Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya ce, “Ina yi maka addu’a da fatan samun nasara. Amma lallai in za ka tafi sai ka sami jarumai, ina ganin kamar guda dari su yi maka rakiya.” Sarki ya juya ya dubi Ma’aji ya ce masa, “Sai a shirya musu dinare dubu ashirin don yin guzuri.” Gari na wayewa Yahaya ya shiga gidan Sarki ya yi www.bankinhausanovels.com.ng sallama da shi da kuma mahaifiyar matarsa. Suka yi masa addu’o’in samun nasara da fatan alheri, suka rabu kowa na kuka. Shi da askarawansa suka hau suka rankaya.
Wannan shi ne labarin Yahaya dan Hamidu.
Bashari dan salihu kuwa wato saurayinnan makwabci kuma abokin da ya fito neman ilmi tare da yayan dan hamidu baiyi tafiyar data wuce ta kwanaki goma sha uku ba saiya tsinci kansa yana kutsawa cikin wani daji mai yawan duhu da itatuwa
Wahala da gajiya suka sashi fara tunanin juyawa da komawa gida amman kuma sai ya tuna da cewa aikata hakan zai iyq zame masa babban abin kunya nan gaba haka nan dai yayi haquri yayi ta kunna kai ciki har saida jikinsa yakai yanayin da bazai iya kara motsawa koda taku daya daga inda yake ba lallai yana buqatar hutu
Sbd haka saiya sami tsakanin wasu duwatsu biyu da sukayi makaifa da juna ya shige yayi rigingine
Bai dade da fara hutawa ba saiya hango wasu mutane suna tahowa wadanda kuma da ganinsu kasan cewa kowannensu akwai alamar kwarjini irinta sarauta tattare dashi sunsa shugabansu a tsakiya www.bankinhausanovels.com.ng gaba suna biye.
Kasancewar Bashari bai san abin da ke tafe da su ba, sai ya sake boyewa a tsakanin duwatsun yadda ba za su iya ganin sa ba, amma kuma shi yana hangen su. Suna wuce daidai inda ya ke kadan, sai ya ga daya daga cikin mahayan ya lababa ya sa kokara ya buge kan shugaban nasu da ke gaba, ya fado daga kan doki. Suka taru suka yi ta bugun sa har sai da ya daina motsi, ga alama dai ya mutu. Abin da ma ya sake dakatar da su shi ne, suna cikin wannan aiki sai kawai ga wani katon zaki ya fito daga cikin daji yana gunji, ya nufo su. Suka taru suka fafata har sai da suka kashe shi, kuma ga dukkan alamu sun yi matukar jin dadin fitowar zakin a daidai wannan lokaci. Dalili kuwa shi ne irin yadda suka tube wancan shugaba na su da suka kashe daga cikin tufafinsa, suka yayyaga sannan suka sa su face-face cikin jini. Suka ciccibi mataccen zakin suka daura a kan dokin marigayin. }
Suka dawo kan gawar mamacin suka dauke ta suka sa a cikin wani buhu na algarara suka daure bakin, suka yi kama-kama, suka jefa cikin wani rami mai . zurfi, sannan suka juya suka koma cikin daji. Duk fa abin da suke yi a kan idanun Bashari ne. Bayan tafiyar su sai ya fito daga inda ya ke boye a tsorace jikinsa na rawa, yana ta mamakin yadda hakan ta kasance. Ya fara tunanin ko zai bi mutanen nan ne don ganin yadda za su yi da rigar dan’uwansu, kuma ina za su je? Sai kuma ya tuna ai su akan dawaki suke, shi kuma yana kasa kuma in har suka gane yana bin su, to babu ko shakka halaka shi za su yi. Sai ya sauya shawara. Ya Kudiri aniyar cewa duk yadda za a yi, ya kamata ya shiga cikin ramin ya gwada ceto mutumin nan, mai yiwuwa yana da rai. In kuma ba shi da rai, to shi dai Bashari dan Salihu ya yi iyakacin abin da zai iya. Ya tube rigar jikinsa ya nufi rami da niyyar shiga, amma da ya leka ya hango zurmukeken zurfi mai duhu da ke wurin ai sai tsigar jikinsa ta tashi. Ya tabbatar da cewa ba zai iya ba. Ya zauna yana ta tunanin abubuwan da suka faru a cikin abin da bai kai sa’a daya ba da ta wuce, zuciyarsa ta rika fada masa cewa, “Babu yadda za a yi a jefa mutum cikin wannan rami sannan a ce zai rayu.” Sai ya yanke shawarar rabuwa da al’amarin wannan mutum wadda tasa ta Kare. Bai bar wurin ba sai ya ji nishi kamar na dan Adam, ya dudduba amma bai ga kowa ba. Can sai sautin nishin ya rika Karuwa, shi kuma sai ya saurara da kyau, ya kuma fahimci cewa lallai mutumin nan na
cikin rami na da sauran numfashi, wato bai mutu ba. A zuciyarsa sai ya ji cewa ko zai halaka ne wurin Kokarin ceto wannan bawan Allah, to shi kuwa zai gwada. Ya tashi ya dan kewaya cikin dajin, ya sami itacen kargo ya sara ya yi ta bare bayan yana tarawa har sai da ya sami wanda ya tukka igiya mai tsawo da kaurin gaske. Akwai wata itaciyar kirga kusa da ramin, a jikinta ya daure igiyar kamar dabaibayi. Ya zura cikin rami ya kama ya yi ta shiga har lokacin da ya ji cewa igiyar tana gab da Karewa, kuma ya sakankance cewa lallai akwai sauran tafiya. Wato dole ya koma ke nan. Ya laluba Kafarsa ta dama Kasa, sai ya ji ya tokari wani abu. Ashe an yi sa’a a lokacin da aka jefa buhun ya sarke a jikin irin itacen nan da kan fito a gefen rami ta ciki. Ai sai murna ta kama Bashari, ya lallaba da sauran igiyar da ta rage ya daure buhun tamau sannan ya saba a wuyansa ya rika kamo igiyar don kokarin fita. Hannayensa duk sun gaji, babu abin da suke fitarwa sai jini saboda sabulewar da suke yi, a dalilin nauyin shi kansa da kuma na mutumin da ke cikin buhu. Ashe matsala na nan waje tana jiran sa. Ya rage kadan ya fito, sai kawai ya ji wata murya daga bakin ramin tana cewa, “Yau kwananku sun Kare kai da shi. Ashe gara da aka ce in dawo, to yau a lahira za ku kwana.” Wannan mutumi daya ne daga cikin wadanda suka aikata aika-aikar nan ta dazu, kuma an umurce shi ne da dawowa don tabbatar da cewa ba su bar baya da Kura ba, amma da ya iso bakin ramin sai ya ga igiya a daure. Kuma ba tare da bata lokaci ba ya fahimci abin da ke faruwa, wato wanda suka halaka wani ke son ya ceta. Hasali ma babu mamaki ya gan su lokacin da suke aikatawar ke nan. Gaban Bashari ya rika duka uku-uku. Nan da nan bakinsa na rawa ya ce, “Ka yi wa Allah ka yi hakuri ka Kyale mu.” *
Mutumin ya ce, “In Kyale ku ka ce? Wato in rufa muku asiri mu kuma namu ya tonu ko? To ko da wasa haka ba za ta yiwu ba.” Da Bashari ya ji haka sai ya ce, “To yi yadda ka so, amma kada ka manta cewa rayuwarmu tana hannun Allah ne baa hannunka ba.”
Mutumin a fusace ya ce, “E lallai, wato kana bakin kabari amma kana fadar bakar magana ko?” Ya daidaici igiyar, ya daga takobi don sare ta a daidai lokacin da ya ke cewa Bashari, “Yi addu’arka ta Kar…”Www.bankinhausanovels.com.ng wata macijiya mesa da ke saman itacen ta duro masa a wuya. Da ma tuntuni take ganin kamar tsayuwar shi mahayin barazana ce a gare ta. Sai kuwa ga shi zatonta ya tabbata; don ta ga ya dago makami ya nuna inda take, alhali kuwa ba ta san cewa shi bai ma san tana wurin ba. Haka wannan Katuwar mesa ta murde mutumin suka fadi Kasa suna ta murkususu yana ihu. Shi kuma Bashari da ma hannayensa tuni sun gama yin tsami, yana gab da sakin igiyar ke nan ko kuma jin an sake ingiza su cikin ramin amma sai ya ji wancan mutumi na ihu. Haba ai sai ya ji wani sabon Karfi ya zo masa da kuma kwadayin ya fita ya ga abin da ke wakana. Saboda haka sai ya Kara yunkurawa yana fitowa har ya samu ya ingizo buhun da ke wuyansa bakin rami shi kuma ya sa hannayensa ya yiwo waje. Yana fitowa ya dan taka daya biyu sai ya zube saboda matsananciyar gajiya, amma duk da haka yana iya kallon abin da ke faruwa. Wancan mutumin da ke Kokarin kwatar kansa da kuma macijiyar da ke Kokarin halaka shi suka shiga wani irin artabu, kowa na ta kansa ba su san halin da suke ciki ba, har suka mirgina suka afka cikin mugun ramin nan. Bashari ya shiga tunani a zuciyarsa, “Da ma ana cewa in za ka gina ramin mugunta, to ka gina shi gajere don watakila kai za ka fada. To wannan ya gina wanda ya fi shi zurfi. Allah mun gode maKa da Ka kubutar da mu.” Bayan kuzarinsa ya dan dawo jikinsa, sai ya yunkura ya kwance bakin buhun. Ya ga ashe wani dattijo ne fari mai farin gemu da saje, duk ya daddauje ko ina jikinsa raunuka ne, ga su nan ba sa kirguwa, sai nunfarfashi ya ke ta yi sama-sama.
Bashari ya debo ruwa ya yi addu’a ciki, ya sa wa mutumin a baki. Aka yi sa‘a kuwa ya dan tsotsa, ya sa ruwan ya wanke masa jikinsa. Ya duba jikin dokin mutumin can da ya fada rami sai ya sami madara a cikin wata gora, ga kuma nama soyayye. Aka yi sa’a mara lafiyar ya dan kurbi madarar. Ya ciccibe shi ya dora kan doki. Ya sami igiya ya daure shi sakwa-sakwa yadda ba zai takura ba. Ya duba wurin don tabbatar da cewa bai bar wata alama da za ta nuna cewa wani abu ya faru ba, ko da mutanen nan sun yi tunanin sake biyo sawu. Ya shiga gaba ya kama linzamin doki yana ta tafiya don neman wani Kauye nan kusa wanda zai samu ya Yi jinyar sa yadda ya kamata. Wannan dattijo da aka lakadawa duka tare da neman halakawa ashe wani Kasaitaccen Sarki ne mai girman mulki, mai farin jini a wurin talakawansa. GaShi yana da dumbin sani ta yadda bayan kasancewar ‘sa limamin Juma’a na garinsa kuma shi ne malamin malamai. Da yammaci sai ka ga an cika makila kofar gidansa kamar ana fadanci, amma ba fadancin ake yi ba,a’a, manyan malamai ne ke Kara ilmi. Sarki Shahzad kuma,dai mutum ne wanda bai yarda da zalunci ba a,Kasarsa, Babu yadda za ka ga wata ;’yar–banza . karuwa: ko: ,kuma ;.dan, daudu ballanta wani shege barawo,; www.bankinhausanovels.com.ng Kasan mutane babu miai iya musu sai Allah. Ashe duk kyan halin wannan Sarki akwai wasu ‘yan tsiraru daga. cikin, mutanen; fada:wadanda ba sa jin dadin yadda mulki ke-gudana. Babba daga,cikinsu shi, ne kanin Sarkin, wanda maganar.da ake ciki a lokacin ita ce Sarki ya fara shawara a.cikin zuciyarsa cewa ya kamata ya sauka daga.karagar mulki ya nada Kanin don shi ya fuskanci harkar karantarwarsa kadai, Shi,wannan kani na Sarki mai suna Rufaidu babu inda suka daidaita da Sarki ta bangaren hali, don, shi mutum ne,wanda yayi amanna da a Kyale kowa ya Sakata ya wala, kowa ya yi nishadinsa da walwalarsa yadda ya ga dama matukar dai bai taba mulki ba, Mai bukatar karatu ya yi mara bukata ya bari. Karuwai da yan daudu in suna bubatar zama www.bankinhausanovels.com.ng a Kasar a Kyale su, in ba su bukata shi ke nan, amma fa a raayinsa. Ko da yake koyaushe yakan yi KoKarin Boye wa Sarki wannan ra’‘ayi tare da nuna masa cewa yana goyon bayansa dari bisa dari. Ya ci da zuci game da sarautar garin, musamman kasancewar Sarki bai taba haihuwa ba a rayuwarsa. Ya sha Kullawa Sarki tuggu da makirci iri dabandaban amma yana tsallakewa. Dole wani lokaci ya kan hakura da Kulla makircin in ya lura da irin yadda jama ar Kasar ke matuKar son Sarkinsu. To shi wannan adalin Sarki mutum ne da ya jarabtu da son fita farauta, kuma can cikin Kungurmin daji. In aka je sai a kafa tantuna a yi sansani, tantinsa a tsakiya, na sauran askarawa kewaye. al’adarsa kuma in za a shiga cikin daji, to yakan ce kowa ya kama gabansa ne ya je tasa farautar, duk abin da mutum ya kamo, to kansa ya kamawa. Sarkin kuma in zai shiga tasa farautar, to ba ya son kowa ya bi shi, sai dai wani lokaci wannan Kani nasa, don ya dauke shi ne kamar dan cikin sa. Karewa ma shi ya raine shi, ya ba shi ilmi da duk wani abu da da kan bukata daga majibintansa.
A ranar da lamarin ya faru an fito wata gagarumar
farauta ce ta kusa da gida, don Sarki ya ce ya tuna wani wuri da zakoki suke a cikin dajin, shi ne ya ke
son ya gwada ko zai yi sa’a ya samo ‘ya yansu don kiwatawa. Ya cewa wannan Kani nasa ya samo jarumai shida duk da shi na bakwai su tafi, su kuma samo buhu wanda in an sami ‘ya’yan zakin za a zubo a ciki. Jin haka sai murna ta kama Kanin Sarki, ya lissafta tare da kintata cewa yanzu dama ta zo wadda bukatarsa za ta biya cikin ruwan sanyi. Saboda haka sai ya je ya zabo irin mutanensa ya sanar da su abin da Sarki ya ce, sannan ya sanar da su shi kuma irin shirin dayayi.
Yace, “Kun dai riga kun san cewa irin wannan rana muke jira, to yau ga ta ta zo da kanta. Kun ga sarauta ta zama tawa ke nan, mu sheke ayarmu mu ci karenmu babu babbaka.” Ya shiga nuna su daya bayan daya yana cewa, “In mun yi nasara, kai zan nada ka Waziri babba, kai kuma Waziri karami. Kai Magajin gari zan yi maka, kai kuma Madaki, kai kuma kujerar Maji dadi na tanadar maka, kai kuma ta Sarkin fada.” Jarumai cikin murna suka ce, “Mun ji mun dauka.” Shi ne Bashari ya gan su suna zartar da wancan mugun nufi nasu. Bayan sun ga sun sami nasarar jefa shi cikin wannan mugun ramin ne, sai suka nufi sansani cike da murna, amma da suka kusa sosai sai suka Bbarke da kuka, suna ihu. Da sauran askarawa suka gan su cikin irin wannan hali, sai suka zo suna tambayar su abin da ya faru da kuma yadda aka yi ba su ga Sarki ba. Shi kuwa gogan naka Rufaidu Kanin Sarki, sai kukan kawai ya ke ta zabgawa, ya kasa yin magana ma saboda nuna irin baKin cikin da ya ke ciki, yana ihu yana yayyaga rigar jikinsa tare da marin kansa. Sai daya daga cikin su ne ya iya ba da labarin cewa wai Sarki ya ce su Kyale shi zai kutsa cikin daji, shi ne aka sami wani Zaki ya fi Karfinsa ya halaka shi ya cinye shi bai bar komai ba sai kai da Kafafuwa kawai. Saboda haka suka haka rami suka bizne shi. Amma Allah Ya ba su ikon kashe zakin. Da mutane suka ji wannan mugun labari sai kowa ya barke da kuka, wani ba ya jin na wani. Kanin Sarki kuwa sai birgima ya ke ta yi a Kasa, ana rirriKe shi ana ba shi magana. Wasu kuma suna tausaya masa saboda rashin yayansa mai kama da mahaifi da ya yi.
Nan take masu busa Kaho suka yi ta busawa, wadanda suke cikin daji suka yi ta fitowa suna dawowa sansani don sun san babu lafiya. Bayan an kammala taruwa, sai aka dunguma zuwa gari kowa na hawaye. Kanin Sarki kuwa duk ya Kuje fuskarsa da faratansa wai shi bakin ciki. Lokacin da labari ya kai gari ai abin babu kyau, kuka yaro da babba, kuma ba mace ba namiji. Da ganin mutanen wannan gari lallai ka san suna cikin wani lamari mara dadi. Shi kuwa Kanin Sarki sai aka sa mutane kusa da shi don su lura da shi, wai kada a Kyale shi shi kada ya kashe kansa.
To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda,



HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 3 Add to Reading List


YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

A JIYA MUN TSAYA

To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda,

ZAMU TASHI

‘yan fashi suka far masa suka Kwace mana dukiyarmu. Shi kuma suka yi masa dukan tsiya, na dawo na same shi cikin wannan hali.”

Nan da nan Ardo Jumare ya sa aka ba su bukka, ya ce aje wurin ‘yarsa can cikin daji a ce ta kawo madara mai zafi za a ba baki.



Wannan Ardo yana da shanun da sun fi dubu biyu. A dalilin haka ne ya dauko jingar wani saurayi yana taya ‘yarsa da suke yi wa lakabi da Bingyel da Kaninta mai suna Harande kiwo.

Yarinya ‘yar Fulani ta tatso madara ta cika gora – makil ta kawo. Mahaifinta ya umurce ta cewa ta mika wa bakin da ke cikin bukka, sannan ta gaggauta ta koma daji ta hado wa mara lafiyar maganin jini. Lokacin da ta shiga cikin bukkar don mika madarar, sai suka yi ido hudu da Bashari. Nan fa suka Kurawa juna ido kamar sun san juna, shi bai karbi gorar ba yana kallonta, ita kuma ba ta ajiye ba. Can sai kunya ta kama ta, abin ka da mace kuma bafillatana, sai ta ajiye gorar madarar ta ruga cikin daji don kawo maganin.


Fitarta ke da wuya sai Bashari ya fara sambatun cewa, “Allah da iko Ya ke, tun da na zo duniya ban taba ganin yarinya mai kyau da cikar halitta irin wannan ba, kuma ikon Allah a cikin rigar Fulani. Ni

Www.bankinhausanovels.com.ng na tabbata ko birnin Misra ko Sin da ake cewa manyan birane ne a duniyar nan ba za a sami mai kyan ta ba.” Ya tsiyayi madara ya tallafo kan Sarki ya dura masa. Can bayan wani lokaci sai Ardo ya fito da wani garin bakin mahadi ya cewa Bashari, “Gobe tun kafin mara lafiyar ya ci abinci, a duntsi maganin dan daidai Kima a gauraya shi da wanda yarinya za ta kawo. Maganin ya zama shi ne zai fara sha, kuma a cika masa cikin sa da shi.” Da yamma yarinya ta dawo daga daji rike da wasu saiwoyin magani, tana zuwa ta gyara su ta hau su da daka har sai da suka daku likis, sannan ta kwashe a cikin wani akushi ta rufe ta miKawa Bashari kanta a sunkuye. Watakila saboda kunyar kada a maimaita abin da ya faru dazu. Bayan an kammala cin abincin dare, sai ta dauko wata sarewa ta fito waje ta yi kwanciyarta rigingine a kan buzun ragon da ta shimfida cikin hasken farin wata. Busarta na tattare da wani irin sanyi wanda a cikin zuciya kawai ake iya jin sa. A daidai wannan lokaci kuwa, shi Bashari abin ya gauraye masa ne da cewa yana can gefe daya kwance a kan tasa tabarmar. Zuciyarsa ta yi sanyi, idanunsa kuma na ta kallon yadda wata ke ta kaiwa da komowa cikin giragizai, -_



Www.bankinhausanovels.com.ng ko kuma giragizan ne ke kai wa da komowa? Oho! Shi dai ba ya iya tantancewa.

Lokacin da dare ya dan daga, sai yarinya ta shige cikin bukkarta. Shi ma kamar ita ya ke jira, tana shigewa sai ya yi zumbur ya mike ya shige wurin mara lafiya. Har gari ya waye dukkan su shi da ‘yar Fulani babu wanda ya samu ya yi wata cikakkiyar runtsawa. Tabbacin cewa sun fara kamuwa da son juna.

Wayewar gari ke da wuya, sai Bingyel ‘yar Fulani ta tatsi madara ta dafa ta zuba zuma ‘yar kadan ta nufi bukkar su Bashari. Tana zuwa sai ta yi sallama, ta shiga ta gaishe shi cikin ladabi, ta ba shi ta ce masa – nasa ne shi kadai tare da tunatar da shi cewa mara – lafiyar ba zai ci komai ba wannan safiyar sai dai magani kadai. Ta yi murmushi shi ma ya yi, ta dukar da kai ta juya cikin . hanzari

Bashari ya tallafo Sarki ya ba shi hadadden maganin nan. Abin mamaki aka yi sa’a ya yi ta sha har sai da ya rage kadan, shi kuma Bashari ya dauki madararsa ya shanye sai kwaryar. Yana ajiyewa sai gyatsa.

Bayan dagawar hantsi sai ga Sarkin Fulani ya shigo don duba mara lafiya. Ya tarar barci ya dauke shi, sai ya cewa Bashari “Da ma na san barci zai dauke shi

saboda haka al’adar maganin ta ke, kuma ba zai tashi ba sai misalin yammaci. Saboda haka kada ka kuskura ka tashe shi sai ya tashi da kansa.”

Bashari ya ce, “To Baba, Allah Ubangiji dai Ya saka muku da alheri.”

Ardo ya amsa da cewa, “Amin yaro, ai irin wannan yi wa kai ne, yau gare ka ne gobe ga waninka.”

Ardo Jumare ya fice ya nufi gindin wata itaciyar cediya ya zauna yana tufkar igiya.

Bingyel ta fito ta nufi garkensu ta kora shanu zuwa cikin daji, tana tafiya tana busa sarewar nan ta jiya. Shi kuwa Bashari gaba daya sai hankalinsa ya rika bin inda sautin sarewar ke nufa. Can bayan wani lokaci, kasancewar ya san cewa mara lafiya ba zai neme shi ba, sai ya sulale ya nufi inda sautin sarewar nan ya nufa dazu. Ya yi tafiya mai tsawo amma bai gan ta ba, ya sami gindin wata bishiya ya zauna tare da tsunduma cikin kogin tunanin abubuwa mabambanta.



Can sai ya sake jiyo sarewar na tashi, ai kamar wata kibiya ya mike ya nufi wurin. Yana zuwa sai ya gan ta a kan reshen wata bishiya tana wasa da Kafafuwanta. Bashari ya yi zamansa KarKashin bishiyar alhalin ita ba ta ma saniba.

Can sai hankalinta ya yi wo Kasa, sai ta ga mutum

Www.bankinhausanovels.com.ng zaune, kuma ba tare da bata lokaci ba ta gane ko wane ne. Mamaki ya rufe ta, sai ta diro.

“Yar Fulani ta ce, “Kai kado yaya aka yi ka zo amma ba ka yi mini magana ba

Bashari ya ce, “Don Allah ki yi hakuri, busarki mai sanyaya zuciya nake matukar jin dadi, sai na yi tunanin in kin san na Zo, to kina iya dainawa, shi ya sa ko sallama ban yi ba. Sai na yi burin da ace ni ma na iya busa irin wannan sarewar mai daukar rai fa?”

Sai ta yi murmushi
DOWNLOAD
DOWNLOAD

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

6 months ago

Reply

Good

avatar
taskar

6 months ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment