Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani karatu Mai zurfi yayi ba, shima Abdullahi abunda yasa yayi karatu Mai zurfi, uban gida ya samu lokacin Wanda ya d'auki nauyin karatun shi.

Mahaifin ibtisam ya amince tayi karatu inda ya kawo ma Granny, uzuri da ibtisam bata da wani tsayayye, Granny Tana ta fad'a AI dole kowa ya'ki zuwa tunda bata kula samari.

Ibtisam chocolate colour ce, colour dinta yana da matukar kyau, tana da tsawo amma ba Sosai ba, haka ba gajera ba, dai dai tsawonta, Tana da manyan idanu Wanda ya k'ara ma fuskanta kyau, bata da jiki kuma ba siriri bace, tana da cikowar kirji, sannan tafiyarta in tanayi kaman bazata taka k'asa ba, sannan tana da aiki Sosai, ga k'okari boko da islamiya, ita da zarah sukai jamb wannan shekaran duka suka saka ABU zaria, kuma ita da ibtisam din duk sun samu score din da ake bukata, sai neman admission kuma.

Najeeb fari ne Sosai domin ya d'auko farin mum d'inshi, sabanin zarah da bata da haske Sosai, Najeeb yana da faffadan kirji, gashi shiba mai jiki ba, ba kuma siriri ba, kana kallon Najeeb Kaga jarumin namiji, gashi da kwarjini Sosai, Najeeb bai wani iya Hausa Sosai ba, domin ba'a kasar yayi karatu ba, ita kam zarah tana ji Sosai.

Abunda yasa Granny take kiranshi miskili saboda rashin yin maganan shi, gashi basu cika shiri ba, domin tana ganin ai raini ne yace bai iya Hausa ko fulatanci ba, sai yaran masu jajayen Fata, sai yasa lokacin da za'a kaishi waje karatu bata so ba, itama mum din najeeb lokacin bata soba, amma najeeb din da Dad d'inshi sun dage, dole suka hakura.

Granny a wajan Umar take zaune, domin tace ita Inba yola ba, toh gwara ta zauna a Kano, akan taje Abuja.

Gidan su ibtisam 3bed room ne, sai wani k'aramin d'aki, dake waje, inka shigo cikin gidan akwai falo Wanda shima bashi da girma Sosai, inda abban ibtisam yake ajiye ba'ki in yayi, sai filin tsakar gidansu inda za'a iya parking din mota biyu.

Ibtisam bata kula samari, saboda tana da burin tayi karatu Mai zurfi Kafin tayi aure, sai dai duk Wanda ya tareta tace anyi mata miji

Granny tayi alkawarin Indai ibtisam ta samu tsayayye, toh zasu sha mamaki, amma ta boye cikin ranta.

Alh Abdullahi yakan zo lokaci lokaci yana ganin mahaifiyar tashi suna gaisawa, Alh Abdullahi yana son zumunci sai dai yana son yaranshi Sosai har baya iya boye son da yake musu, musamman ma akan Najeeb yana son Najeeb Sosai, har gwara mum ita takan d'anyi kawaici, wannan shine takaitaccen tarihin su....









~MARYAM OBAM~
*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE 3*









"koda ibtisam ta shiga cikin gida, a kitchen ta iske ummi tare da fad'in sannu da aiki ummi?

Ummi tace yauwa, har an dawo? Amma kun dad'e

Ibtisam tace ummi ai dole mu dad'e, tunda na tafi da granny, tana tafiya kaman batayi, damma da zamu dawo a mota muka dawo.

Shigowan Granny ne yasa ibtisam barin wajan cikin fushi.

Granny tace kanki akeji.

Ummi tama Granny sannu da dawowa, sannan taci gaba da aikinta tare da duba abubuwan da suka siyo Mata

Granny d'aki ta nufa inda taga ibtisam a kwance tayi ruf da ciki, tace ke Wai fushin Mai kikeyi haka ne?

Ibtisam ta tashi ta Fara magana kaman haka, wai Mai kike nufi dani ne? Akan wani dalili zaki samu mu shiga motar mutumin da bamu Sani ba, sannan harda wani cewa a amsan miki number d'inshi?

Granny tace toh fah, daka Abun arziki, ah lallai ba shakka, naga kin tsaya Jan aji, shine na taimakeki amma shine zaki tsaya kina min tujara, kuma Nasan ya miki munafuka.

Ibtisam tace oh haka kike tunani, toh ai sai ki aureshi tunda ke kika bu'kaci number d'inshi,sannan ni bai mun ba, sarai kin San babu maganan aure a gabana, karatu zanyi, gwara Kibar wannan maganan.

Granny tace au yanzu na gane, kodai Kore samari kikeyi ne? Inba haka ba ai nidai nasan Indai farin jini ne Ina dashi, sanda nake yarinyar kar kiga yanda akemin layi, samari Kala Kala, amma ke sai kace anyi miki asiri babu Mai zuwa, inma anzo kwana biyu mutum bai sake le'kowa, k'asa tayi da murya tare da magana cikin sigar lallashi tace haba takwarata ki fad'amin gaskiya kodai kina koransu ne In sun zo?

Ibtisam dariya ta saki, danta gano wayau take son mata, itama cikin sanyin murya tace Granny bana koransu, sune basa zuwa ta k'arasa maganan cikin sigar tausayi

Granny tace ikon Allah, wannan bakin jinin na dangin uwarki ne wlh, nidai sanda nake yarinya Kinga yanda ake mun layi kuwa? Cikin masu sona harda d'an Mai anguwa, amma na dage na auri kakanki, lokacin auren soyayya mukayi

Ibtisam dariya ta saki Sosai, tare da fad'in toh Granny nima basai ki bari inyi auren soyayya d'inba, kin San aure lokaci ne, Idan lokaci yayi zanyi

Granny tace hakane, lokaci ne amma da niya, ke gaba d'aya keda miskili baku da niyan aure

Ibtisam tace haba Granny Mai yasa ni d'aya kika sama ido, ga zarah bakya maganan ta

Granny tace ai kin girmeta, nafi son in fara ganin d'anki keda miskili, tunda kune manyan jikoki na, kuma ke takwarata miskili kuma takwaran masoyina, Kai Allah yaji kan Habibu.

Ibtisam ta amsa da Ameen, tare da fad'in an tuna da soyayya kenan?

Granny tace Kedai bari, ai in lokacin aurenki yayi Zan nuna miki yanda ake siye zuciyar miji

Ibtisam dariya take Sosai, lokaci d'aya ta tashi tare da fad'in bari inje in taya ummi aiki

Granny tace Mai yakon ki kwanta ki huta, daka kasuwa muka dawo fah, ni kafafuna sai faman zugi suke, danma wannan d'an arzikin ya kawo mu, ni d'an kiramun shi inji yakai inda zashi

Ibtisam tace wa? Lallai ma Toh Wlh bada wayata ba, wai Mai kike nufi dani? Duk fah abunda za kiyi bazan soshi ba, daka had'uwa da mutum, sai kace wacce tayi kwantai haba da dudu guda nawa nake, da zaki dinga tusa ni.

Granny tace Dallah Rufamin baki, kina wani dudu du guda nawa kike, kina shekara Goma sha bakwai, ace har yanzu kina zaune gaban iyaye, wannan wani irin abun kunya ne, Keko kunya bakya ji, kin ri'ka kin ri'ke a gida

Ibtisam tace tunda akanki nake ai dole kice haka, wlh Granny kina takura min, wanda suke Kai shekara talatin babu aure fah, su kuma muce me?

Granny tace aniyarki ta biki, bazan ga wannan abun ba, Bari Umar ya dawo, bazan d'auki wannan iskancin karatun ba Wlh, bazaki sa aita nuna niba, mu Fulani an San muna auren wuri

Ibtisam tace fulanin da kenan, Nina rasa irin wannan jaraban taki Wlh, waini yaushe zaki mutu mu huta ne, haba Mata ta sani gaba

Granny ta tsuke baki a dole ranta ya baci, tace sai a kasheni ai, aure ne dai sai anyi ko anki ko anso.

Fita ibtisam tayi tana fad'in basai kisa dole inyi ba, ni naga jaraba sai kace dole, naga dai auran sunna ne ba farillah ba, da zaki bi ki damu mutum, har takai bakin kofa ta tsaya tare da fad'in ke kika sani koh Ina cikin matan da Allah yasa ba zasuyi aure ba K......

Dallah Rufamin baki, mara hankali, kina son jaza ma kanki fitina da mugun baki, kodai Kema aljanun ne suka aureki irin na miskili? Kuka ta saki wi wi wi tana fad'in na shiga uku

Ganin haka yasa ibtisam ta nufeta tana fad'in, dan Allah kiyi shuru, kai Wlh Granny kina son kasheni, badai aure kike so inyi ba?

Da sauri Granny tace eh

Ibtisam tace zanyi, idan na tafi makaranta hala a can in samo miki santalelen saurayi, kinyi sai ayi

Granny tace ga Kabiru nan, kalla har kud'i Yaban, duba kiga nawa nema.

Ibtisam kaita girgiza tare da amsan kud'in cikin takaici ta kirga, tace dubu goma ne

Granny Tana share kwalla Tana fad'in Allah sarki d'an arziki kenan

Ibtisam ajiye mata kud'in tayi ta fita, cikin takaici

Bayan sallah isha'i, mahaifin ibtisam ya shigo gida, kaman kullum yanda ya saba, gaba d'aya suna falo suna fira.

Ibtisam tayi ma mahaifin nata sannu da zuwa tare da amsan ledan hannunshi

Umar gaida mahaifiyar tashi yayi tare da fad'in Barka da hutawa.

Amsawa tayi da yauwa, Ummaru ya kasuwa? Da fatan an dawo lafiya?

Yace Alhmdlh, tare da shiga cikin d'aki, ummi ta tashi tabi bayanshi

Ibtisam kam tunda ta ajiye ma abbanta ledan daya shigo dashi ta nufi d'akinta, wanda ita da granny suke kwana tare, tana shiga wayarta taga tana wuta, da sauri ta nufi wayar taga number ne, kaman Karta d'auka harya kusa tsinkewa ta danna tare da sawa a kunne.

Sallama yayi mata tare da fad'in Barka da wannan lokacin

Ko bata tambaya ba, tasan Kabir ne, gashi ta d'auka babu daman kashewa, dan haka ta daure tace yauwa.

Yace Nasan baki gane mai magana ba, dan Nasan ba'ayi saving number d'ina ba, but anyway tunda na kira an d'auka babu damuwa, Kabir ne, so yakike?

Dan tsaki tayi mara sauti, wanda koda mutum yana kusa da ita bazai jiba, balle na Waya,tace lafiya, tare da fad'in mun gode da rage mana hanya, Bari in kaima Granny wayar.

Da sauri yace a'ah dake nake son inyi magana, Plz ina bukatar kiban lokacinki koda minti biyar ne In babu damuwa

A hankali tace babu damuwa, zaka iya fad'a inaji

Yace toh gashi ko sunanki ban sani ba?

Tace uhm sunana ibtisam

Yace wow nice name, sunan yamin dad'i

Nagode tace

Yace sunana Barrister Kabir, ina aiki a federal high court dake Abuja, ni dan asalin Kano ne, Ina zaune da iyayena a rijiyar zaki, mu biyar iyayena suka haifa, nine babba sai kanina namiji da kannena mata uku, iyayena sun matsamin inyi aure but sai dai ban samu irin matar da nake soba, sai yau, ibti tunda na ganki naji kin kwanta min a rai, irin shigarki da kamalanki, sabanin irin y'an matan yanzu, ibti nida aure nazo miki bada wasa ba, Allah ya sani yau na fara ganinki amma gaba d'aya kin tafi dani, sai dai ban sani ba, ko zan samu karbuwa.

Shuru tayi ba tare da tace komai ba.

