Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bi ba Kai tsaye inda ake siyar da alcohol ya nufa inda ya siya wajan kwalba goma ya nufi gida

Koda ya k'arasa key yaba driver tare da fad'in ya koma hspt ya jira mum

D'akinshi ya shiga ranshi a bace har wani duhu duhu yake gani, bud'e bottle din alcohol d'in yayi yana k'okarin sawa a baki ya tuna da maganan ibtisam din I hate you duk wasu manya laifi ka had'a, you are drinker womanizer....  Ido ya lumshe tare da kafa kwalban a baki ya fara sha yana surutai yana fad'in even I, I hate you shan alcohol d'inshi yake kaman hauka yana surutai tare da jefar da bottle din ya fashe a d'akin a kalla yasha wajan bottle hud'u kuma duk ya fashe bottle din a d'akin lokaci d'aya ya fad'a kan bottle din a k'asa.......


Mum a asibti ta kwana ita da ibtisam wacce take a kwance har yanzu bata farka ba

Ibtisam sai wajan asuba ta farka tare da bud'e idonta Wanda yake a kumbure ta Fara kallon d'akin, ganinta a asibti ga Mum na sallah ta gane an kawo ta hospital ne, lokaci d'aya abunda ya faru ya fara dawo mata wani irin Abu taji yazo mata tare da fatan Allah yasa cikin ya zube tunda tasha magani da yawa.....

Jin muryan mum tayi tana fad'in kin tashi ne??

Ibtisam cikin dashewan murya tace eh

Ibtisam tashi tayi amma jikinta babu kwari, Mum tace Bari in taimaka miki kar abun drip din ya goce... Ko da yake bari in kira su domin naga ya kusa k'arewa ma, fita Mum tayi ibtisam taba cikinta tayi wanda ya dan Fara tashi saboda yawan cin abincin da takeyi sosai, jin alaman har yanzu yana nan yasa ta saki wani irin kuka tare da fad'in duk wannan wahalan da nasha?? Wannan wani irin jarabban ciki ne haka?? Wlh in bai fita ta sauk'i ba zanje a wanke shi ta yanda zai fita da hujja

Shigowan mum da nurse yasa tayi saurin goge hawayen idonta, nan nurse ta cire mata drip din Bayan mum ta tambaya ko akwai wanda za'a k'ara mata??

Nurse din tace a'a sai dai in dr yazo

Ibtisam toilet ta shiga inda tayi alwala tare dayin sallah, Bayan ta idar ta koma kan gadon ta kwanta wanda Tana tafiyan ne dakyar

Mum Tana zaune har Dr yazo ya duba ibtisam

Dr Ya kalli ibtisam yace ya jikin??

Tace da sau'ki

Yace ibtisam Mai yasa kika sha magani da yawa haka?? Kina son cikin ya zuba NE??

Ibtisam shuru tayi ba tare da tace komai ba, wanda ta tabbata Mum tasan komai wani irin kunya taji Sosai

Dr yace ina son in baki shawara Idan kika k'ara yunkurin yin hakan zaki iya samun matsala domin mahaifarki bata da kwari, so you have to be very careful Indai kina son rayuwarki

Nan Dr yace zata zauna na kwana biyu a nan, inda Mum tace bazasu iya tafiya gida ba

Dr yace zasu iya but tana bukatar hutu sosai, koda Kun koma Karta dinga aikin komai

Nan Mum tace shikenan inda Dr ya sallamesu suka koma Gida, koda suka isa Gida mum saida ta had'ama ibtisam ruwan dumi a cikin bath sannan tace taje tayi wanka

Bayan ibtisam ta shiga toilet mum direct d'akin NAJEEB ta shiga inda ta ganshi a k'asa ga jini dake zuba a jikinshi wani irin ihu ta saki mai firgitarwa da sauri ta nufeshi ta juyo dashi domin ta kife ya fad'i cikin mayen giyar da yasha inda ya fad'a akan kwalba Wanda ya sokeshi a cikin sa, Bayan ta juyo dashi ta Fara kuka ganin kwalba da sauri ta d'auki wayarta tana kuka lokaci d'aya ta kira Dr inda ta fad'a mishi yazo da kayan aiki kwalba ya sokar mata da a ciki

Ciki ta koma inda sai a sannan ta lura dako numfashi bayayi..... Wani irin ihu ta kurma mai ban tsoro wanda yasa ibtisam dake d'aki itama ta fito da sauri ta nufi gefen da taji ihun da yake a bud'e mum tabar kofar ibtisam itama shigowa tayi ganin halin da yake ciki yasa itama ta tsorata ganin jini a daskare Wanda da duka alama ya dad'e shine ya fara bushewa, Wanda ga wani shima yana zuba lokaci d'aya taji tana jin jiri ita dafa bangon d'akin tayi ta sulale tayi k'asa itama........













Read and leave it, dnt share to anyone......*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*

*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*

3138831065 Firstbank Maryam Alhassan

*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*

*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*







Mum ganin haka yasa ta kuma rud'ewa tare da salati, cikin tashin hankali ta nufeta, Shigowan dad ne yasa ya tsaya yana kallon ikon Allah, gaba d'aya kasa magana yayi sai kallo da yake binsu dashi ga NAJEEB kwance jini na zuba ga ibtisam itama kwance, lokaci d'aya yayi karfin halin ciro wayarshi ya fara kiran Dr.....

Jin sallama a falon yasa Dad fita, Dr ne yazo inda Dad ya mishi Iso har cikin d'akin najeeb din, inda Dr yaga kwalban daya sokeshi da kuma irin ciwon da yaji, nan take dr yace dole sai anje hspt, Mum fita tayi ta kira masu aikinta inda aka Kama ibtisam su Dad kuma suka Kama najeeb Wanda gaba d'aya basu San a wani hali yake ba

Kai tsaye hspt aka nufa dasu, inda duka aikai emergency dasu, Dr har uku suka shiga tare da nurse domin ceto rayuwarsu

Dad da Mum kam gaba d'aya sunyi zugum, musamman Dad yau da yaga abunda ya firgita shi, Domin kwalban giyan daya gani a dakin najeeb din, wanda bai shaba da kuma wanda ya fasa yaji mai wannan raunin, yau kawai for the first time yaji ya aikata babban kuskure na tura d'ansa waje karatu, ba tare da mai kula dashi ba, yau ne rana ta farko da Dad yaji ibtisam bata dace da d'ansa ba, yau ne rana ta farko yayi dana sani...... Wani irin fargaba yakeyi tare da tsoran yanzu idan dan nasa ya mutu Mai zaice ma Allah wanda ya tabbata giya yasha har yayi yawa yasa ya fad'a cikin wannan halin, Innalillahi'wa inna ilaihirajiun. Lallai ya cuci kansa tare da d'ansa gaba d'aya bai bashi ilimin addini ba, baima taba Ankara da kula da irin yanda yake gudanar da abunda addini yace ba, shidai d'ansa kawai yayi karatun boko, domin shine yake ganin hanyar data dace bana addini ba......

Mum ce ta katse ma Dad tunani cikin kuka tare da fad'in yanzu ka gani koh??  Ka tabbatar ma kanka koh??? Ka gani da idonka abunda d'anka yake aikatawa, wanda son d'anka da kuma rashin yarda da abun da wani ya fad'a maka saina wanda d'anka ya fad'a gashi yanzu ka gani da idonka, yanzu idan ya mutu Mai zaice ma Allah??  Kwata kwata babu ruwanka da irin rayuwar da d'anka yakeyi Kai komai ya fad'a a wajanka shine dai dai, wlh ka cuceni yanzu inya mutu shikenan ya tafi wanda giya ta zama ajalinsa tunda ita yasha ya bugu ya kasa gane mai ke gabansa Wlh......  Sai kuma tayi shuru can tace ba Kai d'aya bane Mai laifi harda ni Nima uwa ce, ya kamata in kula da irin tarbiyarsa duk da ka nuna akan NAJEEB kai keda power sosai......

Dad jin yanda take magana ga mutane na kallonsu yasa ya janyota tare da fad'in dan Allah kiyi shuru muna asibti ne.....

Mum kuka take Sosai amma gaba d'aya tasan an gama da najeeb, which tasan sune da laifi, wanda dad d'inshi yake ganin kaman gata yake mishi bai San cutanshi yake ba, tunda bai barshi yasan addini ba, gashi yanzu ya girma Wanda d'aukan karatu zai mishi wuya bama lallai yayi ba, domin sun riga Sun bata Abu tun Farko gyaruwanshi zaiyi wuya inma ya gyarun

Koda aka shigar da najeeb da ibtisam nan dr daya yayi kan ibtisam wacce take a sume domin jinin data gani yasa ta jiri tare da tsoro wanda ya sata ta sume, ga jini daya Fara zubar mata a kasanta.......

Shi kam NAJEEB aiki za'ayi mishi domin kwalban Bayan ya huda shi akwai wanda ya karye ya shigan mai ciki, wanda yasa dole sai anyi mishi aiki domin a ciro thank god baima taba mishi hanji ba.....

Dr ne ya fita inda su Dad suka tashi suna tambaya akan ya ake ciki??

Dr yace dole sai anyi mishi aiki, domin kwalban ya shigar Mai ciki, nan yaba Dad takarda yayi signing

Inda Dr ya koma domin Ayi MA NAJEEB din aiki

Gaba d'aya su Mum sun shiga cikin tashin hankali tare da damuwa Sosai, wayar Dad NE yayi k'ara d'auka yayi yaga Abba ne

Bayan yasa a kunne Abba yace gamu Munzo ance wai kuna asibiti

Dad yace eh, kusa driver ya kawo ku, kace mi....  Bari in kira driver din ka shiga ka ajiye motarka a ciki saiya d'auko ku ata gida

Su Abba basu dad'e ba sai gasu sun zo shida Granny cikin tashin hankali

Granny ta Fara magana maiya faru Waye baida lafiya??

Dad yace najeeb da Ibtisam

Granny salati ta saki tare da fad'in ciwo lokaci d'aya haka??  Maiya samesu ni aminatu

Jin ihun ibtisam yasa sukai shuru cikin tsoran maike faruwa da ita.....

Gaba d'aya sunyi jigum..

Ibtisam farkawa tayi tana jin wani irin mugun ciwon ciki wanda ba komai bane ya sata hakan sai miscarriage din da tayi wanda domin abunda zata haifa gashi ya fito a dunkule kaman kwado amma bashi da girma Sosai, wanda hakan ya nuna alaman cikin mace gareta gashi ya zube, sauran jinin dake cikinta shine yasa ta murdawan ciki Sosai take wannan ihun, wanda yasa dole za suyi Mata wankin ciki

Granny dake waje bata san abunda ke faruwa ba, babu abunda take sai kuka domin a duniya bata son abunda zai taba lafiyar ibtisam ita da NAJEEB, domin Tana matukar sonsu, gashi yanzu tana jin ihun ibtisam din Wanda gaba d'aya yasa ta shiga cikin rud'ani

Jin ibtisam din tayi shuru yasa Granny K'ara tsora

Dr ne ya fito inda yace suje office d'inshi kai tsaye dukansu suka bishi

Inda Dr yace anyi nasara anyi ma najeeb aiki, an cire mishi kwalban, sai dai ina Mai baku shawara akan ku tabbata ya daina shan alcohol domin zai iya taba mishi kidney, dan yana sha da yawa wanda hakan yasa har ya fara taba Mai amma ba Sosai ba, idan yaci gaba dasha am sorry to say Indai harya taba Mai Toh mutuwa ne..... Sannan ya zubar da jini da yawa mun K'ara Mai

Salati Granny tasa tana kuka

Dr yaci gaba da fad'in ita kuma macen razanan da tayi yasa cikinta ya fita......

Granny kuka take Sosai, cikin data kwallafa rai dashi shine ya zube??  Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, yanzu jikan nata da take burin yazo duniya shine ya tafi??  Kuka take Sosai tare da fad'in Allah yasa hakan shine alkhairi

Dr yace ita macen yanzu babu wani matsala Domin anyi Mata wankin ciki, shine dai dai bai Farfad'o ba har yanzu

But karku damu any moment from now zai iya tashi

Nan su Dad suka fita koda suka fita inda su ibtisam d'in suke suka nufa wanda take kwance tana hutawa

Najeeb kuma na kwance har yanzu bai farka ba

Ibtisam gaba d'aya hawaye takeyi domin tsintar kanta tayi da ba'kin cikin zubewar cikinta, kuka take Sosai Wanda yasa NAJEEB farkawa tare da bud'e ido a hankali ya ganshi a kwance a asibiti da sauri yayi yunkurin tashi amma saiya kasa tare da ri'ke cikinshi, lokaci d'aya ya koma gaba d'aya Abun daya faru ya fara dawo Mai..... Da sauri ya tashi tare da tsige drip din dake hannunshi Wanda dai dai lokacin su Mum suka shigo

Jini ke zuba a hannunsa da sauri Mum tace najeeb......

Najeeb kam k'okarin tashi yake....

Ibtisam itama tashi tayi ganin jini yana zuba a hannunshi yasa ta nufeshi da gudu tare da cire hulan dake kanta tana k'okarin tasa Mai a hannu ya tureta tare da fad'in don't you dare touch me.......

Tsayawa tayi sororo tana kallonsa

Najeeb kam fita yake son yi amma Mum ta rik'eshi Dad ya fita kiran Dr sai ga Dr da Dad sunzo tare inda ya kamo hannun najeeb din da yake zubar da jini aka samai auduga aka matse

Dr yace najeeb bai kamata ka tashi ba you need to rest.....

Najeeb yace no Dr am OK I have to go, bana son zama a hspt Ina bukatar tafiya gida

Dr yace plz najeeb ka koma ka kwant....

Najeeb yace I said no Dr zan tafi America zan kula dakai na just allow me to go....

Dr babu yanda ya iya yace OK tare da bashi magani inda itama ibtisam aka bata

Kai tsaye gida suka nufa inda najeeb yake ganin dishi dishi Dad ya taimaka aka kaishi d'akinshi inda ya kwanta

Ibtisam kam gaba d'aya jikinta taji ya mutu gaba d'aya zubewar cikinta yasa taji komai baya mata dad'i, bata taba sanin cewa Ashe tana son cikin ba saida akace ya fita kuka ta saki mai cin rai......

Tana cikin kukan mum ta shigo ta ganta cikin wannan halin inda Mum tace tayi hakuri ta tashi taje tayi wanka, sannan ki tabbata kin gasa jikinki domin kina k'aramin jego ne..... Jin muryan Granny sukayi tana fad'in tashi muje inyi miki

Granny ta kalli Mum tace kisa a had'o Mata tea tasha

Ibtisam tashi tayi Granny ta Mata wanka, gaba d'aya ibtisam bata jin dad'in komai, amma da tayi wankan sai taji jikinta yayi mata karfi

Najeeb kam gaba d'aya ya kasa bacci gaba d'aya abunda ibtisam ta aikata yasa gaba d'aya yaji ko ganinta baya son yi, wanda ya tabbatar tsanar da take mishi yayi yawa, tunda har zata iya k'okarin cire cikinshi dake jikinta...... Shida kanshi yasan yayi hakuri yayi accepting d'inta but amma ita ta kasa ido ya k'ara lumshewa yana jin zafin abunda ta aikata, ga zafin aikin da aka mishi domin alluran kashe zafin da aka mishi ya daina aiki, gaba d'aya zafi wajan yake masa Sosai.....

Shigowan mum yasa ya kalli bakin kofar domin yaga Waye, ganin Mum yasa ya kura mata ido harta k'araso inda yake, tace sannu ya kamata kayi wanka ko zaka ji karfin jikinka

Ido ya lumshe alaman baya son magana

Ganin haka Mum yasa tayi dan murmushi tare da fad'in idan kayi wanka zaka ji karfin jikinka, sannan kaci abinci kasha magani

A hankali yace Mum plz I need to be alone, just go out

Mum kallonshi tayi tace son zan fita but sai kaci abinci kasha magani

Yace Mum I told you to leave, bazan shaba just leave me alone plz

Mum ganin haka yasa ta tashi jiki a sanyaye ta fita ta barshi.

Gaba d'aya najeeb jin zuciyarshi yake yana tafarfasa lallai komai zaima ibtisam bai kamata tace zatai yunkurin zubar Mai da ciki ba, duk da yasan ya mata laifi Sosai, but why zatai yunkurin cire mishi jininshi daka jikinshi, ido ya lumshe cikin takaici gaba d'aya zafin da yakeji na aikin da aka mishi bai Kai ko rabin zafin da zuciyar shi take mishi ba, domin wani irin tafarfasa yake ji, lallai inta k'ara yunkurin aikata abunda ta aikata zai Mata abunda zatai mamaki

