Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ci gaba da

Www.bankinhausanovels.com.ng jawabinta na murnar fitarsu daga kafirci, ta ce, “Sai dai kuma ba shiga cikin Musuluncin ba ne kawai, a’a akwai sauran aiki a gabanmu.

Aikin kuwa shi ne, shi addinin Musulunci ba a yin sa da jahilci, kuma a Ka’idarsa ba a yin sa da cewa wai haka na ga wane yana yi, ko kuma haka ya dace da al’adarmu, ko kuma haka ya fi dacewa ayi, a’a. A Ka‘ida mutum ba shi da wata kirKira tasa sai dai abin da Allah da Ma’‘aikinSa suka koyar a yi ne kawai addini. Wato ba kamar tsohon addininmu ba da a kan Kirkiro sababbin dokoki ko kuma a yi musu gyaran fuska daga lokaci zuwa lokaci.

Abin da nake nufi shi ne dole ne kowannenmu ya tashi ya nemi ilmi don da shi ne ake tauna gardin addinin tare da fahimtar inda aka sa gaba, kuma babu wanda zai taba zuwa ya iya sa ku musanya addininku, don za ku sami hujjojin da suka gagari dukkan wani abin halitta wanda kuma hakan ke nuna cewa ku ne ke kan hanya ta Kwarai, wato hanyar da Allah Mahaliccin komai Yake so.



Amma fa matukKar kuka zauna babu ilmi, to shi ne zaayi ta muku yawo da hankali, ko a cikin addinin Musuluncin ma wancan ya ce muku kaza yau, gobe wancan ya ce ba haka ba.”

Nan take wani dattijon aljani ya mike ya ce, “To

Www.bankinhausanovels.com.ng Dailanu duk mun yarda, yaya za mu yi mu sami shi wannan ilmi?”

Nan take Sarki Ifritu ya mike tsaye ya fuskanci wannan dattijo, sannan ya juya ya fuskanci sauran jama’a ya ce, “Ni, a maimakon jama’‘ata na ba ku gudummawar malamai dubu goma don su fara imantar da ku.”

Aljana Dailanu kamar za ta daka tsalle don murna, ta kalli Sarki Ifritu ta ce, “Na gode, na gode, mun gode.”

Kasancewar wancan dattijon aljani bai riga ya zauna ba sai shi ma ya ce, “A gaskiya mun gode Kwarai ya kai mai alfarma Sarki Ifritu. Sai dai kuma akwai wani abu da tun tuni ya dan dame mu game da ke ya ke shugabarmu Dailanu. A zahirin gaskiya muna ganin ba zai yiwu a ce Sarauniyarmu ba ta da miji ba.”

Idrisu kuwa sai murmushi ya ke yi, Dailanu ta dukar da kai Kasa sannan ta dago ta ci gaba da bayani, “To da ma dalilai biyu ne na ce za su hana ni shugabantarku, na kawo na farko sai lamarin farin cikin Musuluntarku ya dauke mana hankali. Dalili na biyu shi ne, a dai dan karatun da na yi na addinin Islama ina fahimtar cewa Shari’a ta fi son shugabancin da namiji a kan jama’ar kasa fiye da

shugabancin mace. Saboda haka abu daya zan iya yi, kamar yadda kuke so ni kuma yanzun nan zan fitar da miji, in har ya amince ya aure ni, to ni na yarda in zama Sarauniyarsa mai ba shi shawara, shi kuma ya zama Sarkinmu, amma fa in kun amince.”



Jama’‘a suka ce sun amince don sun san ba Za ta cuce su ba.

Dailanu ta waiwaya ta kalli Idrisu ta ce masa, “Ya kai jarumin jarumai, in ba ka manta ba lokacin da ka shigo cikin koriyar ciyawar nan, wato lokacin da ka shigo ‘yankin aljanu har kuka hadu da masoyiyarka Nur, na roke ka cewa ina son in Allah Ya ba mu nasafa akwai abin da nake so daga wurinka.”

idrisu ya ce, “E Kwarai kuwa an yi haka.” Ya dubi yarinya Nur ya ce mata, “Ai ke ma kin tuna ko?”

Nur ta amsa musu cewa, “Tabbas an yi haka. Amma dan dakata Kawata, kin san fa ba irin haka tsakaninmu, kada kuma ki ce shi kike so! Ko a ranar ma ina ce wasa kike yi.”

Dailanu ta yi murmushi sannan ta ci gaba, “Ya kai Idrisu ba wani abu ne nake bukata ba face wannan doki naka ya zama mijina.”

Mamaki ya rufe Idrisu, ya ce, “Dailanu ko ban ji abin da kika ce da kyau ba ne?”

‘Tace, “Kwarai kuwa ka ji da kyau, dokinka Jagora

Www.bankinhausanovels.com.ng ne nake so ya zama mijin aurena, sai dai in ba ya so na.”

Jama’a fa suka yi haja-haja ana neman karin bayani daga wurinta, ta yadda a matsayinta na Sarauniya take bukatar doki ya zama mijinta. Hatta kawayenta su Nur abin ya yi matukar kulle tunaninsu.

Dailanu ta nuna Jagora dokin Idrisu da dan yatsanta ta ce, “Don Allah Jagora koma siffarka ta asali, yau ba ranar boye-boye ba ce, in ma kowa bai sani ba, to ninasani.”

Abin mamaki sai ga Jagora ya rikide ya koma asalin siffarsa. Kuma ma babban abin mamaki sai kowa ya ga ashe kyakkyawan saurayin jarumin nan ne wanda ke ta taimakon su jarumi Idrisu da Sarki Ifritu tun daga birni na goma lokacin da Jagora ya fara rashin lafiya. Ashe dai shi ne Jagora, kuma duk lokacin da ba ya kusa da Idrisun rikidewa ya ke ya koma siffarsa ta asali.

Kuma shi ne wanda ya zo da gudummawar dumbin jama’arsa lokacin da yaki ya yi Kamari sosai, kuma aka yi ta dauki-ba-dadi da shi har zuwa yanzu da aka yi nasara.

Mutane da aljanun da ke wurin kowa ya yi shiru ana ta mamaki, shi kuwa Idrisu bude baki ya yi ya kasa cewa komai yana tunanin yadda hakan ta Www.bankinhausanovels.com.ng kasance.

Jagora ya bude baki ya yi magana, ya ce, “Ya shugabana ina roKon kafin in shaida muku labarina, Dailanu ta fada mini yadda aka yi ta san sirrina yadda har ta gane cewa ni ba doki ba ne.”

Kowa fa ya juya ya kalli Dailanu, ita kuwa sai ta ce masa, “Ka tuna ranar da na kai Kawata suka hadu da jarumi Idrisu a cikin gonakin Ifritu? To in ba ka

manta ba kai kana can waje kana kiwo ni kuma da muka gama gaisawa sai na fito waje don in bar su su dan zanta, to ina cikin wasu ciyayi ina shakar Kanshinsu alhalin kai ba ka gani na, sai ka koma cikin siffarka ka je ka yi Sallar Azahar da La’’asar sannan ka sake komawa doki. Ni kuma tun daga ranar na ji babu namijin da nake so a duniya kamar ka.”

Sai Idrisu ya kalli Jagora cikin murmushi ya ce, “To yallabai, kai muke saurara, ba mu labarin dalilin komawarka doki, domin dai ‘yar budurwar nan ta farke maka laya, ta bayyana maka yadda aka yi ta san ka.”

Jagora ya gyara murya sannan ya ce, “Ya shugabana ka gafarce ni kafin in fara bayani, dole ne in yi wa Allah godiya da Ya sa na sami amsuwa a wurin wannan yarinya kyakkyawa mai hankali da tausayi da kulawa da addini. Wato tun lokacin da muke cikin
Www.bankinhausanovels.com.ng
dajin nan wurin malam mahaifin Nur kana daukar karatu, to ita ce kan zo ta kawo wa malam abinci, kuma takan zo daukar karatu duk ina ganin ta, kuma a duniyar nan na ji babu wadda nake bukatar aure kamarta. Ashe ita ma za ta kamu da so na.”

Jarumi Idrisu ya katse shi, “Malam tun da dai ka sami karbuwa kar ka yi ta jan mu da nisa, mu dai ba mu labarin dalilin kasancewarka doki.”

Jagora ya ce, “To, ya shugabana.

Ni dai asalin sunana shi ne Ramalanu dan Rayalanu. Ni dan Sarkin aljanu ne na can Kasar Yamma, mu Musulmi ne, kuma dalilin zamana doki shi ne don in taimaka wa Idrisu ya sami saukin tafiyarsa zuwa nan ya yaki azzalumi Sham’una.

Dalili kuwa shi ne, Sarkin aljanu Sham’una da ‘yan kanzaginsa sun daden gaske suna zaluntar mu kuma babu yadda za mu yi da su kasancewar sun fi mu Karfi nesa ba kusa ba. Haka kawai yakan shiga cikin Kasarmu ya kakkamo matasanmu ya tura su fagen fama su yi masa yaki, ko kuma a wasu lokuta su shiga shi da jama’arsa su sami ‘yan matanmu, kai wani lokaci ma har da matan aure su aikata mummunan aikin fyade da su. Irin wadannan ayyuka na zalunci da makamantansu sun dade suna aukuwa a cikinmu

ta bangaren Sham’una.

Www.bankinhausanovels.com.ng Maimakon abubuwa su yi sauki sai wani lamari ya faru wanda a wancan lokaci ya zama mummuna a garemu. Duk aljanin da ke bautar tsafin su Sham‘una a wancan lokaci ya san akwai wani aljani na hannun daman tsohuwa Bakayalu wanda ta amince wa Kwarai mai suna Ziri-muzi. To shi Allah Ya kaddara masa shiriya, saboda haka sai ya gudo kasarmu a matsayin hijira.

To duk ba wannan ya fi dugunzuma wa aljana Bakayalu rai game da shi ba face lokacin da tsafinta ya nuna mata a wancan lokaci ta ga surar fuskarsa a jikin bakin littafin nan da sirrin rayuwarsu ke ciki, ta tabbarar cewa ya yi mata leKen asiri. Ta bugo tsafinta sai ta fahimci yana wurinmu, saboda haka ta umurci jikanta Sham’una ba tare da wani Kwakkwaran dalili ba ya je ya halaka shi kawai.

Mahaifina shi ne Sarki, a lokacin da Sham’una ya shigo bai zame ko ina ba sai fadar garinmu, ya yi ta kisan aljanu, wanda hakan ya sa dole mahaifina ya ba da umurnin kariyar kai, shi ma ya fito aka gwabza wanda kuma ba a dauki wani lokaci mai tsawon gaske ba, musamman irin yadda suka duro mana babu shiri, suka sami galaba a kanmu.

Sham’una ya sa hannu ya kashe mini mahaifi, sannan ya kashe duk wanda ke gidanmu. Ni kadai ne

Karami Kwarai, watakila kuma bai lura da ni ba ne,

amma a yanzu ma ina kallon lokacin, sannan sai

lauma wani Kanin mahaifiyata da ba ya gari a lokacin da abin ya faru.

A karshe dai suka ga wanda suka zo nema, a nan wurin Sham‘una ya tsire shi tare da fada masa cewa duk da cewa yana son sa, to amma babu makawa zai kashe shi don haka kakarsa Bakayalu ta ce a aikata. Sham‘una ya yanke kan ya je ya kai mata.

Shi wancan aljani Ziri-muzi wanda Sham‘una ya kashe, a lokacin zaman da ya yi a garinmu ba shi da wani amini da malamin da ya wuce wancan kawu nawa da ba ya gari lokacin da Sham’una ya shigo ya yi kisan gillarsa. Lokacin da ya dawo sai ya dauke ni na girma a wurinsa yana koyar da ni ilmi da dabarun yeki.

A kallum cikin zuciyata in na tuna lokacin da Sham‘una ya kashe mini mahaifi da *yan‘uwa da jama’‘a sai in ji babu abin da nake bukata ko da zan rasa raina ne face daukar fansa.

Lokacin da na girma sai kawuna ya ce mini, “Yaro tun da yanzu ka kawo Karfi to abin da kake jira na daukar fansa ina ganin kamar ya kusa, don kuwa zaman da muka yi da Ziri-muzi ya taba bayyana mini

sirrin kashe wannan mugun maKiyi namu Sham’una, wato abin da ya karanta a bakin littafin, kuma tun daga wancan lokaci na wajabta wa kaina gano inda ke da Korama da rijiya kusa da ita a cikin duniyar mutane. Na kuma dace, ko da yake wurin yana can cikin wani kungurmin daji ne mai wuyar shiga ga mutane, kuma wani abin mamaki shi ne ina kyautata zaton akwai wanda ke da irin wannan buri namu, don kuwa jiya da na kewaya na tarar da wasu dakuna guda biyu an kafa su a wurin, kuma na ga wani dattijo dan Adam, malami, wanda kuma ina kyautata zaton zai yi Kokarin tafiya ne shi kansa, saboda haka nake son ka zama doki mu san yadda za a yi tafiyar nan da kai, kasancewar irin wannan tafiya ba za ta yiwu ba sai a kan dokin aljanu. Ni kuma zan ta yi maka addu’a yadda zai yi wuyar gaske aljanu ma su iya tantance cewa kai ba doki ba ne.”

Jagora ya ci gaba da ba da labarinsa cewa, “Sai nida kawuna muka mayar da wancan daji wurin zamanmu, muna lura da malamin nan mahaifin Nur, wani lokaci in zama doki din in rika zuwa kusa da shi ko zai yi kokarin mallakata amma shi sam sai na lura babu ruwansa da ni, saboda haka sai muka sake lura cewa ai ba ya zuba ruwa a cikin rijyar wanda hakan ya tabbatar mana cewa ba shi ne Zai yi tafiyar ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shaihi Ibrahim ya sha kallon irin artabun da nakan yi da manyan jaruman da wani lokaci hanya kan ratso da su ta dajin. Musamman in suka zo gadan-gadan suna son kama ni.

Wata rana muna kan wata bishiya zaune sai muka hango maigidana Idrisu yana tafe shi kadai, sai kawuna ya ce min, “Ka kuwa san wani ikon Allah? Wancan saurayin ne nake ta gani a cikin mafarki cewa zai kashe Sham’‘una, kuma kai ne dokinsa, saboda haka yanzu sai ka yi sauri ka zama doki ka tare shi.”

Shi ne na sauko na je na sa Kafata cikin wata sarkakiya har ma na ji rauni, shi kuma Idrisu ya zo ya taimaka mini ya yi jiyyata, ya sa mini sunan da na yi matukar Kauna, wato Jagora.

Babu shakka Idrisu saurayi ne mai mutunci da tausayi, don tun daga wancan lokaci har zuwa yau din nan bai taba daga bulala ya buge niba.

Wannan shi ne takaitaccen labarina.” AKA fara hada-hadar daurin aure tsakanin Jagora dokin Idrisu, wato Ramalanu dan Rayalanu da kuma Dailanu ‘yar Kailanu. Idrisu ne waliyin ango, shi kama Sarki Ifritu waliyin amarya, bisa amincewar

Www.bankinhausanovels.com.ng sauran dangin ango da amarya da ke wurin.

Jarumi Idrisu ya ce, “A matsayina na aboki kuma uban ango ina son don Allah a dan saurare ni don yanzu zan je in taho da sadakin wannan tsaleliyar budurwa da abokina ya samu.”

Ya debi aljanu ya ce su biyo shi, shi kuma ya haye dardumarsa, bai zame ko ina ba sai cikin kogon nan da ya kashe Bakayalu, ya ce su ciccibo masa Katon gadon nan nata na alfarma, sannan duk wani abu mai daraja da ke wurin shi ma su dauko shi. Haka ko aka yi.

Jama’‘a a filin daura aure kawai sai aka ga abu gingiringin haka tun daga cikin sama yana ta Kyalkyali. Idrisu ya ce, “Ga sadaki nan.”

Murna wurin amarya da Kawayenta in aka ce zaa misalta sai abin ya zama Kauyanci. Aka dai daura aure, sannan aka tabbatar wa Jagora da sarautar wannan babban birni. Jama’‘ar garinsa suka ce su ma suna bukatar don Allah a je garinsu don tabbatar masa da sarautar mahaifinsa, wato a takaice dai Ramalanu Jagora ya zama Sarki a manyan Kasashe biyu na aljanu. Gaskiya an ragargaji buki da shagali yadda ya kamata.

Www.bankinhausanovels.com.ng
BAYAN an natsu sosai sai hankalin kowa ya koma zuwa garinsu. Aka yi shiri mai kyau na mayar da kowa gidansa tare da ya da zango a wasu muhimman wurare. An fara ne da garin Sarki Ifritu, sannan sai birnin Idris inda Sarki Abdurrahman ke mulki, wato tsohon garin Sarauniya Zinkadaziyya mai macizai, wanda a lokacin da aka je suka ji irin rugugin da ke sauka daga sama na jama‘ar aljanu da mutane da ke cikin tawagar sai suka rufe birninsu suka je masallaci suna ta neman kariyar Allah.

Daya ke a bayan gari aka sauka sai Idrisu ya sa wani aljani ya dauke shi ya sauke shi cikin gari, ya same su a masallaci ya yi musu sallama, suna ganin sa farin ciki ya lulluBe su, ya tambaye su lafiya, suka ba shi labari, sai ya yi dariya ya ce wa Sarki Abdurrahman, “Ai baa san jarumi da tsoro ba.” ;

Suka mika masa budurwarsa suka tashi suka Kara gaba, haka nan suka yi ta sauke ‘yan matan nan daya bayan daya a garuruwansu bayan an shiga an yi wa jama’‘arta bayanin yadda abubuwa suka faru.

Duk tafiyar nan da ake yi ‘yan matan nan suna cikin wancan gida ne da Sham’‘una ya gina musu, a ciki ake ta karakaina da su. Duk yarinyar da aka sauke a garinsu sai a kawo dumbin dukiya ta zinare da lu’u’lu’u da yakutu da zabarjadi da sauransu a bata.
Daga Karshe aka je aka sauke wa jarumi Idrisu wannan Kankararren gida a garinsu bayan daurin aurensa shi da masoyiyarsa Nur ‘yar babban Shehi Ibrahim. Murna wurin duk wadanda abin ya shafa ba ya misaltawa musamman ma iyayensu da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki.

Babban abin sha’awa game da wadannan ‘yan’uwa da abokai da Kawaye shi ne yau wannan na garin wancan gobe wancan na wurin wannan. Babu yadda za a yi Dailanu da mijinta Ramalanu su yi wata uku ba su kai wa Idrisu da Nur ziyara ba, ko kuma wani gari inda Kawayensu suke. Ita kama Nur da mijintaa kai-a kai ba su yanke ziyara zuwa garin Bashari, Yahaya, Habu ko Abdurrahman ba.

Haka suka kasance cikin jin dadi da farin ciki da Kauna har mai raba jin dadi kuma mai raba masoya ta zakke musu.

MASHA ALLAH TO JAMA,A NAN MUKA KARKARE WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN NA YAKI MAI SUNA YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA

PLEASE IDAN HAR KA KARANTA KIN KARANTA WANNAN LITTAFI KUMA KUNJI DADINSA KUYI COMMENTS A KASA HAKANNE ZAI BANI KARFIN GWIWAR SAKE NEMO MUKU WANI LITTAFIN NA YAKI MAI DAN KAREN DADI INAMA KOWA FATAN ALKHAIRI


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels

2 Comments On YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAMUNA
avatar
abdullahi-dahiru

1 year ago

Reply

Good

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdullahi-dahiru

Keep following our site for more hausa adventures novels

Please Login or Register in order to submit comment