Jin tayi shuru yasa yace ibti, ya naji kinyi shuru? Koda yake ya kamata in barki kiyi tunani zuwa gobe, amma plz ina son ki duba magana ta, gobe insha Allah Zanzo.

Tace Allah ya kaimu tare da kashe wayan, tana tunani, toh mai yake nufi? Gaskiya ya kamata in fad'a mishi k'udiri na, tun Kafin ya jaza min, dan Wlh Inna sake Mai wannan tsohuwar zata jazamin bala'i ku.....

Jin muryan Granny tayi tana fad'ama abbanta, kasan Mai sunana taci Janus kuwa?

Abba yace Janus? D'an shuru yayi yana nazari miye Janus kuma? Can ya tuna da ibtisam da safe Kafin ya fita tace jamb ya fito tun jiya, murmushi yayi tare da fad'in Kai Alhmdlh Ashe taci jamb

Granny tace eh taci Janus, dole kayi murna ai, burinku ya cika, zata karatu.

Abba yace mama kiyi hakuri ba haka bane, da taita zama a gida babu aure ai gwara tayi abunda zata ci gaba, in mijin ya samu koda Tana karatu sai Ayi auran.

Granny tace nidai wannan abun Anfi karfina, amma tunda kace koda ta Fara karatun inta samu miji zatai aure babu damuwa, kwanan nan kuwa zatayi auran.

Abba murmushi kawai yayi, domin shima yafi bukatar tayi auran Kafin ta Fara karatu, duba da irin yanda duniya ta lalace, musamman yanda ake kallon macen da taje jami'a a matsayin wacce idonta ya bud'e, ake mata kallon y'ar iska wacce ta Waye da yawa, har maza kanji tsoran auransu, sai yasa baiso ta saka har kaduna ba, yafi son tayi karatu kusa dashi, amma mum ta nuna mishi tare da zarah zasu karya damu, yayi musu addu'a kawai.

Granny tashi tayi tare da fad'in Bari inje in kwanta na gaji, sai da safe.

Koda Granny ta shigo d'aki ganin ibtisam tayi tana karanta wata takarda, Granny tabe baki tayi tana fad'in karyan banza, waike y'ar boko koh?

Ibtisam ajiye takardan tayi tana dariya tare da fad'in wai Granny Mai yasa kwana biyu kika samun ido ne? Dan Allah ki barni in huta, ni Mata tabi ta isheni, gashi kin tsufa amma kinki mutuwa

Granny tace dan uban mutum ai saiya kasheni, tunda akan mutum nake rayuwa

Ibtisam tace yauwa Nima haka na gani, Aiba a kan kowa nake rayuwa ba, dan haka kibar takura min, da wani maganan aure dan Allah, kaman yanda mutuwarki lokaci kike jira nima haka lokacin auren nake jira

Granny tace aike baki da burin aure ko kad'an, amma Wlh bazan bari kiyi shekara hud'u a gida ba, wannan abun kunyar har Ina, ace mun ajiyeki babu aure, ni sai naga duk kin Fara min tsufa Wlh

Ibtisam dariya take Sosai tare da fad'in nice na yanke ma k'asa cibi, karshen girma, wlh Granny ki fita harkata

Granny taja tsaki tare da fad'in aikin banza, zaki gani ai, aurene sai kinyi ko zaki mutu.

Ibtisam kwanciya tayi tare da juya mata baya tana fad'in ki kashe mana wutan d'akin in kin shirya kwanciya.

Granny tace Wlh da wuta zamu kwana, in zan shiga tailat wai zatace toilet shine tailat, dame zan haska?

Ibtisam tace ina wayarki, ki haska dashi mana

Granny tace Wlh bazan kashe wuta ba, ni yanzu bazan dinga kwana cikin duhu ba

Ibtisam da takaici ya kamata banza da ita tayi tare da fara bacci, harta Fara bacci taji gurus gurus farkawa tayi, ganin Granny tayi tana cin goro

Ibtisam tace na shiga uku, wai miye haka? Dan Allah granny kibar cin wannan goran ki barni inyi bacci mana, haba ni Wlh kin isheni

Granny tace Dallah Rufamin baki, na hanaki bacci ne ko me? Ina ruwana dake? Goro nedai sai naci

Ibtisam d'aukan filo tayi tana k'okarin barin d'akin, da sauri Granny tace haba takwarata zoki kwanta nabar cin goran, zoki kwanta abunki, tana maganan ne cikin sigar rarrashi

Ibtisam tsaki tayi, Granny tace kinma uwarki bani ba, bata ce komai ba ta dawo ta kwanta itama Granny kwanciyan tayi haka suka kwana da wuta a kunne saboda granny tace in zata tailat Hhhhh.

Washe gari da safe Bayan abban ibtisam zai fita, yace ma ibtisam gobe zata shirya taje Abuja, sunyi waya da d'an uwanshi, yana saudiya amma goben zai dawo shima, yace ibtisam tazo can zai amsa takardun ta ita da zarah.

Ibtisam taji dad'i Sosai, domin ta tabbatar burinta zai cika na son karatu, Mai wuyar shine kawai ta Fara karatun,tasan Indai ta Fara babu zancan cewa ta Bari.

Granny dake zaune a falon ta kalli ibtisam tace Wai yaushe Kabiru zai zo? Kiramun shi mana inji.

Ibtisam tsaki taja tabar falon

Granny tace zanyi maganinki ai, wannan karatun babu inda zaki, aure zakiyi.

Ummi dake zaune tana dariya, kai Granny ko rigima, yanzu ta nuna ta amince da karatun ibtisam anjima kuma ta nuna bata yarda ba, ita har yanzu taki yarda da auran lokaci ne, gani take kaman ibtisam ce bata da niya.

Kaman yanda Kabir yace, suna zaune a tsakar gida su duka, domin Granny koda akwai wuta sai tace tafi son tasha iskar Allah, tafi dad'i, yaro ne ya shigo yana fad'in Wai ana sallama da ibtisam inji Kabir, da sauri Granny tace Jeka ce ya shigo inji grandi, Yaron Ya amsa da Toh tare da fita

Granny kallon ibtisam tayi data d'aure fuska tace Dallah tashi kije ki kaishi falon ba'ki, kin wani zauna kin tamke fuska kaman ba'kar kumurci

Ibtisam tashi tayi rai bace ta d'auko hijab sannan ta fita, da murmushi a fuskanshi, ganin haka itama yasa ta saki murmushi sai taga ya Mata kwarjini Sosai, gaba d'aya maganan da tayi niyan fad'a mishi sai taga bazata iya ba, wanda da ta fito da niyan ta fad'a mishi magana akan karya k'ara zuwa, amma saita tsinta kanta da gaida Kabir din, tare da fad'in shigo muje

Har falon ba'ki ta kaishi sannan ta fita, dan Kawo mishi ruwa, abun gaba d'aya mamaki yake bata, yau kawai data ganshi Wanda shekaran jiya bata ko kalleshi ba, taga had'uwa da cikan kamala a tare da kabir din, lallai inda inada burin aure yanzu dana amince dashi, domin namiji ne dako wace mace zatai burin samu, miji ne na nunama tsara, kabir chocolate colour ne, yana da tsawo amma ba Sosai ba, yana da d'an jiki kad'an shima ba Sosai ba, gaba d'aya ibtisam tsayawa tayi a kitchen tana tunani.... Hmm muje zuwa muga burin ibtisam zai cika, kona grandi ne zai cika Hhhhh?















~MARYAM OBAM~

*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE 4*






Lokaci d'aya ibtisam ta d'auki ruwan ta fita, Granny na tsakar gida ita da ummi, sai murmushi Granny take kaman ance an bata kyautar kujeran makka.

Koda ibtisam ta k'arasa falon da sallama ta shiga, kabir ya amsa, ajiye ruwan tayi da drinks tare da fad'in bismillah

Murmushi yayi yace ngd ibti

Kanta na k'asa Tana wasa da yatsun hannunta, tana tunani mai yasa nake jin nauyin shi? Kai gaskiya da sake, koda yake inna tafi makaranta ai shikenan k....

Katse mata tunani yayi da fad'in ibti, nazo ne muyi magana ta fahimta, kaman yanda na Fara fad'a miki jiya, akan ni auranki zanyi dagaske, bada wasa nazo ba, sai dai baki ce komai ba, ina fatan yanzu zan samu amsa daka gareki?

D'an murmushi tayi tare da cewa naji abunda kace, sai dai..... Shuru tayi ta kasa fad'in abunda take son cewa

Ganin haka yasa Kabir yace Ina sauraranki ibti

Kanta na k'asa tace banki magananka ba, amma sai dai ni yanzu karatu ne a gabana, shi nake burin inyi

Kabir yayi murmushi tare da fad'in, ibti karatu ai baya hana aure, sannan Nima namiji ne mai burin ace iyalina tayi karatu, so inaga wannan ba matsala bace, kawai yardanki nake nema

Shuru tayi tana nazari, toh inta amince Mai cewa zaiyi zai turo? Ko ya? Ita dai gaskiya bata shirya aure ba, dan bata son abunda zai kawo mata tsaiko cikin karatun ta, yanzu Idan tayi aure tana karatu lokaci kad'an ace ta samu ciki, ga karatu ga ciki, haka inta haiyu ga raino ga ciki, gaskiya a'ah bazan yarda ba, ko kuma wasu mazan in ba'ayi Sa'a ba suce su basa son karatun Bayan da farko sunce sun amince mace tayi karatu ga....

Katse mata tunani yayi da fad'in ibti, plz say something

Murmushi tayi wanda bata san tayi ba, tace kana nufin zaka jirani har shekara hud'u?

Kabir yace ibti shekara hud'u yayi yawa, ki kalleni ki gani ya kamata ace na ajiye iyali, mutun kaman ni bai kamata ace banda iyali ba, duk da aure lokaci ne, amma ibti Idan kika amince na turo manya, ni a Abuja nake aiki sai weekend nake samun hutu shima bako yaushe ba, gobe zan koma Abuja da safe, a ina kike son zuwa karatun?

A hankali tace ABU zaria.

Yace toh kin gani, zaki samu lokacin karatu tunda ba gari d'aya muke ba, kina kaduna Ina abuja, sai inna samu time inzo, ko in kunyi hutu ki dawo inda nake.

Ibtisam shuru tayi tana nazari, lallai maganan Kabir gaskiya ne, toh amma abun dubawa da tsoro shine inta samu ciki fah? Anya wannan auren zaiyu kuwa? Koda yake ai nasan ba lallai wani abu ya shiga tsakaninmu ba, kai any....

Kabir yace ibti kiyi tunani akai ki gani I....

Babu wani tunanin da zatayi, Kabiru ka turo iyayenka kaji, Granny ce Mai wannan maganan wanda tun d'azu take labe take jinsu.

Gaida Granny yayi cikin girmamawa, amsawa tayi cikin fara'a tare da fad'in karka damu ka turo iyayenka, a tsaida magana, Kaga a hankali kwa fahimci juna

Ibtisam ji tayi kaman ta saki ihu saboda takaici

Kabir yace Granny zan turo su, amma nafi son mu fara fahitan juna Kafin manya su shiga cikin batun

Tace a'ah Kabiru, ka turo kawai

Yace toh Granny insha Allah zan turo.

Tace Allah yayi albarka, tare da kallon ibtisam ta galla mata harara sannan ta fita.

Kabir murmushi yayi tare da fad'in Granny akwai ban dariya, kallon ibtisam yayi wacce yaga ta had'e rai, alaman ranta ya baci, murmushi yayi tare da fad'in ibti kiyi hakuri na fahimce ki ko bakiyi min bayani ba na gane abunda kike nufi, kina da burin kiyi aure Bayan kin kammala karatu, babu damuwa zan iya jiranki, amma ki bani dama manya su shiga cikin lamarin asan da maganan.

Ibtisam jin haka yasa taji dad'i Sosai, ta kuma yarda Kabir yana Sonta tunda har zai jirata ta kammala karatu, a hankali tace babu damuwa, dama ni babban burina in kammala karatun sai inyi aure ta yanda hankalina zai nutsu waje d'aya.

Kabir yayi murmushi tare da fad'in kice dai ta yanda zaki kula dani .

Hannunta tasa ta rufe fuska tana murmushi alaman taji kunyan maganan da yayi.

Yace yanzu dai kin amince in turo koh?

Kai ta d'aga mishi alaman eh

Wani irin ajiyan zuciya ya sauke Wanda har Tana jiyowa, tare da furta Kalman Alhamdullilah, gaskiya ina cikin farin ciki, ibti na tabbata idan manya suka shiga cikin maganan koda Kinje karatu babu Mai kwace min ke.

Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, mamaki take yanda harta amince akan ya turo magabatanshi, tunda take bata taba jin wani abu akan namiji ba sai yau, kodan kabir shine namiji na Farko data taba doguwar fira dashi haka? Eh tabbas hakane saboda bana magana da maza irin haka, toh mai yasa nake jin nauyin shi? Kai Mai yake damuna ne haka, daka had'uwa da mutum jiya jiya yana son saka min tunani lokaci d'aya ta cire tunanin tare da k'ago murmushi tace baka sha ruwa ba.

Yace Alhmdlh ibti nagode, am Okey, tashi yayi tare da fad'in zan tafi zadai muyi waya, cuz gobe zan koma office.

Tace Allah ya taimaka ya bada Sa'a.

Kabir yaji dad'in addu'anta Sosai ya amsa da Ameen ibti, muje in baki sa'ko.

Binshi tayi har waje inda ya bud'e motarshi ya d'auko Leda guda d'aya babba, yace gashi.

K'in amsa tayi tare da fad'in wannan fah?

Yace ki Fara amsa first.

Mi'ka hannu tayi ta amsa Tana kallon shi ta gefen ido, gskya Kabir ya had'u ta furta cikin ranta

Yace na tafi sai munyi waya

Tace nagode tare da shiga gida.





*London*
Najeeb ne ya fito daka toilet towel yasa ya d'aura a dai dai kugun shi, sannan wani towel din ri'ke da hannunshi yana goge ruwan dake kanshi, yana abun ne cikin sauri daka gani zai fita ne yanda yake sauri.

Janet dake kwance tana kallonshi, lokaci d'aya ta taso babu komai a jikinta, ta rungume shi ta baya, tare da fad'in nagit naga kana sauri kaman zaka fita, ina zaka?

Bai ko kalleta ba balle ya bata amsa, ganin haka yasa ta sakeshi tare da d'aukan kayanta ta Fara sawa, Bayan ta gama ta koma kan gadon d'akin ta zauna tana kallonshi tana murmushi, komai na nagit yana burgeta ya iya love da sarrafa mace, gashi ya had'u ga kyau ga kud'i, sai dai ta kasa gane halinshi, yanzu ya sake maka anjima ya d'aure maka, sai yayi abu kaga kaman bashi ba.

Najeeb ya shirya cikin uniform Wanda yake k'ara mishi kyau da kwarjini, d'aukan wata jaka yayi lokaci d'aya ya bud'e ya cire kud'i ya watsa ma Janet tare da fad'in zaki iya tafiya, yana fad'in haka yayi gaba abunsa

Janet kam da ido ta bishi tana mamakin wannan wani irin mutum ne haka, taga sunyi sex taji dad'i shima yaji dad'i, kodan wannan ai ya mutunta ta, d'an shuru tayi tana nazari tare da tambayan kanta Mai yasa tun ranan data had'u dashi baya komai da ita sai yasha alcohol? Koda wasa ya fara mata zai barta sai yasha alcohol yake sex, kodai saboda alcohol dinne da yake sha baya cikin hayyacinshi yake sex da ita shi

Please Login or Register in order to submit comment