Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

babu wanda zai yadda da shi, kai Shamsu ka bawa Aliyah hakuri saboda ita kayiwa laifin.”

Wani irin bakin ciki ne ya kuma tasowa Shamsu, be tab'a tunanin kalmar so da kyautatawa suna zamewa abin wulak'anci da tozarci ba har sai yau da aka yi masa ya gani, yanzu duk wannan soyayyar da kyautar da yake mata karshe shine zai bada hakuri? Tunda ya fara jin kaunar Aliya be tab'a tsanarta ba sai yanzu, duk wani wulak'anci da take yi masa a da baya gani sai yanzu ya gano cimasa mutunci kawai take yi, nan fa zuciyarsa tayi ba’kik’kirin, bakin ciki ya taru yayi masa yawa wanda yasa yaki bada hakurin da aka ce ya bayar.

“Shamsu maganafa nake yi maka, nace ka basu hakuri ka tsaya kana tunani.”

Shamsu yaki yin koda motsi,Saboda zuciyarsa da take tafarfasa yana jin koda dukan tsiya Abba zai yi masa sai dai yayi amman ba zai bayar ba, ganin yaki bayarwa yasa gwaggo cewa,

“Ka gani ko malam, dama haka Shamsu yake ban sani ba? Lallai toh kayi da 'yan halas, Allah ya kawo Sulaiman (mahaifin Fa'iza) ya dawo daga anambra zan sanar da shi abinda kake neman yiwa 'yar gidan kanwarsa, shi ai zai san yadda zai yi da kai.”

Jan hannun Aliya da Fa'iza gwaggo tayi suka fita, Abba da Umma sai hakuri suke bata amman ina, ta tafi nan suka koma kan Shamsu da fada da masifa yayi shiru yaki tankawa su kansu basu yi tunanin yana da taurin kai irin haka ba, Saboda be tab'a yi musu ba, yana nan zaune har suka yi shiru Abba ya mik'e ya shiga d'aki ita kuma Umma ta juya masa bayanta ta kwanta suka barshi anan tsawon lokaci, Sai da yaya Garzali ya dawo yaji abinda yake faruwa suna kwance a daki ya Garzalin ya fara yiwa Shamsu nasiha amman ko shiga bata yi, Saboda sam zuciyarsa ba a nutse take ba.

Tsawon kwani biyu baya fita yana gida a kwance, ko ciniki aka kawo masa baya lissafawa kawai d'iba yake ya sallami yaran shagonsa sauran kuma ya b'oye su, a kwanaki na ukun ne yana zaune a d'aki yana duba wasu kaya da aka turo masa ko zai siya yaji muryar Abban su yana nemansa, ajiye wayar yayi ya bishi ciki, suka zauna a d'akin abban inda yake ce masa.

“Alhamdulillah duk da yanzu kafi ‘karfin mu, Saboda kaga ka fara tara arziki har kana so ka nuna mana iyakarmu, wannan itace bukata ta biyu da zan nema a gurinka idan itama bata samuba kamar ta farkon to dole na cireka a sahun 'ya'yan da na haifa, sai kaje ka nemo wasu iyayen, duk da cewar ina neman alfarmar ne dan amfanin kanka ba wai danni ba ko mahaifiyarka. Shamsu ina son zaka koma karatu kayi degree program d'inka a can k'asar Switzerland...''

Da sauri Shamsu ya d'ago ya kalli mahaifinsa wanda yayi kicin-kicin da fuska tamkar be tab'a yin dariya ko fara'a ba, cikin.....

______
_Littafin KAI MIN HALACCI na kudi ne, yana d’aya daga cikin ZAFAFA BIYAR NOVELS da aka fara, idan Kina So ki biya kudi ki siya ta; _

Hafsat kabir umar
0225878823
GT bank

*ga mai buqatar littafan zafafa biyar dukansu ko wasu daga ciki sai ya biya 500 ga dukka litattafan,ko 200 ga littafi  daya,ko 300 ga littafi biyu,ko 350 ga liitafi uku,ko 450 ga littafi hudu*






_WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
*KAI MAN HALACCI*


*MISS XOXO🧕🏼*
*PG:5*

Cikin tsantsar mamaki yake kallan mahaifinsa tare da dafe kirji, kenan Abba yana nufin ya tattare kudin sa daya tara yaje yayi karatu? Idan haka ne, Abba beyi masa adalci ba duk da cewar shima yana buk'atar yin nisa da gida, Ko dan ya dena ganin waccan masharranciyar, da a baya yake tsantsar ‘kaunar ta, amman a yanzu kashin alade ya fita matsayi a zuciyarsa. Ganin irin yadda yake kallon sa ne yasa Abban gyara tabarau din idanunsa (eye glasses) yace,

“Nasan zaka yi mamaki dan nace ka koma makaranta bayan kuma ka nuna mana rashin son ka da cigaba, toh ka sani Shamsu yanzu a duniyar nan babu abinda yake tafiya sai da ilimin zamani, nasan kana d'aukar karatun boko a matsayin wahala, toh bari kaji yanzu idan babu wayewar ilimin zamani a tare da kai, kasuwan cin naka nan gaba ba zakaji dad'in yinsa ba, yanzu dai amincewar ka nake buk'ata dan bana son ayi asarar lokaci da kuma kud'i.”

Cike da jimami bakin sa yana karkarwa ‘kirjinsa yana bugawa hankalin sa a tashe yace,

“Toh Abba ta yaya zan tafi wata ‘kasar yin karatu? Ko jarin nawa zan tattara naje nayi ilimin boko?”

Abba yayi murmushi domin yasan matsalar Shamsu shine baya son abinda zai tab'a masa kasuwanci, cikin murmushin yace masa,

“A'a ba kud'in ka bane ba Shamsu, abinda ya faru shine, tunda na fuskanci baka da buk'atar komawa makaranta gashi Umman ku ta sanar min cewar duk littattafanka ka bayar dasu, baka ajiye komai na tarihiba ya sanya ni tattarawa na kyaleka, nasan cewar ‘kuruciya ce take damun ka, hakan yasa lokacin da waec d'in ku ta fito naga kowa yana zuwa ya duba amman kai babu abinda ya dameka, da kai na naje na duba maka naga komai successfully, naji dad'i a raina naso ace ina ma kai d'in mai son ci gaba da karatu ne tunda kana da ‘kwakwalwa, amman banyi kasa a gwiwa ba Shamsu naje na karbo primary certificate d'inka, dama sauran takardun da ake bukata suna wajan Umman ka na tambayeta ta bani, duk baka san anyi wannan abun ba naje na bada sunan ka, gurin d'an majalisar tarayya, da naji ance zai tura yara goma ‘kasashen waje, kasan cewar akwai sanayya a tsakanin mu yasa ya karb'i takardun ka, kuma yanzu komai yazo kan gab'a jiya ya kira yace yana son kaje zaka yi passport za kuma kayi sign a wasu takardun, wannan shine abinda ya faru.”

Shiru Shamsu yayi yana tunani, tabbas ya cancanci tafiya wani gurin, amman kuma sana'arsa fa? ya zai yi ya barta bayan abubuwa sun fara zuwar masa cikin nasara? Baki ya turo, kai daga gani kasan akwai wata a k'asa, ya kuma tsuke fuska yace,

“Amma Abba sana'a tafa?”

“Kar ka damu akwai wanda na yiwa magana zai kular maka da komai wato Nafi'u na gidan kawun ku Sunusi, kaga yaran yana da hankali da nutsuwa.”

Wata nutsuwa ce ta zowa Shamsu, cikin farin ciki ya juya ya rungume mahaifinsa, murmushi Abba da Umma suka yi ganin ya amince, domin basu tab'a tunanin zai yadda da yin karatun ba ko da anan gida Nigeria ne ballantana kuma ya tafi wata k'asar yin karatu, sai gashi yana murna yana farin ciki duk da sai da yayi zancen yadda zai bar sana'o'insa suci gaba.

“Na yadda Abba zan tafi, sannan kai ma ka dinga saka ido akan business din nawa, insha Allahu zanje nayi karatu kamar yadda kuke buri, Allah ya barmin ku kodan nima na faranta muku nan gaba.”

Albarka suka dinga sanya masa har yaya Garzali ya shigo shima nan yake jin labarin tafiyar ‘kaninsa kasar waje, yayi murna sosai inda yake cewa,

“Shikenan Shamsu baka nan za'a yi bikina.”

Shamsu ya kallesa tare da cewa,

“Yaya kawai ka bari idan na dawo ayi.”

Ya Garzali ya zaro ido yana rike baki. Kafin yace,

“Lallai Shamsu sai nayi ta zaman jiranka kamar kaine zaka aurar dani ko?”

“Toh Yaya ai gani nayi kamar kai ma baka so ayi bana nan.”

“A'a yi tafiyarka, kai baka ga saboda ana so kayi karatu, bama anan zaka yi ba sai kaje cikin jajayen fata, gaskiya Shamsu ina tayaka murna nasan idan ka tafi wannan duhun da kayi sai ka koma yadda Umma ta haifo ka.”

Duka suka yi dariya, yayin da Shamsu ya tashi ya tafi, saboda zai je gidauniyar da d'an majalisar tarayyar su yake nemansu. Cikin kwanciyar hankali komai ya dinga tafiya da taimakon Abba har Shamsu ya kammala yin koma inda zasu tashi nan da kwanaki uku, gashi tunda wannan abun ya faru Shamsu be sake sanya Aliya a cikin idanunsa ba, duk sanda zata fita makaranta to shi kuma lokacin ko ya dad'e da fita ko kuma yana cikin gida yana shiryawa, dan ko shago baya zama saboda masu zind'anshi da cewar ya haura zai lalata jikar Talatuwa.

Komai ya kammala ya damk'awa Nafi'u, komai nasa cike da yak'inin zai rik'e masa komai da amana da gaskiya, yayin da Umma tayi masa 'yan soye-soye ta had'a masa abubuwa da yawa naci wanda ta san yana so, ita kanta Umman har ta fara kewar sa, sai dai ba ta nuna masa ba dan karma yace ya fasa, Saboda yanzu shi lallab'a shi suke yi dan karya bijire musu kasan cewar ba k'aramin aikinsa bane yace ba zai je karatun ba.

Ranar da zai tafi, wajan ‘karfe tara na safe yaje shago, sunyi sallama da kowa, gida ya taho inda yabar su Abba dasu yaya Garzali suna jiran sa yazo su kai shi inda suke taruwa, yai gaf da wuce gidan gwaggo Talatuwa sai ga Aliya da Fa'iza sun fito, ko kallo basu isheshi ba, Saboda shi yanzu gidan ma banda dole sai ya ganshi, da ba zai sake kallansa bare kuma mutanan cikinsa. K'ok'arin shiga gidan su yake yaji ana masa magana, kamar ba zai tsaya ba saboda jin muryar mace, amman sai ya juya yaga Fa'iza ce da murmushi a fuskarta mai kyau tace masa,

“Yaya Shamsu! ashe k'asar zaka bari?”

Wani irin wulak'antaccen kallo yayi mata, wanda yasa jikin Fa'iza yin sanyi k'arara, ta rausayar da kai tare da cewa,

“Kayi hakuri nima nasan haushi na kake ji.”

Tana kai wa nan ta juya jiki babu kwari, dama Aliya na gefe tana faman yi mata dariya, ganin haka da har ya kusa shiga gida sai kuma ya juyo murya a sanyaye kamar ba ta shi ba yace,

“Fa'izah..'”

Da sauri ta waigo dan tabbatar da kiran, shine kuwa dan haka ta tsaya sai taga yayi mata murmushi tare da cewa,

“Karatu zan tafi, ya akai?”

“Babu komai Yaya Shamsu, daman sallama zanyi maka Allah ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, ya kuma bada abinda za'aje nema cikin nasara.”

Ta fad'a tana wasa da yatsunta, shi kuma ya daga mata kai tare da yin d'an guntun murmushi, sannan ya shige ciki su kuma suka nufi inda zasu, Aliya sai dariya take tare da cewa.

“Gaskiya Fa'iza baki da aikin yi, kinji abinda kike cewa Shamsu kuwa? Wai Yaya! tsabar shishigi.”

“Na fad'a d'in ai dai ya girme mu nesa ba kusa ba, dan nace masa Yaya ai ya cancanta ne.”

“Ai sai kije kiyi ta fad'a, wahalalliya.”

Banza Fa'iza tayi da Aliya, Saboda taga alamar ‘kiyayar Shamsu a cikin zuciyar ta, dan haka ta canza musu hira, Saboda ita bata son taji ana aibata Shamsu a gaban ta, dan har sab'ani suka samu ita da gwaggo Talatuwa lokacin da aka yi rigimar nan, ta dinga surfa masa zagi da masifa kamar wadda ya dad'e yana yi mata laifi. Yana zuwa jakar kayan sa ya janyo, bayan ya b'oye kudin sa daya d'iba zai tafi dasu saboda halin rayuwa, ya samu su Umma a tsakar gida duk shi suke jira, yaya Garzali yace,

“Ka gama mu tafi ne?”

Shamsu ya kalli Ummansa wadda itama shi take kallo, idanun ta ne suka kad'a suka yi jawur alamar kuka yana gab da fitowa, yayi saurin ‘karasawa gurin ta tare da rungume ta, rabon da ya jisa a irin wannan yanayin har ya man ta domin tun lokacin daya fara balaga ta dena rungumesa, ko shine ya taho zai yi mata zata dakatar da shi tace bata san shashanci.

“Umma kodai na fasa tafiyar nan ne, wallahi bana so naganki cikin damuwa.?”

Umma ta share hawayen da suka gangaro saman kumatun ta, tana shafar kansa tace,

“A'a Shamsudden hawayen nan da ka gani basa nufin cewar bana son wannan tafiyar taka, a'a hasalima ni na fi kowa so ka tafi ilimi ai dad'i ne da shi.”

Ta fad'a ne kawai dan karya samu damuwa, daga nan suka d'auki trolly d'in. Abba da Garzali suka tasa shi a gaba yayin da Umma ta bisu da addu'a, gidan malam Rayya kawai yaje ya yiwa sallama suka tafi cike da fatan nasara. Suna zuwa suka tarar kowa yazo anata cike-ciken tafiya Abba suka yi masa sallama, babu jimawa jirgin su Shamsu ya tashi zuwa k'asar Switzerland, bakinsa cike da addu'a na samun abinda zaije nema.

•••• •••• ••••

Lokacin da mahaifin Fa'iza ya dawo gwaggo ta sanar dashi abinda ya faru, yayi mamaki matuka ganin yadda yake ganin nutsuwa da hankalin yaron, gwaggo Talatuwa ta dora da cewa.

“Shine dan tsabar rashin mutunci suka dauke shi suka kai shi can wata kasar saboda sunji nace idan ka dawo zansa ka dauki kwakkwaran mataki.”

Ransa ya sosu shima ya nuna b'acin ransa, ya tashi zaije suyi magana da mahaifin Shamsu Fa'iza ta lallab'a ta riga shi fita waje, a kofar gida ta tsayar dashi ta sanar masa da komai,jaddada kai yayi shi dama abin ya bashi mamaki amman dan kar gwaggo tace beji maganar ta ba sai yasa aka kira masa mahaifin Shamsu bayan yace da Fa'iza ta koma ciki. Koda Abban Shamsu ya fito hakuri suka bawa juna suka yi sallama cikin mutunci kasan cewar su maza ne masu hangen nesa, da ya koma gurin gwaggo Talatuwa kuwa cewa yayi.

“Naje munyi maganar da shi, Na ce masa kuma dole idan Shamsu yazo garin nan ya bawa Aliya hakuri idan ba haka ba zan had'ashi da 'yansanda.”

“Yauwa d'an albarka, shi yasa nace dasu ai idan ni sun raina ni bari kazo na gaya maka.'”

Shi dai ya samu suka rabu lafiya dan baya san b'acin ranta, mahaifiyarsa ce yasan gigin tsufa yana damunta.

Tunda Shamsu yabar k'asar mu ta Nigeria tamkar sake bud'ewar kan Aliya ne, sosai idanunta suka bud'e ta inda Sahal ya sakar mata bakin aljihu tana yin abinda taga dama, gwaggo kuwa tayi fad'an tayi masifar akan ta dena cusa kanta gurin yaron amman ina, shine yake kaita duk wani guri da zataje a motar gidan su.

