa ba duka mafarki yake zama gaskiya ba agaremu, Annabin mu muhammad saw shine kad'ai wanda yakeyin mafarki kuma ya tabbata dan haka karkisa damuwa dan sun furta zasu dawo kansa bashi ke nuna ko suwaye zasuyi nasara akansa ba Unni kawai kisanya duka wannan mafarkin nasa amizaninb sharrin shaid'an (la'anannen Allah) ba abunda zai iya zama gaske ba,sannann UNNI Addu'o'in ku natare damu mezaisa ki razana,ayanzu ya mayarda maganar sa da hausa inda duk maganar da sukeyi yanaji rad'am akunnensa.


Ajiyar zuciya Unni ta sauke abangaren ta cikin jin dadin furucin na dr aj wanda yasanyata jin sanyi aranta. wanda

Please Login or Register in order to submit comment