Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Da yake da Hausa tayi maganan Granny taji komai, lallai gaskiyan mum ne, komai Najeeb yakeyi laifin audullahi ne, tun Farko irin abunda Granny ta hango kenan, lokacin da za'a kai Najeeb karatu waje bata soba, Amma dan nata ya dage, abunda yasa Granny koda ya dwo bata d'aga hankali ba, tunda taga yana sallah.

Dad kam tsumar tsaye yayi yana mamakin abunda d'an nashi yayi mishi Wanda bai taba zato ba, ko a mafarki ba.

Najeeb kam Bayan ya gama had'a kayanshi, "ya fara jin jiri, alaman giyar da yasha ta gama gauraye jikinshi da jininshi, "lokaci d'aya bacci ya D'aukeshi a zaune inda yake..... Muje zuwa yanzu aka fara.....















~MARYAM OBAM~*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE 11*







Granny tayi gyaran murya tare da fad'in "lallai duniya ta canza, amma ba laifinshi bane, naka ne, komai yayi kaine sila, duk da banji abunda yace maka ba, dan bajin yaranshi nake ba, amma alamu sun nuna ya maka rashin kunya, ko daka yanda yake magana hakan zai nuna min, kwata kwata yanda yake abu babu da'a ko tarbiya a ciki, ni kakarshi ce zai iyamin komai, amma kai mahaifin shine, tana fad'in haka "Ta wuce

Dad shima d'akin Mum ya nufa "inda ya sameta tana ta rusgan kuka, "mum ganin ya shigo yasa ta tsagaita da kukan ta Fara magana kaman haka " Kaga abunda ya faru koh? Abunda tun Farko nake....

Dakatar da ita Dad yayi da fad'in "wannan abunda Najeeb yayi yana tunanin wannan shine zaisa in janye magana ta akan auren da nace zaiyi? "inko haka yake tunani , ya yaudara kansa, wlh zan nuna masa nine mahaifinsa....

Mum tace "inka aikata haka Mai kayi? Kana tunanin wa Innan matan sun dace da Najeeb? Wlh bazan bari ya auri yarinyar da ake k'okarin tura mai ba, akan wani dalili? "tunda nake dakai ban taba maka musu ba, "but wannan karan bazan yarda a k'ara bata ma Najeeb rayuwa ba, "tun yana k'arami ka kaishi waje karatu, daka gama primary school, d'an karatun addini daya samu a nan Kafin ya tafi shine kawai a kansa, baka taba tunanin yana karatun addini ba koya? Kai dai ka kaishi yaje yayi karatun boko, Najeeb yanda yake abubuwa kwata kwata hakan yana nuni da bai San addini Sosai ba, yanda yake haka sai a d'auki y'ar kauye Wanda ban tunani yarinyar tasan addini, ace za'a bashi matsayin mata? "Najeeb baya bukatar mace jahila, "yana bukatar mace Mai ilimin addini wacce zatayi k'okarin wajan sashi a hanya, "Nasan komai Najeeb yakeyi bazan d'auki laifin in d'aura maka duka ba, sai dai zance "A cikin kashi d'ari kana da kaso 90 wajan abunda Najeeb yayi, ni kuma zan iya d'aukan "kaso goma.

Nima uwa ce, nice na haifi Najeeb, bai kamata in barshi haka ba, ya kamata ace Ina duba lamarinsa, "duk da yana da ba'kar zuciya, kuka ta saki tare da fad'in Nayi sakaci Wlh, Nasan halin Najeeb, amma Ka'ki d'aukan shawara ka kaishi waje karatu, "dama k'asar addini ne, irinsu "Saudiya
"Da ya samu ilimin addini K....

Dad ya dakatar da ita, tare da fad'in "Babu zancan rashin ilimin addini a cikin lamarin Najeeb, "ki daina danganta shi da irin haka, Nasan Najeeb yana da zafin rai, wannan na yarda dashi, "zai iya yin komai domin a fasa yin aurenshi da wacce mama ke so, ko sanda nakai Najeeb karatu America har na'ki jin shawaran kowa lokacin saboda na farko can Sun fimu nesa ba kusa ba, yaro zai samu cikakkiyar ilimi ba irin na wannan k'asar ba, "Sannan Indai kina magana akan ilimin addini ne ai yayi tun yana yaro, kuma yana kanshi so kib....

Mum tace Innalillahi'wa inna ilaihirajiun "yanzu haka zaka fad'a? "kenan kai ilimin boko shine mai muhimmanci a gurinka? "wato karatun addini da yayi sanda yana yaro shine kake Kawo hujja akai? " lallai kayi babban kuskure na fad'in haka, amma babu komai zan zuba ido inga iya gudun ruwanka, "but Ina son ka sani a matsayina na Uwar Najeeb bazan k'ara Bari a rusa mishi rayuwa ba, "Inda Najeeb ya samu ilimin addini Sosai da Wlh bazai fad'a maka abunda yayi maka yau ba, sannan ilimin addini shine gaba da komai.


Mum taci gaba da fad'in a cikin...... SURATUL ALAK'

Wacce take karantar da cewa karatu shine gaba da komai, amma a Gama shi da Sunan Allah, kuma ayi aiki dashi domin a sami kiyayyewar Allah daga dukan mak'iya addini.....

Abunda wannan surar take nufi, shine

A nema ilimi addini, saboda duk inda mutum yaje zai iya Kare kansa, tare da taimakon Allah.

Amma kai ka tura d'anka ba tare da ilimin addini ba

A cikin SURATUL ALAK'.... Aya ta 3 Allah yace....

*Kayi karatu, kuma ubangijinka shine mafi karimci*

Sannan a Aya Aya ta 4 yace :

*wanda ya Sanar da mutum game da alkiyama*

*ya Sanar da mutum Abin da bai sani ba* 5

*A'aha! Lalle, ne mutum, hak'ik'a, yana girman kai (ya k'i karatu)* 6

*Domin yaga kansa, ya wadata* 7

*lalle ne zuwa ga ubangijinka makoma take* 8

Mum tace Kar dukiya yasa Ka'ki d'aukan karatun addini da muhimmanci, domin Allah zai tambayeka.

Koda Kaga ina son yarana suyi karatun boko saboda zamani kuma ..... *ALKUR'ANI* yayi rantsuwa da zamani, A cikin...... SURATUL ASR

Allah yace :

*Ina rantsuwa da zamani* 1

Zamani yazo da abubuwa da dama, ina son yarana suyi karatun boko badan komai ba sai dan zamani yazo da hakan, "sannan yana dakyau kota ina mutum yasan abunda duniya ke ciki, yanda zai iya shiga ko ina,.

Amma kai kafi bama karatun boko muhimmanci fiye dana addini, "wannan yana d'aya daka cikin abunda yasa nace Zarah bazata fita wata k'asar karatu ba, "nafi son tayi cikin wannan k'asar inda zan dinga ganinta, "kuma ta samu ilimin addini ita ba kaman Najeeb ba, yau zan iya yarda Zarah taje ko ina saboda na yarda da ita, bazatayi abunda za'a ce Allah wadai ba, "Shima Najeeb nasan bazai aikata Wani abun alfasha ba, ina mishi kyakyawan zato, Sai dai girmanshi a America yasa yake ganin shi mutum Mai y'anci ne zai iya jada kowa, Wanda inda yasan addini bazai yi wannan tunanin ba, uhm Mum kenan ba'a shaidan d'an yau, taci gaba da fad'in Najeeb bai dace da wannan yar......

Dad ya dakatar da ita tare da fad'in "ya isa haka, kince Najeeb zaman da yayi a America yasa yake ganin shimai y'anci ne, "har yake ganin zai iyaja da kowa, toh Wlh Indai Ina Raye saina aura mishi yarinyar da mama tace, "zan nuna mishi nine ubansa, kuma zaman America ba hauka bane

Mum tace "kana son aikata babban kuskure, "Ina Mai baka shawara tun Kafin Najeeb yayi fito na fito dakai kabar wannan maganan, "yau gashi ya fad'ama abunda ban taba tunani ba, har yake fad'in "yasan right d'inshi

Dad tashi yayi yabar d'akin yana fad'in Aure dai babu fashi.

Mum kai ta girgiza alaman mijin Nata yayi nisa.


