Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"kuma Kinga ga yaya Najeeb baiyi aure ba, ya kamata injira in yayi nima sai inyi hakan zaifi.

Granny ta tsuke baki, "can tace ke nifa so nake a had'a bikin duka, dan ban son Ayi ta hidima kan hidima aita abu a rarrabe, gwara a had'a, zaifi, " saiki fad'a ma Kabiru ya turo, inbai shirya ba mu sani. "kallon zarah tayi tace kema ya kamata in kina da manemi anayin nasu Kema kice ya turo, nida so samu ne duka basai a had'a ba.

Ibtisam tace ni saida safe tare da tashi tabar wajan.

Granny tace " oh ni Amina yara basa son zancen aure, daka an fara saisu tashi, kaman masu iska, "Zarah Anya bakya tunanin suna da aljanu kuwa? Granny ta jefo ma Zarah wannan tambayan.

Zarah dariya tayi tare da biye ma Granny "tace ashe bani d'aya nake tunanin haka ba, "Granny tace haba ashe Kema kina tunani kai na shiga uku, "Kinga miskili shi tunda yaji zancen aure yabar gidan har yanzu bai dawo ba.

Zarah tace "Granny nifa ina tunanin wannan matan ne baya so, " inda zaki canza mishi wasu da hakan yafi, ko kice ya kawo wanda yake so.

Granny tace "sam wannan ba abu mai yihuwa bane, "koso kike a maidani karamar mutum?

Zarah tace "kaman ya Granny?

Granny tace "inje in kwaso Mata har hud'u, sannan ace bai d'auki ko guda d'aya ba, "inna koma Mai zance ma iyayen yaran? "Kinga tashi kije ki kwanta, "Granny tashi tayi tana fad'in saida safe, "miskili d'an banza ya'ki dawowa.

Najeeb bai farka ba sai wajan d'ayan dare, "tashi yayi yaji gaba d'aya jikinshi yayi mishi nauyi Sosai, "Kai tsaye ya nufi toilet yayi wanka tare dayin alwala yazo yana rama bashin sallah, Allah dai ya kyauta, "bayan ya idar ya tashi ya d'auki key din motarshi yabar hotel din, " Kai tsaye gida ya nufa inda yayi horn Mai security suka bud'e Mai kofar ya shiga part d'inshi ya nufa direct, "Bayan ya shiga gaba d'aya kayan jikinshi ya cire yasa jallabiya tare da kwanciya bai dad'e ba bacci yayi gaba dashi

Washe gari da safe tunda Granny tayi sallah asuba, ta fito falo ta zauna "wai miskili bai kwana a gida ba Tana jiran ya dawo taji gidan uban wa ya kwana, sai gyangyad'i takeyi, "amma ta'ki tashi tana nan zaune Wai tana jiran miskili, " a haka bacci ya bingirar da ita a nan Hhhhh, "shi dama bacci barawo ne gashi ya sace granny.

Wajan karfe 10 mum ta fito falo "ganin Granny kwance akan kujera tana ta shakar bacci,abun yaba mum dariya, "tare da fad'in badai a nan ta kwana ba? Har zata tasheta ta fasa dan in Granny ce sai tace ta katse mata bacci, dan haka ta Fasa tare da wucewa kitchen taga mai masu aikinta suke dafa musu, "koda mum ta nufi kitchen "gaidata masu aikin suka farayi cikin girmama a harshen turanci ,"Mum tace an kammala komai kenan?

Suka amsa da yes ma

Fita Mum tayi ta koma falo inda ta Tarar da Granny zaune tana hamma "Mum tace ina kwana mama

Granny tace "lafiya an tashi lafiya?

Mum tace lafiya Alhmdlh.

Granny tace "Ina nan tun dazu ai ina jiran dawowan wannan Yaron, tun jiya bai shigo gida ba, saiya fad'amin inda ya kwana, kallon Mum tayi "tace Wlh kuna bani mamaki ace d'anki bai kwana a gida ba amma ku ko a jikinku, baku ma sani ba, kai Wlh wannan halin naku yana bani mamaki.

Mum dai shuru tayi dan bata da abun fad'a, inma tana dashi bazata iya jayya da Granny ba, tunda Uwar mijinta ce, dole itama ta d'auketa matsayin uwa, "Abu d'aya Mum take ganin za tayi jayayya da Granny shine ace Najeeb ya auri matan data kawo, sai dai in shine yace yana So, shine zanyi shuru.

Granny sai faman fad'a takeyi ta inda take shiga ba tanan take fita ba "ace yaro saurayi ya kwana a waje ba tare da saninku ba, wannan wace irin tarbiya ce? "Haya niyan Granny shine ya tashi Dad Wanda ya fito falon da sauri, ganinshi yasa Granny tace yauwa gwara da kazo

Yanzu d'anku ace ya kwana a waje, amma baku damu ba?

Dad yace mama kiyi hakuri Najeeb ba yaro bane, sannan shida yake wata k'asar da bama ganinshi ma, "Allah ne yake karewa n.....

Dakata dakata Granny ta katse shi da fad'in haka, sannan tace "can daban nan daban, Niko can Ameka din da yake aiki baso nake ba, andai fi karfina ne, saboda y'an Ameka basa ji wlh, suko kunyan taba junansu basayi, kai duniya ta lalace, ku ko tsoro bakwayi ya kwaso irin halin..... Shuru tayi na wani lokaci sannan taci gaba da fad'in "koda yake shi miskili bazai yi wannan iskancin ba, yaushe wannan miskilancin nashi zai Bari ya kula wasu, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya "koya yake k'arewa da abokan aikinsa oho? "Nifa ina ganin an canza shi a Ameka, Inba haka ba taya yaro zai'ki son aure? "daka maganan aure sai yabar gida tun jiya, " na taba ji ance a Ameka suna canza ma mutum halitta koso kwashe jinin mutum susa Mai wani, Anya basu ma Najeebu haka ba kuwa?

Ba mum ba harta Dad saida maganan Granny ya basu dariya, "su Zarah da surutun Granny ya ishesu suma suka fito, gaida iyayen nasu sukayi "sannan zarah tace Granny Wlh kin hana mutane bacci,.

Granny tace "aikya fad'i haka, kina zaune a gida hankali kwance babu maganan aure, "wai kai audullahi baka ganin girman yaran nan ne, da suke gabanka?

Dad shuru yayi domin yasan abun Granny harda tsufa, koda yake tsufan ne ma, sai anyi hakuri, kwata kwata kwaya nawa Yaran suke? " yaushe suka taso da Granny zata Fara maganan Ayi musu aure.....

Maganan Granny ne ya dawo da Dad daka duniyar tunanin daya fad'a "inda take cema ibtisam ya hannun?

Ibtisam tace Alhmdlh da sauk'i, "sai dai har yanzu ina jin zafi Sosai "Mum tace sannu yarinyata zai daina a hankali Kinji? Allah ya k'ara sauk'i my dear

Ibtisam ta amsa da Ameen mum, "shima Dad ya mata Allah k'ara sauk'i.

Granny tace ni yunwa nakeji wlh, "shi miskili zai dawo ya tarar dani, "ke Zarah jeki kira yaran da nazo dasu..... Fitowan Najeeb yasa Granny sakan ba'ki "lokaci d'aya kuma tace yaushe ka dawo?

Najeeb daba jin abunda tace yayi ba ya banka Mata harara, tare da gaida iyayenshi cikin harshen Hausa Wanda bai kware ba, "Ina kwanan ku ya furta a gajarce tare da nufa dinning dan yayi breakfast.

Granny tace miskili koda idonka zai fad'o k'asa harshen harara sai kayi aure ja'iri, ke Zarah jeki kira matan nan ya zaba a ciki "Zarah ta amsa da toh tare da tafiya kiransu

Shiko Najeeb abinci ya fara ci, " Ibtisam dake tsaye ta kalleshi cikin ranta tace mugu azzalumi, wlh abunda kamin saina rama, Koba yanzu ba "shi Najeeb bai masan tana wajan ba dan bata su yake ba, so yake ya koma America danya gaji da wannan tsohuwar Sosai take takura mishi.

Granny nufanshi tayi tana fad'in ja'iri dama ka iya Hausa? "harda wani Ina kwanan ku. "toh Bari kaji Nasan kana jina Wlh ka zabi d'aya cikin matan dana kawo, "koka auresu duka.

Najeeb ko kallonta baiyi ba "ji yayi kaman ya bugeta dan haushi take bashi, shi yanzu a duniya ya yarda ta gama raina mishi wayau, "Toh Inba haka ba taya zata kawo mishi wa Innan Buran tace ya aura, ko Dad d'inshi da yake tsoho balarabiya ya aura, balle shi yaro dashi, wanda yasha nonon balarabiya saita kwaso mishi wa Innan masu Kama da Buran, munana y'an kauye kai wannan tsohuwar ta gama dani, amma zan koya Mata hankali wlh

Granny tace baka jina ne?

Tsaki yaja tare da banka Mata harara, cikin harshen turanci yace "Wlh Granny ki kama kanki da tsufanki tun Kafin inyi miki babu dad'i.

Dad yace kana da hankali kuwa Najeeb? Cikin harshen turanci yake Mai maganan, "yace Uwar tawa kake fad'ama haka?

Yace Dad nifa gaskiya na gaji da halin wannan tsohuwar haba, koku bakwamin abunda takemin haba, gaskiya na gaji, tana gab da kaini bango Wlh, ka Mata warning ta fita harka na, ko a kanta nake da zata takura min? Ta tashi ta kwaso Mata wai in zaba in Aura for god sake ance mata Ina bukata ne, ko me? Ya k'arasa maganan cikin zafin rai

Granny daba jin abunda suke fad'a tayi ba, "tace wai Mai kuke fad'a ne haka? Ku fad'amin inji.

Najeeb tsaki yaja tare da ture plate din dake gabanshi na chips din da yakeci tare da tashi yana k'okarin barin wajan

Cikin fushi Dad yace koma ka zauna, mutumin banza,"zama yayi rai a bace tare da tamke fuska

Granny tace ikon Allah, yau naga dan banzan yaro? Wai Mai yake nufi ne Toh haka?

Zarah ce ta fito,"matan na bayanta duk sun sha kwalliya da ba'kin kwalli, da Jan baki ja sai wani fari suke dan sun hango Najeeb din "ibtisam bata san lokacin data saki dariya ba, da sauri tasa hannu ta toshe bakinta, dan bata san dariyan zai fito ba.

Najeeb kam wani shegen kallo ya watsa ma ibtisam Mai nuna da zan hukunta ki, har yayi k'asa da kanshi ya d'ago da sauri ya kalleta Wanda yaga hannunta an d'aure alaman tayi karaya ko gocewan k'ashi , "har ya bud'e baki zaiyi magana idonshi na kanta lokaci d'aya kuma yayi shuru tare da kawar da kanshi daka kanta.

Granny tace yauwa y'an mata an fito? "Sannunku Sannunku "gaida su Granny y'an matan sukayi.

Dad kam da ranshi ke ce da Najeeb akan abunda yayi ma Granny, lokaci d'aya ya "d'aga kanshi ya kalli y'an matan, da sauri ya zare ido cikin mamakin badai su bane Granny ta Kawo ma Najeeb ba, Tashin hankali.

Granny ta kalli audullahi tace gasu nan saika fad'a mishi ya zaba d'aya.

Dad kam mamaki abun ya bashi, taya Granny zata kawo ma Najeeb wa Innan matan tace ya zaba d'aya daka cikin su... "koda yake may be Najeeb din akwai wacce yake so, domin shi so babu ruwanshi abincin wani guban wani

Kallon Najeeb yayi da fuska ke tamke kaman ba'kin kumurci, "yace Najeeb ga mata nan ka zabi d'aya.

Najeeb da sauri ya kalli dad din nashi, sannan yace "Dad babu wacce tamin a cikinsu, Dad taya kaima zaka biye mata? Gaskiya n.... "Dad ya d'aga mishi hannu alaman ya isa haka

Dad ya kalli Granny yace "mama yace babu wacce tayi mishi, "Granny ta saki tsaki tare da fad'in sauran matan su koma mai Yaron ta tsaya wacce Granny ta kira da Hanne, "Granny Jan hannun zarah tayi ta matsa kusa da Najeeb tana fad'in Zarah Bari inyi mishi magana ki dinga fad'a Mai Kinji? Inya fad'a nima saiki fad'amin mai yace

Ibtisam kam babu abunda take ro'ka sai "Allah yasa Granny tace dole saiya auri matan, tare dayin dariya k'asa k'asa ganin yanda Najeeb din ya tamke fuska rai bace, "tace ai yanzu ka Fara gani, "mara mutunci, mugu, wanda bashi da tausayi

Granny ta taba kafad'an Najeeb cikin sigar rarrashi ta Fara magana kaman haka "Haba Najeebu na Mai Sunan masoyi na, in wa incan basu maka ba, ina son kayi hakuri ka d'aure ka auri wannan Hanne kodan yaranta, mijinta ya rasu ya barta dashi, wlh Abun tausayi, gashi bata da uwa wajan matan babanta take ance tana musguna mata Sosai, ita da wannan marayan yaro abun tausayi, "Najeebu ka taimaka ka aureta ita, da nace duka hud'un zaka aura amma yanzu ka auri wannan kaji dan jika na.

Najeeb daba jinta yake ba, sai kallonta yake, "amma ya Lura tana mishi maganan cikin sigar rarrashi ne

"kallon zarah tayi tace fad'a mishi abunda nace Kinji.

Zarah fara fad'ama Najeeb abunda Granny tace tayi, "lokaci d'aya ya d'aga Kai ya kalli matar da Granny take cewa ya aura yayi," fuskanta tasha kwalli tayi d'ige d'ige gata kana kallonta Kaga tsohuwa Hhhhh Allah sarki ba tsufa bane wahala ce kawai Najeeb, lokaci d'aya idonshi ya sauka akan yaron wanda akace ya zama babanshi, yaron ba'ki gashi gashi duk ya fige ya kanjame kaman Mai cuta, daka gani dai yaron bashi da wani jini Sosai yanda najeeb ya Lura, ansa mishi irin rigan Fulani duk ta kod'e tayi datti, ko wando babu a jikin yaron

Granny tace Zarah tambayeshi ya amince?

Zarah ta fad'ama Najeeb abunda Granny tace "kiran Dad akayi a waya yabar falon "Bayan Zarah ta fad'ama Najeeb abunda Granny tace

Tsaki yaja tare da tashi yana fad'in kice Mata ban amince ba, ai Tana da yara ta aura musu ita yana fad'in haka ya fita fuuuu "Mum na kiranshi amma bai tsaya ba......





*Gskya naji dad'in yanda kukai min sharhi jiya, one luv kuci gaba da yanda kukayi jiya, nima insha Allah zan dinga kokarin yi muku posting kullum koda ba yawa*







~MARYAM OBAM~


*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE 10*






Granny ta kalli zarah tace "Mai yace fad'amin.

Zarah shuru tayi "Tana tunanin Mai zata cema Granny, "domin bazata iya fad'a mata abunda Najeeb d'in yace ba, dan tasan rashin kunya ne, bai kamata ta fad'a mata ba.

Granny tace "ina magana kinyi shuru, "gayamin abunda dan banzan yace, "Nasan zagi na yayi koh?

Da sauri Zarah tace a'a Granny, "cewa yayi shi bata mishi ba, baya Sonta.

Shuru Granny tayi na wani lokaci, "sannan ta sauke ajiyan zuciya tare da kallon hanne tace maza ki koma ciki, "Hanne ta amsa da toh tare da juyawa tayi ciki, "Granny wani irin murmushi tayi tare da fad'in zanyi maganin d'an banza Wlh, zai gane shayi ruwa ne.

Najeeb kam gaba d'aya ranshi a bace yake "bukka ya nufa ya zauna yana jin ranshi na mishi zafi tare da fad'in "wai ita wannan tsohuwar Ina ruwanta da rayuwa na? And naga Dad kaman yana biye mata, "kafad'a ya d'aga tare da fad'in mum dinshi ce, but ni ba uwata bace, Dad zai iyayin abunda tace but banda ni, "wata iska ya furzar mai zafi tare da fad'in ta rasa wanda zata bani sai wa innan kazaman matan munana, y'an kauye, harda wani yaro mummuna duk jikinshi a bushe, tsaki yaja tare da fad'in kamata yayi in d'auki wannan tsohuwar in kaita asibitin mahaukata, ina tunanin ta Fara tabuwa, Inba haka ba " how can she think of getting me married with that old lady's," and she asking me to choose one among them" nace bana so tana cewa in auri Mai yaro, "murmushi ya saki alaman takaici da mamaki, ko an gaya Mata ni aure yana gabana? " yaushe zan iya ajiye mata a matsayin matata kullum ta dinga takura min, "women are only for fun..... D'an shuru yayi yana nazari, lokaci d'aya ya tabe baki shi ba namiji bane mai son yara ba, har ake k'okarin aura mishi Mai yaro, shi koda an matsa Mai dole yayi aure ai budurwa zai aura, yaushe zai aura wacce ta taba yin aure, "Dan yasan for sure saita dinga tuna mijinta na baya, "and he can't take it dan yana da kishi, ajiyan zuciya ya sauke tare da fad'in " ya kamata ma kawai in koma inbar k'asar tun Kafin wannan mental tsohuwar ta sani gaba ta cinye d'anye, mata kaman mayya sai nacin tsiya..... Muryan Zarah yaji tana fad'in bros

D'agowa yayi, ya watsa mata sex eye d'inshi, tare da fad'in what?

Tace Bros ina son magana dakai "Plz kaban dama ka saurara kaji, " Zan taimaka maka wajan wannan matsalan na granny

Tsaki yayi tare da fad'in, "don't worry Sis ban d'auki wannan a matsayin damuwa ba, aure ne bazan yiba, sai dai ta mutu, "and inma tayi mistake tasa aka aura min ita saina kashe yarinyar nima a kashe ni, Waye yayi Asara?

Uhm Zarah tace "tare da fad'in amma bros inda zaka ji shawarata da komai yazo maka da sauk'i, ba tare da d'aga hankali ba.

Yace Zarah just leave me for a while, "ban son damuwa.

Tashi tayi tace "OK but in kana bukatan taimako am ready for help, Tana fad'in haka tayi gaba abunta

najeeb yana nan zaune lokaci d'aya ya d'auki wayarshi ya fara dannawa " wani irin murmushi ya saki lokaci d'aya tare da fad'in yes, tashi yayi ya shiga cikin gidan "inda yaga Granny a falo .

Ganin Najeeb ya shigo yasa tace ja'iri, ka Fara kallon kanka a matsayin ango Wlh

Baiko kalleta ba ya wuce part d'inshi, toilet ya fad'a yayi wanka tare dasa kaya, ya shirya cikin k'ananan kaya, "koda ya fito ya tarar da harda Dad d'inshi a falon da Mum da Granny sai su Zarah.

Har zai wuce Dad "yace zonan,

Zuwa tsayawa Najeeb yayi ba tare da yace komai ba

Mum tace bazaka zo ka zauna ba?

Zama yaje yayi rai a bace, danshi baya son su k'ara mishi wani maganan aure yanzu

Dad yace mun riga mun yanke ko ince mama ta yanke zaka auri wannan yarinyar K...

Da sauri Najeeb yace Dad bazan aureta ba, inada wacce nake so in Aura, so ita zan aura, And Dad akan wani dalili za'a ce in auri wancan Y'ar kauyen? For god sake ko Kai bazaka aureta ba sai ni

Dad kallon d'an nashi yake cikin mamaki, Amma da yake yana son d'an nashi sai bai d'auki maganan da yake fad'a mishi da zafi ba, "yace toh wacece kake so?

Najeeb yace ita zanje in d'auko tazo Nigeria tun jiya,

Dad yace Toh hakan yayi, ka kawo ta sai Mama ta ganta " Dad kallon Granny yayi tare da fad'in mama yace akwai wacce yake so, yanzu haka ita zaije ya d'auko ki ganta.

Granny ta washe baki cikin jin dad'i tare da fad'in ko shifa, "Aida ya fad'a tun tuni da banje yola ba, Allah yasa Fulani ce itama.

Itbisam kam haushi taji da Granny bata dage akan saiya auri Hanne ba, taso a aura mishi ita,taga yanda zaiyi

Suna nan zaune, baifi awa d'aya da fitan Najeeb ba sai gashi ya dawo shida wata baturiya.

Da sauri Granny ta tashi ta k'are Mata kallo, yarinyar tasa wata doguwar riga wacce ta tsaya mata dai dai Giwa, ga kanta da Attachment brown, Granny salati ta Fara tare da fad'in amma Najeebu ko dan bantan uba, badai wannan zaka aura ba?

Najeeb harara ya sakar ma Granny danya Lura yanda take maganan kaman wannan dinma bata mata ba

Yarinyar idonta nakan Granny da taji tana Yaren daba ji take ba, "Granny tace Dallah dena kallona, da ido kaman na mujiya

Najeeb ya fara nuna ma yarinyar Dad yace "Gina ga Dad d'ina cikin harshen turanci yake mata magana, Hannu ta mi'ka ma Dad suka gaisa, "Granny salati ta saki lokaci d'aya kuma tasa kuka, tana fad'in audullahi gaisawa da wacce ba muharramanka ba, a gabana a gaban iyalinka.

Mum tace mama hakan ba komai bane ai K...... "Dallah Rufamin baki, mara kishin kai Granny ta fad'ama Mum haka, "yanzu mijinki ya gaisa da mace amma kice ba wani abu bane, oh ni wannan zamani duniya ta lalace,

Dad kam shuru yayi ya kasa magana, "NAJEEB in banda hararan Granny babu abunda yake, Gina kam ita mamaki take tare dason jin abunda tsohuwar take fad'i, amma babu dama

Su Zarah da ibtisam kam dariya suke k'asa k'asa

Najeeb yace Dad itace Zan Aura, kallon zarah yayi yace "ki fad'ama wannan granny d'in ga Matar da zan aura nan

Zarah ta fad'ama granny abunda Najeeb yace,

Granny kallon Alh Abdullahi tayi tace, yau ka nunamin ban isa ba, ka kuma nunamin irin tarbiyan da kayi ma y'ay'anka, Indai wannan shine boko tir da wannan karatun, baka da iko da y'ay'anka, sai kuma ta saki kuka

Cikin tashin hankali Dad yaje gabanta yana bata hakuri tare da fad'in "mama nimai biyayya ne a duk abunda kika ce, wlh komai kika yanke shi za'ayi indai bai sabama Shari'a ba, "Dan Allah kibar wannan kukan, kiyi hakuri

Cikin kuka tace Indai na isa muje yola a nema ma Najeebu auran Hanne cikin satin nan, dan ban yarda ya auri wannan yarinyar ba ta nuna Gina dake kallon ikon Allah

Dad yace hakan za'ayi mama insha Allah jibi zamu, sai a d'aura auren.

Mum najin haka ta tashi tabar falon rai a bace, "Wlh bazata yarda a d'aura ma d'anta wannan matan ba, taya za'a mishi auren da baya so, komai zai faru sai dai ya faru Wlh

Dad kallon Najeeb yayi yace yaje ya maida yarinyar ya dawo yana son ganinshi yanzu yanzu, "yanda Dad yama Najeeb magana babu wasa yasa Najeeb yasha jinin jikinshi duk yanda akayi kukan da wannan tsohuwar takeyi akwai abunda ta k'ulla, "Dan haka ya kalli Zarah yace Sis zo muje in ganki

Koda suka fita yasa Gina a mota yace ta jirashi, magana yake da Zarah akan ta fad'a mishi abunda Granny tace

Zarah bata boye mishi komai ba ta fad'a mishi

Ran Najeeb ya baci Sosai lallai kam zaiba Dad d'inshi mamaki indai dagaske yake zai aura mishi wannan y'ar kauyen....

Zarah ce ta Katseshi tare da fad'in Bros inaga in baka son wannan auren why not kace ma Granny kana son ibtisam zata sa a fasa kuma Kun dace kai d....... "Najeeb ya dakatar da Zarah tare da fad'in keep quiet

Kina da hankali kuwa? Ni zance zan aura wannan yarinyar? Kin mafi rainani akan Granny, "let me tell you" Wlh da in auri wannan ibtisam din gwara na auri wacce Granny ta bani, ya k'arasa maganan cikin zafin rai

Zarah ganin haka yasa taja bakinta ta tsuke, " Dan tasan tunda yace hakan, Toh dagaske yake, cikin ranta tace itama ibtisam din inda tasan nace maka haka ba k'aramin fushi zatayi dani ba, "Toh wai Mai yasa suke ma junansu irin wannan kiyayyan ne haka? Sai kace ba y'an uwa ba, haba abun yayi yawa

Najeeb gaba yayi tare da shiga mota, direct hotel din da Gina ta sauka ya kaita, tare suka shiga dan yana bukatar hutu, koda suka shiga, "Gina ta Fara shafashi tare da fad'in naajit Mai wannan matar take cewa? Naga harda kuka takeyi?

Najeeb yaja tsaki tare da fad'in plz stop asking me dis question. "tare da tashi ya d'auko wata kwalba ta alcohol yasha amma ba Sosai ba,, Yadai kusa shan rabin kwalban

Ganin haka yasa ta kame bakinta ta tsuke, dan tasan Waye Najeeb, abu kad'an yake bata mishi rai, "wani irin tafiyan tsutsa take Mai da hannunta, Tana k'okarin Kai hannunta kan banana d'inshi ya tashi tare da tureta ya fita daka d'akin "tunawa da yayi Dad d'inshi yace ya maida yarinyar ya dawo yana son ganinshi, dan haka gida ya nufa direct

Koda ya shiga cikin gidan Granny da Dad kawai ya gani a falo, zama yayi ta kujeran dake kallon Dad d'in

Dad yace mun yanke zaka aura yarinyar da mama ta zaba maka, saika shirya jibi zamu yola acan za'a d'aura auren

Najeeb ba tare da shakka ba ko kunya, yace Dad Wlh bazan aureta ba, gwara kar kayi gigin cewa zaka aura min ita, so is better kabar wannan maganan, ko ince kabar biyema wannan tsohuwar

Dad yace ni kake fad'ama haka Najeeb?

Najeeb yace gaskiya na fad'a maka, and banga wani abu dana fad'a ba, so baka da right da zaka sani abunda banyi niya ba, Nasan y'ancin kaina..... Tas Tas Dad ya sakar mishi Mari har biyu tare da fad'in ni? Najeeb ni kake fad'ama haka?

Najeeb cikin zafin rai ya tashi yana fad'in Dad do whatever you want amma bazan auri wacce kuke so in Aura ba, ko ince wacce mamanka take son in aura ba.... Dad na k'okarin k'ara maranshi Mum data fito tazo da sauri ta ri'ke hannun Dad Tana fad'in ka kyaleshi

Najeeb part d'inshi ya nufa inda ya fara had'a kayanshi

Mum cikin kuka take fad'in ga irinta nan, gashi nan, tun yaro na k'arami ka daukeshi ka kaishi wata k'asa karatun boko, baka taba tunanin yayi karatun addini ba, wlh yau komai Najeeb yayi laifinka ne tana fad'in haka tabar falon

Please Login or Register in order to submit comment