Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

da dokinka, ba dai dafi ba, sauran kuma sai ka Boye saboda yiwuwar taimaka wa wani.”

Nan da nan aka miko masa Kwarya ya jika magani ya cika cikin sa ya kuma zuba ya mika wa Jagora ya sha sosai sannan sai ya sa sauran Kullin a cikin jaka.

Ba a tashi daga wannan gagarumin taro ba sai da aka sauya wa wannan tsibiri suna zuwa Tsibirin Idrisu. Daga nan kuma sai jarumin ya sanar da su cewa da ma shi a shirye ya ke, abin da ya dakatar da shi ke nan, wato yakar wannan mugun dodo. Ya yi musu godiya sannan ya ce zai wuce.

Sarki da kansa tare da mafi yawancin jama’ar – tsibirin aka shiga cikin jiragen ruwa aka nutsa cikin teku don yin rakiya ga wannan babban bako na su, bayan kamar tafiyar kwanaki biyar suka kawo bakin gaba, Idrisu ya sauka shi da dokinsa aka rabu ana kewar juna. IDRISU ya kama hanya ya ci gaba da tafiya har ya cim ma wata itaciya mai yalwatacciyar inuwa da kuma wani irin falali a Karkashinta, ya sauka daga dokinsa ya sauke masa kaya tare da kwance masa

Www.bankinhausanovels.com.ng sirdi ya sake shi zuwa cikin daji don kiwo, shi kuma sai ya je Karkashin bishiyar nan ya yi kwanciyarsa rigingine, kafin ka ce me har barci ya sace shi, can ya fara nisa cikin barcin sai ya ji wani abu ya fado masaa fuska, ya bude ido da gaggawa har da wata irin zamilya irin tasu ta manyan jarumai, amma sai ya ga ashe takarda ce, kuma har da rubutu a cikinta. Mamaki ya kama shi.

Yana budewa sai idanunsa suka tabbatar masa da ~ cewa lallai ya taba ganin irin wannan rubutun, hasali ma nan take ya gane daga inda takardar ta fito. “

Daga masoyiyarka mai begenka wadda tunaninka ya zama abincin ruhinta safe da maraice, ina fata kana cike da koshin lafiya kuma cike da taimakon Ubangiji.

Yaya ka ji da karo da mazaje da dodanni? Watakila ka yi mamakin yadda na san halin da kake ciki ko? To tun daga ranar da ka bar wurin malaminka wato mahaifina, ni kuma na dawo nan bayan duniya sai ya kasance halin da kake ciki shi ne babban abin tattaunawa da bibiyarmu a kowane lokaci. Hasali ma duk mako kawata aljana Dailanu kan kewayo ka, kuma wannan takarda ma ita ce ta kawo maka.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina samun labarin mahaifina kuma yana can lafiya lau a kullum yana yi maka addu’a da tambayar labarinka, don har yanzu Dailanu kan je wurinsa daukar karatu, kuma duk Asabar takan zo nan wurinmu.

Sauran ‘yan matan da aljanin nan ya tsare mu tare kowacce tana nan lafiya sai dai tunanin iyaye da masoyansu kawai dake damun su.

Ina kuma sake sanar da kai cewa ka yi takatsantsan da Sarauniyar da za ka tarar a gabanka, don mayaudariya ce kuma tana da tsananin jarunta, sai dai kuma muna yi maka addu’ar Allah Ya ba kanasara,a kanta.

in har kana bukatar rubuta mini jawabi game da wannan wasika da aka ba ka yanzu, to Dailanu tana nan kusa da kai, in ka rubuta jefa takardar sama kawai, za ta kawo min. Ka huta lafiya. Ni ce masoyiyarka, Nur ‘yar Ibrahim.”

Murna ba sai an bayyana ba a wurin jarumi Idrisu, tun farkon karanta wasikar har zuwa kammalawa murmushi kawai ya ke yi wanda ke gab da kecewa da dariya. Yana kammala karantawa sai ya daga hannayensa sama yana mai roKon Allah a kan Ya

Www.bankinhausanovels.com.ng cika masa nufinsa. Ya dauko takarda da alkalami daga cikin burgaminsa ya fara rubutawa kamar haka,

“Daga Idrisu dan Hamidu zuwa ga rabin rayuwata baki daya.

Da farko dai zan fara ne da ba ki labarin wani abu wanda ya faru a tsibirin dana kashe dodon nan, inda suka yi mini gargadi game da Sarauniyar da kike magana, wai a kan cewa in yi hankali da kyanta don wai yakan dimauta mazaje har kama su yafi sauki fiye da kama kaza.

A gaskiya wannan almara ta sa ni koyaushe na tuna sai in ta BabBaka dariya, lokacin da suke magana nake cewa a zuciyata da a ce gwanayen sanin kyau za su yi dacen ganin ki ko da sau daya ne, to da kuwa har abada sun daina zancen kyan wata mace adoron duniyar nan.

Ko da yake aka ce rashin sani ya fi dare duhu, don kuwa ba su san cewa a dalilinki ne Sarkin aljanu Sham‘una ya mayar da matan da suka tuke a fagen kyau suka zama masu debe miki kewa ba dalilin cewa ko kadan ba zaa misalta ki da su ba. Ni dai ganau ne ba jiyau ba, don kuwa na gan ki a cikinsu, yadda kike haskakawa kamar wata cikin taurari.

Ya ke wadda zakin muryarta babu zumar da ta kai
Www.bankinhausanovels.com.ng ta, wadda babu wani abu mai haske da na taba gani da ya kai farin idanunta, ina tabbatar miki da cewa soyayyarmu ta fi teku zurfi da fadi.

Saukin da kawai nake samu shi ne kullum da adikonki nake rufe fuskata sannan in sami lafiyayyen barci, kuma duk lokacin da kasala ta rufe ni shi nake ratayawa a wuyana sai in ji wani sabon Karfi ya lullube ni.

Ya ke Nur, ina ganin ya kamata in dakatar da rubutuna haka sai kin gan ni, in Allah Ya so. Sai dai kuma kafin nan, akwai taimako da nake so ki rokar mini Kawarki Dailanu ta yi min: ga wasikar gaisuwa nan zuwa ga dan‘ uwana Waziri Habu, Wazirin kasar Arewa. Shi ma akwai budurwarsa tana nan tare da ku.

Ki huta lafiya. Daga masoyinki har abada, Idrisu dan Hamidu.”

Idrisu na kammala rubuta wannan takarda sai ya dauko wata takardar ya rubuta sakon gaisuwa zuwa ga dan’uwansa Waziri Habu, wanda a ciki ya ke sanar da shi cewa yana lafiya kuma ‘yan matansu duk suna lafiya sai dai begen masoyansu kawai da suke yi. Ya tambaye shi ko yana samun labarin iyayensu da sauran ‘yan’uwansu da suka fito karatu wato Yahaya

Www.bankinhausanovels.com.ng da Bashari, da sauran bayanai dai irin na ‘yan’uwa.

Da ya kammala sai ya daure wasikun biyu ya jefa sama, kamar wasa sai ya ga sun bace, wato aljana Dailanu ta cafe ta tafi da su.

Kasancewar faruwar haka a ranar Asabar ya sa yarinya Nur ta sami wasikarta da jarumi Idrisu ya rubuta mata ba tare ba wani Bata lokaci ba, ‘yan mata suna kewaye da ita amma ta kasa Karanta takardar a gabansu saboda kada zuciyoyinsu su sosu irin yadda saurayinta ya fifita ta, tana karantawa tana murmushi, da suka tambaye ta sai ta ce musu, “Abin sirri ne, kuma sirrin irin na masoya biyu masu matukar begen juna.”

. Sai abin ya zame musu abin wasa da dariya, har maganar ta shiririce.

Can sai Nur ta ce wa aljana Dailanu, “Don Allah ko za ki taimaka, sako za mu ba ki zuwa Kasar Arewa.”

Ai kafin ta kammala sai Dailanu ta yi farat ta ce, “Haba Nur, ai ni yanzu tsakaninmu ya wuce ki roKe ni wani abu don ni ‘yar’uwarku ce, sai dai ko bambancin cewa ni ba’yar Adam ba ce kurum.”

Aljana ta Kara da cewa, “Wannan dan Karamin aiki, kin san kuwa in na ga dama yau cikin sa‘’a uku zan iya zagaye duniya sau biyarP”

Www.bankinhausanovels.com.ng
Nur ta ce, “to ranki ya dade, ai ban ce ina jayayya ba.” Suka yi dariya gaba daya.

Sai Nur ta ce, “Wannan takarda ta Wazirin Kasar Arewa ce, Waziri Habu, dan’uwan_ saurayina. Jarumin jarumai Idrisu dan Hamidu ne ke so a kai masa.”

Budurwar Waziri Habu tana jin an ambaci sunansa sai ta tambaya, “Wane Habun ne wai kuke ta magana ne? Ko wanda dai na sani ne Habu dan Hamidu?”

Nur ta amsa, “EF, shi fa. Af, Fa’izah ke ce budurwar tasa da aka ce muna tare?”

Ai fa sai yarinya ta mike tsaye tana ta Kwalla ihu, “Habuna ne, Habuna ne, ni zan tafitare da Dailanu.”

Ko kadan ba su yi fushi da ita ba, hasali ma sai suka shiga lallabar ta don sun san yadda so ya ke, suka nuna mata cewa ai su ma duk suna da masoya amma suke hakuri.

Wata daga cikin ‘yan matan ta tambayi budurwar Waziri Habu, “Kina son tona wa Dailanu asiri ne, a halaka ta?”

A haka suka samu suka fara ciwo kanta kafin Bingyel ‘yar Fulani matar Bashari ta yi wa Nur wata tambayar, “Ko kina nufin Habu dan Hamidu yana da yaya Idrisu da abokinsu Bashari>?”

a Www.bankinhausanovels.com.ng Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?”

Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.”
Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan’uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.”
Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk ‘yan’uwa muke ba mu sani ba?”

“Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su.

Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.”

A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa.

Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

MUN TSAYA

Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?”

Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.”
Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan’uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.”
Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk ‘yan’uwa muke ba mu sani ba?”

“Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su.

Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.”

A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa.

Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke

ZAMU TASHI

shawarar daukar takardar yana mai cike da tararrabi. Ya bude a hankali bayan zuciyarsa ta natsu kuma ya tabbatar cewa shi ake nufi ya duba takardar, duk da cewa bai ga mai kawowa ba.

Yana budewa sai fuskarsa ta cika da murmushi tun da ya fahimci rubutun dan’uwansa.



JARUMI Idrisu ya mika kamar yadda ya saba ba dare ba rana har sai da ya sami kwana sittin da hudu yana kutsawa cikin daji, kuma duk cikin anakin nan bai hadu da dan Adam ba ko daya. In dai ya ji motsi, to babu shakka manya ko kuma miyagun namun daji ne.

Ya iso wata mararraba wadda ta rabu gida uku, tsakiya, dama da hagu. Bai yi wata-wata ba sai ya mike sanbal.

Wannan hanya ita ce ta zuwa birnin Salsala, wato garin Sarauniya Zinkadaziyya, kuma matukar mutum zai nufi bayan duniya, to dole sai ya bi ta nan.

Sai da ya yi kwana biyar yana tafiya cikin wani irin mugun sanyi da ke zubowa fari sal daga sama kamar KanKara sannan ya hango garin.


Ganuwar garin kamar an gina ta da azurfa ne saboda wani irin sheki da take yi. Shi kansa Idrisu sai da mamakin irin wannan katanga ya rufe shi. Fitilu

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG kuwa a kowace kusurwa ta wannan gari ko allurarka

ce ta fadi da dare, to za ka dauka ba tare da wahalarwa . ba, ko kadan ba abin mamaki ba ne in aka ce wannan



gari aljanu ne suka gina shi. Sai dai kuma mutane ne
ke zaune a cikin sa ba aljanun ba.

Ga wasu itatuwa da furanni iri-iri masu matukar ban sha’awa da Kanshi. Abubuwan bukata na yau da kullum dai babu abin da mutum zai buKata ya rasa, komai suna da shi.

Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne duk garin babu namiji ko daya sai dai mata. In kuwa har ka ga namiji, to an kamo shi ne kawai don ya zama abincin macizan da mutanen garin ke bauta wa. Musamman sukan fita farauta don kamo mazaje, ballantana kuma wanda ya kawo kansa.

Ba su ba macizan nasu ramammen namiji, a’a sai sun kiwata mutum ya yi Bulbul tukuna.

Wadannan mata sun Kware matuka wurin jarunta, suna da wata irin tarbiyya wadda mace daya ko kadan ba ta tsoron tunkarar jarumai arba’in, ita kuwa Sarauniyarsu saboda irin siddabarunta da _ sanin lagon yaki sai an tara jarumai dari sannan ta kan fafata dasu.

‘Ta Bangaren kyau kuma mutanen wannan gari baa magana, ballantana Sarauniya Zinkadaziyya wadda

WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG duk Karfin halinka in har kuka yi ido hudu da ita kuma ka ga zahirin fuskarta, to sai jikinka ya yi sanyi saboda irin cikar halittar da Aah Ya yi wa fuskar tata da jikinta.

Yadda suke jin dadinsu kuma shi ne su sha giya, su yi kida da raye-raye sannan su bauta wa macizai. ‘Tsakanin su da maza kuma sai kisa.

Da Idrisu ya kusa da garin sai masu tsaro da ke kan husumiya suka hango shi, nan take suka sanar, kafin ka ce mene ne wannan mata goma sun yiwo masa dauki a kan dawakansu dauke da makamai. Da suka Karaso sai suka daka masa tsawa, suka ce, “Kai tsaya, dakata a nan, wane ne kai? Daga ina kake? Me ya biyo da kai nan? Ba ka san ka biyo hanyar mutuwarka ba ne sannan kuma ba damar juyawa baya? To, yi maza ka sauka daga dokinka ka kawo takobi da mashinka. Ko kana so ko ba ka so ka zama abincin macizan da muke bauta wa.”



Da ya ji jawabin jaruman ‘yan matan nan sai ya ce, “Haba, ku ba ku kyautata wa bako ne? Shin ba ku san cewa mutumin da ba ya kyautata wa bako ya yi hasara ba? Shin ku ba ku zuwa wani gari ne ku ga yadda ake karramawa tare da mutunta baki? Kuma idan kun ga cewa ba za ku iya sauke ni ba ne, to ku Kyale ni mana

in yi wucewata zuwa inda na yi niyya. Don Allah ku

Www.bankinhausanovels.com.ng yi hakuri ni ba rikici nake nema ba.”

“Yan matan suka ce, “Kai ba doguwar magana muke so ba. Yaya mu da musamman mukan fita farautar mazaje, kuma ga shi ka zo har gida sannan ka ce mu Kyale ka? Ai sai dai wani ba kai ba. Shi kuma wannan kyakkyawan doki naka Sarauniyarmu ce ta fi cancanta da hawan sa… ko da yake kai ma ba baya ba ne a fagen kyau din.”

Suka fara zagaye shi da dawakansu, shi kuma yana tsakiya, suka zazzare takubba, ai sai Idrisu ya yi wa dokinsa Kaimi. Jagora ya buga wani irin tsalle na Kwararren doki ya tsallake ‘yan matan nan ya koma gefe a daidai lokacin da Idrisu ke jawo takobinsa ya saro wani babban reshe na bishiyar da ke kusa dainda dokin ya dira. Jarumin ya rike reshen ya mayar da takobinsa cikin kube.

“Yan matan nan suka yiwo kansa. Idan sun kawo sara sai ya goce, har sai da ya fahimci cewa da gaske suke yi sannan ya fusata ya sa wannan reshe na itace ya yi ta bugun su yana kauce wa saran takubbansu har sai da ya yi musu tilis. Da Kyar suka koma cikin gari.

Kai, ‘yan matan nan sun sha wuya.

Jina-jina suka je suka sami Sarauniya, abin ya yi matukar ba ta mamaki, amma duk da haka saida tasa aka kama su aka daure don sun kasa kamo mutum

Www.bankinhausanovels.com.ng daya tak, ta riKa fada cewa sun cika da mayen giya ne har aka yi musu haka, amma za ta koya musu darasi. Ta sa wasu jarumai wadanda an tabbatar da jaruntarsu a kan cewa abin da take so shi ne azo mata da wannan mutumi da ransa don a azabtar da shi kafin a ciyar da macizai namansa.



“Yan mata suka je suka yi shirin yaki, daga ganin su ba sai an fada ba cewa jarumai ne, suka nufi bayan gari inda Idrisu ya ke. Suka hango shi zaune Karkashin wata itaciya kashingide, ga alama ba abin da ke damun sa. Shugabarsu ta ba da umurnin cewa ashirin su je su kamo shi, amma fa kada a kashe shi.

Idrisu dai ya fahimci sun nufo shi gadan-gadan, sai ya yi wuf ya suri itacensa na dazu ya haye doki. Bai Bata lokaci ba wurin fara jibgar su alhali shi ko rigarsa ba su iya tabawa ba.

Duk ta hanyar da suka Bullo sai su tarar ashe ya fi su sanin ta. Tun da suke ba su taba ganin jarumi kamarsa ba wanda hakan ya ba su mamaki.

Fada ya yi fada, ‘yan matan Sarauniya suka ga dai in aka ci gaba a haka, to babu shakka wannan mutumi zai halaka su, don a halin da ake ciki ma akwai guda goma kwance, saboda haka sai sauran suka juya linzami suka rufa a guje sai cikin birni.

Idrisu ya koma ya daure wadannan jikkatattu guda

Www.bankinhausanovels.com.ng goman tamau kamar ya daure goro.

Sauran talatin da suka sha da kyar suka sami Sarauniya suka tabbatar mata da cewa babu shakka lamarin ba na wasa ba ne, don su dai wannan mutum ba su taba samun jarumi kamarsa ba. Sarauniya ta fusata ta yi musu bulala sannan ta ba da umurnin cewa su maaje a kulle.

Sai suka ce, “Ranki ya dade, mun yarda ma a kashe mu ba daurewa ba kawai, matukar dai aka samu wanda ya je ya kamo shi.”

Jin hakan sai hankalin Sarauniya ya dawo jikinta tace a Kyale su, sannan ta ce, “Lallai babban al’amari ya zo mana.”

‘Tunanin Sarauniya na gaba shi ne a sako wa wannan jarumi zakoki.

Su wadannan zakoki Kwararru ne wadanda aka yi wa kyakkyawan horo na komai jaruntarka sai sun gama da kai. Guda daya kawai daga cikinsu kan karya jarumai fiye da dari biyu. Babban abin da sukan yi kuwa shi ne da sun iso wurin jarumai sai su yi wani irin ruri mai tsananin Karfin gaske, wanda kuma suna yi sai dawaki su rude su yi ta karo suna kayar da mahayansu suna gudu, shi ke nan sai zakokin su bi su karkashe jaruman. Dasun kammala wannan aiki sai su koma cikin gari a guje su shige inda ake killace su.

Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya ta ba da umurnin a sako wa jarumi Idrisu su. Cikin kanKanin lokaci suka nufo bayan gari suna ruri da gunji

Da ya hango su sai ya yi tunani a ransa ko dokinsa zai firgita, shin zai iya fuskantar wadannan girdagirdan zakoki kuwa? Sai ya shafa wuyan Jagora ya dan bubbuga, wato alamar yana Karfafa masa guiwa tare da tausar sa a game da irin Kalubalen da ke tunkarar su. Jagora ya fahimci abin da ake nufi sai ya yi haniniya wadda ta tabbatar wa Idrisu cewa babu fargaba.

Nan da nan sai tunanin Jarumin ya hararo masa dodon da ya taba artabu da shi, irin girmansa, ban tsoronsa da mummunar kamarsa amma ba su sa Jagora ya tsorata ba, ballantana zakoki, saboda haka sai ya sami cikakkiyar natsuwa. Da suka kusa karasowa sai Jagora ya yi ta harbin iska abinsa yana wani irin rimi yana kewayawa.

Cikin murna Idrisu ya sake gode wa Allah da Ya ba shi irin wannan jarumin doki.

Zakokin nan goma da suka Karaso kusa da Idrisu sai suka fara, mai Karaji yana yi, mai ruri yana nasa amma Idrisu ko gezau, su kuwa wadancan ‘yan mata da ke daure sun zuba ido ne suna jiran ganin abin mamaki yadda zakokin nan za su yi watandar naman

Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu da dokinsa a tsakanin su.

Bai yi wata-wata ba ya zare takobinsa, Kara kamar aradu. Wasu irin shimfidaddu kuma dogayen sararraki guda biyu kawai ya kai ta gefen dama da hagu amma ya raba zakoki hudu kowanne da gangan jikinsa. Ko shurawa ba su yi ba.

Sauran shida suka ja baya suna jiran su yi masa dirar mikiya, amma kuma sun makara don kuwa ya rigaya ya gane nufinsu. Kafin su iso ya daga takobinsa sama, sai kuwa baki dayansu suka diro masa, amma kafin su gama sauka har yasara sau uku kamar walkiya.

Sai dai wasu ba su ba. Duk Idrisu ya halakar da su.

Daurarrun ‘yan mata dai sun rigaya sun yanke tsammani da duk wata tantama ko shakka game da jaruntar Idrisu. Tunaninsu ma yanzu ya karkata zuwa ga cewa lallai shi ba mutum ba ne, a’a sai dai wani jarumi ne daga cikin manyan jaruman aljanu, dalilinsu kuwa shi ne, su dai ba su taba ganin mutumin da ya yi nasara a kansu ba ballantana a ce kuma ya yi nasara a kan zakokinsu. Ga shi kuma kyansa ya kai ace dan aljanu.

Idrisu ya karasa wurin wani tafki da ke nan kusa ya wanke jinin zakokin da ya fantsamar musu a jiki shi da dokinsa, sannan suka sha ruwa ya kuma debo ya zo ya bai wa ‘yan matan nan wadanda tuni da ma

Www.bankinhausanovels.com.ng kishirwa ta rigaya ta dame su. Yanzu kam sun tabbatar cewa tun farko ya Ki kashe su ne saboda tausayi.

Suka ce, “Mun gode saboda ruwa da ka ba mu.”

Ya amsa musu cewa, “Af, ashe kuna da saukin kan da za ku iya yin godiya? Don ni ina fahimtar ku ne a matsayin masu girman kai da jin mugunta a rai. Ga alama kuma a fuskarku duk wanda ya gan ku ya ga kyawawa amma a zuciyoyinku za ku iya cinye mutum danye saboda tsabagen rashin imani da kumia rashin tausayi.”

Suka ce masa, “E, lallai ba ka yi Karya ba ya kai wannan jarumi, amma kafin mu ce maka komai, me yasa baka kashe mu ba bayan ka yi nasaraa kanmu?”

Ya ce, “Babu shakka kun yi tambaya, idan za ku iya tunawa dazun nan nace ba ku da tausayi, kuma duk mutumin kirki dole ne ya zamo mai tausayi. Kamar yadda kuke jin zafin jikinku haka ma wani ya ke jin zafin nasa jikin.”

Da ‘yan mata suka ji jawabin Idrisu sai suka ji a zuciyarsu sun natsu da shi, sai suka ce masa, “Lallai mun yarda da abin da ka fada mana, kuma yanzu za mu gutsura maka labarinmu.

Mu dai yadda ka gan mu din nan ba mu jin tausayin kowa. Babu soyayya tsakaninmu da sauran mutane

Www.bankinhausanovels.com.ng don muna ji a jikinmu cewa mun fi kowa, kuma daga cikin mutane wadanda muka fi ki da tsana su ne mazaje. Mu din nan da ka gan mu da yawanmu tun da suke ba su taba sha’awar wani da namiji ba, ballantana har su san shi. Wasu kuma bacin ran da da namiji ya Cusa musu a rayuwa ne da kuma tunanin daukar fansa a kan dukkan jininsa ya sa suka gudo suka zo nan suka zauna. Duk wadda ta kuskura aka ‘ gan ta tana magana ma kawai da wani namiji, to kuwa ranar ba da ranta za ta kwana ba.

; A yanzu haka akwai mazaje sun fi dubu goma suna ‘ nan a kulle a gidaje daban-daban ana kiwon su, don mu tsakaninmu da maza sai dai kawai mu kama, mu ; kiwata mu bai wa macizan da muke bauta wa su ci.”

Sai Idrisu ya tambaye su, “Macizai kuke bauta wa?” Suka ce, “K:warai kuwa, abin mamaki ne? Ai bayan bauta musu ma akwai irin macizan da har dafinsu mukan rika sha don mun yi imanin cewa zai riqa sa mana tsattsaura kuma mugun hali irin na rashin tausayi.” Da jarumi Idrisu ya ji zancen wadannan ‘yan mata sai ya tambaye su, “To yanzu mene ne abin yi?” Suka ce, “Abin yi shi ne kawai mu gudu, don mu daga yau mun yarda da kai.” Idrisu ya ce, “A’a ba za mu
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

6 months ago

Reply

Good

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment