Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Cikin kuka tace mum Dan Allah ki taimaka kisa a bama kabir ni, na yarda zan zauna dashi koda yana da cutar, wlh Mum zan zauna dashi hakan, kuma Wlh nasan kabir baida Shi,sharri ne wlh sharri ne....

Ummi takai Mata duka tare da fad'in yi mana shuru mara hankali kawai, tunda ke baki San inda yake miki ciwo bako? Wlh.....

Mum tace haba ya zaki bigeta? Miye haka kuma? Damai zataji?..

Ummi tace baki ji abunda take fad'a ba? In banda iskanci tanaji ance yanada cuta amma tana fad'in ita zata zauna dashi haka, tunda bata da hankali bata san maike mata ciwo ba.

Zarah kam gaba d'aya ta shiga rud'ani, kenan ibtisam da Kabir ba'a d'aura aurensu ba? Gaba d'aya sai tausayin Itbtisam din ya kamata

Mum tace ai ba'a haka, bakya ganin irin halin data shigane? Komai a hankali za'a bishi

Ummi tace ai zancan Abu a bishi a hankali wlh bai taso ba, dan bazamu bita a hankali ba dan ubanta, tunda an d'aura aure, yanzu ita matar aurece kar in k'ara ji ta kira sunan wani kabir a gidan nan sha sha sha kawai mara tunani

Granny ce ta shigo tazo ta zauna kusa da ibtisam wacce ke kuka kaman ranta zai fita, wai itace matar Najeeb? Wlh da sake, gwara susa ya saketa domin kabir Zan aura

Granny tace ibtisam kiyi hakuri Kinji? Ki d'auki hakan shine dai dai, kuma haka Allah ya tsara, inaso ki sani komai da yake faruwa a rayuwar Dan Adam rubutacce ne, Allah ya riga ya tsara sai hakan ya faru, mu kawai muna bine, "Allah yasa kabir bashi bane mijinki NAJEEB shine mijinki Ina son ki dauki hakan a matsayin kaddara.....

Cikin kuka tace Wlh Granny bazan d'auka ba, ni Kabir nake so, shi kuma zan aura bana son wannan auren, dan Allah ku taimaka ku rabani da wannan ba'kin auren, wlh da nasan zanga wannan ranan dana ro'ki mutuwa Kafin tazo min, wayyo Allah kabir....  Lokaci d'aya tayi shuru tare da Fara dube dube kaman zararra, d'auko wayarta tayi ta Fara dannawa tare da dialing number d'in kabir.....

Amma Abun mamaki sai taji switch off.

K'ara kira tayi shima switch off, kuka ta k'ara saki mai sauti tare da fad'in shikenan, shikenan yaji wannan mummunan labarin, k'asa tayi jiri ya d'ibeta.

Da sauri Mum ta rukota Tana kiran sunanta ibtisam, ruwa aka saka mata amma gaba d'aya ta kasa bud'e idonta sai dai tana numfashi sama sama dan haka Mum tace ma Zarah kamata muje toiket

Kamata Zarah da mum sukayi sukai toilet da ita inda Zarah ta fita Mum ta Fara tube Mata kaya, wanka Mum ta Mata wanda yasa ibtisam ta farka tare da bud'e idonta da sauri, ganin mum yasa ibtisam kallon jikinta da sauri tasa hannunta ta rufe kirjinta Wanda suke a tsaye kyam dasu gwanin sha'awa

Mum ganin haka yasa tayi murmushi tare da fad'in tashi ki d'aura towel

Bata musa ba, ta tashi da sauri duk da jikinta babu kwari ta d'auki towel ta d'aura, sannan suka fito

Gaba d'aya su Zarah na zaune a d'akin, kowa da abunda yake tunani, wato ibtisam NAJEEB ta aura ba KABIR ba, sai taji ibtisam din ta bata tausayi domin tasan irin sonda suke ma junansu ita da kabir din, "amma kabir bai kyauta ba daya boye yana da cutar HIV da yanzu ya saka ma ibtisam, data kwasa

Ta gefen Granny kam dad'i takeji, dan dama ita burinta taga NAJEEB yayi aure shida itbisam, sai gashi Allah ya cika mata burinta sunyi aure an had'asu, wanda ita bata taba tunanin hakan zai faru ba, a hankali tace ikon Allah ya wuce wasa

Ibtisam zama tayi akan gadon d'akin, yanzu ko kukan ma ta kasa saboda tashin hankali, ganin zaman bai mata ba yasa ta kwanta tare da lullube jikinta da blanket harda kanta ta rufe, ba komai bane cikin ranta sai tunanin wani hali KABIR ke ciki yanzu, zuciyarta da kirjinta ji take kaman zasu fito, wani irin zugi takeji, cikin ranta, gaba d'aya duniyar tayi mata ba'ki, lallai an gama da ita a rasa wanda za'a aura ma ita sai wannan mugun azzalumi Wanda bai san darajan d'an Adam ba, lallai su Abba basu mata adalci ba, da suka bata Najeeb, amma koma dai miye bazan taba yarda da wannan auren ba, haka kuma bazan taba d'aukanshi a matsayin miji ba har abada, domin kabir shi d'aya shine mijina

Sanda kabir ya shiga cikin gidan nasu, kai tsaye falon gidan ya shiga inda yaga iyayenshi zaune, ciki harda abokin mahaifinshi wato mahaifin hafsat kenan

Zama yayi tare da gaidasu cikin damuwa tare da kosawa yaji maike faruwa

Nan k'anin mahaifin ya kira sunanshi da kabir

Kabir yace na'am Abba

Kawun Kabir yace ashe k'aramin gida ka Kai mu bamu Sani ba? Mun d'auka babban gida ne wanda suka san mutunci Ashe basu sani ba, tunda har za'a iyayi maka k'azafi sannan su kama su yarda?

Kabir daya k'osa yaji maike faruwa yace Abba wani abu ya faru ne?

Kawun Kabir yace ya faru kam, domin anzo ance musu kanada cutar nan Mai karya garkuwan jikin d'an Adam, wato HIV aid, ana gab da.....

Salatin Da kabir ya saki yasa kawun nashi yin shuru, salati kabir yayi da fad'in Innalillahi'wa inna ilaihirajiun

Kawun Kabir yace, babu yanda bamuyi ba akan Karya ake maka, amma Sun d'age sai anyi gwaji Kafin a d'aura aure, dan haka mu kuma mukace su ri'ke y'arsu suka aura Mata aure da wani, Muma muka aura maka Hafsat, gidan nan ba gidan  mutunci bane tunda har zasu iya yarda da abunda wani yace akan ka  ......

Tashi kabir yayi cikin tashi hankali yana fad'in no ibtisam tawa ce, ban yarda ba fita yayi fuuuuuu Kai tsaye motarshi ya shiga ya fita da gudu, bai tsaya ko inaba sai hspt inda ya buk'aci a mishi HIV test, domin shidai inma yana da cutar Toh bai sani ba, "bayan an gwadashi aka bashi result da sauri ya duba yaga negative, ido ya lumshe tare da furta Alhmdlh Kai tsaye gidansu ibtisam ya nufa inda yaga mutane makil, yaro ya tura akan yayi mishi sallama damai gidan in yana nan, Aiko akaci Sa'a Abba da Dad suna nan a falon ba'ki kuma nan ne Farko Kafin a shiga cikin gidan

Abba fitowa yayi ganin kabir yasa yace ya shigo ciki, "binshi yayi ya shiga cikin falon ba'ki, kabir zama yayi tare da gaida Abba da Dad

Duka suka amsa tare da fad'in lafiya

Kabir mi'ka ma Abba takardan da aka Mai gwajin HIV yayi tare da fad'in Abba dan Allah gashi ka duba wlh sharri ne bani da wani cuta, dan Allah Kar ku hanani ibtisam

Abba duba takardan yayi yana mamaki tare da fad'in ikon Allah,lokaci d'aya ya mi'ka ma Dad shima ya amsa Yana dubawa, Dad yace Toh amma Mai yasa wannan mutumin yayi maka wannan k'azafin?? 

Kabir yace Wlh nima ban sani ba, gashi duka y'an uwana babu wanda ya sanshi.

Abba yace ikon Allah, toh amma kabir ai sai dai ayi hakuri amma wannan bawan Allah ya cuceka ko Waye, amma bakai ya cuta ba, kansa ya cuta, sannan ina son ka d'auki hakan a matsayin itace kaddaran ka, Allah yasa ibtisam ba matarka bace, yanzu ibtisam matar wani ce

Kabir bai San lokacin da hawaye ya fara zubar mishi ba, gaba d'aya ya kasa furta komai, "babu komai a ranshi sai Mai yasa wannan mutumin yayi mishi haka? Ko Waye ya cutar dashi wlh, ya gama dashi,yasa bai samu abunda yake buri ba Innalillahi'wa inna ilaihirajiun.

Abba yace KABIR kayi hakuri, haka Allah ya tsara, ko sanda aka fad'i abun saida nace Ayi test dan a tabbatar amma iyayenka Sun kasa fahimta Sun d'auka da zafi, wlh KABIR Allah shine shaida kai muka so bama ibtisam amma family din'ka sun mana fassara, wanda suke ganin munki yarda dakai ne, amma kayi hakuri haka Allah yaso, ibtisam ba matarka bace

Kabir hawaye yake Sosai yana ro'kan Abba da Dad akan su taimaka su bashi ibtisam

Dad gaba d'aya tausayin kabir ya kamashi,

Abba yace Kabir ka tashi kaje gida zan nemeka

Kabir jin haka yasa ya d'auka ko za'a bashi ibtisam dinne, yasa shi fad'in Abba zuwa yaushe?

Abba yace kaje zan kiraka

Dad yace kai Yaron nan yana son mamana, ina tunanin NAJEEB ya rabu da ita, tunda bawai tana sonshi bane, kuma ban tunanin shi najeeb din shima yana sonta

Abba yace haba haba, sai kace Abun wasa? Taya za'ace NAJEEB ya saketa? Ai wannan bai taso ba

Dad yace suna son junansu Sosai, Kaga halinda yaron Ya shiga abun yaban tausayi, itama kanta ibtisam din ta shiga wani hali, inaga gaskiya ban tunanin zasu iya juran rashin junansu

Abba yace dole kuwa su jura, domin kuwa dole suyi imani da kaddara, dole su amshi kaddaran data fad'o musu.

Tayu ma ana d'aura auren wani a cikinsu ya mutu tunda Allah yasa ba matarshi bace, ai wani baya auran matar wani, haka wata bata auren mijin wata

Dad yace hakane tare da fad'in kaje Kaga wani hali ibtisam din take

Tashi Abba yayi yana fad'in Bari inje in duba

Koda kabir yabar gabansu Abba Jiki a sanyaye ya tafi, tuk'i yake cikin damuwa, lokaci d'aya yaga duhu a idonshi wanda ya bugi wata trailer dake gabanshi, domin irin gudun da yakeyi gashi idonshi ya rufe, motarshi tayi sama tare da kundun bala tana juyi

Nan mutane sukayi kan motar tashi inda aka fara dubawa aga Waye a ciki, Aiko ganin mutum sukayi gaba d'aya ba'a gane fuskan ko Waye domin jini ne gaba d'aya ya bata fuskan, jikinshi gaba d'aya jini ne, babu wanda yayi yunkurin yace a kaishi asibiti aga ko yana da rai koya mutu

Saida yayi wajan 30mnt sannan saiga police da motar ambulance sunzo inda aka d'auko kabir wanda gaba d'aya ban tunanin yana da rai ko yana Raye, wanda dakyar aka ciroshi a motar dan wani k'arfe ya shigar mishi cikin cinyar kafarshi ya faso, ya bullu'ko

Nan akai asibiti dashi inda za'a duba yana Raye koya mutu.....

Ibtisam da Abba ya shigo d'akin dai dai lokacin da kabir yayi accident Wanda take kwance tun sanda tayi wanka, tashi tayi tare da sakin ihu Tana kiran Sunan kabir

Dukansu ido suka zuba mata suna kallonta cikin mamaki

K'okarin tashi ta farayi tana kuka tana fad'in na shiga uku, dan Allah ku kaini inga kabir Dan Allah ku kaini in ganshi na shiga uku wayyo KABIR..

Tsawa Abba ya daka mata tare da fad'in zan saba miki Idan na kumaji kin kira sunan kabir....

Cikin kuka take fad'in Abba kayi hakuri Wlh Abba Ina jin tsoro jikina yana bani wani abu ya sameshi Abba Ina tsoran Kar in rasa KABIR Dan Allah Abba ku barni inje in gansa koda sau d'aya ne....

Gaba d'aya kallonta suke, suna mamaki yanda take abu, sai kace wacce ta zare ko akayi ma asiri

Ibtisam ganin suna mata wani kallo yasa ta rarumi wayarta ta doka ma number d'inshi kira amma still switch off

Cikin tashin hankali tace Abba da.....

Abba yace Yimin shuru ibtisam bana son wata magana, ashe haka kike? Lallai gaskiyan mamane na tabbata wannan jami'a din da kikaje shine yasa idonki ya bud'e haka....

Ibtisam ri'ke kirjinta tayi wanda yake mata zafi Sosai, lokaci d'aya ta zauna wanda ganin haka yasa Abba yin shuru ba tare daya k'arasa abunda yayi niyan fad'a ba

Zama tayi tana cije lebe tare da shafa kirjinta tana lumshe ido

Granny cikin tashin hankali ta Fara fad'in na shiga uku ni Aminatu, ibtisam tashi tashi maike damunki maiya samu kirjin naki??

Ibtisam a hankali tace Granny ina son ganin kabir wlh jikina yana bani wani abu ya sameshi, plz Granny I need to see him help me plz allow me to see him, Tana maganan tana lumshe ido alaman kirjinta yana mata zafi gashi yana buga mata Sosai tare da faduwan gaba

Zarah Gaba d'aya tausayin ibtisam yasa itama ta Fara kuka

Shi kam Abba tsaki yayi tare da fad'in Indai dan kiga kabir ne, kike wannan abun sai dai ki mutu, domin ke yanzu matar aurece kabir ba muharraminki bane, mutuniyar banza yana fad'in haka ya fita fuuuu cikin fushi

Ibtisam kam gaba d'aya idonta ya rufe bata ganin komai, bakinta kabir yake furtawa Wanda jikinta ya gama bata wani mummunan Abu ya samu kabir din......

Ruwa zarah ta kawo mum ta Fara shafa ma ibtisam din, amma ko gezau batayi ba

Duka suka d'auka tayi bacci ne..

Ummi kam ita ta rasa mai takeji a halin yanzu gaba d'aya halinda ibtisam ta shiga yasa jikinta ya mata wani iri, ita ba mara lafiya ba, sannan bazata ita Mai lafiya bace dan gaba d'aya bata gane komai itama

A asibiti kuwa ansa ma kabir oxygen, domin baya ko motsi balle nishi sai dai Anga jijiyar hannunshi yana bugawa.

Gaba d'aya jikinshi duk jini ne, an gano I'd card d'inshi inda aka gano ko Waye, nan take aka kira y'an uwanshi domin ansan barrister Kabir dan ba k'aramin lowyer bane

Cikin tashin hankali family d'inshi suka zo asibitin, amma ganin halinda yake ciki yasa hankalinsu ya k'ara tashi, wanda suke tunanin abubuwa da dama tare da fargaba karsu rasa shi

Koda Abba ya koma wajan Dad fad'a mishi halinda ibtisam take ciki yayi inda ya buk'aci Dad daya kira NAJEEB yazo ya d'auki ibtisam din su tafi

Dad yace kai Anya za'ayi hakan kuwa? Inaga mu Bari ta dawo normal dan gaskiya dole ta shiga damuwa, Sosai ace za'ayi auren mutun zai yaji an canza anyi da wani abun bamai sau'ki bane

Abba yace hakane, amma abunda nake son ka gane shine, shifa kaddara ya riga ya faru, kuma bamu isa mu canza ba, dole hakuri zamuyi kawai,sannan Idan NAJEEB ya tafi da ita inaga hakan shine zaisa ta manta komai a nawa ganin

Dad yace hakane, amma inaga mu Bari nida Mum d'inshi zamu je London mu Kai mishi ita, inaga hakan zaifi

Abba yace duk yanda ka tsara hakan yayi, babu damuwa

Dad yace jibi zamu mu kaita, sai dai maganan karatun tafa??

Abba yace ka manta da wannan karatun taje tayi bautar uban giji kawai, ta nemi lahiran ta, tabar maganan neman duniya..

Dad yace a'a hakan bazai faru ba, dole taci gaba tunda ta Fara, inaga idan muka kaita koda 2week tayi saita dawo Kafin nan sun koma skul, jibi zamu tafi zansa Ayi mata visa

Haka kam akayi dad yasa anyi ma ibtisam visa, domin tafiya London

Ibtisam kam gaba d'aya tunda ta Farfad'o daka suman da tayi wanda da Farko suka zaci bacci take, gaba d'aya bata magana sai hawaye cikin damuwa, ita d'aya tasan mai takeji, duk Wanda yayi mata magana bata bashi amsa sai dai tabi mutum da ido, wai itace yau matar NAJEEB, gaba d'aya ta tsani duniya tare da abunda ke cikinta,inda tasan wannan ranan zaizo data ro'ki mutuwa, wai NAJEEB din data tsana a duniya wanda baida imani shine aka d'aura mata, kuma taga gaba d'aya family d'inta kaman sunji dad'in hakan wanda wannan shine silan da yasa ta share kowa

Harta abinci bata ci, sai da ummi ta mareta da safe saboda yanda ta'ki amsan abinci taci, ganin Ummi tayi zafi Sosai yasa Mum yima ummi fad'a akan ba'a haka, ita ta amshi abincin ta Fara bama ibtisam a baki

Ummi gaba d'aya taji ibtisam ta Fara bata haushi, wanda take ganin akan Mai yasa bazata amshi kaddara ba? Duk da tasan Abun da ciwo Sosai

Kaman yanda Dad ya fad'a haka aka shirya tafiya, ita dai ibtisam komai sukace mata yi takeyi, amma bata furta koda kalma d'aya, gaba d'aya ta koma kaman wata kurma, tsorata d'aya ita Kar ace wani abu ya samu kabir domin ita har yanzu jikinta yana bata babu lafiya

Haka suka tafi London ibtisam bin kowa take da ido, ita gaba d'aya bata tunanin komai da kowa sai Kabir

Mum gaba d'aya tausayin Itbtisam take ganin irin halinda take ciki wanda gaba d'aya ta canza tayi rama sai kace wacce tayi ciwo, sai dai ta k'ara haske sai fuskanta tayi kyau Sosai, dama ga gyaran jiki anyi mata

Bayan su Mum sun sauka a airport wanda dama sun Sanar da NAJEEB akan zuwansu sai dai basu fad'a mishi dalili ba, jin iyayenshi zasu zo yasa duk wata kwalban alcohol dake gidan ya fitar dasu tare da boye wasu cikin bedroom d'inshi tunda yasan ba lallai bane su shiga

Shida kanshi Najeeb yaje airport d'aukosu ganin ibtisam a tare dasu yasa Abun ya bashi mamaki, kallo d'aya yayi ma ibtisam ya kauda kai amma yasan ta tare kaman bata da lafiya, sai kuma ya fara tunanin ba anyi aurenta yau four days kenan ba? Kodai bata da lafiya ne, tabe baki yayi lokaci d'aya tare da fad'in I don't care

Rungume iyayenshi yayi tare da fad'in welcome Dad, welcome Mum

Mum dake ri'ke da ibtisam tace my only son ina motar muje plz

Yace yana waje

Fita sukayi inda suka shiga cikin motar Dad shine a gaba, mum da ibtisam a baya NAJEEB na tuk'i, gidan suka wuce

Bayan sun karasa Mum ta kalli NAJEEB tace ina masu aikin suke?..

Yace mum duk na sallamesu sai mutum d'aya na Bari wacce take Shara da goge gidan, itama nace bana son tana Kwana a nan 

Mum tace akan wani dalili NAJEEB

Yace mum ban son takura dat why

Mum tace Allah ya kyauta

Kallon ibtisam tayi data kafe kanta a k'asa alaman tana tunani, kiran sunanta tayi da ibtisam

D'ago dakai tayi ta zuba ma Mum ido alaman tana jinta

Mum tace kina bukatar ki huta koh?

Ibtisam bata ce komai ba sai ido data xuba ma mum

Ganin haka najeeb daya kura mata ido yasa shi fad'in mum ta samu tabin hankali NE???

Mum Hararanshi tayi

Ita kam ibtisam jin haka hawaye ya fara zubo mata, Aiko tana fara hawayen sai kuma kuka lokaci d'aya ta Fara furta Kalman Innalillahi'wa inna ilaihirajiun

Mum taji dad'i da taji ibtisam din tayi magana, sai hakan yayi mata dad'i Sosai

NAJEEB kam wani irin tsaki yaja, tare dajin haushin kukan da ibtisam keyi, tashi yayi yabar falon danshi kwata kwata baya son yarinyar, cikin ranshi yace ina jin tausayin mijinta, shima idiot ya rasa wacce zai aura sai ita

Rarrashin ibtisam tai tayi inda daka karshe ta kaita wani d'aki dake kusa dana NAJEEB tace ta huta Kafin a Kawo abinci

Bayan mum ta fito daka d'akin, d'akin NAJEEB ta shiga Bayan tayi nocking yace ta shigo

Mum kallon d'akin tayi tace Kai NAJEEB ka canza komai na d'akin nan

Yace Mum bana son tarkace da yawa a bedroom that why na cire

Mum tace Allah ya kyauta, kazo falo muyi magana.

Yace akan me Mum? Yauwa Wai maiya samu wannan yarinyar ba tayi aure ba, maiya Kawo ta nan?  Nifa am scare dan naga kaman hauka takeyi Karta hanamu bacci 

Mum tace Mai yasa kake haka ne

Yace Mum ni ban son ganin yarinyar nan I hate her bata da kunya

Mum tace fita muje ban son shirme

Tashi yayi yabi Mum suka fita falo inda suka tarar da Dad zaune yana kallo

Mum tace gashi nan sai kayi mishi bayani

Dad yace yauwa NAJEEB zauna muyi magana

Zama NAJEEB yayi yana fad'in akan me Dad

Dad yace akan maganan aurenka

Yace what aurena? Dawa kuma? Dad plz ban son wannan maganan just change the topic

Dad yace NAJEEB wannan maganan ta zama dole, domin kuwa aure an riga an d'aura

Tashi yayi tsaye tare da fad'in what?....  Lokaci d'aya kuma yayi murmushi tare da fad'in Dad you are joking right?..

Dad yace ko d'aya, NAJEEB kasan ibtisam zata auri KABIR....

NAJEEB ya Katse Dad tare da cewa wannan bashi bane damuwa ta Dad, nidai Ina fatan maganan aurena bada gaske kake ba

Dad yace na taba maka wasa ne NAJEEB?

NAJEEB zama yayi tare da d'aura k'afa kan d'aya yana juyawa

Dad ya fara magana tare da bashi Labarin abunda ya faru har d'aura mai ibtisam da akayi.....

Idon najeeb ne ya kad'a yayi jaaa saboda bacin rai, tashi yayi cikin zafin rai yana fad'in Dad wa yace kuyi min haka without my permission?

Dad akan wani dalili zaku yanke decision akan biggest thing in my life without my permission how dare......

Mum ta daka Mai tsawa tare da fad'in will you keep quiet?

Kana da hankali kuwa najeeb? Mahaifinka kake fad'ama haka? Kasan abunda kakeyi kuwa!? Kai har ka isa kace sai munyi shawara dakai Kafin mu yanke hukunci? Baka isaba sannan kayi kad'an

Najeeb yace plz Mum ki daina sa baki am respecting you

Kallon Dad yayi yace Dad I won't accept this marriage

Dad yace ko kaso ko kar kaso wannan ba damuwa ta bace, amma Abu d'aya nake son ka sani idan ka cutar da ita zan manta nine mahaifinka Wlh koda sau d'aya tace kayi Mata wani abu I will make sure to punish you.

Najeeb fita yayi daka gidan cikin fushi lallai Dad ya raina shi, eh ya raina shi mana akan wani dalili zai aura mishi wannan karamar yarinyar kuma mara kunya, wace bata da komai, kai tsaye wani club yaje duk da yanzu yamma ne giya ya bu'kaci a bashi yasha inda ya amshi kwalban giyan ya farasha

Najeeb giya yake sha Sosai a kalla yasha kwalba wajan biyar, wanda bai taba shayuwa irin haka ba tunda yake, gaba d'aya ya bugu a nan ya fad'i Bayan ya gama surutai barkatai

Najeeb bacci yayi a nan ganin haka suka daukeshi sukai ciki dashi, dama akwai d'aki ga Wanda suka sha giya suka bugu sai a kaisu nan in bacci ya d'aukesu

Dad Bayan fitan NAJEEB zama yayi cikin bacin rai, lallai najeeb yayi nisa, har zamu dinga fad'a yana fad'a? Lallai duniya ta lalace d'an daka haifa ya dinga fad'a maka haka

Mum ganin irin halin da mijinta ya shiga yasa ta Fara bashi baki tare da fad'in kayi hakuri da halin najeeb, gaba d'aya baya kyautawa, na rasa irin wannan halin nashi

Dad yace karki damu, I will teach him a lesson very soon, zanyi maganin rashin tarbiyanshi

Mum tace Allah ya kyauta

Ibtisam dake d'aki duk taji abunda ya faru, tunda abun ya faru sai yau tayi murmushi tare da fad'in lallai tasan NAJEEB zai iya sakinta tunda baya son auren, wani irin dad'i taji domin tasan zata koma ma kabir d'inta....

*KANO NIGERIA*

Kabir yau kwananshi biyar a asibiti amma babu wani ci gaba, domin har yanzu jiya I yau ne, abun gwanin tausayi kallo d'aya zaka mishi kaga ya canza yayi wani fayau dashi, lallai in baka mutu ba, ba'a gama maka halitta ba, kabir gaba d'aya ya sauya kaman bashi ba

Family d'inshi suna cikin tashin hankali, Hafsat itama tana asibitin duk ta shiga cikin duniyar tunani tare da damuwa, wanda ita tun tuni take son kabir amma bata taba fad'a ba sai gashi Allah ya bata shi, gashi kuma tana k'okarin rasa shi

Ganin irin halin da yake ciki babu wani ci gaba yasa suka yanke shawaran su kaishi waje kawai domin hakan shine suke ganin zaifi

Koda suka ma Dr magana bai musa ba, domin yasan can Sun fisu kwarewa inda ya rubuta musu takarda na neman yarda a fitar dashi domin a duba lafiyanshi a America

Washe garin ranan aka tafi da kabir cikin masu tafiyan harda hafsat da wani k'anin Kabir din sai mahaifiyarshi suka wuce inda zasu sauka a hotel in sunje domin can ba kaman nan bane inda za'ace za'a kwana da mara lafiya, su ba'a kwana da mutum

Koda suka isa America an amshi Kabir inda suka fara sabon gwaje gwaje akanshi domin su gano miye matsalar duk da sun duba takardan asibitin da suka fara dubashi a Nigeria amma basu wani gamsu dashi ba, dan haka yasa suka fara sabon nasu binciken

Najeeb bashi ya tashi ba sai washe gari wajan karfe 1 da wani abu, mi'ka yayi tare dajin ya manta duk wata damuwa dake tare dashi, kai tsaye tashi yayi ya fara kallon d'akin da yake ciki, da sauri ya tashi tare da tunanin maiya Kawo shi nan?

Lokaci

Please Login or Register in order to submit comment