Dad ne da Abba da Granny sai Mum a falo, inda Mum take fad'a musu abunda najeeb ya aikata Bayan yasha giya inda ya saki ibtisam, sannan ya sadu da ita Bayan ya furta Mata Kalman saki cikin Maye

Granny salati ta saki sannan ta kalli Dad tace Wlh duk kaine ka lalata tarbiyan d'anka kaine kasa yake wannan Abun, ka kaishi k'asar da babu addini, k'asar masu jajayen fata, wanda su babu ruwansu da duk abunda wani ya aikata, wlh komai najeeb yayi kaine da laifi, kuma Wlh sai Allah ya tambayeka ka d'auka abunda Kama najeeb gata ne?? Wlh ba gata ka masa ba, domin ka bata mishi rayuwa ne gaba d'aya, ka cuci d'anka, Kai burinka yayi ilimin boko toh yayi Amma na addini bai dashi bana tunanin najeeb ko FATIHA zai iyayi, kai Innalillahi'wa inna ilaihirajiun, yanzu miye amfanin irin haka?? Allah yace ka sanni Kafin ka bauta min, na tabbata najeeb babu abunda ya sani game Da addini, inda ya sani bazai sha giya ba, ku dama masu kud'i daka Allah ya baku duniya saiku manta da komai Idan kuka haifi yara burinku ku kaisu boko islamiya ko oho, wlh wannan tsanar y'ay'anku kuke ba so bane kuke nuna musu, yanzu ko miye amfanin hakan oho.....

Najeeb dake d'aki yana jin maganan Granny domin da karfi take maganan dan haka ya tashi ya fito dakyar ya zauna a falon domin yana dan jin k'adan daka magananta, wanda wasu baya ganewa

Ganinshi ya fito yasa duka suka tsaya suna kallonshi

Granny tace saiku fad'a mana miye yanzu tsakaninshi da ibtisam din?? Ya auransu yake??

Abba yace a kira ibtisam din

Mum tashi tayi ta nufi d'akin da ibtisam din take inda ta sameta tana hawaye domin itama tana jiyo su, sai dai ta fad'a ma mum abunda najeeb yayi amma ta kasa fad'a mata ta kamashi da mace Wanda ta rasa dalilin kasa fad'in hakan.

Mum tace ibtisam wai ba zaki bar wannan kukan ba?? Maza ki tashi muje falo ana kira

Ibtisam tashi tayi tasa hijab tare dabin Mum suka fita

Tunda suka fito idon najeeb yake kanta, gaba d'aya fuskanta yayi fayau kaman wacce tayi kwana da kwanaki tana jinya, lokaci d'aya ya kauda idonshi daka kanta

Ibtisam itama tana kallonshi ta gefen ido, domin gaba d'aya jinin data gani yana zuba a jikinshi ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba, domin tayi mugun tsorata sosai Wanda ganin jinin ya saka mata jiri, for the first time taji tausayin NAJEEB a rayuwarta domin ganin blood na zuba a jikinsa, duk da shi yaja ma kansa da yasha alcohol ya fasa bottle din

Nan Abba ya kalli ibtisam tare da kiran sunanta inda ya fara tambayanta da harshen turanci, maiya faru ranan da najeeb ya sakeki sannan saki nawa yayi miki

Najeeb da sauri ya kalli ibtisam din, wacce ta fashe da kukan da bata san zai fito ba.

Abba yace ke bana son shashancin ki fad'a mana abunda ya faru.....

Ganin yanda abba ya d'aure alaman bada wasa yake ba, yasa ibtisam fara fad'a musu yanda abun ya faru duk da tana jin kunya amma haka ta daure ta fad'a

Najeeb wani irin zugi yakeji cikin ranshi

Abba yace maganan saki ya saku, domin kuwa domin kuwa ba'a wasa da saki, koda da wasa mutum ya furta Kalman saki ya saku, balle a cikin Maye, Abu d'aya ne shine za'ace babu saki Idan mutum yana Maye yayi amma fah sai dai in matse mutun akayi aka bashi shine babu saki, amma idan mutum ne yasha da kansa yayi saki to sakin ya saku, toh amma kaman yanda ta fad'a ya furta Kalman sakin ne sau biyu ya fad'i, kenan ya zama saki Biyu,

Sanda ya tashi kuma wani abu ya shiga tsakanin su, Toh daka k'okarin koda bai furta ya dawo da itaba aure ya dawo, tunda har wani abu ya shiga tsakanin su..... Wanda yanzu suna da igiya d'aya data rage musu a tsakaninsu

Abba kallon najeeb yayi tare da kiran sunanshi yace najeeb Ina son ka sani shan giya haramun ne, shan giya yana d'aya daka cikin manyan laifi, sannan duk Wanda yasha giyar duniya koda ya tuba ya daina bazai sha ta Aljanna ba, sannan kaga abunda ka aikata ma kanka kana k'okarin kashe kanka kasha giya ka fasa kwalban ka fad'a kan kwalban gashi saboda razanan da matarka tayi na ganin jinin dake fita a jikinka yasa tayi Bari.......

Najeeb da sauri ya tashi tare da fad'in what?? Ibtisam miscarriage?? How?? Hannunshi ya d'aura a kai alaman mamakin Kalman da aka fada mishi yake

Lokaci d'aya ya cire hannunshi a fuska wanda idonshi ya kad'e yayi ja, kallon ibtisam yayi tare da fad'in are you happy now?? Yes I know you are happy cikin da kike burin ki cire gashi ya fita....... Shuru yayi yana hura iska Mai zafi sannan ya yace ibtisam just for once kin taba tunanin irin yanda zanji Idan cikin nan ya fita?? I know babu furgicin da yasa cikin nan Ya zuba, da gangan kika zubar.....

Abba yace kaman ya najeeb Dr ya fad'i haka??

Najeeb ya kalli Abba tare da bashi Labarin maganin da tasha domin cikin ya fita wanda shine silan da yasa na dawo nasha alcohol domin in huce saboda raina ya baci sosai and only alcohol zansha inji sanyi....

Tas saukan Marin da abba yama ibtisam yasa NAJEEB yin shuru wanda NAJEEB yaji Marin kaman shi akama Dan irin sautin da Marin yayi......

Abba yace irin tarbiyan da muka koya miki kenan?? Ibtisam ashe baki da tausayi baki da imani?? Kisa?? Kisan kai kike kokarin yi?? Yau koda cikin shege kikayi bazan yarda ki zubar ba, domin ni musulmi ne Nayi imani da kaddara, balle cikin da kika samu ta hanyar sunna.....

Cikin kuka tace Abba naso in zubar da cikin daka jiya da abun ya faru Wlh nayi nadama, domin gaba d'aya idona ya rufe bana gane komai, Abba karka manta abunda kayi shine za'ama d'anka, tun daka irin yanda na samu cikin da irin halin najeeb Wanda yake aikata manyan laifi baya tuna Allah sai yasa gaba d'aya nake tsoran had'a zuri'a dashi, gudun kar Nima aima nawa Yaran, I knw I never love him, but whenever I try to accept him as my husband daka na tuna irin abunda yayi min sai in kasa, Abba nida kaina Nasan ban dace da najeeb ba, Abba karka manta ance ku zabama y'ay'anku iyaye na gari, najeeb baya tsoran Allah, gaba d'aya duk wasu manyan laifi da Allah ya hana shine yakeyi Bayan shan giya harda..... Kuka yaci karfinta tare da fad'in ba komai bane zan bud'e in fad'a amma ina son Ayi min adalci, NAJEEB baya so na Nima bana sonshi duka muna wani irin zama ne wanda gaba d'aya ban San amfanin zaman ba......

Abba yace Yimin shuru, badai ciki kike son ya fita ba?? Toh yanzu burinki ya cika saiki ji dad'i, sannan Wlh zama keda NAJEEB yanzu kika fara, domin wannan auren rai ne dashi Bamu da ikon rabashi har sai ya k'are......

Najeeb dake tsaye yace Abba zan nema mana mafita nida ita Wanda nake ganin shine ya dace, kaman yanda ta fad'a bata so na and Nima bana sonta, yeah is true babu amfanin zaman ni da ita..... Shuru yayi tare da kallon ibtisam dake kuka mai cin rai, yace I know nasha fada bazan
Saki matar dana aura ba, saboda inada kishi yau for the first time naji bana bukatar zama da ibtisam.........







Plz am sorry for late post







Read and leave it, dnt share to anyone*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*

*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*

3138831065 Firstbank Maryam Alhassan

*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*

*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA

Please Login or Register in order to submit comment