Kamar kullum idan ta tashi daga makarantar boko, wanka take yi ta shirya tsab ko abincin gidan gwaggo ba taci, sai taje gidan su Sahal Husnah k'awarta zata d'ebo mata abinci mai rai da lafiya taci ta koshi, ta kwanta tayi kallo ko tayi bacci kafin saurayin nata yazo suyi ta fira. Yauma hakan ce ta faru Aliya tayi wanka ta shirya cikin wando da riga na sari blue ta yafa mayafin, Sahal ne ya bata su lokacin da Mamin su ta dawo daga India ta siyowa Husna amman ya dauke ya kaiwa Aliya sune take kare yawa dasu.

Tayi kyau sosai ta fito tana kallan Fa'iza, wacce ke shirin wanke uniform dinta, cikin yaudara da rainin hankali irin na Aliya tace da Fa'iza.

“Sister dan Allah ki had'a da nawa please.”

“Bazan iya ba gaskiya, ke kenan kullum ni zan dinga yi miki komai saboda kawai kinga ina shiru.”

Zuwa tayi ta rungumeta ta baya tare da sake marairaicewa tace.

“Kiyi mana yau ni kuma gobe zanyi mana dan Allah.”

“Mtswww !Jeki ‘dakko kuma wallahi ba dan halinki zanyi ba, ko dad'in bakin ki, dan nasan ‘karya kike ba wani yi min zaki yi ba goben.”

“Godiya nake sister 'yar uwata mai share min kuka na, kinsan me?kinfi gwaggo fa, saboda ita ta fiye fad'a.”

“Zaki ci ‘kaniyarki ne marar kunyar yarinya.”

Cewar gwaggo tana daga cikin d'aki ta jiyo abinda Aliyar ta fad'a.

Kayan ta kwaso ta kaiwa Fa'iza sannan tayi musu sallama tabar gidan, ga baki d'ayan su haushin ta suke ji, saboda yadda take cusa kanta cikin 'ya'yan masu farci nansusa, gashi ita ba 'yar kowa ba amman yadda take ji da kanta ko wad'anda suke cikin daula basu kaita ba. Tana shiga gidan Alhaji Tahir Abubakar wato mahaifin su Husna da Sahal ta tarar da Sahal zaune a wani gurin hutawa yana game, murmushi tayi kafin ta ‘karasa wajan da yake, kallanta yayi sannan ya dauke kai, ita kuma ta cire takalmin tata zauna kusa dashi kasan cewar akan babbar darduma yake.

“Zo kiyi game liya.'”(Aliya shine ya cire A din)

Dan lek'awa tayi taga irin ta ball d'in nance ta yatsina fuska tare da gyara zama tace.

“Ban iya wannan ba.”

“Taho nan toh na saka miki wani sai kiyi.”

Matsawa jikinsa tayi tamkar wata Husna wadda suke muharramai, sam babu wani tsoro ko jin kunya a tattare da ita kasan cewar shima ba wani abun bane a gurin sa hasalima 'yan gidan basu d'auki kusancin jinsin mace da namiji wad'anda ba muharramai ba a bakin komai ba, gani suke kamar wayewa ce, bayan kuma ko uwa daya uba d'aya kuke ba'a so ku fiye rab'ar junan ku, Saboda gujewa aikin shaid'an.

Karb'a tayi, tare da yin murmushi dan ba k'aramin jin dad'i take yi ba na kasan cewar su tare da Sahal, tana yi yana lalala mata suna dariya, saboda duniyar tayi musu dad'i, kamar daga sama sukaji ana cewa.

“Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Aliya kece kwance a jikin namiji? Lallai ma toh ki zo inji Abba (mahaifin Fa'iza) yazo yana nemanki gwaggo tace kina nan shine yace nazo na kiraki.”

D'an k'aramin tsaki Aliya tayi yayin da Sahal ya kafe Fa'iza da kallo, harara ta dank'ara masa ta juya tayi ficewar ta, tana mamakin wannan banzar ‘dabi’ar wadda Aliya ta daukarwa kanta, banda iskanci ta kwanta jikin namiji sai kace wani ubanta, gaskiya rayuwar Aliya da sake, domin zata iya b'ata musu ahalinsu. A k'ofar gate din gidan Aliya ta tarar da Fa'iza wadda take faman jiranta Sahal na biye da Aliyar, amman idanunsa suna kan Fa'iza, cikin jin haushin kallanta da yake yi yasa tace masa”

“Lafiya?”

Yace

“Kalau ma kuwa.”

“Okay! gani nayi ai kamar naci maka bashi ban biya ba, sai faman kallona kake yi

LKema ai kallona kike yi, idan ba haka ba taya ya kika san ina kallanki?l

Kallansu Aliya tayi ganin duk sun tsuke fuskoki, murmushi tayi tana rik'o hannun Fa'iza ta kalli Sahal,

“Dan Allah me yasa bakwai jituwa ne ha? Fa'iza ya kamata ki gane matsayin Sahal a waje na, kai ma ya kamata ka san matsayin Fa'iza naga kamar haushin junanku kuke ji, nasan dai dalilin Fa'iza na yin wannan abun amman kai ban san dalili ba, duka dai kuyi hakuri.”

“Kizo mu tafi ni ba surutu ko bayani nace ki tsaya muyi ba.”

Fa'iza ta fad'a tare da kwace hannunta daga cikin na Aliya tana yin gaba, Aliya ta kalli Sahal tare da yi masa murmushi tace.

“Kayi hakuri ya Sahal, Fa'iza tana da matsala sosai wallahi, gashi akwai k'arancin wayewa a tare da ita sorry please kaji?”

Yatsina fuska yayi tare da d'age kafad'a alamun ko ajikinsa ya koma cikin gida dama rakota yayi dan ya kuma d'ora idanunsa akan Fa'izar. Da sauri Aliya ta isa wajan Fa'iza cikin marairaicewa ta fara rokan ta, akan ta rufa mata asiri karta gayawa Baba Suleiman cewar ta zauna a kusa da namiji, Saboda idan yaji ba zai saurara mata ba dan lokacin da aka samu sab'anin nan ita da Shamsu yaja mata kunne sosai akan tayi takatsantsan idan ta sake biyewa wani namiji ko ta yiwa wani rashin kunya taje suka yi mata abinda zaizo yasa su yin kuka, ya sanar da ita cewar sai na lahira yafi ta jin dad'i.

“Dan Allah Fa'iza 'yar uwata karki gayawa Baba cewa na zauna a kusa da Sahal, wallahi daga yau ba zan sake ba.”

Cikin rashin yadda da abinda Aliyar ta fad'a, Fa'iza ta tab'e baki tasa hannu tana goge idanunta tare da cewa.

“Haka kike fad'a kullum idan kinyi laifi, toh yau dai kam sai na sanar da komai, dama wallahi na tsani Sahal d'in nan Saboda naga shi d'in mayan mata ne.”

____


_*WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER:MISS XOXO🧕🏼_
*_Littafinnan na kuɗine, zaka iya biyan 200 kacal kasameshi insha ALLAHU, a nemi wannan Numbers ɗin👇🏻._*
*_08030811300_*
*_07067124863_*


*G7/S*

*Switzerland*

*University of Zurich*

Jami’a ce mai d'auke da kusan d'alibai 25,500; The university of Zurich is the largest university in Switzerland, And lays claims to the country's largest selection of study programs.

*Department of international relations*

K'atan d'akin karatu ne mai d'auke da students 25, tsit kake ji, ko wanne yana zaune akan seat d'in sa ta yadda babu wanda zai takurawa wani, saboda tazarar da kowa yake da ita da d'an uwan sa. Seat na d'aya na biyu daga tsakiya, a na ukun seat d'in Shamsuddeen ne. (Shamsu) zaune da littafi da biro yana joting important abubuwan da lecturer d'in yake yi musu, bayani akan ilimin ‘Extradition Law’.

Lokaci zuwa lokaci yake ‘dan ‘daga kansa yana duban malamin, da a saqale a jikin rigar sa tag ne, dake ‘dauke da sunan; ‘Prof. Henry Potter’ ajikin allon rubutun ya rubuta, ‘Concept of extradition law:’ Cikin harshen turanci ya dubi ‘yan class ‘din kafin yace,

“Okay class rep! I will start with you... Get up and highlight the class on the concept of extradition law; A case study of Julian Assange’”

“Okay monita, zan fara da kai, tashi ka ‘karawa yan aji haske akan gundarin ma’anar extradition law. (Extradition law; wani ‘bangare ne na shari’a dake tattare ko ya ‘kunshi shari’ar shaye shaye/ rashin gaskia na zambo/ maula/ ‘ca-ca ko kuma safarar magunguna daga ‘kasa zuwa wata ‘kasar, da sauran su) ka ‘kara musu haske akan shari’ar Julian Assange( wani mutumi ne da America da ‘kasar Ecuador suke rigima akan sa, Saboda ya fitar da wani sirrii nasu a social media/ kafafen yad’a labarai na wayar salula da sauran su, Mutumin ya b’uya ne a Ecuadorian Embassy..)

Masu karatu kasa gano shamsu nayi, wanda sunan sa lokaci d’aya ya koma Shamsudden, Mikewa yayi, hakan yayi nuni da shine class rep/ monitan ajin. Sanye yake cikin ‘kananan kaya, riga da wando ya dora jacket akai , Murmushi Shamsudden yayi, kafin ya mike yana gyara collar rigar sa, cikin zazzakar muryar sa ya furta,

“Okay sir...The extradition process enables governments to bring fugitives abroad to justice, but it can be fraught with political tension, even when a treaty is in place...Extradition is the formal process of one state surrendering an individual to another state, for prosecution or punishment for crimes committed in the requesting country’s jurisdiction. It typically is enabled by a bilateral or multilateral treaty. Some states will extradite without a treaty, but those cases are rare.....,”

Nan ya shiga maganar Julian Assange, gaba d’aya ajin yai tsit suna sauraron sa, British English ne kawai ke tashi daga bakin Shamsudden, ba shamsu gaja na baya ba mai tireda, ya nayi yana daga hannuwan sa alamun bayani, sai da ya kai aya, malamin ya hau tafi shi da sauran d'aliban da ke zaune.

‘Kayataccen murmushi ne kwance a saman fuskar sa, ganin yadda kowa yake tafa masa, fuskar su cike da jin dad'in bayanin sa, hakan yasa shima yake binsu da nashi smiling d'in kasan cewar ance murmushi kan b'ata zuciyar mak'iyi. Komawa yayi ya zauna yana faman bud'e wani textbook dake ajiye a gefen sa, yayin da Prof Henry potter ya koma wajan white board yayi d'an rubutu tare da kallan 'yan hall d'in, yaci gaba da yi musu bayani dalla- dalla yana kuma fed'e musu karatun yadda zasu fahimta.

Sun jima ana fafatawa dama Shamsuddeen akawai k'ok'ari tun yana primary, shi kawai baya son ci gaba da karatu ne a da (back then)saboda yana ganin tamkar ba zai yi masa amfani ba, yanzu kuwa tunda ya baro gida yazo nan, babu abinda yake so fiye da karatun sa, musamman da kullum idan sunyi waya da Abban sa, zai ce masa ranar kaza an samu ribar naira kaza a shago, kajin sa kuma sunyi ‘kwai crate ‘dari biyu, tantabarun sa ansai aure hamsin. Duk lokacin da Abba yayi masa wannan albishir d'in hankalin Shamsuddeen kuma kwanciya yake yi, sai yayi ta harkokin sa hankali kwance.

*NIGERIA*

Rayuwa tayi musu dad'i, musamman yadda suka ga cikin ‘kankanin lokaci duk wani abu da Shamsu ya bari sunyi albarka, dan yanzu k'atan fili yaya Garzali ya siya aka gina wa Shamsu gurin kiwon kaji da kifaye na ‘catfish’s. gashi ‘kato, Kajin masu ‘kwai da marassa ‘kwai , shagon sa kuwa yanzu sai sam barka, domin yayi cikar da sai dai azo ayi sari a cikin sa, sosai Allah yayi masa albarka a ciki.

Khadija yarinya ce 'yar kawar Umman Shamsu, itace yarinyar da Umma take burin idan Shamsu ya dawo ya aure ta, Saboda nutsuwarta da yadda suke
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment