Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace ƴar uwarta ita ce silar batan yarta,amma me tayiwa ammi haka da zafi?me ta tsare mata da har take burin ganin bayanta?

Cikin muryar kuka queen suhaimat tace"uktee,me nayi miki?wane laifin na aikata agareki, da har na cancanci wannan aika aikar agareki?nifa yar uwarkice ta jini,amma kika zabi ki cutar da Ni da abinda nafiso fiye da duniyata"
Cikin zafin rai ammi tace "saboda bana kaunar ki,bana sonki,na Tsaneki,ban taba sonki matsayin yar uwa ba,domin kedin mai nasarace,akan komai, ke kekiyin nasara akaina,an fifita sonki akaina,bayan haka kikazo kika auri mutumin da na ƙwallafa rai akansa,wanda nake fatan aura,amma aka aura mikishi,Ni kuma aka aura min wanda bashine cikin raina ba.suhaimat na Tsaneki,kuma nayi alƙawarin ganin bayanki, keda zuri'arki,dan kuwa ko su zayyad Allah ne ya tseratar dasu daga kaidina, da tuni na hallakasu sun bar duniyar nan"ammi ta fada tana jan numfashi da gyar,tsabar yadda take jin jiki.

Kuka sosai queen suhaimat keyi,tana jin wani irin ciwo da radadi cikin zuciyarta,yanzu yar uwar ta itace ta cutar da rayuwarta haka?wannan wane irin son zuciya ne,
Cikin kuka ta kalli ammi,yadda take fidda numfashi da gyar,ga ƙafarta ta dama sai jini take.
Tace "amma me yasa baki sanar dani kina son habib ba? Wllh Dana bar miki shi kin aura ,meyasa kika yi haka yar uwata?ina yata take ?ina kika kaita?na rokeki ki sanar dani inda kika kaita,zan tafi neman ta, koda zan rasa raina akan hanyata ta zuwa neman ta ne,hakan shine kadai zai sanya Ni farin ciki"queen suhaimat ta fada cikin matsanancin kuka,
Shi kuwa Sultan Habib tsabar kaduwa ya kasa koda matsawa daga inda yake,kallon ammi kawai yake yana jin kamar yaje ya shaketa ta mutu tabar duniyar ma kowa ya huta.

Ahankali Adeeb ya riko hannun fattu,wacce take bin iyayen nata da kallo,tun shigowar su,wani irin shauƙi da farin ciki ke dibarta, ji take ko ahalin yanzu ta koma ga mahaliccinta,tabbas tayi nasara tunda har ta ga iyayenta,wayyo Allah baffa ko kana ina ?dagaka wannan ranar da kake burin zuwanta.
Da sauri ta kalli Adeeb hawaye na zuba cikin idanunta,lumshe ido yayi tare da girgiza kai alamun kar tayi kuka,sannan ya sanya hannu yana share mata hawayen idonta,kafin yayi mata nuni da taje gurin queen suhaimat.kallonsa tayi gabanta na tsananta faduwa,amma ya jinjina mata kai tare da sakin murmushin da zai kwantar mata da hankali.

AHankali ta fara takawa,cikin hikima da fargaba,kasancewar ba wata cikakkiyar lafiya gareta ba, hakan ya kara bata damar tafiya ahankali,kallo su amma da nanny suka bita dashi,cike da tausayawa,saidai nanny tana son gano kamar wani abu ya faru da fattu,duba da yadda take takawa ahankali,kuma tana ɗan dingisawa.amma tunani da sanin da wa fattun ke tare dashi,yasa ta kawar da tunanin da takeyi,ta dauki hakan amatsayin fargaba ce kawai.

Queen suhaimat na kuka gaban,ammi tana faɗin "na roƙeki,ki sanar dani inda kika kaimin yata dan Allah "kawai saiji tayi andafa kafaɗunta .
Da sauri ta juyo tare da kamo hannun wanda ya dafata,
Fattu ta gani tsaye kusa da ita tana hawaye.
Kallon fattu tayi cikin kuka itama tace"dan Allah ƴata ko kinsan in da zan hadu da gudan jinina?wallahi itace rayuwata,bani da wani abinso sama da ita,ki taimaka min idan kina da masaniya akan ƴata"ta kai karshen zancen ta tana Dora goshinta cikin rafin hannun fattu.

Kuka fattu keyi sosai ,ganin yadda mahaifiyarta ke tsananin kaunarta,amma saboda zalunci aka rabata da ita,yanzu gashi suna tsaye tare da juna amma bata san ko wacece agabanta ba.

Ahankali Adeeb ya taka zuwa garesu,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya ɗauko wannan sarƙar,domin tana tare da shi dama.
Kallonsa kowa keyi,harda queen suhaimat,ta bayan fattu ya tsaya tare da daura mata sarƙar nan.nan da nan sarƙar ta dauki walwali da haske ,tuni tambarin hoton zuciya mai dauke da harafin s&h ya bayyana jikin sarƙa.

Cikin kasalalliyar murya ammi tace "a'a Adeeb , a'a karka daura mata sarkar nan, nayi alƙawarin suhaimat harta mutu bazata ga yarta ba,me yasa ka je kasato min sarkarnan?ashe kaine ka ɗauke sarƙar Adeeb,ka cuceni,kai amanata wayyo ni ammi na shiga uku komai ya kare"Ammi ta fada cikin yanayi na fitar hankali,wanda zamu iya cewa kwakwalwarta ta tabu.

Wani shegen kallon tsana Adeeb ya jefo ammi dashi,kafin yace"kaicona rayuwarki ammi,kin cuci kanki,kuma tun yanzu kin fara ganin sakayyar Ubangiji akanki,Allah ya isa tsaninmu dake"
Adeeb ya fadi hakan cikin zafin rai da kumar zuciya.

Tareeƙ ne ya matso ahankali yana mai bubbuga bayan Adeeb,alamun rarrashi.

Cikin tsantsar ruɗu da wani irin farin ciki queen suhaimat ke bin sarƙar da ido,kafin ta kamo sarƙar tana kalla, da sauri ta fizgi sarƙar dake wuyanta,ta kara da sarka wuyan fattu,sak!!irinsu ɗaya komai da komai,
Hakan na nuna cewar fattu itace yarta?fattu itace gudan jininta wacce ta dauki tsawon shekaru tana nema?ya salam yanzu dama soyayyar da takeji azuciyarta ta fattu,tana da nasaba da kasantuwar fattu diyarta ta cikinta?wani irin kuka ne mai tsananin karfi ya kwacewa queen suhaimat,Tana mai kamo fuskar fattu,tana girgiza kai,cikin wata irin murya mai fidda amo tace "FATIMA ZARA, da gaske kece ?kece zarana diyata abin sona?"queen suhaimat ta fada cikin yanayi na rudewa.

Cikin kuka sosai fattu ta jinjina kai tana kallon mahaifiyarta,da wata irin kalar soyayya mai narkar da zuciya.

Kankameta queen suhaimat tayi tare da kara sakin wani irin kuka mai rikitar da mai sauraro,tana faɗin"Alhamdullah ya Allah,Nagode maka ubangiji, kaine mai juya farin ciki ya koma bakin ciki,bakin ciki ya koma farin ciki,yau kukana ya ƙare ka nuna min yata farin cikina abin sona,ya Allah ka kara karemin yata karka ba azzalumai dama akanta,Fatima zata diyata,abin sona "irin kalaman da queen suhaimat keyi kenan,tana ƙanƙame fattu,kamar za'a kwace mata ita,wanda saida ta sanya kowa kuka agurin,
Cikin sassarfa Sultan Habib ya ƙaraso gurin tare da rungumesu gaba ɗaya shima yana kuka.

Duk mai imani idan yaga wannan bayin Allah ,dole ya tausaya musu,dan kuka suke bilhakki da gaskiya.fattu har neman shiɗewa take tsabar kuka.
Su sukuwa sai sum batar fattu suke tare da godewa Allah,daya bayyana musu ita cikin aminci.
Kusan minti biyar suna cikin wannan yanayi kafin abie yayi gyaran murya cike da alhini,yana jin zuciyarsa nayi masa zafi sosai,yace "Alhmdllh ba Abinda zamucewa Allah sai godiya,yanzu kam komai yazo ƙarshe,azzamar matar nan zata girbi abinda ta shuka,tsawon shekaru.dan haka akwai bukatar kowa yaje ya hutawa zuciya da jikinsa.Rashad kuyi hakuri,akan abubuwan da nayi ta nuna muka abaya kaida mahaifiyarka,sam hakan ba yin kaina bane,sharrin wanann makirar ne"abie ya faɗa yana nuna Ammi,wacce take kwance sharaf kamar gawa.

Girgiza kai Rashad yayi kafin yace "abie nima ka yafemin,domin nayi ta sanya ka cikin damuwa da tashin hankali,kuma duk sharrin ammi ne azzaluma"ya fada yana hararar gurin da ammi ke kwance sharkaf.

Matsowa gareshi Adeeb yayi tare da shafa kansa yace "Allah ya baka lafiya lilna, sannan ya kara tsaremi daga sharrin masu hali irin na ammi" da Amin suka amsa gaba dayansu.


Ko kallon inda ammi take Adeeb baisonyi,dan sosai yakejin haushin kansa ,na kasa fahimtar gaskiya da yayi tun dadewa,har ammi tayi wannan gagarumar nasara akansa.

Abie ne ya sanya wasu dakaru suka shigo dan fitar da ammi daga dakin,yace su kaita can kurkuku mafi tsanani da duhu su ƙullewa aciki.kafin ayanke mata hukunci.

Haka suka kinkimi ammi batama san inda kanta yake ba sukayi waje da ita.

Juyawa sukayi gaba ɗaya,Suna shirin barin dakin sukaji kamar motsi cikin dakin da aka kulle Zulaihat,dan haka cikin azama tareeƙ da Adeeb suka nufi ƙofar,da gyar suka balle kofar,dan sun rasa makullin.

Aikuwa suna budewa suka hangi Zulaihat kwance abakin ƙofar adaddaure, gaba ɗaya jikinta jini kaca -kaca.cikin azama suka fara kunceta,ta galabaita sosai kuma har lokacin kanta na zubda jini,

Da gyar ta buɗe idonta ta kalli Adeeb tace "my prince,karkaci abincin nan akwai guba aciki, kuma tare suka hada baki zasu kasheka"ta karasa da gyar,jini na zuba daga bakinta.

Abie ne ya ƙaraso gurin da sauri yana faɗin"Zulaihat Meya sameki haka?waye yayi miki wannan abun,kuma ammi ita da wa suka hada bakin"abie ya faɗa yana jin bugun zuciyarsa na kara tsananta,dan baisan kuma wa Zulaihat zata ce ba.

"Cikin mawuyacin hali,Zulaihat tace"Abba.....na,abba na ne,tare suke kulla komai shida ammi,karku barshi"tana faɗin haka idanunta suka kakkafe jikinta ya saki.

Cikin wani irin bugawar zuciya abie yace "w...a....z.....
Sai kuma ya kasa karasawa kawai ya zube agun asume.


Hmmmmm masu karatu wannan wace irin rayuwace ?wacce amana tayi karanci?dan uwa shine zai cutar da dan uwansa.

Allah kasa nufi karfin zuciyarmu ammen.

Mu hade next page.

Mrs babi ce 💘💘

Share and comment fisabilillah.


More comment
More typing.
[8/26, 9:50 AM] P.A: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 87/88




_______________Cikin wani irin mugun bugawar zuciya, abie ya bude bakinsa dake rawa yace "wa.....z..ii..rr"sai kuma ya kasa ƙarasawa, sakamakon numfashinsa daya dauke.nan ya zube gurin asume.

Cikin hanzari Adeeb da su Sultan Habeeb,sukayo kansa.
"Abie !abie!!Adeeb ya kira sunan Sultan yana jijjigashi.amma ko motsi bayayi,da hanzari suka zareshi suka nufi part dinsa dashi,suna zuwa likitocinsa suka rufu akansa.

Zulaihat ma asibitin cikin masarautar aka nufa da ita kai tsaye,sosai ta galabaita,dan jini sai zuba yake ta bakinta,kamar ma aman jinin take,

Queen Suhaimat,na riƙe da hannun ɗiyarta gam, dan bazata ƙara bari,fattu tayi nisa da itaba in Sha Allah.
Amma ma tabi su Adeeb dan ganin ya jikin Sultan ɗin.
Dan haka nanny ke tura keken Rashad suka fice daga ɓangaren Ammi,kai tsaye bangaren Sultan suka nufa suma,dan hankalinsu yaki kwanciya,suna buƙatar ganin ya jikin nashi.

Cikin ikon Allah kuwa aka samu Sultan ya farfaɗo,saidai banda hawaye ba abinda idanunsa keyi.
Damuwarsa ta ninka ta farko,wannan cin amana da me yayi kama?ace dan uwanka ma baka wuce ya cutar da kaiba,yanzu dama za'a iya hada baki da waziri acutar da rayuwarsa,dashi ake ƙoƙarin kashe masa gudan jininsa?lallai yau da iyayensu suna raye tabbas ba abinda zai hana zuciyoyinsu bugawa.
Duk irin so da ƙaunar daya nunawa waziri,amma ƙarshen halaccin da zaiyi masa kenan?yana tare dashi, komai nashi waziri,ko wace shawara dashi yake,ashe shikuma yana amfani da wannan damar ne yana cin dunduniyarsa?kai rayuwa Allah ya shige mana gaba.

Adeeb ne ya,zauna kusa da mahaifin nashi, tare da riko hannunsa yana kallon idonsa,cikin tattasan lafazi yake rarrashin Sultan"abie dan Allah ka kwantar da hankalinka,Ni dama najima ina zargin uncle,kuma koda muka shiga part din Ammi,Ina kallon lokacin daya zare jiki ya bar part din,Dan haka nayi saurin bada umarnin akamoshi dan dama tuni na shirya komai,yanzu haka yana hannu"Adeeb ya faɗa cikin sanyin murya yana murza hannun abie cikin nutsuwa.
Ajiyar zuciya Sultan ya sauke tare da lumshe ido,kafin ya buɗe su.
"Habeebee mutanen dana yarda dasu,su suka cutar dani,nayi dana sanin kasancewarsu makusantana,kuma na gode Allah dayasa bani da zuri'a da Ammi,da ta gurbatamin zuri'a da mugun iri,Allah Sarki matata Nazli,Allah ya jiƙanki yayi miki rahama,tare da yarana da kuma amintaccen driverna"abie ya faɗa cikin zubda hawaye yana jin zafi cikin zuciyarsa.

Haka su Adeeb da baban fattu sukayi ta rarrashinsa akan ya kwantar da hankalinsa,karya sanya damuwa cikin ranshi har yazo ya samu matsala babba.

Barcine ya dauke Sultan,dan haka suka fito zuwa babban falo,suka zauna dan tattauna yadda za'ayi.

Fattu na zaune kusa da mahaifiyarta,ta ɗora kansa akan cinyar innarta,wani irin nishaɗi da jin dadi takeji cikin ranta,wai yau itace tare da mahaifanta, lallai duk wanda ya mika lamuransa ga Allah,to tabbas zai ga daidai arayuwarsa.
Queen Suhaimat ma cike take da farin ciki,zuciyarta fess,ahankali take shafa kan fattu cike da tsantsar ƙauna,itakam tayiwa Allah godiya da wannan ni'ima da yayi mata,yau gata ga zaranta bayan shuɗewar shekaru masu yawa,ita dama bata taɓa cire rai da tsammani ba.
Suna nan zaune saiga su Adeeb sun fito daga cikin dakin,yana tura keken da Rashad ke kai,dan suna zuwa falon shima ya shiga gurin mahaifin nasu.
Tunda suka fito idon Adeeb yana kan fattu,kamar yadda itama take kallonsa,tana jin wata irin kaunarsa na ratsa dukkan sassan jiki da jininta,haƙiƙa Adeeb ya zame mata alkairi,haduwa dashi nasarace,kuma in sha Allah zata kula dashi,zata nuna masa soyayya ta gaskiya cikin amana da girmamawa.

Murmushi Adeeb ya sakar mata tare da dan shagwabe fuska,irin na nayi kewarki ɗin nan,itama murmushin ta sakar masa tare da lumshe ido alamun rarrashi,kamar yadda yake mata.
Zama yayi kan kujerar dake saitin wacce Queen suhaimat ke zaune,ta yadda zai rinƙa kallon fattunsa.
Duk abinda sukeyi nanny na kallonsu,murmushi kawai tayi tare da girgiza kai.
Queen Suhaimat ce tace "ya jikin Sultan ɗin?"
"da sauki jikinsa kam,yanzu haka yayi barci ma"Adeeb ya bata amsa cikin girmamawa.
Wayar Adeeb ce tayi ƙara, ta jikin agogonsa, dagawa yayi tare da cewa ku "shigo dashi ciki"
Ya kashe wayar.
Ko minti biyar ba'ayiba saiga wasu dakarun fadar sun shigo da waziri yana gaba suna binsa abaya,yayi tsilli tsilli da ido,kunyar duniya ta gama lalata masa zuciya,
Durkushewa yayi atsakiyar falon kansa aduƙe,yana jin kamar ƙasa ta tsage ya shige ciki.
Kallonsa kawai suke cike da alhini da jinjina rashin amana irin na waziri.
Adeeb ne ya miƙe cikin nutsuwa ya nufi gaban waziri,tsayawa yayi tare da sanya hannu cikin aljihun wandonsa, ya kafe waziri da ido,na tsawon lokaci kafin ya nisa ya fara magana"uncle ka bani mamaki,ka sanya zuciyata tunanin cewar lallai mutane ba abin yarda bane,uncle me muka tsare maka arayuwa?me nayi maka kake son ganin bayana tare da mahaifina?uncle me ka nema agurin mahaifina bai maka ba?uncle yanzu da kai za'a hada baki ɗan ganin bayan dan uwanka? Uncle why ?yaushe kazama haka?yaushe ka bari shaidan yayi nasara akanka?har idanunka suka rufe kake cutar da wanda ya aminta dakai sama da kowa?"Adeeb ya faɗa cikin salon sa mai sanya mutum shiga taitayinsu.

Kuka kawai waziri ya sanya tare da kamo ƙafar Adeeb"kayi hakuri dana,ka yafemin wllh sharrin zuciya dana shaidan ne suka sanyani aikata wannan abubuwan,da kuma kwadaituwa da son hawa karagar mulki,dan Allah ku gafarceni"ya faɗa cikin kuka sosai yana riƙe da kafar Adeeb.

Lumshe ido Adeeb yayi zuciyarsa na masa zafi sosai haƙiƙa abubuwan da su uncle suka aikata shida Ammi,sun cancanci hukunci,dan haka dole ahukuntasu.

Cikin salon sa na haɗe rai yake kallon uncle kafin yace "menene gaskiyar al'amari akan asirin zama maciji da akayi min ?"cewar Adeeb kenan yana kallon waziri.

Ɗago kai waziri yayi cikin zubda hawaye,yace "tabbas bazan boye maka ba,nine nan nasa akayi maka asiri ka zama maciji,domin farko nayi niyar ka auri yata Zulaihat,inyaso inbata guba ta sanya maka cikin abinci kaci ka mutu,sai kuma ka nuna rashin amincewa da auren Zulaihat,wannan shine ya kara tunzurani,naje gurin boka aka hada maka zazzafan asiri da kalolin macizai na duniyoyin aljanu da ban daban,wanda idan ka bar fadar nan,shikenan ka barta har abada,kuma nine da kaina na daukeka na kaika can yankin Nigeria,dan ko ganin ka bana sonyi kusa da fadar nan"waziri ya faɗa yana hawaye.

Salati gaba ɗayansu suka dauka,kowa yana Allah wadai da waziri,saboda son zuciya da abin duniya,yake kokarin hallaka dan dan uwansa.
Runtse ido Adeeb yayi cike da kumar zuciya,yama rasa me ya kamata yayi.
Daga bakin ƙofar dakin abie sukaji magana yana faɗin"waziri ka cuceni ka ci amanata ka yaudari soyayya irin ta yan uwan taka,me nayi maka haka da zafi ?kake son ganin bayana?duk irin kulawa da soyayya irin ta yaya da ƙani dana nuna maka,amma yau kaine ke son ganin bayana?kaje dan kanka,duniya zata koya maka hankali,kuma ko yanzu kasan Allah shine ke da iko akan kowa,dan gaka a ƙasa Ni kuma da iyalina muna samanka"abie ya faɗa cikin zubda hawaye yana dafa bango.

Da sauri Adeeb yayi gurinsa tare kamo hannunsa ya zaunar dashi akan kujera.
Cikin kuka waziri ya rarrafo gurin mai martaba yana bashi hakuri,
Suna cikin haka Tareeƙ ya shigo cikin dakin da sauri .
Duk waigawa sukayi suna kallonsa,
Cikin girmamawa yayiwa Sultan sannu da jiki,kafin ya isar musu da saƙon mutuwar Zulaihat .
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un,shine abinda Dukansu suka haɗa baki gurin faɗa.
Shikenan Zulaihat ta riga mu gidan gaskiya,Allah ya yafe mata kurakuranta.
Waziri kuwa daskarewa yayi azaune jin labarin mutuwar ɗiyar tasa guda ɗaya tilo,
Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima...


Mu hade anjima.
Mrs babi ce💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment
More typing.
[8/27, 7:27 PM] Aishat Anty: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE 🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 89/90




_______________Waziri kuwa,daskarewa yayi agurin,tsabar shiga ruɗu da yayi,sakamakon jin abinda tareeƙ ke faɗa.
Ihu ya sanya tare da faduwa agurin yana birgima da kuka.shikenan ya rasa yarsa, Zulaihat ta tafi ta barshi,ita kadaice ƴar da ya mallaka a duniya,yanzu gashi sakamakon mugun nufinsa ya rasata.kuka yake sosai cike da tarin nadama da dana sani.

Gaba daya sun ji mutuwar Zulaihat,cike da alhini suka dunguma har waziri,saidai yana karkashin kulawar dakaru,saboda karyayi yunkurin aikata wani abu.

Haka akayiwa Zulaihat wanka,tare da sallar gawarta aka kaita gidanta na gaskiya.sai muce Allah ya yafe mata kurakuranta.

,Kai tsaye daga gurin makoki,kurkuku aka wuce da waziri.
Sukuma suka dawo falon Sultan suka zauna.anan Adeeb ke sanar dasu Queen Suhaimat cewar akwai wanda ya rike fattu,ma'ana wanda ya tsinceta tun tana karama,kuma shine ya raineta harta girma.
Sannan shine mutumin da suka taimakeshi tare da Fattun.dan haka idan ansami nutsuwa yana son zasu tafi da fattu domin dubo halin da yake ciki.

Sultan Habeeb ne yayi gyaran murya kafin yace "ai wannan tafiya damu ya kamata ayi ta,dolene muje musaka masa da abinda yayi mana,dan kuwa ya cancanci yabo da kyautatawa agaremu"
Sultan ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah daya kula masa da ɗiyarsa.

Shiru falon yayi nadan lokaci kafin Adeeb yayi gyaran murya,yana mai kallon kowa cike jinjina maganar da yake son fadi.
Baisan ya zasu dauki maganar ba.ko zasu yarda da batun aurensa dake kan fattu?duba da yanayin shekarunta.
Dan haka cikin nutsuwa ya fara magana"Abie,uncle da sauran mutanen dake cikin dakin nan,akwai Abinda nake son sanar daku,amma bansan ta yaya zaku fahimci maganar tawaba, saidai nayi hakan ne bada wata manufa ba,saidan kare hakkin addinina.yayi shiru yana da kallon yanayin fuskokinsu,kafin ya maida kallonsa ga fattu,wacce ke jikin mahaifiyarta,ta ɗora kanta akafadun innarta,jikinta yayi mugun sanyi,dan sosai taji mutuwar Zulaihat,dan adam ba abakin komai yake ba,yanzu duba fa dazun nan Zulaihat tana raye,amma yanzu har an kaita makwancinta.Allah kasa mudace.
Haɗa ido sukayi da Adeeb wanda yake kallonta cike da kauna,yana fatan Allah yasa iyayensu su yarda da batun auren dake tsakaninsa da fattu,dan bazai iya rayuwa ahalin yanzu batare da fattu ba.
Fattu ta zama jinin jikinsa,ta zame masa,mahadin rayuwa,kuma farin cikinsa.
"Muna jinka dana, ka fadi abinda ke cikin ranka karka damu,zamu zama masu fahimtar ka"Sultan Habeeb ya faɗa yana mai dafa kafadun Adeeb,dan yana kusa dashi ne.

Jinjina kai Adeeb yayi kafin yaci gaba da faɗin"lokacin da zamu taho kasar nan da Fatima,nayi tunanin haramcin yin tafiya da yarinya mace,wacce ba muharramarka ba,dan haka,nayi shawara da tareeƙ akan cewar,zan auri Fatima in taho da ita amatsayin matata,kuma zata ci gaba da zama matsayin matar tawa,har zuwa lokacin da iyayen ta zasu bayyana.sai In sawwake mata ta koma garesu,lokacin da aka daura auren itama kanta bata sani ba,sannan tareeƙ shine wanda ya zama waliyyinta,shina bawa sadakinta,kafin aka daura mana aure.yayi dan shiru kansa akasa kafin yaci gaba"awancan lokacin nayi aurenne da nufin idan iyayen Fatima suka bayyana zan sawwake mata,saidai kuma ahalin da ake ciki yanzu,bazan iya rabuwa da Fatima ba,ina rokon alfarmar ku barmu, mu rayu tare muci gaba da zama matsayin ma'aurata,domin ina sonta"Adeeb ya kai karshen zancen sa cike da faduwar gaba,yana fatan Allah yasa su amince da batunsa.

Ajiyar zuciya suka sauke dukansu, hakika wannan batun yayi matuƙar daɗaɗa musu rai,domin Adeeb mutum ne wanda duk wasu iyaye zasuyi fatan ya kasance mijin ga yarsu,dan haka ta bangaren su Queen Suhaimat kam,ba wata matsala,dan kallon juna sukayi ita da mijinta cike da jin dadi,suna murmushi.

Abie ma abun yayi masa daɗi,saidai dole abawa yarinyar da iyayenta dama,idan sun amince da batun auren shikenan,sannan itama yarinyar sai sunji ta bakinta idan ta amince shikenan.
Amma ma taji daɗin maganar Adeeb sosai,domin ta jima tana fatan ace,inama Adeeb zai auri fattu,dan ta yaba da hankali da kuma nutsuwar fattu,saidai awancan lokacin ba damar fadin abinda ke cikin ranta.

Abie ne yayi murmushi cike da jin daɗi,kafin ya kalli Sultan Habeeb,ya fara magana"Sultan kaji abinda ɗan nata ya faɗa ko,ina fatan dai zuciyarka tana irin tunani da fatan da nakeyi, dan haka ina jiran jin ta bakinka,kaida mai dakinka"

Murmushi uncle Habeeb yayi kafin yace "ai ranka shi dade,wannan abun yayi min daɗi fiye da yadda kake tsammani,dan haka mudai ba abinda zamuce, sai Allah ya haɗa kansu,ya basu zaman lafiya, sannan ya karesu daga dukkan sharrin abin ki"ya kai zancen sa fuskarsa ɗauke da murmushi.
Wani irin sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Adeeb, Alhamdullah shikenan iyayen fattu ma sun amince da aurensu, shikenan bashi da wata matsala.
Kallonshi ya kai ga fattu,amma bai sami damar hada ido da itaba,dan kanta na duke,murmushi yayi wato fattu irin matan nan ne masu,kunyar ,hmmm zama ta ware ne ,dan shikam wllh zagewa zaiyi ya koyar da ita salon soyayya kala -kala,dan shi mutum ne mai son soyayya daga matarsa.

Hamdala abie yayi kafin yace "tunda yanzu mu Dukansu mun amince da wannan auren,yana da kyau muji ta bakin yarinyar,dan kar'ashiga hakkinta,tunda bada saninta akayi auren ba.dan haka Ƴata karki cuci kanki,ki sanar dani shin kin amince da wannan auren ko kuwa?"abie ya faɗa yana mai kallon fattu,da fatan Allah yasa itama tace ta amince.

Fattu kuwa kunyar duniya ta gama cika mata ciki,ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki,yanzu ta yaya zata amsa muce cewar tana son Hamma?tab !wllh bazata iyaba.
Gaba ɗaya dakin yayi shiru,amsar fattu kawai ake jira,saidai ba alamun fattu zatace wani abu.
Ƙuri !!Adeeb ya kure fattu da ido,karfa Hulwa ta ki amincewa da aurensa?kai baya wannan tunanin, domin yasan Hulwa na sonsa sosai bazata taba kin zama dashi ba.dan haka kallonta yake danjin mezatace.

Ganin fattu ta kasa magana sai kara sunkuyar da kanta take,yasa ammi dafa kafadunta cikin murmushi tace "karki ji tsoro yata,ba wanda zaiyi miki dole,amsarki kawai ake bukata"nan ma dai shiru fattu tayi bata ce komai ba.kunya take ji sosai.
Ajiyar zuciya abie yayi kafin yace "to alamu dai sun nuna Fatima bata amince da wannan auren ba,dan haka habeebee dole kayi hakuri ka sawwake mata"abie ya faɗa yana kallon fattu dan ganin yanayinta.
Aikuwa da sauri ta ɗago kai tana zaro ido waje,cikin muryarta mai kama da shagwaba tace "a'a Abie nifa bance bana sonshi ba,dan Allah karkasa ya sakeni,na amince Nima Ina sonshi"fattu ta faɗa cike da kuruciyarta, idonta akan Adeeb.
Gaba daya saida ta basu dariya,dan dai kawai suna cikin alhinin rashin Zulaihat ne, ya hana su darawa.amma saida suka murmusa.
Ajiyar zuciya Adeeb yayi yana mai kafeta da ido,sosai yake jin tana kara shiga cikin zuciyarsa.

Koda su Sultan zasu koma Ghana,sun bukaci tafiya da fattu, domin ta gana da yan uwanta,sannan ta dan saba dasu,amma ba jimawa zatayi ba tunda da aurenta.

Adeeb ji yayi kamar ya kwalla ihu, dan yasan zai sha wahala zama ba tare da fattu ba,amma ba yadda ya iya dole ya amince,akan idan komai yayi daidai, zaizo sai su wuce Nigeria wajen baffa.
Queen suhaimat kuwa tayi hakanne,dan tana son ta gyara yarta sosai,yadda zata kara martaba agurin Adeeb.
Cikin yanayi na gajiyar jiki da zuciya,ga tarin kewar fattu da Adeeb ya fara tun yanzu,ya mike tare da cewa"Anty bari muje dan ta shirya kayanta"ya faɗa yana kallon fattu,fuska amarairaice.

Kallonsa fattu ma keyi,cike da tausayinsa,dakuma kewarsa,amma dole tabi iyayenta,dan kuwa tana bukatar jin duminsu ajikinta,sannan tana son ta san yan uwanta.

Queen suhaimat ce ta kalli fattu tace "Zara kije ki shirya kayanki maza "ta fada tana shafa kan diyar Tata cike da so da ƙauna.

Mikewa fattu tayi,cike da kunya,tabi bayan Adeeb dan tuni yayi gaba.

Tana fita ta ganshi ya jingina bayansa da jikin bango,idanunsa alumshe.tana zuwa ta tsaya akusa dashi,tare da sanya hannu ta rike hannunsa.ahanakli ya buɗe idonsa tare da saukewa akan kyakykyawar fuskarta.baice komai ba ya rike hannun nata suka nufi part dinsa.

Suna shiga ya janyota jikinsa ya rungume tsam.ahankali yake sauke ajiyar zuciya,idanunsa alumshe.fattu ma lumshe ido tayi cike da jin tsananin so da kaunar Adeeb cikin zuciyarta.

Ahankali ya fara magana"Hulwa komai yazo ƙarshe,Allah ya bayyana mana azzalumai,mun ganesu, yanzu lokacine da nake bukatar kulawar ki da soyayya,saidai kuma gashi zakiyi nisa dani, alokacin da nake tsananin bukatarki kusa dani,Hulwa zanyi kewarki sosai"Adeeb ya faɗa cike da jin kewar fattu sosai yana kara kankameta ajikinsa.

Cike da tausayi fattu tace"Hamma nima fa zanyi kewarka, amma ai ba dadewa zanyi ba,ina son zama tare da iyayena,dan inji dadin da ake ji idan ana tare da su.amma Hamma zanyi kewarka sosai"itama ta faɗa ahankali tana mai ƙara kwantar da kanta cikin faffadan kirjinsa.

Sun jima ahaka,rungume da juna,Adeeb yana ta saukewa fattuhadda,

Please Login or Register in order to submit comment