Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurayi ina ji maka tsoron kada ka zo daga baya kana rokona a kan kana son in sake nuna maka fuskata kawai. Ka ga dai tun da ka zo in banda Kwayar idanuna ba ka ga komai na daga jikina ba, amma na ce zan sallama maka kaina, saboda haka kada ka yi saurin ki ko kuma kore alherin da ya tunkaro ka. Ya kai jarumi ka sani cewa ba wai yabon kaina nake yi ba, amma ina da kyau da halittar da ba maza kadai ya ke girgizawa ba har mata.”

Jarumi Idrisu ya ce, “Watakila su wadancan masu begen naki ba su taba ganin kyakkyawa ba ne sai ke.

Kuma ina tabbatar miki da cewa duk namijin da har ya sake kyanki ya debe shi, musamman ma

jarumi, to bai cika da ba, kuma ni zan fada miki abin da yasa nace kyanki bai kai ba…” Sai ta katse masa magana ta harare shi tace, “Irinku

Www.bankinhausanovels.com.ng ne kuke ce wa mace dokin lado… amma zuwa an jima za mu gani idan kai daban kake da sauran mazaje.” Ta bar Idrisu a nan ta shige cikin wani daki, fitowar da za ta yi sai ga ta daga ita sai ita, ta warware gashin kanta ta rufe rabin jikinta da shi. Lallai ne duk namijin da ya gan ta, in dai ba wata kariya daga Allah ba, to zai zamanto kamar wadancan mazaje na baya da aka ba da labari. Don irin cikar halittar Sarauniya kada ma wani ya fara Kokarin ba da labari, don kuwa dole sai ya rage ta. Ta matso kusa da Idrisu, kansa na duke yana kallon Kasa. Sarauniya ta ce, “Kai Duba nan.” Idris ya ce, “Ai na gan ki.” Sarauniya ta sake tausasa murya ta ce, “To sake dubawa mana.” A hankali bai san lokacin da kansa ke kokarin sake dagowa don sake gani ba, amma sai tsoron Allah ya shige shi kuma ya tuna da yarinya Nur, kawai sai ya sa hannunsa a wuyansa ya shafa adikonta, ya daga kansa ya zare idanunsa ya kalli Sarauniya da ke tsaye Kerere a gabansa ya ce, “Kin ga adikon nan da ke daure a wuyana, to a wurina ya fi ki daraja, ke da mulkinki da duk abin da kike takama da shi wadanda duk na banza ne tun da dai ke fasika ce. Sannan kuma

Www.bankinhausanovels.com.ng ga shi kina da mugun halina kashe ‘ya’yan jama’a. Kin hana wa ‘‘ya’yan mutane ‘yanci, kuma ga shi kina bauta wa abubuwan banza; macizai, kina ba su ‘ya’yan jama’‘a suna cinyewa. To ina yi miki albishir da cewa wata rana ke za su cinye, kowa ya huta.

‘To yanzu dai duk wani kawaici da kawar da kai da nake yi miki ya kare. Abin da nake bukata dake shi ne, ki saki duk jama’ar da kike tsare da su kina ba macizanki. Ki Kyale kowa ya koma garinsu.

Ke kuma ina ba ki shawara ki daina bautar macizai, ki bauta wa Allah Mahaliccin macizan, ki yi aure, kuma ki Kyale ‘yan matanki su ma su zaBi mazaje su yi aure. Wadanda ba su da buKatar zama tare da ke kowacce ki bar ta ta koma garinsu wurin iyayenta.”

Da Sarauniya ta ji irin wannan zance da Idrisu ya ke yi mata gatse-gatse haka sai ranta ya Baci, ta yi fushi mai tsanani har sai da ya bayyana a fuskarta, ta ji kamar ta sha jininsa. Ta ce, “Lallai kai kana da mummunan jawabi, maganarka ta fi dafin bakin kumurci daci, zancenka yana iya kashe mutum kafin Karewar kwanakinsa. A gaskiya da a ce na san zan same ka yadda kake, to kuwa da ban bari ka shigo garina ba, har ka guma mini bakin cikin da tun tsawon rayuwata ban taba samun rabinsa ba ma.”

Sarauniya ta Kara da cewa Idrisu dan Hamidu, Www.bankinhausanovels.com.ng Wai ga shi ma har kana ce mini in bar bautar macizai, to in bauta wa me? Kuma don tsabar wulakanci in nuna maka jikina amma ka ce adikon da

ke daure a wuyanka ya fi ni daraja a wurinka. Lallai

ka zalunce ni, kuma ina roKon macizanmu masu

girma su tsine maka albarka!

Yanzu dai abin da nake so da kai shi ne na sallame ka, yanzun nan ka bar mini garina, in kuwa ka Ki, to zan karya Karfinka in yanka ka da kaina, in raba jikinka biyu sannan in bai wa macizaina masu girma, su cinye namanka.”

Idrisu ya ce, “A’a, saurara, ya ke wannan Sarauniya mai taurin kai da rashin fahimta, ki sani cewa zancen banza kike yi. Ai in kin ga na bar garin nan, to babu shakka na ‘yanto ‘ya’yan jama’a ne maza da mata da ke cikin tarkon makircinki.

Ina kuma sanar da ke cewa a game da wannan ba ki da wani sauran zabi, ko dai ki yarda ne ki tsira da

mutuncinki, ko kuma ki Ki yarda ki rasa sarautarki.”

Yanzu kam zuciyar Sarauniya ta gama kumbura don tsananin fusata da maganar Idrisu. Mamaki da Kunci da bakin ciki suka lulluBe ta, kamar walKiya sai ga shi ta zaro tsafaffen takobinta, kuma kafin Kifta ido ta buga wani irin tsalle kamar wadda ta fado daga sama ta diro wa Idrisu da wani irin suka, amma

Www.bankinhausanovels.com.ng saboda tsananin kwarewa sai ya goce ya fado daga kujerar da ya ke zaune.

Takobinta ya soki kujerar, kuma duk da kasancewar kujerar ta dunkulallen bakin karfe amma sai da takobin ya huda ta, kuma saboda tsananin dafin takobin da sihirin da ke jikinsa sai ga kujerar tana zagwanyewa, Karfe na narkewa kamar kankara.

Nan da nan fada ya kaure aka yi kaca-kaca da kayan

da ke cikin fadar don tsananin gumurzu, babu shakka Idrisu ya san cewa Sarauniya jaruma ce.
FADA ya yi fada tsakanin jarumi Idrisu da Sarauniya Zinkadaziyya, ita tana Kokarin samun sa a makasa ta aike da shi lahira shi kuma yana KoKarin takura ta, don ya kama ta ya daure, kasancewar shi ko kadan ba ya bukatar kashe ta, shi ya sa ma ko takobinsa bai fitar ba. Tun daga cikin fada har sai da suka yiwo waje suna ta gwabzawa.

Babu shakka wannan Sarauniya ta fi Karfin a kama da hannu, ko da a wurin irinsu Idrisu din, don kuwa ba Karamar jaruma ba ce.

Suna dai ta bugawa. Kwatsam sai ga su a wata ‘yar unguwa da ke jikin fada, a can gefe sai ya hango wasu ‘yan matan Sarauniya sun bude wani tafkeken rami,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

CHAPTER 18 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng

MUN TSAYA

saboda tsananin kwarewa sai ya goce ya fado daga kujerar da ya ke zaune.

Takobinta ya soki kujerar, kuma duk da kasancewar kujerar ta dunkulallen bakin karfe amma sai da takobin ya huda ta, kuma saboda tsananin dafin takobin da sihirin da ke jikinsa sai ga kujerar tana zagwanyewa, Karfe na narkewa kamar kankara.

Nan da nan fada ya kaure aka yi kaca-kaca da kayan

da ke cikin fadar don tsananin gumurzu, babu shakka Idrisu ya san cewa Sarauniya jaruma ce.
FADA ya yi fada tsakanin jarumi Idrisu da Sarauniya Zinkadaziyya, ita tana Kokarin samun sa a makasa ta aike da shi lahira shi kuma yana KoKarin takura ta, don ya kama ta ya daure, kasancewar shi ko kadan ba ya bukatar kashe ta, shi ya sa ma ko takobinsa bai fitar ba. Tun daga cikin fada har sai da suka yiwo waje suna ta gwabzawa.

Babu shakka wannan Sarauniya ta fi Karfin a kama da hannu, ko da a wurin irinsu Idrisu din, don kuwa ba Karamar jaruma ba ce.



Suna dai ta bugawa. Kwatsam sai ga su a wata ‘yar unguwa da ke jikin fada, a can gefe sai ya hango wasu ‘yan matan Sarauniya sun bude wani tafkeken rami,

ZAMU TASHI

sai kawai ya ga kamar Riftawar ido an zo da wani jibgegen Kato an angiza shi cikin ramin, babu yadda Idrisu zai itya hana wannan don irin yadda Sarauniya ta ba da Kaimi wurin Kokarin halaka shi ko ta halin Kaka.

Aka zo da wani Katon shi ma aka cilla cikin ramin abin kamar a mafarki.

Ba sai an yi wani dogon bayani ba Idrisu ya fahimci cewa wannan ramin shi ne wanda macizan da Sarauniya da mutanenta ke bauta wa suke ciki, kuma ramin da ake tura ‘ya’yan mutane, musamman mazaje da sauran wadanda suka yi wani babban laifi, don macizan su yi kalaci da su.

“Yan matan da ke kula da ramin macizai ba su ankara ba sai suka ga Sarauniyarsu a cikin yanayin da ba su taba ganin ta ba tana ta fada da jarumin da labarinsa ya karade gari, ai sai suka bar wurin suka koma gefe suna kallon abin da zai ture wa buzu nadi.


Yanzu dai Sarauniya ta matsa kamar wadda ta haukace, da Idrisu ya ga haka kuma ya tabbatar da cewa ba za ta kamu masa da hannu ba sai ya zare takobinsa, karar zarewar kawai kamar faduwar aradu. Ita kanta Sarauniya sai da ta tsorata, amma saboda taurin kai da jarunta sai ta ci gaba da fada.

Ta daga takobinta da Karfi ta kawo wa Idrisu wata

Www.bankinhausanovels.com.ng irin sara, shi kuma sai ya sa takobinsa ya kare, haduwar takubban nan fa sai kawai takobin Sarauniya ya lankwashe ta yadda ba shi da sauran mamora.

Da Idrisu ya ga haka, kuma ya ga alamar cewa jikinta ya yi sanyi sai ya ce mata, “Haba, ya ke wannan Sarauniya, ki ba da kai mana, ki mika wuya, ni da ma ba ni da niyyar kashe ki, ina so ne ki yarda ki zama Sarauniyar kirki, ki kyautata wa talakawanki, kuma ki saki mutanen da kika tsare kowa ya kama gabansa. Ki je ki ci gaba da sarautarki don ni ba sarauta nake so ba, ina ji miki tsoro kada ki zama kamar Sarkin aljanu Sham’una…”



Ai kafin ya rufe baki sai ta zaro wuka a kuibinta ta auno Kahon zuciyarsa ta sako, Idrisu ya sa takobi ya buge wukar ta fadi can Kasa.

Da Sarauniya ta ga cewa ta kowace fuska an yi galaba a kanta, sai ta ce a cikin ranta, “Ai kuwa dajin kunya ga Sarauniya gwamma rasa rai.” ai kuwa sai ta ruga ta nufi ramin macizan can da ba a rigaya an sakaya ba saboda kallon fadan da masu aikata hakan suka tsaya yi, ta yi kundumbala ta afka ciki, ai cikin ‘yan dakikoki sai ya kasance babu sauran ko digon jininta, allolinta sun shanye.

Bayan mutuwar Sarauniya sai Idrisu ya juya wurin

Www.bankinhausanovels.com.ng jama’arta ya ce musu, “To ku mene ne abin yi?”

Sai suka ba shi amsa, “Meene ne abin yi kuwa ranka ya dade, ai yanzu kai ne Sarki, umurninka kawai muke jira.”
Sai ya ce, “To da farkon farawa dai abin da nake so shi ne a je a kwanto mini dukkan mutanen da ake daure da su a gidajen sarka da ma duk wani wuri da ake azabtarwa. Ban ce a rago ko daya ba.”

Mutane suka shiga fitowa salalaf babu laka a jikinsu amma kuma fuskokinsu cike da murna bayan sun fahimci abin da ya faru. Suka Karaso wurin jarumi Idrisu suna yi masa addu’o’in alheri da kyakkyawan fatan samun biyan buKata a game da duk abin da ya sa,a gaba. Nan da nan Idrisu ya sa aka tara ruwa a wasu manya daro-daro guda biyar, daga

_ nan sai ya dauko maganin dafin nan nasa da ya samo a tsibirin dodo ya zuzzuba a cikin kowane daro, aka gaggauraya sannan jama’‘a suka yi ta kurbar ruwan.

Sihirin guban da ke jikinsu ya karye ke nan. Mutane kowa ya ji jikinsa ya warware garau kamar yadda a da ya shigo cikin garin. A nan fa suka Kara sakankancewa da lamarin dan Hamidu.



Umurni na gaba da Idrisu ya bayar ga zaratan ‘yan matan nan masu tsaron ramin maciji shi ne a tattaro manya-manyan guma-gumai don cika ramin, da

Www.bankinhausanovels.com.ng kuma Kone abin da ke cikin sa kowa ya huta.

Sun kammala cikawar ke nan suna zuba mai sai suka ga itatuwan suna yunkurowa sama, ai nan da nan sai suka ruga suka sanar da Idrisu abin da ke faruwa, ya Karaso ya ce kowa ya ja baya, shi kuma ya yi tsaye rike da zararren takobia bakin rami.

Can kuwa cike da fushi sai macizan suka ingizo mafi yawancin guma-guman da aka zuba, suka dago kawunansu kamar kawunan manyan jakuna, idanunsu jajawur, harshensu kamar cinyar Kato, jikinsu kuma sai wani irin bawo-bawo ya ke yi kamar bayan itaciya.

Kowa ya san cewa sun yi niyyar sharri, amma Idrisu bai bari sun kammala fitowa ba ya sa takobinsa mai ban mamaki ya dauke musu kawuna, dole sai da ya sake sara na biyu sannan kan dayan ya kammala rabuwa da gangar jikinsa. Gawarwakin suka koma cikin rami.

Yasa aka mayar da guma-guman nan sannan ya sa aka hura wuta. Sai da aka sami misalin sa’o’i tara wuta na ci don irin kitsen da ke jikinsu. Bayan nan Idrisu ya sa aka cike wurin aka shafe shi kamar ba a taba yin sa ba.

Babu shakka mutane sun yi mamakin irin yadda Idrisu ya kashe wadannan shaidanu, shi ma kansa ya

Www.bankinhausanovels.com.ng tabbatar da cewa ba don taimakon Allah ba, to babu yadda zai yi.

Ana kintata cewa tun kafin kafa garin da misalin shekaru dari takwas macizan suka zo wurin, kuma mutanen garin sun yi imani cewa fushin macizan na iya kama wanda ke nisan duniya ma, ya lalace, amma kuma abin mamaki yau ga wani mutum, dan Adam ya zo ya halaka su, har maya Kone su.
Jarumi Idrisu ya tara dukkan jama’a ya yi musu jawabi mai dadi, kuma ya jawo hankalinsu a game da cewa su rabu da bautar wani abu in ba Allah ba. Bayan ya kammala sai’yan matan nan suka ce, “Mun amince da duk abin da ka zo mana da shi, saboda haka mun amince da addinin Islama din da ka ke bayani.”



Idrisu ya yi wa Allah godiya mai tarin yawa tare da farin cikin cewa a dalilinsa ne mutane dubbai kan dubbai suka musulunta. Ya nuna musu cewa addinin Musulunci addini ne da ba ya son zalunci, kuma addini ne da ba ya yiwuwa sai da ilmi.

Ya ci gaba da bayani cewa, “Ya ku wadannan kyawawan ‘yan mata, akwai babban abin lura ko kuma shawara da nake so in ba ku.

Lallai ne ya zama dole ku yi aure, don ita ‘ya mace darajarta ba ta cika sai da miji. Saboda haka in kun

Www.bankinhausanovels.com.ng amince ga mazaje nan ku zaBi junanku mu kuma mu yi ta daura muku aure bisa sharuddan da addininmu ya tanada. Wata babbar sa’a da aka yi ita ce mafi yawancin mazajen nan naku da ma tun _ tuni Musulmi ne masu ilmi wadanda za su taimaka wurin sa ku a kan hanya.”

Aka fa shiga hidimar zaben juna da daure-dauren aure. Ana haka sai ga gungun wasu kyawawan mata sun zo suka ce duniyar nan babu wanda suke so ya aure su Sai jarumi Idrisu.

Ya yi murmushi sannan ya ce, “Na gode saboda Kauna. A duniyar nan duk wanda ya ce kai ya ke so ya gama maka komai, sai dai kuma ina mai ba ku hakuri, don akwai wani babban aiki kwatankwacin wanda na yi a garin nan na gabana, kuma wancan aikin ya ninninka wannan hadari, alhali kuwa ba na son ya kasance akwai hakKin wata mace a kaina in tafi in barta a cikin halin jiran tsammani wanda babu tabbas a ciki.

Saboda haka ina mai Kara godiya tare da ba ku hakuri a kan cewa ku yi hakuri ku zabi wasu mazajen.”

Babu ta inda ‘yan matan nan ba su Bullo masa baa kan cewa sun amince da komai, amma yatirje ya Ki.

Cikin lokaci aka samar da babban masallaci da

Www.bankinhausanovels.com.ng makaranta a wannan gari, kuma matan garin suka fara fahimtar addini fiye da duk yadda ake zato. Jarumi Idrisu dan Hamidu ya ba su shawarar zaben Sarkin da zai gabatar musu da jagoranci, sannan kuma a nada Waziri, alKalai da sauran masu mulki don tabbatar da ingantacciyar tafiyar harkokinsu na yau da kullum. Jama’ar gari da suka ji haka sai suka ce wa Idrisu, “Yallabai ai kai ne Sarki.”

Jarumi Idrisu ya ce, “Ku kuwa kuna da saurin mantuwa, ina ta maimaita muku cewa ni ba zama na zo yi ba, akwai babban aiki a gabana, saboda haka ina ba ku hakuri.”

Sai suka dage a kan ce masa, “To mun amince maka, ka zabar mana wanda kake ganin ya dace.”

Idrisu ya ce, “A’a, ba zaa yi haka ba. Ko ba komai dai kun dade tare da junanku, kuma zuwa yanzu ya kamata a ce kuna iya fahimtar wadanda kuke kyautata zaton za su yi muku adalci, don kun fi ni sanin kanku. Sannan kuma za ku fi samun natsuwa da ‘yanci in kuka ji cewa da kanku ne kuka zaba, ba wai dora muku aka yi ba.”

A nan fa mutane suka shiga shawarwari tsakanin su, kuma ba tare da wata doguwar takaddama ba suka zabi Abdurrahman a matsayin sabon Sarki. Wato

Www.bankinhausanovels.com.ng jarumin dan Sarkin nan da ya fara goya wa Idrisu baya a zamanin Sarauniya Zinkadaziyya.

Abdurrahman ya tashi ya yi wa jama’a godiya kan irin yadda suka amince da shi har suka zaBe shi a matsayin shugaba, ya ci gaba da jawabi cewa, “Sai dai kuma ina ba ku hakurin cewa ku zabi wani, don kuwa tun da farko na Kudurta wa zuciyata cewa zan bi wannan jarumin bawan Allah zuwa inda duk ya nufa don in tallafa masa tare da Karfafa masa a wurin da bukatar hakan ta taso.”

Jin haka sai Idrisu ya mike ya mayar da martani, ya kalli Abdurrahman ya ce, “Kada ka yi wannan magana. Tafiyata tana da hadarin gaske, wannan tafiya sai ni kadai, kuma ma da a ce ina buKatar abokan tafiya ne, to babu shakka da ka gan ni tare da dubban mutane.

Saboda haka ya kai Abdurrahman, na roKe ka da ka yi hakuri, ka daure tun da dai mutanen nan ne suka zabe ka don zama shugaba, to sai ka yi Kokari ka yi, sannan wani abin sha’awa kuma da ma ga shi kai dan Sarki ne wanda daidai gwargwado na ga alamar ka san harkar mulki.”

A dalilin irin girmama Idrisu da jin nauyinsa da ya ke yi ya sa Abdurrahman ya amince da amsar Sarautar garin, amma kuma duk da haka sai da ya

Www.bankinhausanovels.com.ng tunatar da Idrisu wani abu, cewa, “Amma fa ka san cewa asalin fitowata daga gida a kan neman budurwata ce wadda ta bata, kuma kai can inda take ka nufa.”

Sai Idrisu ya ce masa, “Na yi maka alKawari, idan na je na yaki Sarkin aljanu Sham’una kuma Allah Ya ba ni nasara a kansa, to in akwai budurwarka daga cikin ‘yan matan da ke hannunsa, to babu ko shakka in Allah Ya yarda zan dawo maka da ita.

Sai dai kuma kafin nan, ba ya yiwuwa a ce kana Sarkin wannan Kasaitacciyar kasa a ce ba ka da mata, saboda haka lallai sai ka zabi guda biyu mu daura muku aure.”

Ba tare da wani bata lokaci ba aka daura auren Sarki da ‘yan mata biyu, aka nada Waziri da dagatai da hakimai da wadanda za su rike sauran madafan iko, sannan kuma aka zabi matasa majiya Karfi aka kafa rundunar dakaru. Komai dai irin na mulki ya tsayu tsaf akan kafafuwansa.

Sarki Abdurrahman ya sanar da jama’a cewa an sauya wa wannan birni suna daga birnin Salsala zuwa birnin Idrisu, kuma mutane sun yi matukar murna game da haka. Sarki ya rubuta wasiku yana sanar da manyan sarakuna makwabtansa na kusa da na nesa cewa yanzu fa salama da aminci sun kafu a wannan

Www.bankinhausanovels.com.ng daula tasu, saboda haka yana gayyatar kowa da kowa da kuma’yan kasuwa don huldar kasuwanci.

Lallai kuwa an amsa gayyata.

Komai ya zauna daram, masu mulki sun kama shugabanci, ‘yan kasuwa sun tsunduma cikin harkar nema, malamai da dalibai kowa ya dage, to daga nan fa sai Idrisu dan Hamidu ya fara tunanin ci gaba da tafiyarsa.

Washegarin ranar da Idrisu zai tafi shi da Sarki Abdurrahman suka zauna cikin dare suna tattaunawa. Ya ke ce wa Sarki, “In Allah Ya so dai ka san gobe ne zan kama hanya, saboda haka nake so in sake jaddada maka wata tunatarwa.

Ya kai Sarki Abdurrahman, ina so ka yi tunani ka Kara yi wa Allah Mai girma godiya, ka riKe amanar da Ya ba ka, ka tuna cewa kana cikin kurkuku Ya fito da kai, Ya shugabantar da kai, wanda kuma ba don : taimakonSa ba watakila da tuni ka zama abincin macizai, saboda haka ka yi Kokarin yin mulkinka da adalci. Ka riKa Kokarin bincika hakimai, dagatai da alkalanka, da duk masu rike da kowane irin bangare na mulki don tabbatar da cewa suna aikata gaskiya. Kada ka kuskura ka bari Kasarka ta zama dandalin sabon Allah da kuma aikata Barna.”

Sarki Abdurrahman ya yi shiru cike da natsuwa

Www.bankinhausanovels.com.ng yana sauraron Idrisu har sai da ya kammala bayaninsa sannan ya ce, “Na gode wa Allah da Ya Kaddara haduwata da kai. Ko da yake tuntuni na san wani abu a rayuwa, wato in mutum yana aikata wani abu mara kyau, to wata rana dole sai zuciyarsa ta hararo tare da tabbatar masa da cewa abinda fa yake aikatawa babu kyau, wanda kuma daga nan ya rage nasa, wato in ya so ya ci gaba da aikatawa ko kuma ya tuba ya daina. Saboda haka ya kai shugabana ina son yin wani alwashi a gabanka, ko kuma in ce in yi maka alKawari, cewa a cikin wannan mulki da nake yi, duk ranar da na gane cewa ba na daukar shawarar kirki, ko kuma na fahimci cewa ana jin tsoron a fada mini gaskiya, ko kuma na ji cewa ba zan iya yin adalci ba, to na rantse maka da Allah zan tara al’umma in sanar da su cewa ni da kai mun yi alkawari a kan cewa inna kai tsawon lokaci kaza a kan mulki zan sauka in koma garinmu, su kuma mutane su zabi sabon Sarki, kuma wallahi zan sauka din don su zabi wani.”

Da Idrisu ya ji jawabin Abdurrahman sai murna ta lullube shi don ya tabbatar da cewa zai yi adalci.
Wayewar gari tun da Asuba mutane suka fara

taruwa, kafin ka ce wani lokaci an cika Kofar fada makil ana jiran fitowar Sarki da jarumi don a yi rakiya. Kafin dagawar hantsi an kammala shiryawa

Www.bankinhausanovels.com.ng tsaf, Idrisu ya fito ya hau Jagora, shi kuma Sarki ya hau nasa dokin aka bi su a baya aka dunguma.

Bayan tafiyar kwana uku sai Idrisu ya ga alamar ba su da niyyar juyawa, kuma ya fahimci nufinsu na yi masa rakiyar kwana bakwai ne sai ya ce musu ya kamata a tsaya haka nan don yin bankwana.

Aka dauki lokaci mai tsawon gaske ana addu’o’i kafin daga baya aka rabu, kowa yana hawaye saboda irin kauna da kuma shakuwar da suka rigaya suka

shiga tsakani.

KWANA goma kawai tsakanin rabuwar jarumi Idrisu da ‘yan rakiyarsa sai ga shi

yana fuskantar wani Kungurmin dajin. A cikin sa kuma sai da ya yi wata biyu da kwana goma sha tara yana tafiya ba dare ba rana, ba ya tsayawa saidai in don hutawa ko kuma wata lalura ta rayuwa kadai.

Duk tafiyar nan da ya ke yi bai taba haduwa da dan Adam ba ko daya ba sai namun daji; su ma miyagu.

Ba Kankanin bugun ruwan sama suka sha ba, shi da Jagora, don irin ruwan da ke sauka a dajin tun da Idrisu ya ke ko a mafarki bai taba zaton cewa a kan yi irinsa ba.

A haka suka iso wani wuri wanda babu komai a cikin sa sai kankara tana zuba daga sama kamar ana

yayyafi. Tsananin sanyi ya yi kamar ya halaka shi saboda bai taba shiga cikin irin wannan yanayi ba. Dole a tausaya masa, don ba shakka ya sha wuya.
Yana cikin irin wannan mawuyacin hali sai ya ga
Www.bankinhausanovels.com.ng
Jagora ya karkata ya nufi wani babban kogon dutse wanda a da saboda gigicewa bai lura da shi ba, ai sai wata murna ta rufe shi don tunanin cewa yanzu zai dan sami dumi har Karfin jikinsa ya dawo.

Abin mamaki sai Idrisu ya ga ana ta tafiya kwana da kwanaki cikin kogo amma ba a Kure shi

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment