Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matuƙar jin wahalar yin magana ,shiyasama tun farko yaƙiyi musu magana .

Kallon fattu yayi wacce ke zaune can nesa dasu kanta aduƙe,tana wasa da yatsun hannunta ,sannan ya kalli baffa ,ya kalli kayan hannunsa kuma .
Fahimta baffa yayi cewar ,yana son saka kayan ne ,kuma yana buƙatar fattu ta bar gurin,dan haka baffa yace "fattu muɗan bashi guri ya kimtsa ko"baffa ya faɗa yana mai kama hannun fattun sukayi wajen ɗakin.

Bayan fitarsu daga ɗakin,shikuwa kallon yabo kayan dashi yana juyasu ahannunsa, kusan minti uku kafin ya saka rigar ,dube dube yake ko zaiga boxern sa ,saidai ba alamun boxer aɗakin nan,dan haka ya saka wando yana mai turo baki da ɗan yamutse fuska.sauƙinsa ma ɗaya kayan wanke suke tas ɗasu,sai ƙamshin kilin suke.lol.

Koda ya saka kayan zamansa yayi a inda ya tashi tare da lumshe idanunsa ya faɗa duniyar tunani ,shikam a iya tunaninsa baisan meye dangantakar da da Waɗan nan mutanen ba,abinda zuciyarsa tafi yarda dashi shine,wata ƙila yayi hadarine suka ganshi suka taimakeshi.

Baffa ne yaji shiru baice musu ya kammala saka kayan ba,kuma ga fattu sai rawar ɗari take, dan zuwa wannan lokacin an jima da ɗauke ruwan saman da ake tsugawa,dare ya raba sosai.
Dan haka saiya ɗan leƙa cikin ɗakin.aikuwa azaune ya hangoshi ya jingina kansa da jikin katanga ,sannan idanunsa alumshe .

"Ayya ashe ma ya ida shiryawa fattu, shigo daga ciki kar mura ta mamaki naga kinata rawar sanyi,bana so kije ɗakinki ki kwanta saboda hansai idan ta ganki zata je ta sanar da lamiɗo kina nan"baffa ya faɗa yana mai tura ƙofar dakin nashi ya rufeta.

"Sannu bawan Allah"baffa ya faɗa cike da tausaya wa.

Jinjina kai kawai bawan Allah yayi ,ba tare da ya buɗe idonsa ba.

Zama baffa ya gyara ya ƙara cewa"ko zaka iya tuna wani abu daya danganci rayuwarka"?ya faɗa cike da fatan cewar bawan Allah nan bai manta komai na rayuwarsa ba.

"Ikon Allah ,saikace wanda yayi lossing memery zan manta da rayuwata "bawan Allahn ya faɗa cikin ransa,amma a zahiri ,ɗan buɗe idonsa yayi ya kalli baffa,sannan ya maida idonsa kan fuskar fattu wacce itama shi take kallon kamar ta sami talabijin.
"Kai wannan yarinyar ta cika kallo wllhda wani idanunta masu kama da ruwan Gwale"ya faɗa cikin zuciyarsa yana mai hararar fattun ,kafin ya ɗauke idanunsa daga kanta ya maida kan baffa .
Saida ya kai kusan minti biyu kafin ya buɗe baki ahankali kamar baya so yace "my name is ADEEB
MUHAMMAD ASHRAF "ya faɗa yana jinjina kansa tare da kallon baffa.gani yayi baffa yana kallonsa alamun kamar bai fahimceshiba.
Lumshe idonsa yayi cike da gajiya ,sannan yace "sunana ADEEB MUHAMMAD ASHRAF"yana faɗin haka ya mayar da kansa ya jingina tare da lumshe idanunsa.

"To- to masha Allah malam Adeeb ina ne garinku ? Baffa ya faɗa cikin gamsuwa da jin cewar shiɗin musulmine. Dan da yana ta kokwanto shin musulmi ne shi ko arne? Amma zuwa yanzu ya sami nutsuwar jin cewa shiɗin musulmine.
Shiru yayi kamar bazai yi magana ba, kafin ya buɗe baki yacewa baffa"nidan MISRA ne" ya faɗa yana kallon yadda baffa yayi zugum cike da tunanin ina yakejin Misra?
"Ikon Allah malam adeeb duk da dai Ni ba sanin Misra a ina take nayi ba,amma nasan garine mai matuƙar nisa ,to zahiri gaskiya nan kana Nigeria ne ,cikin ƙauyen ƴar ruga dake jahar Gombe"baffa ya faɗa yana kallon Adeeb wanda mamaki ya mamaye ilahirin fuskarsa , Nigeria kuma ?yaushe yazo Nigeria?bayan rabo da da Nigeria tun last year?

"Who brought me hare"?ya faɗa cikin mamaki da sanyin murya.sai kuma ya ɗan rufe idonsa tare da dage kansa kafin yace "waye ya kawoni nan?
Shiru baffa yayi ba tare da yace komai ba,na tsawon lokaci ,kafin ahankali ya nuna masa fattu yana mai cewa"haƙika wannan yarinyar itace solar haɗuwar mu dakai ,kuma anan garin ta ganka -----nan dai baffa ya bashi labarin abinda ya sani ,da kuma abinda ya faru yanzu harya koma asalin halittar da.

Tunda baffa ke magana Adeeb ya saki baki yana kallo da sauraron baffa,mamaki yake wai shine ya zama maciji?as how ? Me ya faru dashi ?waye ya maida shi hakan?ya Allah who's known how long yake cikin garin nan,ko yaya ƴan gidansu? Ko wane hali suke ciki yanzu?yasan yanzu haka hankalin amminsa yayi matuƙar tashi fiye dana kowa ,lallai dole ya bar garin nan ko ta halin ƙaƙa.

"Na gode sosai da taimakon rayuwata da kuka ,amma bani da wani masaniya akan abinda ya sameni, ina don barin garin nan gobe-dan akwai gagarumin abinda ke gabansa,saidai i promise you I will get you back,zan dawo gareku"ya faɗa cikin wani irin yanayi na ban tausayi,dan gaba ɗaya jikinsa asanyaye yake ,sannan damuwa ta cika fuskarsa taf! Da gani maganar ta shiga jikinsa sosai .
Cikin murmushi baffa yace ba komai malam Adeeb Allah yayi mana jagora ,saidai ina neman alfarma agareka"baffa ya faɗa cikin damuwa.

"Ba komai Abba ka faɗi duk abinda kake don faɗi and I promise zanyi maka shi"ya faɗa cikin sanyin murya mai cike da tarin damuwa.

"So nake ka tafi da ƙanwarka can garin naku ,domin ka taimaka mata wajen saduwa da asalin iyayenta baffa ya faɗa cikin tsantsar damuwa yana mai kallon fattu,wacce taji maganar baffa kamar sauƙar aradu .......



Masu karatu mu tara next page

Taku ce anty mammy Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.
[8/23, 9:05 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE🪱🪱🪱


Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚


Free book

Page 19/20




https://www.facebook.com/groups/1627491150723081/?ref=share_group_link

Masu amfani da face book sai kuyi join wannan group ɗin .




_______________"So nake ka tafi da ƙanwarka can garin naku,dan taimaka mata wajen gano iyayenta na asali"baffa ya faɗa yana kallon fattu ,wacce tunda baffa ya fara maganar take jin wani irin matsanancin faɗuwar gaba ,ji tayi maganar tasa ta sauƙa acikin tsakiyar kanta ,kamar sauƙar aradu,"wace irin magana baffa keyi ne haka" anya kuwa yasan me yake faɗi?kai a'a gaskiya bai gane me yake faɗi ba shima.
Fattu ta faɗa cikin zuciyarta,tana mai sauƙe ajiyar zuciya ,dan ta fahimci baffa yana nufin innar ta kenan,saidai kuma bata da wani dalilin bin mutumin da bata sanshi ba,Gara tayi zamanta agurin baffanta ,inyaso innar tata inhar ta damu da ita ,zata zo gareta.

Ahankali fattu ta buɗe bakinta tace "baffa ina ganin babu buƙatar saina bishi wani garin ,dan neman innata,zan zauna anan ɗin idan da rabon zamu gana wata rana zata zo gareni baffa"fattu ta ƙare maganarta cike da mugun bugawar zuciya ,dan har lokacin kalaman baffa na mata yawo akanta.

Ajiyar zuciya baffa ya sauƙe cike da alhini abinda zai faɗa wa fattun ,kafin yace"ayya fattu amm ki saurareni, da kyau ,ki nutsu ,kuma ki sani kowane bawa da yadda ƙaddararsa ke zuwa masa.

Haƙiƙa Ni malam bukar bani ne na haife ki ba na tsincekine tun kina yarinya ƙarama "baffa ya faɗi hakan yana mai sunkuyar da kansa cike da tausayin fattu.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un baffa me kake faɗi ne haka?dan Allah baffa kayi haƙiri idan nayi maka wani laifin ne,amma karka ƙara nesanta alaƙarka dani, baffa bazan iya jura ba,bansan kowa ba sai kai ,kai kaɗai ne gata na baffa dan Allah karka rabu dani "fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka marar sauti sosai.

Shide Adeeb kallonsu kawai yake cike da mamaki,how can that be possible ace wai ya tafi da wata yarinya har can ƙasar su ,yace a ina ya samota ?kuma ta yaya ma zai fara neman ahalin yarinyar .shifa gaba ɗayama lamarinsu ɗaure masa kai yake ,basu sanshi ba,ba wata alaƙa atsakaninsu dashi,amma yana ƙoƙarin bashi yarinya ya tafi da ita.
Kallon baffa yayi lokacin dayaji yana magana da cewa"nasan zaki shiga ruɗu da damuwa Aduk lokacin da kika sami wannan labarin fattu,saidai bani da yadda zanyi,yazama dole insanar dake gaskiyar abinda ke wakana,kisani fattu ina ƙaunarki fiye da ƴaƴan dana haifa na cikina dan kin fiyemin su sau dubu.amma son da nake miki bazai sa in cutar dake ba ta hanyar ƙin faɗa miki gaskiya fattu , kisani ahalin yanzu zamanki arugar nan akwai haɗari ,idan mai gari ya farka,kinsan hukuncin da zai zartar akanki bazai mana daɗi ba .dan haka kiyi haƙuri wllh badan cutarwa yasa nace tafi dake ba,saidan ko da baya nan to nayi niyar barin garin nan dake Dan tseratar da rayuwarki"
Baffa ya faɗa hawaye na zubowa daga idanunsa.

Kuka fattu kawai take cike da wani irin baƙin ciki marar misaltuwa, wannan wace irin ƙaddara ce ?yanzu shikenan bata ga tsuntsu bata ga tsarki,baffan da take gani matsayin mahaifinta ashe shima ba mahaifinta bane?kenan ita bata da kowa?tunda ta taso take cikin bakin ciki da damuwa ,amma ta kwance zamanta cikin wannan bakin cikin akan zuwan wannan ranar.kuka take irin wanda yake fitowa kai tsaye daga zuciya ba abinda take fata ahalin yanzu kamar ace ta farka taga ashe barci take ,tayi wannan mummunan mafarkin.to suwaye iyayenta?me tayi musu suka yarda ita?shin basa son tane ko yaya?tambayar da take tayiwa zuciyarta kenan,jikinta kuwa nan da nan ya ɗau ɓari,kan kace me tuni zazzaɓi mai zafi ya kamata.

Ahankali Adeeb ya kalli baffa na tsawon lokaci kafin ya buɗe baki cikin salonsa na rashin son magana yace "amma Abba ta yaya zaka bani ƴarka i tafi da ita ?bayan baka Sanni ba,bakasan koni ɗin waye ba ,infact baka saniba ma koniɗin mugune ,Amma kake don bani ƴarka in tafi da ita why?Adeeb ya faɗa yana kallon baffa.

Dan murmushi baffa yayi,irin wanda yafi kuka ciwon nan,kafin yace "na yarda da kai nasan bazaka taɓa cutar min da fattu ba ,dan tun kana wata halittar wacce ta kasance muguwa kake taimakonta, bare yanzu da kake cikakken mutum.sannan na jima ina addu'a akan Allah ya kawo wanda zai zama silar farin cikin fattu ,sai haka Allah ya kawo ka,alokacin da mu bamuyi tsammani ba,kuma kallo ɗaya nayi maka zuciyata ta aminta da kai ,nasan Allah ne ya karɓi addu'a ta.dan haka bani da wani kokwanto akanka." Baffa ta faɗa cikin nuna yanayi na gamsuwa akan hukuncin daya yanke.

Ahankali fattu ta rarrafe zuwa kusa da baffa ,hannunsa ta kama ta riƙe gamm!cikin nata ,kafin tace "baffa su waye iyayen nawa?me yasa suka yarda Ni?a ina ka tsinceni?ta faɗa cikin kuka tana mai jan majina.

Kallon ta Adeeb yayi cike da tausayawa,dan sosai yaji ta bashi tausayi, she's too young ace ta fuskanci wannan babban ƙalubalen.
Baffa ne ya fara magana da cewa"kafin na auri hansai na auri wata kanwata,yar gidan tayar babata. Inda muka kasance duka marayune daga i har ita.itace matata ta farko ,minyi aurene irin na haɗin zumunci,tana da haƙuri da kawaici ,muna zaune cikin aminci da mutunta juna,har Allah ya bata ciki.
Munyi murna sosai da samun wannan cikin ,tare da addu'ar Allah ya sauƙeta lafiya.

Wata rana kuwa naƙuda ta kamata,ganin yadda take shan wahala ,saina tafi jeji dan ɗebo mata maganin gargajiya tasha,ina cikin tafiya nayi nisa sosai da rugar nan,kwatsam saina fara jiyo kukan jariri,haka nayi ta bin sautin kukan harna cimma gurin.
Kwance na iskeki kinata kuka gaba ɗaya jikinki yayi ƙura, sannan kin kukkurje dan ga jini jini nan ma ajikin rigar dake jikinki,
Addu'a nayi tare da ɗaukoki na dawo gida .
Koda na dawo gida na iske matata tana kuka ga gawar jaririya nan gabanta.wato ƴar da ta haifa ta koma.
Munyi baƙin ciki sosai da rashin yarinyarmu,amma haka muka haƙura muka mikawa Allah lamarinmu. Nan na bata labarin samoki da nayi,sai naga tana ta murna da farin ciki,batayi wata- wata ba ta karɓe ki ta fara shayar dake,koda nayi magana saitace"Allah ne ya dawo mana da farin cikinmu.dan haka zamu rikeki matsayin ƴarmu da muka rasa,idan kuma munji anyi cigiyarki saimu bada ke.

Nan da nan nima na yarda da shawarar ta ,dan lokaci ɗaya Allah ya samun ƙaunarki raina. Haka na gayyato mutane akayi suturar ƴarmu,yayinda nake faɗawa Mutane cewar ƴan biyu matata ta haifa ,ɗayar ta koma sai ɗayar.

Lokacin da muka tsinceki akwai wani sarƙa awuyanki,wacce da alama zata yi matukar tsada ,dan haka sai muka cire muka ajiyeta haɗe da rigar dana tsinceki da ita.
Munsha tambaya akan ya akayi baki biyo ko ɗaya daga cikinmuba,dan kin kasance kyakyakywa wacce kaf rugar nan ba wanda ya kama ƙafar kyanki,sannan gashinki ba irin namu bane.haka dai muke samun amsar da zamu rufe bakin mutane da ita.
Shekararki biyu a duniya ,Maryama ta koma ga Allah.munyi kuka daga ni harke na rashinta, kafin daga bisani muka haƙura.

Lokacin ne na auri hansai ,wacce ta kasance ba abinda ta iya banda mugunta da baƙin hali,sam bata ƙaunar ki ,da idan tayi miki wani abun nakan yi magana ,saidai daga baya kuma sainake kasa yin maganar,koda na yunƙuro da nufin yin maganar bana iyawa.
Wannan shine taƙaitaccen tarihinki fattu na.amma na tabbata ko ba daɗe ko ba jima zaki haɗu da asalin iyayenki,jikina yana bani kun kusan haɗuwa. Wanda idan har kikaci gaba da zama cikin rugarnan, hakan bazata faru ba.zan nemeki Aduk inda kuke fattu na "baffa ya faɗa cikin kuka abin tausayi.

Fattu ma kuka take sosai kamar ranta zai fita ,"baffa ina sarƙar take "fattu ta faɗa cikin rawar murya irin ta mai zazzaɓi.
Tashi baffa yayi ya buɗe cikin jakarsa ta kaya ya ɗauko wata leda ya kunce,saiga wata sarƙa mai tsananin sheki da ɗaukar ido,sai wata ƴar riga mai kyau fara ta yara.miƙawa fattu kayan baffa yayi .

Ahankali ta karbi kayan ta rungume ajikinta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Kallonsu kawai Adeeb yake ,dan zuwa yanzu ya gama ɗaukarwa kansa alƙawarin taimakawa fattu ta kowace fuska ,har saita ga iyayenta.
Baffa kansa kukan yake ,yana jimamim rabuwa da Fattun sa.

Tashi Adeeb yayi ,cikin tafiyarsa ta izza da cike jarumta ya ƙarasa kusa da fattu ,tsugunmawa yayi akusa da ita ,yana kallon fuskarta dake ta faman kuka ,gaba ɗaya tayi jajur da ita.
Hannunsa ya sanya ya ɗago habarta ya kura mata ido,buɗe idanunta tayi itama ta sauƙe cikin nashi,sun ɗauki kusan mintuna uku suna kallon juna,kafin Adeeb ya sauke wani kwauron numfashi ,sannan ya sanya babban ɗan yatsanshi ya share mata hawayen dake zuba a idonta.girgiza mata kai yayi alamun ta daina kuka.amma sam ta kasa dainawa.
Sarƙar hannunta ya karɓa yana kallo,sarkar zallar daimond ce sai sirin kwal,da gani wannan sarƙar ta doshi millions ,koma ina yarinyar nan ta fito to tabbas ƴar gidan manya ce,in Sha Allah zai haɗata da iyayenta na asali.

Sarƙar ya buɗe tare da nufar wuyanta wanda yake nan zafi ƙau da zazzaɓi,ya ɗaura mata sarƙar.nan da nan sarƙar ta ɗauki wani sheƙi da walwali.

Dawo da kallonsa yayi kan baffa wanda yake kallon duk abinda ke faruwa,zuciyarsa tana masa wani irin ƙuna da ciwo.
Saida ya ɗauki kusan minti biyar kafin yace "Abba nayi maka alƙawarin zan taimaka wajen neman asalin iyayen yarinyarka,zamuiyi amfani da wannan sarƙa in Sha Allah everything is gonna be ok"ya faɗa cikin muryar sa mai daɗin amo .

Hannunsa baffa ya kama cikin farin ciki yace "na gode Allah yayi maka albarka,ka kulamin da fattu karka bari ta cutu "

Jinjina kai yayi shima yana mai riƙe hannun baffan, akaro na farko ya ɗanyi murmushi.masha Allah masu karatu bakuga yadda yayi wani sihirtaccen kyau ba,Dan murmushin ba ƙaramin kyau ya ƙara masaba.

Kwanciya fattu tayi akan sallaya ta juya bayanta tana ta kuka da rawar zazzaɓi,shikenan yanzu haka zata bi wannan bawan Allah da batasan koshi waye ba,meyasa iyayenta suka yarda ita?me tayi musu haka da zafi?dama baffa ya fasa ƙidurinsa na cewar saitabi wannan bawan Allah mana.

Baffa ne ya miƙe tsaye da sauri tare da leƙawa ƙofar ɗakinsa, dan tabbas yaga gilmawar mutum,aikuwa yana leƙawa ya hango zanin gwogwgo hansai tana shigewa ɗakinta. Ya Salam kenan taji duk abinda suke tattaunawa ?lallai dole su bar gidan nan kafin gari ya gama wayewa.dan yanzu kam asuba ta kawo kai,

Da sauri ya koma ɗakin yace "Adeeb akwai matsala,yanzu yanzu zaku tashi ku dau hanya,dan kuwa hansai taji duk abinda muke tattauna,kuma na tabbata ko bari bazata yi gari ya gama wayewaba zata je ta sanar da mai gari"

Baffa ya faɗa cikin tashin hankali da damuwa.

Shikuwa Adeeb ko ajikinsa ƙara gyara zama yayi ,dan bazai iya kwanciya anan gurin ba ,kafin ya kalli baffa ya ɗan taɓe baki yace "and so what idan ta faɗa masa"?
Ya faɗa cikin ko in kula.

"Bazaka gane zalumcin lamiɗo ba Adeeb zai iya sawa kashe fattu ,dan Allah ku tashi muje In fitar daku hanya ku tafi, ka taimaka min ka ceci rayuwar yata"baffa ya faɗa cikin kuka yana durƙusa akan gwuiwoyinsa.

Da sauri Adeeb ya tashi ya kama baffa ya miƙar dashi yace "is ok Abba zamu tafi yanzu.ya faɗa yana mai kamo hannun fattu ya miƙar da ita tsaye.

Ita kuwa fattu yadda yake jin zuciyarta bayani ace mai gari yasa a kasheta Bama,koba komai zata huta da ƙuncin zuciya da damuwa.tana mikewa tayi baya zata faɗi,dan gaba ɗaya ba ƙarfi ajikinta.da sauri Adeeb ya tallafi ga zuwa jikinsa,kallon fuskarta yayi wacce ta kumbura ,sai rufe idanu take tana buɗe wa,da gani tana shan jiki sosai.

"Muje bawan Allah ,fattu daure kinji"baffa ya faɗa cikin ruɗu ,ba abinda yake ɓukata irin yaga sun bar rugar nan.

Ganin fattu zata ɓata musu lokacine yasa Adeeb ya ɗagata sama tsak!kamar ƴar tsana ya saba akafaɗarsa yacewa baffa" muke Abba"

Wata leda Baffa ya dauko,tare da rigar nan ta fattu ya cusa ciki,sannan yayi waje suka rufa masa baya......


Masu karatu me zakuce game da rabuwar baffa da fattu?

Mrs babi ce💘💘
[8/23, 9:05 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄



MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)


Elegant online writers📚📚



Free book

Page 21/22





_______________Wata leda Baffa ya ɗauko ,ledar da ɗan nauyi ,alamun wani abune acikin ta .sannan ya ɗauki wannan rigar ta fattu ya cusa acikin ledar,safin yayi waje ,Abeed ya rufa masa baya.


Ahankali baffa ke takawa Abeed na biye dashi,saɓe da fattu akafaɗarsa,wacce ke cikin matsanancin hali na zazzaɓi,da damuwa.

Tafiya suke cikin sauri bayan sun bar gidan ,cikin ikon Allah basu haɗu da kowa ba ,har sukayi nisa da garin sosai,saida baffa ya fitar dasu kan kwalta kafin ya tsaya .

Har zuwa wannan lokacin fattu na saɓe akan kafaɗar Abeed ,duk da irin uban nisan dake tsakanin rugar da kwalta.

Ahankali Abeed ya sauƙe fattu ya ɗan jingina ta da jikinsa,dan yaga bazata iya tsayuwa ba .

"Malam Abeed karɓi wannan wasu yan kudadene da nake tarawa saboda irin wannan ranar,nasan zasu toshe muku wata kafar,dan Allah ka riƙe min alƙawari, ka kulamin da fattuna,karka bari wani ko wata ya cutar da ita,sannan kayi iyakar ƙoƙarin ka wajen sadata da magaifanta.
Kaima zaka sami lada"baffa ya faɗa yana kallon bayansa ,hanyar da suka baro ,dan tsoro yake kar yaje ko anbiyosu,dan yasan zuwa yanzu labari ya isa kunnen lamiɗo,tunda gari yayi haske an kusan shiga sallah.

"In Sha Allahu Abba zan kula da amanar ka,na gode da taimakon da kukayimin, sannan zan dawo gareka very soon"Abeed ya faɗa cikin nutsuwarsa da rashin son magana,akwai abubuwan da yake son faɗa amma tsabar rashin son maganarsa bazai iya ba dan haka yayi shiru daga wannan maganar.

Hannun fattu baffa ya kama yariƙe gam-gam cikin nashi,kallon ta yayi yayinda itama take kallonsa cikin kuka wanda muryarta ko fita batayi sosai, shima baffa tuni zuciyarsa ta karaya ,sai hawaye sharrrr!!

"Allah ya shiga lamarin ki fattu, Allah ya karemin ke ka yasa damu da alkairi,ki kula da kanki,ki kama mutuncinsu.Allah yayi miki albarka"baffa ya faɗa cikin kuka sosai,abin tausayi.

"Baffa bana son tafiya ,dan Allah kace na zauna ,Ni nafison zama da kai akan iyayena ma asali,baffa karka tafi ka barni "Fattu ta faɗa cikin kuka harda shashsheka kamar zata shiɗe. Kafin baffa yayi magana saiga wata mota zata wuce ,da alama daga cikin Jos take .

Da sauri baffa yayi musu hannu alamun su tsaya.tambayarsu yayi ina suka nufa ,mai motar yace Kano.

Kallon Adeeb baffa yayi yace "duk da bansan inane Kanon ba amma Gara kubi wannan motar kafin tawagar mai gari su fito nemanku.

Kai kawai Abeed ya ɗada,tare da kamo hannun fattu suka nufi motar,hannunsa ɗaya riƙe da ledar da baffa ya basu.

Kuka fattu take harda ihu tana faɗin"wayyo baffana ,banason tafiya,dan Allah baffa kace na dawo wayyo baffa am wayyo Allah na ,wayyo rayuwata "
Baffa kam ko magana ya kasa tsabar kuka sai daga musu hannu kawai yake yana juya kai.
Abeed ne ya sanyata cikin motar tare da riƙe ta ,ɗan sai ƙoƙarin fitowa take ,haka mai motar nan yaja motarsa yayi gaba,dan kaya zaije ɗaukowa.

Baffa yana tsaye har saida yaga ɓacewar motar ,sannan ya sauke wani kwauron numfashi yana mai share hawayen idanunsa,"Allah ga amanar ƴata nan na miƙa lamarin ta ahannunka ,ya ubangiji kazama majiɓancin al'amarinta "baffa ya faɗa yana mai juya dan koma gida ayi wacce za'ayi.

Aikuwa tun kafin ya ƙarasa cikin garin ,ya hango cincirindon mutane aƙofar gidansa,jinjina kai yayi,dan dama yayi tsammanin hakan .
Suna hangoshi sukayo kan suna wllh koya fito da ƴar Shegiyar daya ɗauka matsayin ƴarsa ,da kwarton ta da suka ajiye agida,ko kuma su kashe shi yanzun nan.

Kallonsu yayi cikin kamala da dattako yace "ikon Allah me kuma mukayi dazaku kashemu?wace yarinyar kuke nema?bayan wacce mai gari ya riƙe agurinsa?baffa ya faɗa kai tsaye ba nuna alamun tsoro.
Nan wani lawwali yace masa"ai jiya yarinyar nan saida ta bari dare ya raba sannan ta sami lamiɗo tayi masa jina jina,gaba ɗaya ƙafafunsa sun ƙarye,ga hannun damanshi ma ya ɓalle baral, sannan ta gudu,kuma munsan tabbas tana gidan nan,dan kuwa hansai ta kai labari,
Kuma ta fayyace mana komai game da yarinyar ,ashe Shegiya ce ka tsinto ka kawo gidanka,sannan ka ajiye mata wani gardin suke lalata dashi,dan haka gaba ɗayanku yau sai hukunci ya hau kanku,dan lamiɗo yana nan banda ihu ba abinda yake yana kiran maciji zai kashe shi,fattu ce tayi masa ture.sannan arɗo ma yana can hannunsa guda ya shanye ya zama kamar sillan kara ,kuma duk aikin fattu ne ,dan haka yau wllh saimun kashe fattu"lawwali ya ƙare zancensa yana mai ɗaga sandarsa sama.

"Toh me yasa baku shiga kun duba fattun ba ?idan nan ta dawo,ita wacce ta kai muku rahoton saita faɗa muku inda fattun take"baffa ya faɗa yana ƙoƙarin shigewa gida.

"Ƙarya yake wllh, saidai in ya boyesu ,ko kuma sun gudu ,dama naji yana cewa su gudu dan haka karku taga masa " na tsinkayo muryar gwogwgo hansai na faɗin haka ,dan taji mugun haushi da ba'a sami su fattu cikin gidan ba.
Aikuwa baffa yana tsaye
Ba zato ba tsammani yaji sun rufeshi da duka ta ko ina.
Har saida suka kaishi ƙasa.sannan suka taitayeshi sai gurin. Mai gari.suna zuwa suka tarar ana yiwa mai gari ɗori sai ihu yake yana kuka.dan haka can ɗakin hukunci suka jefa baffa,wanda yayi kaishi sosai dan ya daku.
Allah Sarki baffa ,Allah ya saka maka.


Fattu kuwa tsabar kuka har muryarta ta dashe,can jikin ƙarshen motar ta koma tare da haɗe kai da gwuiwa tana kuka marar sauti ,jikinta sai rawa yake ,fuska ta kumbura suntum tayi jajur ,abinka da farar fata.

Abeed yana daga gefe yana kallonta ,sosai yake jin kukanta har cikin ransa,haƙiƙa yarinyar tana fuskantar ƙalubalen rayuwa and she's to Young to handle the situation.amma ya zatayi?dole ta ɗauki ƙaddara yadda yazo mata.

Kallonta yayi yadda jikinta ke ta rawa tana shashsheƙar kuka,yaso ace ya iya rarrashi, daya rarrasheta ,koba komai itaɗin yanzu amanarsace,amma Gara tayi kuka ,koba komai zata rage jin raɗaɗin da taleji cikin zuciyarta.

Tafiya suke sosai ,Dan drivern gudu yake tsulawa,kasancewar safiya ce hanyar ba motoci sosai,sai jifa-jifa suke cin karo da motocin.

Abeed yayi shiru ,tare da jingina kansa jikin kujerar da yake zaune,ba abinda ke yawo cikin zuciyarsa,sai labarin da baffa ya bashi na cewar wai shiɗin amaciji suka ganshi,to ta yaya?yaushe hakan ta faru,me yasameshi? Tabbas idan har abinda baffa ya faɗa gaskiya ne baya raba ɗayan biyu cewar sharrin Amma ne wannan ,dan ita kaɗai yake tunanin zata iya cutar dashi ,tunda afili take nuna masa ƙiyayya, amma zaibi abin ahankali harya gano mugun ƙullinta akansa kafin ya ɗauki mataki.

Ya rasa me ya tsareta Amma arayuwa sam bata ƙaunarsa ,kullum burinta ta cutar dashi,tun yana ƙarami yake fuskantar tsangwamarta,har kawo yanzu bata fasa ba ,amma akwai lokacin da ko ance tayi masa wani abun bazata iyaba.

Juyowa yayi ya kalli inda fattu ke zaune ,har zuwa wannan lokacin kuka take ,banda rawa ba abinda jikin ta keyi.wani tausayine yaji ya kama zuciyarsa ,wannan kukan yayi yawa zai iya haifar mata da matsala.dan haka ahankali ya ɗan matsa kusa da ita ,ƙureta yayi da ido ,yana son yayi mata magana amma baisan me

Please Login or Register in order to submit comment