Najeeb kam bai farka ba sai wajajan magrib, "koda ya tashi kanshi ya ri'ke alaman yana mishi ciwo, ido ya lumshe tare da tashi danya nufa toilet yayi wanka, lokaci d'aya ya tsaya "domin ganin kayanshi cikin akwati tunani ya farayi ya akai akasa mishi kaya cikin akwati? Lokaci d'aya ya fara tunawa tun a Wajan Gina yasha alcohol, daka nan yazo gida "Toh Mai ya faru Bayan yazo gida? Lokaci d'aya ya lumshe ido domin tunawa da yayi abunda ya fad'ama Dad d'inshi har marinshi da yayi duk ya tuna, saboda baisha alcohol din da yawa ba, shine dalilin da yasa ya iya tuna, abunda ya faru.

Hannu ya d'aura akai alaman Maina aikata? Lokaci d'aya ya saki tsaki, tare da fad'in "duk laifin wannan old woman dince , "bana shan alcohol a Nigeria, but tunda tazo tasa saida nasha "ta Kawo min wasu yamutsatsun mata masu Kama da birai wai in aura, wani dogon tsaki yaja, sannan ya fad'a toilet yayi wanka tare da dauro alwala dan yaje masallaci

Koda najeeb ya dawo daka sallah, direct gefen Dad d'inshi ya nufa, Wanda ya iskeshi akan dadduma, cikin ran Najeeb yace a gida yayi sallah ashe? Sai yasa ban ganshi cikin masallaci ba.

Dad d'ago dakai yayi ya kalleshi "Lokaci d'aya yace ya akayi Najeeb?

Najeeb ganin yanda Dad ya mishi saiya d'auka kodai abunda yake tunani bai faru bane? "lokaci d'aya kuma ya tuna da ko sanda yana yaro in yayi mishi laifi baya nuna mishi sai dai yaga action, wannan tunanin da yayi yasa Najeeb zama akan bed din d'akin tare da fad'in "Dad kayi hakuri akan abunda ya faru d'azu, rainane ya baci Sosai, "and kuma bazan iya bari a aura min macen da bana soba, "Dad ko Kai kana son Mum ka aureta, nifa plz ka fad'ama granny ta Bari in auri wacce nake so.

Ni mutum ne mai shiga ko ina a cikin duniya, "am a pilot babu k'asar da ban shiga ba, yanzu sai azo ace wannan za'a aura min? Illiterate "haba Dad ya kamata Ayi min adalci, "And yanzu mulkin farar wula ne, kowa Nada y'anci, ko a cikin wannan k'asar ta Nigeria, balle nida na taso a waje, "so Dad plz Kubar wannan maganan and give me sometime zan Kawo irin choice d'inku

Dad shuru yayi yana kallon d'an nashi "sai yanzu ya yarda da maganan Mum, Gaskiya ta fad'a, "Yanzu wai nan yazo ya bashi hakuri ne, amma jiba maganan da yake fad'a babu da'a ko kad'an a cikinta

Dad murmushi yayi tare da fad'in "Toh Najeeb inaga ka manta da Abu d'aya, "Idan ka taso a America karka manta kai bad'an can bane, kai d'an Nigeria, and rayuwarka da tasu ba d'aya bane, kana fad'in kana da y'anci? Right? " Toh zan nuna maka baka dashi, "danka taso a America ba'ace ka koyi irin halinsu ba, na yima iyaye rashin da'a, tare da fad'a musu magana anyhow

Najeeb yace Dad "ni ba magana anyhow nake fad'ama ba, "am just try to tell you what on my mind" and Dad mai yasa kake k'okarin canzawa? Kake son d'aukan shawaran Granny, "just be ur self," ka daina d'aukan shawaran kowa, am ur son, but bazan bari ayimin abunda zai cutar dani ba, plz Dad am begging you kabar wannan maganan

Dad yace OK tashi ta tafi.

Tashi Najeeb yayi tare da fad'in "Thanks for understanding me Dad, "jibi zan koma

Dad yace Allah ya kaimu

Koda Najeeb ya fita Dad mamaki yaita yi, sai yanzu yake ganin maganan Mum gaskiya ne, "lallai Nayi sakaci tun Farko, Gashi yanzu yana son fin karfina, "but Idan nace bazan aura mishi matar da Granny tace ba zaiga kaman munji tsoranshi, "Tabbas dole Ayi wannan aure kuwa

Najeeb koda ya fita waje ya nufa wajan bukka inda yaga ibtisam tana zaune tana waya, tana murmushi, " wani irin kallo ya watsa mata Mai kama da ta tashi tabar wajan " Idonta na kanshi itama tana wayarta amma bata da niyan tashi, domin dashi da banza duk haka ta d'auka

Najeeb ganin haka yasa ya nufeta tare da fusge wayar yayi jifa da ita, cikin zafin rai yace bazaki tashi ba?

Bata kulashi ba, sai tsugunnawa da tayi ta d'auki wayarta, "wanda murfin ya fita batter din ya cire, "domin har yanzu bata fara amfani da wayan da Kabir ya bata ba , da karamim Nata take amfani.

Bayan ta d'auki wayar ta tashi ta kalleshi ido cikin ido, tare da fad'in "bazan tashi ba, babu inda zani, kana tunanin wannan Abun zaisa inji tsoranka Kome? Najeeb bari kaji daka jiya sanda ka mareni duk wani sauran d'an digon mutuncinka da nake gani ya tafi, so komai zakamin bazai dameni ba, Abu d'aya na sani shine bazaka iya kasheni ba

Kallonta yake cikin mamaki, lallai yarinyar nan bata da kunya, Hmm kunji Najeeb Bayan shi ba kunyar gareshi ba shine yake kallon na wani, koda yake bazai ga nashi ba, tunda shi a ganinshi ba rashin kunya yayi ba,

Tsaki taja tare da juyawa, Tana k'okarin zama, "hijab din dake jikinta ya janyo tare dayin jifa da ita ta fad'i k'asa, wani irin k'ara ta saki domin ta gefen hannun da taji ciwo ta fad'i, "matsawa yayi kusa da ita tare da tsugunnawa yace " kince komai zan miki bazan iya kasheki ba koh right? "ido ya lumshe tare da sakin murmushi lokaci d'aya kuma ya bud'e idon ya saukesu akan fuskanta da take ta faman hawaye, "yace kina tunanin Idan mutum ya mutu shikenan, ko kina tunanin duk wani abu da zan miki zaki jure? Tunda wuya baya kisa ko? Murmushi ya k'ara saki tare da fad'in zan aureki inta Azabtar dake, wanda keda kanki sai kinyi nadama kin ro'keni akan in yafe miki Kafin in rabu dake, "Kinga nasan da hakan ta faru dake gwara ki bani hakuri yanzu, kuma ki tsugunna da giwowinki biyu and apologize.

Tashi yayi yana jiran ta bashi hakuri, ganin bata tashi ba ,yasa yace na baki daka nan zuwa gobe, Indai baki bani hakuri akan abunda kikai min ba, wlh saina fad'ama that old woman ke zan aura, yana fad'in haka yayi gaba.

Ibtisam kam, ganin ya tafi yasa ta fad'in, wlh dana aureka gwara in mutu kaman yanda ka fad'a, " lokaci d'aya kuma taja tsaki tana fad'in "hakuri kake son in baka koh? Wlh sai dai ka mutu, nida kama Abu bance kaban hakuri ba sai kai tsaki taja Mai sauti............ Toh fah mai Najeeb ke nufi? Ku biyoni dai



*NAGA SA'KON KI, KAMAN YANDA KIKA BU'KACI AITA YAD'AWA HAR YAZO GAREMU GA SA'KON DA WATA TA TURO*


TABBAS BABU MUNAFUKAI IRIN ONLINE WRITERS!!!

Munafukan banza munafukan wofi masu dorawa yaran mutane dogon buri da kai Kansu in da Allah bai kaisu ba,xan fara da babbar munafukan......zuwairat Ummu maryam,,,,in banda tsabar kinibibi da Gulma duk novel dinki sai kinsaka yarinyar ciki kyakyakyawa ce, to su munanan matan ba mutane bane ko kuma xasu rasa mijin aure ne,,matsiyaciya me qaryar tsiya kina koyawa yara son abin duniya.....nadawo gareki marubuciyar BARIKI NA FITO!!! Wato ke saboda matsiyaciya ce bayan batsan da kk shimfidawa a littafin ki harda koya ma yara suje su gama tambadewar su daga baya su auri salihin namiji ko!munafuka kin taba ganin namiji dan mutunci ya auri karuwa kuma ma dan sarki,, shegiya ke kamata yayi ma a kamaki a daure asa dogarai su zaneki don kinci mutuncin sarauta,ku kuma 'yan mata duk Mara basirar data dauki hudubarta ta watsar da mutuncin ta a waje kuma tana tunanin samun mijin aure da sauqi ita tasani,,,
Nadawo kanki marubuciyar KO BAN AURESHI BA...Kema dayake algunguma ce nuna musu kk suyi wasanni da wani qato indai baxai xarce ba ko,,,,munafukan banxa duk iyalinku na killace kun dage sai kun sauya ma yaran mutane tunani kun dorasu kan turbar kwadayi da buri...shegu ku gidanku miya ake da naman kaji ko ruwan faron da kuketa kwadaita musu ku sha kuke,ko kuma maxajenku son ku suke kamar su bauta muku ko duk wata ko sati sai kun xaga qasashe???ku fada musu gsky aure ba haka yakeba kuma ku koya musu haquri dan yadda suka samu kansu ba wannan karairayin ba..

Daga saudatu shafi'i

Don Allah kuyita yadawa har yaje kunnen marubutan.


*Kunga abunda tace, kaman yanda na fad'a bazan k'ara daukan zagin wata a media ba insha Allah, tace min shegiya, Bayan da aure aka haifeni, in asali ne ko nagarta ban tunanin zata nunamin, ko d'aya, domin na fito daka gidan mutunci, Alhmdlh iyayena sun bani tarbiya, tunda ban fito media ina zagin wata ko wani ba.*


*bazan ce na ajiye rubutu ba, amma daka yau novel din NAJEEB ya koma na kud'i, kunga yanzu sai a zageni da hujja, abunda na Lura muda muke novel a free Anfi zagin mu, toh daka yau na daina insha Allah, duk Wanda zai karanta Littafin NAJEEB saiya biya 200 Naira only*

*Nasan yau zansha zagi a media saboda nace novel d'ina ya zama na kud'i , amma babu damuwa kofar zagin a bud'e take*


*WANDA ZAI BIYA DOMIN YACI GABA DA SAMUN CI GABAN NAJEEB ZAI TURA D'ARI BIYU TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 3138831065 MARYAM ALHASSAN FIRST BANK, SANNAN IN MUTUN YA BIYA ZAI TUROMIN DA SHAIDAN BIYA TA WANNAN NUMBER 08060860886*

*IN KATI MUTUN ZAI TURO ZAI IYA TUROMIN KATIN MTN TA WANNAN NUMBER SHIMA 08060860886*


*IDAN MUTUM YA BIYA D'ARI BIYU ZAN SASHI A GROUP HAR SAI AN KAMMALA LITTAFIN NAJEEB*

*IDAN KIKA BIYA KO KA BIYA INA SON KU SANI KUDIN KARATU MUTUM YA BIYA BANA MALLAKA BA, IDAN HAR MUTUM YASAN ZAI FITAR MIN DA NOVEL DAN ALLAH KARYA BIYA*




*KAMAN YANDA NA FAD'A CEWA LABARIN NAJEEB ZAIZO MUKU DA WANI SABON SALO DABAN, HAR YANZU BAN SHIGA AINIYIN LABARIN BA, WANNAN LABARIN ZAI BAN BANTA DA SAURAN LABARAN, DOMIN AKWAI ABUBUWA DA YAWA DA LABARIN ZAI KAWO MUKU, KAR TWO HUNDRED NAIRA YA HANA MUTUM KARATU*




















~MARYAM OBAM~*NAJEEB*




*PAGE 12*




Lokaci d'aya ta ri'ke hannunta domin jin yana mata zugi, zama tayi akan kujeran dake cikin bukka din tana cije baki, " tare da fad'in Allah ya isa Wlh mugu, "ji yanda ya fama min ciwo na

Zarah ce tazo inda take "hannunta d'auke da tray dasu snack da drinks, ajiyewa tayi, tare da kallon fuskan ibtisam tace "lafiya kike cije baki?

Ibtisam tace nida wancan yayan n..... "sai kuma tayi shuru ba tare data k'arasa abunda tai niyan fad'a ba

Zarah tace Yadai? "Mai yasa kikai shuru, kodai kin fama hannun ne?

Kai kawai ta d'aga mata tare da fad'in na buge ne da wancan Karfen "Zarah tace Kedai kullum cikin fad'uwa da bugewa?

Tsaki ibtisam taja tare da k'okarin kunna wayarta da Najeeb ya jefar mata dashi, Aiko tana kunnawa sa'kon Kabir ya shigo cikin wayar, "lokaci d'aya ta saki wani irin k'ayattacen murmushi tare da fara karanta sa'kon kabir din kaman haka....

*hope lafiya? "muna waya naji shuru, and I try your number switch off*

Murmushi tayi tare da k'okarin ta bashi amsa, amma tana d'aga hannunta ta saki k'ara, "tare da fad'in ahh, "Zarah tace lafiya? "ibtisam tace Wlh hannu na zafi, "ko d'agashi na kasa, zugi yakemin Sosai, "yanda kika san ana ciremin jijiyan hannun.

Zarah tace sannu ko zamu koma hspt dinne yanzu?

Ibtisam tace "gobe Dr yace mu koma "inaga mu jira zuwa goben mu gani, yanzu dare yayi ma.

Zarah tace "wani dare kwata kwata miye time yanzu? Koso kike ki zauna da ciwo a hannunki? "is better kizo muje kiga Dr dan Wlh Idan kika kwana dashi zaki sha wuya.

Ibtisam tace leave it I will manage, "Bari goben kawai muje, ni Bari kiga inje in kwanta na gaji Wlh Sosai " gaba tayi ba tare data jira mai Zarah zata ce mata ba.

Koda ta shiga "a falo ta iske Granny tana zaune, daka gani akwai abunda take jira,

Ganin ibtisam ta shigo yasa Granny tashi tana fad'in yauwa Ina kuka saiga cikin wannan daren? "ko kabirun ne yazo?

Ibtisam tace a'a Granny muna bukka, "Granny tace ku kullum sai kunje wannan bukka dinne? "Mai kukeyi a can? "ibtisam tace Kai granny ka jiki da wata tambaya, sai kace wasu k'ananan yara.

Granny taja tsaki tare da fad'in "Ashe kun San kuba yara bane, kuke zaune gida gadai gadai daku "Wlh kuma kanku fad'a, kuji tsoran Allah, "kunga abunda miskili yakeyi saboda boko kar ku biyema iyayenku kuce ku sai Kunje karatu, Inba so kuke ku rasa mazan aure ba "In banda fitsara da rashin kunya babu abunda bokon ke koya muku, "ni wai yaushe kabirun zai turo ne?

Ibtisam tace Kai Kai na shiga uku, "waike Granny waya fad'a miki boko na lalata mutum da rashin tarbiya? "Wlh Granny ki iya bakin ki, Idan kika bari boko ya jiki zai kamaki.

Granny tace au dama bokon mutum ne? "a Ina yake?

Dariya ibtisam ta saki Wanda a dai dai lokacin Zarah ta shigo itama tana dariyan

Granny tace aikin banza, ni za'a ma k'arya, "tun kan a haifeku Nasan boko ja'irai, nidai bazan fasa fad'a ba Wlh auren dai shine mutuncin mace, Kun zauna sai tsufa kuke a gida, "ai gwara kuyi auran yafi mutunci, "baku ga yanda akai ta tambaya naba da Naje yola, kowa sai yace kunyi aure kuwa? "sai dai ince a'a cikin jin kunya, sai kuma ta saki kuka yanzu god'ai god'ai daku ace kuna gida babu aure, "shi miskili d'an banza an kawo mishi Mata ya nuna baya so, "ke kuma ta nuna ibtisam kince zaki sa kabiru ya turo shuru akeji, in bazaki iya cewa ya turo ba, ai saiki fad'amin ni ince ya turo....

Ibtisam tace Wlh Granny karki soma "ni Dan Allah kibar wannan kukan, haba abu kad'an kisa kuka.

Yanda kuka san ibtisam ta zugata "ta k'ara fashewa da kuka tana fad'in yanzu ko tausayina bakwayi? "so kuke in mutu banga y'ay'anku? " riganta tasa tana share kwallan fuskanta

Zarah kam dariya take mak'ewa, domin wannan abunda Granny take fad'i ba k'aramin dariya yake bata ba, "duk da Tana ganin maganan Granny gaskiya ne, aure shine mutuncin mace, "Toh amma miye na kuka sai kace su zasu kamo mazan suce suzo su auresu, duk da tasan ita ko zata mutu iyayenta ba zasu mata aure ba sai ta kammala degree Kafin zasu Fara maganan aurar da ita

Ibtisam tace Kinga Granny "gwara ki tashi kije ki kwanta, domin wannan kukan naki bashi zaisa muyi aure ba, "sai kace akanki muke duk kinbi kinsa mutane gaba, "wucewa tayi tana fad'in nidai saida safenku bacci nakeji.

Granny ta bita da harara Tana fad'in aikin kenan dama, "daka ci sai bacci ku tashi kuna kallon iyayenku kaman tsaranku, yara Sun girma Sun ri'ke a gida, harta yanda kuke tafiya ta canza saboda ri'ka

Zarah kam dariya take Sosai tare da fad'in Granny "Nima na tafi saida safe bacci nakeji

Granny tace Allah ya kaimu rai da lafiya, " Zarah gaba tayi "granny ta bita da ido tana fad'in jiba yara god'ai god'ai dasu, amma anki musu aure, gaba d'aya in suka juya sak manyan mata, "oh ni aminatu na shiga uku, "tashi tayi itama tana fad'in "Bari inje inbi lafiyan gado in kwanta in huta.

Najeeb kam tunda ya fita hotel din da Gina take ya nufa, "koda ya isa Bayan ya mata nocking ta bud'e shiga yayi ya kwanta tare da lumshe ido, "ba komai yake tunawa ba, sai yanda ibtisam tayi mishi rashin kunya, "murmushi yayi tare da tunanin hanyar da zaiyi hurting d'inta, danya Lura bata jin tsoranshi, sannan bata da kunya"lokaci d'aya kuma yaja tsaki tare da fad'in ya kamata in fita hanyar ta, but she has to apologize to me, Kafin in barta, I have to teach her a lesson that she will never ever forget in her life....

Gina ce ta katse mishi tunani da tasa hannunta cikin riganshi, "Tana wasa da kirjinshi, tana shafawa tare da mishi tafiyan tsutsa, "lokaci d'aya ya bud'e ido tare da janyota jikinshi, ya bata wani hot kiss akan lebanta, lokaci d'aya ya kuma ya tureta tare da tashi ya nufi fridge din dake d'akin ya d'auko alcohol ya bud'e tare dasha, domin har yanzu abunda ibtisam tayi mishi yana cikin ranshi, burinshi yayi hurting d'inta much da bazata k'ara raina wani ba in her life.

Shan alcohol d'inshi yake Sosai tunda ya kafa kai saida yasha kusan rabi, "sannan ya cire bottle din daka bakinshi yana sauke wani irin numfashi tare da lumshe ido, "lokaci d'aya ya bud'e idon tare da kurama Gina ido yana murmushi, "ganin yana sakar mata murmushi yasa ta tashi da sauri ta nufeshi tare da zama akan k'afarshi tasa hannunta akan wuyanshi tana shafawa, "lokaci d'aya kuma ya janyota tare da matseta da karfi a jikinshi yana shakan jikinta lokaci d'aya yasa harshen shi akan lips d'inta ya fara kissing d'inta, "da sauri Gina ta Fara miyar mishi da martani itama

Kissing din junansu suke Sosai, "Gina bakinta nakan nashi take k'okarin cire rigan jikinta, "lokaci d'aya tayi nasara ta cire rigan dake jikin nata, dama babu bra balle pant

Please Login or Register in order to submit comment