Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu fitilun duk sun bace sai dai lambun nan a yadda ya ke a da.

Saurayi Idrisu ya shiga magana da kansa a kan abin da ya dauka tunani ya ke yi a cikin zuci, “To ni dai wannan yarinya ko mutum ce ko aljana in Allah Ya yarda sai na aure ta, komai wahala komai dadi, ko rai ko mutuwa ni duk daya ne a wurina, sai dai in ita yarinyar da kanta ta ce ba ta so na… amma kuwa idan ta ce ba ta so na… hmm, to ai gara in mutu kawai in huta da rayuwa cikin tunanin ta tsawon rai.

Af, to ta yaya zan gan ta har ma in ji ko tana so na din? Shi ke nan in dai har zan zauna a wannan daji har Karshen raina kuma wannan aljana tana fitowa duk dare ina gani tare da jin wakarta, to ni na yi alKawaria nan rayuwata za ta Kare.”

Tun daga wannan lokaci bai sake barci ba, yana ta tunani daban-daban har zuwa lokacin da gari ya yi sha zai waye, nan da nan ya tashi ya yi Sallah waddaa ciki ya roki Allah bukatunsa. Bukatar farko da ya gabatar a kan ilmin da ya fito nema ne, sai kuma bukata ta biyu wadda yanayi ya sa shi, wato samun wannan kyakkyawar yarinya da ya ke gani cikin dare, wadda kuma bai san labarinta ba.

Ya dauki tulu ya rika debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya har sai da ya yi sawu goma. Ya je wurin dokinsa yana goggoge masa jikinsa yana tunani a cikin ransa yana cewa, Lallai komai yana da dalili, kuma duk

Www.bankinhausanovels.com.ng wanda ya yi biyayya ga malaminsa, to babu shakka ba

zai yi a banza ba.” Yana mai Kara mamakin abin da ke wannan wuri.



Gari ya waye sosai, rana ta bayyana, ya nufi dakin malam, suka gaisa tare da cin abinci kamar yadda suka sabaa kullum.

Malam ne ya fara magana, “Ya kai Idrisu, yau ranar hutu ce ba ranar karatu ba, saboda haka idan hantsi ya yi sosai, sai ka zo da dokinka mu tafi ga fili can zan fara koya maka dabarun yaki iri-iri.”

Idrisu ya ce, “To.” :

Idrisu ya shiga tunani a cikin zuciyarsa, “Kai wannan dattijo yana da ban mamaki, ina wannan tsoho mai yawan shekaru zai iya yin wani abu game da yaki bayan duk ya kwararrabe?”

Dagawar hantsi ke da wuya sai ya je ya janyo dokinsa, sannan ya shiga cikin dakin malam ya sanar da shi cewa shi ya riga ya shirya. Nan da nan dattijo ya yi damara kamar wani shahararren mayaki ya fito, sai Idrisu ya cewa kansa, “Lallai wannan mutum da gaske ya ke.”

Idrisu ya bi shi har suka isa Katon filin nan, dattijo ya sa takobi ya saro wani dogon itace, ya sassake shi ya yi tsini kamar mashi. Daga nan fa ya fara koya wa Idrisu yadda ake dabaru da hilolin yaki. Suka yi ta yi

har rana ta take, jikin saurayi ya yi liKis sannan suka

koma dakunansu suka yi wanka. Shi Idrisu yana cikin

wanka yana tunanin irin Karfin wannan dattijo, yana kuma tunanin, “Ni da na fito makaranta neman ilmi ga shi na buge da koyon yaki? … amma dai baa Kin ta manya.” ,

Ya gama, ya sa suturarsa ya je wurin malam, suka ci abinci tare da yin Sallar Azahar. Bayan sun idar ne sai malamin ya shiga karantar da shi hilar yaki a karance cikin darasi har sai da Idrisu din ya fara yin hamma saboda gajiya da kuma tsamin da jikinsa ya yi.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Dattijo ya ce, “Kamata ya yi ka je ka dan huta.”

Idrisu ya yi matukar jin dadin wannan kalami. Cikin dan Kankanin lokaci sai ga shi a kan gadonsa, kuma kafin ka ce haka, barci ya kwashe shi. Malam ya ga Magriba ta Karato babu ko motsinsa, sai ya tabbatar da cewa lallai gajiyar dazu ce ke tambayar sa, saboda haka sai ya je Kofar dakinsa. Ya kira shi karo na daya, ana biyu ya ji ya tashi.

Dattijo ya ce, “Ya kamata ka tashi don Magriba ta kusa. Na Kyale ka ka dan kara ko da sa’a daya ne don ka dan warware.”



Idrisu ya tashi ya gabatar da Sallar La’asar sannan suka yi Magriba tare. Isha’i ta yi suka yi tare da cin abinci kamar dai yadda suka saba. Www.bankinhausanovels.com.ng

IDRISU dai yana tare da malaminsa Shaihi

Ibrahim dan Yahaya yana ta daukar darussa tare

da bin umurninsa, kumaa kullum dare yana ganin yarinyar nan mai tsananin kyau amma bai san labarinta ba kuma babu dama ya yi tambaya. Ya kamu da tsananin son ta amma ba su taba magana ba, kumaa duk ranar da ya yi nufin tsallakawa zuwa wurinta, sai dokinsa Jagora ya hana shi.

Yana nan a cikin wannan kungurmin daji daga shi sai malaminsa da dokinsa da kuma abubuwan mamakin da ya ke ta gani har na tsawon shekara amma bai taba tambaya ba kamar yadda aka umurce shi.

Cikin shekara daya Idrisu ya sami karatu mai dumbin yawa a wurin dattijo, kuma bugu da Rari ya koyi dabarun yaki iri daban-daban da tsananin juriya. Daga cikin mafi muhimmancin dabarun da ya koya akwai kariyar kai da zamiya a wurin yaKi ba tare da amfani da

garkuwa ba, alhali kuwa hakan babbar baiwa ce wadda

samun irin ta sai an tonaa duk fadin duniya da wajenta. A kwana a tashi ba wuya, wata rana sai dattijo Ibrahim dan Yahaya ya ce masa, “Gobe ne kake cika shekara daya cur a nan muna tare ba ka taba saba mini ba, na tabbata ka yi mini biyayya kamar yadda na umurce ka. Na tabbata kai yaro ne mai cikakken ladabi, kuma wannan ya nuna irin ingantacciyar tarbiyyar da ka samu daga wurin iyayenka, babu shakka kana da iyaye nagari, kuma ga shi za ka shiga duniya. Ni dai na tabbata za ka yi nasara in ka ci gaba da kyawawan halaye irin wadanda ka nuna minia nan.”

Www.bankinhausanovels.com.ng

Dattijo ya sa hannu ya dauki akushin dabgen naman jiminar da ke gabansa ya ajiye gefe yana mai ci gaba da yi wa Idrisu bayani.

“Ya kai dana Idrisu, a yau zan ba ka labarina da sauran abubuwan da kake gani a wannan wuri na mamaki. Na farko dai shi ne, wannan doki naka da ka sa wa suna Jagora, to babu shakka ka rada masa sunan da ya dace da shi don zai yi maka jagoranci har sai ka sami nasara.

Babu irin rukukin da ba za ka iya shiga da shi ba, kuma sauran abubuwan mamaki na wannan doki sai nan gaba za ka rika gani. Sannan kuma dai, matuKar ka kasa

gane hanya, to duk inda ya nufa da kai ka yale shi, in Allah Ya yarda zai kai ka inda alheri ya ke.”

Www.bankinhausanovels.com.ng

Dattijo ya ci gaba da cewa Idrisu, “Kamar dai yadda na taba shaida maka ne cewa al’umma tana sakani daya daga cikin shahararrun malaman zamani, wanda kuma shi ne dalilin da ya sa mutanen Kasarmu suke kira na da suna Shaihu kuma suke ganin a wurinsu babu masanin fannoni kamar ni. Da ace ana gadon karatu, to da sai in ce ni na yi gadonsa ne daga wurin mahaifina shi kuma daga wurin nasa mahaifin. In dai girmamawa ce daga Sarkin Kasarmu sai ni. Abin da ya faru da ni shi ne Allah da ikonSa Ya ba ni ‘ya guda daya tak, ita kuma wannan ‘ya tawa Allah Ya jarrabe ta da wani abu wai shi kyau, tsananin kyan nata har mamaki ya ke ba ni, ko da yake babu abin da ya fi Karfin Allah. Saboda tsoron yawan surutai na mutane, ya sa gaba daya ma na hana ta fita waje.

Na karantar da ita karatu mai dumbin yawa, kuma fanni-fanni. Ta fuskar manyan harsuna na duniya kuwa, Allah Ya yassare mata iya yin magana da masu yawa daga cikin su. Da wuya a sami malamin da zai Kure ta ta fannin ilmi sai dai in an yi da gaske. Saboda wannan ne da kuma hankalinta Allah Ya sa nake matuKar Kaunar ta. Kaunar kuma mai tsananin Mutane sun yo ca kowa yana kawo caffa amma Allah da ikonSa ba ta fitar da miji ba. Ya kai dana Idrisu bayan almajirci kuma Allah Ya sa Www.bankinhausanovels.com.ng

ina da wadata irin ta dukiya daidai gwargwado, don har ina da kuyangi mata guda bakwai tsarorin ‘yata. Sannan kuma ita wannan ‘ya tawa, Allah Ya yi mata baiwa da wani abu da ake kira fasaha, sannan ga dadin murya. Ta gauraya wadannan abubuwa biyu a cikin daya daga cikin abubuwan da ta fi sha’awa wato waka, babu shakka wannan yarinya ta shahara a fannin waka, in suka hadu ita da wadancan kuyangi nawa tana bayarwa suna amsawa, to ko kai wane ne sai bege ya kama ka.

Kullum dare abin ka da yara, sai su shige lambun cikin gidana suna wasanni tare da rera wakoKinsu.

Wani dare kamar yadda suka saba, sai hanya ta biyo da wani Sarkin aljanu ta wurin, yana kuma ganin ta sai ya rude, hankalinsa ya tashi kuma son ta ya kama shi yana mamakin wai dan Adam ne da irin wannan kyau.

Tun daga ranar sai ya kasance shi wannan Sarki na aljanu babu daren da ba zai zo wurin ba don sauraren wakokinsu, kuma abin ka da aljani, ka san shi yana kallon su amma su ba sa iya ganin sa. Ya shiga tunanin yadda zai hudo wa lamarin. A karshe dai ya yanke shawarar dauke ‘yar tawa kawai ya kai can inda babu mutane ta zama mallakinsa, Ya yi tunanin wani tsibiria daya daga cikin manyan tsibirai uku da ke bayan duniya. Babu dan Adam din da ya taba sa Kafarsa a wurin. Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan yanke wannan shawara sai aljanin ya nufi wancan tsibiri ya gina wani Kasaitaccen gida, ya rika zabo ‘yan mata ‘ya’yan mutane daga sassa daban-daban na duniya yana fyauce su yana kaiwa yana ajiyewa. Babu wadda ya Kyale, ‘ya’yan sarakuna, malamai, masu dukiya da talakawa, kuma kowacce ko kadan ba za ka yi kuskure ba in ka ce ita ce Sarauniyar kyau a gari ko Kasarsu.

Kamar kullum, wani dare yarinyar nan tawa da wasu daga cikin kuyangina suna cikin lambu suna wasanni da wake-wakensu sai wannan Sarki na aljanu ya sammace su da barci mai nauyi, ya dauke ‘yata ya nufi wancan gida na bayan duniya da ita, yana zuwa sai ya tashe ta. Farkawa da kuma tsintar kanta a wannan wuri suka sa hankalinta ya tashi, tsoro ya kama ta, tayi nan a guje, ta ruga can. Ta gama guje-guje da koke-kokenta kaf ta koma ta zauna tare da zuba wa sarautar Allah ido, tana mai mamakin irin halin da ta sami kanta.

Ganin ta natsu sai aljanin ya rikida ya zama mutum, ya fito, tana ganin sa sai ta sake rudewa, amma darasin da ta samu a baya ya tabbatar mata da cewa babu wurin gudu a wannan wuri, saboda haka ko tunanin hakan ba ta sake yi ba, amma dai a firgice ta ke. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ya ce mata, “Ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai same ki. Ni ne na gina wannan wuri kuma ni na kawo ki. Nan kina bayan duniya ne, babu wani dan Adam da ya taba zuwa nan cikin mutane sai wanda na kawo, kuma babu wanda zai taba zuwa. Kai ko aljani ma zuwa wannan wuri ya gagare shi sai dai irin gidanmu kawai. Don yankinmu ne, kuma kowa ya sani.”

Ya shaida mata cewa shi ne babban Sarkin aljanu na babbar daular aljanu ta Jarirul Waki-waki, sannan kuma ya nuna mata hadarin wannan gida da take ciki, cewa a kan wani dogon tsibiri ya ke cikin tsakiyar ruwa, saboda haka KoKarin gudu yana nufin mutuwa ke nan. Ya ce a cikin wannan gida akwai duk abin da za ta iya tunanin nema.

Ya fuskance ta ya ce, “Duk wannan abu na yi saboda ke ne, saboda irin Kaunar da nake yi miki, shi ya sa ma na shiga cikin duniya da kaina na zabo miki mutane ‘yan’uwanki don su rika debe miki kewa.”

Yana gama fadin haka sai ya bude wani sashe daga cikin gidan, sai ga ‘yan mata zuRa-zuka su hamsin, ya cewa ‘yata, “Wadannan duk bayinki ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng Su kansu sun yi mamakin kyan ‘yar tawa. Bayan ya gama labarinsa sai ya Bace, ya tafi ke nan. BaKin ciki ya rufe ‘yata har ta rera waKar bakin ciki mai ban tausayi. Ta yi ta koke-kokenta sauran ‘yan matan nan suka zagaye ta, wasu suka rungume ta, suna ba ta hakuri don su har sun saduda sun fara sabawa.

Bayan hankalinta ya dawo jikinta sosai, sai ta yi musu jawabin cewa, “Ya zama dole mu kwantar da hankalinmu don tabbas babu yadda za mu kubuta daga wannan aljani, dole sai mun yi hakuri watakila Allah Www.bankinhausanovels.com.ng

Ya kawo mana hanyar kubuta. Tilas ne mu sami _

natsuwa ta yadda za mu iya hilatar wannan mugun shaidani yadda za mu yi masa irin tamu ta mata mu kai shi mu baro, amma in muka ce za mu tayar masa da Kayar-baya, to babu shakka halaka mu kawai zai yi.

Shawara dai guda daya ce, ita ce kada mu kuskura ya – gane cewa muna cikin bakin ciki. In mun ji alamar zuwansa sai mu saki jikinmu mu shiga ‘yan wake-wake har shi ma ya saki jiki da mu, wanda daga nan ne a hankali zan sami damar binciken sirrinsa.”

Bayan yarinya’ ta kammala bayaninta sai dukkan su suka Kara sakankancewa da ita, suka sakar mata komai a hannunta, suka kuma saki jikinsu kamar suna gidajensu. Sai dai su yi wanka, su yi kwalliya don ga kayan kwalliyar nan birjik, kuma iri-iri sai wanda suka zaba. In sun ji aljanin yana zuwa sai su shiga kida da waka, suna rawa da rausaya da rangwada. In ya iso ya ga irin halin da suke ciki sai dadi ya lullube shi. “Yata ita ce ke ba da waka sauran suna amsawa. Ba alfahari ba, idan Www.bankinhausanovels.com.ng ka gan ta a tsakaninsu, sai ka ce wata ne dan daren

goma-sha-hudu a tsakiyar taurari. Yadda suke gane zuwan aljanin kuwa shi ne, wani irin Rugi sukan ji yana cida kamar ana hadari.

Bayan wani lokaci mai tsawo aljanin nan ya saba da su sosai, ya saki jikinsa kamar da ma sun yi shekara da shekaru tare. A duniyar nan kuma ya kasance babu abin da ya ke so kamar wannan yarinya ‘yata.

In suna waKoKinsu sai ka ga kafin lokaci Kankani barci ya kwashe shi saboda tsananin natsuwar da yakan samu a dalilin haka. A kullum yana tare da su, kumaba ya barin wannan tsauni sai yamma ta yi likis sannan zai koma cikin ‘yan’uwansa aljanu. Ranar Asabar ce kawai ba ya zuwa saboda ranar bauta ce a wurinsu.

Wata Asabar ‘yan matan nan suna cikin wani Katon daki mai shimfidun alfarma suna kewar gidaje da garuruwansu don sun san cewa aljanin ba zai zo ba, sai kwatsam suka ji wani irin ruri mai Karfin gaske kamar gidan zai tsage. Dole suka firgita don ba su taba jin rugi mai tsoratarwa kamar haka ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Nan da nan suka shiga addu’a suna neman tsari wurin Allah.

Bayan lokaci kadan da jin waccan mummunar Kara, sai suka ji shiru. Daga nan sai wani irin Kanshi wanda ba su taba jin mai dadin sa ba ya budade wurin gaba daya. Bayan sa sai suka ga wani irin hayaki ya turnuke, siffarsa kamar bakan gizo, yana da launin shudi, ruwan goro, kore, ja da algashi. Can bayan wannan hayaki ya baje, sai suka ji muryar wata mace tana cewa, “Yau kwananku sun kare. Sai dai wasu ba ku ba.”

Suna jin haka sai hankalinsu ya tashi suka dimauce suka sakankance da mutuwa, amma duk da haka sai suka ci gaba da yin addu‘o’in neman tsari, kowacce tana yi da irin abin da ya zo bakinta ko kuma ta yi imani da shi. : Www.bankinhausanovels.com.ng

Allah cikin ikonSa Ya amshi addu’arsu, Ya ba ‘yata Karfin hali ta ce, “Ko wane ne ke son halaka mu ya kamata ya fito fili mu gan shi tukuna, kuma ya fada mana dalilin halakawar, in muna da ta cewa sai mu ce. Amma in wanda ke son halaka mu din ya aikata haka ba tare da mun gan shi ba, to kuwa lallai yana daga cikin azzalumai.” -Suka sake ganin hayakin ya murtuke jajawur, sai ya Bace, sai ga wata mace wadda ta dan dara su shekaru ta bayyana. Babu shakka wannan mace Allah Ya yi mata kyau, kai da ganin ta ka san ba mutum ba ce. Irin adon jikinta kurum ba su taba mafarkin ganin irin sa ba.

Suka ga fuskarta a daure babu annashuwa ko kadan. Lallai da gani ta shiryo sharri a ranta. Aljana ta ce, “Yau kwananku sun kare, mugaye,

Www.bankinhausanovels.com.ng mazinata! Babu mai ceton ku, babu mai kare ku don kuwa lallai yau za ku bakunci barzahu.”

Furta haka ke da wuya sai wadannan ‘yan mata suka

firgita, firgici mai tsanani tare da kara sakankancewa da mutuwa. ‘Yata ce ta yi Karfin hali ta yi saurin amsa mata. “Abin kuwa da mamaki, irin yadda kyakkyawar mace wadda ga dukkan alamu kyan ba na jiki ba ne kawai har zuci… a gaskiya Bacewar basira ce kawai za ta sa kyakkyawa kamar ki ki aikata mugun hali. Me muka yi miki da kike son hallaka mu?” Sai suka ga fuskarta ta yi haske har ta dan murmusa sannan ta cewa ‘yata, “Ashe ina da kyan da har ke kike yabawa? To gaskiya a da na zo da sharri ne amma yanzu na ji zuciyata ta yi sanyi. Yanzu kuma zan ba ku dalilin da ya sa nake son halaka ku.

Www.bankinhausanovels.com.ng

Na dade ina kashe mata da yawa ba don komai ba sai kishi.

Ina daya daga cikin kyawawan matan aljanu, kuma . shi wannan Sarkin aljanu da ya kawo ku nan dan‘uwana ne. Tun yana saurayi soyayya ta shiga tsakanin mu. _

Muna cikin kogin soyayya, haka kurum wata rana sai ya shiga soyayya da wata mace ‘yar. Adam ya yi mini wulakanci mai yawa, ya karya alkawari, kuma -a Www.bankinhausanovels.com.ng al’adarmu in Sarki ya taba neman mace, to ita wannan aljana babu wanda zai sake neman ta har abada. Wannan yana daga cikin dalilan da kan sa ku ga wasu matan aljanu suna auren wasu mazajen na mutane.”

Aljanar ta Kara da cewa, “Bayan wannan aljani ya yi mini wulakanci, sai na yi yunkurin tayar masa da kayar~ baya amma sai ya sa aka kulle ni a cikin wani daki har na tsawon shekara ashirin. Daga baya kakarmu ta roke shi ya sa aka sake ni. Ni kuma na yi alkawarin in dai zan gan shi da mace ‘yar Adam, to babu shakka zan halaka ta. Na kashe ‘yan matan mutane sun fi a kirga a dalilin wannan mugu. .

Yanzu ma abin da ya sa ya kawo ku wannan tsibiri shi ne don babu aljanin da zai iya zuwa nan sai wanda ke da jinin sarautar gidanmu a jikinsa. Kuma ya kawo ku nan din ne don kada wani abu ya taba ku. Niyyata ita ce in kashe ku in ya so duk abin da zai faru ya faru, amma da ya ke kuna da sauran shan ruwa, sai kika yi mini magana, kuma a cikin maganarki na ji kin ce mini kyakkyawa, to mu kuma matan aljanu babu girmamawar da ta fi ki cewa aljana tana da kyau. Duk wadda kika ce wa haka, to kin gama da ita.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Shaihi Ibrahim dai ya ci gaba da ba Idrisu labari cewa, da ‘yarsa ta ji jawabin aljanar nan sai ta sami makama, don irin dabi’ar dan Adam na dogon tunani. Sai ta ce

Hmmm kuci gaba da bibiyarmu donjin cigaba Www.bankinhausanovels.com.ng YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

A JIYA MUN TSAYA

Yahaya ya ce mata, “A nawa zan nome miki ciyawar?” Gimbiya ta ce, “A matsayin Gimbiya ‘yar Sarki.” Yahaya ya ce, “Albarka.” Gimbiya Lubna ta ce masa, “To don soyayya.” Sai Yahaya ya kalle ta don tabbatar da cewa ita ce da kanta ta fadi abin da kunnuwansa suka ji, kuma tabbatar da hakan ya sa kawai ya ji zuciyarsa da bakinsa a lokaci daya suna amsa mata cewa, “An sayar. Saina Zo.” Ya juya zai tafi sai ta ce, “Mu je in raka ka.” Sai yace mata, “Haba yaya ‘yar Sarki za ta raka bawa mai lambu?” Gimbiya ta amsa masa, “Ba ‘yar Sarki ce ke yi maka rakiya ba, masoyiya ce take yi wa masoyinta rakiya. Kuma ba na fata mai magana ya sake irin maganganun da suka wuce a baya, don da ace a yau mahaifina ba ya wannan duniya, kuma a ba ni damar zabo mai maye gurbinsa, to babu shakka zan ce mai lambu, don irin tsananin dimauta da na yi a kan rashin tsoronsa game da gaskiya.” Sai Yahaya ya ce, “Da ace mai magana ta san yadda

ZAMU TASHI

mai lambu ke ji a zuciyarsa game da kyakkyawa abin son kowa, to lallai da kin tausaya mini, ni ma duk maganganun da na yi dole tasa ni, don ba na son raini, sannan kuma da irin zancen nan da masu iya magana ke cewa, “Abin da ba ka samu, to hada shi da bana so.” Lallai ni ina tsoron kada mu zurfafa cikin kogin soyayya, a karya mini zuciya daga baya kuma masu mulki su ki amincewa da talaka mai lambu.” Gimbiya ta yi murmushi sannan ta ce, “Kada mai magana ya karaya, ba a san namiji da tsoro ba. Kuma ina son mai lambu ya tuna cewa ita fa duk wanda zuciyarta ta amintu da son sa, to shi ne sarkinta. Amma in ka ga mace dukiya ko mulki su ne dalilan da take gina soyayya a kansu, to babu shakka mayaudariyar kanta ce.” Jin haka ya sa Yahaya yin murna da kuma tabbatarwa kansa cewa lallai wannan yarinya ta san abin da take yi. Sai ya ce, “Ya ke kyakkyawa, yanzu lokaci ya yi da zan koma lambu, don na tabbata Sarkin lambu zai damu in ya ga ban dawo da wuri ba. Kin san mutumin nan yana ji da ni kamar dan autansa.” Washegari bayan kammala aikin lambu, ma’aikata duk suna ta haramar komawa gidajensu, sai Sarkin lambu ya kira Yahaya yana jan sa da labari a hankali Www.bankinhausanovels.com.ng suna tafiya har sai da suka yi nisa da sauran jama‘a,

suka sami Karkashin wata itaciya mai yawan inuwa suka zauna. Sarkin lambu ya ce, “Ya kai Yahaya. Kai dai saurayi ne wanda babu shakka Allah Ya yi maka hankali da natsuwa. To abin da nake son shaida maka shi ne, ni — na aminta da kai wanda kuma har hakan ne ya sa nake shaida maka wannan sirri. Tun da Sarki ya amince da kai har ya yarda ka rika kai wa Sarauniya kaya marmari, to ina yi maka gargadin cewa ka yi hankali da ita wannan mata ta Sarki, don kuwa ba ta da mutunci ko kadan, sannan kuma ba ta da kamun kai. Ko kadan ba ta jin tsoron Allah. Sannan kuma wani babban abin takaici shi ne ko kara ta gifta a gaban Sarki, to ba zai Ketara ba saboda tsananin tsoron kada ya bata mata rai da ya ke yi. A yau da a ce Sarauniya za ta ce tana son kan Waziri, to babu shakka kuwa Sarki zai sa a saro mata.” Sarkin lambu ya Kara da cewa, “Ai ka gaa da nine Sarkin yaki na wannan kasa, kowa so ya ke yi ya ganni don tsananin jaruntar da Allah Ya ba ni, na shahara matuka da farin jini fiye da yadda kake zato. To wata rana an yi shiri tsaf za a tafi fagen fama, sai Sarauniyar nan ta ce da ita za aje, haka kuwa aka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng Aka dauki mako biyu ana gwabzawa. Na yi budawar tawa irin ta jarumai, na

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment