Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

a matsayin masoyin ki wanda har ni dake muna tunanin zakuyi aure nan gaba kad’an, Inaso ki yafemin dan Allah, ki kuma yafewa Yaya, duk kuwa dama shi can bai tab’a furta miki kalmar yana son ki ba, inaso ki ‘dau laipin kacokan ki dora akaina, Ki kuma dau hakan a matsayin taki kaddarar kenan, Saboda kowa yanada lapses dinsa a rayuwa, dan Allah Kiyi hak’uri, HALACCI d’aya zakiwa zuciar ki shine ki cire son Yaya daga gareta ki nisanta kanki da maganar son sa, In shaa Allahu hakan zai zamto miki alkhairi nan gaba, Dan Allah ki yafe mana, munyi kuskure wallahi, ki yafemana dan Allah.. Kinji Liya?”

Aliya ta goge hawayen dake ‘diga daga idanun ta, kafin cikin sarkewar murya tace,

“Ni ban rike ku a zuciata ba dama, kuma karma ki ‘dorawa kanki laipi wallahi dan har gaban abadan ba zanga laipin ki ba, ni ce mai lefi dana hangowa kaina wanda ya fini komai, domin WUTSIYAR RAK’UMI tayi nesa da ‘kasa cuz ni da Ya Sahal dama bamu dace mu auri juna ba, sai dai tambaya d’aya zan miki, shin wacece Ya Sahal ke so? Da har yake muradin auren ta, bayan duk tsawon shekarun nan iya sani na dashi ko acan baya bai tab’a cewa yayi soyayya da wata ba, ko kema baki sani ba?”

Husnah ta shiga raba idanuwa tana tunanin tafad’a mata kuwa ko tabari shi ya fad’a mata da bakin sa? Cikin yarda da abunda zuciar ta ta amince mata ta fad’a tace,

“Koma wacece ba son sa take yi ba itama, domin yacemin yarinyar daya keso ma yace batasan yana jidalin son taba, kuma dayai bincike akanta yagano wani take so take kuma burin auren shi mutumin, amma yace duk tsawon shekarun nan ita kadai yake so yake kuma muradin aura, Amma abun da kamar wuya saboda ko a mafarki banajin auren su zai tab’a yiwuwa idan kuwa anyi to dama haka alqalamin kudra ya rubuta, fatana dai Allah ya xaba muku abunda yafi alkhairi kawai, dama we plan ne and Allah plans kuma Allah is the best of planners, Saboda haka kisa aranki sufficient for us is Allah and he’s the best dispose of our affairs..”

Aliya ta ajiye nannauyar ajiyar zuciya tace,

“Toh Allah yafimu sanin dai-dai, Allah ya zaba mana abunda yafi alkhairi, ya min text message d’axu da safe wai zai zo da yamma, Bana jin zan fita wajen sama..”

Husnah ta ‘dora hannun ta kan na Aliya, dayan kuma tana ‘dan bubbuga bayan Aliyan dashi alamar ban hak’uri kafin tace mata,

“Ki fita kiji me zai fada miki, Kiyi ko’kari ki cire son sa a zuciar ki, Kinsan Maza mutanen mu idan sunga andamu dasu, ki kara hak’uri tawaje na, Allah ya yaye mana matsalolin mu, ke kinada masoyan dake son ki ma, ni ko kare bai tab’a zuwa yace yana sallama dani ba, gashi kyau da ilimin boko da arabi dai-dai gwargwado inada su, amma banida samarin dake cewa suna so na, Saboda ance ahar kullum ka dinga kallon na ‘kasa dakai kana ganin matsalar dake damun sa, anan zaki tabbatar lalle ke Allah ya miki nasarori da yawa a rayuwa, dama bature yace your first love is not always your truest love..Ki fawwalawa Allah lamurran ki..”

Aliya tai murmushin karfin hali kafin tace,

“Toh shikenan tawaje na, zan fita naji abunda zai gayamin, Sannan ki dena cewa bakin jini ne dake, komai yanada lokacin sa, Kiyi exercising patience domin Allah yana tare da masu hak’uri, In Shaa Allahu nan bada jimawa ba zaki samu mijin aure keda duk wanda ke nema.”

“Amin ya hayyu ya qayyum qawata, Bari na tashi na tafi, zanje school ance time table yafi to, Sannan dodon bango ma (result), an kafe shima amma ‘yan maths da chemistry da nursing aka fara kafewa, Nasan namu ma anytime zaki ji an kafe, Allah dai ya bamu nasara, ya rabamu da samun matsala”

“Ameen kawata, Nagode sosai, Ai kuwa yan new site ma an fara kafe musu, Allah ya wutar damu duka Ameen!..”

Nan dai suka sake yin sallama da juna, Fa’izah ma ta fito daga kitchen tanata sauri zata kai mata abinci tace takoshi wlh, suka ‘danyi maganar futowar result, daganan Fa’izah ta rakata har titi sannan tadawo gidah.

*4:00pm*

Dai-dai lokacin Muhammad Sahal yaje gidan su Aliya! Hijabi kawai ta zura tafita wajen sa, yana zaune akan mota yana danna waya, kallo d’aya sukaiwa junan su kowanne ya janya idanuwan sa, ganin yadda kowanne ya rame, danuwa fal a zukatan su na ciwon son maso wani dake damun su, tabarma ta shimfida musu a soran gidan nasu, ya ‘karasa ya zauna suka gaysa kowanne fuskar sa ‘dauke da damuwa, Suka gaisa daga nan kowanne yai shiru. Sahal ya shiga kwararo mata zancen abunda ya kawo shi, bayan ya nemi gafara awajen ta na halin daya tsomata aciki. Ya ‘kark’are da,

“Kiyi hak’uri Sis, wallahi tallahi banyi haka dan na yaudare ki ba, ko na had’a ruguntsumi a tsakanin ku ba, So makaho ne, So guba ne, So baya shawara dakai idan zai kama ka, Sis! Allah ya dasamin soyayyar wadda duk dunia babu wanda ya isa ya cire ta daga zucia ta fyace Allah daya halicce mu, ban tab’a sanin So haka yake ba sai akan ta, bansan menene So ba sai dana kamu da zazzafar ‘kaunar ta, Wanda wallahi idan har ban mallake ta ba zan iya rasa rayuwata ko kuwa na kamu da wata babbar cutar, domin tun ba’aje ko’ina ba na kamu da larurai kala kala akan sonta, zucia ta ta riga da ta kamu da son ta, wani irin So ne wanda baki ko alqalami bazasu iya rubuta matsayin ba, Nayi nayi nacire soyayyar ta a zucia ta na kasa, batasan ina yi bama, wani daban take so take kuma muradin aura, S...”

Aliya ta ‘daga masa hannu tana goge hawayen dake kwarara daga idanun ta, Fa’izah dake lab’e itama ta goge nata hawayen tana lailayo ashar da kwandon Allah ya isa tana saukewa Sahal a zuciar ta, Domin tasan sai dai idan Allah ne ya tsare kawai, Amma karshen zumuncin su da Aliya yazo kenan, cikin tunanin data tafi ta jiyo muryar Aliya na cewa da Sahal,

“Dakata Ya Sahal, kadena wani yin kwane-kwane, shin wacece wannan wadda kakeso ka sadaukar mata da soyayyar ka gaba d’aya? da har idanuwan ka sun rufe kake kallon tsabar idanuna kana gayamin ita kakeso kuma zaka aura, shin kayiwa zuciata HALACCI kenan? Idan har bata son ka, bata kuma son ta aure ka, Toh nima ka dubi maraici na KAI MIN HALACCI! Ka aure ni Ya Sahal...”

Sahal yai shiru yana goge gumin dake tsattsago masa agoshi da ilahirin jikin sa bayan sanyin da ake zubawa agarin, da alama yana cikin tashin hankali, cikin rawar baki yace da ita,

“Kiyi hak’uri sis! Wallahi tallahi billahi kinji rantsuwar musulmi? Idan har ban mallaki yarinyar nan ba, Toh ni da farin ciki munyi hannnun riga, Kuma ba wai bakuwar fuska bace, Zuciata ta dad’e tana begen son ta da kuma muradin auren ta, KI MIN HALACCI nima kiyi hak’uri ki karb’i kokon gafara ta, Ki yafemin abunda nai miki a baya, ki yiwa zumuncin mu HALACCI ki yafemin ki kuma cire ni a zuciar ki, wallahi tallahi ban yaudare ki ba domin ban tab’a nuna soyayya ta agare ki ba..”

Sahal ya ‘karasa fad’a yana sanya gwiwoyin sa duka biyu yana kneeling down, hawaye kwance kan fuskar sa, ya daga mata hannuwan sa biyu alamun tayi hak’uri ta yafe masa, Aliya ta ware idanu tana binsa da kallon tsantsar mamaki, cikin rawar baki tace,

“Shin wacece wannan da har kake sanya gwiwoyin ka a ‘kasa kana neman gafara ta akan ta? Shin wacece wannan da take wahalar da soyayyar da kake mata? Shin wacece wannan da shekara da shekaru kake tarairayar sonta a zuciar ka?”

Sahal ya sake goge gumin daya tsattsago masa, ya had’iye wani kakkauran yawun tsoro, Cike da rawar baki yace,

“Wallahi ba wata bace fyace Fa’izah Sulaiman....”

Tuni tunanin Aliya so ma gushewa kunsan Idan mamakin abu yayi yawa, Toh ko wanda ka sani aka fad’i sunan sa ma’ana shine silar abun, Wallahi tsabar mamaki ma Idan aka fad’i sunan sa ba ganewa zakai ba, kwata kwata ma tamkar an shafe sanayyar ka dashi a zuciar ka haka zaka ji ka manta koma menene, cikin rashin gano ko sunan wacece Aliya ta dubi Sahal da kallon neman ‘karin bayani kafin cikin rawar baki tace dashi,

“Wacece Fa’izah Sulaiman?”

“Fa’izah Sulaiman, First cousin ‘d’inki dake nan gidan, Fa’izan Gwaggo Talatuwa...”

Ba Aliya ba ko Fa’izah dake lab’e tana jin su saida taji wani jiri ya kwashe ta duk kuwa da tasan shine Muhamman S kuma ya bayyana mata kansa, Amma bata taba kawo rana irin ta yau ba, ko a mafarki bata taba zaton Sahal zai fadawa Aliya gaskiar lamari ba, cikin kamo salati da addu’oin da batasan iya karsu ba taja sanyayyun ‘kafafuwan ta tabar wajen, Domin bama tason ta tsaya ta ‘kara jin tattaunar da Aliya da Sahal zasuyi, Tasan dai kawai ya b’oye zancen tasan shine. ‘Bangaren Aliya kuwa tuni jinta da ganin ta suka dauke na ‘yan wasu lokuta, gaba d’aya tarasa tacewa bakinta ya mata nauyi, kirjin ta da zuciar ta cike suke da jin wannan sabuwar almara da Sahal ya fad’a, idanuwan ta na mata nauyi tamkar bacci take yi, hawaye ne kawai ke kwarara daga idanun ta, takasa gane wane irin mugun hali ta shiga, Sahal kuwa ji yai kamar ancire masa wani babban dutse daga kirjin sa, domin ya jima yana son sanar da Aliya hakan amma ya kasa sai yau da Allah yayi.

Zaune take kai daka ganta kasan cewar bata cikin hayyacinta duba da yadda idanunta suke shararar da hawaye gashi ta kurawa guri d'aya idanuwa. Fa'iza kuwa da gudu ta ruga wajan Umma tana kuka ta rik'e kofar parlour da hannun hagu yayin da na daman yake dafe da kirjinta wanda yake yi mata zugi da rad'ad'i, ba tare da ta kalli Umman ba tace cikin kuka.

“Umma Aliya...Sahal..a zaure..na shiga uku Umma ya sanar da ita wallahi.”

Fa'iza ta karasa managara tana kuma sakin wani rikirkitaccen kukan. Umma tayi saurin mik'ewa daga gurin d'inki ta karasa wajan Fa'iza tare da dafo kafad'ar ta tace.

“Mekike nufi da hakan Fa'iza?”

“Umma Yaya Sahal yana can ya sanar da Aliya ba ita yake so ba ni yake so ya aura..”

Rintsa ido Umman tayi tare da janye Fa'iza daga bakin k'ofa ta zari hijabi akan k'ofar ta nufi zaure, tana zuwa ta d'an tsaya tayi sallama, Sahal da yake ta son lallashin Aliya ya kasa domin sam ta ki bari ya tab'a ta kamar ma bataji bata gani haka yake gani duba da sam taki kallansa tun lokacin da yayi maganar.

“Muhammad ashe daman kaine Muhamman S?”

Kansa a kasa yana shasshafa tafarmar da suke zaune a kai yaji duk kunya ta rufesa sannan ya daure yace.

“Eh Umma.”

“Toh amman mai yasa ka yiwa k'annan naka haka Sahal?”

Kafin ya bada amsa kawai suka ga Aliya ta dafe kirji taka a gurin ta sulale ta kwanta wanda da alama numfashinta ne ya d'auke na wucin gadi. Cikin kid'ima Sahal yayi kanta da nufin taro ta hankali a tashi amman Umma tayi saurin dakatar dashi. Cak ya tsaya idanunsa akan Aliya yaji Umma ta kwalawa Fa'iza kira, aikuwa sai gata da gudu cikin kuka kamar jira dama take yi a kirata. Sahal ya zuba mata ido lokacin da ta shigo zaure, sanye take cikin skirt na wani material da T. shirt mai gajeran hannu, na shanunta suka bayyana daga saman amman kad'an, kanta da d'ankwalin skirt d'in ta karasa wajan Umma dake cewa.

“Temaka mu d'aga ta, an shiga uku yau meke shirin faruwa ne?”

Umma tayi maganar tana k'ok'arin d'ago Aliya inda Fa'iza taje ta temaka mata suka d'auketa aka nufi cikin gida da ita yara sai kallon su suke yi. Sahal kuwa k'ok'arin binsu ciki yake yi, tuni zuciyarsa tayi saurin hanashi tare da tuna mishi cewar karfa ya manta komenene shine sila, mai zai shiga yayi banda ya janyowa kanshi tsana. Jiki babu kwari ya juya zai tafi kawai ya jiyo muryar Fa'iza cikin kuka tana yi masa magana cewar.

“Kaji dad'i? Nasan yanzu zuciyarka shartake tunda kazo ka kunsa mata bakin cikin d'ah namiji. Toh barikaji na gaya maka, ka shirya daga rana irinta yau kaima zaka fara shak'ar bakin kwatankwacin irin wanda kazo ka kunsa mata. Kuma indai nice nan gani nan bari bazan tab'a auranka ba. Zantattaro maka duk wani abu daka kawo min wad'anda zasu iya ajiyuwa, wad'anda kuma 'yan uwana suka ci suka yi amfani dashi za'a siyo suma duk za'a biya ka hatta kayan provision d'in daka dinga kaiwa muna school zan biya ka domin kawai ka rabu dani sannan karkayi min proud cewar naci kudinka. Wallahi barina gaya maka banda wayar da nake amfani da ita babu abinda na tab'a amfani dashi a duk cikin abubuwan daka aiko da sunana. Kaci amanar Aliya, dan ka b'oye mata cewar ba soyayyar aure kake yi mata ba, kuma sai Allah ya saka mata, kaje indai wannan halin mai kyau ne zaka gani.”

Tana kaiwa nan tayi masa wani kallon sama da kasa hawaye basu bar fita daga cikin idanunta ba, sannan ta juya ta shige gida tabarshi tsaye yana bin hanyar da tabi da kallo. Zuciyarsa banda tafasa babu abinda take yi, hakan yasa dakyar ya koma komata tare da kifa kansa jikin sitiyari yana d'an bubbugawa. A hankali ya zaro wayarsa daga cikin aljihu ya lalibo lambar Fareed, cikin sa'a bugu biyu ya d'auka yana ta faman masifa akan yana wajan babynsa ya wani kirashi, amman Fareed yana jin muryar Sahal yace.

“Zoka d'auke ni please.”

“Wai harka gama naka tad'in?”

“Malam idan zaka zo ka d'auke ni kazo, idan kuma surutu zaka tsaya yi min ka barshi kawai.”

“A'ah mai yayi zafi? bari nazo nasan ko wani abun aka tayar maka dashi yau.”

Fareed yayi sallama da budurwarsa ya hau napep ya nufi unguwar su Fa'iza, akan kwana ya hango motar Sahal dan haka ya sauka daga napep din ya biya shi sannan ya karasa wajan Sahal. Yana kallansa yasan babu lafiya dan haka yace ya fito ya koma d'aya seat d'in, sai da ya temaka masa sannan shi kuma ya zauna a wajan driver ya tuka ba tare daya tambayesa abin dake faruwa ba. Kai tsaye asibiti ya wuce dashi duk da yasan Sahal ba wani kaunar shiga asibiti yake yi ba.

Su Fa'iza kuwa hankali duk a tashe musamman da gwaggo taji cewar Aliya ta suma, nan ta nemi jin ba'asi Umma ta sanar da ita komai a takaice. Nanfa gwaggo ta dinga salati tana tafa hannuwa tare da shararo zagi tana antayawa Sahal. Da kyar suka samu Aliya ta farfad'o, sai dai tana bud'e ido taga duk mutanan gidan a kanta suna jero mata sannu sannan ne ta kuma tabbatar da cewar bawai mafarki take yi ba da gaske ne Sahal yazo yace mata Fa'iza yake so ba ita ba.

“Allahumma ajirni fimusibati, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un.”

Haka kawai Aliya ta dinga furtawa tana k'ok'arin danne abinda take ji a cikin zuciyarta amman ta kasa. Tana jin yadda gwaggo Talatuwa take surfawa Sahal zagi tana mamakin yadda ya iya yin wannan rashin kunyar yazo yace na Aliya yake so ba, meya hanashi fad'a tun lokacin da yaje suna yi masa fatan kasan cewa tare da Aliya ai da sai yace bafa soyayya nake mata ba alokacin kowa sai ya sani, amman dan tsabar rainin hankali sai yanzu zai wani ce ba ita ba. Ita dai Aliya bata sake cewa komai ba, hasalima taki yadda su had'a ido da Fa'iza sabida wani irin haushi da tsanarta da taji sun dirar mata a zuciya. Har Baba Suleiman ya dawo yaji abinda ya faru, sam Aliya taki tankawa kowa a cikin gidan har dare yayi gashi ta mik'awa bata iya yi hakan yasa Baba Suleiman yaje ya kira likita aka zo aka sanya mata ruwa (drip).

Fa'iza tazo kusa da ita ta zauna tare da gyara zama, ga mamakinta sai taga Aliya ta lumshe ido tare da kawar da kai ba tace komai ba da alama dai bata son bud'e ido ta ga Fa'iza.

“Kiyi hakuri Sissy w.....”

Cikin sauri Aliya ta d'aga mata hannu alamun bata son tayi mata magana, hawaye suka zubowa Fa'iza tasa hannu ta share su. A ranar basu sake magana da juna ba saboda Aliya taki bada fuska, tsanar Fa'iza ce sosai a cikin ranta dan ko Sahal batajin zafinsa kamar yadda takejin na Fa'iza, ciki harda Umma da Baba Suleiman gani take tamkar munafuntarta suka yi. Washe gari tun da sassafe ta mike ta shirya duk kuwa da yadda zuciyarta take zafi jikinta duk babu kwari kanta yana mugun sarawa amman bata son zaman gidan gabaki d'aya ta tsane su dan haka ko ganinsu bata son yi, ta shirya tayi tafiyarta ba tare da tayi sallama da kowa ba kuma duk Fa'iza tana kallonta.

A kasa ta dinga tafiya saboda babu kowa masu napep basu fara fitowa ba daman sanye take da hijabi har kasa tana tafiya tana share hawaye. Kofar wani gida taje ta zauna taci uban kukanta har kusan karfe bakwai da kwata sannan ta goge fuskatar ta dauki jakarta tana fara tafiya taga mai napep ta tareshi ya kaita gurin aikinta. Sukuku ta dinga yin komai taje ta kai duk wasu abubuwa office d'in Shamsuddeen sannan ta koma kujera ta zauna tana tunanin munafurtata da Sahal yayi ga kuma Fa'iza da ta boye mata wanene Muhamman S. Tana cikin wannan tunanin taji shigowar CEO, tayi saurin mik'ewa tare da gyara fuskarta ta goge hawayen ta gyara hijabin jikinta sannan ta nufi office d'in nashi.

Kanta a kasa bayan tayi knocking yana tsaye ya juyawa kofa baya ya amsa mata tare da bada umarnin a shigo. Da sallama cikin sassanyar murya ta shiga tare da kallon bayansa tana gaida shi.

“Good morning sir.”

Sai da ya rufe wani file ya ajiye gefe sannan ya waigo tare da amsa gaisuwar wadda take mik'a masa. Idanu hudu suka yi da ita tayi saurin sunkuyar da kai wasu hawayen suna kuma zirarowa daga idanunta, ko cikin giya yake ba zai tab'a mantawa da wannan halittar ba ballantana yana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Wani irin kallo yayi mata kanta a kasa tana zubar da hawaye yayi tattaki a hankali sai gashi a gabanta, kamshin turaran da taji ne a cikin hancinta kai kace tana a jikinsa shine yasa tayi saurin d'agowa suka kuma yin ido hud'u ya tsuke fuska tare da......

*DIJAMA*

Gaba ‘daya hautsina ‘dakin ta shiga yi tana neman ‘kullin magungunan da Malam Namuduka ya bata a leda, Tsaki take ta jerawa tamkar dangin tsaka, Gumi sai tsattsago mata yake yi kamar wadda taci gudu, Shamilalliyar katifar ta ta ‘daga ko zata ga magungunan amma ko alamar su bata gani ba, Wani tsakin ta saki tana ko’karin zazzage kayan akwatinta Maman su ta shiga ‘dakin hannun ta rik’e da irin ‘dan ultimate gas dinnan ‘karami, tana ta dokawa Dijaman kira bata amsawa shiysa tana shiga ta rufe ta da fad’a,

“Dan uban ki! Ina faman kiran ki tun ‘d’axu shine zaki k’i amsa ni? Ga marainiyar wayon ki ko? Zaki tashi ki karb’i kudi ki ‘duro gas ‘dinnan ko sai na gunguri uban ki..”

Yatsina fuska Dijama tayi tana mita ‘kasa ‘kasa, cikin turo baki gaba tace,

“Mama da bananan waya shigo ‘dakin nan? Nayi ajiya wallahi bangan taba”

“Kudi ki ka ajiye ko kuwa abinci ne?”

Khadija ta zura hannu tana ‘kwa’kwular cikin hancin ta kafin tace,

“Mama a leda suke, hoda ce Hafsat ta bani to sai ta fashe, sai na zuba a leda, d’aya kuma foundation dita ce na ‘dan debi kad’an a leda na bawa Hafsat sauran, Ina ta saurin dana gama komai sai na tafi gidan su Shamsudden.”

Ta ‘karasa fada tana sake bin ‘dakin da kallo ko zata ga ledojin. Hajia Maryam ta yamutsa fuska kafin tace,

“Tab! Ai kuwa wallahi nayi kwalemar ‘daki rannan dana aike ki, to sai na had’a da naki dakin na sharo yana na gyare shi tsaf, Dan dama nasha miki maganar tsafta Dijama, Shiysa ranar kawai nayi kwalemar ko’ina na gidan nan.”

“Kutm...”

Bata ‘karasa ba Hajia Maryam ta ware idanu, had’e da kaiwa Dijama duka, kafin cikin tsantsar mamaki tace.

“‘Karasa zagi na Dijama, akan shegiyar hoda zaki zagi? Lalle albasa ba tai halin....”

“Mama dan Allah kiyi hak’uri, wallahi Allah ba zagin ki zan yi ba, ya za’ai na zage ki ma? Haba Mama tah..”

“Ke kika sani, ungo rike ya ‘duro miki na dubu d’aya, Kiyi sauri ki kawo na ‘karasa suyar meat pie ‘dinnan ki kai gidan Hajia Bintu.”

“Toh Mama.”

Khadija tasa hannu ta karb’a kudin hade da sanya hijabin ta, ta ‘dauki gas ‘din ta tafi wajen d’urowa, Tana tafe tana zubda hawayen share mata magunguna da Maman tayi, bayan Malam Namuduka ya jaddada mata muhimmancin su idan har ta aiwatar da komai, yanxu gashi layar da akace ta sanya a pillow ce kawai tayi ragowa itama dan a cikin purse ta ajiye.
Koda ta koma gidah wanka tayi ta cancara ado, dama bata cika wanka ko wanki ba sai zata unguwa, biki ko suna. Kayan ta dake can ‘kasan akwati ta ‘dauka tun na sallar bara, tasha ado ta zuba ‘kamshi, tayiwa layar kyakkyawar ajiya acikin kanta, sannan ta ‘dauki bokitin da aka zuba meat pie ‘din ta tafi gidan su Shamsudden..
Haka ta shiga gidan su Shamsudden tana sassaye fuska wai ita surukar gidan, ta tattaya Umman su Shamsudden aiki, atare su ka ‘dora girkin dare ma da Umman, Sannan suka koma parlor suka zauna, Khadija ta ‘dan muskata kafin tace da Umman,

“Ummah nace ko ‘dakin Ya Shamsudden a gyare yake? Gwara shima a ‘dan tattare masa.”

Ummah ta dashe baki, tana sake yaba hankali da nutsuwa irin ta Dijama, Tabbas Shamsudden yayi sa’ar mata, Y’ar purse ‘dinta umman ta zuge ta ciro keyi din ‘dakin Shamsudden ta mik’a mata tana cewa,

“Yawwa y’ar albarka, d’axu nake xancen zan gyara masa wallahi, temaka dijama har bandakin ki wanko, dukda dai autan nawa akwai tsafta, Kullum cikin gyara da tsaftace ‘dakin sa yake..”

“Toh Ummah..!”

Dijama ta fad’a a kunyace, ta durkusa ta karb’i mukullin a hannun Ummah, murmushi kwance kan fuskar ta, Saboda ta samu damar aiwatar da qudurin ta na zura layar a pillow/matashin kai din Shamsudden, komai tsaf na ‘dakin da bandakin domin tashin ‘kamshi ma suke yi, ta ‘kakkarewa hotunan sa kallo kafin daga bisani ta cusa layar cancikin pillow ‘din yadda ba zata tab’a fod’owa ba, Ranta fes ta koma parlor wajen Ummah tana ‘kiyasta yadda qudrinta zai cika akan Shamsudden...

Koda ta koma parlor jefi jefi suke hira da Ummah, daga baya Ummah takoma parlor wajen Abba. Bata jima ba itama tayi musu sallama ta tafi titi ta hate ‘dan sahu, Shawara Dijama ta shiga yi da zuciar ta, har dai ta tsaida hukuncin abunda zata yi, Cike da murmushi ta zaro wayar ta acikin jaka, Ta haukan sunan Shamsudden data yiwa saving da suna ‘Heartbeat’. Ta shiga rubuta masa message da,

“As-Salam Alaikum Yaya na, Mamallakin zucia ta, hak’ika na zauna nayi nazari da zucia ta, na gano tabbas babu wadda ta dace ta zama mamallakin ka iri na, Son ka yayi nitso a kogin zucia ta, kai ne mukullin zucia ta, Saboda haka Yaya na kuma miji na nan gaba kad’an, Na amince zan aure ka, domin ‘kaunar ka nake yi, ka cire waswasin zan guje ka don abunda yake damun ka, Ni Khadija taka ce, Kai nawa ne, Saboda haka na share ma kukan ka, Zan maka HALACCI, Zan aure ka, Ina fatan idan mukai aure hakan zai zamto silar samun lapiar ka...Bissalam! Taka: KhadShams..”

Tana gama rubutawa ta tura masa, domin tanada yak’inin abunda Malam Namuduka ya fad’a zai tabbata, Idan su kai aure zai warke, kuma dama dan ‘ya’yan banki take son sa...
_*KAI MIN HALACCI......!💕_*


_*NA_*


_*MISS XOXO🧕🏼_*


_*NO: 43C_*


DIJAMA

Dijama tayi shiru tana raba idanuwa, jikin ta ya fara rawa kamar mazari, Sai kallon Alhaji Garba take da idanun ta, tayi kalar tausayi wai ko zai tausaya mata, Yatsina fuska yayi ya nunata da yatsa yana nana ta mata,

“Ke khadija minti uku na baki wallahi idan ba zaki magana ba, zan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment