Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa idanu,wato breast ɗin fattu.

Saidai kafin hannunsa ya sauƙa ga inda yayi nufin ,yaji wata irin shaƙa da tunda yake arayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin irin makamancin wannan shaƙar a aduniya ba.
Ta ko ina yaji shi aɗaure dam-dam kamar ƙullin buhun goro.

Cikin azaba da fizgar magana mai gari yace "wayyo Allah hannuna,na shiga uku wayyo zan mutu" ya faɗa idanunsa azazzare kamar zasu fito tsabar azaba.

Cikin hanzari fattu wacce idanunta ke rufe, ta riga ta gama fitar da rai ta sadaƙar cewa yau shikenan ta rasa budurcinta ,dan ta san ba mai zuwa ya ceceta ,koda tayi ihu ba mai jin sautin ihunta,sakamakon ruwan saman da ake tsugawa.ba zato ba tsammani tajiyo ihun maigari lokacin da maciji yayi sama dashi ya cilla shi can gefe guda ,bayan tabbatar da cewa mai gari ya suma.ji kake ƙasss-ƙasss,hannu da ƙafar mai gari na bangaren dama sun karye.

Da sauri fattu ta kalli inda akayo jifa da mai gari dan tabbatar da cewar shiɗin ne kokuma yaya.aikuwa cikin wani irin farin ciki da murna ta yunƙura da ƙyar ta zauna tana kuka da dariya,sai kuma ta tafi gareshi cikin rarrafe tana zuwa inda macijin ke tsaye yana huci ya ƙure mai gari da ido,da alama yana son ganin maigari ko zaiyi wani motsin ne yaje ya ƙarasashi,duba da yadda yake ta uban huci ya kafe mai garin da ido.
Fattu na zuwa ta wani kwaƙume macijin zuwa jikinta ,ta ƙanƙameshi tana kuka kamar ran ta zai fita,kukanta na dalilai biyu ne,dalili na farko shine ganin macijinta na nan araye ba mutuwa yayi ba,kuma masu neman shi basu ganshi ba.na biyu kuma yadda yazo ya kawo mata ɗauki adaidai lokacin da ta fidda rai da cewar zata rasa abu mafi muhimmanci arayuwarta.

"Ina ka shiga mai taimakona?na shiga damuwa na rashin ganinka, naji tsoron ko sun kamaka sun kashe ,dan Allah karka ƙara yin nesa dani na tsawon lokaci irin haka,kalli yadda suke son kawar min da budurcina, bansan me na tsare musu ba ,kowa nufinsa ya cutar dani,kai kadai ke sona,sai baffana ,bana son na rasa ɗaya daga cikinku ,kune rayuwata,farin cikina da jin daɗina,mai taimakona ina sonka har cikin zuciyata, ba ruwana da kasancewarka wata halitta ta daban,Dan kafiyemin halitta irin tawa sau dubu"duk cikin kuka fattu ke faɗin Waɗan nan maganganu,yayi da take ƙanƙame da macijinta kamar zata maida shi cikinta.yadda ta ƙanƙameshi, kai kace uwace ake ƙoƙarin rabata da ɗanta.

Ahankali macijin nan ke sauƙe wani irin numfashi kamar yana hurawa fattu iska mai sanyi ,da alama dai rarrashinta yakeyi,dan yadda yake huro iskar yana wani rufe ido da buɗewa shine zai fahimtar da kai cewar rarrashinta yake .
Zare jikinsa yayi daga ƙwaƙwumar da fattu tayi masa ya zagaye west ɗinta ,Amma Sam bai matseta ba ,sannan ya shigo da kanshi ta ƙirjinta yana kallon fuskarta yadda hawaye yayi faca -faca kan kyakkyawar fuskar tata.kallon -kallo ake tsakanin fattu da macijinta ,kallo yake mata irin na tausayawa dan abin mamaki ne sosai idan kaga yadda ya wani marairaice fuska yana ƙifta idanunsa tare da ɗan matso da kansa saitin fuskarta,sai kuma ya kwantar da kan nashi saitin da hawayenta ke tsiyaya, ta ɓangaren dama, sannan yayiwa ɓangaren hagun ma haka.

"Dariya mai haɗe da kuka fattu take yi cike da tsantsar ƙaunar wannan halitta ,hannu ta sanya ta share hawayen daya ƙara zubowa tace "na daina kukan mai taimako tunda baka so ,bazan ƙara ba ka gani ma ko "ta faɗa tana mai ƙara shafe idanunta ,saidai wasu hawayen na ƙara zubowa.

Zare jikinsa yayi yana mai hawa kan wuyanta zuwa kanta saiya leƙo da kansa ta saman kanta ,idan ta ɗago da nufin kallonsa saiya silale ya koma wuyanta ya ɓoye kansa abayanta.
Dariya fattu take cikin farin ciki da ganin cewar wai wasa yake mata dan ta sami nutsuwa ta daina kukan ,dan haka lokacin daya ɓoye abayanta sai tace "wayyo ni fattu mai taimakona ya ɓata, ya zanyi da rayuwata ,ina kake abinsona shikenan masu son cutar dani zasu sami dama akaina wayyo ga mai gari nan ya taso"ta faɗa cikin yanayi kamar tana son yin kuka .aikuwa cikin sauri macijin nan ya haye kan cinyarta yana mai fasa kai da wani kalle -kalle ya miƙa kansa can ya dawo dashi can yana huci.

Dariya fattu tayi tace "nima ramawa nayi tunda ka boyemin " ta faɗa cikin shagwaɓa kamar wacce ke gaban baffanta ko innarta.

Juyowa macijin yayi yana kallonta sai kuma ya ɗora kansa daidai saitin zuciyarta yayi lamo ,tare da rufe idanunsa.ahankali ta sanya hannu tana shafa kyakyakywan jikinsa mai matuƙar santsi da laushi.kusan minti biyar suna haka,yayinda ake tafaman zuga ruwan sama ,can gefe kuma mai garine shame shame akwance baya motsi.kallon mai gari fattu tayi ,sai taji tsoro ya cika zuciyarta,kodai shima mutuwa yayi, dan ita tama manta da batunsa aɗakin sam,idan kuma ya farka ya ƙara dawo mata fa ,gara fa su gudu daga ɗakin nan tun kafin jama'a su ankare dasu.
Cikin muryar tsoro tace "mai taimako ya kamata mu gudu gida karya farka ko wani yazo ya gammu dashi ahaka"ta faɗa tana kallon macijin dake kwance akan ƙirjinta,da alama kuma yana jin daɗin kasancewarsa ahakan.

Ahankali ya ɗago kansa tare da silalewa ƙasa yayi hanyar ƙofar fita daga bukkar,wacce mai gari ya barta abuɗe tsabar jaraba na cinsa.
Binsa fattu tayi da sauri ,harta fita saikuma ta dawo ta ɗauke tocilan nan ta mai gari ,dan taga garin yayi baƙi ƙirin kuma har lokacin ruwa ake.

Suna fita fattu ta kama sauri -sauri gudu-gudu ,tana tafe tana haska tocilan ɗin nan ,yayinda mai taimako ke biye da ita cikin salon nashi gudun ,saidai suna tafe yana zagayeta ,dan bata kariya ta kowacce kusurwa.

Suna zuwa gida kai tsaye fattu ɗakin baffa ta nufa,tana zuwa ta shiga ɗakin ahankali tana haska tocilan ɗin hannunta.Allah sarki baffa yana kan sallaya ya ɗaya hannunsa sama yana ta addu'a,juyowa yayi dan ganin hasken da ake haskowa.

"Waye anan"ya faɗa yana kunna tashi tocilan ɗin.
Ai da sauri ya miƙe tsaye yayi kan fattu,yana mai cewa"fattu kece alhmdllh fattu na ba abinda ya sameki,?ina mai garin?waye ya fito dake?baffa ya jero mata waɗannan tambayoyin alokaci guda yana mai shafa kanta cikin farin ciki .

Ahankali fattu ta kalli gefenta ta ƙasa inda macijin nan ke nannaɗe ya fasa kansa yana kallon baffa.tace "baffa wannan ne ya taimakeni, kuma shine macijin daya hukunta su jauro "ta faɗa tana haska macijin da tocilan.

Da sauri baffa yaja baya yana faɗin"subhanalla fattu wannan ai MACIJINE ,meye haɗinki dashi,matsa daga gareshi maza karya cutar dake" baffa ya faɗa cikin tsoro yana mai kamo hannun Fattu.
"Baffa ka kwantar da hankalinka ,ba abinda zai min ,domin mun jima tare dashi,zauna baffa in baka labarin haɗuwata dashi ,sannan baffa macijin nan yana cikin matsala ,dan da alama anyi amfani dashi wajen yiwa wani asiri.

Zama baffa yayi ahankali kan sallarsa ,idonsa akan macijin nan ,daya matso kusa da fattu wacce ke zaune kusa da baffanta,kallon ikon Allah baffa keyi, yadda macijin nan yayi kane-kane akan cinyar fattunsa ya waniyi lub kamar jariri akan cinyar mahaifiyarsa.
Kallon fattu baffa yayi ,yaga ko ajikinta saima hannu data ɗora akan bayan macijin tana shafawa.

"Ina jinki fattu faɗa min komai dan hankalinta ya kwanta"
Nan fattu ta fara bashi labari tun daga farko har kawo yanzu.
Sannan ta ɗora da cewa "baffa dan Allah mu taimaki wannan macijin dan wllh yana cikin matsala ,bakaga yadda ya koma ba lokacin dana ke masa karatu,mu cire masa wannan masifar dake jikinsa"ta faɗa tana nunawa baffa waɗannan layun dake wuyan macijin.

Cike da mamaki da al'ajabi baffa ke kallon macijin ,wanda ya ƙara kafewa jikin fattu yana kallon baffa da kuma fattu.baffa yace "haƙika akwai wani ɓoyayyen al'amari dangane da wannan macijin ,kuma in sha Allah zamu taimaka masa iyakar ƙarfin mu,tun kafin mai gari ya farfaɗo ya ɗauki matakin kashe macijin nan ,yanzu kije kiyi alwala ki dawo,dan mu fara aiki akansa.

Cike da ɗoki fattu ta amsa da" to baffa na ina godiya agareta sosai"sannan ta ajiye macijin gefen baffa tace "mai taimako ai kasan baffana ko?to katsaya agurinsa yan zu zan dawo kaji"ta faɗa cikin murmushi tana shafa bayansa.
Kallo ta kawai yayi kafin ya kwantar da kansa ajikin gangar jikinsa dake nannaɗe.

Bayan fattu tayi alwala ta dawo dakin ne ta gabatar da sallolin dake kanta ,sannan tayi addu'ar samun nasara akan ceton macijin nan ta shafa.sanna ta juyo gurin baffa wanda ke ta tofa addu'a cikin wata ƙwarya ,zama ta gyara tana mai kallon baffa da jiran ya kammala addu'ar sa.

Shikuwa macijin nan yana ganin fattu ta zauna ya silalo ya dawo kan cinyarta ya kwanta,gaba ɗaya jikinsa asanyaye yake,kamar wanda yake tsoron faruwar wani abu.kallonsa fattu tayi tace "mai taimako ba abinda zai sameka ka kwantar da hankalinka ,in Sha Allahu zamu cire maka duk wani sihiri da akayi amfani dakai wajen yinsa"ta faɗa tana mai shafa lallausan san jikinsa mai santsi.

Miƙa mata kwaryar nan baffa yayi yace karɓi wannan fattu ki yayyafar masa ajikinsa ,kinayi kina karanta ayatul kursiyyu da falaƙi da nasi, duk abinda zaki gani karki tsorata kinji ?"baffa ya faɗa yana mika mata kwaryar,dan shikam ya gama fahimtar abubuwa da dama aka. Macijin nan.

Karɓa fattu tayi cikin nutsuwa ta fara karatun tana kuma shafa masa ruwan rubutun nan ajikinsa.

Ikon Allah,ai da fara shafa masa ruwan nan ajikinsa ya fara wani irin motsi da jijjiga ,yana murɗewa ,baffa kuma saiya ci gaba da addu'a yana tofa masa.
Ahankali hannun Fattu ya kai kan waɗaɗan na layin dake wuyan macijin nan,aikuwa damƙarsu tayi da Bismillah ta fizge da ƙarfin gaske.
Wata irin ƙara da guguwa ne suka turnike dakin gaba ɗaya baka iya ganin komai sai duhu.....

Masu karatu mutara gaba dan jin ya zata kaya.

Takuce dai Mrs babi💘💘
[8/23, 9:05 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 15/16

Albishirinku masoya,ga dama ta samu ga mai buƙatar a tallata mata hajarta,to ashirye nake dan tallata mata cikin farashi mai sauƙi,dan haka idan kin shirya sai kiyimin magana .

________________Wata irin ƙara da guguwa ne masu matuƙar ƙarfi da firgitarwa , suka cika dakin.ta yadda koda tafin hannunka baka iya gani tsabar duhun da ɗakin yayi,ga guguwa sai juyawa take aɗakin.
Ko kaɗan hakan bai tsorata baffa ba ,saima cigaba da yayi da karanto ayoyin shifa daga cikin alƙur'ani mai girma yana tofawa asaitin dayasan macijin nan yana gurin ,duk da duhun daya mamaye ɗakin.

Fattu kuwa wani irin tsorone da fargabar suka baibayeta , jin yadda macijin nan yake wata irin murɗewa da sakin wani sautin ƙara mai ban tsoro ,sannna kuma sai takejin yana ƙara mata nauyi sosai akan cinyarta.
Cikin tsoro da ruɗewa ta lalubo hannun baffa tace " wayyo baffa tsoro nakeji,wllh kamar yana rikiɗewa ne zuwa wata halittar ,yayimin nauyi akan cinyata baffa, baffa ina tsoron kar wani abu ya faru"Fattu ta faɗa cikin rawar murya mai cike da tsoro.

Hannunta baffa ya riƙe shima cikin yanayi na son kwantar mata da hankali yace"karki damu Fattu ba abinda zai faru sai alkairi,kici gaba da karanto addu'oi kina tofa masa in Sha Allah komai yazo ƙarshe "baffa ya faɗi hakan tare da ci gaba da karanto zafafan addu'oi yana tofawa macijin.

Fattu ma ɗaurewa tayi taci gaba da karanto addu'ar tana tofamasa, jikinta sai rawa yake,yadda takejin alamun sauyin halittar da macijin nan keyi.idanunta arufe gam-gam.

Kusan shuɗewar mintina biyar zuwa bakwai, duhun nan ya fara yayewa ,ahankali hasken tocilolin su baffa ya fara gauraye dakin.

Salati baffa ya farayi da ƙarfi da kiran sunayen Allah yana mai kabbara. "La'ilaha illallah muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasallam,ya Allahu Ya rahmanu ,ya hayyu ,ya ƙayyum,Allahu akbar, Allahu akbar "abinda baffa keta faman faɗi kenan cike da ta'ajibi da jinjina wa ƙudurar Ubangiji,cikin hanzari ya janyo zanin rufuwarsa ya lulluɓawa maciji ,daga cikinsa zuwa ƙasansa dan ba kaya ajikinsa.

Jin yadda baffa ke tafaman kabbara da salati ne ,yasa Fattu buɗe idanunta cikin nutsuwa da kuma jarumta ,har zuwa lokacin bata fasa karanto addu'oi ba.akan fuskar baffa ta sauƙe idanunta ,gaba ɗaya baffa ya shiga al'ajabi da mamakin abinda idanunsa suka gane masa.dan har lokacin yana kallon macijin ne ƙuri kamar ya sami talabijin.

Ahankali Fattu take sauƙe idanunta zuwa kan cinyarta,wata irin bugawa zuciyarta tayi ,lokaci ɗaya komai nata ya tsaya cak. Sai wata irin rawa da jikinta ya kama kamar zata karkarye,ta ɗauki kusan minti biyu cikin wannan halin kafin taja wani dogon numfashi tana mai buɗe baki tace"ba.....f..ff..fa ...mumm.......tttuummm....nnnee.....a..Mamman.cc.....iiii.....sai kawai ta sulale ta faɗi ƙasa daga zaunen da take.
Ba komai bane ya sanya Fattu shiga cikin wannan halin ba , face ganin wani zankaɗeɗen haɗaɗden saurayi ,fari ƙal-ƙal da tayi kwance ya kifa cikinsa akan cinyarta,maimakon macijin dake kwance akan cinyar ta ta.

Kuma wannan shine dalilin salati da baffa keta rafkawa cikin kushu'i da tsarkake baiwa da buwayar mahalicci.lallai duniya ta zama abinda tazama ,yanzu mutum ne aka mayar dashi dabba?maciji?kuma ga dukkan alamu wannan ba ɗan yankin nan bane ,dan ko kaɗan baiyi kama da mutanen mu ba.
Ahankali baffa yayi kokarin janye shi daga kan cinyar fattu ya kwantar dashi rigingine akan tabarmar.
Hannu baffa ya sanya ya gyara masa zanin daya lulluɓa masa dan rufe masa al'aurarsa.sannan ya ture gashin daya lulluɓe fuskar mutumin.
"Masha Allah ,watabarakallahu fi ahsanil kaliƙin"baffa ya faɗa adaidai lokacin da yayi arba da fuskar kyakyakywan matashin mai cike da haiba da kwarjini,ga kyan zati.

Kallonsa baffa yake ƙuri yana jinjina kai cike da mamaki da alhini,lallai duniya abin tsoroce, rayuwa bata da tabbas,Allah ka karemu,ka rabamu da sharrin maƙiya da mahassada. Baffa ya faɗa acikin zuciyarsa yana kallon bawan Allahn.

Ruwa baffa ya ɗebo ya yayyafawa fattu ,ahankali ta fara motsi tana buɗe idanunta ,tar ta buɗe idanun ta sauƙesu akan baffa, kusan minti biyu tana kallon baffa.
"Sannu Fattu kinji?tashi ki zauna kiga ikon Allah ,tashi kiga taimakon da kikayiwa rayuwar wannan bawan Allahn.
Baffa ya faɗa yana nuna mata inda macijinta yake kwance.
Zabura tayi ta tashi zaune cikin tsoro tana kallon inda baffa ya nuna mata,da sauri ta matso kusa da baffa ta riƙe shi gamm! Jikinta sai rawa yake tace "na shiga uku baffa wllh aljani ne wannan ba mutum bane, daga maciji ya koma siffar mutum ,baffa wllh bamu san me zai koma ba nan gaba ,baffa atsorace nake"ta faɗa idanunta yana zubar da hawaye.

Ahankali baffa ya kamo hannunta yace "habaFattun baffa ,kin manta ne?macijin nan ne fa ,wanda yake taimakonki cikin hukuncin ubangiji, shine kuma kikejin tsoro yanzu?kin manta da halaccin sa gareki?meyasa bazaki tsaya tare dashiba?alokacin da yake buƙatar taimakonki kema?ki kwantar da hankalinki Fattu ina ji ajikina wannan bawan Allah shine zai zame miki bango kuma tsanin da zai haɗaki da innarki"baffa ya faɗa cikin yanayi na son kwantar mata da hankali.

Murmushi Fattu tayi cikin kwarin guiwa tace "hakane baffa ,kuma zan kula da bawan Allahn nan in Sha Allahu ,harya sami lafiya"ta faɗa cikin kwarin guiwa,saidai har zuwa lokacin tsorone fal cikin ranta.ahankali ta matsa kusa da macijin saidai can nesa kaɗan dashi ta zauna .

Kallonsa take cike da mamakin tsantsar kyan da Allah yayiwa wannan bawan nashi, ita kam tunda take arayuwarta, bata taɓa ganin wani mutum mai kyan wannan bawan Allah ba.
Dan duk kyanta da ake faɗa ,tayi imani bata kama koda ƙafar wannan bawan Allahn ba.

Ahankali ya fara motsi yana ɗan juya kansa hagu da dama.sai kuma ya fara ɗan fizge fizge kamar yana ƙoƙarin tuna wani abunne ko kuma yana son farkawa daga wani mummunan mafarkin .

"Baffa kaga abinda yake "Fattu ta faɗa cikin zabura tana kallon baffan.

Wata yar jarka baffa ya ɗauko ya buɗe ,ahankali yafara shafa masa ruwan dake cikin jarkar. ahankali maciji ya sauƙe wata ajiyar zuciya mai ƙarfi yana sauƙe numfashi ahankali ahankali.

Addu'oi baffa yake tayi cikin wasu magunguna kala-kala yana shafawa bawan Allah nan da yake kwance ,wanda zuwa yanzu jikinsa yayi sanyi,ba kamar dazu da yayi zafi ƙau-ƙau ba.
Tun daga ƙafafuwansa Fattu ke kallonsa har zuwa fuskarsa,masha Allah.
Wannan mutumin ya haɗu ta ko ina ,anya ma wannan ba haushene?ko bafulatanine irin mu?kai gaskiya wannan bayajin Hausa ko fulatanci,ohhh Ni Fattu yanzu wanann macijina ne haka ?dama da mutum nake ma'amula ashe?waye wannan bawan Allahn?su waye sukayi masa wannan shirin haka?me yayi musu ?inane garinsu?meye sunansa?waɗan nan sune tambayoyin da Fattu ke buƙatar amsarsu ,saidai ba mai bata amsar sai wannan bawan Allah.

Baffa ma tunani yake wannan bawan Allah daga ina yake? ,waye yayi masa wannan sihiri?koma dai menene yayi masa maganin da duk sihirin mutum bazai yi tasiri akanshi ba da yardar Allah.

Suna nan zaune jigum jigum, cike da fatan Allah yasa ya farka ba tare da wata matsalar ba,kawai suka ga ya fara motsi karo na biyu,saidai wannan karon ba fizge -fizgen yake ba ,kawai dai ya ɗan riƙe kansa yana kuma yatsina fuska.

Ido suka ƙura masa ba wanda yayi magana ,daga Fattu har baffa,kowa yayi shiru yana kallon ikon Allah.

Ahankali bawan Allahn nan ya fara bude idanunsa yana ɗan lumshesu ,kafin ya buɗe su tar kamar lantarki dan tsananin haske da sheƙin da suke yi.
Ƙur ya ƙure rufi bukkar dakin baffa da idanu,baya ko ƙiftasu,tunani yake ina ne nan?waye ya kawo shi nan?kuma yaushema suka zo nan ɗin?

Yunƙurawa yayi ya tashi zaune ahankali yana cije light pink lips ɗinsa .kallon ɗakin yake cike da mamaki ,har ya juyo zuwa inda su baffa ke zaune shida Fattu sunyi masa ƙuri suna kallonsa,baffa ya fara kalla cike da rashin sani.

"Sannu bawan Allah ka tashi ?meke maka ciwo yanzu ?me kake ji ajikinka" baffa ya faɗa lokacin da suka haɗa ido da bawan Allahn .

Ahankali bawan Allahn ya lumshe idanunsa tare da jingina da jikin bangon ɗakin.yana mai dafe kansa ,dan ciwo yake masa sosai.

"Ayya Fattu inaga fa wannan bayajin hausa ,kuma bayajin filatanci miƙamin wannan kwaryar In bashi magani ,da alama kanshi ke ciwo.
Cewar baffa kenan, dayaji yayi magana amma bawan Allahn bai bashi amsaba.

Ahankali Fattu ta miƙe ta ɗauki kwaryar ta miƙawa baffa ita ,tana mai cewa "baffa gashi,kuma kamar ma yana jin yunwa ko ?kaga yana shafa cikinsa"ta faɗa tana kallon yadda bawan Allah ke shafa cikinsa zuwa ƙirjinsa wanda gashi yayi kwance luf-luf akai.

Ahankali bawan Allah ya ɗago kansa yana kallon saitin dayaji sassanyar muryar Fattu na tashi.

Aikuwa karaf idanunsa suka gauraye cikin na juna ,wata irin faɗuwar gabace ta ziyarcesu alokaci guda, da sauri bawan Allahn ya kawar da kansa yana mai dafe ƙirjinsa,dan sosai ƙirjinsa ya buga.

Bangaren Fattu ma kuwa,wata irin bugawa ƙirjinta yayi, wacce har saida taji numfashinta ya ɗauke ,wani jiri ne ya ɗebeta ,tayi baya luuuuuuu zata faɗi,ƙara ta kwalla cike da jin tsoro tana mai runtse idanunta, saidai kuma kafin ta kai ƙasan taji ta faɗa kan wani lallausan abu mai kama da katifa tsabar laushi.
Ahankali ta buɗe idonta ta sauƙesu akan.........

Muje zuwa masu karatu yanzu muka fara.

Taku ce dai anty mammy
Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah

More comment
More typing.
[8/23, 9:05 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MACIJI NE🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚



Free book

Page 17/18




______________Ƙara fattu ta kwalla cike da tsoro,dan ta saddaƙar kawai ta gama faɗuwa,saidai kuma maimakon tajita akan ƙasa ,saitaji ta faɗa kan wani abu mai matuƙar taushi kamar katifa.

Da sauri ta buɗe idanunta dan ganin inda ta faɗa,cikin mamaki take kallon bawan Allah nan,dan hannunsa ta faɗo, lokacin da yaga tayi baya zata faɗi ,bai ma san lokacin daya zabura yayi kanta ba ,tare da tareta ta faɗo akan hannunsa .

Kallon kallon sukewa juna basa ko ƙiftawa, yayin da bawan Allah ya zazzaro idanu waje ,irin wanda idan mutum yaga abin tsoro ɗin nan.

Ita kuma fattu mamaki take yaushe ya taso yazo gareta harya tare ta ?bata kai ga faɗuwa ƙasa ba?

Baffa ne yayi gyaran murya tare da faɗin "subhanallah,fattu sannu, Allah ya taƙaita wahala da tuni kin faɗin ƙasa ,bawan Allah sannu kaji,kana fama da kanka amma zuciyarka mai tsafta bazata bari wani ya cituba,ina mai godiya gareka"baffa ya faɗa cike da jinjinawa bawan Allah nan,lallai akwai wani abu da Allah ya ɓoye tsakaninsa da fattunsa, haƙiƙa fattu kam,zuwa yanzu ta sami mai taimako,kuma yanzu ne ya kamata su fara neman dangin Fattu ,dan zuciyarsa na raya masa wannan bawan Allah alkairine ga rayuwar fattunsa.

Ahankali bawan Allah ya miƙar da fattu tsaye ,yana kallon ta sai dai fuskarsa sam ba walwala ,da alama dai irin mutanen nan ne marasa yawan fara'a .

Fattu kuwa da sauri ta juya baya tana mai dafe ƙirji ,dan hango zanin da baffanta ya lulluɓawa mutumin a ƙasa,kuma da alama bai ma san zanin ya daɗi ƙasanba.

Da sauri shima ya ankare cewar ba zanin fa ajikinsa ,wato yana tsaye tsirara ne.cikin azama ya durƙusa ya ɗauki zanin yana cukuikuyewa ajikinsa, idonsa akan fattu yana fatan Allah dai yasa wannan yarinyar bata ganshi haka ba,dan ma dakin ba wani haske sosai.dan tocilolin sun kalli wani direction ɗin ne da ban.

Zama yayi cike da jin haushin yadda zanin jikin nashi ya daɗi kasa,wai ma to ina kayansa ne?me yasa y ganshi haka ba kaya ne?

Daga kanshi yayi yana kallon baffa daya miƙa masa kwaryar da fattu ta miƙa dan abashi magani.

Karɓa yayi shikam nadan yasan menene aciki ba , kallo yabo kwaryar dashi,yana jin wani irin tashin zuciya ,dan kwaryar ta tsufa sosai ,tayi baƙi saboda ruwam rubutun da ake zubawa a cikinta.

"Maza ka shanye bawan Allah zakaji sauƙin ciwon kan"baffa ya faɗa yana nuna masa alamun ya sha da hannunsa ,dan gani yake kamar bayajin me suke faɗi.

Kafa kansa yayi yana shan maganin ,bayan ya runtse idanunsa.saida ya ɗansha da yawa kafin ya miƙawa baffa kwaryar.
Saidai ko minti ɗaya baiyi da sha ba ,ya kama yunƙirin amai.aikuwa tasss ya mayar da maganin nan,sannu kawai baffa ke masa.
Juyowa fattu tayi lokacin daya fara aman, dan tunda ta juya musu baya bata ƙara juyowa ba,saida taji yana aman.
Ahankali ta buɗe bakinta tace "sannu hamma"ta faɗa ahankali.

Kallonta yayi ,tare da kawar da kansa can gefe yana jingina da jikin katangar karan,ba tare da yayi magana ba .itama bata damu da sai yayi maganar ba,dan su tunaninsu bayajin me suke faɗi.

Cikin nutsuwa fattu ta gyara gurin da yayi aman,kanta aduke ,har zuwa lokacin gabanta yaɗuwa yake .shi kuwa bawan Allahn nan yana daga jikin bango Ya lumshe idanunsa ,kamar mai barci.saidai duk abinda fattu keyi idonsa na kanta,mamaki yake da irin kyan da yarinyar ke dashi,gata da nutsuwa komai nata gwanin burgewa.tana da hankali bata da rawar kai duk da ƙaranci irin na shekarunta.dan ya san wannan bata wuce 14/15ba amma Masha Allah,tana kyan diri irin na cikakkun mata ,kalli hips ɗinta kamar wanda aka ɗora mata shi Dass abinta. Jikin fattu ne kawai ya bata cewar kallo ta mutumin nan keyi,dan haka ahankali ta ɗago kanta ,shikuwa daidai lokacin ya ɗan ƙara buɗe idanunsa yana kallon ɗan ma dai-dai cin lips ɗin ta, masu taushi , sai sheƙi suke.aikuwa carab ta kama shi yana mata kallon ƙurillah.
Ɗan hararar ta yayi tare da kawar da kansa ,aransa yace "wannan ta cika kallon mutane "
Kuji fa masu karatu ?ko tsakanin shi da fattun wake kallon wani?
Da sauri fattu ma ta kawar da kanta,azuciyarta tana mai cewa "kuji min mutum shi yana kallon mutane amma kuma baya son akalleshi"

"Abba waye yakawoni nan?kuma me nakeyi anan?sannan kuma ina kayan?

Baffa da fattu suka ci
tsinkayi murya mai shegen daɗi da amon sauti cikin nutsuwa.da mamaki gaba ɗaya suka bishi da kallon ,ba wanda yayi magana dan sai sukaga kamar bashi yayi maganar ba ,dan yana yadda yake bai ko buɗe idonsa ba lokacin da yayi maganar.

Jin sunyi shuri ba wanda yayi magana ne ,yasa bawan Allah buɗe idanunsa da suka ɗan yi ja kaɗan yana kallon baffa,sannan ya ƙara maimaita tambayarsa cikin Hausarsa da bata fita sosai.

"Ashsha -ashsha ikon Allah yaro ashe kana jin Yaren Hausa ?Alhmdllh.sannu kaji bari na baka kaya saika saka,inyaso zuwa wayewar gari nayi magana kaji"baffa ya faɗa yana mai buɗe wata tsohuwar bakonsa ,kaya ya daukowa bawan Allah nan ,waɗanda dasu yake zuwa sallar juma 'a .wani yaɗi ne yollow share dashi ,anyi masa ɗinkin riga da wando dogaye .miƙa masa baffa yayi yace "kasa Waɗan nan tukunna yanzu kaji"

Karɓar kayan yayi yana mai ƙare musu kallo,to ina nashi kayan da za'a bashi Waɗan nan kayan wani iri dasu haka?ɗari kansa yayi ya kalli baffa yana son yayi magana ,amma sam ya kasa,dan ba ɗabi'arsa bace yawan magana ,yana

Please Login or Register in order to submit comment