Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaice mata ba.
Kusan minti uku yayi yana kallonta da yadda jikinta ke rawa sosai,kafin ya sanya hannunsa ahankali ya dafa kanta .
Da sauri fattu ta ɗago kanta agalabaice ,idonta ya mugun kumbura yayi jaaa!sosai lips ɗinta sai sheƙi yake .kallonsa tayi wani sabbin hawayen na kwararowa daga idanunta.
Dan yatsansa ya sanya ya share hawayen dake zuba daga idanunta,amma wasu na ƙara zubowa.

Da gyar ya buɗe bakinsa cikin hausarsa da bata fita sosai yace "menene"ya faɗa yana kallon cikin idanunta ,gabansa sai bugawa yake,ya rasa mai yasa inhar zai sanya idonsa cikin nata ,to gabansa yayi ta bugawa kenan.

Cikin dasashshiyar murya wacce kuka ne yasanya ta dashe fattu tace "Baffana" cikin yanayin shagwaba irin na masu kuka tayi maganar.
Wani yummmmmm!!!Adeeb yaji tun daga tsakiyar kansa har babban dan yatsan ƙafarsa.dan yanayin yadda tayi maganar sai yaji wata irin kasala ta kama shi.
Ahankali ya kumshe idanunsa yayi jimmm!kafin ya buɗe su ya ɗora akan fattu"is ok ki daina kuka"ya faɗa ahankali yana mai janyowa zuwa jikinsa ,dan shikam hakan kaɗai yake ganin zai yi mata tayi shiru.
Allah Sarki fattu kuwa tayi luƙus akan faffaɗan ƙirjinsa sai ajiyar zuciya take sauƙewa,kuma cikin ƙanƙanin lokaci ta fara jin zuciyarta nayi mata sanyi, tana nan kwance ajikinsa barcin wahala yayi gaba da ita.

Shikuwa Adeeb gaba ɗaya jinsa yake wani irin,sam ya kasa samun nutsuwa jinta da yayi cikin jikinsa ,gaba ɗaya yaji yanayinsa na sauyawa zuwa kasala da jin wani abu mai kama da feeling ,ahankali ya jingina kansa jikin kujerar ,tare da kumshe idanunsa yana mai ƙara gyara mata kwanciyarta. Tunanin Abie ya fara yi aƙokarinsa na kawar da abinda yake ji acikin jikinsa ,dan aganinsa wannan yarinyar tayi ƙanƙantar da har zai rinƙa jin wani abu akanta,saidai sam jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai,dan ji yayi lamarin na ƙara rikice masa,ganin ba sarki sai Allah yasashi cire ta daga jikinsa ya jingina ta da jikin kujerar da suke kai.
Ajiyar zuciya ya sauƙe yana mai kallon kyakyakywar fuskarta ,wacce ta ƙara wani jaaa!sosai ,ahankali ya sauƙe idanunsa zuwa lips ɗinta waɗanda ta ɗan turosu Baga cikin shagwaɓa kamar kamar yadda yara keyi idan suna son yin kuka.

Haka kawai ya tsinci kansa da sakin wani murmushi mai ƙayatarwa, hannu yasa ya gyara mata hulɗar kanta,wacce ta ɗan zame har gashinta na gaban goshi yasami damar fitowa .

Bai ankara ba yaji driver na cewa sun iso Kano,kallon garin yake ,yana tunanin inda zasu sami hotel ,dan su ɗan huta sannan ya sai kaya ya cire wannan na jikin nashi,dan sun matuƙar takura masa.

Tambayar drivern yayi nawane kuɗinsa ya faɗa masa ,bashi yayi cikin wanda baffa ya basu da zasu taho, sannan yace wa mai motar dan Allah hotel yake son zuwa .

Nan mai motar ya tare musu dan adaidaita yace ya kaisu hotel mafi kusa. Ganin fattu na barci yasa Adeeb bai tashe ta ba kawai ɗauki ta yayi kamar ƴar tsana ya shiga adaidaita ya zauna ,sannan itama ya zaunar da ita.kuma ko buɗe ido batayi ba ,dan barcin sosai ya kamata.

Bayan sunje ne ya kama musu ɗaki, sannan ya nufi ɗakin ,har lokacin kuma fattu na rike ahannunsa dan baya don tashi ta daga barci.

Da hannu ɗaya yayi amfani wajen bude dakin sannan ya shiga,kwantar da ita yayi akan gadon ya lulluɓawa da ƙarin bargon dake kan gadon,sannan ya ɗan zauna shima yana mai lumshe idonsa ,gaba ɗaya agajiye yake jinsa , dan bai saba irin wannan tafiyar haka ba.

Fita yayi ya siyo musu kaya a store ɗin cikin hotel ɗin sannan yayi musu odar abinci ya dawo,fattu nata barci taji laushin gado da katifa ga ƙaton bargo .lol

Tashi yayi ya shiga bayi yayi wanka,ya faɗa sosai kafin ya fito,agurguje ya sanya kayan daya siyo ,riga da wando ne na jins da boxers and singlet, sai turare ,sannan yayi sallar asuba.
Masha Allah duk da bayani shiri yayi ba ,amma karkuso kuga irin kyan da Adeeb yayi ,sosai ya ƙara zama cikakken Balarabe mai tsananin kyau,sai ƙamshi yake zubawa.

Kwankwasa ƙofar dakin akayi, ahankali ya tashi yaje ya buɗe ,abincin da yayi odar ne aka kawo,kaɓar yayi ya dawo ciki.
Kallonta yayi yaga bata tashi ba ,dan haka ya zauna yana cin abincinsa.kaɗan yaci ya tashi ,da alama bashi da yawan cin abinci sosai.

Gadon da fattu ke kwance ya nufa ,ahankali ya ɗan yaye bargon daya rufa mata,hannunsa yasanya saman goshinta,har lokacin jikinta da zafi sosai.
Filin da take kai ya ɗan bubbuga sau uku, ahankali ta buɗe idonta tana mai turo baki ,sai kuma tayi saurin tashi tana ƙarewa ɗakin kallo ,wai aljanar duniya nan ɗin shine gidansu hamma Adeeb ?lallai yan gayune su,ji laushin gado kamar auduga.fattu ta faɗa cikin zuciyarta tana mai ƙarewa dakin kallo.

Ji dan Allah yadda take ta wani kallon daki kamar bata taɓa ganin daki ba "Adeeb ya faɗa cikin zuciyarsa yana ɗan kallonta.
"Go and get your shower" Adeeb ya faɗa ahankali yana mai kawar da kansa .

Kallonsa take ƙuri tana rarraba ido,dan bata fahimci me yake cewa ba.
Jin bata tashiba yasa shi dan juyowa yana kallonta.
"Ɗan harararta yayi kafin yace " nace kije kiyi wanka ne"ya faɗa fuskarsa aɗaure ba walwala.

Tashi fattu tayi sumi-sumi ta nufi hanyar fita ,tana zuwa bakin ƙifar taja ta tsaya tare da juyowa yana kallonsa.

Shima kallonta yake cike da jin haushi ko ina zata kuma?nace take tayi wanka.
Ganin irin kallon da yake mata ne yasa tace "bazan iya budewa ba"ahankali tayi maganar cikin dasashshiyar muryarta kanta aƙasa.

Harararta yayi cike da jin haushin wai yaje bakin ƙofar fita, kuma tana faɗin bazata iya buɗewa,sai kace nan ne toilet ɗin.

Tashi yayi ya nufi bakin ƙofar toilet ɗin ya buɗe sannan ya juyo yana kallonta.
Shiru tayi itama tana ɗan kallon nasa,dan bata gane nufinsa ba.
Wata iska ya furzar mai zafi yana lunshe idonsa,kafin yace "zo kishiga "ya faɗa yana kallonta ,fuskarsa sam ba walwala,shi wllh ya gaji da wannan shirmen nata fa.

Kanta adurƙushe tazo ta shige toilet ɗin , kayan daya siyo mata ya ɗauki tare da ɗan kwankwasa toilet ɗin ya buɗe kadan yace "take"
Fattu kuwa da tun shigar ta toilet ɗin ta saki baki galala tana kallon ikon Allah,anya kuwa yasan inda ya buɗe mata yace tazo tayi wanka?yo wannan ai Dakin kwanan ne,kalli da harda wani ƙaton gado mai rami,to ma ta a ina zataga ruwan bare har tayi wankan?
Juyowa tayi tana kallon farin hannunsa daya miƙo mata leda.ƙarasawa tayi kusa dashi ta karɓi ledar sannan tayi saurin cewa "inane banɗakin?

"What " ya faɗa yana mai buɗe kofar gaba ɗaya ,sannan ya kalli fattun ko fara wankan ma batayi ba.
Cikin faɗa -faɗa yace "do you expect me to West my time here?Ina jiranki?"ya faɗa yana zaro mata manyan fararen dara-daran idanunsa.

Nan da nan jikin fattu ya kama rawa ,tsoro ya kamata ,har kayan hannunsa saida suka faɗi ƙasa" duk da batasan me yake cewa ba ,tabbas ta san faɗane yake mata ,cikin muryar kuka tace"dan Allah hamma kayi haƙuri bansan a inda zabga ruwan ba"ta faɗa tare da fashewa da kuka tana mai toshe bakinta.

Shiru yayi yana kallonsa,lokaci guda kuma tausayi ta ya kamashi, sai yanzu ya tuna daga inda ya taho da ita,ba abin mamaki bane idan tace bata san ya zata yi ba.dan haka cikin sanyin murya yace "is ok daina kuka "ya fadi yana mai ƙarara shigowa toilet ɗin.

Idan kina son yin wanka nan zaki danna ruwa zai zubo, sannan idan kina biyan buƙata nan zaki zauna ,In kin gama saiki dannan nan ,wannan na wanke bakine and ga soso da soap kin gane "ya faɗa yana kallonta .

Kai ta ɗaga masa alamun ta gane ,
Hanyar waje ya nufa sannan ya juyo yace mata "kiyi sauri yanzu zamu wuce"yana faɗin haka yayi waje.

Zama yayi abakin gadon yana mai dafe kansa,ciwo yaji kansa nayi , sakamakon wannan doguwar maganar da yayi, gaskiya kula da yara akwai wahala ,ji yadda tasa masa ciwon kai rana ɗaya kawai.

Fattu kuwa bayan ta cire kayanta na gado ,wato rigar fulaninta ƴar dingila da zanin ta ,kai tsaye gurin soso da sabulun nan ta nufa ta ɗauka sanna tazo ta tsaya saitin gurin da akace idan ta danna ruwa zai zo ,dannawa tayi tana jiran taga ta ina ruwan zai zubo,ai ba zato ba tsammani kawai taji ruwa akanta shaaaaaa!!!

Wata zabura da fattu tayi tare da watsar da soso da sabulun nan ta kurma uban ihu iya ƙarfinta ta nufi kofar fita ba komai ajikinta "wayyo Allah na hamma wayyo kazo ka buɗe ni na shiga uku dakin yan shan jini ka kawoni ana min ruwan jini akaina wayyo hamma am" abinda fattu ke faɗa kenan cikin rikicewar da tashin hankali gaba ɗaya jikinta rawa yake kamar ɗan mazari.

Adeeb na kwance a gefen gado yayi nisa cikin tunani kawai ya biyo ihunta ,ai baisan lokacin daya zabura da mugun sauri yayi toilet ɗin ba,yana zuwa ya buɗe kofar da da sauri ya danna kansa ciki.

Kicibis sukayi da fattu abakin ƙofar, tayo gunsa ga gudu tana kuka.

Wani irin bugawa ƙirjin Adeeb yayi kansa ya hau juyawa ,sakamakon ganin da yayiwa fattu haka zirr ɗin ta ba kaya.tunda yake arayuwarsa yau ya taɓa ganin mace data fara girma haka ba kaya agabansa. Cikin hanzari ya juya bayansa yana mai dafe ƙirjinsa dake barazanar fashewa."innalillahi "ya faɗa cikin sassarfa lokacin dayaji fattu ta kankameshi tana kuka.

"Sosai shima jikinsa ya hau rawa kamar ɗan mazari,cikin rawar murya yake faɗin"le..a...ve. me... Lea....ve... M....e" yana kasa nutsuwa yayi mata magana.

Fattu kuwa banda rawa ba abinda jikinta keyi,wannan wace irin masifa ce haka?wane irin gida ya kawota ,za'a cinyeta ya sama.

Runtse idanun Adeeb. Yayi da mugun ƙarfi yana ambaton sunan Allah ,ya ɗauki kusan minti biyu cikin halin ruɗewa da rawar jiki.gaba ɗaya jikinsa yayi wani iri,kafin yayi ƙarfin halin sanya hannunsa dake rawa ya fizgota daga bayansa tare da tureta can gefe guda,yana mai sauƙe numfashi cikin sauri ,kawar da kansa yayi daga gareta yana mai cewa"kisa zani ki rufe jikinki Please.
Fattu kuwa cikin rawar jiki ta ƙara matsowa gareshi sam tama manta da batun wasu kaya,"dan Allah ka fitar dani daga ,Ni gurin baffana zani "ta faɗa cikin kuka.

"Kisa zani nace miki"ya daka mata tsawar data ƙara hargitsata.tsugunnawa tayi tare da ƙanƙame jikinta tana kuka.
"Ni ka kaink gurin baffana dan Allah ka maidani gurin baffa "abinda take daɗi kenan cikin kuka da rawar jiki ,gaba ɗaya ta gama tsorata .

Zanin nata Adeeb yaje ya yayumo cikin lalube,dan ko gani batayi sosai .yana zuwa ya lulluɓa mata sannan,ya fice daga bayin, da gyar ya iya ƙarasawa kan gadon yana zuwa ya faɗa kan gadon tare da duƙunƙune jikinsa yana rawar sanyi ......



Masu karatu mutara next oage.

Ina ganin comments ɗinku masoya ta ko ina ,ina matukar jin daɗi da ƙaunarku ga wannan novel ɗin .

Na gode sosai Allah ya bar ƙauna ,

And I love you guys where ever you are🥰🥰🥰🥰

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘
[8/23, 9:05 PM] +234 813 465 3007: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄

MACIJI NE 🪱🪱🪱

Na mammy kabeer
(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book

Page 23/24

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

_________________Kwanci Adeeb yayi akan gadon ,tare da duƙunƙunewa guri ɗaya ,jikinsa kuwa banda rawa ba abinda yake ,idanunsa arufe ruf!
Ba abinda yake gani cikin idanunsa face hoton surar fattu.
"Ya Salam ! Ya Allah save"Adeeb ya faɗa ahankali yana mai riƙe matarsa data ke masa wani ciwo na lokaci guda.

Fattu kuwa tana jin fitarsa da sauri itama ta fito tana kuka.jikin madubi taje ta tsaya tana kallon yadda ya faɗa kan gadon tare da dunƙulewa yana rawar sanyi,cikin ranta take rayawa kodai baida lafiya ne ?ko shima zazzaɓin yake ?
Ganin idan ta tsaya zancen zuci saita shekarar agurin,gashi batayi sallaba.
Dan haka cikin tsoro da fargaba ta fara takawa zuwa jikin gadon ,tana zuwa taka ta tsaya ,tare da sanya bayan hannunta ta share hawayen daya silalo daga cikin idanunta.

Cikin sanyin murya tace "hamma zanyi sallah" ta faɗa kanta a ƙasa.
Yana jinta yayi shiru abinsa, yana ci gaba da jin yadda matarsa ke masa ciwo tana ƙullewa,ahankali yake karanta addu'oi cikin ransa ,fatansa kawai ya daina jin wannan azabar da kuma yanayin dake bibiyar ilahirin jikinsa.

Kusan minti biyar fattu na tsaye kanta aƙasa ,jifa jifa tana share hawayen dake zubowa daga idanunta.aranta kuwa cewa take "wannan hamma wllh baida kirki ,san ba bakinsu ɗaya da macijina ba,dubi yadda nayi masa magana ya wani shareni.

Shikuwa Adeeb yana kwancene yana ci gaba da ambaton sunan Allah,harya samu marar ta kafa masa ,sai wani uban gini dake karo masa agishinsa ,duk da sanyin a.c dake ɗakin hotel ɗin.
Ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya yana ɗan kumshe idanunsa.kafin ya tashi zaune yana mai dafe da kansa.

Ganin ya tashi zaune yasa Fattu ɗan ja da baya,dan ita tsoronsa ma takeji yanzu ,dan wllh da gani masifaffene.

Kallon gefen ta yayi ba tare da ya lalle ta kai tsaye ba,sannan ya ɗan ja tsaki yana mai yamutsa fuska da turo baki,kamar wani mace ,sannan ya miƙe ya shiga bayin ,ruwan wanka ya haɗa mata cikin boket dan yasan ba iya shiga kwamin wannan zata yi ba, sannan ya ɗauki sisi da sabulu ta ajiye mata .ya ratsa makilin acikin sabon burush sannan ya ɗan leƙa cikin ɗakin .tana tsaye kamar gunki ,har lokacin share hawaye take ,kumshe ido yayi yana mai cewa, wannan ta cika kuka ,cikin ransa.

Kafin ya buɗe baki ahankali yace "zo" ya faɗa kamar baya so.badan Allah yasa Fattu mai saurin ji bace da bazata ji me yace ba.
Ahankali take takowa cikin yanayi na tsoro,dan dai tana tsoron masifarsa ne da ba abinda zai sa ta koma wannan ɗakin da ake ruwan jini.

Shiga tayi tare da tsayawa tana kallonsa.jikin sink ya matsa tare da miƙa mata burush ɗin yana mai cewa "oya wash your mouth"
Shiru fattu tayi tana kallonsa tare da kallon burush ɗin data karɓa daga hannunsa.

Kallon ta yayi shima fuska aɗaure yace "wanke baki" ya faɗa cikin ƙosawa ,yana jinjina ƙauyanci irin na fattu wai ko burush bata sani ba.

Ita kuwa fattu kallonsa tayi tare da kallon burush ɗin ,cikin ranta tace ikon Allah ,su nan da wannan abun suke wanke baki,mutuwa saidai hawaye da gishiri.ƙara kallonsa tayi suka haɗa ido,da sauri kowa ya kawar da kansa ,cikin shagwabar da fattu batasan tana da ita ba tace "hamma Ni ban iya wanke baki da wannan ba"ta faɗa tana miƙa masa burush ɗin.

Wani yarrrrr yaji ajikinsa, saboda salon yadda tayi maganar ,saiyaga kamar da gangan take wani abun.harara ya salla mata kafin ya karɓi burush ɗin yace "open your mouth"
Gurun fattu tayi tana kallonsa ba tare da ta buɗe bakin ba.
Runtse ido yayi cikin ciwon rai yace da ɗan ƙarfi"haaaaaa"ya faɗa yana bude dan madaidaicin bakinsa.

Buɗe nata bakin tayi kamar yadda taga yayi, wanda yake nan ɗan mitsitsi kamar gidan tsutsa ,haƙora ta farare tass dasu,ajere reras.

"Masha Allah "Adeeb ya faɗa cikin rashin sanin ya furta hakan.
Saida ya faɗa kafin ya ankare.kallon fattu yayi suka haɗa ido,harara ya watsa mata yana mai cewa"kaki cinyeni da wannan lulu eyes ɗin naki"Adeeb ya faɗa yana mai sanya burush ɗin cikin bakin fattu.

Ahankali yake wanke mata haƙoran nata masu kyau da ɗaukar hankali,yana wanke wa yana kallon fuskarta,ita kuwa ta rufe idanunta ƙam!wani irin takeji bakin nata,gashi abun da shegen zaƙi, anya kuwa ba abin sha bane ya manta yace na wanke baki ne?
Aikuwa wllh saita ɗan sha taji ya faɗinsa yake.Adeeb bai sankara ba kawai yaga ta tattara kumar bakinta ta haɗeye ƙut!

Zaro ido yayi tare da buɗe baki cike da mamaki yace "what!!" Kin shanye kunfar?oh my God" ya faɗa yana zare burush ɗin daga bakinta.
Yace "oya fito dashi"ya faɗa yana zare mata idanu.

Shagwabar fuska fattu tayi kafin tace "ai na shanye zaƙi gareshi" ta faɗa tana mai sunkuyar da kanta.

Girgiza kai kawai Adeeb yayi,baice komai ba ya kunna fanfo yace ta tara ta kuskure bakin,

Hannu ta saka ta tari ruwan sannan ta kuskure bakinta.wani fayau taji bakin nata yayi ,sosai taji yayi mata daɗi ga kamshin strowberry da bakin keyi.

Nuna mata ruwan wanka yayi yace tayi wanka ,yanzu ta fito yana jiranta.
Kai ta daga masa,tana nufar gurin da boket ɗin yake ajiye.
Harya kama handle ɗin kofar sai kuma ya juyo yace "kiyi alwala anan"ya faɗa yana nuna mata jikin sink din tare da ficewa.

Zama yayi abakin gado bayan fito daga toilet ɗin ,haka kawai yaji yana cikin farin ciki,sai murmushin yake,abinda ba al'adar shi bace yawan fara'a.

Fattu kuwa ko minti biyar batayi ba ,sai gata ta fito sanye da Kayan ta data cire .

Kallon ta Adeeb yayi yace " ina kayan dana baki?"
Miƙa masa al'adar tayi tana mai cewa"bazan iya sawa ba harɗe Ni zasu yi"

Kallon ledar yayi sannan ya lalle ta, karba yayi tare da budewa ya zazzage,doguwar rigar baƙa mai dan faɗi sai ɗan kwalin rigar shima baki,kuma yana da girma.wai amma sune bazata iya sawa ba '
"Take it ,ya faɗa cikin hade fuska.
Kallonsa tayi, tare da karɓar ledar,bawai dan ta ji me yace ba ,saidan taga yana miƙa mata ledar .

"Wuce kije kisa"ya faɗa ba alamun wasa afuskarsa.

Juyawa tayi sumi"sumi ta koma toilet ɗin ,amma bata rufe ƙofarba ,ta yadda dataji burum,zata arce.

Haka ta cire kayanta ta sanya wanna doguwar rigar ,masha Allah rigar tayi mata kyau sosai ,saita fito ras da ita.maimaiko ta lulluɓa dan kwalin ,sai kawai ta daura akanta.,sannan ta sanya kayanta wanda ta cire cikin ledar sabon kayan.
Fitowa tayi tana tattare rigar ,dan harga Allah jinta take aharharde,tafi don tsangalallen ,zaninta.

Tana fitowa Adeeb yabi ta da kallon,aransa yana mai yaba irin Khan da tayi ,amma jibi yadda yake wani dage rigar.

"Hamma a ina zanyi sallar?ta faɗa tana kallon gefensa.

Shiru yayi yana kallon ta kafin yace "zo nan"
Cikin tsoro take takowa har zuwa kusa dashi,tana fatan kar yayi mata faɗa irin na ɗazu.

Mikewa yayi tare da zare ɗan kwalin kanta,ya warware shi tare da yi mata rolling irin yadda yaga amminsa da ƙannansa nayi.

Masha Allah ai nan danna fattu ta fito abalarabiya sak, tayi kyau sosai da sosai,kamar ba fattu yar fillo ba.

"Kije can kiyi sallah"ya faɗa yana nuna mata kan dardumar da yayi Sallah shima.

Bayan ta idar da sallar Adeeb yana kallon ta,masha Allah ba wani kuskure cikin sallar Tata,dan fattu tana da ilimin addini sosai.

Abinci ya nuna mata yace tayi sauri taci zasu tafi.bata wani ciabincin kirki ba,dan ji tayi sam abincin baiyi mata daɗi ba,tafi son tuwo ko madarar shanu.

Shima bai wani damu ba ,dan yaga bataci abinci ba sosai.tashi yayi yace mata suje .
Yayi gaba tana binsa abaya. Riƙe da rigarta, hannun dayan kuma tana riƙe da ledar kayanta.

Suna fita daga hotel ɗin kai tsaye gurin masu saida waya ya nufa , wata ƙaramar waya ya siya da layi,ba tare da ya tambayi kuɗi su ba ,naga ya bada duka kuɗin nan dake cikin leda,dan dama suna hannunsa,wanan rigar kawai ya cire daga ledar,sosai naga mai saida wayoyin yana ta murna da godiya har kasa ya durƙusa yana godiya.

Haɗa wayar Adeeb yayi tare da sanya layin ,kati ya karɓa gurin mai saida wayar ,aikuwa da sauri ya ɗauki mata na dari biyar ya mika masa.
Wata number naga ya daddana cikin wayar,bayan ya gama sanya katin acikin wayar.

Magana ya farayi cikin harshen larabci,bayan anɗaga wayar daya kira.ni dai ba dan me yake cewa a,saidai naga kamar yana kwatancen inda yake ne.
Bayan ya kammala wayar ne yana ƙoƙarin sanyata cikin Aljihu,kawai yaji mutum yana ƙwaƙwumarsa kamar za'a shige cikin jikinsa.

Da sauri ya kalli gefen hagunsa ,inda tanan yake jin alamun mutum ɗin,aikuwa fattu ya gani tsaye ta kama gefen rigarsa,jikinsa har rawa yake tana ɓoye fuskarta ajikinsa.

Hannunsa ya sanya tare da kamo hannunta ya dawo da ita zuwa gabansa.
Saida ya ɗan harareta kafin yace "menene kuma"ya faɗa cikin salon maganarsa kamar baya so.

Ahankali fattu ta nuna masa wasu matasa kusan su goma da suka tsaya suna kallonsu.tace "waɗan can ne ke kallona "kallon gurin matasan yayi,yaga yadda suka kafesu da idanu,kuma ba akowa suke kallo ba face fattu,nan da nan yaji wani irin ɓaci rai da ciwon zuciya ya turnuƙeshi,
Cikin hanzari ya maida fattu bayansa yana mai hararar matasan nan,zuciyarsa kamar zata fito dan tsabar ɓaci rai.gaba ɗaya yaji gurin yayi masa baƙi kirin,Bama yason tsayuwa agurin, dan haka cikin zafin nama ya fizgi hannun fattu suka fara tafiya daga gurin,mai saida wayoyin yana ta masa godiya da Allah ya kiyaye amma ko sauraransa baiyi ba.

Can wani guri ya koma tare da tsayawa ,shi kaɗai dai huci yake,dan me zasu tsaya suna kallon ta ,shifa saiyaga kamar ma ɗaya ƙirjin fattu yake kallo. Cikin sauri ya juyo tare da kallon fattu tun daga sama har ƙasa.ba wani abu daya bayyana ajikinta ,wanda za'ace shigarta batayi daidai ba ,saidai fa idan ka ƙura mata ido zaka iya gane ba bra ajikinta.
Lallai ke nan bata sanya bra ajikinta?

"Ke meyasa baki saka wannan abun ba kafin kisa rigarnan"
Ya faɗa cikin fushi da bakin rai.

Kallonsa fattu tayi cikin rashin fahimta dan bata gane me yake nufi ba,kawai saita sunkuyar da kanta ƙasa tace "kayi haƙuri Ni banga komaiba inda rigar ba"ta faɗa Muryar har ta fara rawa,alamun zata yi kuka.
Harya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ringing,tsaki yayi kafin ya ɗaya call ɗin.
Shiru yayi na tsawon lokaci kafin yace "Yes i sawa them"ya kashe wayar .

Dan fitowa yayi daga gurin dasuke tsayen naga ya ɗaga hannunsa .

Wata tsuleliyar mota naga ta taho gareshi,suuuuuu,baka ko jin ƙagarta,kallon ɗaya zakayiwa motar kasan anɓadda Naira agurin,farking motar tayi agabansa,kafin mai riƙon ya fito cikin sauri yana mai faɗin "your highly well come back sir"mutumin ya faɗa yana mai durƙusawa har kasa gaban Abeed.

Kafadar mutumin Abeed ya dafa tare da miƙar dashi tsaye,sannan ya ɗan rungumeshi yana mai bubbuga bayansa.

"Let go hisham"Abeed ya faɗa yana mai nufar motar ,da sauri wanda aka kira da Hisham ya budewa Adeeb motar ,shikuma ya shiga gidan baya ya zauna.

"Hamma " fattu ta faɗa cikin sauri tana mai ƙarasowa jikin motar ganin ya shige cikin motar yana ƙoƙarin barcinta.
Adeeb kuwa da gangan yayi banza da ita ,intaga dama ta ƙara so ta shiga motar,dan haushinta ya keji sosai ,ai da gangan ta wani tsaya har wasu ba zaune ke ƙare mata kallo.

Hisham ne ya kalli fattu yace "yan mata lafiya kuwa?
Shagwabe fuska fattu tayi tana kallon Adeeb tace "gurin hamma zani gashinan acikin nan"ta faɗa tana nuna mai Adeeb ,wanda ya wani ɗauke kai .

"Yallaɓai this ...
"Let her in"Adeeb ya faɗa cikin katse Hisham .

"Yes sir"Hisham ya faɗa cikin bin umarni,ya kauce daga bakin ƙofar motar yana mai cewa fattu"shiga"

Da saurinta kuwa ta shige kusa da Adeeb ta zauna ,harda sauƙe ajiyar zuciya.
Ahankali ta sanya hannunta tare da riƙe gefen rigar Adeeb ta kalle- kallen motar.banda faɗuwa ba abinda gabanta keyi.

"Yallaɓai where are we going now"
Hisham ya tambaya cikin girmamawa.

"Abuja" Adeeb ya faɗa tare da kwantar da kansa jikin kujera ,ac na ratsa shi ta ko ina.

Nan Hisham ya kunna mota suka cilla sai Abuja.

Ko daga Abuja kuma sai ina ?

Ga dai Hajiya fattu cikin mota mai a.c ana baza idanu.

Muje zuwa ku biyoni sannu kan hankali.

Domin samun wannan littafin daga farko sai ku danna bulun dake kasa 👇🏻👇🏻👇🏻

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/07/macijine-shi-page-5-6-hausa-novel.html

Anty mammy ce

Mrs babi💘💘💘

[8/25, 12:25 AM] +234 704 639 6992: 🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄🎄


MICIJI NE 🪱🪱🪱



Na mammy kabeer
(Anty mammy)



Elegant online writers📚📚

Free book

Page 25/26



________________Tafiya suke cikin motar Ba tare da kowa ya ƙara cewa komai ba,ba abinda ke tashi cikin motar dai sanyi a.c da daddaɗan kamshi, gefe guda kuma ƙira'ar sudais ke tashi cikin suratul mulk.

Gaba daya zuciyoyinsu,sun sami nutsuwa,irin wacce mai sauraron Alƙur'ani ke samun tago mashi da ita.

Adeeb yana kwance cikin kujerar, idanunsa alumshe ,ahankali yake ɗan motsa bakinsa yana bin ƙira'ar,al'adar sa kenan dama shi,inda yana cikin mota ,to karatun alƙur'ani yake sauraro. Yayin da can ƙarƙashin zuciyarsa yake jin wani irin farin ciki da annashuwa,duk da baisan tsawon lokacin daya ɗauka cikin yanayi na wata halittar ba,amma yana ji ajikinsa cewa yayi kewar ahalinsa fiye da yadda yake tunani.ba abinda yake fata da buri irin ace yaganshi kusa da abie da ammi.ko wane yanayi zasu shiga idan suka ganshi?
Tunanin da Adeeb yayi tayi kenan cikin zuciyarsa.hakan ya hana masa fahimtar halin da fattu ke ciki.wato ta takure jikinsa sosai,sai rawar sanyi takeyi, sosai sanyin motar ke damunta, ga wani irin

Please Login or Register in order to submit comment