Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gudu ba, don kuwa tun

Www.bankinhausanovels.com.ng da har hanya ta biyo da ni ta nan, to ya zama dole a kaina in hana zalunci in ceci duk wanda ke cikin garin nin da kuma duk wanda hanya za ta biyo da shi nan gaba. Saboda haka ina zaton abin yi kawai shi ne yanzu bari in sake ku ku koma cikin gari, ni ma ba da dadewa ba ina nan shigowa.”

“Yan mata suka ce, “Wai! Ai babu yiwuwar haka. Dalili kuwa shi ne yanzu in ka sake mu muka koma, to Sarauniya tana da matsanancin wayon da za ta iya gane cewa mun yi wani shiri ko kuma wata magana da kai, kuma ko shakka babu da ranmu za a dafa mu. Kasancewar ita a irin nata tunanin babu yadda zaa yi ka yi nasara a kan mutumin da ke son kashe ka amma kai kaqi kashe shi.”
Sai suka ce, “Abin da zai fi dai shi ne ka sa mu a gaba a daure, mu nufi cikin gari, in ta ga haka, to ba za ta yi wani zato ba. Kuma da ya ke mun ga akwai amana tattare da kai, to za mu fada maka wani sirri don kada ka cutu. In kuma ka kuskure, to kuwa ba

shakka za ta halaka ka.

Lallai ka yi matukar taka-tsantsan da kyau, kasancewar mun san a irin abubuwan da ka aikata babu shakka yanzu za ta bukaci halaka ka da kanta ne. Na farko dai tana da wani tsafaffen takobi, ko da yake mun ga naka takobin ya fi nata ban mamaki.

Www.bankinhausanovels.com.ng Tana da wani irin doki, wanda ya yi matukar horuwa, kai hasali ma wani lokaci ya fi dan Adam dabara. Ita wannan Sarauniya tamu tana da wani irin kyau wanda in har ka kalli fuskarta kuma kuka hada ido, to dole ka ji ka yi sororo ka kasa tabuka komai har kama ka ya fi sauki fiye da kama kaza, har in ta ga dama tana iya sa takobi ta buge wuyanka ba tare da ka ankara ba.

In kuma har ta ba ka ruwa ko kuwa waniabin sha, to shi ke nan ka gama yawo, don akwai wani irin dafi da kan lalata kuzarin jiki a ciki. Tana kuma dai da wata kujera ta zinare wadda za ka dauka ta alfarma ce, amma matukar ka zauna a kai, to Sarauniya tana iya sa kujerar ta zame da kai kuma bazakazameko ina ba sai ramin macizanta. Ko kuma duk in ba ta Bullo maka ta nan ba, to tana iya neman aikata masha’a da kai, wanda kuma matukar ka amince, to sai wani ba kai ba.”

Da Idrisu ya ji zancensu sai ya tabbatar da cewa lallai gaskiya suke fada masa, saboda haka sai ya yi musu alkawarin lallai zai yi iyaka Kokarinsa wurin kare su daga sharrinta.

Bayan wannan tattaunawa sai ya sa su a gaba, shia saman doki su kuma a Kasa daure tamau da juna, suna tafiya Kafafuwansu na sarsarkewa ya nufi cikin

Www.bankinhausanovels.com.ng gari yana yi musu hargowar da ke nuna kamar ba ya tausayin su. Da aka hango su nan da nan ‘yan kar-takwana dake kusa da kofar gari suka sanar da Sarauniya ita kuma ta ba da umurnin cewa a bude Kofar gari. Idrisu bai zame ko ina da su ba sai Kofar fada.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye a zaurenta na shiga, tana cikin kaiwa da komowa aka sanar da ita isowar jarumi da ‘yan matan da ya daure. Ta ce a sanar da shi tun da ya shigo cikin garinta, to ya sako mata mutanenta. Shi kuma sai ya amince don kokarin tabbatar mata da cewa ba tashin hankali ya kawo shi ba. Wadannan daurarrun mata suka sami Sarauniya suka zube suka yi gaisuwa. Ta tambaye su dalilin da suka kasa samun nasaraa kan wannan mutum. ;

Suka ce mata, “Ran shugabar duniya ya dade, mun yi iyakacin kokarinmu amma ya fi karfinmu. Kumaa gaskiya mu mun tabbata cewa in ba ke da kanki ba wannan mutum samun wanda zai iya masa sai an tona. Zakokin nan ma fa kashe su ya rika yi kamar , yana kashe ‘ya’yan kyanwa.”

Da Sarauniya ta ji an yabe ta a kan cewa ita ce za ta iya maganin abin da ya gagara sai ta ji dadi a cikin

ranta, ta umurce su da su je su yi wanka su ci abinci su Www.bankinhausanovels.com.ng huta su kuma kasa kunne tare da zura idanu su ga yadda za ta yi da wannan dan tahaliki.

Idrisu kuwa yana can tsaye a inda aka umurce shi a Kofar fada yana ta mamakin irin kyan garin yana kuma sauraren abin da zai je ya zo a daidai lokacin da Sarauniya ta zagaye ta je gidan sarkar da ake ajiye manyan gagararrun jaruman da aka kama ana kiwonsu don bai wa macizai, ta same su ta fitar da wadanda suka fi gogewa guda dari ta kawo kayan yaki ta basu.

Ta fara yi musu jawabi, “Ya ku wadannan jarumai, ga rana ta zo wadda kowannenku zai nuna tare da tabbatar da jaruntarsa har in yi farin ciki da shi. A da na jarraba ku ne na sakaya ku anan don in ga wanda a zahiri zai zauna a garin nan saboda ni, kuma yanzu duk na tabbatar ku masu Kaunata ne, sai dai kun san kuma dole daga cikin gwanaye a fitar da gwani guda daya.

Akwai wani jarumi yana can a Kofar fada, kashe shi ko kuma kamo mana shi a hannu shi ne sadakina, saboda haka daga cikinku duk wanda ya sami nasara

zai zama mijina, kuma in har hakan ta kasance, to kun ga dole ke nan in sauka daga karagar mulki mijin da na aura ya hau.”

Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai,

Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su.

Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi.

Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul.

Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya ta magani ya sha tukuna.

Wannan maganin shi ne makarin dafin da ke jikinsu wanda ke hana su katabus. Yanzu sai suka ji kamar an cire musu kaya, kuma Karfinsu ya dawo jikinsu.

Duk abin nan da Sarauniya ke yi akwai wani saurayi daga cikin jaruman nan da ke ji kamar ya kashe ta don irin wulaKancin da ta yi musu a baya,

HMMM LABARU FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 17 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng


MUN TSAYA

Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai,

Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su.

Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi.

Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul.

Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya ta magani ya sha tukuna.



Wannan maganin shi ne makarin dafin da ke jikinsu wanda ke hana su katabus. Yanzu sai suka ji kamar an cire musu kaya, kuma Karfinsu ya dawo jikinsu.

Duk abin nan da Sarauniya ke yi akwai wani saurayi daga cikin jaruman nan da ke ji kamar ya kashe ta don irin wulaKancin da ta yi musu a baya,

ZAMU TASHI

kuma ya tabbata cewa duk wadannan alkawura da take yi musu na Karya ne da yaudara, amma babu yadda zai yi, musamman da ya lura da yadda sauran abokansa suka dimauta.

Saboda haka sai ya zura idanu don ganin abin da ya gagare ta da har za ta yi Kokarin jefa su cikin hadari, watakila ma, kai ba ma wataKila, ya tabbata abin nan duk yadda aka yi ya fi ta gaskiya.


Wannan saurayi mai suna Abdurrahman dan wani babban Sarki ne. Dalilin fadawarsa hannun Sarauniya kuwa shi ne ya fito neman budurwarsa ne wadda Sarkin aljanu Sham’una ya sace. Sarauniya ta ba da umurnin cewa a je a cika wa Idrisu aiki.



Nan da nan jarumai suka sukwani dawakansu, suka nufi inda jarumi Idrisu ya ke, kowanne yana gudu yana jefa mashi sama yana cafewa, yana sarar iska da takobi. Sai dai kuma da suka kusa da inda ya ke sai gardama ta sarke tsakanin su a kan cewa kowannesu yana son shi ne zai je ya cafko jarumin. Suna tafiya suna jayayya, har suka zo gab da gab.

Jarumi Idrisu ya daka musu tsawa, “Kai! Ku dakata, ina so ku dawo cikin hankalinku, ku tuna cewa wannan mata mayaudariya ce, ku tuna abin da ta yi
muku da farko, babu shakka in kuka yi nasara a kaina

Www.bankinhausanovels.com.ng za ta sake yaudarar ku. Saboda haka ina kira a gare ku cewa ku zo mu hada kai mu yake ta.”

Sai jaruman nan suka fara maganganu, “Kai ba mu son rashin kunya, yaya ga Sarauniya Zankadaziyya da sarautarta gaba daya muna kallo an kasa a faifai sannan ka ce za ka yi mana wani dadin baki? In ba ka son wulakanta ka zo mu je kawai ba tare da wani bata lokaci ba.”

Idrisu ya tambayi dalilin sa sarautar Sarauniya a faifai sai suka ce, “Ranka. Duk wanda ya kashe ka shi zai auri Sarauniya kuma ya zama Sarki a wannan gari.”

Idrisu ya yi murmushi ya ce, “Na tabbatar tare da rantse muku cewa yaudarar ku take yi. Ku yi tunani da kyau, ba na son yin fada da ku, saboda haka ya ku wadannan jarumai masu daraja ku yi hakuri ku kauce kawai ku Kyale ni da ita.”

Sai suka ce, “Zancen banza, ai yau ko digon jininka ne ya rage sai mun lashe shi.”

Can sai saurayin nan dan Sarki, wato Abdurrahman ya ce wa Idrisu, “Lallai malam kana da gaskiya, ni kam ina tare da kai, kuma na ba ka aminci. Ko mutuwa ce, to ni na amince mu mutu tare.”

Yana gama wannan magana sai ya zaburi dokinsa

Www.bankinhausanovels.com.ng ya Karasa wurin Idrisu ya mika masa hannu suka gaisa. Ya ce wa Idrisu, “Kyale ni da wawayen nan marasa tunani, kyan fuska ta sa sun mance masifar da tasa mu ciki.”

Sauran jarumai da suka ga daya daga cikinsu ya Balle, wanda a da suna zaton wata hila ce ya yi don kama Idrisu, amma sai suka ga da gaske ya ke yi cewa ya koma wurinsa, sai uku daga cikinsu suka zaburo, shi kuwa wannan saurayin jarumi ya fuskance su, kuma ba tare da wata matsananciyar wahala ba ya aike da biyu barzahu, dayan da ya ji wuya sai ya juya a guje. Ganin haka sauran jaruman suka yanke shawarar kai dauki baki daya.



Idrisu ya juya gindin mashi, shi da saurayin nan suka zaburi dawakansu, fada ya barke. A gaskiya jaruman nan ba don irin Idrisu din suka samu ba, to lallai kuwa da sun gama da su cikin ‘yan dakikoki kadan, don kuwa jaruman ne sosai.

Duk Kokarin da Idrisu ya ke ta yi har ya ja artabun ya yi tsawo shi ne ko za su ji sun sha wahala su mika wuya don a fahimcijuna amma ina.

Bayan kamar sa’a daya da rabi ana gwabzawa sai su Idrisu suka sami nasara a kan jaruman Sarauniya. Sun kashe hamsin da uku, suka ji wa tara rauni, suka kuma kama bakwai suka daure, sauran kuma suka

Www.bankinhausanovels.com.ng gudu suka koma wurin Sarauniya a guje suka ba ta labarin yadda lamari ya wakana.

Ta ce musu, “Af, kun yiwo gudun mutuwa ne? To ai ita za ku tarar. Kuma in banda wautarku, ai ko da kun yi nasara a kan wannan jarumi kashe ku zan yi, ballantana kuma ku ne aka yi nasara a kanku.” Ta sa takobi ta yi ta dauke musu kai, kasancewar da za su karasa wurinta sai da kowanne ya zubar da makamansa, wanda hakan ya sa babu wani motsi mai tasiri da za su iya yl.

Daya daga cikinsu ne ya yi sa’ar zullewa a guje ya sami nasarar hayewa doki ya zabure shi, kuma umurnin da Sarauniya ta bayar na cewa kadaa bar shi ya kai bai yi amfani ba, don kuwa ya samu ya fice har ya isa gaban Idrisu. Yana zuwa sai ya zube yana cewa, “Ka cece ni kada ta kashe ni, ashe zancenka gaskiya ne.” Su kuwa ‘yan matan da suka biyo shi da suka ga ya isa wurin Idrisu sai suka toge, suka koma suka sanar.

Hankalin Sarauniya fa ya yi matukar tashi, duniya ta yi mata baki-Kirin, Kirjinta ya yi Kunci, ta shiga tunani da magana ita kadai, ta sa aka kawo mata tulun giya ta fara kwankwada babu KakKautawa tana tunanin yadda za ta Bullo wa lamarin. Can dai ta yanke shawarar fuskantar wannan



Www.bankinhausanovels.com.ng jarumi ita da kan ta, kuma ta amince a cikin zuciyarta cewa duk ta yadda za ta yi sai ta ga bayansa. Saboda haka sai ta fito da kanta, ba cikin shirin fada ba, ‘yan mata biye da ita. Ta sa wata daga cikin ‘yan matan ta yi masa shela cewa Sarauniya Zankadaziyya mai girma tana son yin magana da shi, ba fada ba, saboda haka ya mayar da takobinsa cikin kube.

‘Ta matso shi ma Idrisu ya matso, amma duk da haka dai bai saki jikinsa ba. Ta ce, “Me ya kawo ka Kasarmu?”

Idrisu ya amsa mata cewa, “Hanya ce ta biyo da ni, asali na zo wucewa ne kawai.”

Sarauniya ta katse shi, “To dakata. Ka sani cewa ka yi mana Barna mai dumbin yawa a Kokarin da muka yi na kare garinmu daga bakin da ba mu sani ba. Kuma ko kadan kada ka dauka zan yafe maka ne kai tsaye haka kawai, kuma ko kadan kada ka dauka cewa ka gagara ne,

A dalilin dan Kokarin jaruntar da ka nuna ne nake ganin ya kamata ka sami arzikin yin magana da ni. Akwai jarrabawa da na shirya zan ba ka, in har ka yi nasara, to sai ka ambaci buKatarka a biya, in kuma ba ka yi nasara ba, to dole ka amince in yi yadda na ga dama da kai. Sakamakon barnar da ka yi mana.

Shin ka amince?”

Www.bankinhausanovels.com.ng Jarumi Idrisu ya ce ya amince. Ya Kara da cewa, “Ai jarumi ba ya qin takala.”

Sai Sarauniya ta ce, “tsere ne kawai a kan doki za mu yi, in dokin ka ya tsere nawa, to shi ke nan ka ci jarrabawa, in kuma dokina ya tsere wa naka, to ka fadi jarrabawa, sai ka mika wuya sai yadda na yi da kai.”

Abin da dan Hamidu bai sani ba shi ne babu komai a cikin wannan tsere na dawaki da Sarauniya ta bukaci a yi face yaudara, musamman in an lura da irin gagarumin sharrin da ke wurin da akan yi tseren.

Ramuka ne aka harhaka masu zurfi sannan aka sa wasu irin masu wadanda ke da tsananin tsini da dafia jikinsu. Mutum yana fadawa, to sai dai wani ba shi ba.

Wanda bai sani ba babu yadda za a yi ya taba ganewa domin an bi duk ramukan an lullube da wata irin shimfida da kuma turbaya yadda sai ka rantse babu komaia wurin.

Shi wannan doki na Sarauniya a gabansa duk aka harhaka wadannan ramuka, kuma ya sami kwarewa matuka yadda duk ya san wuraren da suke. Babu yadda zaayi ya auka.

‘Ta wannan hanya Sarauniya ta halaka mutane masu dumbin yawa. Nan da nan aka nufi fili, Sarauniya tana kan

Www.bankinhausanovels.com.ng ingarman dokinta, yana tafe yana harbin iska.

“Yan matan Sarauniya kam sai murna, don sun tabbatar da cewa ta faru ta Kare a kan wannan jarumi wanda ya wahalar tare da kashe musu mutane. Wadanda ba sa murna daga cikinsu kawai sai dai daurarrun ‘yan matan nan da ya shigo tare da su cikin gari, su babu abin da suke yi sai jimami tare da tausaya wa rayuwar Idrisu don sun tabbatar da cewa tasa ta zo Karshe, kuma sun yi mantuwar sanar da shi wannan tsere, don an daden gaske ba a yi irinsa ba.

Babu damar su tsegunta masa, kuma babu damar su nuna bakin cikinsu, don sun san sakamakon haka, saboda haka sai suka yanke tsammani da shi.

Jagora dokin Idrisu kuwa sai haniniya ya ke yi yana wata irin rawa da tafiya yana dandangala Kafafu cikin Kasaita. Dole in ka gani abin ya burge ka.

Aka saki dawaki, suka ruga a guje, shi Idrisu bai san

abin da ke Kasa ba, amma abin mamaki in ana cikin gudu sai ya ga Jagora ya daka tsalle, ashe ramukan nan ne ya ke tsallakewa. Maimakon fadawa cikin rami sai ya kasance yanzu akwai tazarar gaske tsakaninsa da dokin Sarauniya.

Kai rannan har ‘yan matan Sarauniya sai da suka

tafa wa Idrisu.

Bayan jarumin ya dawo har ya dan huta sai ga

Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya Zinkadaziyya ta Karaso. Tana zuwa sai ta yi masa jinjina, amma fa na ciki na ciki ne kawai, ta dube shi ta sake duban Jagora ta ce, “Lallai na yarda kai jarumi ne kuma dokinka jarumi ne, to sai mu koma fada ka fadi bukatarka.”

A fadar Sarauniya duk sai aka zaunaa kan kujeru na alfarma. Cikin dabara jarumi Idrisu ya ki zama a kujerar da aka fara nuna masa, maimakon haka_ sai ya je ta nesa da ita ya zauna. Sarauniya ta ba da umurnin a kawo abinci da kayan shaye-shaye, to a cikin wannan abin sha akwai wani mugun dafi, wato dafin nan wanda kan sa mutum ya kasa tabuka komai sai kawai a kama shi yana kallo. To da ma Idrisu yana sane da wannan, sai dai kuma ko kadan hakan bai ba shi tsoro ba, hasali ma sai ya bude cikin sa ya nadi abincin nan ya debi abin sha ya sha har ma da Karawa.

A lokacin ne ma ya tuna cewaa cikin kayansa akwai sauran maganin dafi wanda aka ba shi ko da zai taimaka wa wasu, wato wanda ya samo a tsibirin da ya kashe dodo. Shi da dokinsa tuni da ma wancan maganin dafin ya rigaya ya huda su.

Amma fa duk abin da ake yi shi wancan jarumin dan Sarki da ke Bangaren Idrisu, wato Abdurrahman, da kuma jarumin nan da ya gudu dazu zuwa wurin Idrisu din don samun mafaka ko kadan ba su yarda

Www.bankinhausanovels.com.ng sun ci ba, don sun tuna cewa daga wurin cin abinci ne suka manta inda suke a wancan karon lokacin da

suka shigo garin. Dan Sarki ma har sai da ya tsawatar

wa Idrisu cikin dabara a kan kada yaci ko shan komai wurin amma sai ya ga ko sauraron sa jarumin bai yi ba.

Bayan an kammala cin abinci tsaf, sai Sarauniya ta yi wata irin dariya har da kyakyatawa, sannan saitace, “Dan kyakkyawan jarumi, yanzu fa da kai da kazar da ke cikin akurki tafiyarku daya.”

Sai Idrisu ya tambaye ta abin da take nufi, sai ta ce, “Ai da ace ba ka yarda ka sha wani abu daga gare ni ba da sai in ce har yanzu kana tare da jarunta da Kwarewarka, amma yanzu ai labari ya sha bamban. Yanzu jijiyoyin jikinka ma sun fi ka Karfi. Da ma an ce ta yaro kyau take yi bata Karko.”

Idrisu ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah Sarki. Sarauniya ke nan, to wai kina ce duk mutane daya ne? – ‘To, wannan yaudarar ma ba ta yi nasara ba, sai ki sake wata.” :

Yana gama magana sai ya yi zumbur ya mike tsaye ya daga hannayensa sama da Karfi ya girgiza jikinsa.

Wato guba bata yi masa komai ba ke nan.

Mamaki ya rufe Sarauniya, don ita wannan guba ko giwa ce ko zaki suka lashe ta za su lalace su rasa katabus ballantana dan Adam. Nan da nan

Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya Zinkadaziyya ta mike ta nufi wurin masu kawo abinci ta sami ‘yan matan ta ce, “Wato ni za ku munafunta ko? Na ce ku sa dafi a cikin abin shan jarumin nan amma…”

Suka yi sauri suka ce, “Ranki ya dade mun rantse da macizai mun zuba masa.”

Ba ta ce komai ba, ta umurci wata daban akan cewa ta je ta kwaso kayan abin shan da ke gaban jarumi Idrisu, wanda ya sha ya rage. Da kanta ta tsiyaya ta bai wa ‘yan matan kuma ta umurce su a kan cewa su sha matukar dai da gaske suke yi cewa sun zuba. In kuma sun Ki sha, to a kai su a jefa a ramin macizai.

Dole suka saddakar suka sha, nan da nan jikinsu ya langabe kamar ba mutane ba, Sarauniya ta tabbatar da cewa lallai kam sun zuba kuma shi ne dai Idrisu dan Hamidu ya sha. Mamaki ya sake kama ta.

‘Ta debo makarin gubar ta ba ‘yan matan suka sha, bayan wani dan KanKanin lokaci sai ga shi sun wartsake tangaram.

Sarauniya ta dawo wurin su Idrisu, ta yi umurnin cewa tana bukatar kowa ya fita ya ba ta wuri za ta yi tattaunawar sirri da wannan jarumi.

Bayan kowa ya fita sai ta tashi tana wata irin tafiya ta takama tana magana, “Babu shakka ka isa jarumi, domin kuwa na yi karo da jarumai masu yawan gaske,
Www.bankinhausanovels.com.ng
na kashe dakarun da ban san adadi ba, amma babu wanda ya taba nasara a game da dukkan tuggun dana shirya masa sai kai kadai. Abin mamaki sai na ji na sallama maka, kuma watakila ka yi mamaki in kajina ce a yanzu gaskiya son ka ya shiga cikin zuciyata yana neman mamaye ta.

Ko kadan a da ban yarda da wani abu da ake kira soyayya ba, shi ya sa ba na yin ta. Amma yanzu na fahimci kuskurena, ashe dai soyayya gaskiya ce.

Wannan ya sa ba zan bar ka ka tafi ba, a taKaice dai

bukata nake yi ka zama mijina, kuma gobe a tabbatar

maka da sarautar gari, kuma na yi maka alKawarin

zan zama mace mai biyayya a gareka. Ka yi hakuri abubuwan da suka wakana abaya.”

Idrisu dai bai ce komai ba, ya yi kasake yana sauraren ta. Ta ci gaba da bayani, “Yanzu halin da ake ciki gaskiya babu abin da nake buKata, saboda irin shauKinka da nake yi, face, ko kuma a taKaice ina sanar da kai cewa na sallama maka kaina, ka aikata masha’‘a da ni, yanzu ba sai an jima ba.”

Da Idrisu ya ji abin da Sarauniya take buKata sai ya ce, “Ina neman tsari daga Allah Mai girma da

daukaka, Allah Ya kiyaye ni daga wannan mummunar bukata taki. Ki sani cewa ni ba irin mutanen nan ne da kika sani ba masu dulmuya kansu

Www.bankinhausanovels.com.ng a cikin halaka. Ni addinina ya hana ni rabar matar da ba tawa ba.”

Jin wannan magana sai Sarauniya ta ji kamar an sake zuga ta ne a kan cewa lallai sai bukatarta ta biya, ta tuna yadda sarakuna da jarumai kan niko gari su bar garuruwansu don su zo su ga fuskarta da kyanta da ake labari, amma a karshe duk ta mayar da su bayi, sun yi mata kuka, ta sa su rarrafe da sauran abubuwan da a cikin hankalinsu ba za su yarda su aikata ba.

Ta ce masa, “Dan

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment