Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

jaruman. Kai abin.dai kamar’a

Www.bankinhausanovels.com.ng labari.

Yawan bugawar da ake yi ta sa har takobin da ke hannun Sarki Sham’una ya fara lauyewa. Hakan ya yi matukar ba shi mamaki, da tafiya ta yi tafiya sai ya tabbatar wa kansa cewa yanzu takobin ba shi da sauran Karfin da za a ci gaba da gwabzawa da shi, saboda haka sai ya wurgar da shi, ya daga hannu sai ga wani mulmulallen bakin Karfe mai wasu irin hakora, ya riKa kai wa Idrisu bugu da shi jarumin yana gocewa, can da Idrisu ya sami sa’a sai kawai ya sa kaifin takobinsa ya sare tsakiyar mulmulallen Karfen, ai nan take ya watse.

A irin haka Sarki Sham’una yana kawo miyagun makamai Idrisu yana lalatawa har sai da ya kawo guda tamanin. Abin da kawai bai lalace a hannun Sham’una ba tun fara gwabzawarsu da jarumi Idrisu ita ce garkuwa.

Akwai wata babbar bishiya a kusa da inda gumurzun nasu ya kai su, kuma a takaicen takaitawa itaciyar ta kai shekara dari biyar a wurin, ai kawai sai Sarkin aljanu ya sa hannu ya fisgo ta don yin bulala da ita, a daidai lokacin da jarumi Idrisu ya bi shi ya daga takobi ya kai masa sara, babu shakka Sham’una ya isa jarumi, don irin gocewar da ya yi akwai matukar mamaki, sai kawai ya kare saran da wannan

Www.bankinhausanovels.com.ng itaciya da kuma garkuwarsa.

Irin dirar mikiyar da jarumi Idrisu ya yi masa da sara shi ne karshen labarin wannan itaciya da kuma garkuwa ta Sarki Sham’una, don ita wannan shahararriyar garkuwa rabewa biyu ta yi.

Jikin Sarki Sham’una ya yi matukar sanyi, kuma

wannan abin mamaki ya sa ya mike ya dafe keya a guje. Jama’arsa da ke gefe suna kallon yadda fafatawar ke kasancewa ba su bari ya Karaso inda suke ba, su ma sai suka juya a guje, suka fuskanci babban birninsu na goma sha biyu. Sauran aljanun da ke cikin fagen fama kuwa da ma azabar Sarki Ifritu da na wancan matashin jarumi ta gallabe su, saboda haka ganin shi kansa uban tafiyar ya ranta a na kare sai su ma suka ce Kafa me na ci ban ba ki ba, suka juya karce suka rufawa jagoransu baya. Wato dai suka bar fagen faman da kuma birninsu na sha daya a hannun abokan gaba.

Suka shige birninsu na goma sha biyu suka rufe shi bam yadda ko allura ba za ta iya shiga ba.

Ko bin sawunsu ba a yi ba, an ci wannan birni ke nan, ya shiga hannu. Aka yanke shawarar kada a tsaya wani Bata lokaci kawai, a nufi birni na sha biyu cikin natsuwa ana tafiya ana sake kintsawa da hutawa, wato birnin Sham’una shi da kakarsa Bakayalu, birni

Www.bankinhausanovels.com.ng na Karshe, don ayi ta ta kare. SARKIN aljanu Sham’una dan Damsalu ya isa wurin kakarsa Bakayalu cikin wani irin tashin hankali da bai taba mafarkin tsintar kansa a ciki ba. Ya fadi a gabanta ya yi mata sujuda. Duba daya kawai ta yi masa ta fahimcei irin halin da ya ke ciki.. Ya ce, “Ya ke kakata ke ce kika raine ni, kika koya mini tsafi da muguntar da nake cikin sa, hasali ma ke ce kika kai hi ga wannan daukaka ta sarautar aljanu da duk duniya da wajenta kowa ke shakka ta, to yau tabbas ga abin da ke neman fin Karfina, dole in ba ki sa hannu ba, to za mu tozarta.”. -‘ Ya kara da ce mata, “Makiya suna nan kan hanyarsu ta zuwa babban birninmu. Mun buga ni da wancan jarumi dan Adam din kuma ba yadda ban bullo masa ba amma abin ya gagara. Duk tsawon lokacin da muka dauka muna gumurzu da shi babu wani labari, sai shi ne ma ke neman kunyata ni, ko kuma ma in-ce ya kunyata ni din, don ban taba juyawa a fagen fama ba sai wannan karon! Wani irin takobi ya ke da shi mai tsananin ban mamaki. A gaskiya na hadu da jarumai ban san iyaka ba wadanda na karairaya tare da turmusa hancinsu,

Www.bankinhausanovels.com.ng na shayar da su dacin mutuwa, amma ban taba haduwa da jarumin da na ji cewa wai ina fada ne ba, jin banda Sarki Ifritu wanda muka taba daukar lokacin da gaba daya bai wuce sa‘o’i uku da rabi muna karawa kafin akarshe insami galabarsaba. =

Wani abin mamaki ma game da wannan jarumi dan Adam shi ne irin yadda har ya san sunanki da sunana. Wai ma har yana cewa musamman don mu yazo.” .
‘Da tsohuwa Bakayalu ta ji wannan bayani daga ‘bakin jikanta sai ta-yi shiru tare da tsunduma cikin tunani, san-nan ta ce, “Duk yadda: aka yi wani ya ‘ munafunce mu ke nan, an fita da bakin littafi zuwa ga hannun makiya. ‘ Sham’una-ya tambaya, “Kaka, -me. ya. hada matsalarmu da wani bakin littafi can?” Bakayalu ta ce, “Dangantaka ta kut-da-kut kuwa. In‘ba ka manta ba na taba sanar da kai shekaru masu “yawa da suka wuce cewa asirin rayuwarka na wurina ‘ kuma babu wanda zaitaba iyakashekako? Sham’una ya amsa, “E na tuna kwarai, ai ba zan ’ taba manta irin wancan albishir ba, shi ne ma dalilin “da ya sa na fara tunkatar wadanda nake jin tsoro ada, har ya zo ya kasance babu wanda nake tsoro a cikin tarayyar aljanu da mutane sai dai ni ake jin tsoro.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sai Bakayalu ta ce, “To asirin gagarar taka da rayuwarmu ni da kai gaba daya suna cikin littafin ne.

A kansa ne na taba sa ka je ka nemi aljani Ziri-muzi ka kashe shi, lokacin da na yi zaton ya taba bude littafin, a wancan lokacin ba ka san dalilin ba amma na baka umurnin cewa in ka je ka zagaye garin da ya shiga ka kashe shi taredawadanda suka ba shi masauki.”

Bakayalu ta ci gaba da cewa, “Abin da ban fada maka baa wancan lokaci shi ne, wurin koKarin mayar da kai gagararre, da kuma kare rayuwarka yadda babu wanda zai iya samun nasara a kanka ballantana wai har ya kashe ka. Mun yi amfani da wani irin tsafi ne ajin farko daga cikin tsafuffukan farkon zamani, irin tsafin da yanzu babu irinsa ya bace sai dai tarihi.

Shi ne na sami labari daga cikin kakannina cewa matsafi guda daya tak da ya rage da irin wancan tsafi a wancan zamani wato aljani Jamboro kasancewar ba shi da magaji sai ya dauke bayanan tsafin ya kai wata duniya can mai wahalar zuwa ya Boye, wanda kuma zuwa waccan duniya sai matsafin aljanin da ya isa tukuna. Ni ma nan da ka gan ni sa’ar gaske na samu

har na sami shiga waccan duniyar a cikin irin tafiyetafiyen da na rika yi. Ya kai jikana, ka sani cewa shekara daya da wata -_ –

Www.bankinhausanovels.com.ng takwas na yi ina lalube-lalube har na yi nasarar tono wanda ya Boye, ko da yake a karkashin haka saura kadan ni ma in halaka, kai hasali ma ban taba cin bakar wahala kamar ta samo wancan tsafi ba.

Ya kai Sham’‘una, lokacin da na gamsu da biyayyarka shi ne na hada maka tsafin, har ka zo ka gagara. Saboda kuma tsananin Kaunar da nake yi maka na sadaukantar da raina a matsayin fansa ga tsafin.

Sai Sham’‘una ya ce mata, “Ke ma kaka akwai naki kuskuren! Ta yaya za a aikata irin wannan ganganci haka? Yanzu ya kamata ace Sarkin aljanu mai yawan makiya a rubuta wani sirri nasa a ajiye haka kawai ballantana kuma har asirin rayuwata?

Sai Bakayalu ta ce, “Abin da ka sani ne wanda kuma ba sai na sake maimaita maka ba cewa duk, kuma kowane irin tsafi yana dauke da wata illa ko cutarwa Boyayyiya ko bayyananniya ko kuma duk biyun ga wanda ya aikata shi kansa. To ai bayyanar bakin littafin ne abin da ke nuna cewa tsafin ya hadu, kuma salwantar da shi babban hadari ne, duk da cewa yana Kunshe da bayanin abin da zai kawo karshen tsafin.

A cikin littafin ne aka yi bayanin wasu miyagun makamai da suka gagari kowane irin tsafi, har ma aka

Www.bankinhausanovels.com.ng siffanta rijiyar da suke a cikin duniyar ‘yan Adam, kuma sai dan Adam din ne kawai zai iya fitar da su ya mallakesu to.kuma duk wanda ya mallakesu to shi ma ya zama gagararre ke nan, shi ya sa da ka ce mini daya daga cikin shugabannin yakin dan Adam ne ka gaina tunani. . A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron
rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za – a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda – haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu
ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske.

Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.”

Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko’ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?”

Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.”

Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

MUN TSAYA

. A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron
rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za – a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda – haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu
ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske.

Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.”



Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko’ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?”

Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.”

Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka

ZAMU TASHI

kwance ta duk da cewa jikinta bai ba ta da bayanan ba, har ma take ce mata, “Akwai sharadi guda, yanzu ba lokacin bincike ba ne, lokacin yaki ne, amma babu shakka bayan an kammala zan yi cikakken bincike, kuma duk wanda muka samu cewa ya taba fita da wannan littafi, to babu shakka za mu Kona shi da ransa. Ko wane ne.” Aljana Dailanu ta doddogara ta nufi bangarenta


don fara jiyyar raunukan da ta samu a lokacin azaba. ‘Tsohuwa Bakayalu ta juya ta fuskanci jikanta Sham’‘una tana mai tambayar sa, “Ka ce mene ne sunayen jagororin yakin?”



Sham‘una ya ce, “Sunan dan Adam din Idrisu dan Hamidu, sannan sai Sarki Ifritu wanda muka taba yaki da shi har na sa shi a cikin battar Karfe, sannan na sa shi a tsakanin dutse. Na yi mamakin yadda aka yi ya kubuta shi da jama’‘arsa da ke daure a cikin sarKka.”

Bakayalu ta ce, “Sarki Ifritu dai da na sani kake magana?”

Sham‘una ya amsa, “EF, shi kaka.”

Sai Bakayalu ta nisa sannan ta ce, “Sarki Ifritu kuwa ka san in ba mu ba babu wanda ke ja da shi ya kwana lafiya a duk cikin aljanu, amma wannan karon

zan bayyana masa sharrina baki daya. Abin da nake —

Www.bankinhausanovels.com.ng so da kai yanzu shi ne ka je ka shirya dukkan mayakanka, ni kuma zan fara girka nawa.”

To yadda lamarin ya ke shi ne, ita wannan makirar tsohuwar aljana Bakayalu har rundunonin mayaka take da su na musamman, kuma wadannan zaratan mayaKan aljany ba sa aikin kowa babe sai nata, ta tsaface su da wani irin tsafi mai ban al’ajabi. Ga su nan launi daban-daban, akwai wasu mayu daga _ cikinsu wadanda ba su da abinci sai dai shan jinin aljanu, wasu kuma ga su nan bakake, wasu koraye, algashi, jajaye da sauran launuka gwargwadon abin da ita Bakayalun ta san dalilin da ya sa ta juyar da su haka. Miyagu ne, wanda daya daga cikinsu kawai in rana ta Baci zai iya karawa da jaruman aljanu dari biyar.

Shirin yaki ya kankama a bangaren Sarkin aljanu Sham’una, jarumai da dakaru dubban daruruwa kowanne sai Karaji ya ke yi don za a kara da abokan gaba, sannan kuma duk da haka sai da Sham’una ya sa masu yekuwa cewa su kewaya cikin duniya da wajenta, duk inda wani bakin aljani dan asalin yankin ya ke, to ya koma don kare gida.



Aljana Bakayalu kuma tuni ta shiga don fara girka wadancan mayun aljanu nata.



Amma lamarin aljana Dailanu kuwa bayan an kwance ta don yin jinya, kuma kasancewar ranar

Www.bankinhausanovels.com.ng Juma’a ce, washegari Asabar sai ta zame jikinta ta sulale ta nufi wurin kawayenta su Nur. Ta yi musu sallama suka amsa, suka rungume ta suna tambayar lafiya yau mako biyu ba su gan ta ba? Shi kuma Sarki Sham’una yau kwana takwas ke nan ba su gan shi ba?

Sai aljana Dailanu ta ce musu, “Ina fa lafiya, Idrisu dan Hamidu ya tunkaro, ya tayar wa da matsafa hankali, ai nesa ta zo kusa don kuwa a halin yanzu ya cinye birni na sha daya, yanzu saura birni na sha biyu wanda azzalumin karen aljanu Sham’una da muguwar kakarmu Bakayalu ke ciki.”

Ta Kara da ce musu, “Ai ni ma Allah ne Ya sa kwanana yana gaba, ba don haka ba da tuni shaidaniyar kakata ta babbaka ni.” Saitakware musu jikinta suka ga irin yadda aka tsattsaga shi a lokacin azaba.

Tace, “A kan littafin nan ne dana taba kawo muku, in ba ku manta ba har a wancan lokacin na ce kar ku kuskura ku taba shi da hannunku, har na rika bude muku shafukan da hannuna lokacin da kuke juyewa. To na yi haka ne don tsoron kada bincike ya tashi su ga fuskokinku, to binciken kuma ya taso, an ga tawa fuskar, ko da yake taimakon Allah Mai girma zuwa yanzu ba ta gama tantancewa ba tukuna, lallai da ba ku sake gani na ba, don da a ce ta gane da kuwa

Www.bankinhausanovels.com.ng ni za ta yi kamar yadda ta halaka mahaifina. Ba ni kadai ba, ku ma kanku da tuni muna can lahira tare. Amma in Allah Ya so kafin Bakayalu ta mutu sai na mayar mata da jawabi, muguwar kafira!” Ai fa nan ‘yan matan nan suka jajanta mata da kuma Kara karfafa mata guiwa, kafin su Balle da labaransu yadda suka saba, sai dai yau babu wasanni don ba ta jin dadin jikin. Cikin labaran da suke yi ne har take sanar da su cewa an yi karen batta a karon farko tsakanin jarumi Idrisu da Sarki Sham’una, har shi Sarkin aljanun ya dafe keya ya ranta~a-na-kare. Jin wannan labari sai murna da farin ciki suka cika , zukatan ‘yan matan nan, suka fara tuna dangi da masoyansu tare da addu’o’in Allah Ya bai wa jarumi | Idrisu cikakkiya kuma tabbatacciyar nasara a kan Sarki Sham’una da kakarsa Bakayalu. Aljana Dailanu yau ba ta bari yamma ta yi ba sai ta mike don sallama da Kawayenta. : Nur ta tambaya, “Yau da wuri za ki tafi haka?” Dailanu ta ce, “Kawata na san za ki fahimta, kin san Kasa babu lafiya, kuma kin san akwai dan zargi a kaina, saboda haka ma dai ni ba za ku sake gani na ba sai abubuwa sun lafa tukuna, in Allah Ya so.”

ZUWA yanzu babu abin da ya fi damun jarumi Idrisu fiye da rashin lafiyar dokinsa Jagora. Kuma a dalilin halin da dokin ke

ciki ne tafiyarsu zuwa birni na sha biyu ba ta yi saurin gaske ba.

Tun da suka dunfaro wannan birni, shi kansa Idrisu da kuma wasu da yawa daga cikin aljanun da ke tawagarsu suka tabbatar da cewa ba su taba ganin birnin da ya fina Sham‘una kyau ba.

Tun daga nesa cikin sararin samaniya za ka hango taswirar Sarki Sham‘una shi da kakarsa, wato masu gidan mulki. Kana kallon fuskar Bakayalu da ke cikin taswirar ka san sharri ya zauna daram da gindinsa a wurin. Dole ne ma gabanka ya fadi.

Akalla akwai aljanu dubu dari sau dari a cikin wannan birni na goma sha biyu na Sham‘una.

Kafin su jarumi Idrisu su kammala karasowa tuni labari ya isa, ashe da ma jirace ake da su, kuma da ma tsarin da aka shirya ke nan, ai sai kawai aka bude
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kofar birnin jarumai suka shiga fitowa kamar ba za su taba Karewa ba, tun daga nesa Sarki Ifritu ya lura da haka amma babu abin da ya ke shelantawa a cikin rundunarsa sai, “Kada gabanku ya fadi, Karfi da nasara suna wurin Allah ne ba yawa da Karfin jiki ba, kowaya natsar da hankalinsa.”

A haka har suka Karaso inda suka yi sansani don fuskantar Sham’una da jama’arsa wanda akalla wadanda suka fito zuwa yanzu ‘sun nunnunka yawansu kuma ci gaba da fitowa suke. ‘ anan

Jarumi Idrisu ya ba Sarki Ifritu shawara a kan cewa kada a jira sai sun gama fitowa don ba a ‘san irin shirinsu ba, ya ce, ‘Mu afka musu kawai, tun kafin jikin mayakanmu yayi ganyi.”

Haka kuwa aka yi, aka rufar wa mayakan Sarki Sham’una da sara da suka. Masu harbi na yi karfafa kuwa ba abin da suke yi sai karya wuyaye. –

Jarumi Idrisu, Sarkin aljanu ‘Tfritu da wancan saurayin jarumin kowanne ‘nasa gefe ya ja yana ta Ta yankan aljanu kamar kubewa. Sarkin aljanu Sham’una sai ya ga abin kamar a . mafarki a lokacin da ya fito fagen fama, zuciyarsa ta hasala matuka. A kan wata irin katuwar giwar aljanu ya ke, ya juya ya kealli irin yadda Idrisu mai takobi ke masa Barna, sannan sai ya waiwaya wancan bangaren

Www.bankinhausanovels.com.ng ai sai suka yi ido da ido shi da Sarki Ifritu yana ta kwankwatsa masa kan aljanu da gwalminsa, ai nan take ya nufi wurin Sarki Ifritu din da nufin bari ya fara da shi su yi ta ta Kare.

Suka fa fuskanci juna, Sarki Sham’una a kan giwa shi kuma Sarki Ifritu a kan doki. Abin da Sarki Ifritu ya fara yi kafin ma giwar Sarki Sham’una ta gama tsayawa sai ya dubi Kwaurinta ya buge da gwalmi, ai sai ta durkushe, kafin ta kai Kasa sai ya sake daga gwalmin ya dankara mata a kanta, nan ta fadi a mace, amma abinka da aljani kafin giwar ta kai Kasa

. Sham’una ya tashisama abinsa kamar tsuntsu.

Shi ma Sarki Ifritu sai ya tashi fir ya bi shi suka hade can sama. Ko kadan fadan nasu babu kyan gani, sai Kara kake ji kamar aradu ce ke faduwa, wannan shi ake cewa turnuku fadan iblisai, yaro bai gani ba balle ya raba. Can kuma sai suka dawo kasa aka ci gaba da fafatawa. Da ma Sarki Ifritu ya san karonsu da Sham‘una, shi ma kuma Sham’una ya san shi.

Wani irin mummunan bugu da Sarki Ifritu ya kai wa Sarki Sham’una da gwalminsa wannan karon an sami tangarda bai iya kaucewa ba, ai sai ga shia Kasa, amma abin mamaki ko a jikinsa, hasali ma sai ga shi ya mike yana dariya tare da kakkabe Kura.

Da Sarki Ifritu ya ga haka sai ya sake kai masa hari,

amma ina, ai da ma kowa ya san cewa Sarki Sham’una ba Karamin jarumi ba ne, ai nan take ya zame tare da yin wata irin tsawa mai tsananin firgitarwa, sai ga wata irin sarka mai tsananin tsawo da kauri caf kamar kiftawa da bismillah ta nannade Sarki Ifritu ta yi sama da shi.

Tsawar da Sham’una ya yi ne ta janyo hankalin Idrisu da ke can yana zabge kan abokan gaba, Dubawar da zai yi sai ya ga Sarki Ifritu a daure ana yin sama da shi, kafin ka ce yaya aka yi haka jarumi Idrisu ya nufi Sham’una da sara, amma kasancewar tuni Sarkin aljanun ya rigaya ya tsorata da wannan takobi na Idrisu sai ya janye cikin dabara ya koma cikin mayaka yana mai ci gaba da fada.

Sham’una ya kamo wani farin aljani da hannunsa, ya dunkula hannunsa ya yi masa dundu, tafiyar wancan aljanin ke nan zuwa barzahu. Ya finciko wasu biyu ya gwara musu kai, ai sai ga kwakwalensua waje! Ashe haka kwakwalwar aljanu take?

Cikin wata dabarar kuma Sham’una ya zame daga wurin yakin ya nufi cikin gari ba tare da mayakansa sun fahimci ba ya fagen ba.
Shi kuwa jarumi Idrisu abin da ya yi shi ne sai ya

daga takobinsa ya sari gefen sarkar da ta daure Sarki Ifritu, nan take ta warware, Ifritu ya tashi rike da —_

Www.bankinhausanovels.com.ng gwalminsa ya yi wa Idrisu wata irin jinjina irin tasu ta manyan mayaka, daga nan ko kallon juna
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

6 months ago

Reply

Good

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment