Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

kaɗan ,naga banganta atare da ke ba" ammi ta faɗa tana mai kallon gimbiya suhaimat.
Murmushi matar tayi kafin tace " har abada bazan taɓa rabuwa da wannan sarƙar ba,dan kuwa itace shaidar dazata sadani da ƴata, Aduk inda take,ina ji ajikina mun kusa haduwa da juna kuma nayi alƙawarin saina ɗauki fansar rabani da ita da akayi na tsawon shekaru,akan koma waye keda hannu cikin al'amarin " ta faɗa idanunta cike da kwallah.kafin ta ɗan daga mayafin jikinta ,saiga sarƙar ta bayyana ,ƙurawa sarƙar idanu ammi tayi,tabbas wannan irin sarƙar wuyan yarinyar can ce ,hakan na nufin fattu itace ɗiyar suhaimat da suka rasa shekarun baya?innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.banga ta zama ba. Cewar ammi cikin zuciyarta.
Da sauri ta miƙe tana mai faɗin "suhaimat ina zuwa "bata jira amsar taba tayi gaba.

Rashad ma ganin ammi ta mike yayi saurin bin bayanta dan zuwa ga fattu,yau kam za'ayi ta ta ƙare.

Zulaihat dake zaune cikin ƙawayenta tana ta zuba izza da iyawa ,ganin su duka biyun sunyi waje hakan yasa itama ta mike cikin sauri ta rufa musu baya, dan kuwa tare zasu aikata mugun nufin nasu akan fattu, tana son ganin komai ya wakana akan idonta ,



Ko ina zasu kuma oho?
Muje zuwa masu karatu,
Manage please har yanzu muna cike da alhini.

Na gode sosai da addu'ar ku garemu,waɗanda suka kirani,da waɗanda sukayi min ta waya.
🙏🙏
Anty mammy ce

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.
[8/23, 9:06 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 51/53




_________________Abakin ƙofar hall ɗin Zulaihat ta tarar da Rashad ,yana tsaye da waya ahannunsa ,da alama kira yake ƙoƙarin yi,saidai yana ganinta ya maida wayar cikin aljihunsa yana mai faɗin,"yawwa dama ke nake ƙoƙarin kira,sai gaki kin fito.

Ƙarasowa Zulaihat tayi kusa dashi ta tsaya" ya ake ciki ne ?" Ta faɗa tana ɗan waigen bayanta.
"Yau burina zai cika ,zan sami abinda ke hanani barci,kuma zanyiwa Adeeb illah,saina rama dukan da yayi min akan yarinyar da yake iƙirarin yar amanar da ce,bayan kuma Ni nasan dadironsa ce ,kawai kishine da mugunta sukayi masa yawa,shine ya hanani Nima in ɗana"cewar Rashad yana mai kallon Zulaihat.

"Kaga Rashad karka ƙara cewa dadiron my Prince ce,karkayi masa sharri,dan kuwa nasan halinsa nasan koshi waye,wllh bazai taba ajiye yarinyar nan dan biyan buƙatarsa ba,mutumin da har maganin sha'awa nake saka masa alemo,dan kawai yayi tarayya dani,amma duk yadda ya galabaita bazai koda rungumeni ba.
Dama dai kaine akace ka ajiye ta dan biyan buƙatarka,to wannan kam na yarda dan nasan kai din namamajo ne " Zulaihat ta faɗa tana mai galla masa harara,dan taji haushin sharrin da yayiwa adeeb,ita da take burin ace itace zata fara bude Adeeb aledarsa ina zataso jin wannan batu.
Wani shegen kallo Rashad ya watsa mata kafin yace " banza yar tasha ,ke har Ni zaki cewa na mamajo? Ai duk iskancina ban kaki ba,kefa ƴar maye ce sannan jarababbiya, Ni kaina sau nawa ina taimaka miki ?ina ce wataran har guduwa nake saboda jarabarki ?zaki raina min hankali wawiya kawai" Rashad ya faɗa cikin faɗa.

Haushi sosai ya kama Zulaihat ,ranta ya ɓaci da kalaman Rashad gareta ,wato har gori zaiyi mata ,dan ta neme shi kusan sau uku ?ba komai zai gane kurensa wllh.
"Ni kakeyiwa gori Rashad ?to wllh kasani bazan taimaka maka akan ƙudirinka na yauba ,saidai kayi kai kadai ,banza marar mutunci" Zulaihat ta faɗa cikin ɓaci rai tana mai barin gurin cikin sauri.

Tsaki Rashad yayi yana mai faɗin"aikin banza ,da me zaki iyamin agurin banda kema kice kina so intaimaka miki ,Ni kuwa ranata ta yau duka ta fine baby ce,yar ƙwaya kawai " ya faɗa yana mai nufar part ɗin ammi.

Ammi kuwa tana zuwa part ɗinta cikin ɗakinta ta nufa ,ƙullewa tayi tare da zama bakin gado,tana tunani iri iri cikin ranta, wata akwati ta ɗauko dake can ƙasan gadon ta tare da budewa,
Tana buɗewa wani hayaƙi yayo sama baƙiƙirin dashi,banda wari ba abinda ke tashi cikin hayaƙin nan,da sauri ammi ta toshe hancinta, tana mai zaro ido waje,abayyane ta furta " na shiga ukuna ba dai kwalbar nan ta fashe ba? Shikenan ta faru ta ƙare ,dama nasan hakan zata faru wayyo Allah na" ammi ta faɗa tana mai bin wata kwalba yar gajeriya da ta tarwatseda ido,wani farin abu mai kauri yana ta motsi kamar tsutsa.

Bugun ƙofar da ammi tajine yasata saurin rufe akwatin ta tura can kasan gado,saita kanta tayi cikin ɗauriya ta nufi ƙofar .
Rashad ta gani tsaye abakin ƙofar ,"ammi ya ake ciki ne ?ta yaya zan ɗauki yarinyar ne ?kinsan ba aɗakin ta zan aiwatar da ƙudirina ba,dan wancan mayen zai iya zuwa ya cin mini" ya faɗa yana kallon fuskar ammi .

"Ka tafi can ɗayan part ɗina ka jira zan kawo maka ita da kaina ,ina son kayi mata abinda nan da wata guda ma bazata san inda kanta yake ba,bana son ka tausaya mata ko kaɗan"ammi ta fada fuskarta ahaɗe.

"Kada ku damu ammi bazan taɓa baki kunya ba,nayi alƙawarin saina yi mata abinda Bama ki tsammata ba"Rashad ya faɗa yana wani irin killer smile.

Ficewa ammi tayi tare da nufar part ɗin su fattu.ba kowa afalon,dan kuwa nanny ta ɗan leƙe gurin taron ,ganin fattu kwance tana barci.
Cikin ɗakin ammi ta shiga ,tsaye tayi agaban gadon da fattu ke kwance ,idanunta arufe kamar mai barci,amma idanunta biyu,hammanta kawai take tunani.
Kusan minti uku ammi tayi tana kallon fattu dake kwance ,tabbas ko tantama batayi ,wannan yarinyar gimbiya suhaimat ce ,dan kuwa sai yanzu take ganin tsantsar kamannin dake tsakaninsu,amma ta yaya suka haɗu da Adeeb?har ya taho da ita nan?wannan shine abinda take son sani.
Ganin fattu ta ɗan motsa ne yasa ammi ta ɗan kira sunanta " fateema tashi"
Ammi ta faɗa tana ɗan shafa kan fattu.

Ahankali cikin nutsuwa fattu ta tashi zaune tana ɗan mika ,dan ta jima akwance.
Murmushi tayiwa ammi tare da sunkuyar da kanta ƙasa cikin kunya .

"Fateema Sarkin kunya,ke kadaice aɗakin ne"ammi ta faɗa cikin Hausa ,dan kuwa ta iya Hausa sosai itama.
Jinjina kai fattu tayi tana wasa da ƴan yatsunta.

Murmushi ammi tayi tana shafa kan fattu kafin tace " to ya jikin naki,?"
" Da sauƙi inna"fattu ta faɗa cikin yar karamar muryarsa mai dadi.

"Kinga bai kamata ki zauna ke kaɗai anan ba kowa ba,dan haka maza ki tashi ki koma can ɗaya part ɗin sauki kwanta kiyi barcinki kinji?kafin tashi daga taron" ammi ta faɗa tana mai kamo hannun fattu cikin nata ,suka fice daga ɗakin.

Binta fattu tayi ba tare da ta musaba, dan tana tsananin jin kunyar ammi,saidai haka kawai taji gabanta na faɗuwa,gashi hammanta yace karta fita ko ina ,karya dawo bai ganta ba ransa ya ɓaci.
Haka dai tabi ammi har zuwa wancan part ɗin da Rashad take ciki.

Wani ɗaki ammi ta kaita tare da zaunar da ita akan kado,tace cikin murmushi"ki zamanki anan kinji,idan kina jin barci saiki kwanta,akwai abubuwan ci ,acikin fridge idan kinji bukatar ci" ammi ta faɗa tana mai kallon fattu ,fuskarta ɗauke da murmushi.

Jinjina kai fattu tayi kafin tace "inna !Hamma yace karbaje ko ina ,karya dawo kuma bai ganni ba"ta faɗa kanta aƙasa.

Wata uwar harara ammi ta bankawa fattu,kuji yar iyayi shegiya mai kama da aljanu,zaki gane kurenki, ne yau zaki yabawa aya zaƙinta,dagake har Adeeb ɗin.
Da sauri ta saki fuska tana murmushi,ganin fattu ta ɗago kai tana kallonta,"karki damu habeebtee zan sanar da Adeeb nina kawoki nan kinji?"ammi ta faɗa tana sumbatar goshin fattu .kafin ta fice daga ɗakin.

Rashad ta ci karo dashi abakin ƙofar ,daga shi sai wando iya gwuiwa da singlet,kallonsa ammi tayi cike da murmushi,tana mai faɗin"Rashad kenan,wannan zumuɗin haka?,nidai ka kula da maganata banson asami matsala" ammi ta faɗa tana mai kamo kunnensa.

Murmushi yayi yace "baki da matsala ammina,ke dai kawai kijira sakamako"ya faɗa yana mai murmushin mugunta.

"Amma ka jira sai an jima kadan,zan kulle ƙofar ta baya,inka gama sauka fice ta ɗayan ƙofar" jinjina kai Rashad yayi cikin zaƙuwa da son ammi tayi ta fice daga ɗakin.

Adeeb yana zaune kusa da abie ,saidai haka kawai yakejin gabansa na faɗuwa ,sosai yake jin faduwar gaban.fattu kawai yake tunani yana ji cikin ransa yana buƙatar ganinta ahalin yanzu.

Kallonsa ya kai inda Rashad ke zaune,saidai ba alamunsa agurin.gabansa ne ya ƙara mugun faɗuwa,ina Rashad ya nufa?yaushe ya bar gurin?
Da sauri ya yunƙura zai mike,dan zuwa ya duba fattu,saidai gurin taron ne ya kara de da kiran sunansa Adeeb,ana buƙatar yayi jawabin godiya ga baki .
Kallon abie yayi cikin yanayi na marairaita ,amma abin ya jinjina masa kai alamun yaje yayi jawabin.
Haka Adeeb ya karbi lasifikar nan badan ransa yaso ba,burinsa kawai yaje gurin fattu.

Adaidai wannan lokacin kuma Rashad ya kulle ƙofofin ɗakin daga falon har zuwa toilet duka,ɗakin da fattu ke ciki kawai ya bari abuɗe .kai tsaye ya kunna kansa cikin ɗakin.
Fattu na zaune abakin gadon inda ammi ta zaunar da ita,zuciyarta sam bata aminta da zaman ɗakin nan ba, sai kalle kalle take,
Da sauri ta juyo atsorace jin kamar mutum atsaye akanta.
Ido huɗu sukayi da Rashad tsaye abakin ƙofa yana kallonta ,fuskarsa ɗauke da murmushi irin na yan duniya,
Da sauri fattu ta miƙe tsaye jikinta na rawa,me wannan mutum yake yi anan kuma?ba innar Hamma tace nan ma ɗalibta bane?innalillahi,wayyo hammana kana ina?fattu ta faɗa cikin ranta jikinta na rawa matuƙa.

Murmushi Rashad keta famanyi,yana takowa cikin ɗakin bayan ya kulle ƙofar,cikin harshen larabci yake faɗin"yan mata meye na tsorata haka?nimafa nazone nayi miki abinda wancan wawan yayan nawa ke miki,ki nutsu yarinya musha daɗinmu tare ,dan kuwa yau wllh ko mutuwa zakiyi saina kwashi daɗi" ya faɗa yana mai karasowa bakin gadon.

Kuka fattu ta fara tana mai yarfe hannu, dan kuwa sosai take fahimtar yaren yanzu,dan haka ta fahimci da dama abubuwan daya faɗa,

"Wayyo Allah na kayi hakuri dan Allah ,wllh niba yar iska bace ,kuma Hamma baya min komai,kayi min rai dan Allah"fattu ta faɗa cikin kuka sosai tana ja da baya.
Zagaye suka fara ita da Rashad,yana ƙoƙarin kamota,ita kuma tana zillewa cikin kuka tana masa magiya,akan ya barta karya mata komai.

Ganin zata ɓata masa lokaci ne kawai yayi wani tsalle tare da damko gashin kanta cikin fushi ya wanka mata mari tare da hankaɗata kan gadon.
"Dan ubanki ki nutsu wllh idan kika ɓatamin lokaci,saina yi miki fata-fata anan gurin,kina abu kamar baki san me nake sanyi ba ,ko irin baki taba yi ɗin nan ba,shi wancan wawan idan yazo haka kike masa?Rashad ya faɗa cikin tsawa yana mai haurowa kan gadon.

Cikin azama fattu ta mirgina can karshen gadon tana kuka,tare da kiran "wayyo hammana kazo ,Hamma kazo ka taimakeni"
Ran Rashad ne ya ƙara ɓaci ganin zata ɓata masa lokaci,da sauri shima ya bita ya damko gashin kanta,ya ƙara wanke ta da mari, nan da nan gefen bakinta ya fashe jini ya fara zuba.
Ihu fattu ta kwalla cikin azaba tana kuka tare da riƙe hannunsa daya damko gashin kanta .
Ƙoƙarin Rashad yake ya haɗe bakinsa dana fattu ,amma sai kauda kai take tana kuka tare da juya kai.
Bakinta Rashad ta matse da karfin gaske ,gaba ɗaya kamaninsa sun sauya ,ba abinda yake so da buri illa yabiya buƙatarsa da fattu.gashi sai neman bashi matsala take.
Hannunsa ɗayan ya ɗora akan ƙirjin fattu ,zaro ido fattu tayi cikin tsantsar razana da jin hannunsa inda ba wanda ya taba ɗorawa,da karfi ta dunkule hannunta tare da buga masa aciki.
Ihu Rashad ya kwalla Dan kuwa ta bugeshi sosai acikinsa.
Hankaɗata yayi jikin bango ,aikuwa ta buga kanta ajikin bangon ,ji kake gummm!!ta gwara kanta.

Ihu ta kwalla cikin azaba tana mai dafe goshinta da jini ya wanke ,tsabar azaba numfashinta har ɗauke wa yake.

Ko tashi ta kasayi,da rarrafe ta nufi bakin ƙofa jini na zuba agoshinta.

Cikin mugun bacin rai Rashad ya nufota, rigarta ya kamo ta baya ya fizgota baya.
Mari yayi ta sauƙe mata har guda hudu,sannan ya cilla ta kan gadon,

Gaba ɗaya fattu ta fita daga hayyacinta ,ko hannunta bata iya dagawa,numfashinta sai kaiwa da kawowa yake,
Rashad kuwa cikin rashin imani ya zare wando sa tare da singlet yayi kan fattu gadan -gadan ,yana zuwa ya janye gadon tare da kama rigar fattu ya yagatadaga sama har ƙasa ,sannan ya...........


Wayyo fattu ,Hamma kana ina kazo ka ceci fattunka,shikenan Rashad zai cutar da fattunka .

Da gudu na fice dan nemo inda Adeeb yake .saiki biyoni muje nemansa tare.

Taku ce anty mammy Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah


More comment
More typing.
[8/23, 9:06 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 53/54

________________Gaba ɗaya Rashad ya zama kamar wani mahaukaci,ba abinda ke gabansa face biyan buƙatarsa.
Gaban rigar fattu ya kama da karfin tsiya ya tsargeta ,tun daga sama har ƙasa.

Nan da nan farar best ɗin fattu da baƙin skin tite ɗin ta suka bayya, Allah ma yasa wandon har ƙasa yake.
" Wllh yau ko da zaki mutu ,saina ida nufina akanki,banga wanda zai iya karbarki daga hannuna ba" Rashad ya faɗa cikin wata irin murya ta azzalumai,waɗanda suka manta da cewar Allah yana kallonsu duk abinda suke aikatawa.
Da gyar fattu ta iya buɗe rinannun idanunta ,wanda tsabar mari da kuka suka sanya idanun kumbura sosai.
Ahankali take daga lips ɗin ta magana take amma saiƙa kura mata ido zaka fahimci me take cewa."wallahu galibun ala amrina" shine abinda take ta maimaitawa abakinta.
Ƙoƙarin zare skin tite ɗin Rashad keyi amma sam ya kasa,jikinsa sai rawa yake,yana jin kamar wanda ake jona masa shocking,Amma tsabar masifa da jaraba ,yaki fasa abinda yakeyi,
Cikin haushi,ya ƙara kaiwa kumatun fattu mari mai zafi da shiga jiki."Dan ubanki me kikasa ajikinki?idan na taɓaki nakejin kamar ana zuƙemin jini?"Rashad ya faɗa yana mai kai fuskarsa saitin Tata,bakinsa ya ɗora akan na fattu,aikuwa ba wata wata fattu ta gartsa masa cizo alips ɗinsa.kara ya kwalla yana mai komawa gefe dafe da lips ɗin sa na ƙasa "kai -kai -kai Ni kika ciza Dan uwarki?zaki gane kurenki ,wllh yau saina kusan kasheki Shegiyar yarinya mai taurin kai"Rashad ya faɗa yana mai danƙo gashin fattu ,wanda yayi buju-buju.

Fattu fa ko motsin kirki bata iyayi,gaba ɗaya jikinta ya saki,tunda take a rayuwarta,bata taɓa shiga tashin hankali da azaba irin na yauba.
Sunan Allah kawai take ambata cikin ranta.

Adeeb kuwa cikin gaggawa yayi jawabinsa tare da godiya ga baƙin da suka zo dan tayashi murnar dawowa gida cikin ƙoshin lafiya.sosai ƙirjinsa ke mugun bugawa zuciyarsa kamar zata fito waje,idanunsa sunyi jajur dasu,wani irin ɗaci yakeji cikin zuciyarsa,sannan ko dana second ɗaya ne fattu taƙi barin tunaninsa.
Gefen da Rashad ke zaune Adeeb ya ƙara kai dubansa, baya gurin har zuwa yanzu,kai gaskiya akwai Abinda ke faruwa ,dole yaje ya duba Hulwa.

Dan haka cikin hanzari ya mike tsaye ,kallonsa abie yayi tare da tambayar ina zashi haka ?ya mike cikin hanzari,sanar da abie yayi cewar kansa ke ciwo yana son yaje ya kwanta.
Sanin da abie yayi cewar ,sam Adeeb yana son hayaniyane,yasa shi cewa yaje ya kwanta sannan yasha magani,akwai maganar da zasu yi zuwa dare.

Cikin sauri da sassarfa Adeeb ya nufi ƙofar barin hall ɗin,yana ɗan kallon gefen da tareeƙ ke zaune,saidai baiga tareeƙ agurin ba.dan haka ficewa yayi daga hall ɗin yana mai takawa da sauri sosai.

Bangaren nanny ya nufa kai tsaye,yana shiga ya tarar da tareeƙ da nanny atsaye cirko -cirko,gabansa ne ya ƙara faɗuwa ,da sauri ya karasa gurin nanny yana kallonta,"nanny Ina Hulwa?"ya faɗa cikin muryar damuwa.
Kallonsa nanny tayi itama da alamun damuwa akan fuskarta tace " to magajin fada,nan da ka ganmu wllh ita muke nema,naje gurin taron can kenan,na barta tana barci,kuma ina dawowa naga bata ɗakin,na duba ko ina cikin bangaren nan banganta ba,saiga tareeƙ kuma yana tambayar ko Rashad ya shigo nan"
Da sauri Adeeb ya nufi ɗakin da fattu ke zaune gabansa naci gaba da bugawa da ƙarfi.
Ko ina ya duba amma bata nan,to ina taje?yasan dai ba yawo takeyi ba ,ba inda ta sani cikin fadar nan,ko part ɗin sa ma sau ɗaya ya kaita,da sauri ya juyo yana kallon tareeƙ," Ina Rashad yayi?"ya tambayi tareeƙ cikin wata irin murya mai kama da ta basawa.

"Yallaɓai ina zaune naga lokacin da Rashad ke waya,kuma saiya fito waje,hankalina bai kwanta da fitowar sa ba,dan haka saina biyoshi,ina fitowa na hangesu shida Zulaihat,dan haka na buya ina sauraron me zasuce,yallaɓai amma banji me suke tattaunawa ba,saidai ga dukkan alamu akwai abunda suka ƙulla tare, sai dai kuma basu sami jituwa ba,dan kuwa cikin fushi suka rabu.
Nayi ƙoƙarin bin Rashad Dan ganin inda ya nufa amma ban ganshi ba" tareeƙ ya faɗa yana kallon Adeeb cikin damuwa.

Dafe kai Adeeb yayi zuciyarsa na masa zafi,lallai idan har wani abu Rashad ke ƙoƙarin aikatawa akan Hulwa ,to zai gane kurensa wllh azeem,saiya ɗanɗani kudarsa.

Cikin sauri Adeeb ya nufi ƙofar fita daga part ɗin,tareeƙ ya na biye dashi,ganin zasu fice yasa nanny tayi saurin bin bayansu dan bazata iya zama ba.

Suna fita daga part din, kai tsaye Adeeb part din ammi ya nufa,ko fattu can ta tafi,saidai suna gab da shiga ya tsinkayi Muryar ammi na kiran sa,tsayawa yayi harta ƙaraso,"lafiya na ganku haka afujajan?gashi ka bar gurin taro ba'atashi ba?"ammi ta faɗa tana karantar yanayin Adeeb.

Ahankali Adeeb ya sauke wata ajiyar zuciya mai zafi,tare da lumshe idanu kana yace "ammi mun rasa inda yarinyar nan tayi ne ,shine zamu duba ko tana party ɗinki" Adeeb ya faɗa cikin yamutsar fuska kamar zaiyi kuka.
"Hmmmmm ji dan Allah wai akan wannan Shegiyar yarinyar suka tada hankalinsu haka,dan kawai basu ganta ba.
Tukunnama wllh sai kunga yadda rayuwarta ta koma yanzu,dan nasan Rashad ya kammala aikinsa"ammi ta faɗa cikin zuciyarta,amma azahiri,
Cikin hanzari ta riƙo hannun Adeeb tana mai zaro ido." Ikon Allah ina kuma ta nufa?dan gaskiya bata part ɗina, sai dai kuma ɗazu naga Rashad yana shawagi tsakanin part ɗina Dana nanny,Allah yasa bashine yayi mata wani abu ba" cewar ammi tana mai dafe kai cikin nuna tsantsar tashin hankali.

Gaban Adeeb ne ya fadi ,shikenan dama yasan hakan zata iya kasancewa, dan kuwa sam yau bai yarda da Rashad ba dama ,"innalillahi "Adeeb ya faɗa cikin ruɗu da tashin hankali.
Da sauri ya kunna kansa cikin part ɗin na ammi,suka rufa masa baya.

Saidai nan ma sunyi iya bincike su amma bata nan,wasa -wasa fa sune har part ɗin Rashad Amma bashi ba Hulwa,zuwa wannan lokacin Adeeb ya shiga tsantsar tashin hankalin da bazai misaltuba,gaba ɗaya fuskarsa tayi jaaa kamar manja, idanunsa sun koma kala kalan nan,idan ya buɗe baki har wani turiri zakaga yana fitowa daga bakin nasa.
Hankali kowa ya tashi,tsakanin ammi ,tareeƙ ,nanny dakuma amma ,wacce ta tsincesu abangaren Rashad,Dan itama nemansa tayi ta rasa agurin taron,shine tazo dubawa ko part ɗin sa ya dawo.

Sai kuma ta riskesu suna dubansa.sosai tashiga tashin hankali,karfa Rashad ya janyo mata wata sabuwar matsalar,amma tasan ma bai zama lallai abinda suke zargi ya kasance ba.

Cikin wani irin voice Adeeb ya juyo yana kallon amma tare da fara magana " wllh !wllh!!wllh!!! idan wani abu ya sami hulwa ta silar ɗank,i nayi alƙawarin saina illatashi,ta yadda ke kanki bazaki so ganinsa ba" Adeeb ya faɗa yana mai nuna amma da ɗan yatsanshi, tsabar masifa da bala'i kumatunsa har rawa suke.

Cikin tsoro amma ta ja baya tana mai dafe ƙirjinta ,dan kuwa ta tsorata da yanayin na Adeeb,tana kuma fatan Allah yasa ba hannun Rashad aɓatan fattu.

Can kuwa wajen taro ,anyi addu'oi,kuma anci ansha taro ya tashi lafita,abie yana ta tunanin ina iyalin nashi suka nufa ,dan baiga kowa agurin taron ba,zuciyarsa na raya masa akwai Abinda ke faruwa ,dan haka kai tsaye bayan ya sallami baƙinsa ya nufi bangaren sa ,jakadiyarsa ya tura cikin gida dan ta gano masa ko lafiya.

Adeeb yana gama korawa ammi warning yayi waje cikin zazzafar zuciya da jin jikinsa yana masa wani irin rawa,idanunsa gaba ɗaya ya rine zuwa kalar na macizai.tsoro sosai ya kama su ammi da nanny,hatta tareeƙ atsorace yake,dan bai taba ganin yallaɓan nashi cikin wannan yanayin ba.
Part ɗin sa ya nufa kai tsaye,saidai yana zuwa saitin ɗaya part ɗin na ,ammi yaji zuciyarsa ta tsananta da bugawa ,cak yaja ya tsaya tare da ƙure ƙofar part ɗin da idanunsa.zuciyarsa na raya masa ya shiga ya duba,saidai yana tunanin ammi bata fiye amfani da bangaren nan ba ,kuma me zai kawo Rashad nan ma ?
Idan kuma yazo nan ɗin da Hulwa dan kawar da tunaninka fa ?ɗayar zuciyar ta bashi amsa.dan haka ba bata lokaci ya kama handle ɗin kofar ya murza da zummar shiga,saidai kuma akulle yaji ƙofar ,hakan ya matukar bashi mamaki,dan kuwa kullum part din nan abuɗe yake ,koda ammi bata ciki akwai hadimai acikinsa.amma how comes yau zai kasance akulle haka.nan take zuciyarsa ta bashi lallai Hulwa na cikin part ɗin nan.daidai lokacin su ammi suka ƙara so gurin.kallon tareeƙ yayi cikin wata irin murya yace " na tabbata Hulwa na cikin nan,saidai ina mamakin yadda part ɗin ya kasance akulle karon farko" ya faɗa yana kallon ammi,wacce tayi wiƙi -wiƙi tsoro ya ɗan bayyana akan fuskarta.
Dan kuwa Adeeb ya kafeta da mayun idanunsa.sam ba zargin ta yake ba,kawai yana tunanin yadda aka yaudareta ne itama har akayi amfani da part ɗinta.dan baya raba ɗaya biyu cewar Rashad na cikin part ɗin.

Cikin in-ina ammi tace "habeebe a.a.a...k.wai spy ..kk...eyy " ta faɗa cikin jan numfashi.
Kallonta tareeƙ yayi cike da zargi,dan shikam harga Allah tun farko ita ya zarga dan yasan bakin nufin ta akan abun daya shafi Adeeb sarai.
Amma ma kallon ammi take cike da tuhuma,karfa tuggu ta haɗawa Rashad Dan kawai tana son ganin bayanta?

" Wai wannan wane irin wandone kika sa ?kusan minti nawa ina ƙoƙarin cirewa amma na kasa?wllh idan ma wani siddabarun kikayiwa wandon nan yaƙi fita,to zanyi abuna ahaka, dan ubanki yau ɗin nan nayi alƙawarin ,sai Adeeb yayi kwanan baƙin ciki "Rashad ya faɗa yana hankaɗa fattu kan wani ƙaton tebur dake ajiye gefen gado ,da alama an ajiyeshine ɗan ɗora kofuna ko abinci idan bukatar hakan ta taso.
Aikuwa tana fadawa ta fada kan wani glass cup, nan da nan ya tarwatse gaba ɗaya ya sossoketa aƙirjinta da wuyanta.wani marayan ƙara fattu ta sanya ,wanda koshi Rashad baiji sautin ƙaranba, dan kuwa muryarta tayi mugun dashewa.ahankali idanunta ke lumshewa yana budewa,gaba ɗaya jini ya bata farar best ɗin dake jikinta.amma bako imani bare tausayi haka Rashad yake ƙoƙarin keta mata haddi, ba tare da ya cire koda wannan skin tite ɗin ba.
Wata irin zabura Rashad yayi sakamakon ƙaran da fattu ta kwalla,wanda yayi daidai da ƙarar faduwar kofar dakin .

”RASHAD!!!!!!............"
Aka kwallah kiran sunan Rashad Wanda saida Rashad ɗin ya buge kansa ajikin tebur ɗin nan tsabar razana da yayi da wannan kiran sunan nashi da akayi......

Hmmmmm masu karatu,nima tsabar tsoro bansan sanda wayar hannuna ta fadi kasa ba,mutara zuwa gobe idan na ɗauki wayar .fatana dai wayata bata fashe ba.

Mrs babi ce💘💘
Share and comment fisabilillah

More comment
More typing.
[8/23, 9:06 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE 🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free book

Page 55/56





_________________"RASHAAADDDD"
Aka kwallah kiran sunan Rashad,Wanda saida ɗakin ya amsa.gaba dayan mutanen da suka shigo ɗakin saida suka tsorata ,saboda yadda amon Muryar ya fito da mugun ƙarfi da sauti mai firgitarwa.

Ahankali fattu da ke neman macewa ta buɗe kunburarrun idanunta da gyar,ta saukesu akan fuskar hammanta, wata shashshekar kukace ta zo mata ,numfashinta na hawa da sauƙa ,da gyar ta daga hannunta tana mikawa Adeeb ,

Da wani irin mugun sauri Adeeb yayi kanta yana mika mata nashi hannu,saidai kafin ya ƙara so tuni hannun nata ya koma ƙasa sharaff!! Ahankali kuma idanunta suka kulle ,duk wata jijiya dake jikinta tasaki,ataƙaice dai fattu ta sume.
Wani irin ƙara Adeeb ya kwalla mai matukar firgitarwa ,hayaƙi na fita ta bakinsa da hancinsa, hannun fattu ya kama ya riƙe cikin nashi tare da damkewa kamar zai balla hannun nata.
Jikinsa gaba ɗaya rawa yake kamar ana kaɗa masa gangi,ɗago da kansa yayi afusace ya sauke idanunsa akan Rashad,Wanda tsabar tsoro ya kasa koda matsawa daga kan table ɗin gashi tsirara haihuwar uwarsa.
Da sauri Rashad ya runtse idanunsa,numfashinsa na wani irin hawa da sauka kamar shima zai shide tsabar tsoron ganin yadda idanun Adeeb ya koma,ga wani irin bakin hayaƙi daya fara cika ɗakin,
Wani ƙaran Adeeb ya sake kwalla,wanda yafi na farko sanya tsoro da razani,gaba ɗaya dakin yayi wani irin bakiƙirin ,baka ko ganin hannunka bare na kusa dakai.

Su ammi da amma,nanny tareeƙ ,jakadiya,da Zulaihat wacce zuwan ta kenan,bangaren dan ta sami labari gurin
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment